Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gida, duk da uban sauron da suka yi yawa a wajen hakan bai hana bacci me nauyi sake daukarta daga zaunen da take a gaban shagon ba, bata kuma farka ba sai da kiran sallar asuba ya farkar da ita, ta dinga bin wajen da kallo, can ta tashi da kyar tana tafiya a hankali kamar iska zai hura ta, ta fadi ga wani ciwon kirji da ta tashi da, banda zugi da azaba babu abinda yake mata. masallaci ta samu a kasuwar tai alwala tai sallah sannan ta mike ta cigaba da tafiya.





*Allah ka jikan musulmai ka kyautata namu zuwan amin.*



*Antty*[11/13, 13:59] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 31

By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW

*Bismillahir Rahmanir Rahmin*

HML MY SISTER HASSANA ALLAH YA SANYA ALHERI YA BADA ZAMAN LAFIYA DA ZURI'A MAI ALBARKA. AMIN

Har karfe hudu ba Alkasim ba wayar Yaya Fadima, wannan yasa hankalin Ammi ya dan tashi, amman kuma sai tai zaton ko Alkasim ya riga ya bar gidan Yaya Fadiman ya tafi wani wajen, ita kuma tana can tana aiki kila shiyasa bata kira akan zuwan Maryam din ba.

Tunanin mafita take akan Maryam, tin da tayi sallah isha'i ta kasa tashi a wajen, ji tayi zuciyar ta ta karye so take ta tashi ta kira Fadima amman sai taji ta kasa tashi ta rasa me take ji, sallamar Alkasim shi ya katse mata tunanin da take, ta amsa ya shigo ya zauna a gefen gadon nata yana fadin
"Daga dakin Maryam nake naga bata nan ina ta shiga?"

Kallon sa tayi cike da damuwa, ta sauke ajiyar zuciya tace
"Dazu bayan kun kawo ta Abbin ku yace bai yadda ta zauna masa a gida da cikin da bai san uban sa, lallai sai taje ta nemo masa mahaifin yaron sannan ta zo a yanke musu hukunci."

"What? Abbi me yake so yace? Yana so yace Maryam mazinaciya ce?"
Kai ya hau girgizawa yana fadin
"Ko duniya zata taro akan cewa haka ni ba zan yadda ba, me Maryam ta sani?"

"Na shiga rudani da damuwa amman nace zan tura ta can Saudiyya wajen Ummun ku."
Kallon Ammi yayi yace
"To yanzu Abbi da yace ta bar gidan ina take so taje, meyasa idon Abbi ya rufe akan alamarin nan, ai dole abi komai a sannu bai ga halin da take ciki bane?"

Tagumi Ammi ta sauke, ya mike yace
"Ina yanzu ta tafi?"
"Gidan Fadima tin dazu nace ta tafi."

Da sauri ya juyo yace
"Tin yaushe?"
"Baku dade da kowa ta, yazo yai maganar lokacin ko azahar ba ai ba ta tafi."

"Ammi har bayan la'asar ina gidan Fadima fa, kuma Maryam sam bata je ba."
Ido Ammi ta zaro tace
"Bangane bata je ba, daukon waya ta na kira dai naji ko taje daga baya."

Wayar sa ya zaro ya fara neman layin Fadima tana dauka tace
"Tin dazu nake so na kira naji ya jikin Maryam ka same shi?"
Shiru yayi can yace
"Bata zo gidan ki ba?"

"Wa din?"
"Maryam."
Ya bata amsa. Kai ta girgiza tace
"Bata zo ba nan tace zata zo."

Wayar ya kashe ya kalli Ammi cike da damuwa yace
"Ammi bataje gidan Fadima."

"Anya Alkasim ko dai bata son ta fada ne dan Abbi yace kada taje masa gidan iyaye ko ya'ya tashi maza kaje ka gano min dan Allah."
Mikewa yayi ya dauki mukullin motar sa ya fita a gidan da sauri mota ya shiga ya nufi gidan Fadima.

