Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya taru a ciki, shima take ya shiga damuwa yanayin ta ya sauya idon ta har ya kada yai jawur kallon ta yayi yace
"Subhanallah meya faru?"
Kai ta girgiza ta mike.......



*Allah ka yafe mana kasa muyi kyakyawan karshe Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum*




*Antty*
[10/30, 13:46] My Airtel: πŸ’—πŸ’— *MATAR HAIDAR* πŸ’—πŸ’—
Page 11

By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW



*Bismillahir rahmanir rahim*


*
Ji tayi gaban ta ya fadi abu da ta jima da mantawa ya dawo mata kwakwalwar ta ta shiga kai koma, yadda ta fada duniyar tunani, yace
"My wife."

Da sauri ta dago wanda idon ta tini yai ja, ga hawaye da ya taru a ciki, shima take ya shiga damuwa yanayin ta ya sauya idon ta har ya kada yai jawur kallon ta yayi yA yace
"Subhanallah meya faru?"
Kai ta girgiza ta mike tana fadin
"Kayi hakuri."

Sai tayi cikin gida da sauri, dakin ta ta shiga ta fada saman gado rayuwar ta take son ta tuno so take ko ta halin yaya ta tuno wani abu amman ina ta manta tasan dai ta kasance a wannan gidan wanda yake shine gatan ta a duniya kawai su suka rufa mata asiri suka zame mata iyaye da family, shin su waye iyayen ta? Ina suke? A baya ne take shiga wannan halin na son lallai sai ta tino su waye iyayen ta wanda in tai wannan tunanin yake saukar mata matsanancin ciwon kai saboda damuwa in ba sa'a ba sai ta kwanta ciwo ma.

Bata san lokacin da bacci ya dauke taba, Ummi ta leko dakin ta ganta kwance ta rufe kofar kawai ta barta da dare Aliyu ya aika Haidar ya kira Maryam, lokacin har ta saka kayan bacci, kana ganin ta zaka gane tana cikin damuwa, hijab ta dauka har kasa ta daura sannan ta fita, ba kowa a falo dan lokacin tara ta gota, dakin ta nufa ta kwankwasa aka amsa ta bude a hankali, zaune ta same shi akan kujera da remote a hannu.
"Gani."

Ta fada tana duban shi sai taga ya daure fuska, itama fuska daure dan daman bata cikin walwala tun dazu da aka famo mata inda yake mata ciwo. A ranta tace
"Miskilanci na shi ya tashi kenan."

Bai kalle ta yace
"zauna"
Ta zauna, ya dago ya dube ta yace
"Waye Muhammad?"

"Nima ban san shi ba."
Wani murmushi yayi yace
"Bana son karya, ke kuma yanzu kina son ki koya ko?"

Kai ta girgiza yace
"Nasan kin sanshi tinda ke kika bashi dama zuwa wajen Abba, buri na akan ki, ki tsaya kiyi karatu, kamar yadda kike fita da point mai kyau ya zama har karshen karatun ki haka amman ke kin nuna kin girma aure kike so ko? Ki sani in nace a'ah ba wanda zai ce eh dan haka ba zan bar yaron yana zuwa wajen ki bane dan ya hanaki karatu, ko da tafiya zanyi bana son yawan zance a wata sau biyu ya isa dan ina da buri akan ki, wani can ba zai zo ya lalatan buri ba dan haka ki kiyaye ke kina son sa ne?"

Banza tai masa dan ya fara bata mata rai ina ruwan sa da tana son sa ko bata son sa ya bari ya gani ko yaji mana,
"Ba magana nake miki ba."
Ya fada wanda hakan ya sa ta dagowa da sauri duk da yadda yaga idon ta a kumbure sai ya kau da kai yace
"Uhmmm."

Shiru tayi yace
"Shawara daya zan baki kada ki soma yin kokarin rusa min buri na, in har kikai haka daga ke har ni ba wanda zai ji dadi, ki daure ki cika min buri na akan ki."
Dagowa tayi tana son karin bayani gane haka yasa yace
"Eh akan karatun ki."

