Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta zamo sabuwa ta mata dadi ganin tsawon wannan lokacin babu abunda ya chanja, sannan kuma ga ILHAAM bata taba zuwa garin ba ko da kuwa wuni ne.




Hajiya Mama bata chanja zani ba, domin babu abunda ya chanja na daga kiyayyar da takewa ILHAAM babu abunda ya ragu aciki dai-dai da kwayan zarra.......✍️





09139216255
Sadeey ce
[7/3, 1:50 AM] Oum Juwairiyya Royal Star Writers Association: *LAULAM*
( _Kishiyata_)





*Alk’alamin Sadeey ce✍️*








*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*




*page 29&30*



_____A lokacin da ya Imraan ya dawo ina da shekara goma sha bakwai, wanda kuma muke shekara ta karshe a secondary school.




Hakan yasa Abba da Mamy, yankewa har sai bayan gama makarantar su, wato nan da shekara d'aya ke nan, a cewar su sun san halin Imraan.






*******
Zaune take acikin wani k'aton Juji wanda ko dad'in kallo bayi dashi, domin kallonsa ka d'ai idan an bar mutum dashi to lallai an had'ashi da babban aiki.




A yayin da ita kuma ke zaune ta na faman gabtaran bredi wanda har jikinshi ya fara kore, alamun ya jima da b'aci kenan.




Cikin kad'uwa da mamaki Malam Babayo da hanya ta biyo dashi wajen, Allah ya nuna masa baiwar Allahn da yake neman ta tsawon kwana da kwanaki.




Ba tare da batare da b'ata lokaci ba, ya d'auke ta su ka yi gida, don dama kullum sai ta fita neman ta, ko don jikanyarsa da take cikin damuwar rashin ganinta.




Ai kuwa ba k'aramin dadi Hajara ta ji ba, akan ganin Ummynta ta dawo, ko ba komai za ta ci gaba da walwalanta kaman kowa.




******

Kwance yake akan gadon da yake mallakin sa, jike yake charkaf da zufa saboda mafarkin daya yi a yanzu, wanda ya yi sanadiyya farkawansa ba shiri a yanzu. A fili ya ke furta.


"to ita wannan mata da `Yar me alak'ata da su?



"Tabbas ina ji a jikina tamkar na tab'a rayuwa d'aya daga cikin su ko ma dukkansu.



"Sai dai na kasa tuna hakan, to ko yeni yam?(me ya sameni?)
a duk lokacin da na yi niyyan tuna wani abu daya danganci bayana sai naji kwata-kwata k'wa-k'walwarta ta toshe baki daya,
daga karshe sai naji ciwon kai mai tsananin gaske ya kamani, hakan yake tilasta min dole barin wannan tunanin ko da kuwa Zuciyata da k'wanyata ba su so hakan ba.




"A can kas'an Zuciyata ina jin wani irin ya na yi wanda ba zan iya fassarashi ba akansu, maganan sa ne
ya katse lokacin daya tsinkayi muryan Inna tana ce wa,




"Ah lallai ba shakka, yanzu kana nan kana baccin asara, ka barmu da yunwa,




" ko ni kake tunanin zan tashi nayi ayyukan da ka san naka ne, Inna ta k'arasa maganar cikin tsawa tamkar wacce keyiwa d'anta magana.




Ba tare da yayi magana ba, ya tashi yayu waje, cikin sanyin jiki ya fara ayyukan daya san a yanzu sun dawo hannunsa duk da kuwa shine mijinta.




*****
Tsakanina da Ya Imraan babu wani abu, wanda ya danganci tausayi,kirki, ko makamancin haka, sai mugunta, da kuma hantara.




Hakan yasa naja jiki dashi, saboda ganin ban-bancin da yake nuna min akan Meemy, domin k'arara yake nunamin ni ba []ay uwarsa bace.




Tun abun na damuna har na maidashi jikina, kasan cewar ni ba irin mutanen dake d'aukan d'umi abunda ba ruwansu bane.



