Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*LAULAM* ( _Kishiyata_ )


Na



*{SADEEY}*



*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

```MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊAN TARWA GAMIDA WA'AZANTARWA HUNMM WANI ABU SAI ROYAL STAR'S WRITE'S ✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) / 💪💪💪💪
UP-UP-UP BEST WRITTE'S EVER💖 ```
*ALƘALAMINMU ƳANCIN*






*GODIYA*
~Dukkan yabo da godiya su kara tabbata ga Allah ubangijin halittu, mai kowa mai komai, daya vani ikon rubuta wannan littafin, salatin da aminci su kara tabbata ga Annabi Muhammadu Annabin rahama SAW.~





*TSOKACI*
_Wannan labarin k'ageggen labarine, banyishi don wani ko wata ba, idan har kika ga yazo daidai da labarin rayuwarki, to kuskure ne._



*GARGAD'I*
_Ban yarda wani ko wata ya juya min littafina ba tare da izini ba, ko ya d'auki wani bangare daga ciki ba, don hak a kiyaye._



*SADAUKARWA*
```Na sadaukar dawannan littafin, ga mahaifiyata abun alfaharina, ```HAJIYA AYSHATU UMAR MADAKI``` Allah ya jinkanki ya gafarta miki, yasa kin huta, ubangiji yasa mutuwa hutuce a gareki.mukuma ubangiji ya k'ara mana hakurin rashinki.```




Page....1&2



––––– Nafara nisa cikin gyangyad’in dana fara, wanda haryakai ga mafarkan bazata sunfara ziyartar k’wak’alwata, batare da zato ko tsammani ba naji sauk'ar ruwa mai sanyin gaske yana ratsa sassan jikinta.
Sanyinne ya ratsa ilahirin jikinta wanda yai sanadiyar farkawata cike da fargaba, tsoro, da razani duka lokaci guda suka dirar mini, ba komai ya haddasamin hakan ba sedan sanin cewa INNA ce mai min wannan aika-aikar.

Kuka nafashe dashi wanda yai sanadiyar k’aruwar ɓacin ran Inna haryakai ga tad’aka mini duka tare da cemata...

”Munafukar Yarinya!  yanzu tadakin da nayi donki tafi d’ibamin ruwa ashe baccin naki na asara kika cigaba anan?, lallai kin isa kuma jikinki seya gayamiki, inhar baki tashi a gurinnan ba,”

Inna ta fad’i haka tare dasa k’afa tabuge ni sannan tawuce tana bambami.


Ina kuka tare da rawar d’ari haka nanufi inda tulun d’iban ruwana yake na d’auka sannan na nufi rafi, don dib'o mata, to wallahi muddin bai diboba, to wallahi na kahira sai ya fini jin dadi.....

Ahanya ban had’u da kowa ba saboda lokacin yawancin al’ummah suna gida suna bacci wasuma suna kaiwa ubangijin halittu kukansu kasancewar gari baigama wayeba.


Ina tafiya ina shan wahala haka harna isa rafin, kasancewar muna da tazara sosai da rafin amma hakan baisa Inna ta jin tausayina ba, watannin baya da suka wuce wani mai kud’i yashigo garinnamu tare dasawa akajawo musu ruwa kusa damu, amma saboda son zuciya irinna Inna tace batason ruwan dake fitowa daga k’arfe
na rafi takeso.


Haka  na isah  rafi  na debo ruwa.
 
Wanda ya ɗaukeni lokaci mai tsawon gaske. A  daidan wannan lokacinne
Kuma innah ta fito tana gyara ɗaurin  Zaninta tare da yin dogon hammah.

kallon ILHAAM tayi tare da jan dogon  tsaki "tace   me kike kallona da shegun idanu kaman na mayu  nikam karki cinyeni Mayyah  kawai, mai siffan aljanu,

"Shuru nayi tare da sadda  kaina ƙasa domin ina mugun tsoron innah.

Inna buta ta ɗauka  tayi hanyar band'aki.

tana fitowa daga band'aki tayi hanyar Badauru (madafi) domin yin dumame...



