Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masoyi, tabbas yayi kewar aminin sa saboda ba shi da tamkar sa shi bashi da mai basa shawara da daura sa akan hanya Haidar ne kawai, sai a yanzu da suka kulle da Alkasim wanda suka kara bazama neman Maryam sosai suka bincike a Bauchi amman duk da ba wani cigaba da aka samu, duk da haka Ahmad da Alkasim basu hakura ba duk wasu garuruwa in suka samu sukaje sai sun bincika.


Abuja
Washe gari Mama na tsaye a window tana ganin fitar Ummi ta fito ta yo sashen Ummi yau ma a falo ta samu Aliyu sai ta kara tsarguwa ya dauke kai ya gaishe ta, ta amsa tana tambayar me jiki sannan tayi sama. A kwance akan sallaya ta samu Maryam na jan carbi, dan walha ta idar ta dan kwanta. Mama ta karasa ta zauna a gefen gado tace
"Ya jikin?"
"Da sauki!"
Tai mata nuni. Mama tace
"Nazo muki da wani karuwa ne in har kika yadda zan biki 5million nasan zata ishe ki kije kiyi rayuwar ki ba takura da sa ido."

Ita fa Maryam tin zuwan matar nan jiya taji bata kwanta mata ba dan haka sai ta tsaya kallon ta kawai. Mama tace
"Nasan irin ku da yawa wasu karuwanci ya fito dasu suka samu ciki su rasa mai amsar ciki su zo su makalewa wasu. To abu daya nake so ki min da wannan cikin duk da nasan bai da uba yanzu zan masa uba zan je na fadawa mahaifin yaron nan cewa kin fada min cikin nan na Aliyu ne shi ya hada komai har kuka hadu da Ummi ta kawo ki gidan nan ki nuna musu anan ma neman ki yake in har kikai min haka ko?"
Mama ta fada tana murmushi tace
"Ni na miki alkawarin baki wajen zama da 5 million kamar yadda na fada miki ya kike gani zaki iya?"

Mikewa Marym tayi ta dauko memo da take rubutu ta fara rubutu sannan ta mika mata. Amsa Mama tayi ta fara karantawa.
"Ciki na yana da uba ba zan taba sheganta shi ba dan haka ki rabu dani, ni ba abinda ya kawo ni ba fatana na samu na tuno rayuwa ta ta baya na koma wajen iyaye na. Yau ko da ace cikin shege ne ba zan taba lakabawa Aliyu shi ba mutanen da suke kai na dare da rana ke kuwa me Aliyu yai miki kike son saka sa a wannan halin?"

"Ban sani ba aiki na kawo miki in zaki min shikenan in ba zaki min ba shikenan arziki ke neman ki kike son guje masa."
Rubutu Maryam tayi a paper ta mike mata amsa tayi ta fara karantawa
"Dan Allah ki kyale ni naji da abinda yake damu na. Arziki na Allah ne in ina da rabo zanyi shi."
Mikewa Mama tayi ta fita a falon sama suka hadu Inna ta hau durkusawa tai ta gaishe ta.

Inna tace
"A'ah A'ah bana cin mike ai kinsan sashe na wa ya hanaki kizo ki gaishe ni in kina son ki gaishe nin?"
Tayi ciki. Mama ta harari bayan ta ta fice. Aliyu ta sama a inda ta barshi ta fice da sauri ya girgiza kai kawai.

Kuka Inna ta samu Maryam nayi da sauri ta karasa ta dafa ta tace
"Me ya faru dake Uwa ta?"

Hawaye ya zubowa Maryam ta girgiza kai. Inna tace
"Ko dai waccan matar ce tai miki wani abu?"

Nan ma girgiza kai tayi. Inna tace
"To me akai miki?"
Kai ta girgiza. Inna ta mike ta sauka ta samu Aliyu a kasa tace
"To gata can sai kuka take taki ta fada abinda akai mata kaje kai ko zata fada maka."

