Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

UP-UP-UP```

_🍂"ALƘALAMINMU🖋️ ƳANCINMU"🍂_



Page......11&12

________ Abun da Mairo matar k'anin Ahmad, Usman ke fad'i kenan, wato kishiyar barbalin Fatima, wacce abun duniya duk ya isheta akan cikin da aka ce Fatima na d'auke dashi,

Don a ganinta ita ya kamata ta fara samun cikin, tunda dai ita ta fara aure.



Don haka ta d'auki alwashin ko za ta yi yawo tsirara sai ta zubar da abunda ke cikin Fatima.



Ta yanke hukuncin tafiya wajen bokanta tun wuri, kafin kuma ta b'allowa kanta wani ruwan.




Farin ciki ne lullube zuciyar Mairo, saboda bokanta ya tabbatar mata da wannan cikin kaman babu shi, kawai ta kasa kunne taji labarin b'arin Fatima, domin ko shakka babu zai zube.



Wannan magana ta boka ba karamin farin ciki yasa Mairo ba, a cewar ta karshen damuwarta yazo k'arshe.




*******
Fatima na ta kula da cikinta bisa taimakon mijinta, cikin ikon Allah, ko Laulayin ba ta yi sai dai cin abinci wanda bai da matsaya.



Ahmad ririta Fatima ya ke kaman k'wai, don ji ya ke tamkar ya tabbata da cikin ya dawo dashi jikinsa, ko zai na jin d'an dama-dama,



Ita dai Fatima sai dai ta yi murmushi, amma bata ce wa komai haka kuma bata nuna sonta akan cikin domin d'an fari ne, wanda a al-adan Fulani ba'a bayyana SO akan d'an fari,





Daga Adda har Modibbo kullum sai sun kirashi don jin lafiyar Fatima da na abunda ke cikin ta.



A ya yin da Modibbo ke yawan aiko mata da ruwan rubutu, wanda yake bawa duk mace data samu ciki a cikin family'n, wanda su kansu basu san na me ba ne.


Bayan wata Tara Allah ya sauk'i Fatima lafiya, in da ta samu d'a namiji.


Yaro kyakyawa dashi, son kowa k'in wanda ya rasa, mai tsakanin kama da mahaifinshi.



Ranar suna yaro yaci ABUBAKAR, sunan Modibbo, sai dai suna masa inkiya (lakani) da IMRAAN.




Ranar suna ne, su Mairo dama wasu daga cikin dangin Ahmad da na Fatima suka zo gidan, acikin wad'an da su ka zo har da Mairo, wace tunda suka zo bata da aikin daya wuce zagaye gidan, don Mairo sai da ta kusan hawaye ganin irin gidan da Fatima ke ciki, amma ita an barta a k'auye bata da aiki sai na dafawa surukai abinci, da kuma bak'in Modibbo, to wallahi sai an san na yi, don inta yarda Allah ya tsine mata, mussaman data ga d'ayan gefen da aketa cewa Ahmad ya ginawa Usman.


Washe garin suna, aka maidasu gida dukkansu, bayan Ahmad ya had'asu da sha tara da arziki, Mairo kaman za ta yi kuka, don a kwana d'ayan nan ba k'aramin sab'o ta yi da gidan ba.





Da daddare suna zaune ita da mijinta, cikin sanyin murya irin na mata masu neman abu a wajen miji ta ce "ni kam na tambaye ka mana? cewar Mairo,


Kallonta Usman ya yi, kana ya ce "uhum ina jinki, cikin dakiya ta k'ara cewa "ba Yayanku ya ce gefe d'aya na gidansa naka ne ba?




Cikin kosawa da maganar ya ce "eh haka ne, amma meya faru ki ke tambaya?