Ba kowa a falo sai Ilham dake kallon TV ya shiga ya zauna ta karaso tana fadin
"Uncle ina yini?"
"Lafiya lou daughter ina Momyn ki?"

"Yanzu Dady ya dawo ta shiga ciki."
"To Aunty Maryam tazo yau?"

"Uncle an sallamota a asibiti, zan bika na dubo ta."
Fadima ce ta fito turus tayi ganin Alkasim tace
"Yaya lafiya?"

"Ammi ce ta aiko ni."
"To me ya faru?"
"Akan Maryam ne tace nazo na gani ko kin boye ta ne?"

Zama tayi cike da mamaki tace
"Bangane ba fa."
Fada mata komai yayi salati ta saki tace
"Na shiga uku to ina ta tafi wallahi Yaya Alkasim batazo ba ai sai bayan la'asar ka tafi kuma wallahi tin fitar ka ba wanda ya zo gidanan."

Da sauri ya mike yace
"Bari naje gidan Yaya Ummulkhairi Allah yasa can ta tafi."
Ya fita can ma da yaje ba Maryam ba alamun ta, gidan Yaya Zainab ma, wannan yasa ya kira Aisha bayan sun gaisa yace
"Maryam tazo nan ne?"

"An sallamo ta ne dazu naso na shigo to yau na tashi da zazzabi shiyasa ban shigo ba."
"An sallamo ta dazu bata zo nan ba kenan?"

"Eh!"
Rukayya ya kira nan ma ba wani good information take hankalin sa ya tashi,  a cikin daren nan ya dinga bin gidan yan uwa amman duk inda yaje ba Maryam hankalin sa ba karamin tashi yayi ba har sha biyu yana waje, Ammi taje neman sa ko ya dawo yafi a kirga amman shiru duk ta kasa bacci tana zaune a falo ya shigo gidan a matukar gajiye ga damuwa na rashin ganin Maryam mota ya ajiye Ammi ta leko taga zai yi sashin su ta kira sa juyowa yayi ya nufi falon ta koma ta zauna ya shiga ya zauna kansa a kasa tace
"Tana ina kuwa?"

Dagowa yayi cike da damuwa yace
"Ammi bansan inda ta shiga ba nayi zagayen gidaje da yawa amman ba wanda yaga Maryam a cikin su...."

"Innalillahi wainna ilaihir rajiun."
Kuka mai sauti Ammi ta saka wanda yasa Alkasim shiga cikin wani tashin hankalin, 
"Na shiga uku, ina kika shiga Maryam ina kika je, innalillahi wainna illajir rajiun."

Haka ta dinga maganganu ita kadai kamar wacce ta fara zarewa, Yaa Alkasim ya koma gaban ta ya kama hannun ta yace
"Ammi ki nutsu zuwa gobe da safe insha Allahu tana wani wajen da yaddar Allah."

"Kayya Alkasim ina tsoron kar Maryam ta shiga duniya ban san wane hannu zata fada ba, ga ba lafiya ga rashin baki, ga karacin shekaru ga ciki, ga mutuwar Aliyu ga korar da akai mata ka fada min da wanne zata ji hakika ina tsoro ina ma nabi yarinya ta ina ma na hakura da wannan auren akan na barta ta tafi innalillahi wainna illahir rajiun, Allah ka kular min da yarinya ta Allah ga amanar Maryam nan ka samin ido akan ta a duk inda take Allah ka bayyana min ita"

Abdullah da ya shigo yaji maganganun Ammi sai ga hawaye, Alkasim kuwa tausayin Ammi da Maryam yake ji, da tunanin inda Maryam take, A nan falo ranar suka kwana tin asuba suka fara buge bugen waya gari na fara haske kuwa Abdullah da Yaa Alkasim suka shiga gari sune gidajen kawayenta da yan uwa har da tashoshin mota tare da hoton Maryam suna tambayar ko an ganta.