Dawowar ya Imaan gidan ba k'aramin takura ya haifar min ba, Banason zuwa ko inda yake sai dai Mamy ta dauramin kai duk wani abu daya kasance nasa, kaman kai masa abinci D'aki dafa masa abinci idan ya bukaci hakan.




Wannan abun ba k'aramin damuna yakeyi ba, sai babu yadda na iyya domin kuwa ba abu ne zan sashi a raina ya dameni ba.





★★★★★
Ba tare da b'ata lokaci ba Goggo matar Malam Babayo ta hada ruwan wanka tayi wannan mahaukaciyar wanka kaman yadda ta saba mata tsawon shekara da shekaru.




Aikuwa a take ta fito tayi fess tamkar ba itace cikin daud'a da dotti ba.



Kana Hajar ta d'auki abinci ta fara bata a baki har ta tabbatar ta k'oshi.



Daga haka suka saka mata matakan tsaron da ko kusa da K'ofar gidan basa bari taje, gudun kar abunda ya faru ya sake faruwa.





Haka rayuwar gidan yaci gaba da tafiya a yayin da dukkansu uku suke nuna mata soyayya tamkar ba mahaukaciya ba.






★★★★★
*Bawo Dungu go'o*
( _Bayan shekara D'aya_)




A yanzu mun kammala makarantar mu ta gaba da secondary, wanda har mun zama jarrabawar NECO da kuma WAECK sao fatan fitowar sakamako.





Bayan zana jarrabawar mu da sati d'aya,


Da daddare bayan sallan isha.



Mu hud'u ne zaune acikin palourn Abba, Abba, Mamy, Ya Imraan sannan ni, wacce kirjina babu abunda yakeyi sai lugude saboda kiran da Abba yasa aka mana.




Domin tunda nake ba'a tab'a mana wannan kiran ba, kai daga ganin yadda sukayi shuru na tabbatar wannan kiran ba alkhairi bane, ( A cewarki ba)





Gyaran muryan da Abba yayi ne ya yasa muka nutsu,



Cikin kakkausar muryan dake nuni da lallai abunda zai fad'an ba k'aramin bane yace



" Imraan, ba tare da ya jira amsawara ba, yaci gaba da cewa



"A matsayinmu na iyayenka munyi maka zab'i sanin bamu da kwakwonto akan hak'k'n daka sauk'e na mana biyayya a
amatsayinmu na iyayenka.




Numfashi yaja kana yaci gaba da cewa " Mun d'aura maka Aure da ILHAAM a lokacin da mukaje MARU don kayi sallama a Bab...



Cikin tashin hankalin daya dirar masa lokaci d'aya ta mik'e tsayinsa kana ya fara cewa "




"Chappp ai wallahi bazai yuba, don ni tsarin rayuwata babu auren dole aciki, a tsarina babu wannan, da girmana za'a min auren dole? kuma a rasa da wacce za'a had'ani sai Yarinya yar shekara goma sha takwasa, Yarinya k'aramar, []ar K'auye, sannan bagidajiy....




Abubakar!!
ta tsinkayi muryan Mamy wanda a tarihin rayuwarsa bai tab'a jin ko da Imraan a bakinta ba, ballen tana asalin sunansa, kasan cewarsa d'an fari kuma mai sunan Modibbo.

Tasss! Mamy ta wanke fuskarsa da kyawawan maruka har guda biyu, bayan ta iso gabanshi, cikin tsantsan bakin cikin da take ji ta fara ce wa



"Lallai nan, ashe har ka yi wannan rik'an ban sa ni ba? dama haka kake, ko dai daga baya ne ka aro wannan halin? Ashe har na haifi d'an da maifinsa na magana ta mike ya tsaya a kansa ya dakatar dashi.


Cikin sark'ewar murya ta ci gaba da cewa
"Saboda isa irin na ka, ka na kallon idanunmu wai mu kake gayawa wai ba za ka yi auren dole ba, sannan ba za ka Auri []ar k'auye, jahila bagidajiya ba, to bari na gaya maka wata magana.



"masu iya magana sunce a tone-tonen kaza take tono wuk'an yankanta.




