Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fara k'wabewa, sai da ta ciresu tass, kafin tasa kanta cikin kogon.




Zahiri kogo ne, sai kuma nayi mamakin ganin yadda akayiwa kogon Ado da fatar Damisa, wanda yasa kogon kama da wata masarauta.




Isa tayi gaban wani k'asungumin K'aton Boka, kato ne sosai baki kuma mummuna, mara kyan gani, K'aton jan katon bakin sa mai d'auke da dottin Goro kaman na tsohon najadu, ya bude kana ya fara kyal-kyale wani mummunan dariya, wanda yasa cikin kogon dama Dajin amsawa da wassu amo mara dad'i.




Sai da tazo gabansa sannan ya tsagaitar da dariyan, kana ta fara fad'an




"Ai nasan zaki dawo dole ki dawo saboda kinga yana neman dawowa hankalin sa ,dole ki dawo saboda Gudalle tayi AURE, nasan dole ki dawo saboda duhu na neman rufe rayuwar ki, dole ki dawo, dole ki dawo kekekekehhhhhhh!!! heeeeeehhhh woohhhhhhh!! dole ne ki dawo garemu saboda biyamiki bukata Hhhhhhhhhhhh!!!”




Saida yayi dariya mai isarsa kana ya yayi shuru tare da tsuke tamkar bai taba dariya ba,






Shurun da taga yayi yasa ta gane cewa ya bata daman magana kenan kana yafara magana




" Ran Babban Boka ya dade, ka jima ka dade, kaga jiya kaga yau kuma zakaga gobe,boka ka taimakeni ka sharemin kuka na (wa iya zubillah😢😔) Boka, kwab'ana yana shirin Ruwa, aikina yana warwarewa yakai Boka mena aikata haka da zafi da har wad'annan abubuwana suke warwarewa, naga yana neman yafi karfina, mutumin da ko magana na fad'a masa baya tsallakewa amma wai har zai Aurar da Gudalle batare da ya nemi shawara ta ba, ina tuba ya kai wannan babban Boka ,idan nayi laifi amin afuwa bazan sake,Boka kai ka gayamin cewa Gudalle bazata taba Aure ba,koda tayi auren babu namijin da zai so ta ko da inuwa d'aya bazai so ya zauna tare da da ita ba,Sannan ka sanarmin cewa koda sun zauna inuwa daya bazata tab'a son d'ana namiji ko sha'awarsa ba, haka shima bazai ji Sha'awwarta ba, meya samu aikina yake neman warwarewa? nasan ni ban karya doka ba”







kekkkkky!! hhhhhhhhhh!wohhhhohooooo, "tabbas aiki bai warware duka ba, amma akwai wanda ya warware saboda had'uwar Jini da Jini, wato had'uwar Gudalle da jinin MODIBBO ABUBAKAR SULAYMAN, hakan ne yasa na jikin Umaru ya warware, wanda hakan yasa bā komai zaki gaya masa yayi ba, sannan shakkarki zai ragu acikin Zuciyarsa, haka kuma tsoronki zai ragu acikin Idanunsa,Akan Igiyoyi guda uku na AURE da suka shiga tsakanin Gudalle da kuma Jinin Modibbo, Umaru bazai ji waccan kiyayyar da aka sama duk d'a namijin daya AURE ta ba, idan kuma kika bari ya santa a matsayin ‘ya mace, ya mai da ita cikekkiyar mace, wato ya huda tantanin budurcinta, to duk abunda kikayi na tsawon shekara goma zuwa sha d'aya, acikin kaso D'ari to lallai ki kwana da sanin tamanin zai warware. hhhhhhhhhh!ehhhhhhhehhh!hhhwoooh!owwwhhhhhhheehhhh






"Sannan kuma yanzu ku sani Gudalle tana sallah, a da kuma baki barinta
tayi sallah, to ku sani dama taurarinta suna da haske kaman na Jikan Modibbo, don haka ba lallai bane komai ya kamata, kin tafka babban kuskure! kun tafka babban kuskure, hhhhhhwoooohhhh,kekkkkkekkkk hhhhhhh!hhhhhehhhhh, can ya gimtse Bakinsa
kana yace



