Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

RAHIM*


Kan su shiga gida har Haidar yai bacci suna zuwa ta kai shi d'aki ta canja masa kaya tare da masa addu'a, bandaki ta shiga tai wanka ta fito ta saka kayan bacci, tana shirin kwanciyya ya shigo yana fadin
"Me nake gani haka?"

Ya iso ya dauke ta yana fadin
"Wai me yake damun ki ne?"
Ya fada yana ajiye ta akan gado, idon ta ne ya kawo ruwa, yace
"Ba zan taba kishi da Yaa Haidar ba Maryam, amman wallahi in na ganki a damuwar ni kadai nasan me nake ji dan Allah ki fada min da me kike tina shi ni kuma in maye gurbin hakan."

Murmushi ta saki tace
"Yaya na i love u the way u re, a kullum in zan tuna da Yaa Haidar sai na tina da kai dan sanadin ka na ke raye cikin jin dadi, in Yaa Haidar ya kula dani a baya yanzu kai ke kulawa dani, in Yaa Haidar ya soni a baya yanzu kai ke so na, in na kasance da Yaa Haidar a da yanzu da kai nake tare, ka mayewa Haidar gurbin sa, dan haka ka sani kai kadai ke zuciya ta da tunani na dole na tina Yaa Haidar Yaya amman ba haka zai sa nace bana son ka ba, ina son ka, kuma in na tuna shin addu'a nake masa, please Yaya kada kai fushi ko kaji haushin sa akan haka, yau Haidar karami ya tina min da Abbin sa, kuma na kara sauke mata wani nauyi dake kaina, kai min alfarmar ko ya'ya muka haifa zamu sa musu soyayyar Yaa Haidar, dan suna masa addu'a saboda abinda yake so kenan."

"Ya'yan mu na Yaa Haidar ne Maryam, kamar yadda Haidar yake nima 'dan na, dan haka na miki wannan alfarmar kuma nima zan kasance cikin masa addu'a Allah masa rahma ya kyautata namu zuwan."
"Amin My honey."
Ta fada tana shigewa jikin sa.

Rumgume ta yayi tsam a jikin sa kamar zai mai data cikin sa yace
"In nace nafi Yaa Haidar son ki zaki yadda?"
Kai ta dago tana kallon cikin idon sa, wanda ba abinda take gani sai tsantsar son ta, ido ta lumshe tace
"Ba Yaa Haidar Yaya dole kai ne me sona a yanzu fiye da kowa, ni na isa na karyata Yaya na bayan baka taba batan rai ba kullum kula kake bani kamar 'yar sa, abinda Innan Abbi na ta fada kenan nake ganin ta fada ne kawai cewar ina dacen masoya a lokacin ban san da gaske take ba sai a yanzu nake gaskatawa, hakika nagode Allah da ya jarrabcen ya kuma bani ikon cinye jarabawar har yai min canji da mafi alheri, Allah ya jikan Yaa Haidar, ya barni da kai har a aljanna Yaa Haidar, ina son ka ina kaunar ka kuma na yadda da duk soyayyar ka."

Idon ta cikin nasa take maganar nan wanda yaji son ta da kaunar ta na kara ninkuwa a cikin zuciyar sa, goshin sa ya hade da nata inda hancin su ke gugar juna, ya kara yin kasa da fuskar sa bakin su ya hade da na juna, wani irin kiss yake bata mai ma'anoni da manufa da yawa, a haka ya cigaba da romancing nata tare da faranta ran juna su kamar ba ita ba ta zage suna shan soyayyar su.

*
Washe gari da safe, sam sun manta da Haidar baccin su suka hau yi, wanda Haidar ya farka wajen takwas, da kan sa yai brush ya fito falo, ya kunna kayan kallo ya kai mbc 3 ya zauna yana kallon cartoon, da yaji yunwa ya shiga kitchen ya nufi store ya dauko fresh yoo da biskit ya dawo ya zauna yaci ya koshi daga haka ya cigaba da kallon sa, wanda bai san lokacin da bacci ya dauke shi ba, sai karfe goma suka farka, wanka sukai suka shirya sai da ta zata bude kofa ta tuno da Haidar karami da sauri ta fita ana fadin
"Honey mun manta da Haidar."