Cikin aro jarumta, kana ta k'ara cewa, "to me yasa ba za mu koma cikin gidan ba, ai ko ba komai kaga mu ma mun shiga cikin gari ko? ganin bai yi magana ba, ya bata damar ci gaba da fad'in "ai Yayanka ne, kuma don ka zauna a gidansa ba wani abu ba ne, ni dai gaskiya gwara mu ma mu je, yanzu kai Yayanka na birni amma kai ka na zaune a k'auye kaman wani mara galihu? Matarsa ta haihu amma mu shuru, bayan mu muka rigata aure, to gaskiya ni dai ko ba za ka koma ba, sai na koma da kaina, domin na gaji da zaman cikin k'auye.



Kallon baki da isheshshen hankali ya mata, kana cikin ya na yin dake nuna zallan hatsalan da ya yi ya fara cewa "dama wannan ne tunaninki? to wallahi tun wuri ki maida hankalinki, ni nasan abunda na ke yi, idan ke baki sani ba, kin zo kin ajiyeni, ki na ta min wasu surutai,


Gida ne bazan koma ba, haihuwa kuma Allah ne ke bayarwa ba wani ba, kuma na rantse da wanda numfashi na yake hannunshi, idan ki ka kuskura ki ka sake min maganar, wallahi ranki in yayi dubu sai ya yi mummunan b'aci! ya na gama fad'an haka ya tashi ya fita daga Gidan
baki d'aya.



Bayansa tabi da kallon kana ta ce "wallahi sai sai kayi, sai na sake magana kam, duk abunda zai faru ya faru, ba b'aci ran nawan zai yi ba, ya rub'e, karshen b'aci kenan, komawa Gombe kuma kaman ma anyi an gama ne.


★★★★★
IMRAAN ya na da shekara d'aya, Allah ya bawa Mairo ciki, bayan wata tara ta haihu inda ta samu ita ma d'a namiji, ranar suna yaro ya ci suna Muhammad, suna kiransa da Faisal.


Mairo ta sake komawa wajen bokanta, akan rashin cika mata alkawarin da bai yi ba, in da ya bata tabbacin cewa ya k'asa b'arar da cikin yaron, amma ta bari yana cika shekara goma zai kashe shi.



Don haka hankalin mairo ya kwanta, ta cigaba da hidimominta, kaman ba komai, sai dai duk a lokacin da aka yi maganan Fatima ko na IMRAAN, to tabbas sai anga k'iyayyan da takewa Fatima da d'anta.


Domin Mairo tana layin irin mutanen da basu iya boye damuwa, ko abunda su ke so haka kuma ko abunda suke k'i, wannan dalilin yasa mutane da yawa gane ce wa lallai akwai takun sak'a tsakaninta da Fatima.




Yara nata girma masha Allah, don a yanzu IMRAAN nada shekara biyar a ya yin da Faisal ke da hud'u, shiga makarantar da IMRAAN ya yi haka ya bawa Ahmad daman d'auko Faisal daga gida, bayan zagayowar shekara, shima ya sakashi a makaranta, don haka rik'on Faisal ya dawo hannun Fatima, wacce farin ciki ya isheta kaman zata yi yaya, don dama ita tana son taga ta haifi yara da yawa, sai dai tunda ta haifi IMRAAN bata sake ba.


Wannan dalilin ya sa take nunawa Faisal so fiye da yadda take nunawa IMRAAN, domin shi IMRAAN bata nunawa ta damu shi, kasancewarsa d'an fari.



D'aukan Faisal ba k'aramin ciwo ya yi wa Mairo ba, don a cewarta ai duk salon munafurci ne, taya za'a rabata da d'anta k'waya d'aya, a yi mata k'arya da wata shegiyar Makaranta.


Sai dai ba komai, ai nan da wasu []an tsirarun shekaru ne, da zaran ta kashe IMRAAN shikenan,



An saka Faisal a school in da yake Nursery one a ya yin da IMRAAN ke primary 1, ba laifi kuma suna gane karatun duk da k'ank'antan shekarunsu.

