Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da hawa gadon kasan cewar ILHAAM ta rigashi hawa already, saboda umarnin daya bata.




4:10pm
Ihun da ILHAAM tayi yayi daidai da saukan ruwan sama wanda yake zuba kaman da bakin ƙwarya.




Kukan da ILHAAM tayi shine ya haddasa faruwar abubuwa guda biyu, sannan kuma a mabanbantan wurare wato a *MARU* da kuma
*J.O.S*
.......✍🏻







*Sadeey ce✍️**LAULAM*
( _Kishiyata_)



*Alk'alamin Sadeey ce✍️*




««•–––––––––––––––––•»»
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

•««–––––––––––––––––»»•



*Page 44&45*


_____kwance yake akan Gado, zufa ce ta wanke masa jiki,tamkar wanda yayi wanka, ko ya fito daga cikin ruwa, yana bacci da mafarkai, a dai-dai sanda ya farka a wannan lokacin ne kansa yayi mummunan sarawan da ya haifar masa da ciwon kai mai tsanin gaske,wanda yayi sanadiyyar taruwar futsari a maransa, ba shiri ya dirk'a daga gado yayi hanyar waje don zuwa ban D'aki ya samu daman juye fitsarin da ya tarar masa a mara..




Inda innah ta taɓa masa kashedin karya kuskura yayi fusari a wajen yau anan yayi futsarin, wanda gama futsarin yayi dai dai da kwasar da jiri ya masa ji kake tim! ya faɗi ƙasa ba alamun rai a tare dashi.






*GOMBE*
IMRAAN bai sauka akan ILHAAM ba, har sai da masallacin anguwarsu ya kira sallahn magrib, wanda zuwa wannan lokacin ba numfashi a tattare da ita.




Sai da hankalinsa ya dawo jikinsa kafin ya gane aika-aikan da yayi, jijjigata ya hauyi, sai dai ba alamar za ta tashi.





"ILHAAM! Kiyi hak'uri dan Allah karki mutu wallahi bazan sake ba, ganin hakan bazai fasshe shi ba,yasa ya shiga toilet yayi wanka cikin sauri ya gama shiri, tare da sa mata kaya ya d'auketa sai *_FTHG_* .




Nan doctor’s suka karɓeta tare da shiga da ita.




Sai after 1hr kafin doctor’s su fito daga kanta,
*doctor Safiyah* itace wacce tacewa IMRAAN, ka sameni a office d'ina.




da toh ya amsa tare da bin ta a baya.
Bayan ya shiga office ta bashi izinin zama sannan tace,

"Am Alhamdulillah mun samu mun tsaida jinin dake zuba daga jikinta yanzu, sannan mun mata d'inki sakamakon buɗewar da hanyar yayi,


Fasali taja sannan tace


"Abu na gaba kuma munason gaskiya a kula da ita sosai, ta dinga shiga ruwan zafi ba dare ba rana, sannan zaka d'an haƙura mata ta fanni auratayya fatan ka gane? ta k'arasa maganar tana tura masa Paper'n data rubata magungunan da za'a siyawa ILHAAM d'in.



"Insha Allah Yaushe amma zata farka? cewar IMRAAN
" zuwa 11 Insha Allah, saboda allurar baccin da muka mata.



godiya ya mata kana ta fita.


D'aya daga cikin kujerun dake cikin reception d'in ya samu ya zauna kana ya fara tunanin abubuwa da dama.




**********
Zaune suke acikin Barander, da yamma, akan taburman da Hajara ta shimfud'a musu, su uku.




Ihun da Shatu tayi shi ya dawo dasu daga duniyar tad’in da suka tafi, duk kansu kanta su kayi suna jijjigata tare da kiran sunanta,amma ina ta tafi,



K'arshe Hajar ce ta fita daga gidan da gudu don kiran Baba wanda bai dawo gida ba, tunda ya tafi daga masallaci sallan la'asar.




Ganin Shatu a yashe yasa Baffah cewa Hajar ta kawo masa ruwa,



Watsa mata sukayi kaman sau hud'u kafin ta sauke zuciyan dake nuna ta dawo cikin hayyacinta.



Innanillahi, wa inna ilaihurrajiuna
Ya jomirawo yidam, (Ya Ubangijin ka taimakeni) Addah useni ta fad’d’anam bingel (Addah don Allah karki kashemin `yata) mi yid’u hude'am( Inason abuna) Wad'u mu`yal (Kiyi haƙuri) waɗannan sune surutan da Shatu take yi wad'anda suka sanya Baba da Goggo zubar da hawaye.