"Yanzu me kikeso ayimiki?
Cikin tashin hankali tace


"So nake Ubanta ya sake mantawa da ita, kaman yadda a can baya, baya iya tunata, haka kuma baya iya tuna ALAK'A *GONDAL* (Liffafin Nana M Sha'aban) dake tsakaninshi da ita, so nake kasa tsanarta a zuciyar mijin da ma iyayensa, da danginsa baki d'aya,


hhhhhhhhhhe!hhheeehhh!! bazaiyuba! saboda yanzu tana sallah tana azkhar,sannan kuma ki tura kwana da sanin cewa sihiri bazai kama jinin ABUBAKAR MODIBBO ba bazai yuba bazai yuba, zanyi miki aiki akan auren sannan zan k'ara mantar da Uban Gudalle, sannan ki sani mahaifin Gudalle ya fara sallah a yanzu, sannan kuma yana zuwa wajen neman karatun addini, zanmiki aiki akansa ya dawo kaman daa chan sai dai a kullum zan tunatar dake makarin wannan aikin kinsan inda zai na fisari a bayan gida,(Toilet) muddin kika bari yayi a waccan wajen to kisani kashin ki ya bushe, hhhhhhhhehhhh!!eehhhheeeh! sannan kuma ki sani indai mijin gudalle ya kusanceta to itama sihiri zai daina kamata saboda kusantarta zai jawo had'uwar Jini acikin Jini, jininsu zai gaurayu!! hmmmmm a randa jinin su ya had'u kuwa to ki sani komai zai zo karshe! hhhhhhhhhh hhhhhhhhhh!!!!!!!



"to yanzu boka kenan babu yadda za'ayi da wancan yaron


ke!!! ina gaya miki abunda bazai yuba kina sake tambaya ta! ai kinfini sanin waye ABUBAKAR MODIBBO!


Sannan aci gaba da kulamin da JININA dake wajenki, wanda ba kowa bane yasan da hakan,



" Ran Boka ya dad'e, to yanzu me zan kawo,




Dariya ya babbake da ita, bayan ya gimste fuskarsa yace " abunda aka saba,



"To ai babu damuwa, ta k'arasa mikewa kana ta nufi wani keb'antaccen guri, wanda yake kaman D'aki.



Baki ya kashe, kana ya mike tare da bin bayanta, yana kallon yadd jikinta ke juyawa.
(Wa'iyazubillah, Allah ka tsaremu ka tsare mana Imanin mu,)




*GOMBE*
rayuwar gidan Abba yayi min dad'i, inda a yanzu muna shirin shiga jss, bani da matsala a gidan komai min akeyi, banida damuwa da kowa, sai dai tunanin gidan dake addabata, amma Mamy bata bari abun yayi nisa take hanani, domin itama tana son naje gida sai dai Malam Liman ya hana zuwa.




saboda ta tabbatar wa Mamy da cewa akwai asiri a jikin ILHAAM da ma Bappah, wannan dalilinne yasa idan na nuna inason zuwa Mamy ke kwantar min da hankali tare min wayo.




a bangaren Mama kuwa, tayi tayi taga babu abunda ya sauya, har ta fara tunanin ko zata saduda, sai dai har Yanzu bata jin zata zubawa Mamy ido, sannan kuma ga rashin nasaran da batayi, nasara d'aya tasan tayi shine na sakawa mahaifan Mamy key wanda kuma har yanzu tana da tabbacin da bata kulle ba da maybe Mamy nada []a[]a 6 ko 5, amma tace sai dai ta kare da guda biyun tunda itama Allah bai bata ba, domin Meemy ma, ta ta tabbata rabo ne, ne kawai yasata fitowa.




Haka rayuwa take ta tafiya yau dadi gobe akasin sa,hakanne ya kasance a wajen bayin Allah da dama, irinsu Bappah.



A b'angaren Bappah kuwa zuwa Yanzu ya koma ruwa domin karatun daren ma ya daina zuwa, haka ma bangaren addininsa ya sake komawa ruwa domin babu abunda yakeyi na bautar ubangijinsa, sai dai Yanzu baya ma tuna ILHAAM ko kadan domin dama ya tsane ta tsana mafi muni, amma yanzu ji yake kaman bau tab'a sanin wata wai ita ILHAAM ba.