.....✍️*LAULAM*
( _Kishiyata_)




*Alk’alamin SADEEY ce.✍️*






*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

```MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA HUMMM WANI ABU SAI ROYAL STAR WRITER'S ✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) 💪💪💪💪
UP-UP-UP```

_🍂"ALƘALAMINMU🖋️ ƳANCINMU"🍂_



Page.....13&14


____A b'angaren Mama kuwa, kullum tana kasa kunne taji labarin mutuwar IMRAAN sai dai shuru har yanzu.




Domin Bokanta yayi mata alk'awarin IMRAAN ba zai rufa 10 years ba zai margaya, amma shuru har yanzu, idan ba wai ta b'ata lissafi ba shekaru IMRAAN goma sha d'aya.




To wai me haka ke nufi? kenan Bokanta ya mata k'arya? to ko lallai zatayi maganinsa.





Abbah (Ahmad) Dukiyarsa ta k'ara hab'aka, domin a wannan shekarun, ba shekarar da iyayensa basa zuwa Makkah, don every year idan aka tashi zuwa Hajjih yana biyawa Iyayensa tare da wassu tsiraru daga a cikin dangi.




Sannan marasa k'arfin ma yana ci gaba da taimaka musu,




Hakan yasa yanzu babu inda ba'ajin sunansa a fad'in jihar Gombe dama kewayenta kasancewar yana da taimako kama daga Gidajen Marayu,sansanin []an gudun hijira, masallatai.




Yana zuwa Asibitoci yana taimakawa marasa k'arfin sayan magani da dai sauran wassu abubuwan wanda wassu iya siyawa kansu.







Maamy ita ma ba'a barta a baya ba, tana taimako daidain gwargwadon iyawarta,




Haka kuma ta rik'e Faisal da zuciya d'aya tamkar IMRAAN daya fito daga cikinta,




kasancewar Faisal d'ane shima mai nagartaccen hali domin kwata-kwata bai d'auko mugayen halayen Mama (mayro) ba , duk da kuwa yana sane cewa mahaifiyarsa.




Sai dai bata da halaye na gari, kuma bata k'aunar Mamy da IMRAAN, sai dai hakan bai sa shima yak'i su ba hasalima yafi nuna sonsu akanta.




yana sonsu, duk da k'aranci shekarun da yake dashi. Domin Yaro ne mai tsananin kafinbasira, da saurin gane abu, haka ma IMRAAN.






Son da mayro taga d'anta yana yiwa IMRAAN da Mamy shine ya kara harzukata, har hankalinta ya fara tashi, hakan yasa take cewa,




"ai shikenan za'a rabata da d'anta na cikinta yanzu duk abunda ta saka shi yi akan su Mamy sai yace mata shikam ba zai iya ba, ko kuma ya nuna mata rashin dacewar abun.



A halin yanzu IMRAAN yana da shekara goma sha daya (11) indai Faisal yake da Tara(10).





A wannan lokacinne Allah ya sake bawa Mamy wani cikin bayan ta fidda rai daga haihuwa, tayi farinciki matuk'a daga ita har mijin ta haka kuma sun k'ara gode wa Allah daya sake bawa Mamy ciki, bayan tsawon shekaru goma sha daya, da har sun fidda rai daga samunshi.






Tattalin cikin suke kaman na me kasancewar dama suna so,




Faisal dai yayi mugun farinciki kasancewar shima mahaifiyarsa bata sake haihuwa ba, haka kuwa yasa dashi ake tattalin rainon cikin.





IMRAAN dai ba'a gane tasa kasan cewar sa baud'ed'd'e, domin bai nuna ko a fuska ba duk da yayi farin ciki da samun cikin Mamy, kasan cewar yana son k'anwa mace, sai dai bai sa kowa yaga farin cikin sa ko Hak'orinsa ba yadai adana kayansa a cikin ransa.


