Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

*MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 33

By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW

*Bismillahir Rahmanir Rahmin*

******
Kano
A lokacin da Abbi ya dawo daga masallaci ya shiga bangaren Ammi a dai-dai lokacin Ammi ta farka daga baccin da take tun jiya cikin hanzari Abbi ya karaso yana mata sannu tare da taimaka mata ta zauna, bin dakin Ammi tafarayi da kallo a hankali abunda yafaru yafara dawo mata sabo fil a kwakwalwanta nan take hawaye suka fara zubowa akan kuncinta kallon mijin nata tayi cikin rawar murya tace
"Shin da gaske ne abunda kunnuwana suka jiyemun ko kuma mummunan mafarki nayi..!"

Abbi baice da ita komai ba, dan halin da yake ciki, mahaifin sa Malam ya aiko yaje a yau yau din nan wanda ya tabbata akwai matsala bai sam a yaya Malam zai dauki abun ba.  Kallon ta Abbi yayi ya mike ya nufi cikin toilet itako ta bishi da kallo zuciyarta na bugawa saboda tsabar tsoro da fargaba bai dade ba ya fito yace
"Ki tashi ki kimtsa kiyi sallah lokaci na tafiya..!"

A hankali tafara saukowa daga kan gadon ta nufo inda yake ta dafa bayansa cikin sanyin murya tace "Alhaji Ina tambayarka kamun shiru ina Maryam take, da gaske ba a ganta ba?"

Runtse idanu Abbi yayi cikin tsantsar bakin ciki da bacin rai ji yake kaman ya hadiye zuciya ya huta da kyar ya iya saita kansa ya juyo ya kwakulo murmushin dole ya daura akan fuskarsa saboda Dr yace a guji abunda zai bata mata rai ko ya tsorata ta nan kusa, dafata yayi cikin tsigar rarrashi yace
"Kije kiyi sallah lokaci na wucewa zan miki bayanin komai zuwa anjima..!"

Ya karisa yana mai kama hannunta ya nufi bakin toilet da ita, haka ta rika binshi duk da tana cikin fargaba da tsoro amma kuma haka nan taja bakinta tayi shiru tabi umarninsa, yana ganin ta shige ya juya ya fita falo bai jima ba ya koma daki akan sallaya ya tarar da ita tana lazimi don haka sai ya  koma sashen sa ya shiga  bathroom shima ya watsa ruwa har ya fito ya fara shafa mai bayan ya gama ya kimtsa a cikin fararen kaya a dai-dai lokacin ne ya koma sashen Ammi  ya same ta akan sallaya har lokacin tana ganin sa ta mike tana ninke sallaya hade da gaishesa fuskarsa dauke da murmushi ya juyo yana amsawa hade da tambayarta ya karfin jikin nata yanzun tace dashi Alhamdulillah da sauki sosai kafun ya sake cewa wani abu wayanshi dake kan gado tayi ringing.

Sai da gabanshi yafadi ganin numbern dake yawo akan screen na wayar cikin sanyin jiki Abbi ya daga wayar
"Malam yace a yau yake bukatar ganinka.."
Iyakacin abunda aka fada kenan wayar ta yanke wani yawu mai daci ya hadiye, zuciyarsa cike da fargaba da kuma tsoro dakyar ya saita kansa ya kama hanyar fita yana mai cewa
"Idan kin gama shiri ina jiranki a falo kuma kiyi sauri munkusa makara.....!"

Baki a sake ta bishi da kallo kirjinta na cigaba da bugawa tunani take ina Maryam take? Sannan me Abbi yake nufi da kin gaya mata komai? To wai ma ina zasuje can kuma ganin babu inda tunani zai kaita yasa ta bude wardrobe a kasalance ta dauko kayanta ta saka babu wani kwalliya ta dauki mayafinta kawai ta rufa ta fito a falo kuwa ta tarar dashi.

