Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


"Mama....."

"Rufen baki ka baro asibitin nan yanzun nan."
Abbi ne yace
"kai da waye ne a wayar?"

"Mama ce."
"Bani ita nan."
Ya mika masa. Ya kai kunne yace
"Kowa yana asibiti ke me kike a gida?"

"Kanwar uwa tace a asibitin da zan zo na rashe."
"Ohk!"
Kawai yace ya kashe wayar. Farouk ya kalli Abbi yace
"Ni zan tafi Abbu."

"Akan me? Ita tace ka tafi ko?"
Shiru yayi yace
"To ba inda zaka tinda ita bata zo ba kai ka tsaya nasan an kusa fitowa kaima in ka tafi hankalin ka ba zai kwanta ba gwara ka tsaya kaga fitowar tasu."

"To Abbi."
Ya koma ya zauna.




*Allah ya jikan musulmai ya kyautata namu zuwan yasa muyi kyakyawan karshe. Amin.*





*Antty*[11/24, 12:23] Maryam S IndabawaπŸ₯°: πŸ’—πŸ’— *MATAR HAIDAR* πŸ’—πŸ’—
Page 53

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


Aliyu kuwa yana can masallaci yana ta addu'a ya dukufa a wajen sai wajen tara saura sannan ya mike ya fito jiki a sanyeye zuciyar sa sai bugawa take kamar zata fito daga kirjin sa. Inda su Ummi suke ya dosa yana shan kwana ana bude dakin aikin daya daga cikin nurse din ce ta fito rike da baby a hannun ta da sauri ya fara takowa Ummi ta mikawa Ummi na amsa ya karaso ya zura hannu ya amshe yaron yana leka fuskar sa. Murmushi ya saki sai kuma yai sauri ya mikawa Ummi ya kalli Nurse din yace
"Ya Maman sa?"

"Tana ciki komai lafiya."
A take a wajen ya juya ya kalli gabas ya durkusa yai sujudul shukur ya dago yana fadin
"Alhamdulillah Alhamdulillah."

Dakin ya shiga yaga sun fara turo gadon da Maryam take kai da sauri ya karasa wajen kan ta yana kallon ta idon ta a lumshe amman ta kwarmin idon ta zaka gane ta fad'a bin bayansu yayi.

Su Ummi kuwa suna waje sai murna suke Mami ta amshi Baby, Tana fadin
"Masha Allah tabarakallah!"

Inna ta amsa tana fadin
"Masha Allah, Allah ya raya mana kai."
Farouk ya karaso yana fadin
"Nima a bani dan Allah."

"Iya daukar yara kai?"
"Kai Inna."
Ta mika masa ya amsa yana leka fuskar Babyn yace
"Wow fine Baby me kyau Tarakallah."

Ya mikawa Abbi da Abba suma suka amsa sukai masa addu'a yadda mutanen nan ke farin ciki zaka rantse d'an cikin su ne ko jikan su. A haka su Aliyu suka fito ana tura gadon da Maryam take kai. Bayan su suka bi har aka karasa da ita dakin da aka tanadar dan kula da ita suna shiga su Ummi suka karaso rike da Baby. Bakin Gadon Aliyu ya karasa ya amshi Babyn hannun Ummi yace
"Ummu Haidar Bude idon ki, kiga Haidar din ki."

A hankali ta bude idon ta, ta sauke akan fuskar Baby dan Aliyu ya dago mata da fuskar Baby yadda zata gani tana daga kwance
"Yaa Haidar ya tafi Yaa Haidar ya dawo."
Ta fada, da sauri duk suka kalle ta suna son suji daga ina maganar ta fito babyn ta amsa ta kifa a saman fuskar ta tana sakin wani kuka mai ciwo tare da fadin
"Allah ya raya min kai Haidar, Allah ya maka albarka ya kare ka daga duk abin ki ya baka ilimi mai albarka, Allah yasa alummar musulmi suyi afahari da kai, Allah ya raya min kai Haidar kai kadai ne gata na, Abbin ka ya tafi ya barmu sai gashi Allah ya dawon da me kama dashi."
Ta karashe magana tana mai cigaba da kuka, wanda kukan kanaji daga kasan zuciyar ta yake fitowa.