Mama (mayro) da taji Maganan cikin Fatima this time kam haukane kawai batayi ba, don fad'ar irin tashin hahakalin da ta shiga b'ata lokaci ne, ji take tamkar ta d'ora Hannu a Kanta ta tsala uban ihu, wanda zai nunawa Duniya tana cikin damuwa, amma ba dama, shiri tayi ta tafi wajen bokanta wanda yake a cikin k'auyen *Tind'a* , sai dai ya tabbatar mata da bazai yuwu ba, nan ta dawo gida hankalinta a tashe, Nasara d'aya suka samu akan Fatima na hanata d'aukan ciki shekara da shekaru, amma bayan shi nata sake samun ko wace irin Nasara ba, wai me hakan yake nufi ne? to wallahi duk zatayi maganin su, har Modibbon ma.



Fatima na ci gaba da kula da cikin ta tare da taimakon kwarzon Mijinta kuma Yayanta, SO da tattali yake nuna mata kaman ba gobe,daga Fatima har Mijinta da []a[]ansu duk sun d'auki son Duniya sun d'orawa cikin da bai zo duniya ba.


★★★★★

A Safiyar yau ne Modibbo's family dama K'auyen MARU baki d'aya suka tashi da mummunan kabari, labarin da ya girgiza dubban jama'an gari,

A safiyar alhamis 30-9-2022 Allah yayiwa Alhaji Abubakar Modibbo rasuwa😭😭 sakamakon dan jinyan da yayi mara tsayi, domin zazzabi da yayi na tsawon 5 days, domin ko Abbah bai sani ba don shi da kansa yace wa Addah karta kirasu don kar a tayar musu da hankali, ashe k'arar kwana ne,



MUTUWAR data bugi kaf yan garin domin Modibbo na kowane, kowa yaji mutuwar Modibbo.



Labarin ya isawa su Abbah sakamakon kiran da daddy (Usman) ya kirashi ya sanar masa yana kuka mai taba zuciya, jin MUTUWAR sukayi tamkar saukan aradu domin babu wanda ya sanar musu rashin lafiyansa, idan nace Ahmad da Fatima basuji Wannan MUTUWAR ba to tabbas nayi k'arya, domin Fatima kasan cewar ta mace mai rauni yasa damuwa da tashin hankalinta fito wa fili.

shiryawa sukayi suka kama hanyar MARU inda za'a yi jana'idar sa da Misalin K'arfe 11 na safe.




Anyi jana'zar Alhaji Abubakar Modibbo a babban masallacin juma'a na garin inda ya samu jama'a, domin dama kowa yasan sannenene , wannan dalilinne yasa MUTUWAR sa ta bugi kowa.

garin cike yake da jama'a domin ko ina karan jiniya kawai akeji tamkar garin zai fashe don cika.


Allah sarki Addah matar kirki ko tari batayiba tayi tawakkali ta fawwalawa Allah komai(ya Allah ka uzurtamu da kekkyawar zuciya)


Malam liman shima yaji MUTUWAR tilon d'an Uwanshi da bayida kamarsa duk fad'in duniya, duk da yana Namiji shikam ya kasa rike nasa, domin kuka yake Addah ma tafisa jarumta,


Abbah kam runguman Mamy yayi yayi ta kuka kaman mace domin tabbas bazai iya wannan jarumtar ba, yasan yayi rashi kowa yayi rashi.

Haka akaci gaba zaman makoki inda mutane ke zuwa gaisuwa from deferent place wassu ta dalilin Abba wassu kuma tashi, don Modibbo kowa yasan nashi ne, haka kuma sahi mai jama'a ne, sai dai fatan Allah ya jikanshi ya gafarta masa ya Kai haske kabarinsa mukuma ya kyautata namu.....✍️




09139126255
Sadeey ce
*LAULAM*
( _Kishiyata_)




*Alk’alamin SADEEY ce.✍️*






*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

```MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA HUMMM WANI ABU SAI ROYAL STAR WRITER'S ✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) 💪💪💪💪
UP-UP-UP```

_🍂"ALƘALAMINMU🖋️ ƳANCINMU"🍂_



*DEEJAYS TOUCH💄*

_Makeup price list_
Casual Makeup @3k
Special makeup @6k
Bridal makeup @15k

Location: Kano State, Tudun wada bridge, Opp. Hajara Ahmad Primary school.
For your booking Call or Whatsapp 08122188717

»»•––––––––––•»»



```Wannan page sadaukarwa ga Al'umman Alhaji Abubakar Modibbo, akan rashin da kukayi, fatan Allah ya jikanshi ya kuma gafar ta masa, yasa mutuwa ta zama hutu a gareshi, mu kuma ya kyauta ta namu ```



Page.....15&16





____Bayan sadakan bakwai, mutane sun watse sauran na jiki irinsu Abbah wad'anda suka k'i komawa.




Har yanzu mutuwar Modibbo bata sake suba, saboda daga ganinsu kasan suna cikin damuwa, musamman irinsu Abba kam sai da Addah ta fara ajiye su tana musu nasiha da nuna musu illar wannan rashin walwal da saka kansu a damuwa da sukayi, kafin suka fara sakewa, kana suka fawwalawa Allah.




A b'angaren Mama kuwa, rasuwar modibbo bata cire kaso d'aya cikin dubu na abunda take ji game da su Fatima ba, sai ma k'aruwar da kud'urinta yayi, tana ganin yanzu duk aikin da tayi zai iya kamasu saboda dama Modibbo shine katangan daya hana tsohon burinta cika.





Bayan kwanaki sunja su Abbah suka shirya suka koma, bisa tirsasawar Addah, saboda tayi duba da jikin Mamy, ba dad'i takeji ba, yakama ta suje ko don Asibiti su saboda condition d'in da take ciki,


Sun koma Gida lafiya inda sukaci gaba da hidimominsu ba tare da walwalansu ya dawo normal ba, don suna jin rashin sa, hatta su IMRAAN sunsan sunyi rashi ba kad'an ba ballen tana Iyayen amma ba yadda suka iya sai dai su fawwalawa Allah komai, dama shiya basu Modibbo kuma ya karb'e kayansa, sai dai kawai su bishi da Addu'a shine son da zasu nuna masa.



Abbah ya koma bakin aikinsa inda su IMRAAN suka koma school, yayin da Mamy taci gaba da kula da cikinta, domin babu abunda zai changer
(Hmm saboo turken wawa)

*********************************
*BAYAN WANI LOKACI*
da rasuwar modibbo yanzu ya d'auki a akallah wata biyar da sati biyu, inda cikin fatima yake da wata bakwai kenan, Abbah yana taya Mamy kula da kanta, domin tunda ta samu cikin lafiya yayi mata karanci wannan dalilinne yasa yake tausaya mata, sannan kuma ga wannan rashin da sukayi wanda zuwa yanzu ya bi jikinsu.




Addah ma zuwa yanzu ya gama takaba inda Abbah yaso daukar ta ta dawo gombe duba da jikin ta don tun bayan rasuwar mai gidanta modibbo itama jikin sai a hankali ga kuma tsufa amma sai ta nuna masa tafi son zaman MARU akan zaman
*GOMBE* , rabuwa kawai sukayi da ita kana suka nema mata `Yarinya mai aiki wacce zata rage mata kewa, sannan duk bayan wani lokaci Abbah yana zuwa ya d'auketa ya kaita asibi ayi checking dinta saboda yanayin jikinta ```(ga wadanda suka San darAjaan iyayensu ba irin wassu yaran ba da basu San darajan nasu iyayen ba Allah ka bamu yaya na gari wadanda zasuji tausayinmu allahummah ameen ya Allah.)```




A b'angaren Mama kuwa babu abunda ya ragu akan k'udurin da ta tashi dashi na ganin bayan Mamy da IMRAAN sai dai abun yaci tura domin bokanta ya tabbatar mata da bazasu iya komai ma Mamy ba, wannan kulle mata mahaifan da sukayi ma bawai k'arfin sihirinsa bane yasa mahaifar kullewa, kawai ta kullle ne saboda Allah ya nuna mana babu wanda sihiri bazai iya kamawa ba, sannan kuma yana cikin littafin ‘kaddaranta,(hege boka she yasan gaddara)




************************************
After 2 month
Mamy ta haifo `Yarta mace mai kama da ita sannan kuma kekkyawa fara Soll,


Ranan suna yarinya taci sunan Addah wato *Rukayyah*
inda akayi shagalin suna na gani na fada, IMRAAN da Faisal har ka rasa waye yafi dan uwansa farinciki domin IMRAAN ajiye miskilancinsa yayi a gefe yana nuna wa little sis d'inshi so, don yana jin sonta har cikin ransa haka ma Faisal ji yake kaman Mama ce ta haihu, anci an sha an bararraje inda aka had'a karamar liyafa wacce ta kayatar. da ja jingiji ya raya mana Rukayya.*LAULAM*
( _Kishiyata_)




*Alk’alamin SADEEY ce.✍️*






*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

```MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA HUMMM WANI ABU SAI ROYAL STAR WRITER'S ✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) 💪💪💪💪
UP-UP-UP```

_🍂"ALƘALAMINMU🖋️ ƳANCINMU"🍂_



Page......17&18

________Allah cikin ikonsa da buwayarsa, ya raya Meemy, don yanzu haka tana da shekara biyu da haihuwa, ta girma Masha, ga wayon tsiya, domin babu wanda bata ganewa a gidan, especially Faisal kasan cewar yafi d'aukanta da kuma mata wasa, sab'anin IMRAAN da ko sake mata fuska bai cikayi ba a yanzu, domin shi yana girma rashin maganansa yana k'ara fitowa fili,





tun Mamy tana damuwa tare da masa magana har ta gaji ta zubawa sarautar Allah ido.



Haka ma Mama taki hak'ura da abunda Bokanta ya gaya mata na babu yadda suka iya da jinin ABUBAKAR MODIBBO amma tayi Kunnen uwar shegu k'arshe ma wani sabon Boka ta samo take zuwa tana ta faman kashe kud'inta a banza, domin shid'in ma bawai asirin yana tab'a su Mamyn bane, kawai dai ya rufe ta ne don yaga kaman ita irin sakarkarun matan nanne.




Meemy nada shekara uku Allah yayiwa (HAJIYA RUKAYYAH ABUBAKAR MODIBBO) (Addah) rasuwa, sakamakon zamewar da tayi acikin Toilet (Bayi) kuma yayi ajalinta, rasuwar data sake girgiza familyn Modibbo a karo na biyu, sun shiga rud'ani mai tsananin gaske.




Idan akace basuji MUTUWAR Addah ba to tabbas nayi k'arya, domin ita Addah rasuwar ta asaran kowa ne, kowa a familyn dama k'auyen ya daka kuma tabbas sunsan sunyi asaran Uwa ta gari.



Abbah da daddy rasa inda zasu sa kansu sukayi domin tabbas rashi-rashine sannan MUTUWAR Uwa daban take *UWA*! *UWA*! *UWA* CE MUTUWAR *uwa* daban take a cikin zuciyar `Ya`yanta domin Uwa ta wuce gaban wasa, komanta na dabanne Shiyasa MUTUWAR ta ta zama na daban, shiyasa MUTUWAR Uwa take zamowa Yayanta tamkar Gyambon da baya warkewa,waanda kulluma zai na famewa.


ya Allah ya jikan iyayenmu da suka riga mu gidan Gaskiya.




Tabbas Addah mace ce mai kyawawan halaye, mace ce wacce kowa zaiso yayi koyi da kyawawan halayenta sadai kashh! kana naka shima yana nashi, mutuwa kenan.




Mamy ma taji MUTUWAR Addah ba kad'an ba, domin Addah Uwace ba matar Bappah ba, sannan ba Kuma *UWAR MIJI* ba ita d'in a *Uwace* take d'aukar ta,


Abbah domin shikam daga shi har daddyn Faisal kasa magana sukayi, gwara ma Abbah Mamy ta tausa sheshi da kalamai masu dadi dakuma saka nutsuwa, sannan kuma da Sanyaya rai, (Hmm dama ance *mace ta gari cikon addinin mijinta*), sab'anin Mama da ko kallon inda yake bata yi ba, don a cewar ta, tana abubuwan yi, masu muhimmanci.