Da su Yaya Muhammad suka shigo ma ta fada musu sai suka bazama neman Maryam. Ammi tayi kuka har ta gaji. Su Yaya Fadima, Yaya Ummulkahiri da Yaya Zainab duk sun zo suna zaune jigum jigum, Abbi kuwa yana can bangaren sa sam bai san abinda yake faruwa dan shi fushi yake da Ammi sosai akan wannan abun."

Da Umma taji batan Maryam wani dadi taji tai ta murna abinda take so ya tabbata.

Yaya Zainab, Fadima, Ummulkhairi ne duk zaune a falon Ammi, sunyi jungum jugum tin safe suke zaune har magariba ba wani bayani, suna zaune Yaya Muhammad, da sauran yan uwan duk suka shigo zama sukai, Yaya Fadima tace
"Yaya dai an dace?"

Kai Abdullahi ya girgiza yace
"Ba inda bamu karade ba a cikin garin Kano amman ba Maryam ba alamun ta."
Dai dai shigowar Abbi da fitowar Ammi daga daki, kana ganin ta zaka sa bata cikin hayyacin ta, cikin yini daga duk ta rame, idon ta duk ya kumbyra saboda kukan da tasha,  tana fitowa taji abinda ya fada, kai  ta dafe hade da kirjin ta, juwa ta fara gani wanda kan ta farga ta yanke jiki ta fadi, cikin tashin hankali gaba dayansu suka nufi kanta, amma banda Abbi da ya daskare a gurin ya kasa motsi, Ammi suka dauka suka kwantar suka shafa mata ruwa farfadowa tayi likitan da da aka kira jin tana suruta tai mata allura take bacci ya dauke ta. Kallon su tayi tace
"Jinin ta ya hau dole ku, kula da ita a kula kada a bari ranta yana baci, sannan kar ana fada mata abun da zai na tada hankalin ta."

"Insha Allahu."
Suka fada. Abbi da yake tsaye a kanta yai mata tofi, Juyawa Abbi yai zai fita Yaa Muhammad yace
"Abbi Maryam ce fa ba a gani na."

Juyowa yayi yace
"Ko da kunga Maryam bana bukatar ta a gidan nan.."

"Abbi dan kayi hakuri."
Wani irin kallo Abbi ya juya ya watsa masa wanda yasa shi matsawa baya saboda tsoro, juyawa Abbi yayi ya maida hankalinsa kan su cikin wani irin bacin ran da basu taba ganinsa ba, sai da ya gama kare musu kallo sannan yace
"Why Maryam? Why? meyesa ta lalata rayuwar ta haka? Meyesa ta bari shedan yaci galaba akan ta har ta aikata irin wannan danyen aikin? Wani irin son duniya ne yakai ta ga aikata zina? Me muka rage ta dashi a gidan nan? Irin sakayyar da zatai wa soyayyan da muka nuna mata kenan...?"
Ya karashe maganan idanunsa na tsiyayar da hawaye hannu yasa ya share hawayen dan abun ba karamin damun sa yai ba, daga baya yace
"Hakika Maryam tazo mana da babban Alamari a cikin zuri'armu Allah ya na gani na bata tarbiya iyakan iyawata tunda nake a rayuwata ban taba rike koda hannun mace ba, ban taba kallon mace da wata manufa ba amma sai gashi yau 'yar da na haifa a cikin cikina, 'yar da nake sonta tamkar raina, 'yar da na fifitata fiyeda yayana, 'yar da nakeji zan iya yin komai don ganin rayuwarta ta inganta ta kwaso mun abun kunyar da har na koma ga ubangijina bazan taba wanke kaina a idon duniya ba..!"

Girgiza kansa yayi cikin kunan rai ya dafe kirjinsa da ya soma yi masa zafi cikin shakekkiyar murya ya cigaba
"Hukuncin da na dauka akan ta shine dai dai ba zan iya cigaba da kallon mafi soyuwa a cikin 'ya'ya na dauke da wannan abin kunyar ba, a cikin gida na, ba."

Yaa Alkasim ne yace
"Dan Allah Abbi me yasa ka yanke hukunci akan abunda baka sani ba, Abbi kunsan halin Maryam kunsan abunda zata aikata da wanda bazata aikata ba ku yarda da ita wallahi ba haka halinta yake ba akwai wani abu a kasa..!"