Kai ta dauke yace
"Shine gatan mu, kuma ilimin shine madogarar mu, kina ji ko?"
Kai kawai ta gyada, yace
"Kar kice zaki bar karatun ki kiyi aure wannan duk bata lokaci ne da daurawa kai wahala."

"Ni daman ba aure zan yi yanzu ba, karatu nake so na karasa kuma shima ya sani."
"Na fada miki dai dan kar yazo ya hure miki kunne gashi ni zan tafi amman duk da haka zan saka ido akan ku, na sani ba wai son sa kike ba ko kina son sa?"

Kai ta gyada yace
"Karya kike Maryam, ki koma ga zuciyar ki ta fada miki wanda kike so amman ni nasan ba son Muhammad kike ba."
"Yaya....."

Hannu ya dauran akan bakin sa yace
"Bana son naji wani abu, da kina son sa da dazu dana tambaye ki, kin sanar min amman kin kasa saboda har zuciyar ki ba son nasa kike ba, bana son kije inda za a wulakanta ki, ina son kije inda za a kula dake inda akasan darajar ki."

Dagowa tai tana kallon sa, shima ita yake kalla yace
"Tin ina yaro nake iya gane abinda wani yake ciki, wanda dana girma abin yake ban sha'awa, wannan dalilin yasa bayan na zama likita na koma na karanci halayar dan adam, ina karantar yanayin mutum nasan me yake ciki da manufar sa da yawa in anyi abu ina dauke ido ne kawai akan wasu abubuwan......"

Ido ya lumshe ya bude yace
"Dan haka kada ki min musu, kinso wani a baya kuma ba wanda zaki so a gaba sai wanda yake tamkar na bayan nan mai wasu daga cikin halaiyar sa, duk da kin manta wasu abu amman zuciyar ki ita zata kwadaita miki wasu abun, bama wannan ba in kin tashi mai irin sunan sa zaki aura zaki cike gurbin da a baya baki cike ba dan haka ki nutsu kada ki tsaya batawa kan ki da wani lokaci."
Baki ta dan tabe kawai yai murmushi yace
"Gobe zan tafi wanda zan jima acan shekara daya zanyi ko fi ban sani ba ko zan iya ko ba zan iya ba, amman dai zan tafi ga amanar Haidar nan, dan Allah ki kular min dashi, sannan in kina bukatar wani abu ko na menene kina iya nemana ta waya kar kiji nauyin komai kinji ko?"

Kai kawai ta gyada dan jikinta babu karfi yace
'Shikenan daman sai batun karatu dan Allah kada ki bani kunya."
Nan ma kai ta gyada dan ta kasa magana zuciyar ta na kusa in tace zatai magana zata iya kuka ne tasani, yace
"Shikenan zaki iya tafiya."

Ta mike a ranta ba dadi, har ta kai kofa tace
"Bari na juyo na mishi kallon karshe kila sai shekara lokacin ko ina raye ko na mutu."
Tana juyowa suka hada ido dan shima ita yake kallo, sun jima suna kallon juna sannan ta dauke idon ta hawaye ya hau zubo mata a wajen ta durkushe ta saki wani kuka mai taba zuciya da sauri ya karaso ya durkusa a gaban ta yana fadin
"Menene?"

Kuka kawai take wanda daga zuciyar ta yake tahowa, wanda yake taba tasa zuciyar,
"Maryam!"
Ya kira sunan ta, ta dago kai tana kallon sa hawaye na zuba a guje ta mike ta fice a dakin ya zauna a wajen yana dafe kan sa.

