Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register



Tana tafiya tana mita harta isa bakin K'ofar, shuru tayi, kana ta fara zazzare ido tamkar wacce tayi wa sarki k'arya saboda wad'anda idanunta suka gani.


********
Cewa abbah yayi "dama na yanke hukunci akan zaka tafi Cairo, nasan bazakso tafiya ba, saboda rabuwa da gida, amma kasani wannan tafiyar ba mai jimawa bace, tund kasan Masters ne,



Sai dai bansan ko zayyi maka ba, domin kaine mai zama ba baniba, Amma ya ka gani idan bai naka ba ka gayamin kaji? tunda kai ba yaro bane, you're 26yrs, ya K'arasa maganan yana kallonshi,




Kasa yayi da Kansan kana yace "ba komai abbah idan ya muku babu komai nima yayi min, kawai Addu'arku nake bukata.




Cikin jin dad'in maganan sa suka had'a abaki wajen cewa Allah ya maka "ALBARKA.!


"Ameen
yace a takaice,



Kana abbah ya kara da cewa "sannan kafin ka katafi dole zamuje k'auye domin kayiwa su Bappah sallama.




"Toh yace cikin sanyi kasancewar sa yaro wanda baya musu da abunda iyayensa suka zab'a masa, koda kuwa baya son wannan abun.


*WAYE IMRAAN*?


*ASALINSA*
Alhaji Abubakar Ahmad Sulaiman, shine asalin sunansa, sai dai mutanen garin suna kiransa da modibbo,



kasancewarsa babban Malamin garin, wanda babu kamarsa, domin a kofar Gidansa yake koyar da Yara har ma da manya,



wannan dalilinne yasa suke matuk'ar mutunta shi da Kuma ganin girmanshi.




Malam Modibbo nagartaccen dattijo ne mai son jama'a da kyawawan halaye, wanda kwata-kwata abunda duniya bai tsole masa ido ba.




Haka ma Matarsa Hajiya Rukayyah wacce suke kira da Addah, itama nagarttacciyar macece mai kyawawan halaye da kuma kyawawan d'abi'u da sanin ya kamata,




Uwa Uba ga son mutane da kuma faram-faram da jama'a, wad'annan halayen nata su suka jaa mata so a gurin mai gidanta, Malam Modibbo dama jama'ar garin baki d'aya.




Malam modibbo cikekken ba fulatanine gaba da baya wato usul kenan, haka ma matarsa Addah,



Garin MARU, dake AREWA maso gabacin Gombe, gari ne na asalin cikakkun fulani, masu fararen Shanu, wato JOTTAMA'EN.



Garine da Allah ya yayi masa tarin ni'imomi, asalin garin na fulani ne Amma saboda ni'imar garin yasa mutane ke k'aurowa daga garuruwarsu suna dawowa da zama a garin, wannan dalilin ne yasa garin tara ma banban tan mutune, masu mabanban tan yaru ka.

Hakan yasa suke masa lak'abi da MARU MARAI HOB'B'E (wato Maru mai mallakan baki)



K'auyen MARU
K'auyene da Allah Ubangiji ya azurtasu da tarin ni'imomi masu yawa,




Gari ne mai cike da sanyi, wanda bishiyoyi sukayi masa kowanya, haka kuma Allah ya azurtashi da ruwa mai sanyin gard'i, wanda yake b'ub'ula daga jikin wani k'aton Dutsin da yayiwa garin kowanya wanda suke kiransa da ```(WAANGO)```




haka kuma ta bangaren jin dadi, Allah yayi masa wani irin kekkywan ```DALLOL``` (Lambu), wanda yake d'auke da manya-manyan bishiyoyi irinsu Gwanda, Mangoro, lemu, Inabi, Tufa, da sauransu, wanda ya suke shiga suna cirowa suna anfani dasu, wajen aiwatar da abubuwan yau da kullum.




K'auyen Maru ba wani gari bane babba har can, don mutanen cikinsa a k'allah baza sufi d'ari biyu zuwa d'ari uku ba,


Haka kuma Mutanen garin Sana'a biyu zuwa uku garesu, Noma da Kiwo, sai kuma yan tsirarun cikin dake kasuwanci,
wad'anda ba faluni bane, haka kuma ba mahaifan garin bane.