Bai kai ga karasawa ba yaji saukan wani gigitaccen marin akan fuskarta dafe kunci yayi,  Abbi yace
"Ina fada kana fada, me kake so na bincika, ko kalawa yaro sharri yana kabarin sa ba zan taba yadda ba."

"Abbi kayi hakuri amman tabbas Maryam kome ya faru da ita Kaddara ne."
"Kaddara! Wannan ba kaddara bace son zuciya ce kawai irin nata da rashin godiyan Allah akan ni'imarsa me na rageta dashi da har zataje ta bada kanta ga wani ya lalata mata rayuwa..?"

Yayan Abbi Alhaji Usman da ya shigo yace
"Muhammad me kake fada ne haka? Kada zafin zuciya yakai ka ga sabawa mahaliccinka, kada ka manta fa babu bawan da ya isa ya tsallakewa kaddararsa kaima baka wuce hakan a gurin ubangiji ba bai kamata akan dan wannan  abu ka nemi sa kanka a halaka ba kayi tunani akan hakan..!"

Ya karashe maganan yana mai kamo hannunsa cikin tsigar rarrashi, wani irin murmushin takaici Abbi ya sake yana kokarin kwatan hannunsa yafara cewa
"Yaya Usman bazaka fahimci abinda nake ji ba...."

Yana fada ya juya zai bar wajen, har ya kai kofa ya juyo yace

"Ku barta ban yadda wani ya kuma neman ta ba tinda ta zabi can din taje Allah ya bada sa'a."
Yana gama fada ya juya ya fita, Yaa Alkasim ya mike ya fice a dakin da sauri yana fadin
"Sai dai Abbi ya koren amman neman kanwata yanzu na fara."

Ya fice a gidan, wajen karfe goma ya dawo dakin Ammi ya shiga har lokacin bacci take saboda allurar da akai mata, ganin dare yayi duk suka tafi aka bar mata matan a wajen ta.

*Allah ya jikan mu, yasa muyi kyakyawan karshen Amin.*





*Antty*
[11/13, 13:59] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 32

By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW

*Bismillahir Rahmanir Rahmin*


*
Wani babban waje ta gani gefe wani katon masallaci wanda yake da bangaren maza da mata ga motoci da alama wasu matafiya ne suka tsaya yin sallah da cin abinci dan lokaci daya saura na rana. Ta shiga masallacin, bangaren mata ta nufa ta daura alwala bayan ta zaga bayi sannan ta shiga cikin masallacin ta tada sallah, tana ta zaune bayan ta idar tayi nisa tunanin da take jin agogo ya buga karfe daya da rabi ta mike a hankali ta fita ta don duba abinda zata siya ta ci, tuwo da miya ta siya da ruwa ta dawo cikin masallacin, a haraban ta zauna ta bude ledan abincin tana gutsura guda ta kai baki taji cikinta ya hautsine, tayi saurin tashi ta nufi gun da ake alwala da gudu nan ta dinga amai a wajen kamar zata shide, da kyar ta tashi daga karshe duk jikinta ba kwari ta koma cikin masallacin ta kwanta ba tare da ta sake bin ta kan tuwon ba, tana mayar da numfashi, ta kwanta ta dukunkunewa waje daya jin sanyi na shigarta ta ko ina, wanda hakan na da nasaba da zazzabin da ya rufeta lokaci daya, sai la'asar ta farka jin ana kiran sallah. Daren ranan a masallacin Maryam ta kwana, amma washegari da safe wata dattijuwa dake share sharen masallaci tace ta nemi gun da zata dinga kwana daga ranan don masallaci ba wajen kwana bane da ace kwana ake barin mutane ke yi a ciki da bai yi kyan gani ba yanzu, cike da fada take maganan, jikin Maryam yayi sanyi sosai ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, karfe sha dayan safiyan ta bar masallacin, duk wanda ya ganta sai ya tausaya mata a lokacin saboda yunwa ce kawai ke dawainiya da ita ga zazzabi, ramar da tayi ya fito sosai, karfin hali ta dinga yi tana tafiya, tafiya kuma ba na wasa ba tayi ba tare da tasan takamaiman inda zata je ba, ganin ba zata kara ko da taku daya ba don kafafuwarta sun ma gaza daukar ta kuma ta fara tunanin ta nemi wani masallacin ta samu ta dan kwanta ko na kwana daya ne daga nan in sun kore ta ta kuma samun wani a bakin titi ta tsaya tana son samun napep dan bata jin zata iya yin tafiya kuma. Dayan hannun ne na tafiya dan haka ta nufi kan titin dan ta tsallaka wata mota ta taho da uban gudu tana dannan horn juyowa tayi duk sai ta rikice wanda me motar yana dannan burki amman yaki ya tsaya sai da yazo daf da ita sannan motar ta tsaya. Wanda Maryam ta durkushe a kasa dan ta rasa ina zatayi.