Dago Babyn Aliyu yai yana fadin
"Yau naga raguwar Ammi kuka zaki fara koyawa Babyn ke da zaki masa addu'a gaskiya ba zan yadda d'ana ya koyi ragwantaka ba jarumi ne kada ki manta mai asalin sunan jarumi ne."

Hannu ta saka tana share hawayen idon ta, wani bacci ta fara ji yana fizgar ta bata fargaba ya dauke ta. Ummi tace
"Aliyu kuma bacci take?"

Ya duba yace
"Eh allurar bata gama sakin ta ba."
Ya mikawa Ummi Babyn.

Abba yace
"Ba wata matsala dai ko?"
"Babu Abba."

Abbi ya kalli agogo tara da rabi yace
"To Alhamdulillah dare yayi sai mu tafi ko? Tinda komai ya tafi lafiya."
Mami ta mike tana fadin
"To Ummin Aliyu mu zamu tafi sai da safe amman Aliyu yazo ya amso miki abinci tin safe bakuci komai ba, itama mai jegon kada ta tashi cikin dare tana jin yunwa ko?"

"Haka ne Mami mungode. Dr kaje ka kai su gida sai ka dawo din ko?"
"To Ummi!"
Lokacin har Abbi da Abba sun fita Mami da Inna suka bi bayan su. Farouk ya mike ya karaso wajen Ummi tare da zaro wayar sa dake cikin aljihu yace
"Bari na dauki hoton Babyn mu."

Ya dauke shi sannan yai masa kiss a goshi yace
"Ummi sai da safe ki kular mana da Babyn."
Ummi tai murmushi Aliyu ya fita yana daddana waya. Abba ne ya dauki Inna, Abbi kuma ya dauki Mami Aliyu da Farouk kowa ya dauki motar sa. A kusan tare suka karasa gidan. Abba ya raka Inna har bangaren ta sannan ya dawo sashen sa. Aliyu na shiga ya nufi dakin sa yai wanka ya canja kaya sannan ya fito. Dakin Maryam ya shiga hado musu kayan da zasu bukata sannan ya fito.

Bangaren su ya nufa ya samu Mami a kitchen tana hada wa su Ummi abinci har ta gama dafa tea. A basket ta saka masa da kayan tea da su lemo da ruwa sannan ya dauka ya koma asibitin.


Lokacin da ya koma Ummi na rike da Baby ya shimfida babbar carpet din da ya shigo dashi sannan ya ajiye kayan da yazo dasu a inda ya dace. Ya bude flask ya zuba ma Ummi abinci yace
"Ummi taho kici abinci nasan yau baki ci komai."

"Kai ma haka ai Dr."
"Ummi na dan ci dankali da safe."

"Wannan dashi da babu duk daya ai. Taho muci kaji."
Ya taho ya zauna kusa da Ummi zai dauki plate ta miko masa spoon tace
"Muci tare."

Tare suka ci suka sha ruwa sukai hamdala sannan yace
"Ummi bari naje office na danyi aiki."

"Yaushe zaka tafi gida dare na yi?"
"Ummi anan zan kwana."

"Anan kuma Dr ka tafi gida gobe da safe kazo kaji."
Yai shiru tace
"Jeka kaji dan albarka."

Dawowa yai ciki ya amshi Babyn yai masa addu'a sannan ya sumbaci goshin sa ya mikawa Ummi yana fadin
"Sai da safe to me zan taho muku dashi gobe?"

"Zan duba in akwai abinda muke bukata zan fada maka kan ka fito."
"To Ummi."

Ya kara matsawa kusa da gado ya leka Maryam dake ta baccin ta, sannan ya juyo ya kara leka baby da kyar ya iya cewa
"Ummi sai da safe."
Ya fita.


*
Washe gari tin asuba da ya dawo daga masallaci ya shiga kitchen shi yai musu breakfast ya hadawa Maryam abinda yasan zata iya ci marar nauyi ya hada komai a basket. Karfe bakwai ya fice ya bar gidan bayan ya gaida Abba tare da gabatar masa da abincin sa.

