Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta sauko ta nufi kitchen dan tasan Ummi na can, a can kuwa ta same ta har kasa ta durkusa ta gaishe da Ummi tana dan jin kunya, Ummi amsa tana fadin
"Har kin tashi."

"Eh Ummi kawai nai aiki."
"A'ah barshi kije ki huta."

"Ummi please ni da na tashi yanzu."
Ta karasa tana taya ta aikin. Suna kitchen Haidar karami ya shigo yana ganin Maryam ya karasa ya rumgume ta yace
"Adda anan kika kwana?"
Ta daga sa da kyar tana fadin
"Yaro nan ya kara nauyi ai ban kara daukar ka."

Ummi tace
"Daman ai tin bai kai haka ba kike cewa yana da nauyi."
"Allah Ummi na zata da wasa Yaa Haidar yake, yace Haidar ya fini nauyi."

"Inji shi Aliyun?"
Sai da Ummi tai tambayar sannan ta tina abinda ta fada da sauri ta dauke Haidar suka fice tana fadin
"Bari muje wajen Inna."

A compound suka hadu da Yaa Haidar, Haidar ya sauka a hannun Maryam dake tafiya tana nishi ya rumgume Yaa Aliyu yace
"Morning Abbi."
"Morning my son ka tashi lafiya."
Kai ya gyada, ya juya yana kallon Maryam ta karasa tace
"Ina kwana."

Ba tare da jin kunyar Haidar ko tsoron wani ya gansu a haka ba ya janyo ta jikin sa yana kissing wuya ta yace
"Haka kika saba gaishe ni?"
Janye jikin ta tayi tace
"Haidar dai na nan."

Ya kara janyo ta yace
"Ba ruwan yaro na."
Ya kalli Haidar yace
"Maza muje wajen Inna."

Haidar yai gaba, Aliyu kuma ya dan rakwafo ya kama bakin Maryam yana kissing nata, sannan ya saketa ya kama hannun nata sukai bangaren Inna. A kitchen suka jiyo ta ita da Haidar suna ta magana Maryam ta sa murmushi ta nufi kitchen din tana fadin
"Me Hajiya Inna take girka mana?"

"Ai jiya ina ta zuba ido na zata anan zaki kwana?"
"Bacci ne ya dauke ni da wuri."

"Kaji Inna ga mijin ta sai ta taho wajen ki."
"Ni dai ban maka magana ba ah toh."

"Haba Hajiya Inna uwar gida na nifa da wasa nake miki."
Baki ta tabe ya karasa ya kama hannun ta yana fadin
"Ni dai mu shirya mu daina fadan nan."

Taja kunnen sa da karfi ya rike hannun yana fadin
"Baby zata ciren kunne na."
Maryam da Haidar karami na dariya sukace
"Inna kiyi hakuri."
Ta saki kunnen tana fadin
"Ai dan na huce abinda yai min ne kan na hakura."

Suka fito daga kitchen din gaba daya da kayan da ta hada anan suka zauna, Yaa Haidar ya zuba uwar madara a cup ya hadawa Maryam ya dauka zai hada ta dauke madarar tace
"Wacce ka kawon ta kare ba ita bace wannan."

"Haba Hajiya Inna, ai sai ki magana a dado amman ni yanzu ba za a barni na sha ba ai da yake yar lallen ki ce Maryam kin bari na zuba mata."
"Cokali daya zaka zuba."

"Gaskiya tai min kadan."
Ta zuba masa biyu, ta dauke madarar tana gani Maryam ta mika mata nasa amman sai yaki amsa dauka tayi ta hade musu ta raba sannan suka karya gaba dagan su suna hira da wasa da dariya, Inna na lura da Aliyu abu kadai ya kalle ta ya aika mata da wani kallo, Maryam dai sai basarwa take. Daga baya ta tafi ta barsu a wajen inna.


