Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

inda kaina yake ba, sai budan ido nayi na ganni a gidan mutanen da ban sansu ba, dana tambayesu inda nake, suka tabbar min da a JOS nake, nayi mugun mamaki sosai.



Domin ni nasan kafata bata tab'a taka JOS ba, haka kuma ina mamakin waye kawoni nan, hasalima ji nake kaman bacci na tashi.



Sai dai bansan wai har shekarun sunja sosai ba, sai naji hankalina ya kasa kwanciya, idan har na tuna jaririyata na wajen Adda, don nasan bakar izaya zata gana mata.



Ummy ta k'are maganar tana kallonsu dukkansu da idanunta da sukayi da ja suka kumbura, saboda kukan da tayi.




Dukkansu hawaye ne, suke ta zuba daga cikin idanunsu, don ji suke tamkar a gabansu akeyi komai, a yayin da Ummy, Bappah suke ganin tamkar yau ne abun ya faru, musamman idan ya k'arewa cikin Gidan kallo, domin komai aciki akayi.




Daga haka Bappah ne ya bata labarin abunda ya faru dashi bayan tafiyannta, kana ya kare da cewa "Dije na rasa meyasa hakan ua faru, na manta Yarinyar dana haifa, bana tunata ko kad'an, idan na kalleta sai naji wani irin 6acin rai ya cika min Zuciya, shiyasa tun tashinta magana ta fatar baki bata tab'a had'ani da itama
ba.



Ummy dama mutanen dake zaune babu abunda suke sai jinjina kai kawai.



ILHAAM ma ta zauna ta zayyana musu halin data shiga ciki, da irin zaman wahalan data fuskanta. agidan, kaman zata mutu.




Na k'aramin tausaya mata sukayi ba, IMRAAN kuwa kafeta yayi da ido, yana jin wani abu yana bin dukkan sassan jikinshi, wanda bazai iya fassara wannan abun ba.







Bappah kuwa Zainabu, (`Yar Inna yake kallo), gand'a reriyar budurwa amma ba Aure, a yayin da yake tuna yadda
yadda ta tashi, ido a tsefe, bata ragarwa kowa, ga rashin kunya ga rashin gaskiya, taci mutuncinka kayi magana, Uwarta ta tashi ta wanke mutum, ta maka rashin mutunci kaman an aikota daga sama.



Haka Zainabu ta tashi, rayuwarta abun tausayi ne, domin kuwa bata da abunda zatayi tinkaho dashi, bata da abunda zata bugi kirji tace anyi mata shi daga gidansu.


Ba komai bane wannan abun face *TARBIYA* batada wadataccen tarbiya kwata-kwata ba'a mata ba.


Haka ta tashi tamkar akuyar da bata da mai ita, kuma a hakan wai tana da Uwa. (Ko muna Uwa ba.)



Tabbas samun Uwa tagari, ba k'aramin arziki ba, (Ya Allah, Allah ka azurtamu da iyaye na gari.)



Sai dai ga yadda ta nutsu, tana sauraron duk abunda ake fad'a akan Mahaifiyarta.



Ga yadda ta raku6e a waje d'aya, idanunta sunata zubar da k'walla.



Dama ance *Bone Baba hakkilo* (Wahala uban hankali).





Inna kuwa wassu k'atti aka samo a waje suka fito da ita daga D'akin, aka ajiyeta, kana aka saka igiyan shanu aka had'ata da jikin Bishiyan dake tsakar gidan aka d'aura gam, yadda bazata kunce ba.




Bappah ne ya kalleta, kafin yace "tabbas nayi nadaman aurenki, Aurenki fitina ne, Allah yana gani Aurena dake *AUREN TAIMAKO* ne, jihadi nayi na Aureki, sai yau nayi nadaman Auren wacce ba'a san asalinta ba.


"Tabbas nayi babban kuskure wajen Auren ki,



"Da `Yar dangi da asalin da Aura, da inaga duk hakan bai faruba, amma ba komai kije da Allah, bazan tab'a yafe miki ba.