Haka ma Addayi tasan tayi rashin Addah kuma abokiyar zama na kirki,domin Addah macece mai Hak'uri da tausasa ranta duk da tasan tun dãã wassu abubuwan zaman yau da kullum kan shiga tsakanin su ko akan yara ko kuma na zaman take wa, amma Addah bata tab'a magana ba har ta koma ga mahaliccinta,




Haka rayuwa take yau kaine, gobe ba kai bane, haka Addah tazo ta shud'e kaman modibbo tamkar basu zo duniyan ba bama,


Sai dai fatan Allah ya jikanta tare sa sauran musulman da suka Rigamu gidan Gaskiya (Allahummah ameen ya rabbal alameen)




*AFTER SIX (6)YEARS*

*****************
A shekaru shida da suka gabata abubuwa da yawa sun faru cikin na farinciki dana akasin haka, na farincikin har dawowar daddyn Faisal GOMBE da zama a bisa tursasawar Abbah, sannan kuma ya bud'e masa katon *SHOPPING MALL* mai kyan gaske da Kuma girma, sai rasuwa Addayi (Mahaifiyar mamy) sai fatan Allah ya jikansu.




A gefe guda kuma IMRAAN ya gama secondary school inda Faisal kuma sai next year.




Duk da dawowar Mama Gidan hakan baisa Faisal ya kaurace ma mamy ba, hasalima baya zama a side d'in Mama domin har yanzu a gurin Mamy yake, yak'i komawa wajen mahaifiyarsa,
Wannan abun ba karamin bak'anta ran Mama yayi ba, ganin d'an cikinta yana neman yafi karfin ta,




Mama tayi farinci da dawowarta gombe ba kad'an ba ,domin dama burinta kenan ta dawo gombe don ta shiga gari itama tasa kaya masu tsada, sannan tana shiga Motoci kaman dai Mamy,
Sai dai batasan wanda Allah ya d'aukaka yafi Danda duniya ta daukaka, domin Fulani nace *Mo Allah hokki buri mo baba hokki.* domin Mamy ta wuce ta ba kad'an ba ,don zuwa yanzu ita ma Mamy tayi karatu domin tun bayan haihuwar IMRAAN Abbah yasata a school don ganin rashin karatun bayida amfani, sai dai ba daga primary ta fara ba don Satificate kawai Abbah ya nema mata, kana ta fara zuwa daga JS1 har ta gama secondary sannan ya nema Mata admission a *NOUN* wato inda yake aiki kenan kasancewar dama ma'aikatar *WORK AND LEARN* ne Shiyasa ya saya mata admission a gurin shi yana aiki ita kuma tana karatu, domin a yanzu ta had'a degree d'inta, a yayin da shikuma Abbah yanzu ya k'arasa "PHD."




IMRAAN yanzu yana da 26 years a duniya, a yayin da Faisal yake da 25 na ita kuma Meemy take goma kacal.



Yanzu IMRAAN CAIRO din da zai tafi gidan daddyn Kayrat (Mus'ab kenan abokin Abbah ) wanda aiki ya maida CAIRO da zama tare da matar sa zainab da kuma Yayansu wanda a yanzu yana da Yaya guda hudu(4) biyu maza biyu mata, Kayrat (mai sunan Hajiyar Mus'ab ) sai mai sunan Babansu wanda suke kira waleed, sai Ahmad (mai sunan Abbah) sannan kuma Waleeda (mahaifiyar zainab kenan ) kuma duk sun girma kasancewar shi matarsa akai akai take haihuwa duk da ma bazata wuce Mamy ba, domin waleed da Kayrat ma sunfi IMRAAN Sai Ahmad wanda yake sa'an Faisal sai kuma Waleeda wacce zata bawa meemy shekaru uku zuwa hud'u,

ganin mus'ab yana Cairo yasa Abbah cewa IMRAAN zai tafi chan, inda Faisal ma idan ya kammala nasa nan da shekara biyu zai bishi.......✍🏻




back to labari💃





Manage please🤧🤧

More comments more typing💃💃



*LAULAM*
( _Kishiyata_)




*Alk’alamin

Please Login or Register in order to submit comment