Driver ne ya fito da sauri sannan masu motar da ake tukawa wasu dattawan Mata da Miji suka fito da sauri. Matar babba ce dan a kalla zatai shekara arbain da takwas haka, fara ce sosai wacce ke sanye da doguwar riga ta less army green ta saka milk mayafi akan ta. Indon ta sanye da farin glass, Wanda kana ganin su zaka san manyan mutane ne. Mijin ma manyan kaya ne a jikin sa milk shadda sai kyalli take ya saka yar ciki da babbar riga haka ya saka hula mai kyau da tsada sai tashin kamshi suke. Motar bayan su da take basu tsaro suma suka fito da sauri sukayo kan Maryam. Matar ce ta karasa ta dago Maryam wanda Maryam tayi baya zata fadi, da sauri matar ta kamo ta tana fadin
"Suma tayi!"

Mijin ta, ta kalla tace
"Samo mana ruwa suma tayi!"
Daya daga cikin security ta ne yai maza ya karasa ya dauko ruwa a mota ya kawo, amsa tayi ta zuba a tafin hannun ta, ta shafa mata tayi a fuska amman bata farfado ba. Dago ta tayi ta nufi mota da ita tana fadin
"Ado a samar mana asibiti nan kusa please."

"Ok Maah!"
Ya fada ya shiga mota sauran ma suka shiga cikin mota. Mutumin da suke tare can gidan baya ya shiga matar da Maryam kuma suna gidan tsakiya.

Sai da sukai tafiya mai nisa sannan suka samu wani private asibiti mai kyau ciki suka shiga Matar ta fito da ita da sauri suka shiga ciki. Nurses ne suka amshe ta suka wuce da ita emergency, nan da nan suka shiga wani daki da ita suka kwantar da ita suka fara ceto rayuwar ta. Ko da numfashin ta ya dawo allurar bacci sukai mata saboda sun gane bata cikin nutsuwar ta kuma tana bukatar hutu sannan suka saka mata ruwa.


*
Maryam bata sake sanin abinda ya faru ba sai bayan kusan awa takwas da faruwar abun. A hankali ta bude idonta da yayi mata nauyi ta ganta kwance wani daki da yayi kama da na asibiti da ruwa a hannunta, dafe kirjin ta dake mata zugi sosai tayi ta dinga bin dakin da ido a hankali lokaci daya kuma tana son tuno abinda ya faru amma ta kasa, a hankali ta sauke idonta kan wannan matar da ta fito a mota wacce ke zaune d'an nesa da ita idanuwan ta da hankalin ta gaba daya na kan wayar dake hannunta, kokarin mikewa zaune take da kyar har lokacin tana dafe da kirjin ta dake mata azaba ba kadan ba wanda hakan yasa hawaye ya cika idonta, motsin ta da taji yasa ta kallo direction dinta, mikewa tayi da sauri ganin ta tashi ta karaso kusa da ita tace
"Sannu ya kike ji?"