Yana zuwa ya samu Ummi har taiwa Baby wanka ta shirya shi cikin kayan sanyi sky blue sai kamshin turare yake. Amsar Babyn yayi ya zauna yana fadin
"Ina kwana Ummi na?"

"Lafiya lou ya gidan?"
"Alhamdulillah ya my son da Maman sa?"

"Gata nan tana ta bacci har yanzu bata tashi ba."
Gadon ya kalla ya dauke kai ya mai da kallon sa kan Babyn yana fadin
"Baby nah yayi kyau Ummi tai maka kwalliya kai kyau my baby."

Ya sumbaci goshin sa tare da zaro waya ya dauki babyn hoto yana fadin
"Ummi yaron nan tubarkallah kato dashi gashi kyakyawa."
"Ya maman sa take?"

"Ya fita kyau fa."
"Kai dai kace kafi son yaron ka."

"No ba haka bane Ummi yanzu dai ki yi break din ki tukkuna."
"A'ah bari na fara wanka dai."

Ta debi kayan ta ta shiga bandaki yana zaune rike da baby har ta fito cikin shiri sannan ta karya. Karfe takwas sukaji ana knocking kofar dakin izinin shiga suka bayar sai ga Farouk ya shigo da sallama suka amsa ya karaso ya zauna gefen Aliyu yana fadin
"Ina kwana Hamma?"

"Ka tashi lafiya?"
"Alhamdulillah!"
Ya fada yana leka Babyn sannan ya dago yace
"Ummi ina kwana?"

"Lafiya lou ya gidan?"
"Alhamdulillah!"

Ya kalli Aliyu yace
"Hamma ka ban Babyn mana nifa shi nazo na gani kan na tafi aiki."

Mika masa yayi sannan ya mike yana fadin
"Bari naje Ummi ba abinda kuke bukata?"
"Babu Dr."
Ya juya ya fita. Bai jima da fita ba mai aikin su ta kawo abinci daga wajen Mami. Farouk sai da Ummi ta kore shi sannan ya tafi da kyar wajen tara.

Karfe goma Maryam ta farka Ummi ta karasa tana fadin
"Sannu Maryam!"
"Yauwah Ummi nagode."

Murnushin fuskar Ummi ne ya dado jin da gaske maganar Maryam ta dawo. Ummi tace
"Bari a kira Dr dan ya duba ki ko?"

Kai ta gyada Ummi ta kira Aliyu ta sanar dashi, Dr da tai mata aiki ya kira ai kuwa nan da nan tazo ta duba ta komai normal bayanin abinda zataci tai mata da yadda za ai mata wanka dan kar ruwa ya taba inda aka manne dan ba dinki akai mata ba cealing (like) wajen akai.




*Allah ya jikan musulmai ya kyautata namu zuwan yasa mu cika da kyau da imani. Amin*


*Antty*
[11/24, 12:24] Maryam S IndabawaπŸ₯°: πŸ’—πŸ’— *MATAR HAIDAR* πŸ’—πŸ’—
Page 54

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*



Zaune yake a office dinsa, system din sa ya janyo ya fara kiran Sitti ta ciki dan vedio call yake so suyi yana kira Najwa ta dauka tana fadin
"Yaya ni baka kira na mu dan gaisa kaji ya karatu sai Sitti ko?"

Kai ya shafa yace
"Ke meyasa ba zaki kirani ba. Bawa Sitti wayar nan ko da yake ina system din ki? Ki hada mu tanan zan kira yanzu."
"To mu gaisa mana."

"Ki kira in kina son mu gaisa."
Ya kashe ta tabe baki tana fadin
"Kai Yayan nan haka kake. Uncle Abubakar kuwa kullum cikin kiran mu yake, haka Yaa Farouk amman kai sai Sitti komai Sitti."

Ta dauko system din ta ta fita falo inda Sitti take, Kaykyawar tsohuwa ce zaune akan kujera amman ba tsufa sosai tai ba dan tana samun kula daga ya'yan ta tayi shekaru kusan tamanin amman in ka ganta sai kace batafi shekara sittin ba, karasawa tayi wajen ta, ta tabe baki tare da fadin
"Yaya ne ya kira."
"Yana ina bani wayar?"