Kallon rashin sanin data fara musu ne yasa Baba ya labarta mata yadda sukayi suka sameta,




Kuka sosai Shatu takeyi,
Cikin sheshesheƙar kuka tace,Nagode Baba da Goggo haƙiƙa ku alkhairi ne a gareni da ba don kuba da bansan ya RAYUWATA zata kasance ba, ta karasa maganar tana jawo Hajar jikinta.



Yanzu nan inane? Cewar Shatu,
"Jos cewar Hajar
Cikin mamaki ta sake mai-maita kalman Jos kuma?




Eh ke `Yar inane? Baba ya bata amsa yana mai kallon gefe.



Jihar Gombe cikin yanayin damuwa tace " ni `Yar jihar Gombe ce.




"Uhm karki damu ba nisa sosai don Bauchi ne kad'ai jihar dake tsakanin Jos da Gombe.




" Baba kuyi haƙuri inason komawa gida,domin Inaji a jikina, Mijina da ƴata suna d'and'ana uƙubar KISHIYATA,domin nasan bazata bar min Yarinya ba, tunda nima bata barni ba, takarasa maganar tana k'ara fashewa da kuka,


Domin LAULI RAWO AM, mo kallud'o (KISHIYATA muguwa ce)
```LAULAM mo wawai FAD'D'UKI neddo, gam mo wala ɓerde wonde, TEGAL BINDAGAL fudaniyam joddaki e LAULIRAWO me yida yinbe, tegal am gal koddiraga. mu timmitka gite mako a dufa gondi foudi. (Rubutaccen Aure ya jamaini zama da KISHIYAR da batason mutane, wacce Zuciyarta ta gama kenkeshewa, ta k'arasa maganar idanunta na zubar da hawaye) ```




Cikin rashin gane inda maganganunta suka dosa, Goggo ce tace "to yanzu ki fad'a mana sunanki, sannan ki bamu labarin me ya saki barin gidanki Mahaifanki, Mijinki da kuma Jinjirar `Yarki acikin wannan daren?




Murmushi tayi mai ciwo, don tambayoyi da Goggo ta mata ba k'aramin fama mata tsohon gyambon dake cikin cikinta, kana tace nidai sunana KHADIJAH amma a gidanmu ana kirana da Dije, labarina kuma sai munje Mahaifata, daga haka ta had'a kai da gwuiwa taci gaba da rera kuka mai tab'a Zuciya.





Rarrashinta su Baffa sukayi tare da mata alkawrin Insha Allah gobe zasu tafi,da wad'annan maganganun suka samu suka Shawo kanta.....✍🏻






*Sadeey ce✍️**LAULAM*
( _Kishiyata_)



*Alk'alamin Sadeey ce✍️*




««•–––––––––––––––––•»»
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

•««–––––––––––––––––»»•





*Page 47&48*



*Washe gari*

_______Tunda safe suka shirya suka tafi, don yadda Dije ta kwana tana kukan nan kam babu yadda zasu jinkirta wannan Tafiya.



Da isarsu cikin MARU basu zarce ko inaba sai gidan Malam Umaru (Bappah).





Daga bakin kofar gidan suka kalli dandazon mutane wad'anda suka cika gidan sakamakon Ihu da kururuwan da da Inna keyi, don ko hanyar bi babu, domin mutane har akan katangun gidan wassu ke zaune.


Da k'yar suka samu hanya, suka shiga cikin gidan,


Da zuwansu bakin K’ofar duk birki suka ja suka tsaya, suna kallon Bappah daya zauna ya had'a kai da gwuiwa, abun duniya duk ya masa yawa.


Kaman ance ya d'aga kansa haka kuma yabi abunda Zuciyarsa ga bugata.

Sai dai idanunsa basu fad'a akan kowa ba, sai akan Ummy'n Hajar wacce tsaye tana sanye cikin atamfah Holland blue mai rashin fari.





Ba shiri ya mik'e, ya d'aga Hannu yana nunata da yasta, cikin rawan murya ya ce "Khadijah! dama kina raye? Ina kika shiga kika manta dani haka? ko dai kema abunda ya faru dani ne ya faru dake, ya k'arasa maganar yana isa gabanta batare da ya lura da dasu Goggo ba, ya kama hannunta ya ruk'e.




Hawaye ita ma Ummy take kaman an bud'e tap ganin yadda shima yake zubar da hawaye, don sai gani take tamkar a yanzu abun ya faru, cikin muryanta daya gama dishewa tace "



"Ya Sanda ina raye ban mutu ba, ina nan da raina, amma yaya meke damunka naga ja rame kayi baki? kuma ina J..... sai kuma tayi shuru tamkar wacce ta tuna wani abu.





