Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sauki!"
Ta amsa da amin a zuciya. Sannan tace
"Kina jin dadin nan din ne?"

Kai ta gyada mata tace
"Ko dai zaki zo daki na?"
Kai ta gyada! Tace
"To taso muje kinji!"

Ta mike Inna ta fita Maryam tabi bayan ta. A kasa suka samu Aliyu bata kula shi ba ta yi gaba Maryam ta kalle shi sannan tabi bayan inna. Kai ya jingina da kujera yana mai lumshe idon sa. Suna shiga tace
"Kinga dan dakin nawa ko? Zauna akan kujerar kinji!"

Ta zauna tana bin dakin da kallo kamar dakin amarya ga kyau ga tsafta. Inna tace
"Me zan kawo miki?"
Kai ta girgiza. Inna tace
"Ki saki jikin nice mahaifiyar wanda ya kawo ki gidan nan su hudu na haifa Baban shine babban wannan na dakin da muka baro wai shi Dr sunan sa Aliyu baban nasa shine babba sunan sa Suleiman sai wanda kike wajen matar sa, Usman sai Takwarar ki mai sunan mahaifiya ta wacce ta mutu tin suna yara, sai autar su Nusaiba dake aure acan kasashen waje. Su uku suka rage min amman alhamdulillah ina jin dadi kamar me ya'ya goma dan suna kulawa dani.

Babar Aliyu uwa da uba daya suke da wacce kike wajen ta Aisha ita kuma sunan ta Hauwa ya'yan ta hudu Aliyu ne babba sai mata guda uku ta aurar da biyu Asiya da Hannah daya tana can makarantar kwana me suna Najwa, sai abokiyar zaman ta Barira wacce ta haifi ya'ya biyu Umaru da Bilkisu.
Sai Aisha wacce da ta haihu yaran suke mutuwa ta haifi ya'ya biyar amman duk babu mai rai.
Wannan yasa take rike da Aliyu duk da dai tin kan ta fara haihuwa yake wajen ta dan tana son yara gashi Allah bai bata ba.

Sam Barira bata da dadin zama ta saka Aisha a gaba yadda ta tsani Aisha ko Hauwa kishiyar ta bata tsana ba na rasa dalili ni kuma Allah ya dauran son Aisha dan yarinya ce mai tarbiyya da ladabi ga kyauta ita ta koyawa Aliyu shiyasa hannun sa yake a bude dan duk safiyyar Allah, in zai fita sai ya ban kudi yadda yake min tamkar ni na haife shi bar shi dai da miskilancin sa. Sai dan banzan kwadayi a cikin sa. shi kuwa Farouk sai kyale kyale kamar me haka kullum yake kamar mace ba shi da aiki sai surutu inya zauna ya cikan kunne to kinji kadan daga yan gidan a sannu zan na fada miki irin rayuwar da muke ciki wata ma da idon ki zaki gani."

Murmushi Maryam tayi Inna tace
"Oh na manta ban fada miki siriki na Abubakar ba mijin Nusaiba wacce nace suna waje yaron kirki kenan wallahi uwa ya dauken yana sona ya'yan su uku da Ammar, Widad sai Muhsin."

Kiran sallah aka tada Inna tace
"To kinji sallah tashi muje kiyi alwala kizo muyi sallah nayi dambu zaki ci ai ko?"
Tin da ta samu ciki yau ne aka fadi abu taji tana son ci sai dai tasan in taci me zai biyo baya.

Bandakin Inna ta kai ta wanda yake a wanke a goge tas dashi. Alwala sukai anan falo sukai sallah bayan sun idar Inna ta zauna tace
"Ina wannan Aliyun da kika gani to ba fa aure ne dashi ba yayi aure shekara biyar kenan da mutuwar matar amman yaki ya sake auren ni tsoro na daya ma kar muje aljanna ce ta kuma aure shi."
Aliyu ne ya shigo wanda tin daga bakin kofa yake jin muryar Inna ya shigo da sallama ya samu kujera ya zauna.

Ta kali Maryam tayo kasa da kai cikin muryar rada tace
"Kinganshi ko?"
Kai ta gyada Aliyu ya dauke kai. Inna ta mike tace
"Bari na kawo mana abinci!"