Mugun kallo ta aiki ta masa kana tace

"Bari na gaya maka, aurenka dana ILHAAM tamkar Aure nane dana mahaifinka, har gwara ita akan ni Uwarka, karka manta abu guda d'aya itama auren dole aka mata.



A lokacin dana Auri mahaifinka ni Yarinya ce k'aramar tamkar ILHAAM, haka kuma baya sona bana sonsa, Auren dole akana, a lokacin dana tare a gidansa ko "A" ban iya karantawa ba, ballen tana na iya rubutashi.



"Duk da karatunsa da kuma aikinsa, haka ya yi hakuri ya zauna dani, har na haifeta sannan na shiga makarantar daka girma ka tashi ka ganni dashi.




"To wallahi tun wuri ka yayyafawa kanka dake hayak'i ruwa tun muna shaida juna, if not na rantse da Allah zaka hadu da mummunan fushi na, wanda baka tab'a gani ba!





"Mutumin banza mutumin wofi wanda bai san me duniya ke ciki ba, ta na gama fad'an haka ta yi wajen, ILHAAM wacce tunda Imraan ya fara magana ta kifa kanta take kuka, bubbuga bayanta kawai ta yi kana tayi hanyar d'akin Abba.





Kallon Imraan Abba ya yi kana ya ce ".....✍️[7/5, 8:24 PM] Oum Juwairiyya Royal Star Writers Association: *LAULAM*
( _Kishiyata_)




*Alk'alamin Sadeey ce✍️*





««•–––––––––––––––––•»»
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

•««–––––––––––––––––»»•




*Page.....31&32*


______"Tabbas ka tafka babban kuskure Babana, you really disappointed me, ban taɓa tunanin haka daga gareka ba.



"Ban haifi ILHAAM ba, amma bata mun abunda ka mun ba.


"Me ya sa ba za ka yi haƙuri da zaɓin da mu iyayenka mu ka yi maka ba?




"Yanzu dad'in me kaji da har ka b'ata ran mahaifiyarka? Kana ganin ta tafi cikin bakin ciki wanda kaine musabbabin hakan?



"Ya Subhanallah wa ce irin rayuwa ce wannan ka kawo mu, Allah mun tuba, astagfirulla, ya k'arasa maganar cikin yanayin dake nuna zallan bacin ran da yake ciki,



Kana ya kalli gefen da nake zaune cikin bakin cikin daya dirar min acikin lokaci k'ank'ani, kana ya ce;



"Mamana ki yi haƙuri da katsalandan da muka miki akan zabin da mu ka yi miki kinji ko? Ya k'arasa maganar cikin tsigar tambaya,



Cikin son tsaida kukan dake taho min tun daga cikin zuciyata na ce "Abba kar ka damu kun isa dani ne shiyasa, don Allah ka fad'an haka zan ga kaman baka isa dani ba ne, Insha Allah zan yi haƙuri da zabin da ku ka yi min, zan kuma karbeshi hannu bibbiyu.



Cikin jin dad'i ya ce "miyetti maseen Inna am, jomirawo wad'ane barka (nagode sosai Mamana Allah ya miki albarka) daga haka ya sallameni kana ta juya kan Imraan.



Fad'a sosai ya masa akan abunda ya yi da nuna masa illa abunda ya aikata, inda ya yi nadama kuma ya yi masa alk'awarin bazai sake ba, kana ya umarcesa da yaje ya bawa Mamy haƙuri ya kuma amince.



Haka Imraan ya je ya roki gafaran Mamy, akan ran daya b'ata mata, wanda kuma Alhamdulilah ta yafe masa, tare da masa dogon gargad'i akan ILHAAM.




Hakan yabsa ba tare da b'ata lokaci ba, aka sanya tarewata nan da 2 Months.





*******

Zaune take a tsakar gida, akan tabarma, kaman kullum babu magana, sai dai yanzu hawaye ne keta sintiri akan farar fuskarta, wanda ko ba'a fad'a ba, daga gani babu tambaya, na kullum ne ya motsa.