Sai dai mafarkan da yakeyi, Wanda ya kasa gane kansu, ya rasa inda zai saka kansa yaji dadi, rayuwa ta masa zafi, yana so ya koma wajen Malam Liman, sai dai shi kansa Irin tashin da hankalinsa yakeyi ba, a duk lokacin da Zuciyarsa ta raya masa hakan.



Wannan dalilin yasa yake janye tunanin da zaran yazo masa.





A bangaren Inna kuwa tunda ta dawo daga wajen Bokanta takewa Bappah kallon zaka gane kurenka, domin zuwa yanzu duk abunda ta gaya masa ko da kuwa menene take aikatawa, abunda Bappah yake wa INNA ko 'yar cikin ta, Zainabu taza tai mata ba,


A bangaren IMRAAN kuwa rayuwar gidan ba laifi yana da da'di, sai dai shi gidan baya mishi dad'i kwata-kwata, domin shi yaso ma ya kama hostel domin gidan bai mishi, yafison yaje inda ba'a sanshi ba, sannan inda babu mai takura masa.






"A b'angare na nima sai dai na godewa Allah Ubangijina, domin babu abunda na nema na rasa na jin dadin rayuwa, domin Mamy ta rikeni tamkar Yar cikin ta.




"sai dai matsalana d'aya a gidan, ba kowa bace face Mama, Mama ta sani a gaba, kullum cikin tsangwamata take, tun abun na damuna har na tattarashi na zubar a gwandon shara,domin idan da sabo yaci ace na saba da irin wad'annan abubuwan, musamman ni da dana tashi a gaban Inna, wani Irina k'iyayya ne, ban gani ba, shiyasa nake ganin nata duk sanyi ne.






Mama kuwa abunda ya dameta da ILHAAM wai meya kawota gidan? babu dangin Iya bana Baba, (Kunsan har yanzu Mama batasan cewa an d'aurawa IMRAAN AURE ba. )
ita ba dangin MODIBBO ba, ba kuma na Addah ba, ta dai gane itama yar karere ce.





"A tsakanina da Ya IMRAAN kuwa tunda ya tafi ko magana a waya bamu tab'a ba,ko video call idan ya kira yana neman Meemy amma bai tab'a nemanta ba, hakama Mamy bata tab'a masa maganar taba.








"A yayun da ni kumana manta dashi kwata-kwata, domin ni ba mai sa abunda bai shafeta bane a rai, indai abu bai shafeni ba to bana damuwa dashi....