Malam Modibbo na d'aya daga cikin mutanne masu fad'a aji acikin K'auyen MARU, don daga ARD'O MUSAJO sai Modibbo.




Malam modibbo ya kasance yanada k'ani guda daya wanda iyayensu suka rasu suka barshi tun yana yaro,



Allah ya d'ora masa son dan uwansa tun bai kai haka ba, har suka girma suka tashi sukayi aure a gida d'aya haka ma matan su suka tashi kansu had'e haka zalika `Yayansu, babu wariya a tsakanin su.



Malam Modibbo yana da []a[]a guda biyu duka maza, Ahmad sannan sai Usman.




Malam Liman k'aninsa kuma, yana da []a[]a, uku biyu maza mace d'aya,
Ibrahim shine d'ansa babba sai Adamu, sannan Fatima,






Haka rayuwarsu yake tafiya gwanin sha'awa, a yanzu Ahmad ya sauke alqur'ani mai girma hakan yasa mahaifinsu kai su makarantar boko, shida k'aninsa Ahmad duk da ma ba kowa bane yake kai yayansa makarantar a wannan lokacin kasance war sunada k'arancin wayewa, domin a cewarsu makarantar boko itake lalata tarbiyar Yara.




Bayan sun gama primary, ba b'ata lokaci aka saka su a secondary bayan sun kammala ne suka dawo gida, inda Ahmad ya nuna yanason ci gaba, a dayinda Usman kuma ya nuna bayaso.




Mahaifinsa yaso ya hana amma ganin d'an nasa yanaso sai kawai ya amince tare da binsa da addu'a, dashi aka kai Ahmad makarantar gaba da secondary inda aka nema masa a cikin gombe wato *gombe state university* mahaifinsa ya masa komai inda ya nema masa zaman hostel, nasiha ya mishi kana ya koma.



Haka Ahmad yaci gaba da karatu inda yake karanta Business administration, haka kuma yana maida hankali sosai akan karatunsa, sanna bayi da abokai berkete, abokinsa d'aya mai suna mus'ab, dan cikin garin gombe ne, Ahmad ya lura
Hankali, da kuma nutsuwar mus'ab yasa yake kula shi har suka k'ulla abota.


Haka rayuwa take ta tafiya cikin kwanciyar hankali tare da tarin canzawar yanayi mai d'auke da zafi da kuma sanyi, haka mai dad'i sannan da kuma mara dadi.....


After 5 year
Abubuwa da yawa sun faru, ciki har da aurensu Ibrahim Usman da Kuma Adamu, har ma da karuwar haihuwa Amma matar Usman bata haihu ba har Yanzu.
Sauran Fatima kasancewarta tsakanin ta da Adamu akwai tazaran shekaru, so ita har Yanzu batayi aure ba.




A bangaren Ahmad kuwa....






#Vote
#Team
#follow



09139216255
Sadee✍️*LAULAM*
( _Kishiyata_)



*Alk’alamin SADEEY ce.✍️*






*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

```MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA HUMMM WANI ABU SAI ROYAL STAR WRITER'S ✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) 💪💪💪💪
UP-UP-UP```

_🍂"ALƘALAMINMU🖋️ ƳANCINMU"🍂_


❣️❣️❣️❣️❣️❣️``` MASHA ALLAH OUMUL JUWAIREEYYA DA NERZLAAH,INA TAYAKI MURNAN FARA LITTAFIN KI, ALLAH YA BADA SA'A YASA KIN FARA SA'A, UBANGIJI YA K'ARA DAUKAKAKI, YA RAYA MIKI YARANKI, YA KUMA KADE MIKI FITINA AGIDAN AURENKI,UBANGIJI YACI GABA DA DAFAWA LAMURANKI, ALLAH YA KAWAR DA IDON MAKIYA AKANKI DA ZURIYARKI DA ZURIYATA, DA ZURIYAR DUKKAN MUSULMAI BAKI D'AYA.



HAR NA RASA BAKIN DA ZAN MIKI GODIYA AKAN ADDU'OIN DA KIKAMIN, THANK-YOU VERY MUCH,🥰

`YAR UWATA, ABOKIYATA, KUMA ABOKIYAR SHAWARATA.
BANDIROWA AM.
```
❣️❣️❣️❣️❣️❣️