Sai dai ba su da daman tambayanta domin kuwa ba ta da bakin bada amsa kaman na kowa.




Don haka suka zuba mata na mujiya, domin babu yadda su ka iya, duk da ba wannan ne ka d'ai ba ne take irin haka, a bune wanda ya kwana biyu don su kam gani suke kaman normal ne, domin kuwa ya na neman zama jiki a garesu.




A ya yin da Hajar ta kasa sabawa da wannan yanayi nata, domin idan ta na kuka ita ma zama take gabanta ta na tayata.



Hakan ke sa yanayin gidan ke canjawa, domin kuwa gidan zai zama tamkar gidan mutuwa, babu mai wal-wala haka kuma babu mai kula d'an Uwansa.




A ya yin da ita kuma take zaman kuka, zaman kunci, ba ta ci, ba ta sha, sannan kuma ba ta walwala.....✍️


09139216255
Sadeey ce
[7/6, 10:06 PM] Oum Juwairiyya Royal Star Writers Association: *LAULAM*
( _Kishiyata_)




*Alk'alamin Sadeey ce✍️*





««•–––––––––––––––––•»»
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

•««–––––––––––––––––»»•




*Page....31&31*


____Wannan ita ce rayuwar da mahaukaciyar gidan Malam Babayo ke ciki, dama mutanen gidan baki d'aya.




Ita d'in dai *TSINTACCIYAR* *MAHAUKACIYA* ce, sai dai basayi mata wannan kallon, don kowa da yadda ta d'auke ta. domin kuwa Hajar ta d'auke ta tamkar mahaifiyarta, haka ma Malam Babayo ya d'auke ta tamkar kanwarsa daya fito ciki d'aya da ita, a ya yin da Goggo ta d'auke ta tamkar yar Uwa.




Tunda tazo gidan bata tab'a magana ba, ballen tana wani abu makamcin haka.



Rayuwarta ta ke yi tamkar ba mahaukaciya ba, bata buge-buge, bata duka sannan bata tsince-tsince.



Sai dai ta na da matsala k'waya d'aya, matsalar itace bata juyawa baya, muddin tasa kanta a tafiya to lallai sai an juyata.



Wannan dalilin yasa idan ta fita dawowar ta ke da matukar wahala, domin bata iya juyawa ba.




★★★★★

Ya Imraan ba yadda ya iya akan wannan bikin, domin kuwa yaga idan har ya nuna bayason wannan auren to tamkar yana gayyatowa kansa fushin Mamy ne, abunda baya kauna kenan a rayuwarsa, hakan yasa yaja linzamin bakinsa ya yi shuru, domin ance fad'an da yafi karfinka, sai ka maidashi wasa.




Mamy da kanta ta yi ordern kayan Aurena daga *ABMAR COLLECTION* wajen Oum Juwairiyyah, ta had'a mata komai da komai na kayan aure, kaman yadda ta buk'ata saboda sanin ingancin kayan.




Domin kuwa *ABMAR COLLECTION*, ba baya ba, wajen siyar da kayan da mata zasu bukata, wanda zasuyi Ado dashi don kece raini, da kuma anfanin yau da kullum wanda ko wace mace zata bukata a rayuwarta na yau da kullum.




Akwatuna 12 aka had'a, ko wanne na shake da kayan alfarman na gani na fad'a,


A kwana a tashi ba wuya a wajen Allah Subhanahi wata ala,
Yau har an shiga satin biki, domin kuwa yau Wednesday, hakan kuma yasa har bakin kusa sun fara zuwa.




Saboda gyara mai kyawun da nake samu,tuni fatata ta murje ta yi laushi tare da kyau, na k'ara kyau, sai d'an raman da nayi wanda ya kara fito mini da ainihin kyawuna na cikekkiyar bafulatana.




Washegari Thursday, gida ya cika makil da jama'a, domin babu wanda bai zo ba.



Domin kuwa hatta yan Cairo sun iso, don daga Waleed har Ahmad su ne abokanan ango, duk da babu sa'an IMRAAN a cikinsu, Waleed sa'an Faisal ne, a ya yin da Ahmad kuma ya girmi IMRAAN, sai dai idan ba sani ka yi ba ba za ka tab'a gane hakan ba.