Babyn Najwa taci suna Mami suke kiran ta da Zuhrah, ansha suna sosai akai taron suna inda gidan da yamma ya cika dan anyi walima, ranar ma gaba daya bata ga Yaa Haidar ba tin safe sai karfe biyar da rabi ya dawo lokacin suna conpound ya shigo yai parking, ba inda idon sa ya fara sauka sai akan matar sa, ya lumshe ido dan wani kyau yaga tai masa sanye take cikin wani amry green less wanda akaiwa ado da dark pink yai mata kyau tasa dan kunne da sarka da abin hannu ba tai make up ba amman tai kyau sosai kana ganin ta kaga wacce hutu da jin dadi ya zauna mata ta murje tai kyau fatar ta tai fresh.

A hankali ya bude murfin motar ya fito yana kara kallon inda suke ita dasu Yaya Asiya da Hanna da Bilkisu ne sai hira suke abin sha'awa basu san da dawowar su ba sai ganin sa kawai sukai ya karaso wajen ya nufi wajen da Naryam take, dagowar da za tai suka hada ido kai ta girgiza masa, dan tasan yanzu zai ce zai kamata ai kuwa bata sauke idon ta ba taji ya kamo hannun ta ya dago ta tare da hada ta da jikin sa yana mata magana kasa kasa.

Fuska ta shagwabe kamar zatai kuka tace
"Yaya da fa mutane."
"Ina ruwa na ni dai matata kawai nake bukata, ke haka ake? Ace dan kin samu yan uwa sai ki manta da mijin ki Allah in haka ne zan na hanaki zuwa taro."

"Haba Yaya kayi hakuri kaji."
"Muje ki tayani yin wanka naci abinci ko?"

Fuska ta marairaice ya fara janta, Anty Asiya tace
"Yaya ai ma gaisa ko?"
Anty Hanna dake rike da waya tana daukar Maryam da Yaa Haidar tace
"Masha Allah! Perfect Match Yaya."

Ya kalli Maryam yana sakin murnushi wanda hakan ya kara sawa su daukar shi a hoton, sannan suka gaishe shi yaja Maryam sukai bangaren Ummi ta baya saboda yadda mutane ke cikin compound din gidan.

Suna barin wajen Ummi tazo tace
"Ina daughter?"
"Yanzu Yaya ya dawo ya dauke ta."

"Oh Dr yanzu ana taron ma ba zai barta cikin yan uwan ta ba."
Ta girgiza kai ta bar wajen.

Anty Hanna tace
"Kinga yadda karamar yarinya ta dauke hankalin Babban mutum kamar Yaya."

Anty Asiya tace
"Ni wannan miskilancin da daure fuskar kai duk babu shi."
"Ke kuwa ina zai yi su ya samu yar yarinya yana kwasar dadin sa."
Anty Bilkisu ta fada.

"Ai naji dadi wallahi Allah ya kara basu zaman lafiya ya basu zuri'a mai albarka amman sun dace da juna sosai."
"Kinga fa picturen nan dan Allah kalle su, kamar wanda akayi su dan juna."
Hanna ta fada tana nuna pictures da tai snapping nasu, amsa sukai suna gani kan kace me duk sun tura suna yaba yadda suka dace da juna.


Maryam kuwa sanin Yaa Haidar bai cin abincin taro yasa tin rana ta hada masa nasa ta kai dakin sa, ita ta taimaka masa yai wanka sannan ta fito gabatar masa da abinci sai da ya ci ya sha sannan ya lallalube ta da kyar ya barta ta tafi cikin yan uwan nata.



2 month later
Bikin Rukky wanda ya rage kwanaki biyar, zaune take a jikin sa sai shagwaba take masa akan tafiyar tata dan Aisha tini suna Kano, dago ta yayi yace
"Menene kuma Baby?"
"Honey dan Allah ka bari gobe mu tafi da Najwa."

"In kinje kuma ki kwana nawa?"
"Sati biyu, kaga fa Yaya tinda muka tare banje gida ba wajen wata shida."
Ta fada tana shigewa jikin sa tare da bashi wani irin kiss, ido ya lumshe yana amsar abinda take masa.

Sai da ta saki bakin nasa ya saki wani numfashi tare da fadin
"Yanzu a haka kike so na barki ki tafi Baby wa zai na kula dani."

"Yaya please please!"
Rumgume ta yayi yana fadin
"Baby zan duba."