Page....7&8

''''''''''Ahmad ya kammala Degree d'insa cikin tarin nasarori da manyan-manyan kyaututtuka,wad'anda suka saka modibbo cikin farinci mara misaltuwa, tabbas har yau bayyi nadaman sakashi a makarantar boko ba, dama shi yana ji a jikinsa makarantar boko ba kaman yadda yan k'auyen suka dauketa take ba,gashi yanzu kam ya daina kokon to ya gani a kan dansa gudan jinisa, don haka shi ganau ne ba jiyau ba.



Ahmad ya tarkato komatsensa ya dawo gida,tabbas yayi kewar gida, dama ance duk wanda yabar gida to tabbas gida ya barshi.

Bayan kwana biyu da dawowar Ahmad modibbo ya fara masa maganan AURE sakamakon damunshi da Addah takeyi akan ya fara girma bayyi aireba, gasu Adamu duk har matan su sun haihu, matar Usman ne har yanzu shuru.



Shuru Ahmad yayi domin shi bai tab'a tuna wannan ranar zata zo ba, shi dai ko a School bai da kula yan mata, duk da mata suna kawo Kansu a wajenshi da sunan suna sonshi, amma shi kwata-kwata basa gaban shi, domin daga matan har mazan baya kula tarkace, wassu kanzo wajen sa saboda ilimin shi, Amma shikam baya iya sakar musu fuska, mutum d'aya yake mu'amala dashi wato mus'ab, wannan dalilin yasa wassu ke masa kallon mai girman kai, mai wulakanta jama'a saboda yaga yana ilimi.



Daga shi har abokinsa Mus'ab basu damu ba kasan cewar sunsan ba haka halin su yake ba.



Maganan Modibbo ne ya dawo dashi daga tunanin da kwanyar kansa ya tafi yi.



Modibbo ne yace
" bakace komai ba akan maganan, ```wolwu ne``` (Kayi magana mana),


Kansa ya sunkuyar komai ba, kana ya tsuke bakinsa batare da yace komai ba.


Addah cikin kawaici irinna iyayen dake kunyar []a[]an farinsu tace


" ba Kai zaka sunkuyar ba, magana zakayi idan kana dashi to ka gaya mana, idan Kuma baka dashi sai a nema maka ko ananne, don ni kam nagaji da wannan zaman na rashin Aure.



Cikin kunyar iyayayen nasa yace " nidai gaskiya babu, sai dai ta wajenku,


Shuru modibbo yayi kana yace "tunda kace baka dashi, to ko lallai zamuyi maka zabi, wamda muke fatan ya zama alkhairi a gareka, amma bazance komai ba har sai na nemi zabin ALLAH nayi ISTIHARA, insha Allah zaka sani sani ta hanyar sanar da mahaifiyarka.

Tashi yayi kana yayi musu sai da safe, bayan sun sallameshi.


Yana tafe yana tunanin da waye Malam zai had'a shi, kafadunsa ya d'aga irin i don't care d'innan kana yace ko wacece ina maraba da ita.



Da daddare Malam ne zaune da addah suna hira cikin hiranne malam yake cewa " Rukayyah me kika gani za'ayi a akan al'amarin yaronnan?

Shuru addah tayi kana tace nikam malam INA da shawara,

Yace "fada naji

Addah" tace mezai hana a hada auren yaronnan (bata kiran sunan kasancewarsa d'an fari )
da Fatima,

Shuru Modibbo yayi kana wannan shawararki abar dubawace, nima nayi wannan tunanin, don har nayi ISTIHARA kuma insha Allah akwai alkhairi mai tarin yawa acikin wannan Auren, amma insha Allah zan sake yau da daddare.



