Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

SADEEY ce.✍️*






*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

```MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA HUMMM WANI ABU SAI ROYAL STAR WRITER'S ✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) 💪💪💪💪
UP-UP-UP```

_🍂"ALƘALAMINMU🖋️ ƳANCINMU"🍂_



Page......17&18

________Allah cikin ikonsa da buwayarsa, ya raya Meemy, don yanzu haka tana da shekara biyu da haihuwa, ta girma Masha, ga wayon tsiya, domin babu wanda bata ganewa a gidan, especially Faisal kasan cewar yafi d'aukanta da kuma mata wasa, sab'anin IMRAAN da ko sake mata fuska bai cikayi ba a yanzu, domin shi yana girma rashin maganansa yana k'ara fitowa fili,





tun Mamy tana damuwa tare da masa magana har ta gaji ta zubawa sarautar Allah ido.



Haka ma Mama taki hak'ura da abunda Bokanta ya gaya mata na babu yadda suka iya da jinin ABUBAKAR MODIBBO amma tayi Kunnen uwar shegu k'arshe ma wani sabon Boka ta samo take zuwa tana ta faman kashe kud'inta a banza, domin shid'in ma bawai asirin yana tab'a su Mamyn bane, kawai dai ya rufe ta ne don yaga kaman ita irin sakarkarun matan nanne.




Meemy nada shekara uku Allah yayiwa (HAJIYA RUKAYYAH ABUBAKAR MODIBBO) (Addah) rasuwa, sakamakon zamewar da tayi acikin Toilet (Bayi) kuma yayi ajalinta, rasuwar data sake girgiza familyn Modibbo a karo na biyu, sun shiga rud'ani mai tsananin gaske.




Idan akace basuji MUTUWAR Addah ba to tabbas nayi k'arya, domin ita Addah rasuwar ta asaran kowa ne, kowa a familyn dama k'auyen ya daka kuma tabbas sunsan sunyi asaran Uwa ta gari.



Abbah da daddy rasa inda zasu sa kansu sukayi domin tabbas rashi-rashine sannan MUTUWAR Uwa daban take *UWA*! *UWA*! *UWA* CE MUTUWAR *uwa* daban take a cikin zuciyar `Ya`yanta domin Uwa ta wuce gaban wasa, komanta na dabanne Shiyasa MUTUWAR ta ta zama na daban, shiyasa MUTUWAR Uwa take zamowa Yayanta tamkar Gyambon da baya warkewa,waanda kulluma zai na famewa.


ya Allah ya jikan iyayenmu da suka riga mu gidan Gaskiya.




Tabbas Addah mace ce mai kyawawan halaye, mace ce wacce kowa zaiso yayi koyi da kyawawan halayenta sadai kashh! kana naka shima yana nashi, mutuwa kenan.




Mamy ma taji MUTUWAR Addah ba kad'an ba, domin Addah Uwace ba matar Bappah ba, sannan ba Kuma *UWAR MIJI* ba ita d'in a *Uwace* take d'aukar ta,


Abbah domin shikam daga shi har daddyn Faisal kasa magana sukayi, gwara ma Abbah Mamy ta tausa sheshi da kalamai masu dadi dakuma saka nutsuwa, sannan kuma da Sanyaya rai, (Hmm dama ance *mace ta gari cikon addinin mijinta*), sab'anin Mama da ko kallon inda yake bata yi ba, don a cewar ta, tana abubuwan yi, masu muhimmanci.



Haka ma Addayi tasan tayi rashin Addah kuma abokiyar zama na kirki,domin Addah macece mai Hak'uri da tausasa ranta duk da tasan tun dãã wassu abubuwan zaman yau da kullum kan shiga tsakanin su ko akan yara ko kuma na zaman take wa, amma Addah bata tab'a magana ba har ta koma ga mahaliccinta,