Baice da ita komai ba ya nufi hanyar barin dakin ta bishi a baya suka nufi parking space inda Alkasim da Abdulah suke tsaye suke jiran fitowansu, da daddaya suka rika gaishe ta da tambayar ta ya jiki itama jiki a sanyaye ta rika amsawa tana mai karewa gidan kallo kamar ranar ta fara ganin sa, haka nan suka shiga suka tada motar maigadi na musu Addu'an dawowa lafiya.

Alkasim ne ke Jan motar a yayin da Abdullah ke zaune a gefensa su Abbi kuma suna zaune a baya, duk yadda Ammi taso tambayan Abbi abunda ke faruwa hakan ya faskara saboda bai bata fuskan hakan ba haka suka cigaba da tafiya shiru babu mai magana.

Dan su Yaa Muhammad da su Yaa Ummulkhairi sun rigasu barin garin tin safe saboda Ammi bata tashi ba shiyasa su Alkasim basu tafi ba, duk da Alkasim bai so ya tuka Abbi ba dan ba yadda zai yi amman yana jin ciwon abinda Abbi yayiwa Maryam yanzu ko tana wane hali duk damuwar sa ya take ya jikin ta.

******
ADAMAWA
4:20pm

Tassss.... Kakeji Malam ya dauke Abbi da wani gigitaccen marin da ya tsorata dukkan wadanda ke cikin dakin saboda hakan bai taba faruwa ba a tarihin gidan, Malam mutum ne shi da bai yadda da dukan ya'yansa ba duk wani laifi da zakai masa sai dai ya kiraka yayi maka wa'azi ko matansa ne baya barin su dakar masa ya'ya sai dai idan a bayan idonsa amma sai gashi yau Malam harda mari, cikin tsananin bacin rai Malam yake bin Abbi da kallo idanun nan nasa sunyi jazur kaman garwashin wuta babu wanda bai tsorata da ganin yadda Malam ya koma ba saboda basu taba ganin hakan ba daga gareshi duk tsawon zamansu dashi cikin wani irin yanayi Malam yafara magana
"Hakika Muhammad ban taba tunanin cewa baka da hankali ba sai yau, bantaba tunanin zaka aikata irin wannan danyen hukuncin batare da ka sanar dani ba"

Cikin zubar hawaye Abbi ya kalli mahaifin nasa yana kokarin yin magana amma Malam ya dakatar dashi ta hanyar daga masa hannu, wani yawu mai daci ya hadiya kirjinsa na cigaba da bugawa, Malam maida idanunsa yayi ya kalli Ammi yace
"Sannan ke kuma kika kasa kira ki sanar dani abinda ya faru tinda shi yafi karfin ya fada min ko? ya koreta daga gidan batare da kunyi yunkurin fada min ba ko? To ina zata in ba nan ba?"

"Yace kada tazo wajen iyayen sa da yan uwan sa...."
Wani kallo da ya watsa mata ne yasata hadiye maganartata ba shiri tana mai sauke idanunta kasa saboda bazata iya juran ganin nasa idanun ba, safa da marwa Malam yake yi a tsakiyan falon tsit kakeji kaman babu wata halitta dake motsi a cikin perlourn duk da cewa a cike yake saboda family house ne Abbi ne da Yayan sa Usman kadai suka bar garin da gidan, gaba dayansu a tsorace suke da yanayin mahaifin nasu don basu taba ganin bacin ransa haka ba juyowa yayi ya kara maida idanunsa kan Abbi sannan cikin kunan rai ya cigaba da cewa,
"Dan kai ka hada mu da ita shine kake so ka nuna iko akan ta kace kar tazo wajen yan uwan ka, to ka sani zan iya rabuwa da kai amman ban rabu da ita ba, akwai wata karin hausa da aka ce abin kwan yafi kwan dadi...."