Ranar abu biyu ne ya hadar mata ga tunanin dazu ga rabuwa da Yaa Aliyu, mutumin da ya zamo mata tamkar uba baya gajiyawa da kula da ita da kudin sa da aljihun sa da lokacin da komai nasa, yau zai tafi yai mata nisa a rayuwa. Ranar kwana tayi batai bacci ba wanda daga karshe ta mike tayo alwala tazo ta tada sallah. Hakika addu'a da tai ta rage mata damuwar ta sai dai ciwon kai da ya matsa mata dan daman ita ba dama ta shiga damuwa kanta zai farai mata ciwo, washe gari da matsananincin ciwon kai ta tashi wanda take jin kan kamar zai fadi ga damuwa da ta hadar mata, dama dama ma da tayi addu'a sai ta samu sassauci, amman da an kalle ta za'aga bata cikin walwala. Sanin halinta da rashin cin abinci yasa Ummi tazo ta kira ta har kasa suka sauka suka karya gaba dayan su, ita da Yaa Aliyu da ka kalle su zaka gane suna cike da damuwa abincin ma basuci wani na kirki ba suka barshi.

Tana dakin ta a kwance, Haidar ya shigo da gudu yace
"Adda Abbi zai tafi kizo ki masa bye bye."

Bata so fita ba amman ko dan tai masa bankwana na karshe ta leka, ta dauki hijab din ta, ta saka har kasa ta fito yana tsaye a falo yana duba wayar sa Ummi na masa magana ta sauko dukka kallon ta sukai, ta sunkuyar da kai kawai ta fita, bangaren Inna ta nufa Aliyu ya kalli Ummi yace
"Ummi me yake damun ta ne? Tin jiya naga sauyi a tare da ita tana da matsala taki fada min Ummi please ki tambayar min ita zan kira naji ko menene please Ummi ga Haidar nan ki kula min dashi."

"Insha Allahu Aliyu Allah ya bada sa'a da nasara ka gaishe min da su Yaya."
"Zasuji."

Yace
'Bari naje naiwa su Mami da Inna sallama."
"Ok Son."


Ya fita bangaren Mami yaje yai musu sallama sannan ya nufi bangaren Inna anan ya samu Maryam da Haidar bayan sunyi sallama Farouk da zai kai shi gidan Sitti daga nan su wuce airport yace
"Ko zaki zo muje tare?"

Aliyu ta kalla taga ya mike ya fita, Yaa Farouk yace
"Taso muje kiga gari ko Haidar?"
Kai Haidar ya gyada ta mike kawai tabi bayan su, a baya suka zauna ita da Haidar Aliyu, da Farouk suna gaba, tin da ta shiga bata ce kala ba sai jingin da kujera da tayi ta lumshe idon ta, a haka suka zo gidan Sitti suka sauka suka shiga nan suka gaishe ta Maryam ta zauna a can gefe a haka sukai sallama suka fita zuwa airport har da Najwa da akaje airport kowa ya fita ya rage Maryam dake jingine da kujera bama tasan anzo ba sai Aliyu dake dannan waya ya dago zai fita ya hango ta juyowa baya yayi ya kalle ta yace
"Maryam!"

Bata san ma yanayi ba sai da ya kira ta wajen sau uku sannan ta bude idon ta, kallon ta yayi da damuwa yace
"Tunanin me kike?"
Kai ta girgiza yace
"Ki fadan gaskiya."

"Ba komai Yaya."
Ta duba taga su Najwa a waje ta bude mota ta fice ya bita da kallo shima ya sauka suka shiga lokacin da zai tafi tana zaune Najwa da Farouk na tsaye kusa da Aliyu dake rike da Haidar, sai aka kira suna su kowa na masa sallama Haidar kuka ya saka, Farouk ya amshe shi yana lallashi Maryam na zaune tana kallon su, har zai juya sai ya hango Maryam tsayawa yayi yana kallon ta har Najwa ta juyo taga wa yake kallo? sai taga Maryam yake kallo kai ta kawar tana murmushi.
Kai Maryam ta langwabar sannan ta daga mashi hannu alamar bye bye hannu ya daga mata ya juya ya tafi zuciyar sa ba dadi.

Sai da sukaga tashin sa sannan suka koma gida, a cikin gate taga motar Muhammad tana fitowa ya kure ta da ido, Haidar yaje ya gaishe shi ya amsa ya karaso wajen Maryam da takasa takawa,
"Good afternoon princess na kasa samun nutsuwa tin jiya, kwana nayi ban bacci ba saboda bansan damuwar ki ba gashi ina kira wayar ki a kashe."

