Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta fita, kurawa kayan abincin ido yayi daga karshe saboda yasan halin Momy in bai ci ba da kanta zata zo ta tsaya har sai yaci wannan yasa ya dauki dan fulas din dake kan tray din ya tsiyaya tea din a cup, bai saka komai ba sai dan sugar ya dauka ya fara sha, yana gamawa ya mike ya shiga toilet ya jima a ciki ya fito yana kara tsane jikin sa da alama wanka ya karayi, kan gado yazo ya kwanta amman me sam bacci yaki ya dauke shi sai juyi ya dinga yi, abubuwa na damun sa ganin ba baccin zai ba yasa ya mike ya shiga ya dauro alwala akan sallaya ya kwana yana addu'a.


*
Washe gari Ummi ta samu Abba tai masa bayani kai ya dafe yana fadin
"Wallahi Aisha na sha'afa sam saboda mantawa nake da Maryam ba 'yata bace amman insha Allahu zan kira yaro sai nai masa bayani in yaga yana son ta a haka shikenan Allah yasa mu dace."

"Amin nima na damu bana son damuwar ta gaba daya."
"Insha Allahu komai zai tafi normal."
Kan Abba ya fita ya kira Muhammad yace yazo da dare in ya dawo daga aiki.


Haidar ne ya tashi Maryam da safe yana fadin
"Adda cornflask zan sha kinji Adda."
Ido ta bude tana kallon sa tace
"Ina Ummi?"

"Ta fita aiki?"
"Bakai breakfast bane?"

"Nasha tea ni cornflask zan dada."
"Ai Iyya na kitchen dan Allah jeka ta hada maka."

Ta fada tana dafe kan ta dan har lokacin ciwo yake, baki ya turo kamar zai kuka yace
"Adda nata ba dadi na Abbi na yafi, Adda ki kira min Abbi ya hada min."

Kai ta dafe tana fadin
"Ni muje na hada maka."
Ta mike ta fita har ya kai kofa yaji wayar ta na kara komawa yai ya dauka ya fita a guje yana cewa
"Adda ana kira."

Bata falo har ta sauka dan haka ya bita kitchen tana hada masa madara ya karasa ya mika mata yace
"Adda ana ta kira."
Amsa tayi tana kallon screem din ganin sunan Yaa Aliyu yasa ta zubawa screen din ido tabbas itama tana son taji ya ya sauka tinda bata samu ta tambayi Ummi ba. Wayar ce ta kara yin kara ta duba da sauri ta dauka ta kai kunnen ta, sai dai ta kasa furta komai, sallama yai mata cikin muryar sa mai dadi da sanyi wacce take kwantar da hankalin mai sauraron ta ido ta lumshe tana amsawa a kasan makoshi tare da yin shiru.

Aliyu dake kwance yace
"Tinda baki iya gaisuwa ba bani yaro na."
Duburburcewa tayi tace
"A'ah Yaya ina kwana? Ya ka sauka? Da fatan ka sauka lafiya?"

"Alhamdulillah ina Haidar!"
Haidar dake zaune a dining ta kalla tace
"Gashi nan."

"Ok bashi wayar."
Mika masa tayi tana fadin
"Ga Abbin naka."

Ya amsa ya kai kunne yace
"Abbi ina kwana?"
"Lafiya lou My son ya kake?"

Ya fada yana jingina da kujera.
"Alhamdulillah Abbi."
"Masha Allah me kake yi?"

"Abbi, Cornflask Ummi ta hada min nake sha."
"Iyyee dan gatan Adda, na kira Ummi mu gaisa tace ta fita."

"Yes Abbi."
Maryam fita tayi daga kitchen din, Aliyu yace
"Ina Addar taka?"

"Ta fita Abbi."
"Ok zan fita yanzu in na dawo zan kiraka kaji."