Jikin sa ta kara shigewa tana kara rikitashi da salon ta, sai da ta gama rikirkita shi sannan ta kara maimaita bukatar ta, bai san lokacin da ya amince mata ba.

Sai daga baya bayan ya dawo hayyacin sa da dare ya ganta tana hada babban akwati da karami, zama yayi yana kallon ta yace
"Duk kayan nan fa?"
Kamar zatai kuka tace
'Na tafiya man."

Yai murmushi yace
'Menene na kukan to?"
"To ai nasan halin ka, Yaya har da Jawahir fa kuma duk danni zamu tafi amman kai kana son ka hanani zuwa haba Yaya na."

"So nayi ana gobe daurin aure sai mu tafi."
"Amman Yaya ai an gama event kuma na fada maka dalili na wata shida banga Ammi na ba."
Sai ga hawaye na bin kuncin ta da sauri ya karaso yace
"Nifa bance a'ah ba."
Rumgume ta yayi yana lallashin ta.


*
Bayan ya tafi masallaci ya nufi gidan Ummi, a dakin ta ya same ta akan sallaya ya karasa ya zauna ta shafa addu'a tana fadin
"Ina ka baro daughter ka fito da daren nan?"
"Tana gida sai rigima take."

"Rigima kuma?"
"Eh wai sai ta tafi Kano Ummi."

"Haba Aliyu saboda me to ba zatan ba? Bikin kawar tane fa bama wannan ba wata wajen bakwai da tarewar ku fa amman bataje gida ba haba Aliyu ka barta taje kwana nawa take so?"
"Sati biyu fa Ummi ai yayi yawa."

"Aliyu kana dagawa yarinyar nan kafa fa, kullum kuna tare dan taje taga iyayen ta na sati biyu shine zakace a'ah kuma naga kaima nan da kwana hudu zakabi ta uhm."
"To Ummi shikenan goben sai suje."

"Yauwah Allah maka albarka, sai su tafi tare da Haidar zan hada masa kayan sa shima yaga yan uwan sa."
"To Ummi bari naje naji ana kiran sallah, da daga can zan tafi gida."

"Allah bamu alheri agaishe min da ita."
"Zata ji."
Ya fada yana mikewa ya fita.


*
Washe gari kamar ba zasu rabu da juna ba makale da juna suka yini har lokacin da ya fito dan kawosu gida daga nan su tafi airport bayan sun shiga taje taiwa Mami da Inna sallama, bangaren Ummi ta shiga sukai sallama sannan suka tafi tare da Haidar dake ta dagawa Ummi hannu.

A airport suka hadu da Jawahir da Najwa bayan Haidar ya fita ya jata jikin sa yana kissing nata sannan ya sake ta yace
"Zanyi kewar ki."

"Nima yaya i love."
"Love u more."
Sannan suka fito hannun ta rike da nashi haka da suka karasa da kyar suka rabu, sai da yaga tashin su sannan ya koma asibiti.

Suna sauka ta kira ta fada masa, wanda Yaa Abdullah yazo daukar ta, har suka karasa gida waya suke da Yaa Aliyu sai da suka shiga falo sannan sukai sallama ta rumgume Ammi tana fadin
"Ammi nah i miss you."
"Dan Allah jibe ki kin fa girma kalli Haidar"
Yaa Abdullah ya fada

"Ina ruwa na ni."
Ammi tai murmushi tanawa su Najwa da Jawahir sannu da zuwa tare da amsar Zuhrah, nan aka kawo musu kayan abinci sai da sukaci sukai nak sannan Aisha ta shigo da Babyn ta wanda shima yayi wayoo.

Ranar sunga gata a gidan wajen matan yayen Maryam, komai suka kwaso su Maryam, haka komai in za ai sai an tambaye su me za ai musu ma suke so. Yaa haidar kuwa baya minti goma bai kira Maryam ba haka suka kusan kwana ido biyu suna hira a waya, haka washe gari ma suna zaune gaba daya zai kira dole sai ta bar wajen dan sai su dauki wajen awa suna abu daya.