Da sauri ya mike yai sama ya same ta tana ta kuka ya durkusa a gaban ta yace
"Menene kike kuka?"
Kai ta girgiza yace
"Ko wani abu ke miki ciwo?"

Nan ma ta girgiza kai yace
"Me kike so to?"
Nan ma same. Nan yai ta lallashin ta da kyar ta samu tai shiru tana sauke ajiyar zuciya a haka bacci ya dauke ta ya tsaya kallon ta yana tunanin to me Mama tai mata. Mikewa yai ya fita ya nufi sashen su. Ba kowa a falo sashen Mama ya nufa a falo ya same ta zaune ya tsaya a bakin kofa yace
"Kada in kara ganin kafar ki a sashen Ummi, sannan ba ruwan ki da yarinyar can in ma wani abu kike bukata da ita tafi karfin ki."

Yana fadar haka ya juya ya fita. Mama ta yi kwafa tace
"In ban ga bayan ka ba, ba sunana Barira ba."






*Allah ya jikan musulmai ya kyautata namu zuwan yasa mu gama da duniya lafiya Amin.*



*Antty*
[11/21, 10:19] My Airtel: ο»ΏπŸ’—πŸ’— *MATAR HAIDAR* πŸ’—πŸ’—
Page 47

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


Ajiyar zuciya Ummi ta sauke ta janyo shi jikin ta da sauri ya daura kan sa a kafadar ta. Kansa take shafawa tana fadin
"Say Alhamdulillah and you should always say it if good or bad things happen Allah will give you the best of best for you."
"Alhamdulillah!"
Ya furta wanda furtawar da yayi ya sa ya samu saukin abinda yake ji.

"Nasan wacece Maryam Aliyu amman in kai hakuri ka amshi kaddarar ka Allah zai sauya maka da mafi alheri. I know a zamanin nan samun mace like Maryam is not a small thing but anything if we say Allah, that Allah will do it for us. Kai ma baka zalunce ta ba so Allah willl not let someone to bullying ur life so be patient Allah is with u!"
"I love you Ummi!"

"I love you son. Amman kaga da ka amshi Maryam's sister ai da ka dinga kallon copyn ta."
"Ummi ba zan iya ba gani zan yi kamar naci amanar Maryam ne, ya zanyi dasu a aljanna ina son na tashi da Maryam a gidan aljanna so gwara na auri wata daban."

"Kamar gaske ka samo watan."
Kai ya shafa yace
"Ummi na kasa, my heart has close and the key is with Maryam how should i open it, i am not the one whose control my heart!"

"Aliyu ya kamata ka samu kai settling life dinka girma kake fa Maryam tatafi ba abinda zamuyi mata sai addu'a itama samun nutsuwar ta ta ganka cikin nutsuwa da farin ciki."
Kai ya lafe a jikin Ummi.
"Tashi muje kaci abinci i left Maryam alone!"

