Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nan da nan hankalin sa ya tashi, ya hau tambayar
"Menene Baby? Meya faru? Dan Allah ki daina kukan nan, fada min menene?"

Kukan ta kuma saki tana fadin
"Ba kai bane!"
"Ni kuna Baby me nayi?"

"Fushi kake yi dani!"
"Ni na isa, ba zan taba fushi da Matata ba, please stop crying kinji da wasa nake fa na kashe ne dan ki dan kwanta ki huta kinga safiyya tayi ko?"

Dariya tayi tace
"I love you My! Sai anjima!"
Ta fada ta kashe wayar daga shi har ita murmushi suke wanda su kadai suka san ma'anar sa.

Kwanciyya yayi yana karatun Alkur'ani ita kuma mikewa tayi ta nufi kitchen. Ammi ta gani da me taya ta aiki, har kasa ta durkusa tana gaishe da Ammi ta amsa tana fadin
"Har kin tashi ko baki koma ba?"

Kai ta gyada mata ta gaishe da Baba Ramma Mai aikin su ta amsa tana kara taya ta murnar kammala karatu ta amsa tana godiya.

Baba Ramma tace
"Kinga Maryam je ki kwanta nasan tinda kuka fara jarabawa ba wani baccin kirki kikai ba ai Ina jin kin ma daina shiga kitchen sai na gidan ki."

Kasa tayi da kanta, Baba Ramma tace
"Jeki abinki ki huta kinji!"

Kai ta gyada ta juya ta fita, gidan sai kamshi yake dan an share anyi mopping an saka turaren wuta sai kamshi. Ido ta lumshe ta nufi bangaren Abbi.

Shima ko Ina fes sai kamshi ke tashi a dakin da sallama ta shiga falon nasa yana ciki inda yake zama yayi ibada.

Amsawa yayi ya bata izinin shigowa sannan ya dago yana kallon kofar dakin. Shiga tayi ta karasa ta zauna a gefen sa. Murmushi ya saki yana fadin
"Mamanah!"

"Na'am Abbi barka da asuba!"
"Barka ka dai! Da fatan kin tashi lafiya?"

"Alhandulillah!"
"Masha Allah, Allah yayi albarka yayi jagora ya bada sakamako mai kyau. Hakika Ina alfahari dake uwata duk cikin ya'ya na kece kika fita daban ta fannin son karatu sosai bama na addini da kuma dagewa, daga ke sai Aliyu shi da bama 'dana ba amman ina zaton shi zai gajen a wannan fanin nan gaba Allah muku albarka!'

"Amin Abbi!"
"A cikin waccan satin Alkasim da Aliyu suka zo da zancen shagalin bikin ku!"

Kai tayi kasa dashi, yace
"Alkasim yaso a kwashe sati ana biki amman ni da Aliyu muka ce a'ah ayi kamu, yini da walima Friday a daura aure yafi. Kinsan Yayan naki wai shi ba party ko daya, Aliyu yace ba za ai ba shine yace shi ya dauki nauyi, ni ba zance a'ah ba amman nace ayi a tsarin addini banda kide kiden nan dan albarka muke nemar muku me kika ce ke?"

Kan ta a 'kasa, kamar 'kasa ta bude ta shiga dan kunya tace
"Abbi duk yadda ka yanke yayi mungode!"

Sallamar Aliyu sukaji a kofar dakin. Suka amsa tare ita da Abbi dakin ya shigo ya karasa gefen Abbi dan Maryam na dayan gefen nasa.

Gaishe da Abbi ya karayi dan sun gaisa tin da asuba. Kan ta a kasa ta gaishe shi ya amsa yana murmushi.

Abbi ya kalli Aliyu yace
"Ina fada mata yadda mukai rannan ne!"

Murmushi yayi ya kara 'kasa da kansa. Wani littafi ya dauko a gefen sa ya turawa Aliyu amsa yayi ya bude inda suke ya fara biyawa yana masa bayani har ya karanta shafi uku sannan ya dago ya dan kalli Abbi yace
"A satin nan naga alama zan sauke."

"Masha Allah! Allah ya amfana."
Maryam dake zaune tana kallon su ce tace
"Abbi tinda na gama karatu nima a saka min wani littafi da bamuyi ba a makaranta."