Dariya ta k'yal-lyale dashi, cikin yanayi na galabaita tace".....✍️







*Sadeey ce**LAULAM*
( _Kishiyata_)




*Alk'alamin Sadeey ce✍️*



*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*




*Page 57&58*


________"Ba Dije bace, tuni bokana yace bazata sake dawowa ba, ya tabbatar min da hauka zata mutu, don haukan daya had'ata dashi, na mutu ka raba ne.



"Meyasa zai mun haka? yamun karya kenan? "A'a, ai nasan bazai mun karyaba ba, saboda aikinsa sadidan ne. (Hajiya Inna kin kama kumfa)




Cikin yanayin nutsuwa, tamkar ba ita ta gama fiffige gashin jikinta yanzu ba, kana ta kalli
Ummy kafin tace



" Bafulatanar banza da wofi, wato kin rantse, sai kin zauna da Umaru ko? bayan na gaya miki shi d'in nawa ne, ni kad'ai. Ta ida maganar cikin wani yanayin da babu wanda ya iya fassara shi.



Kallonta ta mayar kana Zainabu, cikin rawan, muryan da sukayi mamakin jin tanayi dashi, kana tace



"Kiyi hak'uri Abullena, ki daina kuka, nasan Babanki zaizo ya d'aukeki, bazakici gaba da zaman gidannan ba, zaizo ta d'aukeki, gidansa yafi wannan kuma yana K'udin.



Ba shiri Zainabu ta d'aga kanta, kana tace " Inna? Babana kuma? dama ba Bappah bane ya haifene? to waye ne Baban nawan? ta kare maganar cikin yanayin firgici.



Kallonta tayi, cikin yanayi na karayar zuciya tace " tabbas idan da gaskiya to Bappah'n ILHAAM ba mahaifinki bane!



Daram! Dammm, zukatansu suka sauti.



"Me! Bappah da Zainabu suka had'a baki wajen tambayar Inna.




Karon farko da taji nadama da danasanin abubuwan da take aikatawa yazo mata, nan take sai ga hawaye sun fara zuba akan kuncinta.



Cikin muryan kuka tace " Boka shine mahaifinki Zainabu,




Mikewa Bappah yayi tsaye, Hannu ya d'aga yana nunata da yatsa, a yayin da Zainabu kuma ta yenki jiki ta fad'i.



Dukkansu kanta sukayi, don yayyafa mata ruwa, ko a samu ta farfad'o.




******

Bayan fard'owan Zainabu, kuka take kaman ranta zai fita, domin abun ya da yawa yake, dame zataji? da abun kunyan da mahaifiyarta ta aikata ko kuma asalinta, lallai Inna bata kyautawa rayuwarta ba,





A sanandin Mahaifiyarta
ta samu bakin tabon da babu abunda zai iya gogeshi.





ILHAAM kuwa jin abun take tamkar sauk'an araduwa daga sama, wai yanzu Babansu ba d'aya bane da Zainabu, lallai abun da mamaki yake.



Inna dai hauka ta tabbata, don karshe D'aki suka maida ita, aka kulle.



Zainabu kuwa tunda ta farfad'o take jikin Ummy tana kukan bakin ciki.



K'arfe biyar dai-dai, su Abba sukayiwa su Bappah da Ummy sallama,



ILHAAM kuka take, don ita tafison a barta ta kwana, Ummy da Bappah ne suka rarrasheta, inda Bappah ya tabbatar mata da suma suna hanyar dawowa Gombe, nan bada jimawa ba.




Ban kwana suka yiwa juna, kana su Abba suka kama hanya.




★★★★★★
*B’AWO LEBBI JOYI*
_Bayan wata biyar_



Abubuwa sun dai-daita a wajensu Ummy, don tuni suka bar MARU suka dawo Gombe bayan Bappah ya saya musu gida, a yayin da Bappah ya bar dabbobin Ummy a chan, inda aka samu, mai kula dasu.