Da sauri ya mike yana fadin
"Na manta maganin ta."
Ya dauko suka fita. Maganin ya bata ta sha sannan suka sauko da Ummi da kyar ya samu yaci abinci ya tashi yaje ya wanka sannan yai alwala sallah ya hau yi yana wa Maryam addu'a. Haka ya kwana kan sallaya sai wajen hudu wani bacci ya dauke shi.


*
```Zaune ya hange ta a cikin wani lambu sanye da fararen kaya ta kara haske tana tai masa murmushi karasawa yayi yace
" *Matar Haidar* "
" *Mijin Maryam* "

"Ita kadai!"
Fuska ta bata tace
"Bana son haka Yaa Haidar wa yace maka ana halittar mutum dan abu daya kawai. Ka daina fadar ni kadai. Allah ya baka ni kuma ya amsa sai ace me? Sai ace ba zaka kara aure ba. A'ah fushi kake da wa da ba zaka kara aure ba please Yaa Haidar in har kana son farin ciki na ka samu kai aure kaji Maryam zatai farin ciki in kuwa ba kai ba zanyi akasin haka. Kalle ka duk ka rame kana saka damuwa a ranka baka cin abinci ni da na tafi menene na damuwa to ina tare da kai ka bar damuwa ko bama tare muna tare a jikin juna. Yaa Haidar ka cire damuwa ka sani kai kaidai nake so. In kai aure baka ci amanar soyayyar mu ba ka raya sunna Allah zai baka lada."

Dagowa yai zai magana```


Kiran sallah ne ya tada shi ya fara waige waigen dakin salati yayi tare da addu'a ya nufi bandaki ya kara watsa ruwa ya tafi masallaci. Bai dawo ba sai bakwai ya nufi sashen sa ya kara wanka ya sauya kaya ya fito falon su. Ba kowa sai kamshi dake tashi. Kitchen ya nufa ya samu Ummi na gyara wajen ya karasa yace
"Barka da safiyya Ummi nah!"

Kansa ta dafa tace
"Ba kai bacci ba jiya saboda me?"
Idon sa ya shafa yace
"Aiki na danyi!"

"Uhm uhm fah Haidar!"
Yai murmushi yacs
"Ummi ya me jiki?"

"Da sauki Alhamdulillah!"
"Zazzabi fa."

"Shima yau da sauki ba zafi sosai."
"Allah sauwake!"

"Bari naje wajen Inna!"
"Agaishe ta kan na shiga!"
Ya mike ya fita. Sashen Inna ya nufa tana Kitchen tana ta aikin abinda zata ci ya shiga da sallama. Sam bata ji ba sai da ya kusan minti nawa yana zaune ta fito rike da flask din tea tana ganin sa ta dafe kirji tana fadin
"Ni dai gaskiya in za a shigo min ana daga sauti a wani shiga hakki ne tin ban san da mutum yanzu da na yanke jiki na fadi fa saboda tsoro."

Bai ko tanka mata ba har ta gama fadan ta ajiye flask din tace
"Dadi na da kai ai ta magana ka maida mutum mahaukaci yau miskilancin yafi na ko yaushe kenan, ni dai wallahi yau ka shiga hakki na."

Mikewa yayi ya zura hannu a aljihu ya zaro kudi ya ajiye sannan ya wuce ya bar ta tsaye tana ta magana. Sashe su ya nufa a compound ya hadu da Farouk zai je gaida Inna. Ya gaishe dashi sannan ya juya ya tafi.

A inda Aliyu ya barta anan Farouk ya same ta tana ta fadan ya zauna yana fadin
"Ke kuma Inna haka kike ke kadai ma ki ta magana."
"Kada nayi dan uwanka ne ai ko me ma ya sakani magana."

"Kai Inna ke kullum baki da aiki sai tsokanar Yaya dan kinga baya tanka miki ne shiyasa."
"Na tsokane shin ko zaka rama masa ne kaji mutum ni akwai wanda ya isa ya rabani da Aliyu ne ko uwar sa karya take bare kai yaron da a guna ya tashi kuma dan yayi ba dai dai ba, ba za'ai masa fada ba haka ake duk iyayen ku su suka bata ku bakwa laifi su muku fada."