Ta shiga kitchen ta hado musu abinci kowa a plate din sa. Ajiyewa Maryam tayi tace
"Allah yasa yai miki dadi!"
Ta zauna ta fara cin nata tace
"Ai dai ba nama bane bare kace na maka rowa."

Maryam ta dauki spoon ta dibi dambun Aliyu ta kalla da yake kallon ta. Maida spoon din tayi ta tura masa abincin kai ya girgiza sai kuma ya mike ya dauki plate din ya kalle ta yace
"Tashi muje kici a can kisha magani."

Bai jira jin ta bakin Inna ba ya fice. Inna tace
"Oh kada ta zauna a waje na kenan lallai Aliyu!"
Maryam ta mike ta kalle ta, tanaiwa mata alamar zata dawo ta fita. A hankali ta fara tafiya zuwa sashen su.

Farouk da ya dawo zai je sashen Inna ne ya kusan yin karo da ita dan waya yake dannawa bai kallan gaban sa, da sauri taja baya, ya dago da sauri yana ganin Maryam yai baya da sauri yana hade fuska yace
"Menene haka bakya kallon gaban ki ne?"

Hannu ta hade tana bashi hakuri, wani kallo ya watsa mata ya bar wajen da sauri, itama da sauri ta nufi sashen Ummi tana waiwaye. Aliyu ta sama a falo ya nuna mata kan kujera ta karasa ta zauna ya mika mata maganin da ya ballo sannan ya bata ruwa. Amsa tayi ta fara sha tana sha tana hawaye dan bata son shan magani. Bayan ta gama ya kalle ta yace
"Me kike so ki ci?"

Plate din da ya shigo dashi na dambun da Inna tayi ta kalla, yace
"Zaki ci wannan ne?"
Kai ta gyada ya kalli dambun yace
"Kar ya saki amai fa!"
kai ta girgiza alamar ba zai sa ta ba

Daukowa yayi ya dauki spoon yai cokali daya, yayi dadi yaji gyada da zogale dan haka ya mike mata, amsa tayi sai kuma ta mika masa tai masa alama da yaci. Kai ya girgiza yace
"Ci abinki!"
Diba tayi taci cokali uku taci ta ajiye dan ji tayi ya tsaya a wuyan ta. Ruwa ta sha ta koma ta kwanta a gefe.

Ya kalle ta yace
"Har kin koshi?"
Kai ta gyada kawai ta lumshe idanun ta. System din sa ya janyo ya cigaba da aikin da yake yana yi yana satar kallon Maryam dake kwance har bacci ya dauke ta.

A ransa yace
"Tana can ta cika mata kunne da hira ko wa yace mata hira take so yanzu hutu take bukata."
Ya dan saki tsaki yana cigaba da aikin sa. Yana zaune mai aikin su Baba Habi ta fito dan a bangaren su Mami take ita da sauran masu aiki ta karaso falon tace
"Dakta na gama ni zan tafi sai Hajiyar ta dawo."

"To Baba sannu sai anjima!"
Ta fita ya cigaba da abinda yake yana zaune akai sallah la'asar, Maryam ya tasa ya shiga yai alwala ya fita masallaci. Alwala tayi tai sallah ta dauki Alkur'ani tana karantawa. Hudu da kwata ya dawo kitchen ya shiga ya bude firij ya dauko Fresh Yoo ya dawo falo ya same ta tana karatu a cup din tangaran ya zuba ya fara sha yana aiki yana kallon ta.

Bayan ya gama ya mike ya kunna TV ya koma ya cigaba da aiki, karfe shida saura Ummi tayi sallama a kofar dakin nata. Aliyu ne ya amsa Maryam kuwa sai bin kofar tayi da kallo. Ummi ta shigo ta karasa wajen Maryam dake ta kallon ta tace
"Sannu ya jikin?"
Da sauki tai mata nuni sannan ta kalli Aliyu tace
"Doctor ya gidan da me jiki?"

"Alhamdulillah!"
"Allah kara sauki!"

Ta mike tace
"Bari na hau na sauko!"
Ta mike tayi sama. Bata jima ba ta sauko ta canja kaya hannun ta rike da leda ta karaso ta dafa Maryam tace
"Sannu!"

