Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Mum ta kalle su tace
"Ba dai tafiya ba Maryam?"

"Eh wallahi!"
"Mum kati ta kawo ga naki dana Dad!"
Aisha ta fada.

"Masha Allah! Allah sanya alheri ya kaimu lokacin."
"Amin!"
Aisha ta amsa.

Maryam tace
"To Mum sai anjima!"
"To ki gaida Ammin taki!"

"Zataji!"
Suka fice ita da Aisha. Motar takarasa ta bude yana inda yake tace
"Yaa Haiydar!"

A hankali ya bude ido ya sauke akan ta murmushi ta saka masa ta shiga ta zauna wanda hakan yasa yaga Aisha dake bayan ta. Murmushi ya sakar mata yace
"Kawar Amarya."

"Na'am Yaa Haidar ina yini?"
"Lafiya lou ya gida yasu Mum?"

"Suna lafiya."
"Amman tare dai zamuje gidan su Rukaiyyan ko?"

"Ban fadawa Mum bafa."
"To jeki fada mata kizo muje ma dawo dake."

"To bari naje!"
Ta mikawa Maryam lemon ta juya tayi cikin gida. Kofar ta rufe tace
"Ga ruwa!"

Ta fada tana bude masa ta bashi, amsa yayi ya dan kurba sannan ya bata tasha kadan ya kara sha ya rufe. Lokacin Aisha ta dawo ta shiga baya suka tafi gidan su Rukky.

A compound suka same ta tana zaune a gefen gidan su inda garden din su yake tana ganin su ta mike tazo suka rumgume juna. Yaa Haidar ta gaisar sannan sukai ciki a falo suka sami Mom din ta suka gaishe ta, ta amsa sannan suka tafi dakin ta suna shiga mai aiki ta fara kawo musu lemo da kayan motsa baki.

Maryam tace
"Mu da zamu tafi!"
"Uhmm ke haka kike daga zuwa sai tafiya."

Murmushi tayi tace
"Sauri muke!"
Ta kwaso katin ta ajiye mata tace
"Kema ki basa su Sakina, Hibba, Izzatullah, sannan sauran ku sasanta yadda zaku rabawa sauran yan ajin mu, gana Mom da Dada!"

Ta bata amsa tayi tace
"To Aisha ya zamuyi?"
"Kinga kawai in zaki fita ki biyo ta gida mukai ko?"

"Eh hakan yayi gobe sai mu fara kinga lokaci ya kure ko?"
"Allah kaimu."

"Yauwah wai yaushe zaku taho?"
"In munzo ranar kamu shikenan ko?"

"Har sai ranar kamu please kuzo Talata mana!"
"Ba dai ranar Laraba kamu ba, Alhamis dinner, Juma'a daurin aure da yini da kai amarya so kinga muzo Laraba mu taho Friday ko?"

"Lallai ma ni Talata zaku zo ku dawo Asabar!"
"Kai Besty kin fiya rigima."

"So kuke na zauna ba kowa a tare dani kunsan bani da kowa dai sai ku ko?"
"To shikenan ya isa zamuzo Talatar amman sai yamma ko dare saboda zamu lalle da gyaran kai ko?"

"Kuzo da wuri mu tafi tare ko?"
"Shikenan zaki ji mu."

Ta mike tace
"To nidai na bar Yaa Haidar a waje fa."
" *Matar Yaa Haidar* Allah tabbatar da alheri!"

"Amin!"
Ta nufi kofa. Rukayya tace
"Ke bakici komai ba shima ba zaki kai masa komai ba."

Aisha ta dibar masa suka fita sukai sallama da Mom. Mota suka shiga suka maida Aisha gida sannan suka tafi gida. Yana parking ya kalle ta yace
"Nawa zan bayar kudin abubuwan ne?"

"Ka barsu zanyi magana da Ammi in akwai bukatar abu zanyiwa Abbi magana."
"Yakamata mu na hutar dasu Abbi by now zan turo miki kudi ko da bukatar su zata tashi, in kina bukatar dadi ki min magana."

Har ga Allah ta manta da tana da wani account dan ko kudin da aka bata 1m ma yana ciki tacewa Abbi ya amsa yace ta ajiye a wajen ta, bayan Yaa Aliyu da yake yawan saka mata kudi banda duk lokacin da yaji alert har in ya samu kudi tura mata yake.