Mikewa yayi yace
"Ke kika tarbiyyar dasu a haka ai!"
"Au zakace min nima ya'yan nawa basu da tarbiya ko me?"

"A'ah fa ni na isa nace mahaifana basu da tarbiyya bayan duk duniya ina ganin babu mai tarbiyya kamata kuma wa ya bamu in basu ba ni dai kada ki hadani da Abbi da Abba dan nasan halin ki sam bakya son zama lafiya."
Ya juya ya fita. Inna tace
"Wallahi Umaru zaka hadu dani kuma sai Suleimanu yazo ya fada min shi ya baku damar min rashin kunya ko kuwa? Yara kowa sai rashin mutunci shi wancan ana magana ya tanka ma yaki sai kace wani kurma ai wannan shine dukum din, shi kuma wannan sai dan banzan baki kai su Suleiman dai sun iya haihuwa Allah ya shirya musu zuri'a."

Yana fita ya nufi parking space ya bude motar sa zai fita kenan wayar sa ta hau kara yana dubawa yaga Mama ce dauka yayi tace
"Kana ina tin jiya nake neman ka!"
"Gani zan fita!"

"To kazo ina son ganin ka!"
"Lafiya dai ko?"

"Lafiya Ahamdulillah!"
Ya kashe motar ya fita ya koma cikin gida. A dakin ta ya same ta ya shiga da sallama ya zauna.
"Fita zakai baka zo mun gaisa ba."

"Mama gaisawa ta nawa kuma?"
"To ba zaka biyoni daki ba ka sani ko akwai ahinda nake bukata sai ka gaishe ni a gaban kowa haka kaga dan uwan ka yanayi ko ya gaishe da uwar sa sai ya bita daki sun kara kuskus."

"Kai Mama shima fa ba kullum ba kina gani sai su kwana nawa ma Mami bata ganshi ba"
"To naji ya ake ciki maganar yarinyar nan?"

"Wacce yarinya?"
"Au kama manta wacce nace ka binciko min."

"Oh Mama na tuna Ummi ce ta tsince ta a hanyar su ta dawowa yadda na gane shine Yaa Haidar ke kula da lafiyar ta. Dan ciki ne da ita."
Nan ya dan mata bayani kadan. Shiru tayi tana nazari can tace
"Shikenan tashi kaje!"

Ya mike yace
"Sai na dawo!"
Ya fita. Da sauri ta mike ta nufin sashen Abbi. Yana zaune shi kadai ta zauna tace
"Amman dan Alah abinda ake min a gidan nan ana kyauta min kenan?"

"Me kuma ya faru Barira?"
"Har a kawo yarinya gidan nan tai kwana da kwanaki amman ba za a fadan ba ai ko ba zanje na duba ta na mata sannu bare ina son samun ladan duba ta."

"To kiyi hakuri ni kai na har yanzu banga yarinyar ba itama Hauwa sai shekaran jiya ta samu ta ganta kiyi hakuri kije ki duba ta Allah bada lada."
"Ah toh shikenan!"

Mami ce ta shigo ta zauna Abbi yace
"Mita take wai ba a fada mata zuwan Maryam ba."
"Ayya tayi hakuri!"

Mama ta mike tace
"Ai dai ko dan na samu ladan duba mara lafiya a fada min!"
"Ba dai nace ki hakuri ba to."

Mami ta juya ta kalli Abbi tace
"Yau zanje unguwar da na fada maka."
"To Allah kiyaye!"

Mama ta fita tana murmushin mugun ta sannan tace
"Zaku dauko wacce zata tarwatsa muku farin ciki indai aikin ku dauke dauke."
Tayi dakin ta.

Ummi ce ta fito cikin shirin ta, ta samu Aliyu zaune a falo tace
"My Son!"
Dagowwa yayi daga kallon system din da yake yace
"Ummi na kin fito!"

"Na fita son zan tafi Maryam na bacci please ka kular min da ita ba zan dade ba."
"Insha Allahu!"

Ya mike ya rakata har ta fita sannan ya dawo. Bai jima da dawowa ba yaji sallamar Mama mamaki ya fara me ya kawo Mama bangaren Ummi bayan yasan basa shiri sam Mama bata zuwa sashen Ummi. Tana sako kai ta tsaya tai turus dan bata taba zaton ganin sa ba tayi zaton ya tafi aiki. Cikin borin kunya ta fara in ina tana fadin