A bangaren su Goggo kuwa, tuni Baba (Malam Babayo) ya koma JOS ya siyar da komai nasu kana ya dawo Gombe, a d'an kusa dasu ya sayi gidanshi suka koma, a yayin da Hajar tace zata zauna da Ummy, inda Ummy ke rik'e dasu, ita da Zainabu, wacce tun da taji asalinta, murmushi ko dariya, ya k'auracewa fuskarta,
don rayuwar kunci ta dorawa kanta.



Babu yadda Ummy batayi ba, amma inaa tayi nisa batajin kira.





***

A bangaren Hajiya Mama kuwa, tuni ta nutsu, ta jira kanta, don a cewarta lokaci yayi daya kamata ta daina kashewa k'attin banza kud'i.


Haka kuma ta bawa Mamy hakuri, akan abubuwan da tayi ta mata, sai dai Mamy ta nuna mata babu komai.



Tayi mugun canjawa tamkar ba ita ba, Daddy kansa yayi mamakin ganin ta yadda ya canja, tamkar ba ita ba, sai dai ya godewa Allah daya shiryar masa da Mairo, don har gafaransa ta nema, haka ma ILHAAM sai data nemi yafiyarta, domin tasan ta musguna mata.




A watannin biyar d'innan tuni akayi Auren Meemy da Ahmad, yanzu anyi aurensu da wata uku daya wuce, inda suke Cairo da zama. a yayin da aka bada Hajar wacce Faisal ya nuna yana so, haka kuma zan bashi, bayan su Abba sunje har JOS tambaya wajen mahaifinta.





Zainabu kuwa wani yaro d'an makobtansu ne, ya nuna yana sonta. Yabawa da hankalinsa da Bappah yayi ne, yasa ya bashi, bayan anyi tambaya, inda aka saka biki nan da wata 3 masu zuwa, bayan dolen da aka mata, a cewarta ita bazatayi Aure ba.


Nan Bappah da Ummy suka mata tass, aka kuma sata kulashi don dole.




★★★★★★★
A bangaren su ILHAAM kuwa.



Tuni aka d'inke, don yanzu son junansu suke tamkar me, haka kuma nunawa juna juna soyayya suke tamkar tattabaru, basa kunyar kowa, musamman Imraan, agaban kowa, yake fad'an duk abunda yazo bakinsan, sai dai ya barta da kunya.




Tuni Imraan ya yada girman kansa, a yayin da ita kuma tuni ta watsar da miskilancinta, ta bada kai, bori ya hau, aka bude *SHAFIN SO.*




Tattalinta yake tamkar kwai, ko aiki baya barinta barinta tayi, saboda cikin wata biyun dake mak'ale acikin maranta.







#share


*Sadeey ce**LAULAM*
( _Kishiyata_)




*Alk'alamin Sadeey ce✍️*



*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*



_Ina mai k'ara jaddada GODIYATA GA Allah ubangijin talikai daya bani ikon da daman kammala littafin nan lafiya, ALHAMUDILLAH YA ALLAH._



*Page 59&60*
( _LAST PAGE_ 🤧)






*THE END*
____Bayan wata uku akayi bikin Hajar da Faisal, inda suke zaune Anguwansu ILHAAM, don Gidajen suna manne da juna, kasan cewar Abba ne ya gina musu a tare.


Zainabu kuwa inda aka kaita Abuja, saboda aikin mijinta dake can.


Sai fatan Allah ya k'ara zaman lafiya, da hakuri da juna.


***
ILHAAM a yanzu cikinta nada wata biyar, sai dai girman da yayi tamkar mai wata bakwai.


Babu abunda take iya aikawata acikin gidan, saboda rashin lafiyar da take fama dashi, domin kuwa tunda ta samu cikin tayi Kolaps,
don ta zama tamkar jik'ek'k'en tsumma, bata iya aikata komai, hatta gyara jikinta da kyar takeyi.


Hakan yasa Mamy ke mugun tausaya mata, don ba k'aramin wahala take sha ba akan wannan cikin,


Shi kansa Imraan d'in ji yake tamkar ta cire mata cikin ya dawo dashi jikinsa, ko ya daina ganin ta acikin wahala, da rashin lafiya, domin bayajin dad'in ganinta haka.