"Tunanin me kike?"
"Na tuna ina da kudi ne Yaya ba sai ka turon ba zanyi amfani dasu nagode!"

"A'ah wannan hakki nane ki amsa kawai."
"To nagode Allah saka da alheri ya biya maka bukatun ka. Ya rabaka da iyayen ka lafiya."

"Amin *Matar Haidar* ki shiga gida ana kiran magariba bari naje masallaci."
"Ai mana addu'a!"

"Insha Allahu!"
Tayi ciki shi kuma yai alwala anan compound sannan ya tafi masallaci.


Washe gari tin safe aka farai mata gyara na musamman wanda daga daki sai daki ko babban falo bata fitowa duk abinda take bukata Biba ke mata ta kai mata. Wanda cikin kwana biyun nan ta kara haske sosai kirjin ta ya kara cikowa, kamshi kuwa har ya zauna a jikin ta duk inda ta zauna sai ya kama.

Kwance take akan gado lokacin karfe goma saura sanye take da wando three quarter da vest a jikin ta kan ta sanye da hula waya kare a kunnen ta tana fadin
"My kayi hakuri jibi zani lalle da gyaran kai sai mu hadu kaji!"

"Ba zan iya ba wallahi ba zan iya ba kawai ki fito in ba haka ba zanyi knocking Allah ko Ammi tace menene zance ke kika kirani gwara ma ki tashi tinda Ammi ta kwanta kizo ki bude ki fito naganki kawai."
"In ganina kake so kayi in hada mana vedio call!"

"No bana son ido cikin ido nake so na ganki!"
"Please....."

"Ma'ul Ayn kada kice komai kinsan dai ba kyau ko?"
Jikin ta ne yai sanyi dan daga yadda yai maganar ma kasan yana cikin damuwa. Mikewa tayi tace
"Shikenan ka taho bari na bude maka!"

"Ina kofar part din naku!"
"Toh!"



*Allah ya yafe mana ya jikan mu yasa muyi kyakyawan karshe amin*


MS INDABAWA
ANTTY

ο»Ώο»ΏπŸ’—πŸ’— *MATAR HAIDAR* πŸ’—πŸ’—
Page 17

By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW


*Bismillahir Rahmanir Rahmin*


Ta saka hijab ta fito tana sanda a hankali ta fito ta bude ta juya ta kalli kofa sannan ta rufo ta fito da sauri. Tana juyowa taji ya rumgume ta.

"Yaa Haidar ka bari a waje fa muke kada wani ya ganmu!"
"Ina ruwa na, ni dai tinda naga matata."

Tai murmushi ta tsaya kallon sa tace
"Ai ka ganni ko sai da safe!"
Ta juya zata shiga yai saurin kamo hannun ta wanda ya dada taushi kamar auduga, ido ya lumshe yace
"Kin dai mai dani kakanki ko?"

"Ah haba ina fa."
Hannun ta ya kai hancin sa yana shinshinawa tare da sakin ajiyar zuciya hadi da lumshe idanun sa. Yace
"Wannan kamshin fa? Wane irin turare ne haka?"

Hannun take son janyewa ya janyo ta jikin sa gaba daya yana son cusa kansa cikin jikinta dan yadda kamshin ta ke tada masa hankali. Idon sa ya gama rufewa ga kewar ta ga kamshin ta mai tada hankalin ya rikita masa lissafi. Jikin ta sai rawa yake na tsoro a hankali tace
"Yaa Haidar, Ammi fa!"

Da kyar ya sake ta yana mai da numfashi yace
"Wannan turaren ki daina saka shi sai mun tare kina ji ko?"
Kai ta gyada sai yai sauri ya juya yace
"Koma kije ki kwanta sai da safe!"

Yai magana muryar sa a sanyaye. Gaban sa ta dawo tace
"Menene Yaya nah."
Murmushin karfin hali ya sakar mata yace
"Ba komai!"

Ya kamo hannun ta ya bude kofa ya saka ta sannan ya rufo maimako ya koma dakin Alkasim sai kawai yayi gidan su dake gefen nasu Maryam.

Wanda a tsarin ginin da girman sa har yafi nasu Maryam girma da tsaruwa. Mai gadi yana kwance yaji knocking ya taso ya bude masa yana shiga ya wuce bangaren sa. Sanin ba anan yake kwana ba yasa bai rufe kofar ba kawai ya koma ya zauna.

Aliyu yana zuwa bangaren sa ya shige wanda yake kamar na wani magidancin dan komai akwai. Yana shiga ya fada bathroom din sa ya fada ya sakarwa kan sa ruwa ko zai samu saukin abinda yake ji amman ina kamar ana kara masa wutar sha'awar ta. Kan gado ya fada yana jin yadda jijiyar sa ta mikewa tana bukatar agaji. Ido ya runtse dan jin yadda marar sa tayi tauri kamar dutse.

Wayar sa dake cikin aljihun jallabiyar sa ce tayi kara da kyar ya saka hannu ya zaro wayar ba tare da ya duba wanda ya kira ba ya kai wayar kunnensa ya saki nishin wahala sannan yai sallama da kyar. Da sauri ta mike daga kwanciyyar da take ta amsa sallamar hadi da fadin
"Lafiya Yaya meyake faruwa ne?"

"Me kika ji *Matata* "
"Jifa muryar ka, ka fada min me yake damun ka."

"Ba komai fa."
Kuka ta saka masa tana rokar sa ya fada mata wanda kukan nata ke kara ingiza yanayin da yaje ciki sai faman nishi yake da danna marar sa yana mai hade kafafun sa.

"Dan Allah ka fada min!"
"Zan fada miki amman ki min alkawari zaki sama min mafita."

"Nayi Yaya zan sama maka nasan addu'a ce zan maka ka fada menene?"
"I need you *Matar Haidar* wallahi ina cikin wani hali Matata, ki taimaken ki gusar min da wannan yanayin da nake ciki dan Allah "

Hawaye ne yake zuba a idon ta, ta rasa me zata ce masa yace
"Kina ji na?"
Sheshekar kukan ta ya jiyo ya cije baki yace
"Ni nasan ba zaki iya ba, ciwo na ba naki bane ko? Damuwa ta ba taki bace ba ko? Shikenan sai da safe ki kwanta kiyi bacci."

Yana gama fadar haka ya kashe wayar gaba daya ya cilla ta gefe ya dinga fama shi kadai. Yana kashe wayar ta fada kan gado ta fashe da kuka a ranta take magana can ta dauki wayar tana girgiza kanta, ta fara neman layin sa amman a kashe. Da sauri ta mike ta saka hijab ta fita falon. Kofa ta bude tayi bangaren Yaa Alkasim tana isa ta tsaya ta kasa taba kofar tafi mintina sannan ta tura kofar a hankali taji ta a bude ciki ta shiga ba kowa a falo dan haka ta nufi kofar bedroom din sa ta fara knocking.

Alkasim dake bacci ne yaji knocking ya mike yana salati ya duba yaga ba Aliyu mikewa yayi ya fita ya bude kofar. Maryam ya gani tsaye kallon ta yayi yace
"Menene?"

"Ina Yaa Haidar?"
"Ina jin yana bandaki menene?"

"Ina son ganin sa ne!"
Ciki ya koma ya tsaya bakin kofa yace
"To kai kayi sauri matar ka na waje tana jiran ka."

Ya koma ya kwanta kawai. Maryam dake falo ganin kusan rabin awa yasa ta kara komawa tai knocking Alkasim yana bacci ya kuma mikewa. Agogo ya kalla yaga sha daya da rabi mikewa yayi ya kara fita da mamaki yake kallon ta wannan lokacin yace
"Menene kuma?"

"Ina yake?"
"Wa?"

"Yaa Haidar?"
"Bai fito ba?"

Kai ta gyada tana share hawaye komawa yai da sauri ya bude bandakin ba kowa dan haka ya fito yace
"Kila ya tafi gida fa."

"Yaa Alkasim dan Allah ka kira min shi mana."
Waya ya dauka ya fara kira amman a kashe ya dago yace
"Wayar tasa a kashe lafiya?"

"Muje ka kira min shi dan Allah."
"Dare yayi fa har sha biyu saura menene?"
Durkusawa tayi tana kuka tace
"Ni dai ka kira min shi."

"Zan kira shi amman kinsan menene tashi kije ki kwanta kar Ammi ta leko taga kofa a bude kinji in na kirasa zan zo sai mu taho."
Ta mike ya rakata har kofar part din su sannan ya fita amman sai ya kasa buga kofar gidan su Aliyu dan dare yayi kada ya tada musu da hankali ya jima a haka dai ya jingina da kofar ji yayi kofar taja baya ya shiga kawai ya samu mai gadi na ta baccin sa. Kai ya girgiza kawai yayi sashen Aliyu. Kwance ya same shi ko numfashi bayayi da sauri ya dago shi yana kiran sa amman ina bai ji. Ruwa ya debo ya shafa masa nan ma bai farka ba da sauri ya mike ya je ya taso mai gadi yazo ya taimaka masa suka sashi a mota ya tafi asibiti dashi yana zuwa aka amshi shi emergency, sai wajen daya sannan suka samu ya farfado allurai sukai masa sannan suka barshi dan ya huta take baccin wahala ya dauke shi.

Alkasim ya shiga ya zauna a kusa dashi karfe uku ya farka yaga Alkasim akan sa dakin ya kalla ya mike da sauri yana fadin
"Me muke anan? Tashi mu tafi."

"Aliyu baka da lafiya fa!"
"Ni lafiya ta kalou."

"To bari na kira Dr!"
Ya fita yaje ya taho da Doctor wanda abokin Aliyu ne yana zuwa yace
"Alhamdulillah jiki yai sauki ko?"

Kai ya gyada yace
"Dadin tama dai ka kusa aure amman da baka kusa ba wannan matsalar zata iya halakaka, kana kiyayewa!"
Kai ya gyada yace
"Insha Allahu."

Alkasim yace
"Me yake damun sa ne?"
Mikewa Aliyu yai ya fita. Dr yace
"Yana da matsananciyar sha'awa wacce take sa shi shiga wannan halin in ta motsa masa."

"Shege jarababbe ai na jima da gane hakan zan fadawa Abbi ai maza a daura auren kar ya mutu."
Ya mika Dr hannu suna murmushi yabi bayan Aliyu.

A mota ya same shi yana zaune kan sa jingine da kujera ya lumshe ido. Murmushi yayi yace
"Ashe jarabarce ta motsa ince zuwa kayi ka tadawa yarinya hankali dazu tazo tana tai min kuka sai na kira ka."

Bai motsa ba bare ya kulasa, Alkasim sai iya shege yake masa amman ya ki kula sa. Suna shiga ya wuce yai wanka ya shirya suka tafi masallaci. Shida suka dawo gida a falo ya kwanta Alkasim ya shige yana fadin
"Bacci nake ji wallahi."

"Wa ya hana ka bacci?"
Aliyu ya fada yana gyara kwanciyya kan three sitter.
"Au haka kace?"

Alkasim ya fada yana yin ciki ya cigaba da cewa
"Zaka sani ne."
Ido ya lumshe ya fara karatun Alkur'ani a hankali cikin muryarsa mai dadi da sanyi.


*
Maryam kuwa gaba daya ta kasa sukuni dan ba alamun Yaa Alkasim ta kira sa amman baya dauka wajen daya ta koma dakin nasa babu shi ba Aliyu daki ta koma ta zauna akan sallaya sai kuka. Haka wajen biyu ma ta kara komawa amman babu su kwata kwata. Karfe uku ma ta kara zuwa babu su. Daki ta koma ta dinga kuka dan ta rasa nutsuwa me yake faruwa ina Yaa Haidar ya tafi. Har aka kira sallah asuba ta tashi tai alwala tai sallah.

Ta na idar da azkar ta mike ta fito ba kowa a falo kitchen ta shiga ta gaisar da Ammi da Baba Ramma sannan ta fita ta nufi bangaren Yaa Alkasim tana bude kofa ta fara jiyo kira'ar sa, ido ta lumshe sannan ta shiga kwance ta ganshi akan three sitter da sauri ta karasa ta zauna a kasa gaban kujerar cikin muryar kuka tace
"Yaa Haidar!"

Idon sa ya bude a hankali ya sakar mata murmushi yace
" *Matar Haidar* "
Sai ya fara kokarin mikewa. Kallon sa tayi har ya zauna duk ya fada na lokaci daya.

"Ka yafe min Yaa Haidar!"
Hannun sa ya daura akan ta yace
"Na yafe miki *Matar Haidar* na yafe miki. Kin tashi lafiya?"

Hawaye ne ya zubo mata yace
"To menene na kukan?"
"Yadda kake so na, ni na bata maka na kasa kawar maka da bukatar ka duk da....."

Hannun sa ya daura akan bakin ta yace
"Kada kice haka ni nasan kina so na kuma kin damu da bukatata nasan dalilin ki na bijire min ba komai mun kusa mu zauna cikin inuwa daya wacce zamu kasance cikin nutsuwa nasan a lokacin zaki ban duk kulawar da nake so kada ki damu kinji sauran kwana nawa ne?"

Kai tayi kasa dashi, yayi murmushi yace
"Sauran kwana hudu ko?"
Kai ta gyada masa a kunyace yace
"Ina fatan kinyi bacci dai!"

Kai ta girgiza tace
"A'ah Yaya nakasa na kasa saboda bansan a halin da kake ciki ba nace Yaa Alkasim yaje ya kira ka amman bai dawo ba da tini nazo da kai na to kada Ammi tazo taga bana nan ne kayi hakuri!"

"Ba komai, *Matar Haidar* bata laifi kuma bana fushi da ita."
"Nagode Yaya nah!"

Ta mike tace
"Ban gaishe da Abbi ba bari naje!"
Ta nufi kofa mikewa yayi yabi bayan ta yana fadin
"Muje nima na gaishe sa."

Tare sukaje suka gaishe sa ya sa musu albarka dukkan su ya karai musu nasiha sannan ya sallame ta shi kuma ya zauna shi da Aliyu suna tattaunawa. Bayan sun gama ya dago ya kalli Aliyu yace
"Aliyu me yake damun ka ne?"

Kai ya dan shafa yace
"Ciki na ne ke ciwo da shi na kwana jiya."
"Allah ya sauwake ya kamata ka samu magani akan ciwon cikin nan."

"Insha Allahu Abbi."
Tare suka karya sannan yaje ya shirya ya tafi asibiti. Sai yamma ya dawo yana dawowa gidan su ya wuce yai wanka sannan ya nufi part din iyayen nasa. A falon Mamah ya samu Mamah da Abbah.

Zama yayi ya gaishe su. Mamah tace
"Har ka dawo?"
"Eh Mamah."

"Yau ana can ana kafi a gidan naka."
"Haka Ammi ta fada min dazu."

"Masha Allahu Baba na ka rike amanar yarinyar nan duk da nasan yadda kake son ta amman zaman tare dole a saba wata rana kayi hakuri da ita kaji ka dauke ta matsayin kanwa in tai maka laifi kaji?"
Kai ya gyada yace
"Insha Allahu!"

"Allah maka albarka."
"Amin!"

"Kaje ka gaishe da Umman taka?"
Kai ya girgiza. Abbah yace
"To kaje kaji dan albarka."

Kai ya gyada ya mike ya fita. Bangaren Umma ya nufa yana zuwa yai addu'a sannan ya shiga bangaren Umman tana falo zaune akan kujera kafa daya kan daya tana kallo. Yai sallama ta amsa ko kallon inda yake batai ba. Zama yayi yace
"Ina yini?"
"In ban yini ba zaka ganni? In ma fata kake na mutu to ka sani kai ne zaka mutu da wannan shegun kuma ka sani sai tarihin ka ya bace a duniya."

Bai tanka mata ba ya mike yace
"Na barki lafiya."
Ya juya ya fita yana girgiza kai da halin Umman nan tasu. Hakika yasan Mamahn sa na hakuri wannan yasa sam bai son zaman gidan dan in har yana gidan sai ya gaishe da ita abinda shi kuma baya so kenan dan da yaje sai ta bata masa ran sa da irin wadan nan maganganun.

Waya ya dauka yaiwa Maryam transfer dubu dari biyar sannan ya koma dakin Mamah acan yaci abinci har akai isha'i ya kara komawa. Mamah ta kalle shi tace
"Me yake faruwa ne yau?"
"Me kika gani?"

"Naganka a gida ne."
Yai murmushi yace
"Na fara missing Mamah na ne."

"Kai din da kake dokin a daura maka aure ka dauke Matar ka, katafi ka bar ni."
"Ah haba dai!"

Sallamar Alkasim ce ta katse masa magana ya shigo ya gaida Mamah sannan yace
"Ai na zata jikin ne?"
"Bashi da lafiya ko?"

"Jiya sai da mukaje asibiti amman da sauki ai."
"Yanzu nake masa ai nace yau lafiya yazo ya makalen?"
Mamah ta fada.

"Tsoron mutuwa yake kar ta dauke shi shine ya taho wajen ki."
"Ai mutuwa ba yanzu ba sai naga ya'ya na."
Aliyu ya fada.

Mamah tace
"Me.....?"
Da sauri ya mike ya fita yana dariya. Alkasim ta kalla tace
"Me yake damun sa ne wai?"

"Ciwon ciki ne amman an bashi magani ai."
"Kasan kuma bai fada min ba."

"Ai ba zai fada ba ko ita ma nasan bai fada mata ba."
"Aliyu kenan."

Haka suka dan taba hira sannan ya mike yai mata sai da safe dan har tara tayi. Dakin Aliyu ya nufa ya same shi har yayi shirin bacci zama yayi yace
"Anan zaka kwana kenan?"
Kai ya gyada yace
"To ni bari naje sai da safe."

"Allah tashe mu lafiya."
Yana fita ya fara neman layin Maryam, dauka tayi tace
"Yau ba ruwa na dakai Yaya!"

"Ya salam menayi kuma?"
"Yau baka neman ba sai zuwa naje dakin Yaa Alkasim baka nan."

"Naje aiki ne! Sai yamma na dawo ina gida me kike so?"
"In ganka kawai!"

"Kina ina to?"
"Ina falon Ammi."

"Bari nazo to."


*Gaskiya ina jin zan daina posting a whatsapp ace ba wani appreciation da kuke nunawa, always thanks ba wani comment kuma a haka kuke so ina muku two pages a rana, in har kuna son two pages a rana to naga ruwan comment nima nai alkawari daga gobe har na gama book din nan two page zan nayi amman fa sai naga comment, yawan comment yawan posting karancin sa ma zai na sai na gadama nayi posting, dan haka in kuna so naga sauyi. Ngd*


*Allah ka yafe mana kasa mu cika da kyau da imani Amin.*


*Antty*


ο»ΏπŸ’—πŸ’— *MATAR HAIDAR* πŸ’—πŸ’—
Page 18

By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW


*Bismillahir Rahmanir Rahmin*


Ya mike ya nufi kofa ya fita. Gidan ya nufa ya shiga Babban falo ba kowa dakin Ammi ya shiga ya same ta zaune gaban ta gashin nama da madarar Ammi zaune tana duba wasu kaya. Zama yayi ya gaishe da Ammi sannan ya zauna a gefen ta yana fadin
"Kayan dadi aka samu ashe!"

"Muci!"
Cikin sa ya shafa yace
"Na koshi!"

Tace
"Shikenan!"
"Goben zaku gyaran kai ko?"

"Eh!"
"Karfe nawa zan zo na kai ku.?"

"A'ah kaje aikin ka ko driver ya kai su."
Ammi ta fada.
"Ammi na dauki hutu ai!"

"Au to shikenan. Allah ya taimaka."
Ta mike tayi cikin dakin ta. Ya kalli Maryam yace
" *Matar Haidar* kinga Haidar din naki?"

Kai ta gyada yace
"Zan iya tafiya?"
Fuska ta bata tace
"Bamuyi hira ba fa."

"In na zauna kar naje....."
"Kar kaje me?"

"Shikenan!"
"Naga sako dazu Amman Yaya yai yawa!"

Hannu ya daura akan lips din sa masu taushi pink kala yace
"Kada kice haka sunyi kadan ma nake gani."

Tai murmushi jin Ammi zata fito ya mike yace
"Zanje na kwanta gobe wajen 10am zanzo sai mu tafi."
"Allah kaimu nagode!"

Har ya juya, sai kuma ya juyo ya kara kallon ta, mikewa tayi yace
"Muje na rakaka!"
Suka fita. Bakin gate taga yayi tace
"Ba anan zaka kwana ba?"

Kai ya gyada, idon ta ne ya kawo ruwa tace
"Saboda me to? Saboda jiya ko? Baka yafe min ba ko Yaya?"
"Na yafe miki *Matar Haidar* ni namanta da wani abu ya faru ma jiya, kawai ina hada kayana da wasu abubuwan ne me kike so na baki?"

"Ni da zaka kawo abin gidan mu in akwai abinda nake so in ka kawo na dauke."
"Shikenan sai da safen ko?"