09139216255
Sadeey ce
[6/25, 10:17 AM] Oum Juwairiyya Royal Star Writers Association: *LAULAM*
( _Kishiyata_)




*Alk’alamin SADEEY ce.✍️*






*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

```MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA HUMMM WANI ABU SAI ROYAL STAR WRITER'S ✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) 💪💪💪💪
UP-UP-UP```

_🍂"ALƘALAMINMU🖋️ ƳANCINMU"🍂_

________________*DEEJAYS TOUCH💄*

_Makeup price list_
Casual Makeup @3k
Special makeup @6k
Bridal makeup @15k

Location: Kano State, Tudun wada bridge, Opp. Hajara Ahmad Primary school.
For your booking Call or Whatsapp 08122188717
______________



*MAMAN ARIFULLAH DATA SERVICES*

Ku garzayo ku kwashi Rahusa ga Araha ga karfin Network📶📶📶📶📶

Monthly ce ma'ana sai tayi Miki wata guda kina amfani da ita💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼 1GB #300 only
2GB #600 only
3GB #900 only
4GB #1200 only

1235133114
Maryam Koki Sule
Access bank 🏦.

Akwai Datar Airtel, 9Mobile,
Domin Karin bayani call /WhatsApp 07040084359
💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼
________________



Page.....25&26


Bayan shekara 6

4:00m
*GOMBE INTERNATIONAL AIRPORT*

_____Sauƙowa yake akan matakalar Jirgin AZMAN, wanda ya sauka karfe hudu dai-dai na ranar.




Kyakyawan saurayine ajin karshe mai cikekken kamala, da cikar haiba, wanda daga ganinsa kasan ibada da bautar Allah sun zauna masa, ƙak'k'arfane mai budedden jiki ya na da tsayi sosai, fari ne amma ba tass ba, yana da d'an fad'in fuska mai d'auke da manyan idanunsa, kansa cike yake da bakin gashi mai laushi na salain fulanin JOTTAMA'EN, goshinsa akwai tabon sallah wanda ya k'ara wa fuskansa kyau da kuma kwarjini, *ABUBAKAR AHMAD MODIBBO* ( *IMRAAN*) kenan.




Airport d'in ya k'arewa kallo, kana ya lumshe idanunshi ya daga kansa ya kalli sararin samaniya, tare da shaƙar iskan ƙasarsa, garinsa kuma mahaifansa, wanda rabonsa dashi yanzu tsawon shekaru,



Lallai bahaushe ya yi gaskiya da ya ce "wanda ya bar gida, to tabbas gida ya barshi, rayuwa kenan.



Faisal ne ya hangosa kana ya ƙwala masa ƙira, don ganin yadda ya kalli sama bai ɗago ba. (kasancewar Faisal bai tafi Cairo ba saboda Mama ta hana ya tafi, wannan dalilinne yasa ya yi nasa a jihar Gombe.



Isoshi keda wuya suka rungume juna, suna masu jin tsananin kewan junansu, kana suka dunguma zuwa cikin mota, hanyar gida suka kama yana karewa hanyar, ganin yadda komai ya canza, kallo ya na tuna kaman yau su Abbah suka masa rakiya.



Gaskiya ya yi kewar komai na 9ja, yayi kewar kasarsa ba kaɗan ba.




Parking d'in da Faisal yayi ne ya dawo dashi daga doguwar tunanin daya tafi, gidansu ya k'arewa kallon tabbas babu abunda ya sauya a gidan sai abunda ba'a rasa ba da kuma irin gyare-gyaren da ake yiwa gida, lokaci bayan lokaci, jin an bud'e masa K'ofar motar yasa ya sauke nannauyan ajiyan zuci,




Fararen kafafunsa ya sanya a waje, said a ya kwashe tsawon wassu second, kafin ya yunkura ya fito da gangar jikinsan zuwa waje.




Sannu da zuwan da su Baba mai gadi ya amsa, kana ya daga musu hunnu, tafiya ya fara tamkar mai yanga, ko Kuma wanda aka masa dole,
tafiya yake yana ji yadda gajiyar jikinsa ke kara warwarewa yana bin dukkan ilahirin jikinsa.




Handle K'ofar ya murd'a tare da yin sallahma cikin zazzakar muryarsa, kana yasa kansa a cikin parlour.




Meemy ce wacce take zaune tun tuni cikin kwalliyar dataci tayi kyau sosai tana jiran isowarsa domin taso bin Faisal Mamy tace ta bari a k'arasa kimtsa komai da ita, ihu ta sa kana ta taso da gudu tayi kansa tana dad'in




"Oyoyo big Bro jikinsa ta fad'a tare da kankamesa,



Karbar Yar kanwar tasa yayi kana ya sake mata kekkyawar murmushi wanda ya kusan ya karawa fuskarsa, cikin cool voice dinsa kaman ko yaushe yace




"Kai Meemy bakisan kin girma bane?,har yanzu dai kina nan da halinki.




Sakinsa tayi tana zumbura baki kana tace




"Haba ya IMRAAN nayi kewar Kane fa,



Kumatunta ya ja yace"kai little sis kin girma fa ashe? Hannunta ya rik'e yana mai karasawa cikin palour'n, inda Mamy ke tsaye tana kallon su cikin farincikin ganin d'anta mafi soyuwa a gareta, wanda tayi kewarsa na tsawon shekaru ba tare da ta gansa eyes-to-eye ba, kamshin turarensa na sanar mata da zuwanshi waje.