"To Abbi yaushe zaka dawo."
Dan murmushi yayi yace
"Haidar kenan jiya fa na tafi zan dan jima ban dawo ba, ina son ka maida hankali a school sosai da sosai kaji?"

Kai ya gyada yace
"Insha Allah Abbi."
"That is my good boy Allah maka albarka."

"Amin Abbi."
Yace
"Ok bye ka gaida Inna da Mami."

"To Abbi, bari naje na fada musu."
Ya cire wayar a kunne ya karasa falo inda Maryam ke kwance ya mika mata waya, yana bata yace
"Zanje wajen Inna da Mami Abbi ya aike."

"To agaishe su."
Ya fita da gudu, Maryam ta maida ido ta kwanta.


Yini tayi tana bin waje tana kwanciyya, har Ummi ta dawo yace
"Maryam jikin ne?"

Kai ta girgiza tace
"Bana jin dadin jiki nane."
"Munyi waya da Aliyu likita zai zo ya dubaki yanzu."

"Ummi ni naji sauki fa."
"Daman tinda bakya son magani ba, kuma Allah yazo ya duba sai kinsha magani."

Baki ta turo ta koma ta kwanta kawai, Ummi ta mike ta wuce sama tana fadin
"Ki gama turo bakin ki, dan Aliyu baya nan ba zan zauna dake ina ganin ki, kina ciwo ba."




Flash Back
July 2017
Kano State







*Allah ka yafe mana kasa muyi kyakyawan karshe Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum*




*Antty*

💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 13

By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW


*Bismillahir Rahmanir Rahmin*



~Flash Back~
```July 2017
Kano State```

```*MANS GIRLS COLLAGE* shine sunan dake rubuce a saman wani katon gini wanda aka kwata shi rubutun kan sa abun kalla ne, banda ginin da yake katon gaske wanda ginin mai kyau ne, da tsari dan ba dan an rubuta makaranta ba da ba zakace makaranta bane dan kyau da tsarin ginin, wanda yake da bene har wajen hawa uku. Wanda makarantar tai fice a cikin garin Kano da kewaye duk wani d'an wane wato masu kudi, yan siyasa, da masu mulki, da wanda ke ji da kansa nan ba wai dan tsadar makarantar ba a'ah sai dan yadda makaranta take da manyan kuma kwararrun malamai. Dan malaman duk kan su kwararrun ne kuma suma dan suna samun salary mai kyau shiyasa suke kara zama a wajen duk da wasu suna aikin gwamnati kuma suke kara zuwa suna aiki a wajen.

Da ka shiga babban gate din babban harabar (compound) wanda yake dauke da wajen adana motoci (parking space) an saka masa rumfa an kwawata harabar wajen (compound) da shuke shuke, wanda har wani round about akai a tsakiyar makarantar an rubuta sunan makarantar da manyan baki kuma an kwatashi. Duk ka makarantar an malaleta da kwalta wajen yayi kyau, kato ne sosai dan in anzo ziyara (visiting) din dalibai duk anan ake ajiye motoci (parking) duk yawan mutane wato iyayen yaran da zasu zo wannan harabar (compound) din na dauke su kamar yadda yau yake ma cike da manyan motaci masu kyau, tsada duk ka dai saboda yau dalibai makaranta ake yaye su (graduation) wanda duk iyaye suka zo daukar yaran su.

Ba motar da ta karewa kowa in zai fita duk da wajen ba kowa sai d'ai d'ai kun drivers sauran ma kuwa duk suna cikin mota iyayen kuma suna can cikin makarantar. Wanda bayan wannan harabar (compound) din akwai wani a ciki wanda anan bangaren malamai yake da ajujiwa (classes) din daliban makarantar shima wannan compound din an kwata shi sosai dan har filin (wasanni) sport, Assembly hall, meeting hall, da Special hall wanda anan ake duk manyan taro na yaye dalibai ko speech and price giving day da holidays da sauran abubuwan duk anan suke, wanda iya nan wajen da dalibai suke iya fitowa daga nan sai can cikin makaranta wanda a can ne hotel yake da sauran abubuwan entertainment na makaranta.