Murmushi Abbi yayi yace
"To Mama nah ai sai dai nace Aliyu ya samar miki kwana nawa ne zaki tafi shi sai yana koya miki ko Aliyu?"

"Haka ne Abbi!"
Ya fada yana yi mata wani kallo 'kasa 'kasa. Murmushi tayi kanta a 'kasa tace
"To Abbi!"

Mikewa Abbi yayi ya shiga daki. Aliyu ya matso yace
"My love!"
Kofar dakin Abbi ta kalla sannan ta dawo da kallon ta kan sa.

Murmushi suka sakar wa juna. Aliyu yace
"My love sai naga kin Kara kyau!"

"Baka gajiya da fadar haka Yaya nah."
Jin tahowar Abbi sukaji yai sauri ya koma gefen ita kuma tai 'kasa da kai tana wasa da yatsun ta.

Wata jaka ya fito da ita ya ajiye sannan ya bude ya dauko wasu kati ya mikawa Maryam yace
"Ko su Rukkaya kya bawa su bawa iyayen su ko?"

Kai ta gyada tana godiya. Yace
"Anjima Aliyu zai baki na yini da kati sai ki bawa kawayen naki ko?"

"Nagode Abbi!"
Aliyu yana zaune yana kallon su. Ta mike ta 'kara godiya ta fita. Ya bita da kallo ta kasan Ido.

Abbi yace
"To wane littafi zamu saka in kagama wadan nan."
Kai a kasa yace
"Zan kawo bayan biki sai a fara."

"To shikenan!"
Yana zaune Ammi a shigo hannun ta dauke da tray saman sa flask na abinci da na tea. Ajiyewa tayi, Aliyu ya gaishe da Ammi ta amsa ta dauko plate da cups ta ajiye.

Abbi ta zubawa sannan ta kalli Aliyu tace
"Ka zuba kaci."
"To Ammi nagode."

Ta juya ta fita, Abbi ya dauki kunun gyaɗa da yaji madara ya sha, kallon Aliyu yayi yace
"Bismillah Aliyu."
Cup ya dauka ya zuba kunun sannan ya zuba dankali da farfesun kayan cikin. Tare suka ci abinci sai da suka gama ya dauke ya fitar da kayan kitchen ya kai kayan hango ta yayi a gaban gas cooker a hankali ya karasa ya rumgumeta, ta baya ajiyar zuciya ya sauke ita kuma tace
"Myyy!"

" *Matar Haiydar* ina kewar ki da yawa fa!"
Shiru tayi can tace
"Yaya ba kyau fa."

Juyo da ita yayi yana kallon lips din ta wanda yake pink sirara ga dauki sai kyalli yake ji yai kamar ya tsotse bakin yace
"Sai aikin ba kyau *Matar Haiydar* kada ki manta fa, ni mijin ki ne!"

Kofa ta kalla tace
"My Hayyat kada wani ya shigo fa."
"To menene! Me kike?"
Gun gas ta juya tace
"Indomie nake so."
"Kawo na dafa miki."

"A'ah kaje zan karasa."
Kallonta, ya tsaya ita kuma ta zuba indomie dan ruwan ya tafasa sannan ta juyo dan dauko kwai ta fasa ta soya sai ta ganshi a gefe yana ta kallon ta.

"Kallon fa *Mijin Nah* "
Ido ya lumshe sannan ya bude yana murmushi ya matso kusa da ita yana fadin
"Ina son ki *Matar Haiydar* "

"Nima haka *Mijin Maryam* "
Murmushi ya kara saki ya kamo hannun ta ya sumbata sannan ya saki yace
"Bari naje kisan yau juma'a!"

Murmushi ta saki tana kallon sa tace
"Ayi kwalliyar juma'a nima zanwa mijina ya gani."
Murmushi yayi yana shafa sajen sa yace
"Godiya nake bari naje. I miss you!"

"Miss you more!"
Ya juya ya fita ta dauko kwai da kifin gwangwani sannan ta dawo ta yanka albasa ta juya kifin gwangwani da albasa sannan ta fasa kwan wanda yasa karnin ya dake ta, ta tafi sink da sauri ta fara amai sai da ta gama tazo zata soya.
Biba ce tace
"Ke Anty da bakya son karnin kwai."
"Wallahi Biba har amai ya sani yau bari na dauko curry ya 'kara rage karnin ina son naci ne."