Washhhh



★★★★
*B’AWO DUB'I SAFFO E GO'O*
( _Bayan shekara goma sha d'aya_)


Abubuwa da yawa sun faru acikin shekaru goma sha d'ayan nan, na *Alhamdulilah*
da kuma na *Masha Allah*,

Cikin na *Alhamdulilah* kuwa, ba komai bane face na rasuwar Mama (Mairo, Mahaifiya a wajen Faisal.) wacce tasha jinyan tsawon shekaru biyu, sakamakon Dajin jinin (Blood Cancer) daya shiga jikinta.


Haka kuma acikin shekaru shida da suka wuce su Ummy sukaji labarin rasuwar Inna, wacce mota ta kad'e ta, a yawon haukanta, cikin tsautsayi mai babban mota yayi gaba da ita, yazo da ajali rai yayi halinsa.


Zainab tasha kuka sosai, domin kuwa Uwa dai Uwace, sai fatan Allah ya jikan ta.


Bayan rasuwar Inna ne, Zainab Taje gidan Ummy dama ILHAAM ta nemawa Inna yafiyarsu, inda kuma take fatan su yafe mata, Kota samu sauk'in wani abun, acikin Kabarinta.


Saboda tausayinta yasa suka tabbatar mata da sun nyafe mata, musamman Bappah da yake mugun jin tausayinta, don yasan Inna ta bar mata abunda bazai tab'a fita a ranta ba.


Ana *Masha Allah* kuwa, bai wuce HAIHUWAR da aka tayi ba, acikin Iyalin.


Don Ummy ma da kanta sai data k'ara HAIHUWA `Ya`ya uku, maza biyu mace d'aya,


Zainab da Hajar ma suna da yara uku-uku. A yayin da ILHAAM ke da guda hud'u, maza uku mace d'aya.



Mamy da Abba, wad'anda a yanzu tsufa ta cin musu, kullum cikin godewa Allah suke, daya had'a musu kan zuri'a, suka zama tsuntsiya mad'aurinsu d'aya.


★★★★
Shigowa yayi cikin palour'n, kallo ya k'arewa cikin parlour'n, ganin yadda ya barshi hakan yazo ya yarar dashi.


Ko ina a gyare yake, sai turaren wutan dake tashi, tako ina, sai dai kallon parlour'n ta tabbatar masa, da tabbass tunda ya fita, ILHAAM bata fito cikin,



Hakan na nufin kenan tana kwance a D'aki har yanzu bata fito.



Kana ya nufin D'akin da yake da yakinin tana ciki


***
Bud'e idanunta da sukayi nauyi tayi, saboda ciwon kan dake addabarta tun da jiya da dare, tare da jawo `yar k'aramar Yarinyar dake gefenta wacce ba zatafi shekara d'aya ba, take ta kuka, kana tafara bubbuga bayanta.



B'ude kofan da akayi da kuma khamshin turaren da taji, ya tabbatar mata da ko waye ne.



Gefenta ya zauna kana ya kira sunanta har kusan sau biyu, sai dai shuru tamkar bata ji ba, bai damu da rashin amsarwar nata ba ya ce



"Yanzu kenan haka zaki ci gaba da kwanciya baza kici abinci ba? kenan kina nufin fushi kike da irin ni'imar da Allah ya baki, karki manta fa wassu neman haihuwar suke ido rufe, amma basu saba, sai ke da kika samu ne zaki nuna wa Allah bakyaso? ya ida maganar cikin d'acin murya,



Fuska ta yamutsa, a lokacin data k'arasa tashi zaune, a yayin da hannunta ke kan Narmin dake kwance, tana ci gaba da bubbuga bayanta.