"Uhmm dama.. dama... daman zuwa nayi na duba yarinyar da aka ce ba lafiya dan kar ace ban zo ba."

"Tana sama!"
Ya fada ya cigaba da dannan system din sa da sauri tai sama tana hawa ta sauke ajiyar zuciya dakin dake farko ta nufa ta bude a kwance ta samu Maryam amman idon ta biyu mikewa tayi ganin mutum Mama ta karasa ta zauna tana mata murmushi tace
"Sannu!"

Hannu ta daga tai mata nuni da yauwah. Mama tace
"Ya jikin?"
Nan ma nuni tai mata. Mama tace
"Bakya magana ne?"

Kai ta gyada mata. Mama tace
"To sannu zuwa nai na duba ki sannan na taimake ki."
Shiru Maryam tai tana kallon ta tace
"Kin ganni nice kishiyar Babar Aliyu ina fatan zaki ban hadin kai a taimake ki?"
Kai Maryam ta gyada. Mama ta mike tace
"To sai gobe zan fada miki abinda zaki kinji?"
Kai ta gyada Mama ta mike ta fita. Aliyu na a inda ta barshi ta fito tanayi tana waiwaye.

Ya bita da kallon gefen ido kawai ya cigaba da aikn sa bayan minti ashirin ya mike ya hau sama dakin da Maryam take ya shiga tana zaune lokacin ya tsaya a bakin kofa yace
"Ki sauko kasa!"

Yana fada ya juya ya fita. Dining ya nufa ya dauko flask din Inna ya ajiye ya dauki ledar magunguna suma ya ajiye yana zama yaji saukowar ta daga benen ta zauna akan carfet tana mikar da kafar ta. Ya kalle ta, da gefen ido yace
'Gashi nan ki dauka ki sha!"

Kallon flask din tayi ta janyo ta bude kamshin kayan kamshi ya doki hancin ta wannan yasa taji kwadayin son shan sa. Ta dauki cup din ta tsiyaya kunun sannan ta dauka tai bismillah tare da runtsa ido ta fara sha. Tsami tsamin kunun yasa ta saki idon ta sai da ta shanye wanda ta zuba sannan ta ajiye cup din ta daura kan ta akan kujera. Duk abun da take yana kallon ta ta gefen ido. Lemo ya mika mata wanda take sha da sauri ta amsa ta bude ta kafa kai sai da ta shanye sannan ta ajiye tana mai da nunfashi tin da ta baro gida yau ne taji cikin ta ya cika dan da ta fara shan abu sai amai. Sai da ta jima ya balli magani ya bata amsa tayi kamar zatai kuka ta sha sai ta hau dafe kirji dan amai taji yana taso mata tin tana daurewa har sai da ta mike ta shige bandaki a guje taje tai aman. Yana daga falo yana jin tashin aman nata abin tausayi a hankali ya mike yabi bayan ta sai kwara aman take, dafe mata baya yai har ta gama sannan ta jingina da bango tana son zamewa ta kwanta kamo ta yayi tai sauri ta lafe a jikin sa dan yadda jiri ke dibar ta ya kamata suka fita ya kwantar akan kujera ya koma ya gyara bandakin. Kan ya fito har tai bacci ya kwashe kayan ya dawo ya zauna yana aiki yaji knocking yana budewa yaga mai aiki ya bata hanya ya koma ciki bayan sun gaisa.

Karfe uku Ummi ta dawo lokacin Maryam ta kara shan lemo da magani tana zaune rike da Alkur'ani Aliyu na dining area yana shan fresh yoo Ummi ta shigo da sallama Aliyu ne ya amsa Maryam kuwa dagowa tai tana binta da kallo direct wajen Maryam ta nufa ta kama hannun ta tace
"Ya jikin?"
"Da sauki!"
Tai mata nuni da hannu sannan tace
"Sannu!"

Ta mike ta nufi dining ta ajiye ledar hannun ta tace
"Sannu my son ya me jikin?"
"Alhamdulillah!"