Kallona tayi kana tace " kije daki ki tayar min da yar lele, sauran ki mata mugunta, wallahi sai na sab'autaki,


Da to na samsa kana na kama haryar shiga ɗakinmu, inda muke kwana tare, ita a gado ni ka akan taburma,


Kallon yarinyar dake bacci nakeyi wacce a girme na girmeta, kafin nasa hannu a gefen kumtunta na fara tada da daga bacci,


Ido ta buɗe tana ganin nice tasa kuka ta ƙarfin gaske, wanda yasa INNA faɗowa ɗakin kaman an jehota,


Cikin kidima tace " `Yar Lele mene? Gaya min meke faruwa?


Cikin maganan ta na taɓararrun yara ta fara cewa "ba ILHAAM bace ta dinka kwad'amin mari, ta k'arasa maganar tana saka kukan karya,


Tass! INNA ta d'auke `yar k'aramar fusktata da mari, wanda yayi sanadiyya ganin duhu na wani lokaci,


Kana ta fara cewa " wato dai ni ban isa na saki kiyi abu, kuma kiyishi ba ko? tayar da itan da nace kiyi shiya baki daman marinta, to wallahi irin haka ya kuma sake faruwa kiga yadda zamu kwashe adashen tsiya dake, shegiya munafuka mai fuskar salihan bayi, wallahi ILHAAM idan kikayi wasa ni zanyi ajalinki! wuce ki ban waje, kuma yau baki da abincin safe a gidannan,




Kuka nakeyi tamkar raina zai fita, tunda naji sauƙin mari akan kumatuna, dama nasan hakanne zai kasance dani, kullum haka Zainabu take min, bandaketa ba tace na daketa, INNA kuma sai ta yarda kuma ta rama mata.


Hannun Zainabu taja suka fita waje, kafin tace min "aikin san ayyukanki ko? to dan Allah karki zo kiyi kici gaba da tsayuwa kina min kukan munafurci,



Fita sukayi hakan yasa nabi bayansu, ruwa tasa a buta ta miƙawa Zainabu a yayin da ni kuma na d'auki tsintsiya don yin shara,


*******
Bayan  innah ta gamane
Ta kalli gefen da nake, tare da jan dogon tsaki mtswww kana "tace wato ke bakisan ya kamata ba ko? sai na gaya miki kullum?

Shuru nayi  tare da tashi saga inda nake zaune na iso gurin da innan take,

Sunkuyawa tayi da niyyar ta daukan akushin da aka saka tuwon Bappah,. ba zato ba tsammani naji saukan  dundu a bayana wanda najishi har cikin ranta, kuka tasa tare da tsugunawa kasa,

Kafah innah ta sa sake  shuretah, wanda yayi sanadiyyar  buguwan kanta ajikin gini, ihu tasa  wanda ya k'ara hasalar da Innah, cikin haushi da kuma rashin controlling anger ta wawuri itacen murhu wanda yake da wuta ta jefini dashi.....





Idan naga ruwan comments sai naci gaba.




Ayi sharing fisabillah👏👏




09129216255
Sadeey ce

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/H0U1Ksenq6qD6oJn9H2Iyc


*LAULAM*
( _Kishiyata_)