Kai ta gyada ta kalle Aliyu tace
"Dr sannu da jinya Allah ya saka da aheri!"
"Haba Ummi sai kace wani abu nayi ai is my job!"

"Allah maka albarka!"
"Amin."

"Me zamu dafa ne?"
"Ummi just do sometime simple dan naga kin gaji!"
Maryam ta kalla tace
"Daughter ke me kike son ci?"

Kai ta girgiza ta kalli Aliyu tace
"Me taci ne yau?"
"I can say nothing since she just eat three spoon of dis thing!"

Ya nunawa Ummi plate din da ya rufe na dambu. Ummi ta bude tace
"Wa ya bata?"
"Kema kin sani. Inna ce."

"Maryam to bakya so?"
Kai ta gyada ta kalli Aliyu tace
"Kai fa?"
Baki ya tabe ya girgiza kai.

Ummi tace
"To ni bari naci da a zubar sai na girka ko supagette ce!"
Ta zauna ta ci sannan ta shiga kitchen ta wanke yalon da ta siyo sannan ta fito ta ajiyewa Aliyu da Maryam ta koma kitchen dan yin aiki. Daya Aiyu ya dauka ya mike yabi bayan ta.

Tana aiki suna hira akan aikin ta yawanci yace
"Ummi yanzu ya za ayi da yarinyar nan?"
"Name fa?"

"In zaki aiki da safe wajen wa za a barta!"
"Ba matsala ko da Baba Habi na barta kan dai mu dawo."

"Ummi tana bukatar kulawa fa."
"To Aliyu ya za ai?"

"Shekara ta kusa karewa gashi ban dauki hutu ba i think, i am going to take it now dan na kula da ita sosai dan akwai magani da allurar da na daura ta akai na matsalar rashin maganar ta ne me kika ce?"
"Hutun ai ba zai fi 1 month ba Son!"

"Yes is just one month Ummi! But by then nasan cikin ya kara girma since yanzu yana four month ina sa ran in ya kara kwari zai rage bata wahalar nan me kika ce?"
"Bansan me zance ba Aliyu, my son u are such a kind person Allahu ya biya ka ya baka lada yai maka albarka Amin!"

"Amin ya Hayyu ya Qayyum thank you so much Ummi!"
"U are always welcome my son!"

"Ramadan remain three week fa!"
"Allah nuna mana zaki Umrah ne?"

"Tayaya zan tafi na bar Maryam.".
"Sai ku tafi tare!"

"Ba wahala?"
"Mu bari muga yanayin jikin ko tinda goman karshe zamu tafi."

"Shikenan! Abbah naji yace in anyi 15 zai tafi shima yai min magana nace Maryam."
"Insha Allahu by then jikin ya kara sauki."

"Allah ya yadda!"
"Amin!"
A haka take girkin yana taya ta aiki har suka gama fried supagette da papper chicken suka jere a dining. Maryam kuwa taji dadin yalon taci da yawa. Tana zaune su Ummi suka gama. Aliyu ya shiga yai alwala ya tafi masallaci Ummi da Maryam sukai sallah anan falo.



*Allah ya jikan musulmai ya kyautata namu zuwan yasa mu cika da kyau da imani. Amin.*


💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 45

By
*MARYAM S INDABAWA*



*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)



Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


Karfe takwas da kwata Aliyu ya shigo tare da Abbah a falo suka zauna Abbah ya kalli Maryam yace
"Ya jikin?"
Tai masa alama da sauki. Sannan ya kalli Aliyu yace
" ya jikin nata kuwa?"

"Abbah da sauki sosai!"
"Allah kara sauki ta ci abinci kuwa?"

"Ai kasan sai a hankali zatana ci a sannu zata daina duk aman nan da rashin cin abincin insha Allahu."
"Allah ya yadda!"

Ya mike yai sama. Ummi tabi bayan sa, sun jima sannan suka sauko Abbah sanye da jallabiya daga gani wanka yayi dining suka shige. Ummi tace
"Ku taso muci abinci!"
Aliyu ya mike yana kallon Maryam dake girgiza kai. Yace
"Bazaki ci ba!"