Ya fito da sauri yana fadin
"Kuma ya tashi?"
Suka fita a falo suka same shi yana bacci gefen sa robar fresh yoo da ledar biskit din da yaci, karasawa Yaa Haidar yayi ya dago Haidar yana rumgumewa Maryam ta nufi kitchen dan hada musu breakfast. Sai da ta gama suka zo ta je ta karai masa brush suka karya, a jikin su ya yini daga ya fada jikin wannan sai na wannan, da yamma Yaa Haidar ya dauke su suka je park, wanda daga can suka shige wani reaturant acan sukai dinner daga nan store sukaje sukai shopping sannan suka koma gida, haka the next day ma da yamma suka fita zaga gari sai dare suka dawo.

Washe gari Monday suka shirya suka tafi aiki, bayan sun ajiye Haidar a makaranta, sai yamma Yaa haidar ya dauko Haidar sannan suka wuce suka dauki Maryam daga school, satin sa daya yace wajen Ummi zai koma wannan yasa suka mai dashi.


*
Yau sai shida zasu fito daga lecture wannan yasa tin kafin su shiga karfe hudu ta kira shi, lokacin fitowar sa kenan daga treater ya ji kiran nata dauka yayi yana fadin
"My Baby."
"Uhmm i miss you Honey."

Wani sihirtacen murmushi ya saki yace
"I miss you more ko nazo na dauke ki muje gida mu rage gajiyar dake tare da mu."
"Da kuwa naji dadi."

"Karatun fa."
"Uhmmm Allah yaya na fara gajiya da ba dan burin ka bane da tini na ajiye shi na zauna na rumgume miji na ina samun lada, amman Honey kalla fa kaga yau tin safe har shida ban kara saka ka a ido na ba ban jini a jikin ka a uhmm uhmm ni wallahi i miss you Honey."
Ta karashe maganar da sakin kukan shagwaba, da kyar ya iya bude office din sa ya shiga ya fada samman kujerar dake office din tare da sakin wata irin ajiyar zuciya ido ya lumshe hannunsa d'aya cikin sumar kansa, yana jin yadda tsigar jikin sa ke tashi na kukan da Maryam take masa wanda ba hawaye sai tsabar tsokana da son tada masa da hankali, A hankali cikin laushin murya ya kirata
"My Noor!"

"Uhmm Honey!"
Tai maganar cikin zallar shagwaba, kina so nazo makarantar yanzu ko? Kin tadan hankali na ba abinda nake so sai kasancewa dake gashi na bada appointment da wani Babban mutum zai zo karfe biyar kina so na taho ne?"
Ashagwabe tace
"No honey amman ka sani i miss you so much."

"Na sani Baby nima haka baki ji jiki na ba duk ba dadi na rashin ki, gaskiya in ba a canja muku wannan lecture ba zan na zuwa ina dauke matata sai na dawo da ita four din."
"Uhmm"
Ta sauke masa wani nunfashi duk da ba sa tare sai da ya sagar masa da jiki yace
"Baby am sorry kinji sauran watanni mu huta ko?"

A shagabe tace
"Eh Honey i love you i miss you."
"Miss you more me kika ci?"

"Bana jin yunwa."
"Hmmm ban yadda ba kije kici abinci yanzun nan kan ku fito zan zo daukar ki kan six kinji?"

"Yes honey bye."
"Bye."


*
Karfe biyar da rabi ya gama da asibiti, gida ya nufa cikin hanzari so yake kan six din ya karasa wajen Maryam.

Karfe biyar da arba'in ya iso k'ofar gidansu ya fito a gaggauce ya shiga gidan yai bangaren Mami a tattsaye suka gaisa sannan ya fito yai bangaren Ummi.

Lokacin daya shiga falon ba kowa, yana sallama kai tsaye ya nufi stair amman motsin Ummi da ya jiyo a kitchen yasa ya juya ya nufi kitchen din, a gaban sink ya gano ta tana wanke wanke kitchen din ya dumame da kamshi.