Murmushi yayi don ya gane me take nufi, baki ya bude da niyyan zai yi magana yaji sallama a bakin kofa, juyawa yayi don ganin su waye,





Sai dai idanunsa suka fad'a akan Abba, Mamy,
Imraan, sannan Ilhaam wacce take tsaye a yayin da ta kurawa bayan wata mace dake tsaye ta bawa K'ofar shigowa baya.




Bugun Zuciyarta taji ya k'aru, lokacin da idanun ta suka sauka akan bayanta dake lullube cikin farin Hijaab wanda ya kai mata k'asa da gwuiwa kad'an.




Yanayin tsayuwanta ne ya bata mamaki ganin komai irin nata ne, dunduniyanta, yanayin tsayuwarta tamkar nata ne, tunanin ta ne ya katse lokacin da Bappah ya gama yiwa su Abba sannu da zuwa.


Kana ya matso gabanta cikin sanyin murya ya kira sunanta tare da kama hannunta.



Bao sake hannunta ba, sai daya kawota gabanta,


Kallonta ta farayi daga fararen kafafunta masu d'auke da dogayen yatsu, wad'anda ke d'auke da fareren Faracu, wad'anda ba alamun jan lalle a tattare dasu.



Daga nan idanunta suka fad'a akan farar fuskarta, wacce ke tsananin kama da nata kaman an tsaga k'ara, sai dai fuskarta ta nuna mata zallan kuruciya, duk da itama matar ba wani girman azo a gani fuskarta ke nunawa tana dashi ba.




Sai dai kallo d'aya za ka yi fuskarta zaka san ita d'in ba Yarinya bace.



Tsigar jikinta taji yana tashi a yayin da taji jinin jikinta yana tsinkewa, idanunta taji suna tsatstsafo da wani abu kaman hawaye, sai dai ba hawayen bane.



Wani abu ta ke ji yana tasowa daga cikin Zuciyarta yana watsuwa cikin naman jikinta, daya haddasawa naman jikinta rawa, sai dai ba za ta iya fassara menene wannan abun ba,


nan da nan taji rauninta ya bayyana a fili, cikin rawan da naman jikinta ya ke yi ta.....✍️






*Sadeey ce✍️**LAULAM*
( _Kishiyata_)



*Alk'alamin Sadeey ce✍️*




««•–––––––––––––––––•»»
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

•««–––––––––––––––––»»•





*Page 49&50*


____Fad'awa jikinta tayi cikin wani irin sanyin jiki, nan da nan taji rauninta ya k'ara bayyana a fili, take hawaye suka wanke mata Fuska.




Cikin muryan kuka tace " tunda na tashi bansan wacece ni ba, bansan wacece mahaifiyata ba, haka kuma babu wanda ya bani fuskar da zan Tambayeshi.



"Sai dai jikina da kuma Zuciyata sunsa naji ked'in mai daraja ce a wajena, tamkar wata tsoka mafi daraja dake cikin jikina.




"Inaji a jikina tamkar ke d'in mahaifiyata ce,



Dan Allah karki kice mun ba haka bane, ta k'arasa maganar tana k'ara shigewa jikinta.




Ummy wacce tunda Ilhaam ta tsaya a gabanta tayi mata kallo d'aya ta gane itace `Yarta idanunta ke ta zubar da hawaye, cikin muryanta wanda ke tsananin kama da na Ilhaam d'in tace




" JININA dake cikin jikinki bazai bar na kasa ganeki ba, ked'in `Yata ce, wacce na bari tun bayan haihuwarta da sati d'aya, ked'in `Yata ce! ked'in `Yata ce.
ta k'arasa maganar tana saka hannayenta ta k'ara kankameta,



Ba k'aramin tausayi suka bawa su Baba da Abba ba, don mamy, Hajar da kuma Goggo tuni ruwan hawaye ya wanke musu fuskokin.




Bappah ma jikinsa yayi mugun sanyi, a yayin da hawayen idanunsa suka k'ara gudu.




Ilhaam ce ta d'an raba kanta da kirjin Ummy'n kana tace



"Indai har haka ne, to amma meyasa kika gujeni? Meyasa kika wofantar dani? meyasa kika tafi kika barni wajen mahaifin da baya sona? a lokaci d'aya jera mata wad'annan tambayoyi.



Numfashi ta sauke, domin idan har ba zama sukayi ba, babu yadda za'ayi ta iya fad'a mata komai.




Abba ne ganin abun bana kare bane, yace " Mamana kiyi hakuri mana mu zauna,



Murmushi tayi cikin yanayin rashin karfin jikin da kuma tsamin da taji wassu wurare a jikinta sunayi ya tuna mata abunda ya faru.