To yau special hall ne ya dauka dan yau SS 3 student sukai graduation wanda tin 9:30am suka shiga exam suka fito 12:30pm suna fitowa dukkan dalibai cikin makaranta suka koma suka wanka sukai sallah sannan suka shirya cikin kayan su na graduation. Duk kan su yan mata ne wanda suke daga kan shekara 16, 17, 18 and 19 kuma duk wacce zaka kalla zaka gane yar hutu ce domin in kana *MGC (MANS GIRLS COLLEGE)* tamkar kana gida ne yadda ake kula da kai da komai na rayuwa dan kowa yana da system a hannun sa haka suna da wayoyi amman duk inda takwas na dare yayi an amshe wayoyin su haka nan karfe tara duk dalibai dole su tafi su samu entertainment sunyi kallo na awa daya zuwa awa daya da rabi da sun tashi kowa zai wanka da alwala sannan a kwanta kan sha daya dole kowa yai bacci kuma duk bayan awa daya zuwa daya da rabi Nanin dakin zatana mikewa tana duba lafiyar kowa wanda karfe biyar duk suke tashi suyi wanka suyi alwala sannan su shirya suyi sallah. Kan 6:00am sun gama komai har azkar wanda daga nan dining hall suke tafiya a can kowa zai zabi abinda yake bukata wanda kafin 7:00am an kawowa kowa nasa yai break daga nan su tafi assembly hall minti talatin suke yi ake tafiya aji wanda a ragowar minti talatin din zasuyi kintsa kan a fara class activities at 8:00am wanda karfe 10:30am ake fita tara, shima kowa abinda yake so zai zaba ya amsa, 11:00am ake dawowa 1:30pm ake tashi wanda ana tashi ake sallah daga nan abasu minti talatin dan suje suyi wanka suci abinci sannan su fito isilamiyya. 3:45pm kuma ake sallah sannan su koma sai 5:30pm ake tashi wanda anan kowa ake bashi wayar sa inda abinda zai yi yayi har ai magariba da isha'i a amsa. Haka rayuwar su take daga Litinin zuwa Laraba wanda Alhamis da Juma'a basa isilamiyya suna shiga catering class ne a koya musu girki kala kala wanda Asabar da Lahadi kuma tahfiz suke zuwa tin 7am har 5pm. Hatta uniform wanke musu ake kowa da sunan sa a jiki za a ajiyewa kowa nasa. Kuma basa taba saka kayan gida kullum kayan makaranta suke sakawa (personal wear they always put uniform) wanda suke da na normal school, na Isilamiyya, na catering, na tahfiz, sport, entertainment, da kayan bacci (sleeping dress) duk iri daya sai dai kowa da sunan sa ko kuma yan room kaza su zama on one colour like red, blue, yellow, pink etc

Babu zancen wannan yafi wannan aji ace za a saka wani aiki ko makamantan su duk sun dauki junan su yan uwa bama in dakin ku daya ko hostel din ku daya. A ka'ida tin kana JSS 3 suke saukewa wanda suke walima mai kyau shima iyayen ka zasu zo a bada kyaututuka (gifts) da sauran su. Wanda a SS 3 kuma suke haddace Alkur'anin wanda ba a tashi walima da bada kyauta sai a ranar kammala karatun (graduation) gaba daya anan ake yi.

Shiyasa duk iyaye da yan uwa da abokan iyaye dake wannan makaranta suke jiran wannan ranar domin kuwa rana ce ta farin ciki d'an ka ya haddace Alkur'ani mai girma kuma ya gama karatu wanda ilimin ke da inganci saboda samun kwararun malamai da kulawa da suke sosai.