"Ummi nah."
Ya fada yana karasawa tare da amsa abin da take dauraye wa ya karasa wanke wa, tace
"Dr ya kake ya gida? Ina daughter?"

Murmushi ya saki yace
“Lafiya lou Ummi, Baby fa Ummi tin safe dana fita daga gida ban k'ara komawa ba yanzu nan ne ma zanje na dauko ta yau six zasu fito, Ummi nasan ta gaji ba abinda zata iya in mun koma shiyasa nazo na amsar mana abincin Ummi."

“Allah sarki My Daugther, Allah muku albarka, ai kune kunki mai aiki da kan ku koma ta rage mata wani aikin, yanzu ace kan ta fita sai tayi aiki, sannan ta dawo ace sai tayi aiki? Gaskiya dai Aliyu dole a samar mata mai aiki."
Ta fada tana nufar wajen kwanukan ta dauko flask ta fara zuba masa abincin da tayi, vegetables rice tayi sai miyar da taji kaji sai hadin salad da zobo da ya sha kankana ta zuba a basket tana fadin
"Gashi nan maza kaje dan shida saura kada tai ta jiran ka."

Amsa yayi yace
"Thank you so much Ummi, we really love you."
"Maza jeka Allah muku albarka."

Ya juya har ya kai kofa ya juyo yace
"Ummi My Son fa?"
"Nasan suna hanya shima."

"Agaishe shi zamu zo mu dauke shi yai mana weekend."
"Ba inda zashi kuna barin sa da yunwa bakwa tashi da wuri in kaga yazo to sai na samar muku mai aiki ita ta kular min dashi."
Kai yai kasa dashi kawai ya fice yana murmushi, dakin Inna ya karasa ya same ta zaune daga bakin kofa ya tsaya tace
"Au bazaka shigo ba."

"Ina sauri nake zan dauko Matata daga makaranta."
"Aliyu ai bance ba matar ka ace da kake kara jadadda min wai zaka dauko Matar ka."

"Nifa gaishe ki nazo dan sauri nake Hajiya Inna."
Ya juya tace
"To tsaya ka kai mata abu mana tin shakaran jiya nayi jiya na manta ban baka ba yau ma kada na manta Umaru yazo ya cinye mata "

Ta shiga kitchen bata jina ba ta fito da bowl ta mika masa tace
"Ka gaishe da ita kwana biyu ma bata leko ba, gobe Najwa ma zata dawo gida haihuwa ita tana da cikin ko tukkuna dai?"

"Zan kawo ta sai ki auna mana ita."
Ya fita yana fadin
"Mungode Inna."

Ya fita karfe shida da minti goma ya shiga cikin makarnatar a can gefe ya hango ta tsaye ita da Jawahir a jikin motar su, har inda suke ya karasa ta kalli Jawahir tace
"To sai gobe."

"Allah kaimu."
Ta daga mata hannu ta shige cikin mota, Maryam ma ta fara tafiya wajen Yaa Haidar da ya zuba mata ido, tafiyar tata ma kadai abar sha'awa ce, a haka ta karaso tana shiga ta zame nikaf din fuskar ta tana fadin
"Sannu Honey."

Ta fada tana fadawa jikin sa tare sa makalkaleshi tana kissing d'in goshinsa kumatunsa, tana zuwa kan labb'ansa ta kamesu baki d'aya ta sak'alo hannayenta wuyanshi, idanunsu cikin na juna ta fara tsotar labb'an nasa tana lumshe idanunta, ta tura hannunta cikin yalwatacciyar sumar kansa tana shafawa, ta fara wasa da harshensa cikin irin salonsa da ya koya mata, take kamo harshen nashi tana tsotsa tana had'awa da labb'ansa tana lalubar bakin nasa lungu dan sak'o cikin wani irin salo mai jeda mutum cikin wani hali, kissing nasa take tana shafa sumar kansa ta maida hannunta d'aya saman fuskarshi tana shashafawa. Idanunsa kawai ya zuba mata cike da tsantsar k'aunarta wacce ta gama gauraye jini da b'argonsa.