"Hmmm ina yini?"
"Daga gani na zaki gane ba lafiya ba."

"Me yake damun ka?"
"Abinda yake damun ki, ke kike jin ciwon abun amman nafiki jin zafin sa, kalle ki fa Maryam me yake damun ki daga jiya zuwa yau kawai kin canja saboda kinsa damuwa dan Allah fada min damuwar ki."
Kai ta girgiza kawai. Ya sauke ajiyar zuciya yace
"Wajen Ummi nazo."

Dagowa tai tace
"Ummi kuma?"
Kai ya gyada yace
"Ko bata nan?"
"A'ah muje sai na fada mata."
Suka shiga harabar gidan su, a nan ya zauna ya shiga ta samu Ummi a kitchen ta karasa tace
"Ummi wai Muhammad ne yazo wajen ki."

"Waje na kuma? Lafiya?"
Hannu ta ta daga tai nuni da itama bata sani ba, Ummi tace
"Jeki shigo dashi."
Ta fito falo ta yafa mayafinta, Maryam ta fita ta same shi zaune tace
"Ka shigo."

Ya mike ya shiga dakin a falo ya samu Ummi, ya zauna akan carpet, Ummi tace
"Taso ka zauna aka kujera."
"Ummi nan ma ya isa."

Tayi tayi amman yaki yadda, Ummi tace
"To shikenan."
Yai kasa da kai yace
"Ina yini Ummi?"

"Lafiya lou ya gida yasu Mamin taku?"
"Alhamdulillah!"

Sai yayi shiru, Ummi tace
"Lafiya Muhammad?"
"Lafiya Ummi, daman akan Maryam ne nazo."

Sai yai shiru Ummi tace
"Me ya faru tsakanin ka da Maryam din?"
"Ummi ni bansan me ya faru ba tin jiya da naiwa Maryam magana naga tana kuka, ina ta kiran wayar ta ma sam bata dauka ba kuma yau da na ganta ma tana cike da damuwa, Ummi ni da gaske nazo da son auren ta, dan haka dole na shiga damuwa na halin da na same ta a ciki, dan Allah Ummi ki tambayar min ita me nayi mata in nine da laifi sai nasan menene sai na bata hakuri."

Shiru Ummi tayi can tace
"To nima tin jiya Aliyu ya damu da halin da ta shiga, yai min magana kuma nima naga canji a tare da itan zama ne bamuyi ba amman insha Allahu zan tambaye ta duk abinda ake ciki zan neme ka na sanar da kai. Nagode da kular da kai akan ta Allah saka da alheri."

"Amin Ummi nagode."
Ya russunar da kai yace
"Zan tafi sai anjima."

"To ka gaida gida dasu Mamin."
"Zasuji nagode."
Ya mike ya fita. Ummi ta mike ta koma kitchen ta cigaba da aikin ta.

Maryam dake waje zaune jiran sa taga ya fito ta mike tana kallon sa, ya kalle ta yace
"Zan tafi."

"Tin yanzu?"
"Kina so na zauna ne?"
Shiru tayi yace
"To bari na tafi sai munyi waya."

Kai tai kasa dashi tace
"Ka gaida gida."
Ya juyo yana kallon ta, ta juya tai ciki da sauri.


*
Da dare Ummi ta samu Maryam kwance akan gado tai shiru ta kurawa waje daya ido, har ta zauna bata san ta shigo ba sai da ta dafa ta sannan ta juyo da sauri, ganin Ummi yasa ta sauke ajiyar zuciya, ta matso da kanta ta daura akan cinyar Ummi tana fadin
"Ummi yaushe kike shigo?"

"Kina can tunani."
"Ba tunani nake ba."

"To me kike?"
Shiru ta danyi sai kuma tace
"Ummi Yaya fa?"

"Ga tambayar da nake miki kina min wata ko?"
Shiru tayi, Ummi tace
"Tashi ki zauna muyi magana."