Haka rayuwa take yau kaine, gobe ba kai bane, haka Addah tazo ta shud'e kaman modibbo tamkar basu zo duniyan ba bama,


Sai dai fatan Allah ya jikanta tare sa sauran musulman da suka Rigamu gidan Gaskiya (Allahummah ameen ya rabbal alameen)




*AFTER SIX (6)YEARS*

*****************
A shekaru shida da suka gabata abubuwa da yawa sun faru cikin na farinciki dana akasin haka, na farincikin har dawowar daddyn Faisal GOMBE da zama a bisa tursasawar Abbah, sannan kuma ya bud'e masa katon *SHOPPING MALL* mai kyan gaske da Kuma girma, sai rasuwa Addayi (Mahaifiyar mamy) sai fatan Allah ya jikansu.




A gefe guda kuma IMRAAN ya gama secondary school inda Faisal kuma sai next year.




Duk da dawowar Mama Gidan hakan baisa Faisal ya kaurace ma mamy ba, hasalima baya zama a side d'in Mama domin har yanzu a gurin Mamy yake, yak'i komawa wajen mahaifiyarsa,
Wannan abun ba karamin bak'anta ran Mama yayi ba, ganin d'an cikinta yana neman yafi karfin ta,




Mama tayi farinci da dawowarta gombe ba kad'an ba ,domin dama burinta kenan ta dawo gombe don ta shiga gari itama tasa kaya masu tsada, sannan tana shiga Motoci kaman dai Mamy,
Sai dai batasan wanda Allah ya d'aukaka yafi Danda duniya ta daukaka, domin Fulani nace *Mo Allah hokki buri mo baba hokki.* domin Mamy ta wuce ta ba kad'an ba ,don zuwa yanzu ita ma Mamy tayi karatu domin tun bayan haihuwar IMRAAN Abbah yasata a school don ganin rashin karatun bayida amfani, sai dai ba daga primary ta fara ba don Satificate kawai Abbah ya nema mata, kana ta fara zuwa daga JS1 har ta gama secondary sannan ya nema Mata admission a *NOUN* wato inda yake aiki kenan kasancewar dama ma'aikatar *WORK AND LEARN* ne Shiyasa ya saya mata admission a gurin shi yana aiki ita kuma tana karatu, domin a yanzu ta had'a degree d'inta, a yayin da shikuma Abbah yanzu ya k'arasa "PHD."




IMRAAN yanzu yana da 26 years a duniya, a yayin da Faisal yake da 25 na ita kuma Meemy take goma kacal.



Yanzu IMRAAN CAIRO din da zai tafi gidan daddyn Kayrat (Mus'ab kenan abokin Abbah ) wanda aiki ya maida CAIRO da zama tare da matar sa zainab da kuma Yayansu wanda a yanzu yana da Yaya guda hudu(4) biyu maza biyu mata, Kayrat (mai sunan Hajiyar Mus'ab ) sai mai sunan Babansu wanda suke kira waleed, sai Ahmad (mai sunan Abbah) sannan kuma Waleeda (mahaifiyar zainab kenan ) kuma duk sun girma kasancewar shi matarsa akai akai take haihuwa duk da ma bazata wuce Mamy ba, domin waleed da Kayrat ma sunfi IMRAAN Sai Ahmad wanda yake sa'an Faisal sai kuma Waleeda wacce zata bawa meemy shekaru uku zuwa hud'u,

ganin mus'ab yana Cairo yasa Abbah cewa IMRAAN zai tafi chan, inda Faisal ma idan ya kammala nasa nan da shekara biyu zai bishi.......✍🏻




back to labari💃





Manage please🤧🤧

More comments more typing💃💃






09139216255
Sadeey


09139216255
Sadeey



Aka bar mamy da kula da Yarinyarta wacce suke kira Meemy, sai fatan Allah ya days mana memeey akan tafarkin manzo...✍️*LAULA*
( _Kishiyata_)




*Alk’alamin SADEEY ce.✍️*






*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

```MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA HUMMM WANI ABU SAI ROYAL STAR WRITER'S ✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) 💪💪💪💪
UP-UP-UP```

_🍂"ALƘALAMINMU🖋️ ƳANCINMU"🍂_

*DEEJAYS TOUCH💄*

_Makeup price list_
Casual Makeup @3k
Special makeup @6k
Bridal makeup @15k

Location: Kano State, Tudun wada bridge, Opp. Hajara Ahmad Primary school.
For your booking Call or Whatsapp 08122188717

Page.....19&20

*An dawo daga labari.*
_____Tana saka kanta a bakin 'Kyauren Gidan Idanunta suka sauk'a akan Malam Liman da kuma Abbah.



Wanda isarsu kenan wani yaro mak'obtanmu yaje ya gayawa Malam Liman, domin shi kad'ai Inna ke say a duk fad'in MARU.



Malam Liman wanda zuwa yanzu tsufa ta gama isar masa.




Innah kanta ta saddar a k'asa domin duk masifarta tana jin nauyin Malam Liman cikin yanayi na kid'ima tace



"Malam Liman barka da war haka da kanka? fatan dai lafiya?”ta jera masa tambayoyin duk a lokaci d'aya, kana ta ida maganan tana zazzare idanu alamun bata da gaskiya.




Malam liman dai Idanunsa ya kafe ta dasu,
ba tare da ya amsa koda tambaya d'aya na daga cikin tambayoyin data jera masa ba, domin yasa idanunsa kad'ai hukuntawa ne, ga mai laifi.





Haka ma Abbah wanda yake mamakin irin rashin gaskiyar da yake hangowa k'arara a cikin idanun wannan matar, sannan kuma ya rasa rawan jikin me takeyi haka, daga ganin su.




Malam Liman ne ya katse shuru ta hanyar cewa "Kulu Ina AISHA take?




shuru Inna tayi tamkar ruwa ta cita, kana ta fara inda indan rashin gaskiya kana tace "taaa.... ta...na... Umm... da kyar bakinta ya iya furta Gaaa.....rke, Garke, ta k'arasa fad'ansa a rarrabe,




Cikin fad'a Malam Liman ya ce




"Saminu d'an Gidan Malam Yusha'u, ya tabbatar min AYSHA tana gidannan domin sunji ihunta, son haka ki gaya min a ina take kafin nasa Amadu ya kira Folisawa don su ladabtar da ke! ya karasa maganan cikin tsawa!



Inna dai ta rasa Yaya zatayi, ba abun ta tasa na Kare ba.




Wayan da taga Abbah ya ciro a aljihu ne ya k'ara tsurar da ita,



Hannu ta d'aura a saman Kanta kana tace


" Hand'e mi woni, Min bi d'id'o, tanad'o nayo, ( Yau na bonu, ni `Ya mutum biyu jikar mutum hud'u.)

"Inna, tana ganin Abbah yasa wayan a kunnensa cikin sauri da kuma hardewar magana tace



"Wallahi zan gaya muku, basai an kirasu ba, tana cikin Gidannan,



Malam Liman kallon Abbah kawai yayi ba tare da yayi magana, kana suka saka Kansu a Gidan kai tsaye, domin a wannan yanayin basa buk'atar neman wani izini, saboda sanin ya yake da Umaru.




Hannun mutum suka hango a bakin kitchen, cikin sauri sukayi hanyar Kitchen d'in (Madafi) salati Malam Liman yayi sannan ya dubi innah cikin zallan b'acin rai yace " Kulu kashe AYSHA kikayi? toh wallahi muddin AYSHA ta rasa akanki sai na d'auki mummunan mataki akan ki! tunda ke mutumiyar banza ce!



Abbah ne yayi inda yaga ILHAAM take yashe tamkar ba rai a jikinta, tattab'a jikinta yayi kana yace




"malam ko zamu kaita domin ga zuciyar ta tana bugawa,



Cikin amin cewa da maganar Abbah yace



"Shikenan tukunna d'auketa mu kaita gidana don wallahi shima Umarun zai zo ya sameni.




