Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

flowers aka fara spraying daga sama, sai kuma aka sake waka mai taken *Beginning* daga IMRAAN har ILHAAM babu mai rawa a cikinsu sai da Kamal ya zo kusa dasu ya ce


"Haba dan Allah karku bamu kunya mana, ko ɗan gigirgizawa ku taimaka ku dan yi mana, ya karasa maganar cikin neman rigima don yasan IMRAAN bai taɓa rawa ba.



ILHAAM dai ba ta cuci kanta ba ta fara girgiza Inda Ahmad ya fara hararanta.




Bayan sun shiga ciki suka zauna a kan kujerun da aka tanadar don su.



Abokannan ango ma sun yi ankonsu cikin
farin shadda.




An fara gabatar da abinci daga nan sai shagali ya biyo baya.





An ci an sha an caskale ba karya masu rawa sun yi rawa, marasa rawa sun yi kallo, sai 7 kafin su ILHAAM su koma gida in da kowa ya koma a gajiye ILHAAM kaman zata kifu don ma bata sallah ne yasa ta bari.




Ta na dawowa sai wanka Anty Fauxiyyah ta na gama bata ɗure-ɗuren ta da aka saba, don shi kaɗai ta ke sha, ba jimawa ta bingere don ta ce wallahi yau babu gyran jikin daren da za'a mata, (ni kam na ce kin yi wa kanki)
daga nan ta kwanta kasanncewar gobe in da zai kama Saturday kuma program ɗin 8pm su ke dashi.



*********
*JESUS OWN STATE (JOS)*
Murmushi d'auke akan kyakkyawar fuskarta, saɓanin hawaye, murmushi take ta yi tun wayewar garin ranar, wanda ya matuƙar bawa Goggo da Hajar mamaki, ganin tsawon shekara goma sha tara(7) bata taɓa magana ba ballen tana wani abu makamancin wannan.


Hajar dai farinciki ta ke yi ganin Ummynta na murmushi, don tasan tun ta na ƙarama bata taɓa jin maganan Ummy ba, amma yau sai gata ta na murmushi,




*WAYE MALAM BABAYO*
Cikekken sunansa shi ne Muhammad Dauda, wanda aka fi saninsa da Babayo kasan cewar ya ci sunan Kakansa.




Haifeffen jihar Gombe ne a ƙauyen *KOMFULATA* dake karamar hukumar *ƘWAMI*,wanda kasuwanci ya mai dashi JOS, ya na da mata ɗaya mai suna Amina (Goggo) sai `Yarsu guda ɗaya tilo da Allah ya ba su mai suna Hajarah wacce Allah ya mata rasuwa, a wajen haihuwa in da ta haifi ya mace wacce suka mayar mata da sunan mahaifiyarta, (Hajar) Malam Babayo ba mai kuɗi ba ne, haka kuma ba talaka ba ne, wato dai mai rufin asiri,


kasuwanci shi ne ya maida Malam Babayo JOS daga baya ya so komawa amma karewar dangi sakamakon fadan ƙabilan da aka taɓa yi a cikin garin ya sa shi ci gaba da zama a JOS.



15-3-2002
A tsakatsakiyar daminar shekarar bayan an gama ruwan dare, da asuba Malam Babayo ya fito don tafiya masallaici a bakin kofa y aci karo da wata mata da take kwance bata san inda kanta yake ba, a cikin mutane masu bin hanyar don tafiya masallaci ya samu wassu samarin da ya sa su daga masa matar wacce bata wuce
20 ba, cikin gidan suka shigar da ita kana shi kuma ya wuce Masallaci.


bayan ya dawo ne ya yi wa goggo bayani abunda ya faru, kwata-kwata Goggo bata nuna zata iya kula da wannan matar ba, saboda taga yanayinta, babu ɗigon walwala a fuskarta ta furta Allah ya kyauta.




Sai da wannan Matar wacce Baba (Babayo) ya sawa (Aisha) ta kwashe tsawon wuni ta na baccin da basu san me ne farkonshi ba, ko abunda ya saka ta yinsa ba.




Sai dai sun yi mamakin abunda suka gani bayan farkawanta, domin kuwa akwai alamomin da suka gani, bayan na rashin magana da sauransu.....✍🏻




09139216255
Sadeey*LAULAM*
( _Kishiyata_)




*Alk'alamin Sadeey ce✍️*





««•–––––––––––––––––•»»
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

•««–––––––––––––––––»»•




*Page....33&34*


"Wato har wannan ɗan gashin zaki fitar waje ko? ke gaki mai gashi ko? "to wallahi idan ki ka kuskura na sake ganin wannan gashin a waje sai na saka razor na yankeshi, ya kasara magana ya na haɗe fuska tamkar ba shi ya yi maganar ba.



A time d'in da ya kai bakinsa dai-dai kunnenta ne ya bawa mai ɗaukan Photon daman ɗauka, domin ba ƙaramin kyau su ka yi ba, hasalima kama su ka yi da masoyan asali.