Tashi tayi, ta zauna Ummi ta kalle ta tace
"Dazu Muhammad yazo kuma akan ki ne. Me ya faru?"
Hawaye ne ya hau zubo mata Ummi tace
"Ni ba kuka nace ki min ba."
Hawayen ta hau sharewa. Ummi tace
"Tin jiya Yayanki ya lura da kina cikin damuwa, kuma nima naga haka, ki fada min me yake damunki?"

Shiru tayi, Ummi tace
"A duniya wa kike dashi, da zaki fadawa damuwar ki sama dani?"
Kai ta girgiza tace
"Babu."

Ummi ta kama hannun ta tace
"To fada min me yake damun ki?"
Kuka ta fashe dashi ta rumgume Ummi, Ummi ta hau shafa bayan ta tana fadin
"Fadamin damuwar ki shi zai kawo karshen damuwar ki, domin zanyi iya yi na ganin na cire miki damuwar ki, ko da zan rasa komai nawa ne, ki fada min me kike so? Me yake damun ki?"

Shiru tayi Ummi tace
"Ko Muhammad din ne bakya so?"
Shiru Maryam tayi kawai, Ummi tace
"Fada min kinji yar albarka."

ο»ΏHawayen idonta ta goge tace
"Ummi ina mantawa dani ko wacece saboda yadda kuke bani kulawa wannan yasa bana damuwa da tina asali na, Ummi kin dauken tamkar yar cikin ki, kin bani so da kauna da kulawa gareni da abinda nazo muku dashi duk family din ku, kun dauken yar uwa bakwa nuna min bambanci da ya'yan ku wannan ya mantar dani rayuwata da koni wacece bana damuwa da komai da kowa."

Ta shige jikin Ummi wani kuka yana kara taso mata, hawaye take wanda yake fitowa tin daga kasan zuciyar ta, ajiyar zuciya ta sauke tace
"Ummi a jiya duk aka dawon da abinda na manta, a jiya aka dawo dani haiyaci na a jiya komai ya dawo min, naso a jiya na tino da kowa nawa amman sai dai tino dani din da akai bai sa na tina abinda ya mance a kwakwalwata, Ummi...."

Sai tai shiru tana ajiyar zuciya kukan take so tayi amman yaki ya fito, ido ta runtse jin wani abu na damun ta a kasan zuciyar ta, Ummi ta hau shafa bayan ta tana jin damuwa akan halin da Maryam take ji, ita kanta ciwo take ji, zatafi kowa son sanin asalin Maryam amman tayaya ta ina zasu fara ko Bauchi zasu koma suyi cigiya tinda anan suka samo ta. Maryam ta kalla ganin ta dan samu nutsuwa sai ajiyar zuciya take saukewa Ummi tace
"Ki daina damuwa mune komai naki, mune iyayen ki, yan uwanki, komai naki ki daina damuwa kinji daughter."

Kai ta gyada Ummi tace
"Yauwa waya tada miki wannan abun?"
"Ummi a baya bana tunanin aure zai gagareni amman a yanzu ina tunanin ni da aure har abada saboda babu wanda zai auri mara asali, nasan duk wanda yazo neman aure na dole yaso sanin asali na, Ummi to tayaya zan yi aure a haka, ga yaro a tare dani, shin wasu wane kallo zasuyi min da yaro na, Ummi tayaya zan aure, a baya na zata zamu sasanta da Muhammad, sai dai haduwar mu dashi yasa ya dawo dani haiyaci na, Ummi jiya yaso sanin halakata da Yaa Aliyu wanda daga nan dole yasan wacece ni? Ummi yakamata Muhammad yasan wacece ni, dan zan bata masa lokaci ne, yadda yake so na zai shiga wani hali tin a jiya ya fara bani tausayi yadda yake kirana kiga fa yau haka ya taso yazo wajen ki akan sanin me yake damu na. Ummi ya zanyi to hakan ai shine yasa na fara janye jiki na."




*Allah ka yafe mana kasa muyi kyakyawan karshe Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum*


Barka da hutun karshen mako.