Kai ta gyada ya nufi Ummi ta fara zuba masa ya dakatar da ita wai ya ishe shi. Ta kalli dan abincin tace
"Haidar what wrong with you!"
"Nothing Ummi!"

Abbah ya dago ya kalle su yace
"Me yake faruwa?"
"Abbah baya son cin abinci fa sam!"

Kai yai kasa dashi yace
"Ciki na ne ya cunkushe two days kuma ban jima da shan youghurt ba."
"Alright kadai na kiyayewa bana son rashin cin abinci da girman ka."

"Insha Allahu Abbah zan kiyaye!"
Suna Dining suka jiyowa Inna, Ummi ta mike tana fadin
"Barka da zuwa Inna!"

Aliyu da ya gama ya mike ya shige dakin sa. Inna ta bishi da kallo tace
"Yaron nan ya nuna min iko akan yarinyar nan yanzu dan Allah abinda yai min dazu ya kyauta."
Abbah ya mike yace
"Me Aliyun naki yayi?"

"A'ah naku dai. Wallahi yaron nan muna tare da uwata yazo ya dauke ta dan na bata abinci ni fa tsurfar sa na damuna ace mutu ba zai ci abincin gargajiya ba sai na zamani rayuwa ta tafi a haka kuwa. Yana yaro dai kato dashi amman yanzu rashin cin abinci da tsurfa duk tasa ya kare."
"Kiyi hakuri Inna."

"Wai me yasa baku da aiki sai nayi hakuri karfin ku Aliyun yafi da zai abu baza ana masa fada ba."
"Kiyi hakuri Inna za ai masa."
Ummi ta fada. Inna tace
"To Allah yasa."

Ta nufi Maryam da ta jingina da kujera tana fadin
"Sannu Uwata ya jikin?"
Dagowa tayi ta sakar mata murmushi tai alamar da sauki.

Inna ta mika mata cup din kunun da tayo mata tace
"Maza sha abin ki kan wancan bokan turan ya fito ya hanaki sha bana son ki kwan da yunwa sam!"
Amsa tayi ta kafa kai kadan ta sha ta ajiye cup din dan bata so tasha yadda zai saka ta amai.

Inna tace
"Yai dadi ko?"
Kai ta gyada. Inna tace
"Ai nasan zai miki dadi."

Ta mike tace
"Bari naje na kwanta sai da safe ko?"
"Allah bamu alheri Ummi da Abba suka fada."

Abbah ya bita suka fita. Suna fita Aliyu ya fito yana bata fuska. Ummi tace
"Zo nan!"
Aliyu ya karasa tace
"Bana so daga yau ka kara hanata cin abun Inna naga ba wani cin abincin take ba bare ace zai mata illa da ace bata ci ba ai gwara taci ko yaya ne ko? Kana gani anan baci take ba na Innan take dan tabawa kadan fa."

"To shikenan Ummi ba zan sake ba."
"Allah maka albarka."

"Amin ya hayyu ya qayyum tasha maganin ta taje ta kwanta ko?"
Da kan sa ya bata sannan ya nufi dakin sa.


*
Washe gari tare suka je asibiti dan Ummi ta tafi aiki dan haka tana kwance yana mata karin ruwa ya gama abinda zai yi karfe biyu bayan ya dawo daga masallaci suka koma gida lokacin Ummi ta dawo dan ranar da wuri ta dawo. A falo suka zauna gaba dayan su.

Karfe 5:15pm suna zaune Mami ta shigo dakin da sallama. Suka amsa ta karaso tana kallon Maryam. Mikewa Ummi tayi tana fadin
"Sannu da zuwa!"

Samun waje tayi ta zauna sannan ta kalli Aliyu dake daddana waya. gaisawa sukai da Ummi sannan Aliyu ya dago yai mata barka da gida. Ta amsa Maryam ta gaisheta da hannu ta amsa tana fadin
"Ya jikin?"
"Jiki da sauki!"
Tai nuni da hannun ta.

Ummi ta kalli Maryam tace
"Wannan sunan ta Mami ita Yaya tace kuma mahaifiyar Aliyu mata ga Yayan miji na kin gane?"
Kai ta gyada tana murmushi. Mami tace
"Ya jikin nata dai?"