Sunje gidan su Rukayya wanda ake ta shirye shirye Yaa Ahmad ma har gida yazo yaga Haidar suka gaisa dasu Maryam. Aisha ce ta dauko musu mai kunshi akai musu lalle da gyaran kai.

Haka akai kamu da dinner wanda Yaa Haidar ya iso ranar juma'a dan asabar za a daura aure, Ammi da kan ta ta shirya masa abinci dan ranar da ya iso su Maryam suna can gidan su Jawahir ana arabi'an night, sai wajen karfe tara da wani abu suka karaso gidan wanda tana fitowa wayar ta na daukar kara, dauka tayi tana ganin mai kiran, kunnen ta takai tana fadin
"Yaya na ka iso ne?"

"Na iso yaushe zaku dawo?"
Dai dai shigar ta bangaren su tace
"Gamu mun dawo yanzu. Kaci abinci?"

"Ammi ta kula da d'anta sosai."
Murnushi tayi tace
"Masha Allah yanzu sai ka kwanta ka huta ko?"

"Wane irin na kwanta na huta ina jiran matata yanzun nan."
"Yaya....."

"Shittt bana son jin komai kizo kinji kema kinsan nayi kewar ki."
"To ina zuwa."

Ta shiga falon inda suka samu Ammi zaune ta kalle su tace
"Yan biki kun dawo?"
"Wallahi Ammi, ai wai sai mun kwana acan to ita Marham mai gida zai zo ina taga ta kwana."

"Kai Najwa Yayan ya zo ne?"
"Kaji mata yanzu fa kuka gama waya."
Mikewa tai ta fira tana fadin
"Wallahi zan rama ne."

Ta nufi sashen Yaa Abdullah da nan ta gyara masa tin jiya dan yafi sakewa tin da shi yaki yai aure.


*Allah ya jikan mu yai mana rahma Amin.*





*Antty*
[12/12, 19:36] Maryam S IndabawaπŸ₯°: ο»ΏπŸ’—πŸ’— *MATAR HAIDAR* πŸ’—πŸ’—
Page 86

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


Yana zaune a falo sanye da dogon wando da riga mai gajeren hannu wacce akai layi-layin fari, ja da ba'ki, sai kamshi yake kamar ka dauke shi ka gudu kwana biyu da tayi bata ganshi ba kawai sai taga ya kara kyau, itama gani yai ta kara kyau da haske sanye take cikin doguwar riga pink kala wacce duk jikin ta stone ne tai kyau sai walwali take, hannu ya bude mata ta karasa ta fada jikin sa tana sakin murmushi tare da kissing nasa a kumatu, ya dago kan ta ya hade bakin su yana bata wata irin sumbata wacce ta nuna mata yayi kewar ta sosai da sosai.

Daga nan wasan ya canja salo, sai da suka samu nutsuwa sannan ya fara fadin yadda yai missing nata, tana jikin sa har wajen sha daya ta mke tace zata tafi, yadda ya marairaice mata yasa ta zauna lallashin sa, wanda Aliyu ya kara cika ta da salon sa tafiyar da batai ba kenan sai kwanan sashen.

Ai kuwa asubar fari yana tafiya masallaci itama ta koma bangaren su, sallah tayi sannan ta shiga kitchen dan haka musu breakfast. Bayan ta gama tai wanka ta debi nashi ta nufi bangaren sa, yana zaune akan kujera hannun sa rike da waya ta shiga ya amsa sallamar yana kallon ta har ta karaso sanye take da doguwar rigar atamfa tai mata kyau ta ajiye tray din aka stool din dake dakin ta karasa ta zauna akan cinyar sa tare da tallafo kansa tace
"Morning Honey."

Tare da kissing lips din sa, lips din nata ya kama ya dan tsotsa sannan yace
"Morning too My Noor."
Ya bi ta da wani kallo yace
"Ina Haidar?"

"Yana can bangaren Yaa Muhammad."
"Uhmm yaga yan uwa."
Ta saki murmushi ta mike tare da nufar kayan da ta shigo dashi, kunun gyadan da tai masa ya sha madara ta mika masa ya amsa tare da janyo ta jikinsa yana bata tana sha shima yana sha a haka suka shanye ya fara bata dankalin da ta soya masa sai da suka gama sannan tace
"Yaya yanzu fa zamu tafi?"