Ya dago ya kara kallon Abbi yace
"Hakika yau ina cikin wani irin bakin ciki da bacin rai wanda bantaba tsintar kaina a cikinsa ba tunda nazo duniya, wai shin anya ma kanada tunani kuwa, kana tunanin wannan hukuncin daka dauka akan Maryam kayi daidai kenan? Daka koreta gidan ubanwa kake so taje? Shin kayi tunanin hannun wa zata fada? Kayi tunanin wani irin hali zata shiga? Kana tunanin Maryam zata aikata wannan gagarumin laifin? Kafun ka tuhumeta yanada kyau kai kafara tuhumar kanka saboda Allah subhanahu wata'ala yace " idan kabi Matar wani kaima za'abi naka, idan kabi kanwar wani kaima za'abi naka, haka nan idan kabi yar' wani kaima za'abi naka" shin kayi tunanin hakan kafin ka koreta daga gidan ka..?"

Malam ya karasa maganan yana mai bin dukkan mutanen dake falon da kallo zuciyarsa na suya kaman zata ballo kirjinsa ta fito, wuri ya nema ya zauna yana mai sauke ajiyar zuciya ya dauki tsawon lokaci kansa a kasa baice komai ba, a cikinsu babu wanda yayi koda tari ne saboda a tsorace suke, Abbi ne cikin sanyin murya ya fara magana
"Ya Allah kaine shaida akan komai tunda nake a rayuwata ban taba aikata zina ba."

"Shiyasa nake tabbacin cewa Maryam bazata taba aikata abun ashsha ba na tabbata kaddarace kawai ta fado mata saboda ban gina zuri'ata da gurbataccen jini ba kaman yadda nima nawa mahaifin bai ginani akan hakan ba, Allah ka wadatani da arziki dai-dai gwargwado ka kuma wadatani da ya'ya' ka horemun ilimin addini ka darajani a idon duniya tun ina matashina, a cikin ya'yana babu wanda ya taba dauko wata hanya da ta kwaucewa fadin ka ya Allah, tunda nake a rayuwata baka taba kaddaramun wani abu na batanci ba a cikin zuri'ata sai wannan abu da yafaru yanzun wanda ni inada tabbacin cewa wannan wata kaddarace wanda ka saukar mana a cikin zuri'armu baki daya amma maimakon mu rungumi wannan kaddara hannu bibbiyu mu kuma yi kokarin cinye wannan jarabawa daka daura mana sai gashi muna kokarin butulce maka muna kokarin mantawa da irin ni'imar da muke ciki na tsawon shekaru muka...........!"

Malam kasa karasawa yayi saboda muryarsa da yafara sarkewa da alama kuka ne yake son kubce masa don haka sai yayi shiru kawai yana maida kansa kasa idanunsa kuma suna fidda ruwa, dukkansu kura masa idanu sukayi kowa jikinsa yayi sanyi jin furucin Malam hakika maganganun sa ya shige su sosai sai a yanzun ya tabbatar da ganganci da kuma kuskuren da ya tabka a rayuwarshi wani hawaye mai dumi ne ya zubo masa akan kuncinsa a hankali ya rarrafa ya nufi inda mahaifin nasa yake ya kamo kafarsa cikin muryan kuka yace
"Dan Allah Malam kayi hakuri hakika ni Muhammad na zama mai butulci ga ubangijina bacin rai ne ya kaini ga aikata hakan amma dan Allah kayi hakuri karkayi fushi dani...!"

Sai da ya dauki tsawon lokaci batare da yace komai ba kafun daga bisani ya mike ya basu baya cikin kakkausar murya yace
"Na baku kwana biyu rak daga kai har yan'uwan naka kuje ku nemo inda Maryam take ku dawo da ita cikin gidan nan...!"

Yana kaiwa nan ya fice daga falon ya nufi waje, suma da daddaya suka rika barin perlourn har suka watse ya rage daga Abbi sai su Yaa Muhammad da su Inna, a hankali Abbi ya matso kusa da Inna amma kafun yayi yunkurin yin magana ta mike tabar masa perlourn, zuba mata idanu yayi har ta bacewa ganinsa, Hajja ce ta dafa kafadarsa jiki a sanyaye ya juyo yana kallonta, cikin muryan rarrashi tace
"Muhammad ka kwantar da hankalinka insha Allahu za'aga Maryam ka cigaba da yi mata addu'a kai mahaifinta ne fushin ka akanta mummunan hadarine a gare ta don haka addu'a shine maganin komai!"