Karfe 1:30pm Special hall da aka kwata shi da decoration ya cika da iyayen yara maza da mata, wanda a hall din akwai sarakuna na mabambanta garuruwa da yawa ga gwamna da mataimakin sa da wasu kusoshin gwamnati ga manyan malamai da yan kasuwa dukka da iyalan su dan a cikin su kowa da akwai nasa da zai gama makarantar. Yara guda dari ne suka yi graduation da haddar Alkur'ani wanda suke aji guda hudu dan duk aji daya ana saka dalibai ashirin da biyar.

Iyaye ne zaune atsakiyar hall din akan kujeru kowa gaban sa an anjiye masa lemo da ruwa da tissue wanda manyan baki kamar shugaban kasa da gwamna da sarkin garin da Babban malamin garin suke gefe suma gaban su lemo da ruwa ne. Dayan gefen kuma malaman makarantar ne a wajen. Wanda saman benen kuma gefe daya na sauran student dake JS 1 to 3, haka nan SS 1 to 2 wanda a gaban hall din kuma wajen zama ne na dalibai guda 100 din da suka gama makarantar.

Suna zaune daliban suka fara shigowa cikin shigar su ta iri daya wanda kowa ya saka graduation gown a ciki kuma wasu kaya ne iri daya riga three quater da wando red colour sai farin hijab wanda ya sauko kan kirjin su. Sai takalmi cover shoe baki da white socks kowa wuyan sa sakale da tag kowa da matsayin sa kamar headgirl, assitant, prayer, da sauran su.

Suna zama aka fara gudanar da taron kamar yadda aka fara. Wanda Babban malamin dake zaune a gefen Sarki uba ga daya daga cikin daliban shi zai bude taron da addu'a wanda aka kira sunan shi Sheihk Muhammad Jabeer Muhammad. Wanda ya mike cikin shigar sa ta babban malami yayi addu'a sannan ya zauna. Sannan akai national anthem da national plag, Daliban JS 1 aka kira dan suzo suyi barka da zuwa ga iyayen su. Nan suka sauko cikin shiga iri daya wanda kusan kan su daya haka kamar su ma iri daya ake gani suka zo sukai musu barka da zuwa da Hausa da Turanci sannan sukai da Larabci suka koma. Nan aka bada tarihin makarantar da irin nasarar da makarantar ta samu, haka aka dinga gudanar da program din har aka bawa kowa allon sa da certificate na cewar sun haddace Alkur'ani.
Wanda a cikin manyan baki su suka dinga represnting suna bawa yaran wanda yan jarida gidan radio kamar Freedom, Express, Rahma, Dala, Gurantee, Vision, da gidan television na Arewa 24, NTA, ARTV, Farin wata, Tauraruwa da sauran su, suka dinga dauka haka nan photo graphers na makarantar sai aikin su suke yi. Wanda bakin iyaye ya kasa rufuwa kowa murna yake da farin ciki nasarar da yaran su suka samu.

Maryam Muhammad Jabeer 'ya ga Sheikh Muhammad Jabeer Muhammad kenan wanda shine babban malami a jigar Kano babu wanda ya kai shi ilimi, shine sunan da aka kira wacce ita ce head of student wato headgirl, kuma tinda ta fara makarantar tin daga JS 1 har SS 3 ba ai daliba kamar ta ba mai kwazo dan ita ce overall duk section tana fin kowa mark kuma duk gasar da zata shiga sai tayi nasara dan haka ba karamin ji makarantar keyi da ita ba.

Wani Balaraben saurayi ne ya mike da sauri, lokacin da ya hango Maryam tana saukowa dan zuwa inda akai kiran ta. Na kusa dashi ne ya kamo hannun sa, juyowa yai ya kalle sa. Kai ya dan langwabar masa sannan yace
"Haba Aliyu ka zauna mana."