Haka Abbah ya ciccibeni ya sani a mota basu zarce ko inaba sai gidan Malam Liman.





Mamy basusan komai ba sai ganin Abbah sukayi da Yarinya a hannu kaman gawa , cikin saurin ta mik'e ciki kid'ima, ta ce Abban Meemy wacece? kuma me sameta? `Yar waye? duk a lokaci daya ta jero masa tambayoyin, Goggo ( matar malam liman wacce ya auro bayan rasuwar addayi, itama tsohuwace)
Tace " haba Fatima ki barshi ya ajiye ta mana tukunna, sannan Mamy tayi shuru Ruwa aka miko kana Abbah ya kar'ba ya yayyafa mata ajiyan zuciya ta sauke mai k'arfin gaske, sai kuma kuka ya biyo baya, sannan wassu surutai nakeyi wanda suke nuni da kaman a firgice nake, ga rawan da jikina yake, ko ido ban bud'e ba illar kawai maganganun da suke fitowa a bakina.



Mamy idanunta ne sukaci gaba da zubar da hawaye, yayin da take tunanin wace yarinya ce wannan haka? Sannan kuma me aka mata?



Duk wadanda suke gurin sai da suka tausaya min jin irin magan ganun da nake Fad'a,



Mamy kam ganin irin rawan da jikina yake yasa ya jawoni jikinta ta rungumeni, a yayin da idanunta keci gaba da zubar hawaye.




Abban meemy meya sameta? yar waye? dan Allah ka gaya min tun dazu nake tambayar ka amma kaki gaya min , ta k'arasa maganar tana sakin kuka tamkar karamar yarinya.




Cikin kwantar da murya yace. "Mamyn yara ki k'ara hak'uri
mana, Insha Allah zan gaya miki idan mun gama magana da Baba,

gya d'a masa kai kawai tayi, ba tare da ta k'ara cewa komai ba,


Meemy ma tanaganin halin da nake ciki, sannan kuma ga kuka da taga mahaifiyarta tanayi yasa itama fara kuka, had'asu Mamy tayi duka ya rungume, a yayin da takejin son a k'asan Zuciyarta.




Jina a jikin mutum yasa na k'ara lafewa tamkar mage, domin babu wanda ya tab'a min irin haka, sannu sannu a hankali nutsuwata ya fara dawowa, domin babu wanda ya taba min haka a fad'in rayuwata,


A b'angaren su Malam Liman kuwa jiran Malam Umaru(Bappah) sukayi har sai daya dawo daga kiwo kana suka je suka sameshi,

Bayan gaisuwar daya wanzu a tsakaninsu, kana Malam Liman ya gayawa Bappah bukatarsu,


Ciki girmamawa Bappah ya amince, duk baso yake ba, yafi son yaje tambayi Inna tukunna, sai ance wai sawun Giwa ya taka na Rak'umi.






A bangaren Innah kuwa ta kasa zama ta kasa tsaye, yau kam bataji ta tashi da sa'a, ita dama Malam Umaru bai dameta ba domin indai akaina ne, ne dashi da babu duk d'aya ne a wajenta,



Cewa take 'yau kam tawa ta sameni ni Kulu, na shiga uku na lalace, Allah kana gani bada wata manufa nake azabtar da itaba, akan gyara ne kawai.




Dole ne tasa su Abbah kwana, don basu zo da niyyar kwana ba, sun ajiye akan washe gari idan sun gama komai zasu wuce insha Allah.



*************************
Washe gari daya kama Asabar, bayan su Mamy sun gama kimtswa, don a zaune suke suna karin kumallo,



Bansan wata kalman wai ita gata ba tun da nake, sai daga jiya zuwa yau, domin naga gata a gidan Malam Liman, kowa nan-nan yake dani.