Kamo hannunta yayi cikin sanyin murya yace
"Haka ne Hajja amma dan Allah ki tayani bawa Malam da Inna hakuri saboda bazan iya jure fushinsu akaina ba..! Maryam kuma na daina fushi da ita Hajja na yafe mata, Allah ya bayyana mana ita."

Shafa kanshi tayi tana Murmushi cikin son kwantar mishi da hankali tace
"Karkadamu insha Allahu zanyi iyakan kokarina akan hakan yanzun dai ka tashi kufara shirin tafiya saboda kufara bada cigiyar ta kasan da karfi karfi akan bugi karfe..!"

Jinjina kai yayi yana mai mikewa a yayin da take mishi Addu'an Allah yabada sa'a, fita yayi ya nufi dakin mahaifiyarsa don bayajin zai iya tafiya batare da neman addu'a ta ba sai dai kuma ya shiga dakin ya kare maganarsa ko uffan batace dashi ba haka ya karashi zamansa ya fito, sai dai kuma wani abun mamaki a lokacin da suka shiryawa tafiya sai suka nemi Ammi suka rasa abun yayi bala'in dagawa kowa hankali cikin rawar jiki Abbi ya kira layin ta amma kuma yaki shiga kowa fa hankalinsa ya fara tashi magana har yakai kunnen Malam dake zaune a masallaci don haka cikin hanzari ya shigo cikin gidan don jin gaskiyar zancen.

Inna ce take sanar sa Malam cewar Ammi da Alkasim sun tagi neman Maryam in sun dace to in basu dace ba tace can wajen Ummun ta zata tafi ba zata iya zama ba tare da tasan a halin da Maryam take ciki ba.

Malam na jin haka ua juya kawai yayi ya wuce batare da yace komai ba, Abbi ji yayi gaba daya duniyar tai masa zafi shin da wanne zaiji da fushin iyayensa akansa ko kuma da rashin matarsa uwar yayansa?

A haka yayiwa yan'uwansa sallama cikin sanyin jiki suka wuce shida su Fadima da Yaa Muhammad. Sai Yayan sa Kawu Usman, Kawu Abubakar, Kawu Aliyu da Kawu Umar saboda su shiga cikin gari su bada cigiyarta a gidajen redio ko Allah zaisa a dace  dan Malam gaba daya yake fushi dasu

Su Abbi kuma sunje duk inda ya kamata su samu information akan Maryam amma shiru basu samu ba don haka suka wuce gidan TV da radio da kuma police station suka bada cigiyarta amma kuma duk da haka basu hakura ba sai da suka rika yawo a cikin garin Kano amma ko alamanta basu gani ba har washe gari, sai bayan kwana uku su Kawu Abubakar suka wuce Adamawa a yayinda shi kuma Abbi ya cigaba da aikin neman Maryam yana mai addu'a a cikin zuciyarsa akan Allah yasa a dace ga Ammi da dole sai yaje biko.

Bayan su Kawu Usman sun dawo suka fadawa Malam ba wani abu da aka samu akan Maryam har lokacin, zama yayi a daki yai duba, a halin da yaga Maryam tabbas tana cikin wahala amman kuma yana ganin wani hasken alheri na tunkaro ta wanda yasa ya samu nutsuwa sannan a duban da yayi ya gane har da asiri a barin ta gida wanda ya rasa wanda ya aikata mata wannan abin, yarinya karama a jefa ta duniya, wannan yasa ya kara tashi sosai da addu'a ba gashi ba har ga almajiran sa wanda ake kwana mata sauka da addu'oi.