Fad'awa yayi a jikinta yana mai shakan kamshin humran dake jikinta, hawaye ne yaji suna tsatstsafowa daga cikin idanunshi jinsa a jikin mahaifiyarsa yasa yaji raunin sa a kusa,tabbas Uwa! rahamace ga []a[]anta tabbas Uwa kyauta ce da Allah ya bamu! uwa! uwa! uwa! uwace abun tink'ahon kowa,abar son kowa, abun alfaharin kowa, farincikin kowa, mahaifiya kenan, Allah ya jikan wad'anda suka rasu, wad'anda ke kuma Allah ya k'ara musu nisan kwana mai anfani, ya azirtani da kekkyawar tsufa.




Mamy ma hakanne ya kasance a wajen ta jinshi a tare da ita ya tayar mata da kewansa na tsawon shekaru, ji take kaman a mafarki, ji take kaman bacci take, tabbas yaya rahama ne ga iyayensu, kaman yadda Iyaye ke rahama ga 'Yayansu, hawaye taji a kunchinta suna sauk'a, wanda batasan yaushe ne suka fara ba,ko ba'a fad'a ba tasan na farinciki ne.





"Toh wannan wace irin Uwace haka maimakon farinciki sai kuma kuka, maganan Abbah ya dawo dasu daga duniyar da suka tafi, wanda ya dawo bayan shigowar IMRAAN ba dadewa, IMRAAN janye jikinsa yayi daga na Mamy kana yayi wajen Abbah shima ya rungume sa.






Shima Abba rungumarsa yayi tare da bubbuga bayansa ganin yadda idanunsa suka kad'a,murmushi ya sakar masa kana yace





"Babana nidai nasan jarumi ne, ya k'arasa maganar cikin zolaya,murmushi sukayi dukansu har da Meemy wacce ya sakewa hannu lokacin isarsa inda Mamy ke tsaye.




Zama sukayi kana suka kana suka fara gaishe-gaishe, tare da d'an tab'a hira.




ganin yana hamma yasa Mamy cewa ya tafi D'akinsa yaje yayi wanka zata sa a kawo masa abinci, toh ya amsa kana yayi musu sallahma,




Ya shiga D'akinsa wanda Mamy tasa ni gyarawa tun daga rana, D'akin ya k'arewa kallo ganin babu abunda aka cire haka ma babu abunda aka sa,yana nan a yadda yake sai changer yanayin zaman D'akin da akayi wanda ya k'arawa D'akin kyau da tsari,kayan jikinsa ya cire kana ya fad'a a toilet wanda yake ta zuba uban kamshi.




Fitowarta daga wanka kenan tana d'aure da towel peach colour babba, sai d'an k'arami fari a hannun ta, tana goge dogon gashin kanta baki sidik, sauri take domin Mamy tace mata tayi sauri ta shirya kafin Faisal yaje d'auko ya IMRAAN daga Airport.





Ita kwata-kwata bata son ko had'uwa da ya IMRAAN wallahi,wajen dressing mirror taje ta fara shafa lotion
dinta mai kamshi, bayan gamawarta.





Taje gaban wardrobe ɗinsu wanda ya kasance mallakinsu ne ita da Meemy, wani ɗan ubansu baƙin less mai fari da touch d'in blue ta d'auko mai d'an karen kyau da tsada wanda Mamy ta dinka musu ita da Meemy, Fitted gown ne dinkin ya zauna mata ɗas a jiki, gaban mirror ta dawo inda kayan makeup dinsu yake.




Kujeran mirror naja na zauna,
don yin kwalliyar da Mamy ta tilasta min yinsa.




Domin tace min karna kuskura na fito da fuska kaman namiji,




Ni dai banga anfanin wannan kwalliyar ba amma babu yadda na iya.



Simply makeup nayiwa kyakyawar fuskata wanda ya dace da make-up din, kana na murza ɗan daurin ɗan kwalina,






Kiran da naji Mamy na min ne ya sani amsawa, tare da d'aukan veil d'ina nayi waje.




fitowa nayi daga ɗakin ina tafiya ina k'arasa saka dan kunnenta,




kallona Mamy tayi kana ta ce "Masha Allah Daughter kinyi kyau sosai, murmushi na yi tare da cewa "nagode Mamy,




"yauwa please ɗauki abincin nan ki kaiwa Yayanku a ɗaki,
cewar Mamy.



Ban san lokacin da na gwalo idanuna waje ba, kana na ce "ni kuma Mamy?





Mamy ta ce "me zaki wani gwalo manyan idanu, kaman na aikeki dakin Kura ko Damisa? dauka ki tafi,





kasan cewar musu baya cikin dabi'una yasa na yi kasa da kaina.





Dauka na yi tare da nufar hanyar ɗakinsa, wanda aka sani wahala akansa dazu, don masa shara ga gyarawa.





Isowata bakin ƙofar ya sa na tsaya,
sallama nayi jin ba'a amsa ba ne ya sa na murɗa handle din ƙofar kana nasa kaina tare da shiga dakin.





Abunda idonuna
suka gane min ne ya sa na kusan sakin
tray din abincin dake hannuna.....✍







09139216255
Sadeey ce
[6/27, 10:33 AM] Aishatouh Royal Star 🌹: *LAULAM*
( _Kishiyata_)




*Alk’alamin SADEEY ce.✍️*






*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

```MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA HUMMM WANI ABU SAI ROYAL STAR WRITER'S ✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) 💪💪💪💪
UP-UP-UP```

_🍂"ALƘALAMINMU🖋️ ƳANCINMU"🍂_



Page.....27&38


____IMRAAN na gani daga shi sai d'an k'aramin towel d'aure a k'ugunsa,
wanda fitowarsa kenan daga wanka don ko knocking din da nayi bai jiba.




baki na bud'e da niyyar k'walla ihu sakamakon karon da naci da murd'ad'd'un gab'b'an jikinsa, domin a tarihin rayuwata ban tab'a ganin K'aton balageggen Namiji haka ba, shiyasa abun yazo mini a wani iri.



"Idan kika kuskura kika sake wannan ihun wallahi sai kin yi nadama!




Na tsinkayi muryan sa,
kaina na saddar kasa cikin inda-inda da kuma son barin D'akin nace




"Dama Mamy ce tace na kawo maka abinci, na k'arasa maganar ina k'arasawa bakin Gado akan Capet d'in D'akin na ajiye kana na juya nayi hanyar waje Abuna.





da kallo ya raka bayan ta yana mai mamakin wai ma yaushe wannan yar tatsitsiyar yarinyar nan ta girma haka?





Fitowa nayi ina haki kaman wacce ta tasha uban gudu, Mamy ce ta kalleni kana ta ce




" Ke kuma fa? lafiya kike ta haki kaman wacce aka biyo, amsa mata nayi da lafiya Mamy,




Cikin rashin yadda ta k'ara cewa "har kin kai masa? da eh na amsa mata, don na kosa da tamboyin.





"amma kinyi serving dinsa?
shuru nayi bance komai ba, wanda ya k'ara tabbatar wa Mamy cewa amsar itace a'a "meyasa haka ILHAAM wai! jeki yi serving dinsa kinji daughter? da toh na amsa kawai amma ba wai so nake ba, kana na komai cike da zullumin yaya za'ayi ayita aikanta dakin wancan basamuden mutumin? da wannan tunanin na iso bakin K'ofan D'akin, rasa ya zanyi nayi kawai tayi shahada ta fara knocking, sai da nayi kusan sau biyar har na fara k'uluwa naji daga cikin yace " yes, baki na murgud'a kana na murd'a Handle d'in tare da sallahma, samun sa tayi har ya shirya cikin Jallabiya Ash colour yasani sauk'e ajiyar zuciya,




Tsayawa nayi cikin jin haushinsa nace "wai inji Mamy nayi serving dinka,

kallon fuskana yayi kana ya tabe tare da cewa " da kika tafi dama izinin neman serving d'ina kika tayi yi? ko kuma yaya?


shuru nayi domin zuwa yanzu haushi yake bani mutum sai iyayi,
da shegen kinibibi.




Tsugunawa nayi ba tare da nayi magana ba, na fara serving d'insa sai dana gama, ganin wani abun yake daban yasa yin hanyar waje har ta isa kofa naji sautin yatsunsa sakamakon kadasu da yayi,kaman bazan juya ba sai kuma na juya na dawo har gabansa na tsaya masa kegege a kaa kana cikin takaici nace "gani,



" Magani zaki bani ne da kika tsaya min a kaina,



gane me yake nufi ne yasani zama ina b'ata fuska,



A k'alla na kai
Minti biyar(5) har na gaji, amma shi yana shuru hasalima waya yake dannawa tamkar bai sai da wanzuwata a wajen ba.