Da idanunta da suke zubar da k'walla ta kalleshi, cikin muryan kukan data fara saboda maganganun da suka ratsa jikinta ta ce


"Ya Imraan kayi hakuri, bawai ina fushi da abunda Allah ya bani bane, kawai ina gujewa Narmin wahala ne, kwata-kwata shekaranta d'aya, kuma ashe inada wani ciki? ba yadda ban yi da kai ba, akan nayi planning ama kaki, yanzu dan Allah ya zanyi, numfashi ta sauk'e kana tace, ba komai amma dan Allah kayi hakuri, insha Allah bazan sake magana ko nuna damuwata akan hakan ba, ta k'arasa maganar, tana fad'awa jikinshi, a yayin da ta k'ara karfin kukanta.



Hannayensa yasa duka biyu ya rungumeta, kana ya ce "



Kiyi hakuri insha Allah zaki sauk'a lafiya kaman yadda kika haifi Ajmal, Akmal, da kuma Hudallah,


Hararan wasa ta masa kana tace "amma kasan a haihuwar Narmin mutuwa ce kad'ai banyi ba, jini kad'ai nasha yakai Leda hud'u, ruwa kam ba'a magana, amma yanzu ka sake baro min wani aikin, bayan na gaya maka, Narmin itace Autana.




Autah a gidan wa? Allah dai ya saukeki lafiya *KECCEL* am, amma nikam indai `Y`aya ne to, dozin nakeson ki haifa min, ya ida maganan yana kashe mata ido,




"Kallon lallai kam ta masa kana tace "Ameen kana ta k'ara cewa " kaje ga kaiwa Mamy fitina, yanzu zasu dameta, maimakon mu mu zauna dasu.



Murmushi yayi kana yace " to za zasuyi, Ajmal da Akmal suna gidan Mamy, amma Hudalla kam tak'i zama, tace sai gidan Ummy, wajensu Zarah, murmushi tayi ba tare da tace komai ba,



Kansa yakai daidan kunnenta ya rad'a mata wani magana, wanda ni Sadeey banji me yace mata ba, sai dai gani nayi, tayi wani irin shegen murmushi kana ta rufe fuskarta da jikinsa,



Narmin data koma bacci ya tura karshen Gado, kana ya kwantar da ILHAAM tare da jan Duvet ya rufesu kiribbbb!!....✍️



Ba shiri na tattara yan koma tsaina nayi waje, don barinsu suma su hole.





TAMMAT BIHAMDULLAH!!!!



```DUKA-DUKA A NAN NA KAWO KARSHEN WANNAN K'AGEGGEN KABARI, ABUNDA NA FAD'A DAI-DAI ALLAH YA BANI LADANSA, KUSKURAN DA NAYI UBANGIJI YA YAFE MIN.




A RUBUTUNA IDAN AKWAI WACCE NA B'ATAWA RAI, TO INA MENAN YAFIYARTA, NIMA KUMA NA YAFEWA KOWA, DOMIN NI YAR ADAM CE, AJIZA CE.```







*GODIYA*
~GODIYA GA OUM AYRAH, D'AYA TAMKAR DUBU, ALLAH YA RAYA MIKI AYRAH'NKI DAMA KANNEN AYRAH MASU ZUWA.~




*GODIYA*
*GA KUNGIYATA ABUN ALFAHARINA, ALLAH YA SAKA MUKU DA ALKHAIRI, UBANGIJI YA K'ARA HAD'A KAYUKANMU. ALLAH YA KAD'E MANA FITINA, UBANGIJI YA TSOLE IDON MAKIYA. INA ALFAHARI DA ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION.... HAKIKA RUWA KAD'AI KE MAGANIN K'ISHI... Up Up best Writers ever.....*





*INA K'ARA MIKA GODIYA GA ANTYNA, KUMA ADDATA, DA BANI DA BANI KAMARKI, OUM JUWAIRIYYA, ALKHAIRIN ALLAH YAJE MIJI HAR GADON BACCINKI. ALLAH YA RAYA MIKI ZURI'ARKI UBANGIJI YA D'AYYABA.*



Ina kar'a godiya ga masoyan littafin LAULAM, Allah ya barmu tare.



Sai mun had'u a sabon littafinna....




*ALLAH WAJJORO KAIRU...*






*SADEEY CE,* `yar Fulani✍️

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment