Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaka auro mana karuwa a cikin zuri'ar mu ba."
Rarrafawa yayi wajen Ammi yana fadin
"Ammi ba haka bane ku tsaya nai muku bayani."

Ido Ammi ta zaro tace
"Ashe kama sani har so kake ka kare ta."
Ganin Ammi ba zata saurare shi ba ya karasa wajen Dad hawaye na zubo masa yace
"Dad dan Allah ka saurare ni wallahi ba haka bane, Maryam yarinya ce mai ladabi da biyayya ga hankali da nutsuwa..."

Hannu Dad ya daga masa yace
"Khalifa ka makaro ba zan saurare ka ba sam, meyasa tin tini baka fada mana ba, duk matan garin nan ka rasa wacce kake so sa wacce ba asan asalin ta ba, a gaskiya ba zan iya wannan abun ba kayi hakuri amman tabbas bakai ba auren wannan yarinyar."
A razane Muhammad ya dago yana girgiza kai, Dad ya mike yai daki kallon Ammi yayi ya rarrafa wejen ta ta mike tana fadin
"In ka sake kai min wannan magana akan wannan yarinyar tabbas ranka zai baci."

Tana fada ta mike ta bar wajen, kai ya hade da gwiwa yafi minti uku sannan ya mike ya nufi dakin Dad a zaune ya same shi ya shiga yace
"Dad dan Allah kayi hakuri wallahi ina son Maryam ita ce rayuwa ta in kuka hanani auren Maryam wallahi mutuwa zanyi....."

"Sai dai ka mutu Khalifa ba zan taba yadda d'ana ya auri wacce bata da asali ba dan azo ana mana yarfe kasan ni dan siyasa ba abinda bakai tsamani bama zakaji dan haka ba zan yadda ba kayi hakuri kawai."
"Dad amman ka duba a yanzu naje musu da zancen nan abun ba zai musu dadi ba sam..."

Kallon sa Dad yayi yace
"Maganin su da basu sanar mana ba."
"Wallahi Dad sun fada min kuma sunce na fada muku..."

"Me ya hana ka fada manan?"
Shiru yayi, Dad yace
"Maganin marar neman shawara da fadar gaskiya da tin can ka fada haka ba zai faru ba zamu taka maka burki wallahi Khalifa ban yadda ka auri wannan yarinyar ba dan haka tashi ba bani waje"
Ya fada yana nuna masa kofa, yadda yai maganar cikin bacin rai yasa Muhammad tashi ya fita da sauri, yana fita ya shiga mota ya bar gidan, gidan su Maryam ya isa wanda ya kira Abba ya sanar masa anan akai wannan abun.



*
Yadda yaga rana haka yaga dare, sam ko bacci bayaji haka da safe ko yunwa bai ji ba bare yaci abinci yana dawowa daga masallaci ya nufi sashen Dad, wanda shi har ya shige anan falo ya zauna yana jiran fitowar sa, har karfe goma sannan Ammi ta shigo tana ganin sa ta dauke kai ta nufi sashen Dad da sauri ya sha gaban ta dago tana kallon sa idon sa cike da hawaye yace
"Ammi ke uwa tace dan Allah kada ku hukunta ni ta wannan hanyar wallahi ina son Maryam Ammi dan Allah...."

"Khalifa, ka riga ka bata mana rai wanda yasa ran Dad dinku baci dan haka ba abinda zan iya."
Ta shige komawa yai ya zauna wajen karfe goma sha daya Dad ya fito ya nufi dining karyawa yayi sannan ya mike zai fita Muhammad ya karasa cike da tashin hankali yace
"Dad dan Allah kayi hakuri naji ku hukuntani amman ku aura min Maryam dan Allah."

"Khalifa kayi hakuri domin na yanke hukunci zan aura maka yar wajen kanwar Ammin dan na riga na gayyato mutane ba zan yadda sunana ya baci akan ka ba."
Yana fadar haka ya juya ya nufi kofa har ya karasa Dad ya juyo yace
"Ina jiran a masallaci."