Ya sanya hannayenshi dukka biyu ya rungumeta tsam yana shafa bayanta, a hankali yana kara taimaka mata, ba abinda kake ji sai sautin tsotsar bakin su da fitar da numfashin su. Tinda yaji wayar su ta dazu yadda take masa shagwaba da cewa yazo a time din shi kan sa yasan Maryam really need him.

Maryam jin yadda yake romancing nasa yasa tai luf a jikin sa tana jin dad'in yadda yake tsotsar bakin nata, ta sanya hannunta cikin rigarsa tana shafa kwantaccan gashin k'irjinsa.

Tuna a inda suke yasa ta manna masa cizo a harshe yadda bazaiji zafi ba. Ya saki bakin nata da gangan yana, yana shagwabe fuska kamar yadda take masa tare sa yarfe hannu yace
“Aushhhhh harshe na”

Kyalkyalewa tayi da dariya tana ruk'unk'umeshi tace
"A titi dai muke Yaya."
Har ya sha'afa a inda suke dan da ta barshi zai iya zarce inda yake, murmushin ya sakar mata yace
"Ai kam sai kim ban yar nutsuwa zan iya kai mu gida."

Ya janyo ta ya cafki bakin ta tare da fara romancing nata da zadi da zafi, sai da ya samu ya dan nutsu sannan ya rumgume ta a haka ya tada motar suka tafi.


Yana parking ya kalle ta yadda jikin ta duk ya mutu, fita yayi yana murmushi ya bude side din da take ya dauko kamar Baby har bedroom ya kaita sannan ya fito ya dauko saura kayan dake cikin mota ya kai ciki, yana shiga ya jiyo ta tana wanka shima wankan ya shiga yayi ya fito ya nufi masallaci wanda yana zuwa sauran raka'a daya yabi su sai da aka idar har yayi isha'i sannan ya fito ya nufi gidan, akan sallaya ya samu Maryam ta daga hannu yana addu'a hawaye na bin fuskar ta, karasawa yayi ya zauna yana kallon fuskar ta yace
"Lafiya Baby?"

Ya fada yana janta jikin sa, rumgume ta yayi yace
"Baby i love u!"
"I love u more Honey."

Kan ta ya dago yace
"Fada min me yake damun ki?"
"Yaya ina son ka bana son na rasa ka."

"Waye yace zaki rasani?"
"Ina tsoro ne Yaya yadda na rasa Yaa Haidar kar na rasa ka, ji yadda kake so na fa."

Hannu ya daura akan bakin sa yace
"Wayace miki dan ana son mutum sai ka rasa shi, shima Haidar din lokacin sa ne yayi, kuma kowa lokacin sa yayi dole ya tafi, fatan mu dai Allah yasa mu cika da kyau da rahma."
"Amin."
Suka amsa.

Ya hau share mata hawaye yana fadin
"To ki bar kuka da damuwa, *Matar Haidar* "
Murnushi ta sakar masa yai kissing lips din ta ya dauke ta suka fito yace
"Me kika ci a school?"

"Snacks."
"Shiyasa naji baki dan yi nauyin kin ci abinci ba."
Dariya ta saki tace
"Kai Yaya?"

"Allah yanzu in kika ci abinci na dauke ki zanji kin dan dada nauyi."
Tai murmushi, tare suka ci abinci, sai da suka gama sannan suka fita zagaya gidan dan abincin ya sauka. Bayan gidan sukaje da zasu taho ta tsaya tare da kin tafiya juyowa yai ya kalle ta yace
"Ya dai?"

Kafa ta hau bubbugawa tace
"Ni na gaji."
Juyowa yai yana murmushi yace
"Shine kuma sai kinyi kuka?"

Baki ta turo, ya durkusa yace
"Hau to."
Da sauri ta hau ya dauke ta, tana dariya a haka suka karasa cikin gidan akan gado ya ajiye ta ya fara massaging jikin ta.