Ta wuce ta dauko mata. Biba ta amsa ta soya tace
"Amman naga abinda kike so Ammi tasa yau akai dan kin dawo."
Fuska ta dan shagwabe tace
"Ji nayi kuma bana so."

Ta dauki plate ta juya indomie dinta saka kwan a gefe sannan ta dibi kunu ta nufi dining dake Babban falo. Tana zama Yaa Alkasim ya shigo ya kalle ta yace
"Antyn kwadayi."

Murmushi tayi tace
"Ina Kwana?".
"Lafiya ya gajiya?"

"Alhamdulillah!"
Yaa Abdullah ne ya shigo yana hango plate din ta ya karaso yana fadin
"Daman yunwa nake ji."

Fuska ta bata ta dago tana kallon Yaa Alkasim tace
"Yaya kace masa breakfast din sa na kitchen ni bana son shi ne fa."

"Nima wannan zanci."
Yaa Abdullah ya fada. Yaa Alkasim yai murmushi yace
"Ni ba za kusani rabon fada da safen nan ba amman dai Abdullah kaje ka dauko naka sai ta sammaka ko ka saka Biba ta girka maka "

"Yaya nata yafi dadi"
"To je ka dauko kaji"
Ya mike ya nufi kitchen ta dauki plate da cup din ta tayi dakin Ammi.

Ammi na zaune a kan kujera ta shigo ta zauna a kasa ta fara ci. Kallon ta tayi taga yadda take cin abincin tace
"Yunwa kike ji ne?"

Kai ta gyada tace
"Kinsan bakwai mun karya a makaranta."
Kai ta girgiza. Tana gama ci Abdullah ya shigo yana fadin
"Ammi nan Maryam ta shigo?"

"Gata nan!".
"yauwa!"
Maryam tayi murmushi tace
"Ni na cinye abu na."

"Wanda yaci shi kadai dai shi kadai zai mutu!"
"Ko mu nawa mukaci ni kadai zan mutu ko Ammi?"
Murmushi Ammi tayi tace
"Haka ne kam."

"Kai Ammi kice a'ah!"
Alkasim ne ya shigo ya durkusa ya gaishe da Ammi sannan ya kalli Maryam yace
"Kawon abinci ni."

"Yaa Aliyu fa?."
Maryam ta tambaya, Yaa Alkasim yace
"Ai shi da Abbi suke karyawa, in ya tafi dani Abbi zai na karyawa dai."
"Kana aikin bacci?"
Ammi ta fada.


Maryam ta dauke kanukan ta fita a dakin. Bayan ta kai masa ta shige daki tayi wanka ta shirya cikin wani less din ta peach kala da akai wa ado da maroon kala dinkin doguwar riga ne ya kama ta daga sama daga kasa ya bude da yake piece ce tai daurin ta mai kyau ta saka fashion dinta maroon ta dauki maroon mayafi ta yafa tana ganin yadda rigar ta, ta kamata tace
"Ni karatun ma ko ramar dani bai ba!"

Wayar ta taji tana kara ta dauko ta duba taga Aisha dauka tayi, Aisha tace
" *Matar Yaa Haiydar* "
"Na'am kin tashi lafiya?"

"Alhamdulillah ya gidan?"
"Alhamdulillah yasu Mum?"
Haka suka gaisa sannan sukai sallama ta kira Rukayya suna waya taji alamar ana kiran ta wannan yasa ta katse kiran ta dauki nasa.

" *Matar Haiydar* kina ina ne?"
"Ina daki!"

"Ok!"
Ya fada ya kashe wayar. Rukayya ta kira suka cigaba da magana bayan sun gama ta wuce gaban mudubi tana kara shafa turare kofar dakin ta ji an bude ta jikin mudubi tagan sa ya shigo cikin manyan kaya riga da wando farare tas sun masa kyau ya saka hula mai kyau da tsada sai tashin kamshi yake.