Anan ya zauna ya dinga kuka, Ammi ta fita da kyar ya mike ya nufi sahsen Momy wacce tana falo cike da yan biki taga shigowar tasa da sauri ta mike ta jasa suka nufi wani daki ta zaunar dashi tace
"Lafiya Khalifa?"

Ido ya runtse yace
"Momy akwai matsala fa."
"Wacce irin matsala karfe nawa yanzu? Kana nan baka shirya ba."

"Momy bansan wanda yazo ya fadawa su Dad cewar wai Maryam bata da asali wannan yasa su Dad suka ce to ba zan aure ta ba, Momy dan Allah ki taimaken wallahi ina son Maryam in ban samu Maryam ba zan iya mutuwa."
"Innalillahi wainna illahir rajiun me hakan ke nufi? Yanzu ya ake ciki? Meyasa tin jiya baka sanar min ba, tabbas in Maryam taji wannan abun zata rasa sauran lafiyar ta, Allah ka tausayawa wannan yarinyar."

"Na shiga uku."
Muhammad ya fada. Momy tace
"Je ka shirya insha Allahu komai zai zo dai dai."

Cikin sauri yaje ya shirya yana fitowa ya samu Abdul a falo, Abdul yace
"Me ka tsaya yi ne har lokaci yana son kurewa."

Dagowa yai ya kalli Muhammad yai kyau cikin farar shaddar sa daga kallo kasan ango ne sai dai yadda idon sa yai jajir ya nuna cewa akwai matsala. Da sauri Abdul yace
"Lafiya Muhammad?"
"Muje zamuyi magana a mota."

Suka fita Abdul ke tuki suka nufi masallacin da za a daura auren, Muhammad ya fada masa komai, Abdul cike da mamaki yace
"Bansan da haka ba a tunani na Maryam yar uwar su Najwa ce."

Dai dai lokacin da suka karasa masallacin wanda har an tada sallah, jam'i suka hau wanda aka tayar da sallah, bayan an idar yaji an kira waliyan amarya da ango yana zaune inda yake banda bugawa babu abinda zuciyar sa take, lokacin da yaji ana fadin an daura auren Maryam da Aliyu, yai dai dai da tsayawar numfashin sa wanda ya fadi anan da sauri Abdul da wasu abokan sa suka dauke shi suka fita dashi ruwa suka shafa masa amman sam bai farka wannan yasa suka tafi asibiti dashi.



*
Duk abinda ake Maryam bata fahimta sai da taji abinda Abba ya fada a karshe wato an daura auren ta da Aliyu, sai a sannan ta gama fahimtar abinda Abba ya fada few seconds ago, don tun bayan maganarsa taji komai na kanta ya kwance ta kasa apprehending, da kyar ta gano me yake nufi, ji tayi kirjin ta yai nauyi, kan ta kamar an daura dutse a hankali ta dago kai tana kallon mutanen dakin kowa fuskar sa babu wani tashin hankali, Aliyu ta kalla wanda kansa ke a kasa, ba zata gane a wane hali yake ba sai Farouk da ke gefen sa cikin sarewa yake kallon yan dakin, kan ta ta mayar saman cinyar ta bata kara magana ba a haka su Inna da Sitti suka gama tattaunawa wanda bata san me suke fada ba dan tayi nisa a tunani abinda Aliyu ya gudar mata kenan gashi nan yau ya faru, lallai wadan nan mutanen masu son ta ne ji yadda suka rike ta ba kyama duk da basu san asalin ta ba har yau suka bawa dansu auren ta wannan wane iin mutanen masu tausayi tabbas ko bata son Aliyu zata zauna dashi tai masa biyayya ko dan ta saka masu da hallicin da sukai mata. To amman ta ina Aliyu zai so ta bayan yana rike da soyayyar marigayiyar matar sa ita kuma haka Allah ya kaddarar ta mata rayuwa daga wannan sai wannan amman ba abinda zata ce sai alhamdulillah. Kuka take wanda bata san tanayi ba dan a yau take kukan rashin sanin wacece ita so take ta tuno wacece ita amman ta kasa sam.

Anty Nusy ce ta kamata suka fita a dakin suka koma bangaren Ummi inda su Jawahir, Najwa, Basma da Aisha kawar Najwa da take cewa zata dawo, sai Hauwa'u wacce take kawa ga Najwa tace in bikin yazo a fada mata kuma ta gayyato tan.

Bedroom Anty Nusaiba ta shiga da itace
"Kinga dai muna da baki dan Allah kada ki tada hankalin ki kinji?"
Kai ta gyada, kawai Anty ta juya ta fita. Najwa da Basma ne suka shigo dakin, suka samu Maryam na ta kuka wanda ya daga musu hankali suka rasa kukan me take?

Duk yanda Najwa tayi da Maryam ta gaya mata abinda ya faru ganin yanda take kuka kamar ranta zai fita amman taki ta ce mata komai. Basma da Najwa hankalin su ya tashi ba kadan, Anty Asiya da Hanna ne suka shigo.

Anty Asiya tace
"Wai meye haka Maryam? what's happening, talk to us plsss"
Fadawa jikin Najwa tayi ta kara rushewa da wani kukan tana shessheka, Anty Hanna ta dinga kallonta tana fatan Allah yasa ba tunanin da take bane ya tabbata da sukaji ana cewa ba aure tsakanin Maryam da Muhammad.

Anty Hanna jikinta yayi sanyi ta zauna gefen gadon ta ma rasa abinda zata ce tayi tagumi tausayin Maryam ya cikata, Hawaye Basma tafara yi tana dago Maryam tace
"Don Allah me ya faru Maryam ki gaya mana, wani abu ya sami Muhammad din ne? Ki mana magana don Allah" Mikewa Basma tayi ta fita dakin a sanyaye hawaye na sakko mata.


Mami, Anty Nusaiba da Ummi ne zaune a falon Mami. Mami tace
"Wallahi ni yanzu nafi samun kwanciyyar hankali."
Anty Nusaiba tace
"Nima haka amman halin da yaran zasu shiga shine damuwar mu, kina ganin Maryam ba cikakkiyar lafiya ba ga Aliyu yadda yake."

"Haka ne komai mai sauki ne nasan Maryam zata amshi Aliyu ko da baya son ta, shi kuwa wannan nasan ko tausayin da yake mata ba zai sa ya kuntata mata ba zai amshe ta a sannu su dai daita. Fatana dai Allah yasa alheri."
"Haka ne yanzu ya Maryam din take?"

"Na tura mata su Asiya nasan zasu lallashe ta."
"Amman iyayen Muhammad basu kyauta ba."



*
"Fada min me ya faru Maryam"
Dafata Anty Asiya tai ta dago murya na rawa tace
"Anty wai.. Ba da Muhammad aka daura auren ba da Yaa Al.. Ali..yu aka daura."

Maryam ta karasa fada tana fashewa da kuka, ido Anty Hanna da Asiya suka zaro cike da mamaki, Anty Asiya yace
"To menene na kukan? Kiyi hakuri haka Allah ya kaddara cewa Muhammad ba mijin ki bane, kuma ya baki Yaya shin menene aibun Yaya, namiji ne na nunawa sa'a mai hankali nutsuwa ilimi ga kyau to me zaki nema wallahi na tabbata Yaa Aliyu yafi Muhammad so dubu dan haka kiyi hakuri kinji."

"In yafi Muhammad amman Muhammad yafi shi so na."
"Wannan ba matsala bace Maryam kema zaki saka Aliyu ya soki, amman dole kiyi hakuri dan rayuwa da miskili akwai wahala amman daga baya zakiji dadi."

Haka suka dinga lalallashin Maryam har ta daina kuka sai dai yadda kanta da kirjin ta ke ciwo kamar zai fashe yasa ta kwanta kawai. Ganin tana bukatar hutu suka mike suka fita.

A falo suka samu su Najwa suna hira da kawayen su, Najwa na ganin sun fito ta mike ta karaso tana fadin
"What happened Aunty?"
"Hmmm auren ne fa aka daura da Yaya ba da Muhammad ba."

Ido ta zaro tace
"Are sure?"
Kai ta gyada tace
"Sure."

"To meya faru?"
"Nima ban sani ba bari muje ta kwanta ne shiyasa."

Komawa ciki tayi ta zauna wanda a lokacin taga Jawahir ta mike rike da waya ta nufi stair, Basma tace
"Lafiya kuwa Najwa?"
"Hmmm auren ne fa aka daura da Aliyu ba da Muhammad ba."

Hauwa tace
"Ke kice Allah."
"Wallahi."
Buda Hauwa tayi tace
"Kai ba shi kuke fada yana son ta ba."

"Uhmm Yaya ba'a iya masa fa, shine amman."
"Ke zasu dai daita, bama da take ita macece tinda shi da alamun ehhh...."

Aisha dai batai magana ba sai cewa tai
"Allah sanya alheri."
Suka amsa da amin.

Daki Najwa ta shiga ta samu Maryam a kwance ta zauna tace
"Antyn mu."

Wani kallo ta aika mata, sannan ta juya mata baya, Najwa tace
"Please dear ki daina wannan damuwar ni naji dadi banji dadi ba rashin jin dadi saboda..."

"Dan Allah Najwa ki kyale ni bana so wannan maganar."
Ta fada tana kifa kanta akan filo tana mai fashewa da wani kukan, lallashin ta Najwa tayi ta mike ta fita. A haka aka cigaba da yini wanda amarya tana daki, taki ta canja shiga bare ta fito da Ummi ma tazo dan tasa ta shirya ta same ta kwance zazzabi ya rufe ta dole yasa ta hakura ta bar ta a daki, amman Mami tace ta daure ko dan jama'ar da aka tara, mai make up Mami ta shigo da ita ta saka tai mata light make up ta shirya cikin wani coffee less wanda akaiwa ado da brown tai kyau sosai kamar ka sace ta ka gudu duk da tana jin zazzabi haka ta fito ta saka flat brown half cover mayafin aka ta daura wanda ya dan rufe fuskar ta.

Najwa da Basma suka kamata suka fito har harabar gidan dake cike da mutane inda aka tanada dan zaman amarya aka kai ta, suka zauna aka fara shagali amarya na zaune half face nata rufe da mayafi aka dinga shagalin bikin, wanda ko liki za ai mata har inda take ake mata liki. Har doshin magariba sannan aka bar kidan, Najwa ta kama Maryam da har jikin ta rawa yake saboda zazzabi da faduwar gaban da take, sama suka nufa wanda ta shiga daki ta hada mata ruwan dumi dan tayo alwala ta fito.

Falo ta karaso inda Aisha ke zaune tace
"Maman biyu sannu."
Aisha tai murmushi tace
"Kema kin kusa zuwa hakan."

Tai dariya tace
"Uhmm taso kiyi alwala ko?"
Da kyar ta dafa kujera ta mike suka shigo dakin wanda yai dai dai da fitowar Maryam, Najwa tace
"Yauwah Aisha ga Amarya dai ranar da suka zo kawo kati bakya nan yau ma baku hadu ba."

Dagowa Aisha tayi tana kallon Maryam da kanta ke kasa, wata uwar bugawa zuciyar ta tayi ta kurawa Maryam da ta dago tana daura dan kwalli ido
"Mar....yam....."
Aisha ta fada tana nuna ta, Maryam ta dago a razane tana kallon wacce ta kira ta, kallon ta take ba ko kiftawa na seconni, wanda a hankali Maryam ta sulale ta fadi kasa sumammiyya.

Da sauri Aisha da Najwa suka karasa wajen ta suna kwada mata kira, Najwa fadi take
"Maryam Maryam dan Allah tashi."