A can na hango Mamy Uwar ango da amarya, taci adonta cikin lace din ta mai masifar tsada da d'aukan hankali, wuyanta da hannayenta sun sha danyen gold wanda kallo d'aya zaka masa kasan ba k'aramin tsada gareshi ba, sai kai wa da komowa take, don ganin komai ya daidata,


HAJIYA Mama kuwa, wuri ta samu ta shantake abunta, don a cewarta ba za ta wahala a bikin wad'an da basa sonta ba.




Ranar Thursday su ILHAAM su ka yi bridal shower, in da amarya ta yi wankanta cikin farin gown mai masigar kyau ga make-up d'in daya k'ara fito da ainihin kyanta, su kuma kawaye sunyi ango cikin bakin tummy skert da red d'in riga, cikin ikon Allah su ka yi taronsu suka watse lami lafiya.



Ranar Friday bayan an sauk'o daga sallan juma'a abokanan ango su ka yi shiri don tafiya reception.



Bayan Salla, suka d'ugunzuma su ka yi *Madugu hotel* don gudanar da reception.




Ango IMRAAN wanda dana k'yallara idona na ganshi sai da yawun bakina ya kafe.


Sanye yake cikin farin yadinsa na gazner wanda ya samu aiki da bakin surfani,takalman kafansa cover shoe, suma bakakene sai hulan kansa shima baki, wanda ba k'aramin kyau ya yi ba, dole ya amsa sunansa na ANGO,



Kasancewar sai sun je gida an yi hotuna tukunna kafin su wuce yasa su na gama shiri sukayi nufi *Shongo Housing Estate* wato gidansu IMRAAN ke nan, don daukan pictures da amarya da dangi, bisa umarnin Mamy,




*ILHAAM*
Sanye nake cikin farin less mai Gold d'in flowers, wanda Mamy ta yi min orden shi a wajen ABMAR COLLECTION, Sai Sark'an wuyana daya kasance gold mai fad'i, wanda ya zubu a akan kirjina hakan ya k'arawa suran fito da ainihin kyawuna da babu algus aciki, sai Takalman dake kafana, masu uban tsini da d'an karamin Jaka, da ke hannuna kiran kamfanin *Vine* suma bakake.


'Dauri aka daura mata mai masifan kyau akan gashin kanta daya sha gyara sai sheki yake, wanda aka mayar mata ta jelan gashin baya, sannan ga make-up dinta mai shegen kyau wanda ya kara fito da kyan fuskan wanda *Beauty and beyond* ta yi mata, jell din da aka saka mata a gaban gashi ya ya sanya dole aka jaa d'an k'walin ta baya kasancewar ana son ya fito shi ya k'arawa daurin d'an kwalin kyau, hannayenta sunsha Baki da jan lalle a yayin kafafunta suka samu jaā kadai, wanda *IDAYA SPA ND HENNA* su ka yi mata.



Shigowar su IMRAAN ya yi dai-dai da gamawarsu ILHAAM, sai dai ILHAAM taki fitowa, don tace sai dai su kwana a wurin don babu inda zata ,yan dakin duk sunyi-sunyi amma ILHAAM ta kyenkyashe ido tace bata san zancen ba, ka san cewar babu manya a d'akin sai kayawensu kawai, su kuma suna ganin haka
suka maida abun na dariya da tsokana kasan cewar basu san dawar garin ba, cikin kawayen sunne wata mai suna Asmah ta ce




"Haba ILHAAM mene abun munafurshi har ce wa ba za ki ba, kawai ki tashi muje, ba wani kora kunya da haukan da zaki mana,



Ihuuu duk yan D'akin suka sa tare da shewa,



Ita dai in banda ta fasa babu abunda zuciyar ta ke yi, tun safe ta ke kuka, don ta ga karta kashe kanta ne akan mutumin da baisan tanayi ba, yasata ce wa ba za ta sake kuka ba.



Meemy ce ta fita daga take ta gayawa Mamy.