"Karfe nawa ne daurin auren da zaku tafi yanzu?"
"Sauran awa daya fa Yaya gwara muje da wuri so tayi mu kwana fa."

"Amara kenan."
Tai murmush tace
"Bari muje mu shirya."

Ta masa kiss ta fice, kaya ta canja ta saka wata Sky blue din shadda wacce ta sha aiki da stone ja sosai tai kyau ta dauki half covern takalmin ta, da jan mayafi ta saka dan kunne da sarka na mai red stone sosai tayi kyau kamar ka dauke ka gudu da ita ta fito tare dasu Najwa da Jawahir, Yaa Alkasim ne zai kaisu, Yaa Abdullah ya bawa Aliyu mukullin dayar motar gidan nasu, wanda ya dauki Maryam da Jawahir, Aisha da Najwa kuna suna motar Yaa Alkasim sai da suka ajiye su sannan suka tafi wajen durin auren.

Bayan an daura aure da yamma akai yini inda dukkan su suka saka ankon atamfar da akayi sunyi kyau abinsu, karfe biyar aka kai amarya gidan ta inda aka bar su Maryam a wajen ta, sai da ango yazo sannan su Yaa Alkasim da suka rako su sukai tafi da matan su.

Yau ma dauke matar sa yayi sukai bangaren Yaa Abdullah acan suka kwana sai washe gari ta koma wajen su suka shirya wajen sha biyu suka tafi gidan Rukayya. Kwanan su Najwa bakwai suka tafi suka bar Maryam dan sai ta kara yin sati daya wanda shi kuma Yaa Aliyu kwana biyu yayi ya tafi ya barta.


Bayan tafiyar su kuma sai ta fara zazzabi, da wani irin ciwon kai, da yamma bayan sun dawo daga gidan Mami ita da Haidar kaami suna zaune a falo, yace
"Adda Ummi ita ce maman Abbi, ita kuma Mami maman Abbi na da ya mutu ko?"

Hannu ta saka tana shafa sumar kansa tace
"Eh Habiby."
"Adda da Ummi da Ammi wacece Ammin ki?"

Murmushi tayi tace
"Duk Ammi nane, amman Ammi ita ta haife ni."
Kai ya gyada, yace
"Adda, su Momy fa?"
Yana nufin su Yaya Fadima, tace
"Yayye nane."

"To Adda su Momyn Abuja fa?"
Tai murmushi tace
"Suma Yayye nane."

Dagowa yayi yace
"Adda su Abbi na na nan gidan fa?"
Dariya tayi tace
"Suma dukka haka."

"Adda kina da yan uwa da yawa."
"Kai ma haka my son."
Murmushi yayi ta rumgume shi a haka, Ammi ta shigo ta same su, ita kan ta da ta gansu sai da ta tina da Yaa Haidar da yana raye da kila suna da ya'ya wajen nawa, da yana raye da suna tare dashi, ba abinda zasuyi masa sai addu'a Allah jikan sa ya kyautata namu zuwan, Amin.

Gidan yan uwan ta ta fara ziyarta tare da Haidar, taje gidan Yaya Ummulkairi, da Yaya Rukayya, a gida Yaya Fadima da taje yiwa kwana daya ciwon nata ya fara zafi, wani dare suna zaune suna hira, Maryam take fadawa Yaya Fadima yadda Yaa Aliyu baya son ta matsa ko nan da can. Yaya Fadima cikin jin dadi tace
"Ni daman na sani a sannu zaku so junan ku, wallahi kun dace da Aliyu kuma nasan ba wanda zai samu 'kanwata yaki ta."

"Ah ah fa Yaya Fadima banda cika baki."
"Ai nasan wacece 'kanwata shiyasa, kada ki damu tsananin son kine yasa haka ke dai ki kula da mijin da fatan kina abinda nace kina yi?"

"Eh Yaya Fadima ina yi kuma ina jin dadin sa, Yaya Fadima Humran nan ta kare kuma naga Honey yana son ta."
"Ai na fada miki Humra na da kyau kada ki damu kan ki tafi za kawo miki, dan Allah Maryam na san ki da tsafta da gayu da son turare ki daure ki cigaba kinji."