*Antty*
[10/31, 09:18] Maryam S IndabawaπŸ₯°: πŸ’—πŸ’— *MATAR HAIDAR* πŸ’—πŸ’—
Page 12

By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW


*Bismillahir Rahmanir Rahmin*

*Happy Birthday Our Autah Hauwa'u Yasmeen wish your more benefit years ahead, Allahu ya kare ki daga duk sharrin abun ki, Allah ya buda miki kwakwalwa ya baki miji na gari mai son ki, Allah ya raya ki yasa ki zama mahadaciyyar Alkur'ani Allah yasa muyi alfahari dake, addini yai Alfahari da, really love you my lovelly sister. HBD once again* πŸŽ‚ πŸŽ‚ πŸŽ‚



*
"Shikenan na gane matsalar da aka samu tin daga wajen su Abba ne ya kamata su farai masa bayani in yasan wacece ke shikenan, naji anan anyi ba dai dai ba, amman ki daina fadar ba zaki aure ba, menene aibun ki, ina da yakinin duk daga inda kike kina da asali da tsatso mai kyau, a halaiyar ki menene marar kyau, kina da hakuri tarbiyya ilimi ga hankali me za kuma a nema a wajen ki, ki bar damuwa da izinin Allah zaki tuna da kowa naki zaki ga iyayen ki kuma zaki aure ki kara haihafa dan Allah ki daina kuka da saka damuwa, ko Muhammad yaki ki wani zai zo ki duk aibun ki bare ke baki da wani aibu dan haka kiyi hakuri ki cire damuwa kinsan kina da ciwon zuciya ko so kike in rasa ki, kina zaton in na rasa ki wane hali zan shiga, ban taba haihuwa ba sai gashi Allah ya hada ni da yara biyu a lokaci daya ni me zanyi to nagodewa Allah na amshe ku to kema ki godewa Allah kuma mu kara tashi da addu'a zamu kara komawa asibiti a duba ki muga ko za a samu wani cigaba da yaddar Allah zakiga iyayen ki da yan uwan ki, ki daina kuka kinji?"

Rumgume Ummi tayi kawai tana sauke ajiyar zuciya. Ummi ta shafa bayan ta tace
"Sorry kinji Daughter."
A haka bacci ya dauke ta, Ummi ta dade a dakin sannan ta mike ta rufe mata dakin.

Daki ta shiga ta zauna tare da zuba tagumi, wayar ta ce tai kara tana dauka taji muryar Aliyu, ta sauke ajiyar zuciya tace
"Son ka sauka lafiya?"

"Lafiya lou Ummi ya gidan? Ina Maryam"
"Tana nan kalau."

"Masha Allah. Ummi kin tambaye ta?"
"Aliyu ba yanzu ka sauka bane kaje ka kwanta ka huta ko?"

"Ummi kar ki damu ki fada min me tace miki? Maryam na cikin damuwa Ummi bana son ya taba mata lafiyar ta please Ummi ki fada min."
"Shikenan yanzu kaci abinci?"

"A'ah Ummi bana jin yunwar Ummi."
"To shikenan akan batun wanda yazo neman auren ta ne."

"Cewa tayi bata son sa?"
Ya fada da sauri, Ummi tace
"Ba haka bane, bansan me ya mantar da Abba ba bai masa bayani akan wacece Maryam ba......"

Da sauri ya katse ta da fada yace
"Cewa yai baya son ta dan bata san iyayen ta ba?"
"Haba Haidar cool down mana, ba haka bane, yaso yaji wani abu akan ta ne."

"Bashi da hankali yaje yai bincike mana a wajen ta zai ji lallai...."
"Aliyu ba haka bane ya tambaya ne kawai."

"To me yace akan haka?"
"Ba haka bane Aliyu, i think ma ita bata bashi amsa ba, shine abinda yake damun ta dai."

"Shine take kuka dan kada yace baya son ta, ce mata akai ba zata samu wanda yake son ta ba haka? Menene da ita da za a 'ki tan?"
"Aliyu dole ta damu ai."