Da lallabi Mamy ta samu ta shawo kan ILHAAM wacece har idanunta sun changer colour.




IMRAAN banda tsaki babu abunda yake yaja, a ransa yake ce wa "lallai dole nayi maganin yarinyar nan har kaman ni zata Shanya kaman wani bawanta




Fitowar ta ne ya katse masa tunaninsa, kallo ya fara k'are mata daga bakin hill shoe d'in dake kafanta har zuwa saman kanta, sannan ya sauk'e numfashi tare da fara tasbihi a ransa yana mai kara kallon fuskanta tare da mamakin irin kyan da yaga tayi mass na musamman wanda bai tab'a gani ba, nan da nan yaji bacin rai wand baisan dalilinsa koda ina ya ke ba.



D'aya daga cikin abokanansa mai suna kamal ne ya katse masa tunani ta hanyar ce wa

"gaskiya abokina ka iya zabe, irin wannan kekkyawar budurwa haka? Shi ne don munafurshi kake ta abu kaman miskiniya ka aura? ya k'arasa maganar ya na dariyar shakiyanci sauran abokan suna tayavshi, domin vme ya ce ba, sautin dariyan kawai su ka ji,
Shidai IMRAAN shuru ya yi,

kamshin turarenta ne ya sanar dashi isowarta, juyawa ya yi yana
kallon fuskarta ganin yadda ta tsume tamkar bata tab'a dariya ba, kana I know I do ya sunkuyo da kansa, in bakinsa ya kawo dai-dai kunneta kana ya ce.... ...





09139216255
Sadeey ce
[7/7, 10:45 AM] Oum Juwairiyya Royal Star Writers Association: *LAULAM*
( _Kishiyata_)




*Alk'alamin Sadeey ce✍️*





««•–––––––––––––––––•»»
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

•««–––––––––––––––––»»•




*Page....33&34*


"Wato har wannan ɗan gashin zaki fitar waje ko? ke gaki mai gashi ko? "to wallahi idan ki ka kuskura na sake ganin wannan gashin a waje sai na saka razor na yankeshi, ya kasara magana ya na haɗe fuska tamkar ba shi ya yi maganar ba.



A time d'in da ya kai bakinsa dai-dai kunnenta ne ya bawa mai ɗaukan Photon daman ɗauka, domin ba ƙaramin kyau su ka yi ba, hasalima kama su ka yi da masoyan asali.



Bayan an gama ɗaukan pictures a loakcin har 3 ta yi kasan cewar ba'a fara ɗaukan picture ɗin da wuri ba yasa ba'a gama da wuri ba.



Ahmad ne ya ja IMRAAN gefe cikin muryan kasa- kasa ya ce "abokina nifa naga iri acikin ƙawayen amaryan nan, don haka na kama kafarka,



cikin dariya Imraan ya ce "haba dai Daddyna (dama haka ya ke gaya masa kasan cewar sa mai sunan mahaifinsa) wacce daya,

da yatsa ya nu na wacce ya gani,

murmushi IMRAAN ya yi ganin Meemy ya nuna, cikin zolaya ya ce "gaskiya Daddy daga yau ni ne babban Yaya, cikin rashin fahimta Ahmad ya ce "meya faru?"

cikin dariyan zolaya IMRAAN ya ce "sister na ne, ya karasa maganar cikin kosawa da maganan, don ba karamin gajiya
ya yi ba,


"whattt!!! you mean ita ce Meemy?
"yes of course"



Ƙafada Ahmed ya daga sannan ya ce "koma me ne dole ka min hanya, ya karasa magana cikin tsare gida irin gashi babban nan ai IMRAAN bai san sanda ya fara dariya, tare da ce wa
" ba damuwa"


Suna gamawa suka nufi MH wato *MADUGU HOTEL* ke nan don gudanar da reception wanda zai daukesu tsawon 1hrs za su fara 3:pm su gama :pm ke nan i nda su ILHAAM za su yi nasu 3-4 ke nan.