Ba karamin kyau yayi mata ba, Yaa Haidar fari ne tas, wnda yake da faffadan kirji basi da rama kuma dogo ne masha Allah, yana da manyan idanu wanda suke a lunshe ko da yaushe sai pink lips din sa masu laushi, hancin sa dogo a tsaye, sai saje da ya zagaye fusjar sa, koyaya yai magana kuma motaa baki sai gefen kunatun sa ya dan loba, ido ta lumshe tana mai sakin murmushin da bata san ya fito ba a hankali ya karaso sai ji tayi ya sakalo da hannun sa ta gaban ta. Ya saka kan sa a kafadarta yana mai shinshinar wuyan ta wanda yake kamshin turaren da ta shafa Oud 24.

ido ta bude da sauri tana kokarin ta zame jikin ta a nasa amman yaki sakin ta wannan yasa ta dago ta kalle shi ta mudubi sam bai ma san tanayi ba dan idon sa a lumshe yake sai shakar kamshin ta da yake yana sauke numfashi.

"Myyy!"
Ta kira sunan sa. Bai amsa ba ta kara cewa
"My Hayyat!"

A hankali yace
"Uhmm!"
"Kada wani ya shigo fa ka bari!"

"To menene a ciki?"
Fuska ta shagwabe kamar zatai kuka,
"Please My!"

Dagowa yayi yana kallonta ta jikin mudubi,
"Menene to?"
Kai ta girgiza.
"Don't cry to!"

Kai ta gyada ya dago yana fadin
"Kinyi kyau *Matar Haiydar* !"
"Kafini kyau *Mijin Maryam* "

"Anya kuwa?"
Ya fada yana kallonta ta mudubi itama kallon nasa takeyi kallo mai cike da so da kauna. Sakin ta yayi ya juya ya nufi kofa dan wani abu da yake ji game da ita.

"Ina zaka?"
Ta fada a shagwabe
"Masallaci!"

"Baka tambayen addu'ar da zakai min ba!"
Juyowa yayi ya harde hannun sa a kirji yace
"Kece duk kin rikita ni ai."

Murmushi tayi tai 'kasa dakai. Yace
"Wacce addu'a zan miki yanzu banda Allah ya bamu zuri'a mai albarka, da zaman lafiya, dan samun ki na riga na gama, kuma wannan kullum ne"
A hankali ta dago tace
"Ka roka min in riga ka mutuwa Yaya!"

"Saboda me?"
Ya fada cike da mamaki
"My Hayyat bana son na rasa ka in na rasa ka ban san halin da zan shiga ba, kai kadai nake so kai kadai nake son rayuwa dashi dakai kadai na shaku na saba."

Ta fada hawaye na zubo mata a ido da sauri ya karaso, wanda kana ganin sa zaa san hankalin sa a tashe yake dan a duniya ba abinda ya tsana kamar yaga Maryam na zubar da hawaye, kanta ya dago yana fadin
"kada kiyi kuka insha Allahu tare zamu mutu mu hadu har a aljanna ki daina kawo wannan Allah zai iya jarabtar ki yaga halin da zaki shiga ki daina kinji ko dani ko bani zaki rayuwa."

"Zan yi rayuwa tabbas amman cikin kunci Yaya please ka dage da tayani da wannan addu'ar!"
Janyo ta yayi ya rumgume yace
"Insha Allahu stop crying kinji my love, sai munga ya'yan mu da jikokin mu kinji."
Kai ta gyada ya kalli agogo har daya saura ya sake ta yace
"Bari naje sai na dawo zan kira ki."

"Allah tsare ya dawo dakai lafiya."
"Amin me zan taho miki dashi?"

"Dabinon masallaci"
"Wannan daman wajib ne, sai me?"

"Duk abinda ka gani."
"Bye!"
Ya daga mata hannu ya juya ya fita, itama hannu ta daga masa ta koma ta zauna a gefen gadonta tana murmushi.

Wayarta, ta dauka ta kunna data ta hau online tana hawa Aisha na mata vedio call. Dauka tayi suna kallon juna Aisha tace
"Kai wannan kwalliyar fa Besty?"

"Ina kwalliyar anan?"
"A'ah gata nan ince Yaa Haydar akayiwa."

Murmushi tayi tace
"Wallahi shi nayi wa"
"Ai na sani nidai har Allah, Allah nake wata friday tayi mu mika ki mu huta."

"Au ku huta?"
"Eh mana."

Murmushi sukai Ammi ce ta shigo ta zauna Aisha tace
"Bani Ammin mu gaisa!"
Ta mika mata bayan sun gaisa ta bata waya sannan suka kashe wayar.