Shuru addah tayi kana tace "to Allah ya tabbatar da alkhairy.


Acikin daren modibbo yayi istihara kuma da safe idan Allah ya kai rai yake son fad'awa Addah me ya yenke.




After 2 days:
Ahmad ne zaune da iyayensa da daddare bayan Modibbo ya gama karantar da magidantan da yake koyawa karatu da daddare bayan sallahn isha,
Modibbo ne ya dubeshi kana yace masa "nasan kai mai biyayyane kan duk abunda muka gaya maka koda bakaso, shuru modibbo yayi kaman mai nazari, kana yace "
kaman yadda mukayi maganan zamu nemeka akan duk abunda muka yanke akan wancan maganan, haka ne?


Ahmad yace eh hakane malam,
kana malama yace "na yanke hukuncin zan hadaka AURE da Fatima,


Shuru Ahmad yayi

Modibbo yace bakace komai ba
Ahmad yace" ba komai Malam Allah ya tabbatar da abun da yafi alkhairy,


Cikin farinciki
Addah da Modibbo suka had’a baki wajen cewa "Ameen".


Modibbo yayi magana da k’aninshi Malam Liman akan ko Fatima tana da wani tsayayye bayan malam Liman ya tambayeta tace " a'a daga nan suka yanke maganan AURE tsakanin Ahmad da Fatima, inda aka tsaida ranar nanan da wata biyu za'a daura musu AURE.


bayan Malam Liman ya samu Fatima da maganan abunda suka yanke akansu a matsayinsu na iyaye, Fatima batayi gardama ba kasancewar ta mai tarbiya duk da bata sonshi, amma kuma bazatace ta tsaneshi ba.




Ahmad ne kwance a d'akinsa yaji wayansa yana ringing kaman bazai d’auka ba sai kuma ya mika hannu ya lalubo wayar a kasan pillow, ganin mai kiranshi ne yasa shi picking Call daga cikin wayan yaji ana cewa


" haba Namiji Duniya, kana Duniya amma shuru, dariya Ahmad yayi kawai kasan cewar bamai irin wannan wasan bane shi, sai ya bari mus'ab ya gama tsokananshi, kana suka gaisa daga nan suka d'an tab'a hira a cikin hiranne Ahmad yake fad’a masa abunda yake faruwa game da auren sa, mus'ab yace masa yayi biyayyan kawai insha Allah ita alkhairy ce a gareshi saboda zab'in iyaye ne,




Sai da suka gama magana kana Mus'ab yace "dama na kiraka akan wata magana, jiya baba yace mu kawo credentials d'inmu zai sama mana aiki nida kai,



Tashi Ahmad yayi cikin cikin murmushin da zai nuna maka zallan farincinkin da yake ciki yace "da gaske abokina?

Mus'ab yace" wallahi"

Cikin sauri yace to nagode Insha Allah zanzo, bai jira komai ba yayi ending call d'in.


Tashi yayi yaje ya samu Addah ya gaya mata, tayi farinciki sosai kana tace masa zata gayawa malam idan ya shigo da Dare.


Bayan Addah ta gaya masa Malam yayi farinciki sosai kana ya d’ora da Addu'a.


Bayan kwana biyu Ahmad yaje gidansu Ahmad tarba mai kyau ya samu daga yan gidansu kasancewar dama shi ba bak'o bane a gidan, bayan dawowar babanshi da daddare ya karb'i takardunsu yace zai nemesu bayan kwana biyu Insha Allah.


Washe gari Ahmad ya juya gida bada son ran mus'ab ya tafi ba, inda ya samu Mahaifansa ya gaya musu sunyi farinci sosai inda suka yiwa baban mus'ab addu'a da fatan gamawa da duniya lafiya.



Bayan kwana ki baban Mus'ab ya samawa Ahmad aiki a *NATIONAL OPEN UNIVERSITY OF NIGERIA(NOUN)*
Inda suka bashi Gida da Mota, su Modibbo sunji dad'i sosai akan abunda Alhaji Ali yayi musu, Modibbo da Addah sunje har gidansu Mus'ab sun musu godiya sosai.