A hankali ya birkitota ta dawo k'asa yana samanta ya tallafo fuskarta bakin su ya hade daga haka suka shiga bajaulin soyayyar su.


*
Kwance suke rumgume da juna Maryam da idon ta ke a lumshe tana jin yadda Yaa Haidar ke massaging jikin ta da hannun sa, tace
“Uhmmm I love u Honey i can't live without u, taya zan iya rayuwa babu kai a haka? Wallahi bazan iya ba."
Ta fada tana sakin wani kukan,
"Baby wai menene yau kike ta kuka ne?"

Shiru tayi ya shiga share mata hawaye yace
"In dai nine Haidar insha Allahu i will always be with you, bani da kowa bani da komai sai sonki da kaunar ki su na saka a gaba kawai, a baya in ance zan so wata mace ba zan taba yadda ba, so please Baby ki bar kuka da sawa a ranki zan rabu dake, insha Allahu i will always be with u for ever uhmmm?"

Wata irin rumguma ta bashi tare da kissing bakin sa tana kara rikita shi da salon ta duk abinda tasan yana so shi take yi ai kuwa ta ruda shi.



*
Washe gari da rana tana school Najwa ta kira ta ta sauka lafiya tana asibiti murna wajen Maryam kamar me haka ta kira Yaa Haidar yana ganin kiran ta ya dauka yace
"Baby na!"
"Uhmm Yaya dan Allah kazo ka dauken naje na gano Baby."

"Ba lectures zaki shiga ba? Kiyi hakuri zan zo biyu dai dai kinji?"
"To shikenan pkease Yaya kaje ka daukon picturen ta."

"An gama ranki ya dade."
"Thank you My love."

Ta kashe wayar, shima tana kashewa ya karasa dakin da Najwa take, Babyn na hannun Ummi ya karasa yace
"Baby ce take ta rigima naje na dauko ta, tazo taga Baby."

"Aliyu ya kamata ka bata mota tana driving itama."
"A'ah Ummi ni bana son ta wahala wallahi."

Sai da yai maganar ya tuna da wa yace sai ya share kawai yace
"Baby tace nazo na daukar mata kan ta karaso."
Ya dauke shi yana fadin
"Bari naje Ummi."

Ya juya ya fita. Tana aji amman ta kunna data, yana turowa ta bude wani murmushi ta saki tana fadin
"Allah sarki Sis Allah ya raya mana."
Ta kashe datar. Har Allah Allah take malamin ya fita dan sai taga lokacin ma baya gudu a haka har biyu tayi sallah kawai tayi sai ga Yaa Haidar, sallama suka da Jawahir suka tafi asibitin.

Lokacin da sukaje ta dauki Babyn kuwa ta hana kowa sai sannu takewa Najwa, har yamma suna nan sai da aka sallame su gaba daya sukai gida.


Da dare ya shigo dakin Ummi inda Najwa da Maryam suke, bayan ya zauna ya mike yace
"Tafiya fa zamuyi."
"Yaya please na kwana?"

Wani kallo ya aika mata yace
"Kada ma ki soma ki sauko mu tafi."
Ummi da ta shigo tace
"Ah Dr kaci abinci ne?"

Kai ya girgiza yace
"Wa zai bani?"
Ummi tai murmushi tace
"To tashi ki zuba masa."

"Ai tafiya zamuyi ma."
Yaa Aliyu ya fada.
"Ummi please ya barni na kwana."

Kofa ya nufa da sauri yana fadin
"Ina kasa ina jiran ki."
Ummi ta kalla ta tabr baki tace
"Ummi please."

"Maryam kwanan me zakiyi?"
Ummi ta fada tana zama kusa da Najwa. Mikewa tayi tana turo baki tace
"To sai da safe."

"Allah bamu alheri ki dibar masa abincin fa."
Fita kawai tayi, Ummi tace
"Kuje ku karata, ni nasan ba barin ta zai ba."