Manya-manyan Taburmai aka shumfud'a guda biyu a karkashin bishiyar dake cikin Gidan.



Bayan gaisuwar daya wanzu a tsakanunsu ne, Bappah ya kalli Ummy kana yace



"To bissmilahi Khadijah, bi bawa BINGEL labarin rayuwarki da nawa.




Numfashi Ummy ta sauk'e kana tace



"*Wace ce ILHAAM*




"Sunana Khadijah sai dai iyayena dama yan gari suna kirana da Dije,


"Sunan mahaifina Muhammad sani bello, mahaifiyata kuma Maryam, ni kad'ai iyayena suka haifa, bani da wa, bani da k'ani.



"Mahaifina cikekken bafulatani ne, wanda bayi da sana'ar data wuce noma da kiwo.



"Mahaifina ba talaka bane, sai dai yana K'udin da za'a iya ce masa K'udin K'auye, wato K'udin da ba'a ci kenan.



"Duk da ni kad'ai iyayena suka haifa, sai dai hakan bai hanasu min kekkyawar tarbiya ba, haka kuma ina zuwa islamiyyan Allo, sannan kuma kaina yana gane karatu sosai.




"Ni a lokacin banfi shekara goma da haihuwa ba, mahaifina yana matukar sona kasan cewar ni kad'ai ya haifa, a yayin da mahaifiyata kuma take 6oye son da take min kasan cewata `Yar fari a wajenta, don ko sunana bata kira.




"Wata rana bayan mahaifina ya dawo sallah'n asuba lokacin ma har gari yayi haske, ya shigo da wassu mutane guda biyu mace da namji, daga gani dai mata da miji ne.



"Ni dai ina zaune gefen Ummana, haka kuma daga gaisuwa babu abunda ya sake shiga tsakanina dasu,



"Bayan sun gaisa da Ummana shine namijin yake ce mata da ita da Baba, su bakine acikin garin, nan haka kuma basu da kowa daga shi sai ita, basu da iyaye, sai dangi danginsa.



"Yanzu ma sun gudo ne saboda gadon da za'a raba bayan rasuwar iyayensa, sai dai kuma rikici ya ya 6arke tsakaninsa da yan uwan babansa, akan gadon.




"Wanda har ya kai yakai suna neman kasheshi shi da matarsa mai suna Hauwa'u (Kulu), don haka ya yenke hukuncin guduwa ya bar musu dukiyar baki d'aya




"Babana da Ummana sun matukar tausaya masa, inda Babana ya tabbatar masa daya kwantar da hankalin sa, insha Allah zasu zauna tare ba tare wani takura ba.


"Godiya yake ta yiwa Babana shida Matarsa, tamkar zasu masa sujjada.



Babana bai samu matsala daga Ummana ba, kasan cewarta mai biyayya, akan abunda mijinta
yace ko da bataso.



"An bawa Ya Umar shi da matarsa acikin d'aya daga cikin dakunan dake cikin Gidan nanmun, inda sukaci gaba da zama.



"Ya Umaru ya zama D'a ko nace k'ani, domin duk abunda ya zama babanmu ne keyi to a yanzu shi yakeyi, hatta kiwon Dabbobin Banana ya dawo hannunsa.
Idan lokacin Noma ne kuma sai suyi tare, haka ma Matarsa ita takeyiwa Ummana ayyukan cikin gida.


"Munajin dad'in zama dasu, matarsa tana da kirki sosai, domin kaman kanwarta haka ta d'aukeni, kullum ina karkashinta.




Haka rayuwar gidanmu yaci gaba da tafiya cikin farinciki da annashuwa....







*Sadeey ce✍️**LAULAM*
( _Kishiyata_)




*Alk'alamin Sadeey ce✍️*



*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*





*Page 51&52*



____"Adda (Kulu matar Ya Umaru) bata tab'a nunamin wani hali ba, hakan yasa mukayi mummunan shak'uwa a tsakanin mu.


Muna zama munayin tad'i, kowa yana fad'awa d'an uwansa abunda yake ciki,


Banida da abokiyar shawara data wuce Adda, haka itama bata da abokiyar shawaran data wuce ni.



A zamanmu da ita na fuskanci ta tsani KISHIYA, domin kuwa daga yanayin magan-ganunta na gane tabbass bata k'aunar KISHIYA, ta tsanani KISHIYA, hakan yasa nake mugun tausayawa matar da ya Umaru zai Aura.



Ko wani d'an Adam ana rubuta masa K'addarorinsa ne, tun yana cikin Mahaifiyarsa, kaman yadda ABDULLAHI BIN MAS'OUD ya fad'a acikin Hadisi na hud'u cikin Arba'una Hadith (Annawawi collection)