*Alk'alamin SADEEY ce.✍️*






*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

```MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA HUMMM WANI ABU SAI ROYAL STAR WRITER'S ✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) 💪💪💪💪
UP-UP-UP```

_🍂"ALƘALAMINMU🖋️ ƳANCINMU"🍂_



Page....3&4


–––––––Jifana tayi da itace wanda cikin tsautsayi ya sauka akan ƙafata, cikin azaba na kurma ihuu, wanda ya k'ara hatsala inna cikin tsawa tace
"dallah rufemin bakin tun kafin na ƙona wannan jememmiyar fuskar mai kama da na tsohuwar jimage, wuce ki tafi dallah munafuka kawai yarinya k'arama sai shegen iyayi da gulma, munafuka annamimiya, wuce ko na sa'bautaki, ai wallahi idan kikayi wasa sai nayi ajalinki".



tashi nayi kawai ta nufi inda naga an ajiye akushin tuwon Bappah, da nufin na d'auka don kai masa, hakan ma Inna bata barni ba sai ta bata kyakyawan rangwashi, wanda sanadiyyar zubowar hawayena akan kyakkyawar fuskata.

d'auka tayi ta nufi hanyar waje,

tafiya nake cikin sand'a da kuma nutsuwa irinna nutsatstsun Yara.


Tafiya mai nisa ce ta kaini bakin wani Babban garke, mai cike da arzik'in dabbobi, duk dama garken jinsin dabbobi biyu kad'ai ya hada shanu da kuma tumaki, sai hakan bai hanashi cika ba.



Mutane biyu ne a cikin garken, wani farin dattijo mai cikar kamala, Wanda yake tsananin kama dani, yana tsugeni ƙarƙashin wata farar tsohuwar Saniya, yana tatsa cikin k'warewa, sai kuma wani d'an saurayi, dake d'an nesa damu kad'an.


Cikin sanyin muryan da Allah ya azurni dani, na gaishesa, duk da nasan ba amsawa zayyi ba. Don tunda nayi wayo ban tai taɓa yi min magana ba, baya shiga harkana, baya kulani,


Gefe na samu na rakuɓe, tamkar wata MARAINIYA ko kuma wata Mara galihu,



Bai d'au lokaci mai tsayi ba, ya kammala tatsan, sannan ya tura k'waryan gefe, kafin ya fara kunce dabbobin don tafiya kiwo,ganin haka yasani yin wajen k'waryan domin nasan koda zan kwana a wajen bazai taɓa tanka min ba.

cikin sanyin murya nace Bappah "Useeni rondam (dan Allah kad'aura min) shuru yayi tamkar baiji me tace ba, ko kuma wanda baya gurin.



sai daya gama abinda zaiyi kafin yazo ya d'aura mata, ba tare da ya kalli ko fuskarta ba, "Miyetti " (nagode) itace kalman data fito daga bakina.

Daga haka ta juyo don tafiya gida, ta samu ta isar da Nonon cikin gari, don wallahi idan nayi letti mai rabani da Inna sai na sama,


hanyar gida na kama ina tafiya cikin sanyi kasancewar k'waryan babbace sannan tana rawa-rawa, yasani tafiya a hankali,

Ina cikin tafiyanne naji ana kirana.
Sanin cewa bazan iya juyawa ba ya sani tsayawa a gurin tamkar an shukani, domin nasan ko wa cece mai kirana,

ba kowa bace fa ce k'awata, kuma Mak'ociyarmu wato
Malle Yar gidan Malam Liman abokin bappana,

tsayawa nayi mukad'an tab'a hira, acikin hiranne Malle kece mini ko yau zamu fita wasa kofar mai gari?



Cikin sanyin daya zama d'aya daga cikin d'abi'una nace " a'a

Cikin b'ata rai Malle tace meyasa?

"Nikam gaskiya bazan jeba, ranan ma da naje Inna tamin duka, kuma ta hanani abinci na wuni banci komai ba, kin tuna ranar sai da na ɓuya naje gidanku? ta k'arasa maganar cikin sigar tambaya .



Kai Malle ta gya d'a alamun ta tuna,
sannu tace "toh sai mun had'u ko a rafi ne kinjiko?.


Sallama mukayi
kana muka rabu kowa yayi hanyarsa.