After 2 month:

A yau juma'a dubban jama'a suka shaida d'aurin Auren AHMAD ABUBAKAR MODIBBO tare da amaryarsa FATIMA BELLOW SULAIMAN, akan sadaki Naira dubu hamsin lak'adan ba ajalan ba. Daurin Auren daya tara dubban mutanen kauyuka da dama, kasancewar Malam Modibbo mutum ne mai jama'a sosai.


Washe gari aka kai amarya Fatima gidanta dake *New g.r.a* gombe, bayan an mata dogon nasiha mai ratsa jiki, yadda zata kula da igiyoyin Auren dake kanta, da kuma yadda zata zauna zama da miji,


gidan Fatima gidane mai d'an karen kyau komai na gidan yayi kyau sosai, gidane mai 3 bedrooms 1 parlour each Room yana da Toilet a ciki, sannan kitchen da Store ,infact gidan very simple and nice.👌👌


Zaman Ahmad da Fatima zama ne fahimtar juna. Fatima tana yiwa Ahmad biyayya daidan gwargodo iyawan iyawarta, duk abunda yace tayi tanayi kuma idan ya hanata tana bari.

A bangaren Ahmad baya musgunawa Fatima, yasan koda Aure bai had'asu ba shi yayantane sannan kuma yasan kaman yadda ba sonta yake ba itama ba sonshi take ba.


A takaice zaman Fatima da Ahmad zama ne na Masha Allah, duk da ba masoya bane amma babu Wanda zai iya ganewa, kuma kowa yana sauke hak’k’in d'an uwanshi dake rataye a wuyanshi.




SHONGO HOUSING ESTATE
Ba wanii bakin wani kererren gida na tsaya mai milk colour din gate, kallon na gama karewa gidan, kana nasa kaina ta k'aramin K'ofa na shiga.


Kallo na k'arewa compound d'in gidan,


Gidan babban ne Amma ba har can ba, gidan zagaye yake da shuke-shuke,

Kofan dana gani ne nabi, wanda nake kyautata zaton shine na ainihin cikin gIdan, Hannu nasa na murd'a handle d'in a hankali, tura kofan nayi a hankali na shiga sanyine mai hade da k'amshi suka bugeni, bansan sanda na lumshe ido ba na shiga cikin palour.


Tana zaune akan d'aya daga cikin kujerun palourn tana kallon zee world channel, glass cup ne a hannun ta tana shan juice, kallo na kare mata, Hmm idona na rufe na sake budewa Hmm masu karatu Fatima na gani ta zama Hajiya tayi kyau ta k'ara haske ta cika tayi mugun kyau, vowel ne a jikinta mai d'an karen kyawu da tsada, a yayin da wuyanta da hannayenta ke samne da gwala-gwalai.


Horn taji hakan ya tabbatar mata da cewa mijinta ya dawo.


flash back:
bari muji meya faru a five years back.





More comments more typing




#Follow
#Vote
# comments



Sadeey✍🏻*LAULAM*
(_Kishiyata_)