Bayan an gama ɗaukan pictures a loakcin har 3 ta yi kasan cewar ba'a fara ɗaukan picture ɗin da wuri ba yasa ba'a gama da wuri ba.



Ahmad ne ya ja IMRAAN gefe cikin muryan kasa- kasa ya ce "abokina nifa naga iri acikin ƙawayen amaryan nan, don haka na kama kafarka,



cikin dariya Imraan ya ce "haba dai Daddyna (dama haka ya ke gaya masa kasan cewar sa mai sunan mahaifinsa) wacce daya,

da yatsa ya nu na wacce ya gani,

murmushi IMRAAN ya yi ganin Meemy ya nuna, cikin zolaya ya ce "gaskiya Daddy daga yau ni ne babban Yaya, cikin rashin fahimta Ahmad ya ce "meya faru?"

cikin dariyan zolaya IMRAAN ya ce "sister na ne, ya karasa maganar cikin kosawa da maganan, don ba karamin gajiya
ya yi ba,


"whattt!!! you mean ita ce Meemy?
"yes of course"



Ƙafada Ahmed ya daga sannan ya ce "koma me ne dole ka min hanya, ya karasa magana cikin tsare gida irin gashi babban nan ai IMRAAN bai san sanda ya fara dariya, tare da ce wa
" ba damuwa"


Suna gamawa suka nufi MH wato *MADUGU HOTEL* ke nan don gudanar da reception wanda zai daukesu tsawon 1hrs za su fara 3:pm su gama :pm ke nan i nda su ILHAAM za su yi nasu 3-4 ke nan.



4pm dai-dai muka gama shirin mu ita da ƙawayenta sanye take cikin yadi omo blue and dark blue in da ya yi masifar kyau ba kadan ba,

ƙawaye kuma su Meemy ke nan sanye suke cikin blue black din gown sai black head sun yi kyau Masha Allah,


ƙawayensu dukannisu sun ta fi kasancewar lokaci ya fara tafiya, Meemy ka dai ta rage wacce IMRAAN ya hana ta tafiya (domin sun hada plan da Ahmed akan ya na so ya kebe da Meemy)

sai 4:30 kafin a sanar wa su ILHAAM ce wa ya zo, fita su ka yi cikin takunsu na cikakkkun yan mata kuma *`Yan Jami'a* masu ji da kansu da taken kuruciya, Hill da su ka sanya shiya kara changer musu salon tafiya, sai kiga tamkar yanga su ke yi, sai dai abun ba haka ya ke ba.


ganin motoci biyu ne a wurin yasa su ka yi hanyar motar da suke tunani ita ce ta ya IMRAAN, sit ɗin baya suka bude, ganin IMRAAN a hakimce ya sanya Meemy ce wa

"Ya IMRAAN ina zan shiga?"

da hannu ya mata nuni da wata bakar mota wacce suka wuce,


ILHAAM dai ganin Meemy ta bude sit din baya ya sata shiga abunta ta zauna ko ci kanka ba ta ce masa ba sai dai da idonta ya fad'a a kansa da kyar ta iya janyewa, sanye yake cikin blue din shadda shi ma wanda aka masa aiki da dark blue din saurfani hulan kansa dark blue ne, haka ma takalmin kafansa daya kasance dark black, sai ROLEX din agogonsa mai shegen kyau ita dai ta san ya yi mugun kyau amma sai ta basar kaman bata ma gan shi da kaya ba, haka shi ma IMRAAN kallo ya kare mata, ganin yadda Colours d'in suka karb'i jikinta, ya na mai kara jinjina irin wannan kyawun da ya san ta yi, kasan cewar abokin su IMRAAN Alee shi ne mai driving yasa ya yi shuru domin sun tsara motan Ahmad ita ce a gaba.





A ɓagaren Meemy kuwa
bata sake magana ba ta yi wajen mortar tare da tunanin waye ne.



Ƙofan gaba ta bud'e gefen driver, wato sit d'in mai zaman banza, zama ta yi ba tare da ta juya taga ko waye ba ne, reverse ya yi ba tare da ya yi magana ba shi ma, ya kama hanyar
TH wato *GOMBE INTERNATIONAL HOTEL*



ganin bata da niyyar magana cikin zolaya ya ce


"Ranki shi dade barka da yamma,



Gabanta ne ya bada sautin rass, ba shiri ta juyo ganin bata san shi ba ne ya sata ce wa



"Ka na ta gaisheshi cikin girmamawa, amsawa ya yi cikin sakin fuska, daga haka suka fara hira.


nan ya fa ra introducing kansa ganin bata ganeshi ba, ( Meemy ba ta san su Ahmad ba kasan cewar tunda aka haifeta ba su sake zuwa ba sai wannan bikin).



Hancin motan Ahmad ne ya fara shiga cikin harabar Makarantar kafin ya samu gefe ya yi parking sannan Alee ma ya zo ya yi parking.