*Allah ya jikan iyayen, yasa muti kyakyawan karshe. Amin*

*Antty*
[11/14, 12:40] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 34

By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW

*Bismillahir Rahmanir Rahmin*

Satin su Yaa Alkasim daya a Kano suna aikin cigiyar Maryam amman ba wani labari, wanda Ammi ta sa ya samar musu visa suka tafi, lokacin da Ammi taje gida yan uwan ta sunyi murna da zuwan ta duk da daga kallo daya suka gane tana cikin damuwa bayan an bata waje tai wanka taci abinci ta shirya ne, da yamma ta nufi dakin Mahaifiyar ta, Ummu na zaune ta shiga Ammi ta zauna, Ummu tace
"Ina Maryama na zata tare zakuzo ai, tinda ba lafiya ce da ita ba."

Damuwar dake kan fuskar Ammi ce ta kara daduwa tace
"Mahaifin ta ya korata duniya Ummu, bamu san inda Maryam ta shiga ba, na taho akan ba zan koma ba har sai ya nemo min diya ta."

"Me yake faruwa ne?"
Zama Ammi ta gyara tace
"Bayan doguwar jinya da Maryam tayi, mun dawo gida jikin yaki dadi gaba daya wannan yasa muka koma asibiti ana zuwa aka gane tana da ciki har na wata uku da kwanaki."

Shiru duk sukai can Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace
"Ummu, wai ace Abbi ni yake zargi da daurewa Maryam gindin yin ciki ki fada min tayaya zan bar Maryam ta zubar da mutuncin ta, shin ya manta daga gidan da na fito ne ko? Bayan kwana biyu da aka sallamo mu yace sam bai yadda Maryam ta zauna masa a gida ba, ki fada min tayaya haka zata faru, bama wai gidan sa ba har gidan yan uwan sa, a ranar na tura ta gidan Fadima kam na shrya mata tahowa nan, to shine fa tinda ta tafi ba a ganta ba ba duban da ba ai ba, amman ba a ganta ba."

"Innalillahi waina illahir rajiun me ya samu Muhammad ya yanke wannan danyan aikin da ilimin sa da sanin sa?"
"Shaidan."

Mahaifin Ammi ya fada yana shigowa dakin, zama yayi yana kallon Ammi yace
"Shine a lokacin kika kasa kiran kowa ki fada masa sai a yanzu da abin ya lalace, kun batar da yarinyar ku me kika zo yi anan to?"

"Abbu ba zan koma ba har sai ya nemon 'yata."
Wani murmushi Abbu ya saki yace
"Kinsan dai ba a yaji bare saki a gida na ko?"

Kai ta gyada yace
"Yauwa."
Ya mike ya fita, Ummu tace
"To yanzu cikin waye da Maryam din?"

"Ummu nima ban sani ba bamuyi maganar ba ina son muyi ba lokaci."
Ajiyar zuciya ta sauke tace
"Na yadda da Maryam, alamarin cikin nan tabbas akwai wani boyayyen abu a ciki, Muhammad bai kamata yai haka ba ya kamata ya bata dama ta fadi na wane in ma nemo sa ne ayi amman ba ace ita taje ta nemo sa ba sam wannan bai yi ba. Ina Malam shi me yace?"

"Daga can muka taho nan yace lallai su nemo Maryam cikin kwana biyu ransa ya baci sosai."
"Dole ai hukuncin da Muhammad ya yanke sam bai dace ba Allah ya kyauta Allah ya bayyana min Maryam dole a tashi da rokan Allah, Allah ya kare ta ya bayyana ta Amin."

Shiru sukai, Ummu tace
"Amman kema baki kyauta ba da kika taho me kike nufi kenan?"
"Ummu tayaya zan iya zama ba Maryam yarinya karama shekarar ta duka duka nawa ko sha takwas fa batai ba Ummu na kasa samun nutsuwa kullum tunani na tana ina, wane waje take, wane hannu ta fada, kar abinda ake zato taje ta aikata dan na tabbata Maryam ba a son ranta ta aikata abinda ta yadda ta aikata ba."