*Alk'alamin SADEEY ce.✍️*






*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

```MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA HUMMM WANI ABU SAI ROYAL STAR WRITER'S ✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) 💪💪💪💪
UP-UP-UP```

_🍂"ALƘALAMINMU🖋️ ƳANCINMU"🍂_




Page.....9&10

*Flash back*


______A shekaru biyar d'innan abubuwa da yawa sun faru ciki harda karo karatu wato masters da phd, da Ahmad yayi wanda ya k'ara masa girma a office d'insu, yanzu fa arziki ya zaunawa Ahmad, ba laifi domin har yayi gidan kansa, mai kyau, gidane mai side guda biyu,wato shi da k’aninsa Usman kenan,sai dai kuma bai dawo ba, cewarsa yana tare dasu Malam, haka kuma yana taimakawa iyayensa,



Yayin da Ahmad yayi renovating gidansu, ya tsantsara musu gini na ganin na fad'a, yayi musu family hause, wanda babu irin sa a fadin garin.

wannan kud'in da yan garin suka ga yayi yasa acikin family suka fara k'ananan maganganu akan rashin haihuwar ta, wanda yasa ran modibbo b'aci matuka kuma yayiwa tufkar hanci.


A bangaren zamansu
babu wanda ya tab'a jin kansu, ko musu bai tab'a had'a su ba ballen tana wani raini ko makaman cin haka.


A Duk tsawon wadannan shekarun ko b'atan wata Fatima bata tab'a ba, ballen tana b'ari, haka suke zaune duk da yana damunsu Amma ba'a ganewa gwara ma ita Fatima kasan cewarta mace mai rauni, kuma kowa yasan rashin haihuwa matsalace babba.

Fatima tana kiyaye duk abunda tasan zai b'atawa gwarzon mijinta rai.
zamansu zama ne na amana da fahimtar juna, Alhamdulillah yanzu zan iya cewa zaman masoya suke ba na biyayya ba.



Haka ma Addah surkuwar kirki ko tari bata tab'a ba akan rashin haihuwa surkan nata, saboda tasan Allah shine mai bayarwa kuma shine mai hanawa, duk da tanason ganin `yan jikokinta, amma kuma ko a fuska ba'a gani , ita dai cewarta nata Addu'a ne kawai,


matar Usman wato mairo itama shuru Kaman an shuka dusa domin yanzu aurenta yana daukan shekara goma Amma Shuru kake ji Malam yaci shirwa.



Bayan Auren su Fatima da shekara d'aya shima mus'ab yayi Aure, ya Auro mata mai suna Zainab wacce ya dauko daga jihar Bauchi.



Back to labari

★★★★★★


Tashi tayi ta tsaya, domin ko ba'a fad'a mata ba tasan yanzu mijin tane ya dawo, domin lokacin dawowarsa yayi, sallaman da taji ne yasa ta kalli k'ofa tare da wadata fuskartar da sahihin murmushi, barka da zuwa ta masa tare da karban jakar office din dake hannunshi, amsawa yayi tare da kai idonsa kanta ganin yadda tad'an fada a kwana biyun nan shuru yayi kawai ya nufi hanyar side d'insa, domin kimtsawa.


Juice da ruwa sai kuma food flaks ta had'a a akan dan madaidaicin tray kana tayi hanyar side d'inshi dashi.



Da dare bayan sunci dinner suna kallon TV,Kaman bazaiyyi magana ba sai kuma chan yace " Fatima!
d'agowa tayi tare da cewa "Na'am cikin sanyin murya, kallon 2 seconds ya mata yace

" me yake dumunki? baki ta bud'e da niyyar cewa "bab..... kafin ta k'arasa ya daga mata hannu tare da cewa " don't tell me babu please! na sanki, na kuma san halinki, Shuru tayi tare da sadda kanta kasa,
tambayar ya sake maimaita mata cikin sanyi murya tace " Wallahi yaya nima bansani ba kawai dai nasan banajin dad’in jikina a kwana biyun nan,
kallon ta yasakeyi kana yace jeki dauko veil d'inki kizo mu tafi asibiti, kaman zata musa sai dai kasan cewar musu baya cikin dabi'unta yasa ta tashi.

'Daki taje dauko gyalenta ko da ta fito bata ganshi ba hakan yasata yin hanyar waje, tana fitowa ta ganshi zaune a cikin mota har yayi reverse tana shiga ya tada motar suka fita a gidan.