"Allah kara sauki ya baka lada yai maka albarka."
"Amin Ummi nah!"

Ledar da ta shigo dashi ta tura masa tace
"Ga fruit nan ka wanko ka kawo mata ko zata ci bari na watsa ruwa."
Tayi sama ya mike ya shiga kitchen. Ya bude ledar Water melon, pineapple, Pawpaw, Banana, orange and Apple. Dauka yayi ya wanke ko wanne sannan ya yanka mata Apple ya ajiye a gefe yai blending banana da madara ya hada a cup ya dauka ya fita falo.

Cup din ya ajiye mata da bowl din Apple da fork. Yace
"Ki sha wannan!"
Dauka tayi ta kai baki ta kurba ido ta lumshe dan tana son Banana tas ta shanye shi ta dauki fork taci slice din Apple guda biyu ta ajiye fork din tana mai lumshe ido.

Ummi ce ta sauko sanye da daguwar riga marar nauyi ta nufi kitchen tana hada abincin dare. Karfe shida saura ta gama ta fito ta dawo falon ta zauna tana fadin
"Wa kinje wajen Inna?"
Kai ta girgiza. Aliyu ta kalla tace
"Kai ka hanata ko?"

"Haba Ummi batace zataje bane kuma ma bacci tai tayi sai da na dawo daga masallaci ma fa ta tashi shine tai sallah kika dawo."
"Tayi aman ko?"

"Da ta sha kunu ne tin safe!"
"Me taci da rana?"

"Juice kadai ta sha."
Ummi ta kalle ta tace
"Bakya sha'awr komai?"

Kai ta gyada ta shafa cikin ta tai mata alamar ta koshi. Aliyu ta kalla tace
"Sannu Allah maka albarka!"
"Amin!"
Ya amsa ya mike ya fita.


*Allah ya jikan mu ya yafe mana yasa muyi kyakyawan karshe.*


*Antty*[11/22, 13:46] Maryam S IndabawaπŸ₯°: πŸ’—πŸ’— *MATAR HAIDAR* πŸ’—πŸ’—
Page 49

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


Dakin da Maryam take ya koma ya same ta tana bacci fitowa yayi falo ya zauna yana tunanin me to Mama ta fadawa Maryam lallai yasan halin Mama sosai.

Zaune yake har Ummi ta dawo ta kalle shi, shi kadai a dakin tace
"Ina Maryam kuma?"
Sama ya kalla yace
"Tana daki!"

"Lafiya dai ko?"
"Eh na tashe ta dai tayi sallah ban sani ba ko ta koma."

Sama tayi tana fadin
"Amman kuma ai yamma tayi ta sauko."




A haka ya cigaba da kula da Maryam na tsawon sati biyu shi ke bata magani na safe, rana da dare haka nan Ummi in ta fita taga dan abu ta kawo mata shi kuma yan kayan kwadayi in suna gida yake hada mata duk da wasu da ta ci take yin aman su. Haka nan Inna ba ta daina kawo mata abun ba wani taci wani ko kalla bata yi.

Jikin dai da sauri dan maganin da ya daura ta akai kuma sun koma asibiti jinin ta yai kasa, zuciyar ma da sauki, kuma ta fara samun sauki dan sai ta kusan yini tana bacci.

A haka aka Fara azumi wanda Maryam taso tayi amman Aliyu ya hanata sam. Da azumi Ummi ko ta fita kafi karfe 2 ta dawo da ta dawo take shiga kitchen duk yadda Maryam ke son taimakawa Ummi a kitchen da ta shiga taji kauri ko wani abu za tai ta amai wannan yasa Ummi ta hanata.

Aliyu kuwa a daki yake yini karatu Alkur'ani wanda da anyi la'asar baya dawowa gida sai an sha ruwa dan a can masallacin alfurqan yake jin tafsir. Ana tashi zasuyi sallah da ya sha ruwa yake tahowa gida ko ya dawo ba wani abun kirki yake ci ba.


Tea ne sai dabino kawai. Daga nan in ya tafi masallacin sai goma zai dawo. Da ya dawo zai wanka ya dan kwanta karfe daya yake tashi kwana yake akan sallaya haka rayuwar su take gudana a koda yaushe.

A haka azumi ya Kai goma sha biyar lokacin tafiya Umrah Ummi hakura tai da zuwa saboda yanayin jikin Maryam. Abbi da Abba da Aliyu ne suka tafi. Mami sai saura sati daya sallah ta tafi. Gidan sai ya rage daga Inna sai Mama da Ummi da Maryam. Aliyu ma acan ba zama yai ba kullum yana harami yana sallah da addu'a ga matar sa da Maryam akan Allah ya bata lafiya. Kullum zai kira Ummi sau uku ya tambaye ta ya jikin Maryam kuma a tafiyar sa taje an kara dubata tare da cigaba da shan maganin ta. Sosai ta dan samu sauki dan cikin ya kara kwari.


*
Bayan Sallah da sati daya su Aliyu suka dawo, Ummi ce ta hada musu abinci na tarba, kala kala, lokacin da Aliyu yaga Maryam yai mamaki domin kuwa ta dan murmure ba kamar da ba.

Inna ta mike ta fita tana fadin
"Bari naje na bar wajen nawa ba kowa!"

"To Inna sai anjima angode! Maryam tai ma mata godiya ta tafi. Ummi tace
"Kina shiga kuna gaisawa da safe kinji?"

Kai ta gyada. Suna zaune a haka Aliyu ya shigo ya hangi Maryam zaune da dan cikin ta a gaba. Kai ya dauke dan ganin ta a wannan yanayin ya tino masa da Maryam matar sa. Ido ya dauke da sauri ya shiga dakin sa. Da kallo Ummi da Maryam suka bishi, yana shiga ya fada saman gado yana lumshe idon sa. Maryam kawai yake gani tana masa gizo a indon sa. Ido ya runtse yana fadin
"May your gentle soul continue to rest in peace Hayyaty"

Da kyar ya mike ya shiga ya watsa ruwa ya dauro alwala kiran sallah yaji ana yi ya fita da sauri, rike da ledar da ya shigo da ita. Ba kowa a falo Dan haka ya ajiye akan dining ya fita.

Bai dawo ba sai wajen Tara. Ummi, Abba da Maryam zaune akan dining. Ummi da Abba na cin abinci, Maryam Kuma gaban ta gashin kaza ne sai lemo da take Sha.

Aliyu ya karaso yana kallon ta, ta gefen ido sannan yaja kujera ya zauna a gefen Ummi. Yace
"Barka da dare Abba!"

"Ya kake Aliyu?"
"Alhamdulillah!"

Ya kalli Ummi yace
"Sannu da gida Ummi!"
"Yauwah Aliyu ka dawo lafiya?"

"Alhamdulillah!"
Ya kalli Maryam ya dauke Kai da sauri tare da fadin
"Ya jiki?"

Da hannu tai masa Alama da sannu. Abba ya kalle ta yace
"An samu abin Dadi ko motsin ta ba a ji."

Sukai murmushi gaba dayan su. Aliyu ya mike Ummi tace
"Abincin fa!"

"Ummi zanci amman sai anjima."
Ya fada yai cikin daki. Ummi plate ta dauka ta zuba abinci sannan ta kalli Maryam tace
"Kisha maganin ki fa!"

Fuska Maryam ta bata. Ummi tace
"Kin fison allura ko?"
Kai ta girgiza. Ummi tayi dakin Aliyu kwance ta same shi a kan gado ta ajiye abincin ta karasa ta dafa shi ya juyo yana kallon ta. Ta kamo hannun sa suka dawo kan kujera ta mika masa plate. amsa yayi ya fara ci sai da ya cinye ya sha ruwa sannan ta mike ta fice a dakin da kallo ya bita yana mai kara jin son Ummi yau da ba Ummi ya rayuwar sa zata kasance. Ummi itace hope din sa yana godiya ga Allah da ya bashi Ummi kamar yadda Ummi ke godiya da Allah da bai bata haihuwa ba amman ya bata yaro mai son ta da jikan ta.




*
Washe gari kafin Ummi ta tafi aiki tace mata tashi ta gaida Inna. Ta amsa bayan mai aikin su tazo ta gama aikin ta ta rufe sashen ta tafi wajen Inna. Sosai Inna taji dadi komai

Please Login or Register in order to submit comment