Aisha kuwa rumgume Maryam tayi tana fadin
"Alhamdulillah, Masha Allah yau Allah ya nuna min ke Maryam bayan shekaru masu yawa da rabuwar mu Maryam dan Allah ki tashi kizo muje su Ammi su ganki ko sa samu nutsuwa, Maryam Maryam."
Ta fada tana girgiza ta, Basma ce ta shigo taga halin da suke cike wannan yasa ta nufi firij ta dauko ruwa mai sanyi shafa mata tai amman ko gezau wannan yasa ta tuttule mata shi amma sam bata farfado ba. Fita tai a guje dan Najwa da Maryam sun rasa hankalin su a kasa ta hadu da Ummi ta nuno mata sama tana fadin
"Ummi Mar..ryya...am"

"Me ya faru da Maryam din?"
Ummi ta fada tana yin sama a guje, itama ruwan ta shafa mata amman bata farfado ba wannan yasa ita da Najwa suka kamo ta dan tafiya asibiti suna matatakala Aliyu ya shigo dakin dawowar sa daga masallaci kenan, da sauri ya karasa yana fadin
"Meya faru da ita?"




*Allah mana rahma yasa muyi kyakyawan karshe amin.*



*Antty*
[12/2, 11:07] Maryam S IndabawaπŸ₯°: ο»Ώο»ΏπŸ’—πŸ’— *MATAR HAIDAR* πŸ’—πŸ’—
Page 69

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




Ya amshe ta yai dakin sa da ita akan gado ya kwantar da ita yana fadin
"Meya faru?"
Kuka kawai Najwa da Aisha suke sun kasai masa bayani, duk kokarin sa na ya samu nunfashin ta ya dawo ya kasa wannan yasa ya kira Farouk ya fito da mota, shi kuma ya fita da ita a hannun sa, asibiti suka nufa Ummi da su Najwa uka mara musu baya, office din sa ya shiga da ita ya kwantar akan gadon marar lafiya, tin kan ya karaso yaga kira likita da nurses dan haka a bakin office din ya same su, yana ajiye ta suka rufa akan ta suna kokarin taimaka mata sai da numfashin ta ya dawo sannan sukai mata allurai, take ta fara bacci.

Aliyu dake tsaye a gefe yana kallon yadda suka taimaka mata take numfashi har tai bacci tana maganganu kasa kasa wanda ba ajin me take fada ya kalli Dr Yasmeen yace
"Me kika gano matsalar ta?"
"BP ta ya hau Dr and zuciyar ta tana kara rauni in tana cigaba da saka damuwa zata iya rasa rayuwar ta dan jijiyoyin sunyi rauni sosai kuma saka damuwar ya haifar mata, bama wannan ba a gaskiya yarinyar nan tai kankanta da wadan nan matsalolin ga hawan jini, ga ciwon zuciya, Dr tana bukatar kulawa da lallashi please a bata kulawar da ta dace."

Yana jingine da bango hannun sa harde a kirjin sa yake sauraron ta, har ta gama yai mata godiya ta juya ta fita ido ya lumshe a hankali ya sauke akan Maryam dake bacci, abinda ya fara guje mata kenan heart broke domin yasan ba ko wanne ahali ne zasu amshe ta ba yasan da haka amman a time din ta kasa fahimta su Ummi ma haka, in ta shine Maryam ba zata taba soyayya da wani a waje da zai cutar da ita ba su suka fi sanin matsalar ta dan haka su zasu iya zama da ita da kula da ita. Gashi nan yanzu tana neman halaka kan ta kenan tana son Muhammad har haka ta kasa hakura dashi yau in ya mutu wa gari ya waya, su dan shi gashi can an daura masa aure nan da wani lokaci zai manta da ita su kuwa da Haidar har abada ba zasu manta da ita ba.

Ido ya kara lumshewa yana mai fadin
"In har aure nane bakya so Maryam zan sauwake miki ba zan taba takura miki zama da wanda bakya so ba har hakan ya kara jefa rayuwar ki cikin hatsari."

Fita yai dakin Ummi ta karaso tana fadin
"Ya dai Aliyu?"
Dakin ya nuna musu yace
"Bacci take me ta gani yasata a wannan halin?"

Najwa ta saki kuka tace
"Ni na rasa menene dan mune dai a dakin daga Aisha ta kira sunan ta ta dago shikenan ta kura mata ido ta zube a wajen."