Ina cikin tafiya kawai naci mugun tuntuɓe, kaman an d'agani sama haka naji,
Timm na faɗo ƙasa, ƙwarya tayi gefe, gammo gefe sannan ni gefe.
Acikin mutane masu wucewane wasu suka taru a kaina har aka tada ni,

kuka nake mai tab'a Zuciya, kuka nake na fitan hankali, irin kukan mai tsoron abunda zaije ya dawo, nasan ko wace irin mugunta na Inna duk da a shekara banfi 10 ba, amma babu abunda bansaniba, na daga komai na gidanmu.

Ina cikin wannan tunanin karaf idanuna suka sauka akan ƙwaryan nono wanda sanadiyyar fad'uwan da nayi ya rabe gida kusan biyar...






Wannan kenan



******
Kwance yake akan tank'amemen gadonsa k'iran Italy, Idanunsa lumshe suke tamkar mai bacci sai dai kuma nazartaccen kallo na minti ɗaya mai kallensa zai gane tabbas ba bacci yake ba.



K'aran murla handle ɗin da yaji anyi ne yashi sauke ajiyan zuciya, duk da yasan babu mai shiga masa d'aki ba knocking, ko sallama, sai mutum d'aya,



wato Meemy little sis d'inshi,(ƙaramar ƙanwarsa)
sai dai hakan baisa ya bud'e idonshi ba,
da gudu ta shigo tare da fad'awa jikin shi, tana haki irinna wanda ya gudu,



cikin sauri tace " ya IMRAAN Mamy tace na kiraka, wai kazo, daga fad'ar haka ta tashi da niyyar fita a guje hannunta ya rik'e, ciki sanyin murya yace "Meemy wai nikam ban hanaki shiga min D'aki ba sallama ba knocking ba?

Zumɓuro baki tayi cikin surutu tace "sorry bross na manta ne but bazan sakeba, i promise, next time zanyi sallama,



Shuru yayi don dama yasan abunda zai fito daga bakinta kenan, don kullum idan ta shigo kuma ya mata gyaran haka, to abunda zata gaya masa kenan.



Ganin bai saketa bane yasata cewa cikin shagwaba tace "please let me go, zanyi failing game dina,
cikin ƙosawa da maganan yace mata " ina Mamyn take?
cikin sauri tace "tana side ɗin Abba,



daga haka ya sake mata hannu , ai kaman jira take ta falfala da gudu, a d'ari ta bar masa ɗakin.

Tashi yayi ya nufi wajen wardrobe ɗinshi, don saka kaya, kasan cewar singlet ne sai 3quater a jikinshi.



Ana na samu daman k'arewa ɗakin kallo ganin irin had'uwar da ɗakin yayi ba kad'an ba ne, furnitures d'in ɗakin brown an milk colour ne, haka ma cotton milk, sai k'aramin carpet d'in dake ɗakin shima Brown ne da d'an ratsin milk, sai a d'an gefe akwai study table,(teburin karatu). Ɗakin bayida tarkace, komai a kimtse yake, ba k'aramin had'uwa yayi ba.


Bud'ewa yayi ya d'auki jallabiya White colour kana ya saka, daga nan ya d'auki wayoyinsa dake kan Bed side drower, d'insa ya zura acikin Aljihun Jallabiyansa , kana yayi waje, don amsa kiran Mahaifinsa.

Corridor d'in da zai sa dashi da side ɗin Abba ya nufa, tafiya yakeyi a hankali, tamkar mace mai ciki,



A kallon tafiyarsa mai kallonsa zai dauka cewa shi d'in ya hada jini da sarauta, sai sai shi ba kowa bane jinin MODIBBO. sai daya yaje dab da bakin ƙofa kana ya tsaya,



cikakkiyar sallama yayi cikin muryansa mai d'adin sauraro.

Chan ciki yaji an amsa kana ya kutsa kansa cikin palourn.



Magana yake taji k'asa-k'asa, acikin palourn. Kallon inda wajen nayi nan na hango mata da miji a zaune akan kujeran 3str daga gani kasan hutu, da kuma kuɗi sun samu wajen zama.
Mijin zai kai kaman 57-59 years. Itakuma matar bazata wuce irin 45-47 da haihuwa ba Amma kuma yanayin hutu da kuma jindaɗi yasa baza kice takai waɗannan shekarun ba suna tsananin kama da IMRAAN sosai especially ita ma don har kaman ta baci.