Kallon Ammi tayi, Ammi cikin kunya tace
"Yayar kice ta aiko miki mai gyara sun zo tin sauran wata daya a fara to makaranta tasa ba a samu an fara ba dan haka daga yanzu in an fara ba fita dan haka yau ki samu ki kaiwa su Aisha katin kinji ko?"

"To Ammi!"
"Yauwah! Anjima zata karaso."

"Allah kawo ta lafiya!"
"Amin. Ba abinda kike bukata ko?"

"Babu Ammi. To Allah yayi albarka."
Ta mike ta fita.



Karfe biyu duk suna falo Yaa Muhammad, Ibrahim, Alkasim, Abdullah da Yaa Aliyu dawowar su kenan aka kawo musu lemo mai sanyi dan ba karamar rana ake ba. Sai da suka sha duk masu auren Yaa Muhammad, Ibrahim, sukai bangaren su, Yaa Aliyu da Abdullah da Alkasim kuwa dining suka zauna suka fara zuba abinci suna gamawa suka zauna a falo suna hira, sai da akai la'asar sannan suka tafi masallaci dan yin sallah.

Bayan sun dawo garden Yaa Aliyu ya wuce ya samu waje ya zauna, number Maryam ya fara nema tana dauka yace
"Gimbiyya ta *Matar Haiydar* kinga sakon ki ko?"

"Nagani Yaya nagode!"
"Kina ina yanzu?"

"Ina ciki yanzu zan fito zanje gidan su Aisha da Rukayya!"
"Me zakiyi?"

"Zan kai musu kati ne!"
"Oh fito na kai ki daga nan sai mu amso sauran ki basu."

"Toh Yaya!"
Ta kashe wayar sannan ta fito. A babban falo ta samu Ammi zaune ta karasa tace
"Ammi na fito zan tafi!"

"To waye zai kai ki?"
"Yaa Haiydar ne!"

"Ina Alkasim da ba zai kai ki ba shi?"
"Ni ban ganshi ba kuma shi yace zamu biya mu amso sauran!"

"To ki kula da kanki dai."
Kan ta tayi kasa dashi tace
"Insha Allah!"

Sannan ta mike ta fita a parking space ta hango shi yana tsaye a gefen motar sa. Kallon ta ya tsaya yi har ta karaso bai daina ba gefe ta tsaya tace
"Ba kyau dai!"

"See ur mouth kamar ba kyau din!"
Tai murmushi shima murmushin yayi yace
"Naga Matata ce ko?"




*Allah ya jikan iyayen mu yasa muyi kyakyawan karshe Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum



MS Indabawa
*Antty*

💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 16

By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW


*Bismillahir Rahmanir Rahmin*



Murmushi tayi tai gaba zata shiga da sauri ya karaso ya bude mata mota ta shiga ya rufe sannan ya zagaya. Motar ya tayar mai gadi ya bude musu suka fita. Sai da suka hau titi yace
"Ya zancen kudin kwalliya da gyaran amarya banji ance na bayar ba."

"Oh amsa ake yi daman?"
"Baki sani ba. Nasan da Fadima na nan da yanzu ta damen da zancen."

"Ni ai nasan Abbi zai bayar ba sai ka wahala ba."
"Wacce irin wahala kuma ai hakki nane nifa za a gyarawa ke."
Ya fada yana kashe mata ido daya.

Kai tai saurin daukewa tace
"Kai Yaya ni ka bari."
Dai dai karasowar su shagon da zai amshi sakon waya kawai yayi ya fito ya bashi sakon suka dauki hanya. Sai da suka hau hanya sosai yace
"Me zan bari *Matar Haiydar* ni dake fa mun riga mun zama daya wannan kunyar please a ajiye ta gefe kar ta hanani sakewa da Matata."

Murmushi tayi tace
"Uhmm naga katin?"
Mika mata bag din yayi ta bude kati ne kala biyu daya na kamu da yini ne dayan kuma na dinner ne duk sunyi kyau sosai ko wannen yana cikin envelope din sa na Dinner har da sit number.

Bag din ta rufe tace
"Amman sunyi kyau!"
"Basu kai Matata kyau ba."

Murmushi tayi tace
"Yaushe Yaa Ahmad zai dawo."
"Wannan dan iskan sai ja min rai yake yaki ya fada min yaushe zai taho amman ya kamata ace dai dis week end ya taso since wenesday za a fara biki."