"To da sauki zamuce amman fa ba abinda take ci, ko taci zata amayar ne."
"Ikon Allah irin cikin Maryam kenan. Irin wannan cikin wahala ne dashi wallahi Allah ya raba lafiya dai amman kinyiwa Inna magana a samar mata na hausa kuwa?"

" 'Dan naki zai yadda ne?"
Mikewa yayi ya kara waya a kunne ya fice. Da kallo suka bishi sannan Ummi tace
"Kisan sa sam bai yadda da traditional things din nan. Kina gani common dan abu Inna ke kawo mata amman sai yayi ta kwakwafi ya ga abun is nutritive in na fada ma sai ya fara cewa is not first class kaza da kaza, kinsan likitocin nan sam basu yadda da gargajiya ba su dai komai nasu ne mai kyau."

"Ai fa nasan za ai haka kin manta Maryam dauke ta yayi suka bar kasar amman kuma da Allah yayi ba rabon yaron da ita suyi rayuwa gaba ba gashi mun rasa su ba kinga kuwa dole ya saka ido sosai akan ta dan kar abun da ya faru baya ya sake faruwa."
"Haka ne Allah ya raba lafiya!"

"Amin. Abbi na son ya shigo yaganta but late yake dawowa ya fita da wuri amman yace na duba ta Allah bata lafiya."
"Amin Yaya!"
Ta mike tace
"Ni zan koma sai da safe!"

Mikewa Ummi tayi tabi bayan ta. Lokacin dan har bacci ya dauke Maryam. A bakin kofa suka samu Aliyu yana jin motsin su ya kara waya a kunne. Ummi ta karasa tace
"You better stop this pretending!"

Kai yayi kasa dashi ya nufi kofa ya shige da sauri, Dariya Ummi da Mami sukai. Sannan suka cigaba da tafiya suna tattaunawa akan aiki daga baya suka dawo maganar Maryam. A bakin gate din Mami suka tsaya suna cigaba da hirar. Suna tsaye motar Hajiya Mama ta shigo aka shige akai parking sai da ta jima a cikin mota tana kallon su sannan ta fito fuska a hade. Zata shige ciki.

Ummi tace
"Sannu da zuwa Hajiya Barira!"
Ko kallon ta batai ba ta shige. Mami tace
"Ai maganin ki!"

"Yaya ni ba zan iya gaba da ita bayan babu kyau."
"To ai sai kiyi tayi."
Ummi tai murmushi tace
"Bari na wuce sai anjima!"

"To sai anjima!"
Mami ta fada tai ciki Ummi ta nufi sashen ta.


**
Washe gari Ummi a gida ta zauna da Maryam dan yau da amai ta tashi zuciyar ta tai ta tashi da Aliyu yai mata allura ya dan lafa bayan ya tafi aiki kuma sai abun ya kara gaba ga ciwon ciki ga kirjin ta da take ta kuka dashi. Wannan yasa ba shiri Ummi ta dauke ta suka nufi asibiti.

Yana zaune a office yana tunanin ko a wane hali Maryam take ko ya jikin nata. Wayar sa ta hau kara dauka yai ya duba yaga Ummi ce take kiran sa. Dauka yayi yace
"Ummi ba dai jikin nata bane."
"Gamu nan karasowa asibiti!"

"Sai kun karaso!"
Ya fada ya mike yafita ya fara zagaye parking space yafi minti ashirin a wajen duk motar da zata shigo sai ya kalla dan yadda ya kafe bakin gate din da kallo. Yana tsaye motar Ummi ta karaso da tai parking ya karasa ya bude baya inda Maryam ke kwance dafe da kirji tana juyi. Ummi ta fito ta zagayo ta kamata wasu nurse biyu suka karaso da kujerar tura mara lafiya aka daura ta akai office din Aliyu suka nufa gaba dayan su.

Kan suje har wasu likitoci sun shiga suna jiran su suna zuwa aka rufa akan ta. Allura sukai mata ta samun relief sannan suka farai dubata.