Najwa tai dariya tace
"Itama Maryam rigima dai kawai Ummi."
Sukai dariya Ummi ta mike tana fadin
"Taje can tai masa."
Ta fita, a kitchen ta samu Maryam tana dibar masa abinci, sai da ta gama suka nufi kofa tace
"To sai da safe?"

Kai ta gyada, ta fita tana daga mata hannu kamar zatai kuka wai duk dan Ummi taji tausayin ta.




*Allah mana rahma kasa muyi kyakyawan karshe Amin.*


*Antty*
[12/12, 09:51] My Airtel: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 85


By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


A mota ta same shi ta shiga ta zauna ta dauke kai tana kallon waje, murmushi kawai yayi ya tada mota suka fita a gidan, hannun ta ya kamo yana murzawa a hankali yace
"Wai yau dani ake fushi."

Bata juyo ba a haka ya dinga murza hannun ta har suka karasa gida yana bude kofa ta bude ta fita tare da dauka flask din da ta shigo dashi, a falo ya same ta zata shiga daki ya karasa ya rumgume ta yace
"Tab Allah baki isa ba ki ma daina tin wuri kuma abu daya zan fada miki kada ki soma sawa a ranki zan iya barin ki zuwa wani waje kwana dan ba zan taba iya kwana ba a jikin ki ba ki tausayawa dan Babyn ki mana, kema kinsan komai dai."

Dariya da tausayi ya bata dan tabbas tasan ba zai iya ba, yini daya in bai yi da ita ba ma ya ba lafiya bare ace kwana. Haka ya dinga lallashin ta da kalamai masu dadi da nuna mata illar barin sa shi kadai din da haka ta hakura ta taya shi sukai wanka ta bashi abinci da kanta sannan suka zauna suna shan soyayyar su.


Tin ranar da Najwa ta haihu kullum daga makaranta can yake kai ta sai dare suke dawowa, ana ya gobe sunane da kyar ya yadda zata kwana.

Duk abinda take bukata ta saka a cikin akwati, tana cikin hada kaya ya shigo ya tsaya a bakin kofa yana kallon yadda take ta zuba kaya a cikin akwati, dagowa tayi ta saki murmushi tace
"Yaya in ta so mu tafi?"
"Ba zaki lecture ba?"

Baki ta turo tace
"Yaya ba dole ne yayi ba ni kawai ka kaini gidan Ummi."
Ya karaso ya amshi akwatin yana rufewa yace
"Wannan uban kayan fa?"

"Kala uku ne fa Yaya."
"Gobe dai zamu dawo."

"Naji."
Ya dauke akwatin ya ajiye, a kasa yace
"Dauko mayafin naki."
Ya fita da akwatin.

Har gida ya shiga ya dauki kayan ya shiga dasu sama ta wuce dakin Najwa acan ta samu Aisha tana shiga Baby ta dauka suka gaisa sannan ta tafi wajen Ummi da Babyn

A can ta samu Yaa Haidar, gaisawa sukai da Ummi sannan ta koma dakin Maryam, da kallo Haidar ya bita, har Ummi ta gane, yana dagowa suka hada ido da sauri ya mike yana sussunne kai yace
"Ummi bari naje sai na dawo."

"Allah kiyaye hanya Allah bada sa'a."
Yana fita ya fara neman layin Maryam, tana zaune cikin su Aisha kiran ya shigo, dauka tayi tace
"Yaya."

"Matar Haidar zan tafi."
"To Yaya Allah kiyaye hanya."

"A'ah a'ah ban yadda ba."
"To me zan maka Yaya?"

"Maza ki zo ki wa mijin ki bye bye common my dear.'
Babyn ta mikawa Aisha tace
"Honey ba dai rigima ba bari naje."

Dariya sukai ta mike ta fita, a kasa ta same shi zaune, ta karasa tana fadin
"Honey gani."
Hannun ta ya janyo ta fada saman sa ya rumgume ta kallon dakin ta fara tace
"Yaya a gidan Ummi fa muke."

"Bake kika zaba ba."
Baki ta turo ya matso da face din sa ya fara kissing lips din ta, kofa sukaji an bude da sauri ta zare bakin ta tana barin jikin sa, Mami da ta gansu ta dauke kai kamar bata san da mutane a falon ba, Maryam ce tace
"Ina yini Mami?"