"Akan me? Akan me zata damu? Dan kada ya guje ta? Wai yaushe ta san shi ma da zata saka shi a zuciyar ta haka? In ba zai iya ba ya kyale ta mana me zatai da shi itama, ai tafi karfin sa, Ummi in ta tawa ce a hanata kula sa in har zai na saka mata damuwa bana so sam"

"To menene na daukar zafi ne haka, ai laifin mune da bamuyi masa bayani ba zanwa Abban ku magana sai ai masa magana ya sanar dashi in yaga yana so to in baya so ni nasan wani zai zo mata insha Allahu."
"Is better dai."

"To kaje ka huta."
"Sai da safe."
Ya fada ya kashe wayar sa dan ransa ba karamin baci yai ba, kwanciyya yai akan gadon yana dafe kansa da yaji ya dau zafi, kila fa yanzu tana can tana kuka akan wani can yazo ya tada mata da hankali yasa mata damuwa. Mikewa yai ya dauki wayar sa, layin Maryam ya fara nema amman sai aka ce masa a kashe take kira ya kara yi same a kashe take wayar yai cilli da ita, ya mike ya shige ban daki. Yana shiga ya sakarwa kan sa ruwan ya jima a karkashin shower ruwa na zubo masa amman bai bar wajen ba, sai daga baya ya fito daure da towel, jallabiyya ya dauka ya saka, ya hau kan sallaya dan yayi sallah yana idarwa yaji ana knocking budewa yayi yaga Yasmeen yar yar Ummi ya saki murmushi yace
"Baby Yasmeen."

"Big bro Momy ce tace wai kazo kaci abinci."
Hannun ta ya kamo yace
"Am not hungry dear."

"But Big bro u having eat any thing since u came."
"Yess Baby i take something there."

Kai ta gyada ta juya ta fita, komawa yai ya kwanta, bai jima da kwanciyya ba yaji ana knocking kofa kamar ba zai tashi ba amman jin muryar Antyn sa, yasa ya mike yana budewa ya koma ya zauna a gefen gado, Momy ta shiga tana kallon sa, ta jima a tsaye har sai da ya dago yana kallon ta sannan ya dan saki fuska yace
"Momy nayi laifi ne?"

Zama tayi akan resting chair dake dakin tace
"Me yake damun ka? Tin zuwan ka na gane kana cikin damuwa."

"Momy zuwan ne bana so kwata kwata."
"Oh wajen namu ne baka son zuwa."

"A'ah Momy in wajen ku ne nasan zanyi two to three week na juya amman yanzu shekara fa, ina da abubuwa da nake son yi a can da yawa."
"But Aliyu naga kai ka nemi tahowa ko?"

"A lokacin da na nema basu ban dama ba sai a yanzu da bana so."
"To ka daina damuwa kaji kayi addu'a Allah yasa zuwan naka a wannan lokacin shine mafi alheri, ka sani ni ba zan yadda da rashin cin abinci ba, balle ka koma rame ayi zaton bana kula dakai ko da dura sai kaci kaji ko?"

"Momy naci abu a jirgi fa yanzu hutawa kawai nake son yi."
Mikewa tayi tace
"Ni dai na fada maka za a kawo maka ko tea ne ka sha."

Ta juya ta fita, kansa ya dafe yana mai lumshe ido, Basma Yayar Yasmeen ce ta shigo da tray a hannun ta, dagowa yai ta ajiye akan stool ta matso masa dashi gaban gado, dagowa yai ta zauna tace
"Big bro ina ta zuba ido ka fito amman shiru?"

Murmushi ya saki yana fadin
"Na gaji ne."
"Yasu Sitti?"

"Suna lafiya suna gaishe ku."
"Big bro dan kai ta tafi kaima kuma ka dawo."

"Ni ba jimawa zan ba zan koma"
Tai murmushi tace
"Bikin Anty Najwa?"

"Kila."
Ganin bai son surutu yasa ta mike tace
"To sai anjima."

"Alright."
Ta mike

Please Login or Register in order to submit comment