"Haka ne duk da ance ba'a shedar yaro amman nima ina ji a jikina Maryam ba zata taba aikata abinda ake zargi ba wannan boyayyen abun dai Allah ya kawo mai bayyana shi."
"Amin."
Ammi ta fada tana hade kai da gwiwa, dafata Ummu tayi tace
"Ba kuka zaki ba addu'a zaki mata kinji?"

Kai ta gyada tana mikewa ta shiga daki, kwana ta biyu Abbi yazo, zuri'a Alhaji Ahmad suka amshe shi hannu bibbiyu ba tare da nuna komai ba, sai da aka bashi masauki, da dare suna tare da Abbu, Abbi ya dukar dakai yace
"Abbu nayi kuskure wanda tin ba aje ko ina ba nayi nadama wanda bansan har yaushe zan daina wannan nadamar ba."

"Me ya faru?"
Nan Abbi ya bawa Abbu labarin komai, Abbu ya girgiza kai yace
"Muhammad ai hannun ka baya taba rubewa ka yanke, kayi kuskure kamar yadda ka fada wanda akace bakin alkalami ya riga ya bushe sai dai addu'a Allah ya bayyana Maryam da bayyana wannan gaskiyar."

"Amin Amin."
Sukai shiru, Abbi ya kara dukar da kai yace
"Daman tahowar Ammin tasu yasa nace bari na biyo bayanta na bata hakuri."

Murmushi Abbu yayi yace
"Ba komai ai ta sani ba'a yaji a gida na bare saki dan haka dole ta koma ko tana so ko bata so, me kayi mata ai kaima yar kace in za taji ciwo kaima zakaji, ni ba zan yadda akan ta a farai min yaji ba, ko zalunta ake ci gwara ta zauna tayi ibada bare bata taba kawon karar ka ba, sama da shekara kusan arba'in dan haka dole ta koma a cigaba da hakuri, Maryam kuma mun bayar da addu'a insha Allah za a ganta kuma tana cikin waje mai kyau da izinin Allah."

"Allah ya yadda."
Daga nan suka fara hira a tsakanin su, har suka kusan raba dare, washe gari da safe da Abbi ya shiga gaishe da Ummu, Ammi na zaune a falon sam bata san yazo ba dan ba wanda ya fada mata sai ganin shigowar sa tayi, kai ta dauke suka amsa sallamar ya gaishe da Ummu, Ammi ta gaishe shi ba tare da ta kalli inda yake ba ya mike tayi ciki, da kallo ya bita sai da ta shige ya sauke kai yana fadin
"Ummu ayi hakuri nima nasan nayi kuskure sharrin shaidan ne."

"Ba komai Muhammad wannan tamu kalar kaddarar kenan yanzu fatan mu kawai Allah ya bayyana Maryam, kuma yasa tana hannu na gari."
"Amin Ummu."

Bai jima ba ya bar wajen, Ammi da Alkasim kuwa kwana suke yi a harami suna addu'a Allah ya tsare Maryam. Kwanan Abbi biyu yacewa Abbu zai koma dan ya cigaba da cigiyar Maryam, Abbu yace tare da Ammi zasu tafi, sam Ammi bata so ba har da hawaye haka tabi Abbi suka bar kasar har da Alkasim.

*
Bauchi
Tinda aka fita da ita sai daya aka dawo da ita lokacin ta farka. Tea matar ta hada mata ta bata amsa tayi idon ta na cikowa da kwalla dan tasan ba iya sha zatai ba kuma yunwa take ji.
"Menene?"

Kai ta girgiza. Tace
"To kisha kinji!"
Baki ta kai tea din bata sauke cup din ba sai da ta sha kusan rabi dan yadda take jin yunwa tana gama sha ta mike a guje ta shiga toilet ta fara kwara amai tin tana iya yi har ya zama sai kakarin kawai. Ummi na dafe da ita har ta gama sannan ta dauraye mata baki ta fito da ita ta kwantar ta gyara wajen. Dankalin ta dibar mata tayo wajen gado dashi. Maryam na ganin haka ta juya mata baya tana girgiza kai.
"Ki tashi ki daure kici rashin ci shi yake sawa kike wahala a aman da ba komai a cikin ki."