Mami ta juyo tana fadin
"Ah yaushe kuka shigo?"
"Dazu."

Aliyu ya mike ya sauka kasa yana gashe da Mami ta amsa tana yin sama, mikewa tayi ta nufi stairs tana fadin
"Ni dai Yaya sai ka dawo."
Hannun ta ya kamo, ta juyo kamar zatai kuka tace
"Yaya ni dai ni dai."

"Allah in baki zo kin ban goodbye kiss ba, ba kwanan da zakiyi."
Kafa ta hau bubbugawa, ya juya ya nufi kofa da sauri ta bishi da gudu tana fadin
"To ba gani ba."

A bakin kofa ta cimmasa ta rumgume shi ta baya, ta daura kan ta a bayan sa, ya juyo da ita, ta tsaya a gaban sa wanda ya fita tsayi, dage tayi ta kamo baki sa ya saka hannu ya zagaye kugun ta, kissing juna su suke cikin kwanciyyar hankali, sai da suka jiyo motsi ana tahowa sannan ta janye bakin ta, rumgume ta yayi sannan ya sake ta yana fadin
"Sai na dawo."

"A dawo lafiya Honey."
"Take care."
Ya juya ya fita ta leka tana kallon sa har ya fice, sannan ta koma sama. Tare da mai jego akai musu lalle da kitso.


*
Karfe shida ya dawo alwala kawai yayi ya nufi massalaci sai da akai isha'i ya shigo gidan a dakin sa ya shiga yai wanka yana fitowa ya kira Maryam lokacin ta fito daga wanka tana shafa mai ta dauka yace
"Shine ko ki nemen ko?"
"Ba haka bane Honey lalle ne a hannun fa, ka dawo?"

"Eh yunwa nake ji."
"To ya za ayi?"

"Ki kawon abinci."
"To ina zuwa."
Ta nufi akwatin ta kayan bacci ta saka doguwar riga ta saka hijab, kitchen ta shiga ta dauki abincin sa, dakin sa ta nufa ta shiga da sallama baya falo, dan haka ta nufi bedroom din sa yana zaune a gefen gado, yana ganin ta, ya mike ya karaso ya amshi tray din ya ajiye, sannan ya jayata jikin sa yana kissing, da kyar tace
"Yaya baka ci abinci bafa, kuma kace yunwa kake ji."

"In na same ki ai zaki gusar min da ko wacce irin yunwa."
"Naji amman ka fara cin abinci."

Ta sauka tana zuba masa, ita ta dinga bashi yana ci sai da ya gama ta dauki kwanon zata fita dashi ya kamo hannun ta yace
"Zo tukkuna."
Ya janyo ta jikin sa yana mai aika mata da sakon da dole ta biye masa.


10:00pm
Ummi ce ta shiga dakin da Najwa take, ita kadai ta sama kwance akan gado, ta karasa tana fadin
"Ina Maryam din?"
"Ummi kema kinsan Yaya ai ba barin ta zai anan ba."

Shiru kawai Ummi tayi tana girgiza kai can tace
"Shikenan sai da safe."
"Allah bamu alheri."


5:15am
Ta bude idon ta, ta sauke akan Aliyu dake zaune akan sallaya, yana ganin ta tashi ya mike ya karaso yana shafa fuskar ta yace
"Morning Baby Love."

Baki ta dan turo tace
"Shine ka hanani tafiya ko Yaya ni wallahi kunyar Ummi nake ji."
Murnushi yayi yace
'Bazaki makarar dani da rigimar ki ba Baby."

Yai kissing goshin ta ya mike ya fita dan har an tada sallah, bayan sa tabi da kallo sannan ta mike ta shiga tai wanka ta fito ta tada sallah bayan ta idar tai azkar sannan ta muke ta gyara masa dakin ta saka turare ta fice ta koma dakin Najwa.

Tana kwance tana bacci ta shiga kaya ta canja

Please Login or Register in order to submit comment