"So yake ya ganki."
Nan ta kunna ta kira sa ta mike ta bar wajen. Fuskar Aliyu na bayyana tace
"Likita bokan turai. Abin so! Jikana dan Albarka."

Wani murmushin ne ya kara sauka a fuskar sa yace
"Sitti na, farin ciki na, gwarin gwiwa ta ina kaunar ki."
"Fadan albishir din Abin so."

"Mu fara gaisawa Sitti."
"To ya yan gidan ina fatan kowa lafiya?"

"Alhamdulillah Maryam ta haihu jiya an samu Baby Boy."
"Alhamdulillah Masha Allah. Allah kara mata lafiya ita da babyn Amin."

"Amin Yaa Hayyu ya Qayyum!"
"Wannan shi ya saka farin ciki abin so?"

"Shine Sitti ban taba jin son wani abu a duniya kamar yaron nan ba Sitti baki ga babyn ba tubarkallah!"
Ya fada yana daukar wayar sa ya nuna mata hoton babyn tace
"Masha Allah Tubarkallah Allah ya raya yai masa albarka."

"Amin Ya hayyu ya qayyum."
"To ya aikin ina Babyn da Maman sa?"

"Sitti aiki akayi mata dan jiya yanzu mun fitar da rai da ita tasha wahala amman yanzu komai ya wuce tana lafiya ita da Baby."
"Alhamdulllah Masha Allah. Anjima ka hadani dasu mu gaisa."

"Insha Allah!"
"Madallah."

"Sitti bari ma naje dan naga wannan tsohuwar na can dakin ma yanzu."
"Kawar tawa kake cewa tsohuwa ai nafita tsufa."

"Kai Sitti ita waccen kinsan dai halin ta."
"Sai hakuri ai kasan in mun tsufa ai."

"Ke bakya haka."
"Kowa da irin sa ita daman haka take tin da kuruciyar mu tana da fada"

Baki ya tabe yace
"Bari naje zan kira ki a wayar ki, yauwa ki daina barin yaran nan na daukar wayar ki."
"To Abin so a daki na batar ita kuma tana ciki shiyasa."

"To bari naje."
Ya kashe ya nufi dakin. Acan sukai waya da su Ummi da Mami har da Inna da maijego.


*
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya cikin kwana biyar din da Maryam tayi taga kulawa gata daga wannan ahalin sosai suke bata kulawar su da nuna mata kauna baga ita ba baga Babyn ba. Farouk kuwa safe, rana, dare sai yazo kuma kullum da siyayyar da zai yo wa Baby.

Aliyu kuwa in ya dauke Babyn sai su Inna sunzo sun ishe shi da kira yake dawo dashi. Sam ya hana a bawa yaro ruwa dan yace a nonon ma akwai ruwa dole suka hakura duk fadan Inna sai cewa tayi
"In ya kashe shi ai shikenan."

A haka sukai kwana biyar aka sallamesu suka koma gida Maryam ta cigaba da jego. Ranar suna kuwa Abba ya siyo rago Aliyu kato sa ya kawo yace a yankawa Baby Aliyu Haidar. Mami da Abbi kuwa kaya masu tsada da kyau sukaiwa Maryam da Babyn ta Inna ma ba abarta a baya ba ta kawo mata atamfafofi da kayan Baby da turare da sabulu Farouk kuwa kullum akwai siyayar da yakewa Haidar Abba ma ya bada kudi masu yawa yace ayi duk abinda ya dace.

Abinci mai rai da lafiya akai aka yi walima yan gidan su Yaa Asiya, Hannah da Yaya Bilkisu da masu gadi da masu aikin gidan sai yan kawayen Ummi na gun aiki da suka san da zaman Maryam din. Maryam ranar suna ta sha kuka bama da taga gatan da aka nuna mata ta tabbata ko a gidan su sai haka ta samu abinda bata taba tunani ba. Babyn ta ya zama dan gata wanda kowa ke so da son faranta masa da ita dan haka ba abinda zatace sai Alhamdulillah.