*METRO SPECIAL HOSPITAL* suka nufa, da isarsu sukayi office din doctor muktar (family Doctor )kasan cewar ya kirashi kuma shine da night duty , suna zuwa sukayi hanya d'aya, wato hanyar office d'inshi, kana suka shiga bayan yan gaisuwa da zolaye-zolayen daya wanzu a tsakaninsu, sannan Ahmad ya fad'a masa abunda yake faruwa.
kallonta kawai yayi yace madam yadai? Fatima tace bakomai, Ahmad ne yace" Wallahi doctor batajin dadi kuma idan na tambayeta sai tace "Babu"
murmushi kawai doctor muktar yayi kana ya sake kallonta a karo na biyu,
tambayarta yayi, me dame takeji? fad'a masa tayi, ganin haka yasa Doctor kiran daya daga cikin Nurse d'in asibitin, fad'a mata abunda zata yiwa Fatima yayi,

Bayan an kawo. Result doctor ya gane Fatima na d'auke da cikin 2 months,
cikin zumud'i doctor ya fada masa Abunda yake faruwa.

Fad'an farin cikin da Ahmad yake ciki bata lokacine, sauka yayi akan kujeran ya kalli gabas yayi "suduju shukur"

haka itana Fatima taji abun kaman a mafarki wai yau itace da ciki, rasa me za'ayi tayi kawai sai jin gangarowar hawaye tayi akan kuncinta.



Godiya yayiwa Doctor'n kana suka dawo gida,
Bayan magungunan daya rubata mata, da wasu shawarwarin daya basu a matsayinsa na k'warerren Doctor.


Duk da yanajin kunyan fad'a amma hakan bai hanashi kiran iyayensa ba, wato su Modibbo,
Baya Sun gama gaisawa sai kuma yayi shuru, modibbo daya san cewa akwai magana sai yayi gyaran murya, kana yace " Ahmad akwai wani Abu ne?

Sosa keya Ahmad yayi kaman yana gabansa kana yace dama Dama
Umm...... Fatiiiii...ma ce sai kuma yayi shuru, modibbo yace "uhum inaji cigaba, cikin kunya mahaifinshi yace" dama Fatima doctor yace tana da cik.....
Kitttt! ya yenke kiran.

murmushi yayi tare da godewa Allah, cikin gida ya shiga ya samu Addah, Addah dai ganin fuskan sa washe yasa ajiye rariyan dake hannunta kana ta kade hannayenta, sannan tace "Malam lafiya naga kana murmushi zama yayi akan taburman da ta gama shumfud'a masa kana ya kwashe komai ya fad'awa mata,


Addah tayi farin ciki sosai sannan ta godewa Allah da wannan abun farin ciki, sai ga hawaye suna zuba a idonta,


Hannunta Malam ya rik'e kana yace "Rukayyatu ba kuka zakiyi ba, kuka ba godiya bane, ki gode masa shi kuma sai ya k'ara miki, hannu ta daga sama kana tace"Allah na gode maka, har dai yanzu hawaye basu daina zuba a idonta ba, hannunsa yasa ya goge mata hawayen kana ya fara rarrashinta tare da fad'a mata kalamai masu sanyaya zuciya.



Maganan ciki babu inda bai je ba a cikin kauy'en MARU anata nanatawa akan Fatima na d'auke da ciki, masu farinciki nayi haka ma masu hana ruwa gudu.



Addayi ( mahaifiyar Fatima) itama tayi farinci sosai akan Wannan lamarin, sannan ta gode wa Allah ko ba komai zata huta da maganganun mutanen garinnan akan rashin HAIHUWAR Fatima.



★*★*★*★
kaiwa take da komawa a tsakar D'akinta kai, kace safa da marwa take yi, huci take kaman wata mayunwa ciyar Zakanyar data ga d'aya daga cikin Namun Daji,
cikin muryan da yake nuna zallar bakin cikin da take ciki tace


" Wallahi bazata sab'uba, wai Bindiga a Ruwa, Wallahi Fatima kinyi kad'an, wane ke Wallahi ko addayi bata isaba ballen tana ke, waima ni meyasa komai nasa a gaba bana nasara ne? chaffff ai wlh idan an haifi wannan shegen cikin, to ba ladiyo bace ta haifeni, ni ya kamata na samu wannan abun ba keba kullum arziki ke yakebi, amma ni Shuru, yarinya k'arama kanwar bayana amma ni did'im, to wallahi ko mai zai faru sai dai ya faru, kai da sakel Wallahi.......




09139216255
SADEEY CE✍️*LAULAM*
( _Kishiyata_)




*Alk’alamin SADEEY ce.✍️*






*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

```MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA HUMMM WANI ABU SAI ROYAL STAR WRITER'S ✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) 💪💪💪💪


Please Login or Register in order to submit comment