Maryam ya kara kalla sannan ya kuma kallon na kusa dashi sai kuma ya kalli gefen mata yaga Ammi na kallo sa murmushi ya sakar mata sannan ya koma ya zauna. Na kusa dashi da yace ya zauna wanda daga kallo zaka san dan uwa ne ga Maryam saboda yadda suke kama da ita. Shima kyakyawa ne dan na rasa wane jinsi ne shi balaraben ne shi ma ko kuwa bafulatani ne. Muje zuwa dai a sannu zamu san su waye su.

"Aliyu kana rage wannan abun fa!"
Juyowa yayi ya kalle shi sai kuma ya mai da kan sa kan Maryam dake karasawa inda aka kira ta cikin tafiyar ta mai daukar hankali wacce a nutse take yin ta kamar baza ta taka kasa ba, ba yanga take ba sam haka yanayin ta yake a ko da yaushe.

"Daliba mu mai kwazo wacce ta kawo mana cigaba da nasara marar adadi a wannan makarantar, jiha da kasa baki daya, wanda ita taci gasar musabaka da akayi last month wanda ta samu kujerar makkah da umrah, shugaban kasa kuma ya bata kudi har 1 million haka nan a yanzu makarantar nan ta dauki nauyin karatun ta na gaba wanda aka bata zabi ta zabi duk kasar da take so dan karasa karatun ta, domin hakika irin wandan nan yaran ba karamin cigaba suke kawowa ba."
Dai dai lokacin da Maryam ta karasa ta tsaya inda aka dauko award da gift da akai raping nasa mai girma shugaban kasa da kansa ya mika mata wannan kyautar sannan aka miko mata kyauta daga bangaren isilamiyya wanda aka ce Malam, Sheikh Muhammad Jabeer shi zai bata a matsayin sa na malami kuma uba ga Maryam wanda wajen ya dau kabbara wasu suna fadin
"Ah ai dole ashe yar Malam ce za tayi abinda yafi haka ma."

Wata tace
"Ai fa ko maganin karatu ya bata."
Dayar dake gefen su wacce take mahaifya ga aminiyar Maryam tai murmushi tace
"Hmmm daga Allah ne dan Malam bai taba basu abu dan suyi kokari ba dai dai tin suna yara na basu tsari da kuna duk abinda ya dace wanda tin a can suka samu gogewa a kwakwalwar kuma ma banda abin ku, ya'ya nawa ne a ya'yan nasa basu da kokari su kuma ace me?"

"Ai fa kuma haka ne. Amman dai yarinyar ta burgeni kuma karama da ita."
"Shekarar ta sha bakwai watan azumi zata shiga sha takwas"

"Allah sarki Masha Allah."
Ta fada ta mai da ido kan Maryam wacce hawaye ke zubo mata a idon ta. Lordspeaker aka bata dan tayi bayanin karshe a makarantar, wanda ta amsa tayi kasa da kan ta. Hawaye na zubo mata.

Aliyu dake zaune ne ya fara kokarin mikewa da sauri na kusa dashi ya rike shi juyowa yayi yace
"Menene haka Alkasim?"

"Ina zaka je?"
"Bakaga kuka take ba!"
Ya fada kamar shima zai kukan.

"Haba Aliyu wai meyasa kake haka yanzu can wajen ta zakaje ko......"
Ai bai barshi ya karasa ba ya kwace hannun sa ya mike da sauri ya nufi stage din wanda security ke tsaye a wajen yana zuwa suka bashi hanya ya wuce. Handkerchief ya zaro a aljihun sa ya karasa ya amshi lordspeaker ya mika mata, dagowa tayi ta kalle shi ya sakar mata murmushi cikin muryar sa mai dadin sauraro yace
"Goge mata hawayen ki *Matar Haydar* "

Amsa tayi ta goge hawayen nata wamda kamshin turaren Aliyu ke jikinsa, abin da ya kara kwantar mata da hankali kenan, sai da ta share hawayen sannan ta dago, murmushi yake sakar mata, dan haka itama murmushin ta sakar masa.