Da dare bayan kowa ya tafi Ummi tanawa Baby wanka, Maryam ce ta fito daga wanka, daure da towel ta zauna a gefen gadon Ummi tace
"Ina fatan dai ruwan bai taba wajen?"

"Eh Ummi."
Ta dauki mai ta fara shafawa, wayar Ummi ce tai kara ta dauka tana fadin
"Mutanen Canada!"

"Ummi ina yini yasu Maryam da Babyn?"
"Suna lafiya, gasu nan."

"Bani mu gaisa tinda baki ya bude ai ana gaisawa yanzu ko?"
Mikawa Maryam wayar tayi ta amsa suka gaisa, sannan yace
"Me take so?"

"Ba komai Uncle."
"Kin tabbata?"
Kai ta gyada yace
"Shikenan ga Auntyn taki tace zaku gaisa."

Amsa tayi suka gaisa sannan ta mikawa Ummi, Ummi tace
"To Sadik sai anjima?"
"Eh Ummi amman gobe zan sako kaya a jirgi in yazo zasu kiraki kayan Maryam da Baby ne."

"To madallah Allah yayi albarka."
"Amin Ummin mu Allah kara miki lafiya ina alfahari dake."

"Nima ina alfahari dakai Sadik."
Sukai sallama, doguwar riga Maryam ta saka ta zauna a gefen gado tana shirin kwanciyya akai knocking, hijab ta zura sannan suka bada izinin shigowa, a hankali ya bude dakin ya shigo, sanye yake da milk din wando da blue din riga sai kamshi yake ya shigo daki da sallama suka amsa ya karasa wajen Ummi dake zaune a kan carpet rike da Baby Haidar, amsa sa yayi ya mike yana kallon sa, addu'a yai masa yace
"Yau yasha hannu."

Ummi tace
"Ai baka ga ba shiyasa ina masa wanka ya fara bacci."
Kwantar dashi yayi yana kara tofa masa addu'a ya kalli Maryam yana fadin
"Akwai abinda kike bukata ne?"

Kai ta girgiza ya kalli Ummi yace
"To sai da safe Ummi."
"Allah bamu alheri."

"Amin."
Ya juya ya fita.


*
Haka Ummi ta cigaba da kula dasu suna jego cikin sati uku Haidar yayi wata uwar kiba ya kara kyau kamar sa da mahaifin sa ta kara fitowa sosai yaron kamar d'an larabawa gashi da farin jini duk wanda ya ganshi sai yaso ya dauke shi dan in sunje asibiti ma ai ta son daukar sa wannan yasa Ummi take tofe shi tare da saka maman sa ta tofe shi a ko da yaushe.

Ba abinda Maryam take sai jegon ta kullum tana daki daga wanka sai ci sai kwanciyya itama cikin sati ukun tai kyau ta murnure kai ba kace ita ce me shayarwa dan kuruciyyar ta sai ta kara fito wanda a da cikin yasa zakaga kamar babba ce amman yanzu kowa ya ganta yasan yarinya ce karama. Ba abinda takewa Haidar Ummi da mai aikin da ke tayata kula da ita su ke masa komai dan in ba shan mama zai ba, bata ganin sa a wajen ta daga bayan Ummi sai bayan Karima dake tayasu aiki. Da yamma kuwa Aliyu na dawowa zai dauke shi duk aikin da zai yana tare dashi yake aiki dan Haidar bai da rigima sam ba zakace da yaro a gidan bama dan kan yai kuka ana jima. In zaije sallah ne zai kaishi amman da ya dawo yana wajen sa kwana ne kawai bayayi a waje sa. Yana son Haidar dan komai ya gani sai kawo masa. Maryam kuwa sai suyi sati ma bai ganta ba dan tana sama da ya dawo yaga yaron sa shikenan ya manta da ita a office ne wani lokacin yakan yawan tina ta.