Shiru tayi. Matar ta karaso ta dafa ta tace
"Are you there?"
Da sauri ta dago kan ta, ta gyada mata kan ta. Juyawa tayi ta fita bata jima ba suka dawo da nurse da doctor. Likitan ya karaso yace
"Hello... how you feeling now?" Shiru tayi yace
"Hey... Are you there?"

Kai ta gyada yace
"Ok... How you feeling madam?"
Ganin yanda duk suka tsura mata ido, ta sauke nata idon a hankali tai musu nuni da hannu alamar
"Alhamdulillah"

Kallon ta likitan ya danyi sannan yayi murmushi yace
"Daman bakya magana ne?"
Kai ta gyada masa. Yace
"Ok, hope babu Inda ke maki ciwo yanzu koh?"

Ta gyada masa kai duk da azaban da kirjin ta yake mata. Yace
"Good"
Sannan ya juya ya fita, kallon matar dake tsaye tayi cikin sanyi matar tace
"Sannu ya jikin?"

Abun rubutu tai mata nuni da tana bukata jakar ta dake gefen ta dauko ta dauki memo da pen ta mika mata rubutu tayi ta rubuta mata
"Me nake yi a nan?"

Amsa tayi ta karanta sannan tai murmushi tace
"Kar ki damu za a sallame ki nan da anjima ki wuce gida, munzo zamu wuce ke kuma kinzo tsallaka titi shine kika tsorata daga nan kika suma muka kawo ki asibiti. Ina fatan babu wata matsala dai ko?"

Kai ta gyada mata. Matar tace
"Mun jima anan wajen eight hours ki bani number 'yan gidanku a kira i know duk inda suke hankalin su a tashe yake dan awa takwas da yawa. you passed out since in the afternoon... And this is...."

Ta kalli agogo dake daure a hannun ta tace
"Ten minute pass Eight pm"
Waya matar ta dauka tai magana ba dau minti biyar ba sai ga wata nurse da magunguna a leda, dayar kuma ledar abinci ne. ta ajiye tai mata sannu sannan ta fita.

Matar ce ta matso ta bude mata abincin tace
"Kici kinji!"

Waya ta miko mata tace
"Before then, ki kira gida ki sanar musu."
shiru tayi bayan ta karbi wayar, ta fada mata sunan asibitin sannan ta fita, hawaye ya cika idon Maryam ta saki kuka a hankali tana tausayin kanta, bayan kusan minti goma ta dawo dakin... kallonta tayi sannan ta kalli abincin ta d'an daure fuska sai kuma ta karaso ta dauki cokali ta mika mata ba musu ta karba tana kallon jollof rice da naman, matar tace
"Kin sanar dasu?"

Kai ta Gyada mata. Kallon ta tayi tace
"Tayaya kikai musu magana."
Ido tai tsuru tsuru dashi. Wani kallo matar tai mata sannan ta amshi wayar ta duba ko text tayi amman ba wani text kallon ta tayi tace
"Ki ci abinci ki sha maganin yanzu, na maidaki gida."

Dibar abincin tayi ta kai bakin ta. amai ne ya taho mata bayan ta kai baki ta sauka kan gadon da sauri ta shiga bayi ta dinga amai kamar zata amaye hanjinta, jikinta a mace ta fito ta kwanta bisa gado tana sauke ajiyar zuciya ta kudundune waje daya daga haka bacci ya dauketa sanyi na shiga jikinta. Kallon ta matar ta tsaya yi cikin tausayawa take tambayar kan ta ko dai bata da lafiya ne daman dan duk a rame take kuma ta dashe duk da ba sanin ta tayi ba before.