"Insha Allahu Yaya Fadima ina godiya sosai dan in kika sani abu nayi ni kadai nasan albarkar da nake sha a ranar."
Tai murmushi tace
"Ki rike mijin ki da yan uwan sa, kinga yadda suma suke son ki kada ki soma kin nasa, ki na sashi yana taimaka masu ba wai yan uwan ki kadai ba dan Abbi yace duk wata sai yayo masa aike."

Ido Maryam ta zaro tace
"Ikon Allah wallahi Yaya fadima ban sani ba sai dai Abbi yace nai masa godiya ko naji suna waya yana fadin ai shima mahaifin sa ne ya daina godiya da makamantan su, in na tambaye shi ma sai yace ina ruwa na shima Abbin sa ne."

Sukai murmushi, Yaya Fadima tace
"Bawan Allah kenan, Allah ya barku tare ya baku zuri'a ta gari."
"Amin Yaya Fadima."

"In kina da matsala kar kiji nauyin na ki sanar min kinji Autah."
Tai dariya tace
"Wallahi har nayi missing diin ku Yaya Fadima, sai kika tino min da Yaa Haidar."

"Allah masa rahma."
"Amin."

Haka ta cigaba da zama da yayar tata wanda zazzabin kamar wasa sai ga Maryam har da kwanciyya a asibiti dan yadda ciwon kan ya matsa mata bayan sun mata aune aune ne suka gano cikin dake jikin ta wanda bai kai watanni biyu bama, zo kuga murna wajen yan uwan ta, abinda aka kasayi a cikin Haidar kenan, Yaa Aliyu dake can Abuja hankalin sa ba karamin tashi yayi ba da ya kira wayar tata akace masa tana bacci saboda jikin nata, dan tin da ta fara zazzabin shi ya rubutowa Yaa Alkasim Maganin ya siyo mata amman sai abun ya kara yin gaba, wanda yau tin safe yake kiran ta Yaya Fadima tace suna asibiti bacci take yi.

Gida ya koma ya fadawa Ummi abinda ke faruwa, Ummi ta kalle shi yadda duk ya damu tace
"To menene na damuwar Dr?"
"Ummi yau ban san a halin da take ba sam ban ji murtar ta ba. Please ki kira Ammi nasan zata fada miki komai."

"Shikenan bari na kira tan."
Ta dauki waya ta kira Ammi bayan sun gaisa ne Ummi tace
"Ashe daughter ce ba lafiya."

"Uhmm ai ciwon na karuwa ne Ummin Maryam, da akai mata test dai sai ya nuna tana dauke da ciki."
"Ah Masha Allah! Alhandulillah Allah raba lafiya."

"Amin Yaa Allah, ai mata sannu in tashi zan kira sai na duba jikin nata."
"To Ummi mungode."
Sukai sallana, Yaa Haidar da ya zuba mata ido yana son tai masa bayani ta kalla tace
"Ka zuban ido."

Zama yayi yace
"Me ya faru Ummi naji kina Allah raba lafiya, ba dai ciki ne da Baby ba?"
Hararar sa tayi tace
"Ni kake cewa Baby a gaba na ko?"

Baki ya danne da hannu ya dariya dan ba yau ya fara ba yau ne dai ta magantu, yana dariya yace
"Ni dai Ummi please ki fada min."
"To mun samu karuwa, jika na yana wahalamin da Babyn ka."

Ido ya zaro yana fadin
"Please Ummi da gaske?"
Dariya tayi tace
"Sure."

Ummi ya rumgume yana fadin
"Alhamdulillah!"
Sai hawaye, Ummi ta kama hannun sa tace
"To menene na kukan?"

"Ummi ki tayani addu'a Allah ya bata lafiya ya sauke ta lafiya, ina son nima naga jini na Ummi ina son naga jini nan Ummi."
"Insha Allahu zakaga jinin ka har ma tattaba kunne Aliyu."

"Allah yasa Ummi."
"Amin."

"Gobe zani Kanon Ummi."
"Ai tare zamu na dubo ta."