Farouk ma kan ya fita sai yazo ya ganshi haka in ya dawo shima duk abinda ya gani na yaro da na babba da ya burge shi zai kawowa Haidar. Wani Ummi har dariya take dan kafin yai amfani dashi ma yasan za a dade.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya har sukai arba'in. Maryam ta zama budurwa sosai ko dan shayarwa take ne ita da yaron ta kullum kara kyau suke Haidar kuwa ya zama dan lukuti sam Aliyu bai bari a bashi komai mama kadai yake sha yace sai yayi wata shida Inna tai fadan har ta gaji in Maryam taje tai ta zugata wai ta bashi ruwa su daina daukar hakkin yaro Maryam sai tace to tana dariya.


**** **** ****
Yamma ce mai cike da ni'ima wacce ya hade da sanyin damuna ta fito cikin atamfa riga da zani lemon green da akai kwalliya da red colour riga da zani ne, rigar ta zauna cif a jikin ta sai zanin dake zaune a 'kugun ta yai das dashi. Ta saka dan kunne da sarka na gold wanda Ummi ce ta siya mata, ba makeup a fuskar hoda ce kawai sai man lebe ta sauko daga bene kafar ta sanye da wani red flat half cover sai hijab din ta ja dake rike a hannun ta.

Ummi ta gani zaune a kan kujera Haidar na hannun ta tana masa wasa. Zama tayi a hannun kujera tace
"Haidar da matar shi."

Dariya Ummi tayi tace
"Ah kina so dai ki ganmu a rana ne kawai ko?"
"Uhmm Ummi wajen Inna zani."

"Zauna ki bashi ya sha dan nasan kika fita sai an ganki."
Dariya tayi tace
"Ummi wannan yaron ya fiya ci."

"Dadin ta jiki na nunawa ko zakin fama."
"Wallahi Ummi ni dai na fara gajiya da shan shi."

"Kai Maryam in ba dan na ganki ba kila har ayi magariba bai nema ba, kawai dai dan kar ki fita ki jima ki dauki hakkin sa ne."
Zama tayi ta juyawa Ummi baya tace
"To zugen."

Ummi ta sa hannu ta zuge mata sannan ta sauka kasa ta zauna akan filo ta tankwashe kafa dan Aliyu ya hanata zama akan kujera ta bashi mama yace in ta zauna a kasa sai ita da yaron sun fi jin dadin.

Maman ta fito da shi ta saka masa a baki tare da furta bismillah cafkar da yayi yasa ta runtse idon ta tana fadin
"Ummi zai cire mamana."

"Wallahi Maryam ke raguwa ce, ace har yanzu kinki ki saba da shayarwa."
Ido ta bude tana cije baki tace
"Uhmm Allah da zafi Ummi."

Tai maganar kamar zatai kuka. Murmushi Ummi tayi, Maryam ta kalli Haidar dake shan maman yana lumshe ido hannu ta daura akan sa tana shafa sumar kasa wacce take kwance luf luf a haka har ya koshi ya zare bakin yana bangale mata bakin sa yana mata dariya kumatun sa na lotsawa. Tissue ta dauka akan center table tana goge masa gumin da ya tattsafo masa a goshi, tana masa murmushi sai da ta goge ta dagashi ta daura a kafata tana shafa masa baya gyatsa yayi ganin Ummi a bayan sa ya dinga mata dariya yana mika mata hannu alamar ta dauke shi.

Amsar sa tayi Maryam ta mai da maman ta sannan tace
"Ummi zugen."
Ta zuge mata ta mike tana fadin
"Har ya zuke ni bari naje wajen Inna ko zan samu kayan dadi."
"Kwadayi dai zaki daman."
Dauke filon tayi ta saka hijab din ta tana dariya tace
"Sai na dawo."


*
Ta fice daga dakin tana fita compound Farouk na karasowa wajen daga gani bangaren Ummi zai je,
"Sannu da zuwa Yaa Farouk."
Ta fada kan ta a kasa. Kallon ta yai yana murmushi yace
"Yauwah ina my son."

"Yana ciki."
Yayi bangaren Ummi ita kuma ta juya tayi bangaren Inna. A compound ta same ta tana gyara shuke shuken dake harabar wajen.

Ta shiga da sallama Inna ta dago tana fadin
"Ai da zan zo biko."
Murmushi Maryam tayi tace
"Biko kuma Inna?"