4pm dai-dai muka gama shirin mu ita da ƙawayenta sanye take cikin yadi omo blue and dark blue in da ya yi masifar kyau ba kadan ba,

ƙawaye kuma su Meemy ke nan sanye suke cikin blue black din gown sai black head sun yi kyau Masha Allah,


ƙawayensu dukannisu sun ta fi kasancewar lokaci ya fara tafiya, Meemy ka dai ta rage wacce IMRAAN ya hana ta tafiya (domin sun hada plan da Ahmed akan ya na so ya kebe da Meemy)

sai 4:30 kafin a sanar wa su ILHAAM ce wa ya zo, fita su ka yi cikin takunsu na cikakkkun yan mata kuma *`Yan Jami'a* masu ji da kansu da taken kuruciya, Hill da su ka sanya shiya kara changer musu salon tafiya, sai kiga tamkar yanga su ke yi, sai dai abun ba haka ya ke ba.


ganin motoci biyu ne a wurin yasa su ka yi hanyar motar da suke tunani ita ce ta ya IMRAAN, sit ɗin baya suka bude, ganin IMRAAN a hakimce ya sanya Meemy ce wa

"Ya IMRAAN ina zan shiga?"

da hannu ya mata nuni da wata bakar mota wacce suka wuce,


ILHAAM dai ganin Meemy ta bude sit din baya ya sata shiga abunta ta zauna ko ci kanka ba ta ce masa ba sai dai da idonta ya fad'a a kansa da kyar ta iya janyewa, sanye yake cikin blue din shadda shi ma wanda aka masa aiki da dark blue din saurfani hulan kansa dark blue ne, haka ma takalmin kafansa daya kasance dark black, sai ROLEX din agogonsa mai shegen kyau ita dai ta san ya yi mugun kyau amma sai ta basar kaman bata ma gan shi da kaya ba, haka shi ma IMRAAN kallo ya kare mata, ganin yadda Colours d'in suka karb'i jikinta, ya na mai kara jinjina irin wannan kyawun da ya san ta yi, kasan cewar abokin su IMRAAN Alee shi ne mai driving yasa ya yi shuru domin sun tsara motan Ahmad ita ce a gaba.





A ɓagaren Meemy kuwa
bata sake magana ba ta yi wajen mortar tare da tunanin waye ne.



Ƙofan gaba ta bud'e gefen driver, wato sit d'in mai zaman banza, zama ta yi ba tare da ta juya taga ko waye ba ne, reverse ya yi ba tare da ya yi magana ba shi ma, ya kama hanyar
TH wato *GOMBE INTERNATIONAL HOTEL*



ganin bata da niyyar magana cikin zolaya ya ce


"Ranki shi dade barka da yamma,



Gabanta ne ya bada sautin rass, ba shiri ta juyo ganin bata san shi ba ne ya sata ce wa



"Ka na ta gaisheshi cikin girmamawa, amsawa ya yi cikin sakin fuska, daga haka suka fara hira.


nan ya fa ra introducing kansa ganin bata ganeshi ba, ( Meemy ba ta san su Ahmad ba kasan cewar tunda aka haifeta ba su sake zuwa ba sai wannan bikin).



Hancin motan Ahmad ne ya fara shiga cikin harabar Makarantar kafin ya samu gefe ya yi parking sannan Alee ma ya zo ya yi parking.


Meemy ce ta fito da Ahmad ta na d'auke da sihirtaccen murmushi akan kyakkyawar fuskarta,




IMRAAN ne ya fara fitowa kafin ILHAAM wacce ganin idon jama'a ya sa ta jin wani irin, hannuta daya kama ne ya dawo da ita daga dogon tunanin data tafi, jin tattausan hannunsa a cikin hannunta, jerawa su ka yi a tare suna tafiya cikin nutsuwa a ya yin da kawaye su ka yi layi guda biyu ta gefen ango dana amarya suka saka su a tsakiya, inda hakan ya ƙara kawatar da mai kallo, hanyar Hall d'in suka nufa sai da su ka zo bakin Hall d'in suka tsaya bisa umarnin MC, red an white

Please Login or Register in order to submit comment