Murmushi tayi ya kalle ta yace
"Monday in naje zan dauki hutu, wata nawa kike so na dauka?"

"Wata kuma Yaya?"
Ta tambaya tana zaro ido, murmushi ya saki yace
"Eh wata nawa?"

"Haba My Hayyat wata ai yayi yawa sati daya fa ake dauka zuwa biyu!"
"Inji wa?"

"Mutane!"
"Baby nah ke daban ce wallahi sati daya ya min kadan zan ce su bamu three month dan daga nan zamu wuce honeymoon ko ya kika ce?"

Hannu ta saka ta rufe fuskar ta tace
"Kai Yaya aikin fa, kaga sati biyu ya isa honeymoon ai kullum muna cikin sa dan kaje ka dawo dai kawai."
Motar ya tsayar ya juyo yana kallon ta wanda yasa tai saurin yin 'kasa da kan ta tana wasa da yatsun hannun ta.

Hannun ta ya kamo yace
"Ma'ul Ayn kinsan yadda nake jin ki kuwa a zuciya ta, ina yawan fada miki amman kamar kina mantawa daga lokacin da na sanki daga lokacin so, kauna, shakuwa, tausayin ki suka dadu a zuciya ta, wallahi ko awa daya bana so naji na nisanta dake, hakika Allah shi ya dauran son ki, tin baki da abinda za a kalla a soki, sonki shine rayuwa ta duk lokacin da na rasa ki mutuwa zanyi, ba da wasa nake ba duk fitar numfashi na ko bugawar zuciya ta da sunan ki suke bugawa, ki gane yadda nake kaunar ki, bana son na nesan ta dake ko na minti daya, kina gani dan haka nai 'kaura na dawo gidan ku, dan numfashi na da naki suna gauraya a cikin waje daya, hakika duk lokacin da muke tare zan nuna miki so da kaunar da bazaki taba mantawa da ita ba, Ina sonki da kaunar ki, fatana mu rayu dake har tsufan mu ki haifa min ya'ya shine kadai burina na gaba....."

Hawaye ne ya fara zubo mata a idon ta ya dago kan ta yace
"Kuka kuma Baby menene?"
Ya fada yana lashe hawayen idon nata jikin sa ta fada ta rumgume shi sosai tana fadin
"Na yadda da kai Yaa Haiydar shiyasa na baka duk rayuwa ta, Yaa Haiydar nasan bazan taba samun makamanciyyar soyayyar ka ba, da kai na rayu, na tashi nayi wayo son ka na budi ido na ganni a cikin sa dan Allah kada ka tafi ka barni, kada kayi nesa dani ko yaya ne Yaya na, zan kasance maka yadda kake so na kasance zan maka biyayya iya kar iyawa ta zan baka farin ciki Yaya nah ina son ka da kaunar ka, kaine hasken rayuwa ta."

Kara rumgume ta yayi a jikin sa, yana sauke numfashi a hankali, jin kukan ta yake har cikin zuciyar sa, a hankali ya dago kan ta yana kallon cikin idon ta dake zubar da hawaye harshen sa ya saka yana lashe hawayen nata da sauri ta rumtse idon ta, sai da ya shaye su tas sannan yace
" *Matar Haiydar* ki daure ki rage kuka wallahi bana son kukan ki ko kadan, nasan daga hallitar ki ce amman please ki rage su. Kuma ki sani ni *Aliyu Haiydar* ina nan tare dake har karshen rayuwar ki ko bana tare dake zan kawo miki mai saki farin ciki wanda zai karasa cika min burin ki, amman ki sani har abada *Aliyu Haiydar* nason ki kuma kece kadai *Matar Haiydar* kinji ko?"

Rumgume shi tayi sosai abunda zai ce bata tabai masa ba sai dai lokacin yarinta sai ko in bata cikin haiyacin ta amman kalli yanzu yadda ta rumgune shi tsam a jikin ta. Shima hugging nata back yayi yana mai kara jin son ta da kaunar ta hadi da tausayin ta.

Sun dauki minti kusan goma haka kowa da abinda yake sakawa a cikin zuciyar sa, shine yai karfin halin cewa
" *Matar Haiydar* ba kyau fa!"
Kan ta, ta sunne a jikin sa sai kuma ta zame jikin ta daga nashi ta koma jikin kujerar motar tana fadin
"Ai miji nane!"