"Eh mana ina jin jiya da shekaran jiya fa baki zo ko gaishe ni ba, bare yar hirar da muke."
"Lah Inna jiya ne fa shima kuma dan munkai Haidar asibiti ne. Ai yau gani nazo mu sha hira."

"To shiga gani nan shigowa."
"Ah haba dai Inna kawo na karasa."

"A'ah a'ah je ki zauna na gama wanke tsintsiyar kawai zanyi."
Tayi ciki Inna ta karasa bakin famfo ta wanke tsintsiya sannan ta shiga dakin. A kan kujera ta samu Maryam ta shige kitchen bata jima ba ta fito da dan bowl tana fadin
"Dan ke nayi fa jiya kuma baki zo ba, shine nace zan zo biko sai na taho miki dashi."

"Kai Hajiya Inna shiyasa nake sonki."
Ta bude bowl din kaza ce akai mata pepper chicken ajiye bowl din tayi tace
"Bari na wanko hannu na."




*Allah ya jikan musulmai ya kyautata namu zuwan yasa mu cika da kyau da imani. Amin.*


*Antty*[11/25, 11:27] Maryam S IndabawaπŸ₯°: ο»Ώο»Ώ
πŸ’—πŸ’— *MATAR HAIDAR* πŸ’—πŸ’—
Page 55

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*





Ta shiga kitchen ta wanke ta fito dauke da lemo mai sanyi ta zauna tana ci Inna na bata labari tana ji tana dariya hade da lumshe ido dan dadi nama bata farga ba taji sallamar mutum dankwallin ta dake ajiye akan kujera tai saurin dauka ta yafa a jikin ta, tin kan ya shigo kamshin sa ya danno kai.

Dakin ya shigo, sanye yake da dogon bakin wando da farar riga, mai dogon hannu, ba a inda idon sa y fada sai akan Maryam, kai ya dauke ya karaso gaban Inna ya ajiye mata ledar da ya shigo ya juya ya nufi kofa Maryam tace
"Sannu da zuwa."

"Yauwah."
Kawai ya fada ya sa kai za fita, Inna tace
"An gode Allah maka Albarka."
"Amin!"

Ya amsa tare da ficewa. Inna ta tabe baki tana fadin
"Duk jikoki na nafi son yaran nan amman shi matsala wani lokacin miskilanci da nukufarci ji dai yadda ya ke magana kamar bai so. Dubi dai yanzu fura ya kawon da nono kusan kwarya guda dan yasan ina so."

Ta fada tana leka ledar da ya ajiye mata. Murmushi Maryam tayi, Inna tace
"Wallahi shima yana so na, da sam ba haka yake ba yaro mai fara'a da son mutane amman daga mutuwar matar sa duk ya koma haka, nayi nayi suyi masa aure sunki, da sun masa da kila ya koma yadda yake Allah dai ya bashi mai tausaya masa da son sa kamar matar sa. Ina fada miki yar yayar Babar sa ce acan turai suke inda Najwa take karatu in kinga yadda suke soyayya a da sai sun burge ki, wallahi ban taba ganin Aliyu da ita sunyi fada ba tana da sanyi hali da hakuri yarinyar kirki mai tarbiyya da son mutane ga kyauta to Allah ya fimu son ta shekarar su biyu bata haihu ba sai da ta samu ciki kuma ya hau bata wahala, haka aka sha fama ke dauke matar sa yai ya kai can uwa duniya sai da cikin ya isa haihuwa da kyar ya kawo ta gida ashe rabuwar ta kusa lokacin basu kwana ashirin ba ta tashi da nakuda ina fada miki, ta sha wuya baki ga yadda ya tashi hankalin sa ba ke kace shi ke nakudar haka sukace ba zata iya haihu da kanta ba shine fa za a shiga aiki, ba ai aikin ba Allah ya amshi a barsa kan ai wata wata yaron yabi uwar zo kiga Aliyu wallahi kamar ba zai rai ba ya daina ci ya daina sha ga tunani ai fa nan ciwo yai raf dashi, ciwon nan da yanzu ba tsoho ba babba ya kama shi wai hawan

Please Login or Register in order to submit comment