A yayin da ni kuma duniya tamun zafi, ga radad'in ciwo, sannan ga tashin hankalin da nake ganin yake tunkaroni na rashin komawata gida,
duk kuwa azabtarwan da Inna tamun tamkar Makullu ne na budewar
rashin lafiyata, domin tunda nazo a kwance nake.



da misalin karfe11:30am su Mamy dama mutanen Garin baki d'aya suka cika da tarin mamaki dama al'ajabi, ba komai bane yasa haka sai abunda kunnuwansu ya jiyo musu, marokin an cewa



" An d'aura Auren ABUBAKAR AHMAD MODIBBO, tare da amaryarsa AYSHATU UMAR HUSAINI.akan sadakim naira dubu hamsin lak'adan ba ajalan ba,(Jomirawo hokku jod'e jam)nidai nace ameen.



mutane da yawa sunyi mamaki duba da shekarun yarinya domin kwata-kwata bazata wuce nine years(11) ba,



a bangaren hajiya Inna kuwa......✍🏻





09139216255
Sadeey ce✍️*LAULAM*
( _Kishiyata_)




*Alk’alamin SADEEY ce.✍️*






*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

```MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA HUMMM WANI ABU SAI ROYAL STAR WRITER'S ✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) 💪💪💪💪
UP-UP-UP```

_🍂"ALƘALAMINMU🖋️ ƳANCINMU"🍂_




Page.....21&22

_____Ji tayi tamkar tashin duniya ne, wai yau ILHAAM taji an daurawa Aure,



Koma mene Bappah zai dawo kuma ta sameta, sannan dole tayiwa tufkar hanci, don ta ga yana neman dawowa layi...


Bayan gaisawan da sukayi, bayan an gama d'aura Aure,
Abba ya nunawa Bappah akan ko zaije su gana da ILHAAM, sai dai ya nuna masa baya bukatan hakan..






Bayan dawowar su Abba gida. Ba tare da bara lokaci ba suka d'ugunzuma sukayi mota don tafiya,a yayin da nake tallafe a jikin Mamy,




Sai dai nayi mamakin ganin dani za'a tafi, kaman zan yi magana, amma saboda zazzabin dake jikina, sai ko bakina yamun nauyi.





Da isarmu cikin Gombe kai tsaye SPECIALIST muka wuce, domin zuwa wannan lokacin ban san inda kaina yake ba..




Ba'a bata lokaci ba, aka bani Gado, bayam anyi min duk abunda ya dace...




Sai Doctor ya tabbatar da baza'a Discharging d'ina ba, a yayin da wata ke zaune dani,
hakan yasa su tafiya gida, ganin na samu bacci, domin Mamy taje tayi shirin kwana.




____Bayan Mamy tayi wanka sannan tayi shirin kwana, acikin kayan Meemy ta d'aukawa ILHAAM kana ta d'auki duk abunda tasan mara lafiya zai bukata sannan tayiwa Abbah magana kana ya maidata asibiti.





Har lokacin ban farka daga bacci ba, kasan cewar a cikin drip din akwai Alluran bacci wannan dalilin yasa bacci mai tsananin nauyi yayi awon gaba da ni.


Mamy itace take zama da ni har na tsawon kwana uku, inda yau Monday suke sa ran sallahma duba da jikina yayi sauki, sannan kuma a yaune IMRAAN zai tafi Cairo kuma duk tsawon wad'annan kwanakin da nayi a asibiti IMRAAN bai taba zuwa dubani ba,sai dai Faisal shikam yana zuwa kullum yana dubani saboda yana zuwa da Abbah,





★★★★★
Jirginsu IMRAAN na 6:00pm


Abbah da kuma Mamy sun zabi b'oye musu maganan har sai IMRAAN ya kammala karatunsa Kafinnan itama ta girma ta mallaki hankalinta,Wannan dalilinne yasa babu wanda ya tada maganar auren sannan a gidan ya zama mutum biyu ne kadai suka San maganan auren wato Mamy da Abbah sauran duk basu saniba sai kuma Daddy Wanda Abbah ya gayawa daga baya sannan ya umarceshi daya rufe maganan, wannan dalinne yasa Daddyn faisal bayyi tad'in da Mama (Mairo) ba, haka ma su IMRAAN basu saniba kasan cewar ba'a nemesu a wajen d'aurin auren ba wannan dalilin yasa basu saniba.





Da misalin karfe biyar daidai na yamma mutanen gidan sukayi wa IMRAAN rakiya zuwa Airport, kasan cewar daga cikin gari zuwa airports 40 minute ne, babu wanda baijeba sai Mama da Daddy, ita Mama cewa tayi kanta na ciwo bazata iya zuwa ba, shi kuma Daddy ta tafi wajen sana'arshi kasan cewar Abbah yace masa ba sai yaje ba, isarsu bai jima ba aka fara kiran sunan matafiya har sai da aka iso kan IMRAAN.





Tashi yayi ya fara bankwana da iyayensa, rungumursu ya fara daya bayan d'aya,da Abbah ya fara sai Mamy, Faisal kana Meemy wacce take ta kuka kamam ranta zai fita, sai da yazo kan ILHAAM kaman zai wuce amma ganin tana kallon shi ga Kuma raunin da yake hangowa a cikin idanunta wanda baisan name bane, hannun damanshi yasa ya shafi gefen kumatunta na hagu, bai yi magana ba sai dan gundun murmushin daya sakarmata kana yace" Take care.