"Ina Aishan?"
Aliyu ya fada yana kallon ta waige waige ta fara sai ga Aisha nan ta taho daga wata hanya bayan ta wani namiji na biye da ita da kallo suka bisu har suka karaso, namijin shi yai karfin halin mikawa Aliyu hannu suka gaisa, Aisha tace
"Nan aka shiga da ita."

Da mamaki Ummi da Aliyu ke kallon ta dan so suke suji wa aka shiga da ita. Alkasim ya dago ya kalli Aliyu a karo na biyu yace
"Sunana Alkasim Jabeer ni dan garin kano ne aiki ya kawo ni garin Abuja ga mai daki na sunan ta Aisha, mu makwabtan Najwa ne wanda bamu jima da dawowa daga Canada ba muka tadda anyi auren ta, matata tazo bikin yar uwar Najwa inda yanzu ta kirani take shaidamin taga Maryam dan Allah da gaske Maryam ce a dakin nan dan ina mamakin ta ina ta ganta ban sani ba ko gezo ta farai mata dan kwanaki tazo tana fada min tana mafarkin Maryam tana fada mata tana kusa da ita dan Allah da gaske Maryam ce a dakin nan?"

Ummi da Haidar kallon sa suka tsaya sama da shekara biyar basu taba ganin wanda yace yasan Maryam ba sai a yau kenan da gaske wadan nan sun san ta ko kuwa? Aliyu ne yai karfin halin fadin
"Tabbas sunan ta Maryam amman bamu sani ba ko wacce kuke nema ce, amman kafin nan a ina kuka san ta ko ince menene alakar ku?"

Ajiyar zuciya Alkasim ya sauke yace
"Kanwata ce uwa daya uba daya."
Kallon sa Aliyu da Ummi sukai sosai, sai kuwa suga kamar da suke da Maryam, dan haka Aliyu yace
"Muje ka ganta dan bata cikin hankalin ta an mara allurar bacci zata iya daukar awa goma ko sama da haka tana bacci dan ana son ta samu nustuwa."

Suka shiga dakin har da Ummi, yana shiga dakin ya karasa wajen gadon da sauri yana ganin Maryam da gaske ya kalli alkibla ya tada sallar yayi godiya ga Allah sannan ya dago ya rasa me zai yi sai ya kama Aliyu ya rumgume tsam a jikin sa yana fadin
"Alhamdulillah!"

Ummi da Aliyu dai kallon sa kawai suke, Alkasim da ya kasa daina murna yace
"Me yake damun ta? For how long take tare da ku?"

"Likita yace taga wani abu da ya sa ta shiga shock ta zurfafa a tunani wanda ake tunanin ko ita matar taka ta gani take son ta tuna a ina ta san ta."
"Alhandulillah Allah ya bata lafiya."

"Amin."
Ummi ta fada yace
"But please for how long is she with you?"

"Ummi tace
"Six years."
Kai ya jinjina yace
"Tin batanta kenan da karamin ciki?"

Kai Ummi ta gyada tace
"Haka ne."
"I am sorry for the questioning but please ina babyn?"

Ummi ta girgiza kai tace
"Ba komai, Haidar yana gida he is fine ya kusa six years dan he is five and half."
Kai ya jinjina yace
"Bari na waya da gida na sanar musu anga Maryam."

Ya fita a dakin ya fara kiran layin Abbi, yana zaune a falo suna magana da Ammi wanda akan Maryam ne dan ba a kwana biyu a gidan ba ai maganar Maryam ba batan Maryam sam bai sa sun manta ta ba kullum basu sare ba kullum cigiya suke da addu'a. Wayar ya dauka yace
"Assalamu Alaikum Alkasim."

"Abbi Albishirin ku. Ina Ammi sa a speaker."
Abbi yasa a speaker yace
"Ina jin ka Alkasim Aisha ta sauka ne?"

"A'ah Abbi yau dai Allah ya amsa addu'ar mu munga Maryam."
Dif kake jin su Abbi, dan sun shiga mamaki da gaske anga Maryam.