"Yauwah Ummi na sai muga jikin in da hali sai mu taho gaba d'aya ko?"
"A'ah fa Aliyu kada ka matsa mata dan Allah ka barta kawai in tawarware sai ta dawo, ni dai yaro na kawai zan dauko saboda makaranta."

"To Ummi ita kuma nata karatun fa, kina gani sauran wata daya su fara exam fa."
"Insha Allahu zata ji sauki kan lokacin."

"Ina tsoro kada ta sha wahala kamar yadda ta sha a cikin Haidar."
"Insha Allahu wannan zai zo mata da sauki."

"Allah ya yadda."
"Amin."


*
Washe gari da yamma suka sauka a Kano, a gidan su Ammi suka sauka sai da sukaci abinci Yaa Alkasim ya kai su asibitin, Maryam tana bacci suka shiga bayan sun gaisa da su Ammi da Yaya Fadima suka dan fita suka basu waje, suna fita Yaa Haidar ya matsa wajen gadon yana kallon yadda ta dan fada, hannu yasa ya shafi wuyan ta, a hankali ta bude idon ta, tana ganin Yaa Haidar ta saki murmushi tana fadin
"Yaya."

Zama yayi yana kama hannun ta yace
"Ya jikin Baby?"
Baki ta tabe kamar zatai kuka tace
"Yaya kai na shi yake damuna."

Hannu ya daura akan nata yana fadin
"Sannu kinji Allah sauwake."
Kai ta tace
"Ya hanya ina Ummin?"

"Suna waje ita da Ammi? Me kike so?"
Kai ta girgiza tace
"Ba komai Yaya baki na duk ba dadi."

"Sannu kinji?"
Kai ta gyada ya zura hannun sa cikin rigar ta ya daura a kasan marar ta yana shafa wajen a hankali a hankali, ido ta lumshe tana jin kewar mijin nata, daya hannun ya daura akan ta yana shafa kan nata, a haka Ummi da Ammi suka shigo har da Mami da zuwan ta kenan wannan yasa Aliyu ya tashi da sauri ya gaishe da Mami tare da fita ya barsu a wajen ta, jikin Ummi ta lafe tana zuba mata shagwaba, Ummi na ta biye mata, sosai Mami da Ammi abun ya burge su suka kara yabawa Ummi na yadda take son Maryam.

A haka sukai kwana biyu wanda Ummi ce ke kwana a wajen Maryam sam ta hana Ammi da Yaya Fadima sai dai su zo, Yaa Aliyu ma sai kula yake da matar sa, dan dakin aka bar musu in ba wani ne yazo dubata ba suna makale da juna, ranar da sukai kwana biyu aka sallamo su suka kom gida, washe gari suka daga da Haidar Karami saboda makaranta, haka ta cigaba da jinya wanda sai da tai sati hudu a Kano sannan ta koma gida wanda shima ba gama warwarewa tayi ba, anan gidan Ummi suka cigaba da rainon cikin ta wanda a haka da kyar take zuwa makaranta, wani abun ma sai ta dawo Yaa Haidar yake kowa mata, satin ta uku da dawowa suka fara jarabawa wanda a lokacin aka kai kudin auren Yaa Farouk da Jawahir.

Da kyar a haka yau lafiya gobe babu suka gama jatabawa wanda a lokacin bikin Jawahir saura sati uku, wanda yai dai dai da cikar cikin Maryam wata uku, ba laulayin nan sam sai kwadayi kuma, ganin ta murmure yasa Yaa Haidar ya dauke matar sa suka koma gidan su da mai aikin Ummi dan Yaa Haidar yace sai ita in ba ita ba baya son wata mai aiki.

Satin su biyu da komawa gida aka fara bikin Jawahir inda suka sha shagali har Rukkayya sai da tazo itama da cikin ta wata biyu, Maryam na mata tsiya tace
"Daman nace tare zamu sauke."

A lokacin bikin su Momy da Basma suka zo har da su Tasleem, wacce itama an sa mata ranar auren ta amman son Aliyu na nan cikin zuciyar ta, a dinner suka hadu lokacin zuwan

Please Login or Register in order to submit comment