A zahiri waya yake dannawa, sai duk yamutse-yamutsen da nakeyi yana kallona ta wutsiyar Ido, murmushin gefen baki yayi a ransa yake jinjina miskilancin wannan Yarinyar



ki duba acikin akwatunan nan ki d'auko min brawn da red dinnan ki bar sauran biyun, ki kawosu gaban wardrobe d'in ki jeramin kayan a aciki.


Ai bansan sanda na d'ago kaina ba, amma ganin yadda ya fuske kuma ya tamke fuskan tamkar ba shi yayi bane yasani tashi ganin babu fuskar musu,


Wajen akwatunan naje amma ganin duk wanda na daga ko motsi bayayi, idan nayi niyyar kwantarwa da nufin taja sai nauyin akwatin ya rinjayeni kaman zamu fad'o tare, yasani bata fuska, cikin gajiya da kuma kosawa da aikin da daya sani tace





" Ya IMRAAN please kazo to ka daga min bazan iyaba.




Sai dai idan Gadon da yake D'akin zai yi magana to shi yayi, domin tamkar bai ji me tace ba, sai da ya kwashe tsawon lokaci kana ya tashi ya iso gurin, rankwafowa yayi wanda ya kawo kusanci a tsakaninmu, ai ba shiri naja baya, ko inda nake bai kalla ba ya daga su duka biyu ya kai su har gaban wadrobe d'in, ya ajiye kana ya koma kan kujera 3str dake dakin ya zauna, kana ya jawo plate d'in abincin da bai ci ba.




Wardrobe d'in na bud'e kana na fara jera kayan bayan ta samu towel ta kara goge kuran daya taru
duk da ma ta goge data zo yin shara.






Sai dana kwashe lokaci mai tsawon gaske kafin na kammala jera duk kayan cikin akwatu guda biyun nan, komai sai dana jerashi cikin tsari da tarin nutsuwar da Allah ya azurtani dashi,komai daki-daki na jera wajen k'ananan kaya daban, Jallabiya's daban, 3Quater daban, wajen jere Boxers da Singlet ne nayi ta magana a raina tana cewa wannan mutumin bayida kunya ko kad'an ni zaisa na jera ma wad'annan abubuwan, shiko kunya bayaji.




Haka na k'arasa komai cikin tarin gajiya, dama yau ko komawa bacci Mamy bata barmu munyi ba, tun 6 ta tashe mu akan girki a gyara gida.




Mamy dai tun tana d'aukan abun na wasa har tazo ta gane tabbas bana wasa bane ganin yara duk sun makale a daki, amma bata damuba kasancewar tasan ko ma mene ai akwai AURE a tsakanin su,amma bazata so hakan ya faru ba.


sai da taga fitowarta kafin hakalinta ya kwanta, wanda dakyar ya barta ta fito, Mamy ganin ta a galabaice gata wujiga-wujiga ga d'an kwalinta daya karkace wanda ya kalli kudu maso gabas, tana tuna yadda taci kwalliya kafin ta tafi amma ta dawo wata daban.




★★★★★
A shekaru biyar d'innan abubuwa da yawa sun faru ciki har da rasuwar Malam Liman, wanda family suka girgiza da rashin sa kasancewar bayan MODIBBO shine ya zamo musu mahaifi, amma wanda ya basu ya karb'e, sai dai fatan Allah ya ji kanshi.




Duk da tarin shekarun nan basu sa asirin da Inna tayiwa Bappah ya karye ba saboda kullum tana hanyar zuwa wajen Bokanta, domin shi Bappah tun ranar da dawo daga wajen Bokanta ya manta da ita,kwata-kwata baya iya tuna cewa akwai wata Yarinya ILHAAM, bai taba tuna cewa ya tab'a haifar yarinya mai suna ILHAAM, shi dai `Ya d'aya gareshi itace Zainabu.




Innah duniya

Please Login or Register in order to submit comment