*BAWO DUB’I JE-D’ID’I*
_After 7 years._




"A shekaru bakwai d'innan babu abunda ya ragu na daga cikin halayen wad'annan bayin Allah guda biyu, sai ma k'ara gaba da komai yayi, domin Alhamdulilah suna da kirki,




Hakan yasa Mahaifina bai tab'a danasanin kawosu cikin iyalinsa ba, haka kuma ya k'ara yadda dashi d'ari bisa d'ari, don ji dashi yake kaman wanda suka fito ciki d'aya ko kuma Ya Umaru D'ansa ne.





"A yanzu inada shekara goma sha bakwai da HAIHUWA, zuwa wannan lokacin kuma na girma, na zama cikekkiyar budurwa, komai nawa ya girma haka kuma na bayyana ya k'ara bayyana, na zama tamkar tauraruwa, haka kuma son kowa k'in wanda ya rasa.



"Ni farace , irin fari mai cike surke da jaja-jaja, sannan ina da madaidaicin tsayi, haka kuma a bangaren jiki, ni ba mai k'iba bace, haka kuma ba siririya bace, inada bakin gashi na asalin Fulanin usul, wanda yake sauka har gadon bayana, nidai a tak'aice bana sahun munana haka kuma bana sahun kyawawa, kaman dai ke haka nake a wancan lokacin, Ummy ta k'arasa maganar tana kallon ILHAAM, wacce ta tsura mata ido ko k'iftawa batayi.



"Hawayen idonta ya share kana taci gaba da cewa



"Zuwa wannan lokacin kuma na sauk'e haka ma na gama littatafai kusan hud'u wad'anda suka shafi Addini,
don har ma ina koyarwa wassu yara karatu a Makarantar dana sauk'e.




*Key*


"Ana cikin haka Mahaifina ya kwanta rashin lafiya, wanda zan iya cewa na ajalali ne, ciwo ya kwanta wanda ya daukeshi kusan wata shida bai tashi ba yana fama da jinya.



"Mahaifina yaji tsoro karya tafi ya barni cikin `Yan uwan da ba sonsa suke tsakani da Allah ba, ballen tana su so abunda ya haifa, kar kuma hakan yasa rayuwata ta tagayyara.



"Hakan yasa yayi shawara da Mahaifiyata, haka kuma ta bashi goyon baya d'ari bisa d'ari, a nan sukayi magana da Ya Umaru, a yayin da ni kuma bansan me suka tattaunawa ba.




"Acikin jumma'ar satin aka d'aura aurena da Ya Umaru, ba k'aramin tashi hankali na yayi ba, domin kuwa nasan dawa zanyi kishi, ni nake zaune da ita, ni kad'ai na kuma nasan irin alkaba'in da take ik'irarin yiwa duk macen data kuskura ta shigo gidanta da sunan ta Auri Mijinta.




"Beside idan na duba irin zaman da nakeyi da ita, na d'auketa tamkar Addata haka kuma itama ta d'auke tamkar kanwarta,ina ganin kaman cin amana ne Auren mijinta.




"Masu iya magana sukace wai sanin hali yafi sanin kama, Ya Umaru yaji tsoron fad'a ma Adda, domin yasan halin kayansa, yasan yadda take da bak'in kishi.


"Sai dai yayi mugun mamaki bayan fad'a mata, ganin ko d'aga hankali batayi ba, don shi kad'ai yasan abunda yake tunani.



"Sai dai ya godewa Allah daya tak'aita abun, don wallahi yasan halin Adda sai a hankali.



"A D'akin dake gefen na Adda na tare, bayan anyi min jeren kayan D'aki.



"Zama na da Adda babu wani abu, haka kuma bata nuna min komai ba, hakan yasa naji kaso sittin cikin d'ari na damuwar da nake ciki ya tafi, sai dai na rasa dalilin dayasa har wannan lokacin bana jin hankali a kwance, inajin wani irin tashin hankali daga chan k'asan Zuciyata, wanda kuma na rasa mene.



"Haka mukaci gaba da zama kaman da, babu wani sauyi, a tsakanina da Ya Umaru kuwa, babu abunda ya tab'a shiga tsakanina da Ya Umaru na auratayya.



"Ummana ta bawa Adda hakuri, tare da k'ara janta jiki, don tana ganin kaman ba'a kyauta mata ba, saboda anzo gab'a ne na KISHIYA.....






#share

*Sadeey ce✍️*LAULAM*
( _Kishiyata_)





*Alk'alamin Sadeey ce✍️*




*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

••••••••••••••••••••••••