Haka suka kwana a dakin Sam matar batai bacci ba tana kallon Maryam dake ta rawar sanyi da motsa baki wanda magana bata fitowa wanda ke nuna tana jin jiki. In zaka gane sunaye biyu kawai take motsa baki ta kira ko tace Ammi ko Yaa Haidar sune sunayen da take kira kawai. Suma sai da ta kurawa bakin ta ido sannan ta lura sosai. A haka aka kira sallah asuba matar shiga tai wanka ta fito ta canja kaya. Wani less ta saka blue black ta yafa farin mayafi sannan tai sallah anan kan sallaya. Bayan ta idar tazo ta tashi Maryam da har lokacin zazzabi bai bar jikin ta ba. Ita ta kamata ta kai ta bandaki ta hada mata ruwan tai alwala a zaune tai sallah dan jiri take gani. Tin jiya da dare aka sallame su amman saboda ba wanda yazo daga gida kuma itama tana gama cin abinci bacci ya dauke ta yasa suka kara kwana. Dakin likita taje ta sanar masa patient din nan fa bata da lafiya. Tare suka dawo ya same ta cikin tsananin zazzabi.

Kallon Matar yai yace
"Tasha maganin ta na jiya?"
"Bata sha ba dan abinci ma tana yin one spoon ta amayar shine take ta bacci sai yanzu ta tashi."

"Bari na aiko nurse ta dibi jinin ta naga ko akwai abinda ke damun ta."
"Ok!"

Ya fita bai jima da fita ba nurse ta shigo ta dibi jinin ta sannan ta fita. Tana zaune wayar ta, ta hau kara dauka tayi tare da murmushi tace
"Son ka tashi lafiya?"
Ta can gefen yace
"Alhamdulillah sai dai missing Ummi na zai kashe ni."

"Subhanallah! Am sorry my Son insha Allahu yau zamu karaso. Jiya mun samu dan accident ne!"
Da sauri yace
"Garin yaya shiyasa bana son tafiya mai tsayi a mota ya kuke ba wani problem ko?"

"Haba Son Calm down ba wata matsala wata yarinya ce ta shiga gaban titi bama mu buge ta ba ta suma so shine muka kai ta asibiti yarinyar dai bata da lafiya ne ma tin jiya aka sallame ta amman ba wanda nata yazo shiyasa."
"Ummi to ya take ya jikin nata?"

"Da sauki yanzu za ai mata test duk abinda ake ciki insha Allahu zuwa anjima zamu taho nasan yanzu Abba ma zai karaso."
"Ok Ummi ki kula min da kanki sosai da sosai."

"I will insha Allahu! Ina Yar uwa ta?"
"Tana nan ban fita ba yanzu na tashi da missing Ummi na."

"Ok bari na kira ta mu gaisa. Nima nayi missing naka fa My Son two week din nan kamar two month haka nake jin su."
"Love you Ummi!"

"Love you too My Son bye!"
Ta kashe wayar tana kiran number Yayar tata. Sun gaisa take fada mata matsalar da suka samu.
"Kina da matsala wallahi Aisha ki taho kawai ba dai kin ce ta kira yan uwan ta ba sa zo su cigaba da kulawa da ita ke menene naki na tsayawa kina fama da ita uhmm!"

"Yaya ai taimako ne ni nasan taimakon da zan nema nan gaba."
"Ai kinyi na Allah. Allah kuma ya gani zai baki lada."

"To shikenan sai anjima"
"Aha!"

Sukai sallama. Abba ne ya kira ta akan ya karaso tace ya shigo dakin ya shiga ta gaishe shi ya kalli Maryam dake bacci yace
"Yarinyar nan amman tana wahala da yawa bata da lafiya dai ko?"
"Haka nake tunani shiyasa nasaka Doctor yai mata test a gano me dame ke damun ta."

"Allah bata lafiya."
"Amin!"

Ya kara kallon Maryam yace

"Yan uwan ta basu zo ba."
"Ina tunanin wani abu akan ta, bari dai ta farka muji."

"To!"
Knocking akai suka bada izinin shigowa, daya daga cikin securityn su ne ya shigo ya gaishe da Ummi sannan ya ajiye mata basket din ya shigo dashi. Suna zaune doctor yasa aka zo aka dauki Maryam a wani gado.




*Allah ya jikan musulmai, ya kyautata namu zuwan. Amin*




*Antty*
[11/14, 12:39] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗

Please Login or Register in order to submit comment