Ta fada, tana dagota kuka ta sakar mata, Matar tace
"Dan Allah ki daure kici kinji!"
Ta dauki fork ta dauki dankali daya takai bakin ta, bata gama hadiyewa ba ta fara kakarin amai kan ta kai bandaki ta dawo dashi a tsakar dakin. Anan kasa ta kwanta tana dafe kanta da kirjinta. Ummi ta kamata ta shiga bandaki da ita ta dauraye mata baki ta dawo da ita kan gado wajen ta gyara sannan ta fita ta kira doctor dan ya saka mata ruwa tinda ba abinda take iya ci. Ruwan ya saka mata sannan tace
"Ya gwaje gwajen?"

File din da ya shigo dasu ya dauka yace
"Yadda nayi bincike na gane rashin maganar ta ya samu asali ne na shiga shock da tayi, sai ciki da take dashi na wata uku, bayan nan jinin ta ya hau sosai, ga ciwon zuciya dake son kama ta. Ko cikin zai sa jinin ta ya hau ya saukar mata da zazzabi da ciwon kai to bare ga hawan jini kuma gashi ba ruwa sosai a jikin ta dan bata iya cin abinci and she is too young tana bukatar kulawa sosai dan tana bukatar abubuwan gina jiki, dan ba jini da yawa a jikin ta."

"To yanzu ya za ayi, bata iya cin koma fa da taci abu sai amai ya za ayi da haka?"
"Babu wani magani da zai magance hakan sai dai tana samun abunda take so zan dai bata maganin rage aman."

"Toh nagode ya sallamar tamu fa!"
"A gaskiya halin da take ciki gwara ku kara zama a dan kula da ita sosai zaman ta a gida hatsari ne"

"To shikenan!"
Ya ajiye magani yace
"In ta tashi ta daure ta sha wadan nan."

"To insha Allahu!"
Abba ta kira tai masa bayanin komai yace to bari ta farka suji inda yan uwan ta suke dan ba zasu tafi su barta a haka ba.

Bayan sallah la'asar tana zaune akan sallaya Maryam ta farka. Ummi ce ta taimaka mata tai wanka ta dauro alwala wata doguwar rigar ta, ta bata ta saka tayi sallah sannan ta zuba mata abinci da juice a cup.

Juice din ta dauka ta kurba da yake na orange ne da dan tsami tsami sai taji dadin bakin ta ita ce har da shanye cup daya ta lumshe idon ta.

Gyaran murya Ummi tayi wanda yasa Maryam bude idon ta. Ta gyara zama Ummi tace
"Mu ma tafiya ne munzo Bauchi satin mu biyu a jiya zamu juya muka samu accident dake wanda yasa har muka kwana anan. jiya da na baki waya da nace ki kira gida baki kira kowa ba saboda me?"

Idon ta ne ya kawo ruwa. Matar ta bata paper ta amsa ta rubuta
"I don't have anybody to call, ni bansan ko ni wacece ba i only know two people in my life My Ammi and Yaa Haidar, bansan inda Ammi na take ba da Yaa Haidar ba....."

Ta kasa karasa rubutun dan yadda kuka ya kwace mata. Amsa matar tayi ta karanta sannan tace
"What is your Name?"
"Maryam Muhammad Jabeer!"

Ta rubuta. amsa tayi tace
"Where is you Father?"
Da hannu tai mata alamar bata sani ba.
"Your relative?"

Nan mata tai mata haka.
"Ina ne garin ku?"
Shima tai mata alamar bata sani ba.

Kallo ta sosai Matar tayi tace
"Ki fada min gaskiya Maryam bana son karya kinga taimakon ki nayi."
Paper ta dauka ta fara rubutu
"Wallahi bansan komai ba na ganni ne kawai anan ina rayuwa i can't recall my past My Ammi kawai nake tunawa ita ce Mama na. Sai Yaa Haidar my husband, wamda i know i loss him."


*Allah

Please Login or Register in order to submit comment