Aliyu na tsaye ya kasa komai dan sam ya rasa me zai sun dauki kusan rabin awa kowa ya tafi yin gwaje gwajen da zasuyi da Maryam. Ummi da Aliyu na zaune duk sun kasa magana. Sai bayan wajen awa daya suka dawo da ita aka kwantar. Doctor Hauwa ce ta pkaraso tana fadin
"Doctor gaskiya jikin ta ba kwari Sam rashin cin abincin ta yana neman illata ta da babyn cikin ta ga ulcer da take da ita. Daga ita har babyn are suffering!"

Ta mika masa result din ya amsa yana kalla, Doctor Lukman ne ya shigo da file a hannu ya samu waje ya zauna Yana fadin
"Doctor Ina yan uwan ta yarinya nan she is in danger fa, abun yai yawa ga ciki, ga hawan jini, ga ciwon zuciya sannan babban illa ne ga mai ciki fa..."

Ya fada cikin damuwa da halin da Maryam take ciki. Kai Aliyu ya dafe ya amshi file din yace
"Thank you all doctor Allah saka. Zan dau hutu na yau insha Allah zan kula da komai, komai zai zo da sauki."
"Allah Kara sauki!"

Suka juya suka fita. Ummi ta mike ta koma gaban gadon da Maryam take bacci, Ummi tace
"Son ina tsaro kar mu rasa yarinyar nan ba tare da taga iyayen ta ba."

Wani kwarin gwiwa yaji duk da zuciyar sa na karyewa shima wani lokacin a hankali ya mike ya karasa gaban Ummi ya kamo hannun ta yace
"Kada ki karaya Ummi na. Ki cigaba da addu'a zan tayaki da kula da ita sai yadda karfi na ya kare insha Allahu zata tashi da kafafun ta da bakin ta zata koma gida cikin aminci da izinin Allah."

Hannun sa ta matse a nata tace
"Allah ya yadda ya bamu sa'a!"
Ta fada hawaye na zubo mata. Ya saka hannu ya goge mata ido sannan ya ja mata kujera ya zaunar da ita yace
"Bari naje na amso magungunan da suka dace sai nazo mu tafi gida ko?"

"Ok!"
Ya fita. Ta kamo hannun Maryam tana kallon ta hawaye na zubo mata na tausayin ta. Yarinyar ta kuma ramewa gaskiya tana wahala. Hannu ta daura akan ta tana shafawa a haka Aliyu ya dawo ya same su. Ya karasa yace
"Bata tashi ba?"

"Eh!"
"Mu bari ta tashi sai mu tafi ko?"

"Eh!"
Ya koma kan kujera ya zauna yana kallon su. A haka aka kira sallah ya tafi masallaci Ummi tayi anan. Yana dawo ya samu Maryam zaune akan sallaya.

Zama yayi yace
"Ummi ta tashi kenan?"
"Eh har tayi sallah!"

"Zamu iya tafiya?"
Kai ta gyada ta mike ta kama Maryam ta zaunar akan kujera sannan ta ninke sallaya. Ta kama hannun ta suka fita Aliyu na binsu a baya.

A haka suka karasa parking space ya amshi key din motar Ummi ya bawa messenger sa akan ya kawo masa gida ya shiga tasa su Ummi a baya suka tafi gida. A main parking space yai parking ya fito ya zagayo wajen su Ummi ya bude musu kofa. Ummi ta fito rike da maryam. Dai dai fitowar Hajiya Mama daga gate din su kenan. Kallon su ta tsaya har Ummi tai gaba Aliyu ya mara musu baya da ledar magani.

"Wacece wannan kuma?"
Ta fada tana kankance ido ta ina zata san su waye wannan. Ciki ta koma da sauri ta dauki waya ta fara kiran Farouk. Yana dauka tace
"Kana ina?"

"Mama ina hanya akwai abinda kike bukata ne?"
"Da ka dawo kazo kaji ko?"

"To Mama."
Ya kashe wayar yana fadin
"Allah yasa lafiya dai!"

Da sauri ya shigo gidan ya nufi sashen su. Dakin Mama ya nufa ya same ta tsaye a bakin kofa tana safa da marwa da sauri ya karasa yana fadin
"Lafiya dai ko Mama?"
Juyowa tayi ta zauna akan kujera sannan ta kalle shi tace
"Zauna mana!"