Zama yayi a ƙarƙashin ƙafafunsu, kana yace



"Barka da rana Abba,


Fallonne ya d'auki shuru bakajin karan komai sai karan AC da kuma TV, kowa da abunda yake tunani acikin ranshi, musamman Mamy wacce tunanin rabuwa da d'anta, da Ubangiji ya mallaka mata guda biyu.



Chann Abba ya numfasa kana yace "Babana dama na sa a kira kane akan maganan nan tamu, meka yanke akai?

Shuru yayi kaman mai nazari,

Harga Allah baya son tafiyannan, ba kaunar rabuwa da gidansu, Yan
uwansa yake ba,

Ganin yayi shuru bai tanka ba ne yasa Mamy cewa " amma kanaji magana dai ko?

Cikin yanayinsa na rashin son magana yace " ba komai abba, komai ku kayi a kaina dai-dai ne,
Ku iyayena ne, nasan bazaku zab'a min abunda zai cutar dani ba".


Numfashi ya fara mayarwa da sauri, saboda seconds d'in ɗaya daya ɗauka yana magana.



Numfasawa abba yayi kana yace.....




**********
Ihuna ne ya k'aru, saboda tashin hankali, da fargaban dana shiga,


don wlh nasan yau mai kwatana a hannun Inna babu shi a duniya, domin wannan k'waryan dana fasa k'waryane da take mugun ji dashi, saboda na gadone,wanda mahaifiyarta ta bar mata.

Da k'yar na tashi ina kuka mai ban tausayi, da tab'a zuciya, hanyar gida na nufa, ina tafiya ina kuka, har ta isa gidan,



Inna dake zaune da tsinke a hannunta tana sakace haƙora,


kukana ne take ta jiyowa daga nesa, har na shigo cikin gidan,


Harara Innah ta gallamin kana tace


" to yau kuma me aka kwaso ƴar jaraba? jarababbiyar banza, ke kallum kuka,


toh Wallahi ahirr ɗinki nikam alkhairi zan gani, munafuka mai rokawa mutane wahala,
yo idan ba wahala ba yarinya sai shegen iyayi,da munafurci, munafuka kawai, idan ba jaraba ba, ke kullum baki da aikin daya wuce kuka,! kuka! to Wallahi sai dai ki kokawa kanki da Ubanki, badai ni Kulu ba, don wallahi alkhairi zan gani ba sharri ba ehe.
Dallah rufemin baki!" ta daka min tsawa
wanda yasa firgici ya dirar min,


Cikin hasala tace" baza kiyi magana ba kin zubamin ido kaman na tsohuwar mayya?

Cikin tsoro, da kukan daya ci k'arfina nace

"In.....inaa... inaaa cikin tafiya ce, sai nayi tuntuɓe shine na fad'i sai kwarrr..



"Kutturun ubancan karki cemin Nonon ya zube? sannan kuma kwaryana ya fashe? don na rantse da Allah idan na d'auki landi ya landani,



"Kinsan waceceni, kin kuma san bana ɗaukan asara,
shuru tayi, don a tarihin Kulu bata d'aukan asara,



Sai kuma taci gaba da cewa

" cikin biyu ki zabi d'aya, ko ki biyani, wallahi ko kuma na fanshe su a jikinki,
ta k'arasa maganar tana fincikoni zuwa gabanta.



Ganin nayi shuru ne, ya k'ara hasalata,


Hannu ta d'aga ta kwashe fuskata da wani shegen mari, wanda yasa sai da naga wasu jajayen taurari,



kafin na dawo daga magagin wannan marin Innah ta sake d'auke fuskata da wani, wanda yafi na d'azu, ihuun azaba da tashin hankali nasa,



Inna cikin rashin tausayi tasa hannu ta damƙo tulin gashin ƙeyata, Wanda baisan kalman da ake kira da gyara ba,


kana tayi wurgi da ni, wanda yasa kaina buguwa azaban da na jine yasa na buɗe bakina na kurma ihu mai shegen ƙarfi
wanda yasa matar Malam Liman shigowa cikin gidan da d'an gudu,



Cikin saurian tasa hannu da niyyar karɓana a hannun Inna...









09139216255
Sadeey ce.*LAULAM*
( _kishiyata_)



*Alk'alamin SADEEY ce.✍️*






*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

```MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA HUMMM WANI ABU SAI ROYAL STAR WRITER'S ✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) 💪💪💪💪
UP-UP-UP```

_🍂"ALƘALAMINMU🖋️ ƳANCINMU"🍂_



Page.....5&6



––––––––Tsawa ta dakawa Innayi matar Malam Liman, kuma abokin Bappah, sannan mahaifiyar Malle k'wata,


cikin tsawa da magana sama-sama tace "wallahi! Hansai ki kiyayeni,idan baki fita a gidannan ba kinsan ba karamin aikina bane na had'a dake ko?”
ta karsa maganar tana nunawa innayi yatsa,



Cikin muryan lallami tace "haba Kulu dan Allah meyasa kike haka ne?Rayuwa fa da sauki ake d'aukanta bada zafi....”
" an d'auka da zafin, nace an d'auka da zafi d'in ina ruwanki?” Inna ta katse Innayi,


Kana ta ci gaba da cewa
"dama Wallahi hansai na lura da take-takenki, da samin ido a lamuran Gidana,to na rantse da Allah ki fita idona na rufe, babu ruwanki da gidana,idan ba munafurshi ba mutum bai isa ya d'aki yarsa ba sai kinzo? toh Wallahi daga yau ki kara zuwa gidannan da sunan kinzo karb'an wannan shegiyar yarinyar nan”




Sai na had'a dake na muku shegen duka naga mai min magana aikin banza aikin wofi, aikin buhu da masilla kawai,



Wallahi duk Mutum mai munafurshi, da da ido wa Kulu, to zasu gane kurensu musamman masu irin halinki,




Innayi dai shuru tayi don Yanzu taga abun Innah sai addu'a, juyawa tayi ta gefena taga yadda nake kuka kaman raina zai fita, Amma innah ko a bakin zaninta.



Cikin sanyin jiki ta nufi hanyar waje tana share hawayen tausayina, don itakam ta rasa ta inda zata bullowa wannan al'amarin, yarinyar da batafi shekara goma ba, amma bala'i da masifa duk aun had'e mata.




Tana ganin innayi ta fita ta koma kaina fincikoni tayi kana ta k'ara kifa min mari! kuka na k'ara sawa mai karfi! wanda ya kara kular da innah,




hannu tasa ta Mangare bakina, ta tare da cewa "dalla rufewa mutane baki ko na k'arasa fasa wannan shegen jan leb'una, masu kama dana tsohuwar mayya,



shegiya kawai muguwa mai siffar ifiritai,



don mugunta da munafurci K'waryan gado na kika fasa? Kwaryan gado?



ai wallahi yau mai karb'anki a hannuna babu shi a duniyar nan,


ko da kuwa matacce zai dawo, shegiya kawai, wlh da kinsan darajan K'waryannan da kinfi rik'eshi da muhimmacin akan lusarin ubanki, bari na gaya miki idan baki saniba ki sani wannan K'waryan gado nane wannan uwata salame ta mutu tabarmin, ta karasa magana tana jijjiga kaina,


wanda tsabar maruka da kuma bugu ta kai har fuskata ta kumb'ura ga goshina da yayi k'aton k'ulu ga bakinta daya fashe sakamakon bugeshi da innah tayi wanda a nan take zazzzabi mai k'arfin gaske ya rufeni amma innah ko a jikinta,



Fincikana ta karayi cikin sauri tayi hanyar (Badauru) wato kitchen da ni, dakekken yajin borko ta dauko,



Ina ganin haka na k'ara sa kuka don nasan inda zancen ya dosa, ina ganin Innah ta d'auki wannan Yajin kuka na sake sakawa tare cewa innah (wad'u mu`yal useeni) Innah kiyi hakuri dan Allah.


Amma Innah bata saurara mata ba, yajin ta dauka, hankad'a ni nayi tangal-tangal na fad'i,



babu tausayi Innah ta ficike zanin jikinta cikin rashin tausayi innah saka hannu ta dumb'uli wannan yajin borkon ta sakamin acikin bom-bom.


Ihu nayi saboda radadi, da azabar da suka taru had'u, sukayi mini taron dangi a lokaci d'aya, sannan suka sani fita cikin hayyacina.





Dariyar mugun ta innah ta kece dashi cikin dariyar take cewa ay Wlh duk wada yaci tuwo dani miya yasha, na gaya miki dama duk wanda ya kuskura ya tab'ononi to wallahi ya tabo tsuliyar dodo, ko babba ya tab'ani, bazai share ba, ballentana ke karan kad'a miya don wannan K'waryan tafimin wassu mutanen dake cikin wannan duniyar, ta k'arasa maganan tana taka kafarta.

Nikam a zuwa yanzu bani da bakin magana, haka kuma bani da bakin kuka, don wahala tayi wahala, azaba tayi azaba ga radadin yaji gana zazzabi abun ya hadu ya min yawa, inbanda juya kai babu abunda nakeyi, kafarta innah ta kama ta fara ja kaman kayan wanki har waje,



"Salamu alaikum
taji a murya wani a waje,

dogon tsaki taja kana tace "jarababbu kawai, sake kafataa tayi ta nufin hanyar waje tana warware dankwalin kanta.

Please Login or Register in order to submit comment