"Ma'ul ayn!"
Ya kira sunan da yake kiran ta dashi dagowa tayi yace
"Nasan kukan farin ciki ne but please kiyi komai kamar yadda aka tsara ina tare dake (am with you) kinji!"

Kan ta tayi kasa dashi, tace
"Stay by my side please (Ka tsaya a gefe na dan Allah) My Hayyat!"
Kai ya gyada mata sannan ya mika mata lordspeaker ya koma bayan ta ya tsaya kamar bodyguard din ta.

Rukayya da Aisha dake wajen zaman su wanda suke kawaye ga Maryam ne suka sakarwa juna murmushi. Rukayya tace
"Oh Yaa Haiydar da Maryam ko?"
Dariya Aisha tayi tace
"Allah har so nake ayi bikin nan naje naga irin soyayyar da za a sha kina gani dai ko kwana biyu bayayi bai zo ya ganta ba."

"Kinsan ni ba wannan ke dauren kai a soyayyar su ba sai ko ciwo daya yayi sai daya yayi."
"Shakuwar tasu ce tayi yawa. Allah dai ya kaimu wani satin mu mika masa matar sa mu huta."

"Sai su cinye kan su, mu huta ba. Ma huta da kullum yace *Matar Haiydar, ko Ma'ul Ayn"
Sukai dariya. Aisha tace
"Kin manta da *My din My* kenan"

"Sunan nasu ne ba adadi but wanda suka fada din kenan *Matar Haiydar* sunan yana min dadi."
"Ko *My din My* "
Sukai murmushi.



Maryam kuwa jin sa a bayan ta sai ya kara mata kwarin gwiwa tayi gyaran muryar sannan ta bude baki cikin muryar ta mai zaki da dadi tace
"Assalamu alaikum!"


Wanda sautin muryar ta mai dadi da zaki ya karade duk wajen ya janyo hankalin kowa ya dawo kanta, akai shirubkanarbruwa ya cinye su, sai ido da suka zuba mata,
"Sunana Maryam Muhammad Jabeer wacce nake matsayin Head student ta wannan makarantar gaba daya.
Ina Mai farin ciki da Allah Ya hadamu a wannann rana Mai Albarka wacce take cike da abubuwa da dama, ranar da ta kasance ranar farin ciki, Ina miqa godiya ta ga Allah (S.W.T) da ya hada mu a wannan rana, Ina miqa gaisuwata ga manyan ba'ki na musamman da malaman mu da sukayi tsayin daka dan ganin cewa burin mu ya cika, suka bada gudunmuwa dari bisa dari, Ina kuma mi'ka gaisuwata ga Iyaye na Yan uwa na, Yaye na, da suka tsaya min har na kawo wannan matakin da aljihun su da jikin su da addu'ar su, sannan ina mika gaisuwa da fatan alheri ga duk member ta makarantar nan class mate dina da duk suka ban goyan baya wajen ganin komai ya tafiyu dai dai dan ba wayo na bane ko da bara ta bace."

Ta dan tsagaita taja numfashi sannan ta cigaba da magana wanda in tana maganar kamar baturiyya dan yadda take fitar da komai dai dai a tsare cikin nutsuwa da iyawa

"Wannan makarantar tana daya daga cikin makarantun da wuya a same su amman cikin hukuncin Allah yasa na zamo daliba a ciki wanda wasu na neman gurbin da kudin su ma basu samu ba. Gaskiya fadin irin karuwar da muka samu a wannan makarantar ba karama bace, domin kuwa ko ba komai mun ilmantu kuma mun fa'idantu sosai, ko a yau na mutu na cika buri na, na zama hafiza na haddace Alku'ani wanda shine babban buri na a duniya, wanda ya tsaya maka wajen samuwar cikar burin ka kuwa babban masoyi ne a gareka wanda suka hada da malamai na, iyaye na, My Hayyat duk ina godiya dan ban da abinda zan biya ku sai addu'a Allah ya saka muku da gidan aljanna ya bani ikon amfani da abinda na sama"