Ido ya zaro yana fadin
"Da gaske?"
Kai ta dauke tace
"Mu tafi!"

"Sai kin fada min da gaske?"
"Kaima fa ka sani."

"To naji dan Allah a taimakawa wannan mijin naki ya samu yar nutsuwa."
"Kaje kai azumi kawai"

"Wallahi da kansa yake karyewa."
Fuska ta rufe da hannu tace
"Ba kyau fa."

Yai dariyar sa mai kyau yana shafa sajen sa hadi da bin ta da wani kallo yace
"Naga Matata ce menene ba kyaun?"
"Nidai mu tafi dan Allah!"

Gyara zama yayi ya kunna motar suka karasa gidan su Aisha. Katon gida ne wanda tsarin gidan kamar zane ne gidan ya tsaru daga gani mai gidan ya tada kai da naira. A bakin gate yai horn mai gadi ya leko Aliyu ya bude window yana ganin sa ya rissina yana gaishe shi sannan ya koma da sauri ya bude masa gate din. Ciki suka shiga a parking space yai parking, inda wajen aka kawata shi da shuke shuke a compound din gidan ya kara kyau da sanyi. Bag din ta bude, ta dibi kati nan sannan ta kalle shi yace
"Kada ki shanya Mijin ki dai!"
Murmushi tayi tace
"Insha Allahu!"

Ta bude motar ta fita, ya bita da kallo yadda take tafiya a nutse yarinya karama ta gama tafiya da shi gaba daya. Idon sa ya sauke kan mazaunen ta da suke a bude a cikin doguwar rigar tata, ido ya lumshe yana cije lips din sa na kasa tare da shafa sumar kan sa. AC motar ya dado ya lumshe ido kamar mai bacci.



Sallama tayi a bakin kofar sitting room din, aka amsa mata ta shiga Mum din su Aisha ce a zaune a kan daya daga cikin kujerun da suka kara kawata dakin masu kyau. Dakin sai kamshin yake da sanyin AC, tana ganin Maryam tace
"Ah Maryam kece a tafe?"
"Wallahi Mum! Ina yini?"

Ta fada tana durkusawa har kasa suka gaisa sannan tace ya mutan gidan. Bayan sun gaisa tace
"Aishan na ciki yanzu ta shiga bata ce min kuma zaki zo ba."

Kan ta a kasa tace
"Eh bance mata zan zo ba."
"Ayyah to shiga tana ciki."

Ta mike ta nufi dakin ta. Knocking tayi Aisha dake kwance akan gado tace
"Yes come in!"
Maryam ta bude ta shiga, Aisha ta juyo tana ganin Maryam ta mike da sauri ta sauko tazo ta rumgume ta tace
"Daman kina hanya baki gaya min ba dazu!"

"Nima bansan zuwan ba sai da muka gama waya."
"Zauna bari na kawo miki lemo!"
Ta nuna mata gefen gadon ta wanda ya sha zanin gado mai kyau ga laushi kayan dakin duk lemon green ne sunyi kyau sosai.

Zama tayi tace
"Daga gida fa muke kuma tafiya zanyi"
"Haba daga zuwa."

"Ni da Yaa Haiydar ne fa!"
"Ah ai nasan ba zama zaki ba tinda kuka zo tare."

Ta mike ta nufi fridge ta dauko mata lemo biyu da ruwa biyu tace
"Kisha ki kai masa wannan!" Jakarta ta bude ta dauki kati nan tace
"Gasu ki bawa Mum ni wallahi kunyar ta nake ji na bata da kai na. Dan Allah ki kaiwa su Abra, Widad, da Muwadad!"
Yan uwan su Aisha ne wanda tare sukai graduation ya'yan yayen Mum din ta ne da kuma Kanenen Dad din ta.

"Sannan duk wanda yake na kusa dake anan zan kaiwa Rukky ma please Sister kinga Ammi tace wai daga yau bazan kara fita ba."
"Kada ki damu insha Allah zan bawa duk wanda ya dace zanyiwa Rukky magana sai muji yadda abin zai kasance."

"Nagode!"
Ta fada tana mikewa.
"Menene na godiya ai mun zama daya."

Ta dauki lemo kan tace
"Tinda kinki dauka bari na kai masa da kai na."
Suka fita a falo suka samu

Please Login or Register in order to submit comment