Ammi ce ta amshi wayar tana fadin
"Hello Alkasim me kace?"
Cikin murna da farin ciki yace
"Tabbas Ammi yau naga Maryam"

"Alhamdulillah Alla kulli halin, Akasim tana ina? Ya take? Ina cikin? Bani ita."
"Ammi ki kwantar da hankalin ki yanzu muka rabu amman zuwa da safe zan kai mata sai kuyi magana"

"Ba zan iyaba Alkasim hadani da 'ya dan Allah."
Abbi ne ya amshi wayar ya fita ya maida ta normal yace
"Alkasim fada min me yake faruwa?"

"Abbi, Maryam tana asibiti bata cikin hankalin ta saboda ganin Aisha da tai ta suma to bata farka ba amman tabbas naga Maryam yanzu ma muna asibitin."
"To shikenan zan sa ai mana booking flight insha Allahu gobe da safe zamu iso ka kula da yar uwar ka."

"Insha Allahu."
Ya kashe wayar ya koma wajen dakin Maryam inda ya samu su Abba da Abbi sun zo suka gaisa Ummi tai musu bayani, suka kalle shi sukaga tabbas suna kama da Maryam.

Karfe goma Abba yace kowa yazo a tafi gida a bar Maryam, Aliyu yaso ya zauna amman Ummi ta kada shi, haka Aisha ma dan haka duk suka tafi cike da fargaba.


*
Washe gari kan goma asibiti ya cika da yan uwa dan su Anty Asiya, Hanna, Bilkisu, Aunty Nusaiba, Najwa da Basma ga Farouk duk sun zo, duk sammakon su Yaa Alkasim da Aisha sai suka tadda su sunyi mamakin wannan alamarin da karamcin wadan an mutanen sosai. Amman har lokacin bata tashi ba Aliyu hankalin sa ya tashi ya kira likitoci suka kara dubata da kansa ma ya duba komai lafiya dan baccin ma lafiya zai kara mata dan in ta samu wadatacan bacci zai sa damuwar ta ta ragu sosai da sosai. Karfe sha biyu jirgin su Ammi ya sauka da tawagar Yayen Maryam su Yaa Muhammad, Yaa Abdullah, Yaya Fadima Har da Mami mahaifiyar Haidar.

Wanda daga nan asibiti suka taho kai tsaye, wanda wajen da suke ya cika ba masaka tsinke dan har daki guda aka basu dan sun cika kofar dakin da Maryam take. Bayan sun shiga sun zauna Ummi tace
"Sannun ku da zuwa."
Suka gaisa cikin mutunta juna. Ummi ta nuna Ammi tace
"Kece mahaifiyar Maryam ko?"

Kai ta gyada, Ummi tai murmushi tace
"Ga kama nan."
Ta nuna Fadima tace
"Wannan yayar ta ce kenan?"
Kai ta gyada.

Ummi tace
"Yanzu Aliyun zai zo sun shiga dakin da su Abba ne shiyasa..."
Bata rufe baki ba Abba da Abbi suka shigo dakin bayan su Yaa Aliyu sai Yaa Abubajar dake biye dasu a baya, wanda yana shigowa Mami ta mike tana kallon Abubakar shima kallon ta yake cike da kaduwa tace
"Sadik...."

Ya matso yana nunata bakin sa yai nauyin furta komai, sai kuma a hankali ya sulale ya fadi kasa a sume ruwa aka yayyafa masa ya farfado yana waige waige tare fadin
"Ina Mami na dan Allah ku kira min ita."

Nami ta dafa sa tace
"Sadik gani nan nice."
Da sauri ya shige jikin ta ya rumgume ta tsam, Ummi, Mami da Abba da Abbi mamaki suke to wacece wannan kenan Maryam tana da alaka da Abubakar tinda ga gashi a yan uwan Maryam ne Abubakar yaga wannan matar yake kiran ta Mami wanda basa dai kama amman ta jini zaka gano akwai alaka.

Abbin Aliyu ne yace
"To Alhamdulillah, wadan nan ne iyayen Maryam din?"
Suka gaisa sosai sannan Abba da Abbi da Abbin Yaa Aliyu suka mike suka nufi dakin

Please Login or Register in order to submit comment