Hawaye ne ya zubo mata ta sa handkerchief ta dan share sannan tace
"Nayi matukar farin ciki da har bansan da wane kalma zan mika godiya ta ba, da nuna farin ciki na ba zan bawa yan uwa na shawara akan mu dage mu samu mu cika burin mu da na iyayen mu dan duk wanda iyayen suka kawo shi wannan makarantar da kudin ya kusa 1M ya kamata ya tsaya ya basu farin ciki ya bawa kan sa da malaman sa farin ciki a karshe ina muku fatan alheri."

Juyawa tayi ta fuskanci Malam Muhammad Jabeer ta dan duka tace
"Fatan Alheri a gareka, "
Sannan ta kalli Iyaye mata tayi musu haka ta juya ga Director da malamai tayi musu haka sannan tace
"Nagode kwarai da karamcin da muka samu Ina fatan yadda muka hadu lafiya Allah ya maida kowa gida lafiya. Maryam Muhammad Jabeer Bisalam!"

Tafi aka dauka raf raf. Har ta bada lordspeaker zata juya Malamin yace
"Maryam kan ki zauna ina son ki jan hankali akan ilimi da mahimmancin sa ga mata."

Juyowa tayi ta amsa lordspeaker sannan ta kara sallama wanda yasa aka karayin tsit sannan tace
"Alhamdulillah duk wanda yake nan nasan yasan mahimmancin ilimi amman nasan maganar da nake ba iya nan zata tsaya ba kila a wata kasa can ma wasu su gani ko anan kasar to ni fata na gareku ko da an gani ayi amfani da abinda zan fada.
Ilimi shine haske da yake haskaka maka hanyar da kake zagaya duniya baki daya. Hakika daga lokacin da baka da ilimi ka zama makaho, kurma, bebe ku fadan tayaya mutum zai ji dadin rayuwa a haka to ilimi zai kore maka duk wannan abun.
Masana na cewa in ka ilimantar da namiji ka ilimantar da mutun daya amman in mace ka ilimantar tamkar ka ilimantar da duniya ne.
Ina masu cewa ilimin mace haram ne hakika ba haka bane sabida a duk lokacin da matar ka take da ilimi ko a mu'amala zamantakewar aure zaka ga canji da abubuwa dan Allah maza ku gwada in kana da mata guda mara ilimi auro mai ilimi wallahi hatta matar ka ta gida zata koyi abu a wajen ta shin ta samu ta kawar mata da wannan jahilcin ko kuwa haka nan ko ta tarbiyyar ya'ya in ka hada mai ilimi da marar shi zaka ga banbanci ta tarbiyya kai har kula da kai kan ka.
Ba wai kin bawa mace ilimin zamani kawai ba har na addini ba wai in ka bata aka ce tai aiki ba babban aikin ta zaka ganshi a gida dan wallahi daga ranar da ka dauke ta ka kai ta, ta samu ilimi kai da kanka zaka gane banbanci.
Babban misalin da zan baku shine akwai wata mata wacce tana zaune da mijin ta da yaran ta cikin rufin asiri mijin ta yafi karfin komai ya dauke mata komai na rayuwa wanda ya bata ilimi amman yace aiki sam ba za tayi ba haka ta zauna dashi lokaci daya Allah ya dauki rayuwar sa, bayan ya rasu ta koma gidan yar ta suka cigaba da rike ta da ya'yan ta bata da damuwar kowa, wanda kowa ke taimaka mata yaran in sallah tazo sai su samu kaya sama da kala goma, shekara daya a tsakani da mutuwar mijin ta mijin yar ta ya rasu, daga lokacin suna samun rufin asiri itama yayar bayan shekara ta rasu rayuwa ta fara basu kashi wanda a lokacin matar nan ta dauki takardun ta, ta koma ta nemi aiki ta samu dashi ta

Please Login or Register in order to submit comment