``` TSAWON SHEKARU TAKWAS KENAN BA TARE DA KE BA, ALLAH YA JIKANKI YA GAFARTA MIKI, YASA MUTUWA TA ZAMA HUTU A GAREKI, YASA HASKE DA NI'IMA A GABARINKI, ALLAH YASA KYAWAWAN AYYUKANKI SU BIKI. INA KEWARKI MAMANA😭😭😭😭😭 ```
••••••••••••••••••••••



*Page 53&54*



________"Haka rayuwar gidanmu yaci gaba da tafiya,


Mahaifina yana jinya har wannan lokacin, bai samu sauk'i ba,



"A zamana da Adda kuma babu abunda ya chanja, bata fasa min abunda takemin ba, haka kuma bata chanja min fuska ba,



"A zamana da ya Umar kuma babu abunda yaci gaba, don ko kallo ban isheshi ba, muddin Adda na gida.



"Bayan aurena da wata shida Allah ya karb'i ran mahaifina, bayan dogon jinyar d'aya sha.


"Bayan Ummana ta fita a takaba rayuwar gidan yaci gaba da tafiya kaman ko yaushe, sai dai sanyin da gidan yayi.



"Bayan rasuwar Mahaifina da shekara biyu Allah yayiwa Ummana rasuwa, naji mutuwarta fiye da tunanin mai karatu,



"Sai dai ba yadda na iya domin Allah'n daya bani ita shi ya karbeta.




Malam Liman ya bawa Ya Umaru amanar dukiyata, dake hannunshi, inda ya tabbatar masa Insha Allah zai rik'e.








•••• *MAFARI* ••••



"Rasuwar Mahaifiyata shine Makullin d'aya bud'e *K'ADDARAN AURENA* daga wannan ranar komai nawa ya changer, d'an farinciki da nakeyi tuni ya nemi hanyarsa.




"Adda tayi mugun chanjawa, ta canja ta zama tamkar ba ita ba, ta zama tamkar dodo awajena.



"Gashi tazo ta tsiri wani irin yawo mara dalili, tunda ta samu wata K'awarta mai suna Mairo, babu ranar da bata fita, kullum sai ta fita kaman taci kafar Kare, haka kuma take fita ba tare da nemi izinin Ya Umaru ba.



"Haka rayuwar gidan yayita tafiya, tuni na fige na rame nayi baki, duk da kuwa inada haske, tuni duhu ya rufeshi.



"Babu wanda yasan halin da nake ciki sai Innayi matar Malam Liman mak'obtanmu, itace kad'ai ta damu da halin da nake ciki, kuma take bani hakuri,







"Bayan rasuwar Ummana da shekara, d'aya ciki ya bayyana a jikina.


"Wanda ya haddasa tashin hankali mara misaltuwa, acikin gidan.



"Don kusan hauka Adda tayi, daga wannan ranar komai na gidan k'ara canjawa ya zama sai a slow, kullum cikin tashin hankali ake a gidan, kullum cewa take Ya Umaru ya yaudareta, yamun ciki bayan yasan ya yayi mata alk'awarin bazai tab'a kusantata ba, a yayin da shi kuma yake bata da hakuri, inda yake mai-maita kalman tayi hakuri, wai tsautsayi me, wannan kalman ta tsautsayi tayi mugun yimin ciwo.