Zama yayi ya zuba mata ido, tace
"Wata yarinya ce a gidan nan?"
"Gidan nan kuma Mama? yarinya kuma?"

"Eh a sashen Aisha take!"
Shiru yayi yana nazari. Mama tace
"Naga kamar bata da lafiya!"

"Ohhh wata yarinya ce!"
Ya fada yana ya mutsa fuska.
"Yar wajen wacece?"

"Mama gaskiya ban san ta ba duk yayan su Anty Umma na san su amman wannan ban san daga ina take ba."
"Ina son na san wacece ka tambayar min Aliyu!"

"Wanne Aliyu Mama? Kinsan Hamma ba magana yake so ba bare nai masa magana ya ban amsa wallahi ba zai fadan wacece ba."
"To ya za ai ina son nasan wacece?"

"Amman Mama saboda me? Ina ruwan ki dasu?"
"Ban sani ba."

Kai yai kasa dashi. Tace
"Tashi kaje ina son ka samon wacece yarinyar nan ko a wajen Innar kuce!"
Mikewa yayi ya mike ya fita. Ya nufi sashen inna yana fadin
"To ita Mama dan Allah ina ruwan ta da su bayan ba shiga harkar su take ba."

Inna na zaune tana cin gashin naman da tayi Farouk ya shigo da sallama. Dagowa tayi ta amsa tana fadin
"Umaru har ka dawo kenan!"
Zama yayi yace
"Eh ya gidan?"

"Lafiya ni kuwa su Aisha sun dawo daga asibitin ka kira min su dan Allah muji ya me jikin?"
"To Inna amman wai wacece yarinyar nan?"

Gyara zama tayi tace
"Aisha ce ta samo ta kasan Aisha da tausayi fa."
"Bangane ba Inna!"

"Kai fa haka kake da tambaya kamar dan jarida in kai shiru ma ai zan fada maka kasani. Ba ranan Aisha da Shehu sunje Bauchi ba?"
Kai ya gyada yace
"Eh yafi sati nawa da dawowar tasu ma."

"Yauwah to acan suka same ta."
"Kamar yaya kenan wai Inna?"

"Suna cikin tafiya suka kade ta daga nan shine fa ta suma to da tafarka kuma ba lafiya haka sukai jinyar ta na kwanaki wanda a jinyar suka gane ta samu matsala ta manta iyayen ta da komai. Abun dai kamar aljanu kamar asiri ga ciki mutum biyu take iya kira daga mijin sai mahaifiyar ta. To fa shine suka taho da ita Aisha ke dawainiyya da ita yarinyar kirki mai hankali da nutsuwa. To kaji Aliyu ke ta dawiniyya da ita. Yau dai jikin yaki yi tin safe take amai wannan yasa Aishan suka tafi asibiti har yanzu ban sani ba ko sun dawo."
Baki Farouk ya tabe, ya zaro waya ya fara dadananawa. Wayar ta Inna ta miko masa tace
"Ni dai nasan wayata da kudi bare ka wulakantani nace ka kira min Aisha kaki, danno min a wayata."

"Nifa bance ba zan kira ba!"
Fara neman layin Ummi yayi lokacin tana zaune Aliyu na sakawa Maryam ruwa. Wayar ta ce tayi kara Aiyu ya miko mata ta amsa ta kai kunnen ta.

Inna ya mikawa, Inna ta rafka sallama Ummi ta amsa tana fadin
"Inna barka da rana!"
"Yauwah Aisha ya jikin Maryam din?"

"Inna da sauki mun dawo ma yanzu."
"To madallah bari nazo naga jikin!"

Tashi tayi ta mikawa Farouk wayar dan ya kashe mata tare da fadin
"Tashi muje mu duba ta?"
"Inna muje kuma? Kije dai!"

Wani kallo tai masa sannan ta mike tace
"Sai kaje wallahi ka duba ta kila baka tabai mata sannu ba."
Ta yafa mayafi ta kalle shi tace
"Tashi muje!"








*Allah ya jikan mu, ya jikan musulmai ya kyautata namu zuwan yasa mu cika da kyau da imani. Amin.*



*Antty*
*Antty*[11/20, 12:32] Maryam S

Please Login or Register in order to submit comment