Kai ta gyada ta daga masa hannu tana masa bye bye har ya juya ya fita. Juyawa tayi ta koma ciki. Dakin Ammi ta koma ta dauke kwanon dan kai wa kitchen Ammi tace
"Amman naga baki ci ba fa!"

"Ammi na koshi ne!"
Kallon ta Ammi ta tsaya yi tace
"Zo nan Maryam!"

Karasawa tayi ta zauna, Ammi ta bita da kallo sannan tace
"Meyake damun ki ne? Tinda kika dawo daga makaranta bakya cin abinci sosai ga tsurfar zabar abinci."

Cikinta ta shafa tace
"Nima Ammi ban sani ba."
Ta karasa magana tana hamma alamar bacci takeji.
"Je ki kwanta sai da safe."
"Allah tashe mu lafiya."
"Amin!"
Ta fita ta ajiye plate din sannan ta shiga tai wanka tare da brush tazo ta kwanta. Tana kwanciyya bacci ya dauke ta.


Aliyu na shiga ya isa kan gadon sa, kwanciyya yayi yana mai lumshe ido, juyi ya fara akan gadon wanda sam ya kasa baccin har wajen karfe dayan dare mikewa yayi ya shiga bandaki ya watsa ruwa yayo alwala sannan ya fito ya hau kan sallaya nifala ya fara wanda har karfe uku idon sa biyu yana karatun Alkur'ani. Sai da yaji an fara kiran sallah sannan ya mike ya kuma watsa ruwa ya nufi masallaci.

Ba mutane sosai ya shiga ya zauna yana karayin karatu, sai kusan rabin awa sannan Abbi da Alkasim suka shiga daga can aka kara kiran sallah sannan mutane suka fara shiga dan yin sallah, ana idarwa suka gaisa da Abbi sannan ya tafi. Alkasin ya zauna a gefen sa yana kallon sa yace
"Ahmad yana ta kiran ka baka dauka ba."

"Bansan inda wayar ma take ba, me ya faru!"
"Zancen zuwan sa ne."

Mikewa sukai suka fita, a kofar gida suka tsaya yace
"Me yace maka?"
"Ba zai samu damar zuwa bane saboda wani aiki da ya tasar masa aka tura shi wani waje kuma a cikin week din nan ake son ya kai report yace kayi hakuri da ya gama zai zo yaci girkin amarya."

Tsaki ya saki yace
"Yai zaman sa ma kawai dan rainin hankali."
Ya juya ya nufi gidan su. Dakin sa ya shiga ya kwata anan falo bacci ne ya dauke shi, takwas da rabi ya tashi ya shiga yai wanka da sabulun sa mai dadin kamshi. Ya fito ya shafa mai ya saka bakin wando da farar riga mai gajeren hannu ya saka turaren sa na Oud Kareem mai kamshi da dadi ya gyara sumar kansa wacce take a kwance ko da yaushe luf luf, agogo ya daura a hannun sa ya kalli fuskar sa karfe tara har da kwata. Wayar sa ya dauka guda biyu ya fita dasu a hannu.

Bangaren Mamah ya nufa yana tafe suna gaisawa da masu aikin gidan a haka har ya karasa bangaren Mamah, ba kowa a falon ta sai tashin kamshi da sanyin AC dake tashi.

Bedroom din ta ya nufa yai knocking kofar tana daga ciki ta amsa masa ya shiga tana zaune gaban mirrow tana daura dankwalin ta ya shiga. Har kasa ya durkusa ya gaishe ta, ta amsa tana dafa kan sa tare da saka masa albarka. Mikewa yayi yana fadin
"Me kike dafa mana?"

"Ni Abbahn ka na dafawa ba kai ba."
Yai murmushi yace
"Mamah sauran kwana nawa ne nima da zan tafi, kuma ko rabon Abbah ne ci zanyi ayi masa wani."

Ya fada yana fita, Murmushi Mamah tayi tabi bayan sa tana fadin
"Baka da magana sai ta tafiya kullum kace sauran kwana nawa ko? To ina fatan in ka tafi ba ka tafi ba kenan ai dole wata rana kana zuwar mana ko? Kuma kaci abincin dai wata rana ko?"

"A'ah Ma'ul Ayn ba zata barni ina cin abinci a waje ba, dan haka abincin ki sai da kallo Mamah!"
Ya fada yana daura kan sa a kafadar ta.

Please Login or Register in order to submit comment