Ni da MIJINA amma don ya kusanceni, zai cewa KISHIYATA wai tsautsayi ne, amma haka na mazge, na hadiye damuwar da bai kamata ashe a shekaruna ina fuskantansa ba.




Haka nake fama, ga laulayin ciki ga tashin hankali, tuni rayuwa tamun zafi, na rasa inda zan tsoma kaina.



******

Haka naci gaba da rainon cikina, duk da k'arancin shekaru na.



Idan Adda bata nan zai shiga har D'akina muyi hira, yayi duk abunda zai yi, sai dai tana dawowa komai yake canjawa, na lura kaman Ya Umaru yana mugun tsoron Adda, amma nasan idan ma hakanne babu yadda zanyi, sai kawai naci gaba da addu'a da kai kukana wajen Allah, Ubangiji kowa da komai.




Ni kad'ai na raini cikina har ya shiga watannin HAIHUWA'nsa, ranar da safe na tashi da nak'uda, kaman zan mutu, yayin da Adda kuma tasa kai ta tsallakeni tayi ficewarta abunta.



Nasha wahala kafin Allah ya sauk'eni lafiya, na haifi `Ya mace mai tsananin kama dani, da taimakon Innayi na gyara jikina, wacce Ya Umaru yaje ya kira don ta taimakamin.



Ko da Adda ta dawo bata bi ta kaina ba, tayi shigewarta D'aki, tana cewa ita ba ruwanta, bataci buzu ba, bazatayi aman gashi ba.



Haka naci gaba da kula da Yarinyar dana haifa, a yayin da Innayi ke shigowa cikin Gidan tana mun wankan jego da duk abunda mace mai HAIHUWA zata buk'ata, don Adda kam cewa tayi ba nata aciki.



Ranar suna Yarinya taci suna AISHA (mai sunan Ummana)
amma ni inason ayi mata inkiya, da ILHAAM don
6oye sunan, duk dama ba kiran sunan zanyi ba.




Babu wani taron da akayi, hasalima gidan babu mutane daga Innayi wacce itama ke da cikin, sai wassu tsiraru daga cikin makobta, wad'anda basufi biyar ba, dukkansu idan an had'a.



Tunda aka haifeta,Ya Umaru bai sayawa Jinjira kaya ko da k'yalle ba, ballen tana ni da nake Uwarta, da kayan da `Yan balle suka kawo shi aka saka mata.



Ranar suna da daddare ina kwance, tsurawa idanun Jiririyata ido wacce ta bude idanunta itama tarr akaina, kaman tasan me duniya ke ciki, a yayin da nake sauranro fad'uwar da gabana yakeyi, haka kuma inajin yadda Zuciyata ke tsinkewa, ji nake tamkar kallon RABUWA mukewa juna nida ita.



Kaman daga sama na nakejin kiran da Adda take k'walamin, yunkura nayi da niyyar zan tashi, sai naji Yarinyata ta saka kuka, don haka na koma na kwanta, a yayin da ita kuma tayi shuru.




Wani kiran na sake ji, na yunkura zan sake tashi, sai yanzun ma ta sake saka kuka, haka kuma nima na sake komawa tare saka mata nono a baki, aikuwa kaman jira take ta chapke ta fara shasha, kaman minti goma da kiran aka sake kwala min wani k'arfi, sai dai kuma har zuwa wannan lokacin Jaririyata batayi bacci ba, haka kuma bata sake nonon ba.




Wannan karon kam cire nonon nayi daga bakinta, ai kaman jira take ta callara kuka, ban kulata ba, duk da kuwa irin tashin hankalin da nakejin kaman yana tunkurata, mik'ewa nayi kana nayi hanyar waje ina amsa kiran da Adda take mun......✍️




Shin mezai faru idan Dije ta fita???




Share fisabillah👏👏





*Sadeey ce***LAULAM*
( _Kishiyata_)




*Alk'alamin Sadeey ce✍️*



*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*




*Page 55&56*


__________"Ji nayi kaina yayi wani irin sarawa, sannan naji jikina duk ya sake, najini cikin wani irin yanayi mara misaltuwa.



Daga haka, ban sake sanin

Please Login or Register in order to submit comment