tsintar kaina nayi da mayar masa da martanin murmushi,
da sauri ya bar gurin saboda jin heart-beat d'inshi na changer wa, ga kuma hawayen kewan gida da suke son fitowa daga Idanunsa masa,






Bye bye suka fara masa tare da masa addu'o'in samun nasara dana sauka lafiya, amsamu yake da 'ameen' kana shima yana mayar musu da martani 'bye-bye' daga nan ya juya ya fara tafiya hawaye masu dumi yaji suna sauka masa akan kunshi, hannu yasa ya dagesu kana yaci gaba da tafiya har ya bacewa ganinsu,
dukanmu babu wanda bai yi k'walla ba na tafiyarsa, kana suka koma gida cike da kewarsa.





Haka rayuwa taci gaba da tafiya inda Abbah ya sani acikin school d'insu Meemy class d'aya yasa aka kai ILHAAM saboda a cewarsa yafison mu had'a kansu, sannan ko ban gane wani abu ba Meemy zata min bayani, suna primary 4 yanzu a gefe guda kuma an sama min lesson Teacher yana zuwa har gida yana k'ara bud'a min kai akan abubuwan da ban sani ba, sannan anshigar da ni islamiyyah shima daya dana Meemy kuma Alhamdulillah kuma ina ganewa ba.





Inajin dad'in zama dasu kasan cewar babu mai musguna min babu mai hantarata, sai Mama(mairo) don Mama ta tsaneni bata sontlna ko kad'an, sannan kuma a fili ta nuna bata sonta, wannan dalilin yasani jan jikina gefe, don ko side d'inta bata son zuwa, ko Meemy tace mata su tafi side d'in Mama sai inak'i, tun Mamy bata sani ba kai har ta fara fuskan tar akwai matsala, amma sai tayi zipping bakinta gudun afkuwar wata matsalan,



Ni ce da Meemy Zaune a pallown Mamy muna game a iPads dinmu kowa yana rike ta tasa sanye suke cikin dogayen riguna iri daya na kanti wadanda basu kai mana har k'asa ba, kasan cewar yau Thursday ne ba islamiyyah, musu muke akan Coins d'in da muke dashi a game, kowacce tana fadan nata yafi na `yar uwanta duk sun cika falourn da hayaniya, Mamy ce ta fito daga side d'in Abbah wacce hayaniyarmu yasa ta fitowa cikin bacin rain tace " enough!! dukkanmu a firgice muka juyo don kowa yasanta babu wasa a lamarin Mamy, kuma munsan ta hanamu wannan k'aran.




kawunanmu muka saddar k'asa, kana muka had'a Baki wajen fadan "sorry Mamy" karasowa tayi kana tace "ILHAAM Meemy, ban hanaku wannan karan ba?



Sake had'a Baki mukayi wajen fadan" Kin hana, to meyasa kukeyi? tun a dakin Abbah nakejin kuna hayaniya bayan kunsan bayajin dadi yau ko office baije ba meyasa ne idan an hanaku abu sai kunyi ne? especially ma ke Meemy don kece ja gaba,, dukkanku ku bani iPads d'in nan, ai sai da dashi kuke ihun!
cewar Mamy



"Sorry " muka sake fad'a "Ku bani nace!! ta karasa maganan cikin tsananin tsawa a firgice duk suka tashi suka mik'a mata iPads din, karbansu tayi kana da juya ta nufi D'akin Abbah,





Kallonta Abbah yayi daya ke kwance sakamakon zazzabin daya tashi dashi a safiyar yau,kana yayi murmushi sannan yace Mamyn yara meya had'aki da yaran naki yau kuma? guntun tsaki taja kana tace wallahi Abbah yaranne basajin magana ko kad'an kullum idan ba islamiyyah haka suke min suyita cika min gida da hayaniya kaman gidan magajiya, yau kam ai ta kare na huta don wallahi bazan basu iPads d'in su yanzu ba.



Hannunta ya kama kana yace "kiyi dai Hakuri Mamy wata rana bazamuyi ba, tace "kayya duk sun dameni, dame zanji a d'aya, ni suna gama primary next year Idan ka yarda gwara a kad'asu Boarding School kawai kowa ya huta.




Abbah yace" haba Mamy har haka aka gaji damu? gaskiya nikam Yarana bazasuje Boarding School da raina ba,


"Hmm' kawai tace sannan ta k'ara da cewa "shikenan zan shiga kitchen fatan jikin da sauki ko? gyada mata kai yayi kana yace



"Alhamdulillah" tace "to bari na leka Kitchens shikenan yace kana ya lumshe idanunshi alamun bacci zayyi, ita kuma Mamy ta fita a dakin don tafiya ta k'arasa aikinta a Kitchen,






Zaune suke a pallon sunyi jugum alamun abunda Mamy tayi bai musu dadi ba, kallo daya tayi musu suka bata dariya amma sai ta had'iye kayanta kana tace.......✍🏻








09139216255
Sadeey
[6/24, 9:53 AM] Sarauniyar Royal Star Writers Association: *LAULA*
( _Kishiyata_)




*Alk’alamin SADEEY ce.✍️*






*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

```MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA HUMMM WANI ABU SAI ROYAL STAR WRITER'S ✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) 💪💪💪💪
UP-UP-UP```

_🍂"ALƘALAMINMU🖋️ ƳANCINMU"🍂_



Page.....23&24

_______Tafiya take cikin wani Daji,dashi mai duhuwa,


Domin Dajiin ko wadataccen hasken sararin samaniya bashi da shi.




Idan ba duhu mai firgitar da d'an Adam ba, babu abunda yake cikin wannan Dajin.



Sai dai nayi mugun mamaki, ganin a haka take tafiya ko waiye batayi.



Nana na ga ta iso daidan wani waje, wanda yake fili ne, babu alaman Bishiya a wajen.




kana na ga ta ja birki ta tsaya, wassu surkullen maganganu ta fara, wanda ban iya gane me take fad'a ba, ba'a jima ba aka fara wata iska mai had'e da guguwa mai masifan k'arfi, wanda har yana d'aukan busassun Ganyanyakin dake k'asa, iskan na lafawa sai ga k'aton Bishiyan kuka mai katon kogo ya bayyana, agabanta, take kuwa Dajin ya hargitse da wassu irin k'ara-k'ara da kuma surutai kaman kukan mutane ko kuma na Jarirai, wanda dai mutum bazai iya gane me bane.



Takalman K'afanta ta cire, a lokacin data iso bakin Kogon.




Kayan jikinta ta

Please Login or Register in order to submit comment