Meemy ce ta fito da Ahmad ta na d'auke da sihirtaccen murmushi akan kyakkyawar fuskarta,




IMRAAN ne ya fara fitowa kafin ILHAAM wacce ganin idon jama'a ya sa ta jin wani irin, hannuta daya kama ne ya dawo da ita daga dogon tunanin data tafi, jin tattausan hannunsa a cikin hannunta, jerawa su ka yi a tare suna tafiya cikin nutsuwa a ya yin da kawaye su ka yi layi guda biyu ta gefen ango dana amarya suka saka su a tsakiya, inda hakan ya ƙara kawatar da mai kallo, hanyar Hall d'in suka nufa sai da su ka zo bakin Hall d'in suka tsaya bisa umarnin MC, red an white flowers aka fara spraying daga sama, sai kuma aka sake waka mai taken *Beginning* daga IMRAAN har ILHAAM babu mai rawa a cikinsu sai da Kamal ya zo kusa dasu ya ce


"Haba dan Allah karku bamu kunya mana, ko ɗan gigirgizawa ku taimaka ku dan yi mana, ya karasa maganar cikin neman rigima don yasan IMRAAN bai taɓa rawa ba.



ILHAAM dai ba ta cuci kanta ba ta fara girgiza Inda Ahmad ya fara hararanta.




Bayan sun shiga ciki suka zauna a kan kujerun da aka tanadar don su.



Abokannan ango ma sun yi ankonsu cikin
farin shadda.




An fara gabatar da abinci daga nan sai shagali ya biyo baya.





An ci an sha an caskale ba karya masu rawa sun yi rawa, marasa rawa sun yi kallo, sai 7 kafin su ILHAAM su koma gida in da kowa ya koma a gajiye ILHAAM kaman zata kifu don ma bata sallah ne yasa ta bari.




Ta na dawowa sai wanka Anty Fauxiyyah ta na gama bata ɗure-ɗuren ta da aka saba, don shi kaɗai ta ke sha, ba jimawa ta bingere don ta ce wallahi yau babu gyran jikin daren da za'a mata, (ni kam na ce kin yi wa kanki)
daga nan ta kwanta kasanncewar gobe in da zai kama Saturday kuma program ɗin 8pm su ke dashi.



*********
*JESUS OWN STATE (JOS)*
Murmushi d'auke akan kyakkyawar fuskarta, saɓanin hawaye, murmushi take ta yi tun wayewar garin ranar, wanda ya matuƙar bawa Goggo da Hajar mamaki, ganin tsawon shekara goma sha tara(7) bata taɓa magana ba ballen tana wani abu makamancin wannan.


Hajar dai farinciki ta ke yi ganin Ummynta na murmushi, don tasan tun ta na ƙarama bata taɓa jin maganan Ummy ba, amma yau sai gata ta na murmushi,




*WAYE MALAM BABAYO*
Cikekken sunansa shi ne Muhammad Dauda, wanda aka fi saninsa da Babayo kasan cewar ya ci sunan Kakansa.




Haifeffen jihar Gombe ne a ƙauyen *KOMFULATA* dake karamar hukumar *ƘWAMI*,wanda kasuwanci ya mai dashi JOS, ya na da mata ɗaya mai suna Amina (Goggo) sai `Yarsu guda ɗaya tilo da Allah ya ba su mai suna Hajarah wacce Allah ya mata rasuwa, a wajen haihuwa in da ta haifi ya mace wacce suka mayar mata da sunan mahaifiyarta, (Hajar) Malam Babayo ba mai kuɗi ba ne, haka kuma ba talaka ba ne, wato dai mai rufin asiri,


kasuwanci shi ne ya maida Malam Babayo JOS daga baya ya so komawa amma karewar dangi sakamakon fadan ƙabilan da aka taɓa yi a cikin garin ya sa shi ci gaba da zama a JOS.



15-3-2002
A tsakatsakiyar daminar shekarar bayan an gama ruwan dare, da asuba Malam Babayo ya fito don tafiya masallaici a bakin kofa y aci karo da wata mata da take kwance bata san inda kanta yake ba, a cikin mutane masu bin hanyar don tafiya masallaci ya samu wassu samarin da ya sa su daga masa matar wacce bata wuce
20 ba, cikin gidan suka shigar da ita kana shi kuma ya wuce Masallaci.


bayan ya dawo ne ya yi wa goggo bayani abunda ya faru, kwata-kwata Goggo bata nuna zata iya kula da wannan matar ba, saboda taga yanayinta, babu ɗigon walwala a fuskarta ta furta Allah ya kyauta.




Sai da wannan Matar wacce Baba (Babayo) ya sawa (Aisha) ta kwashe tsawon wuni ta na baccin da basu san me ne farkonshi ba, ko abunda ya saka ta yinsa ba.




Sai dai sun yi mamakin abunda suka gani bayan farkawanta, domin kuwa akwai alamomin da suka gani, bayan na rashin magana da sauransu.....✍🏻




09139216255
Sadeey*LAULAM*
( _Kishiyata_)




*Alk'alamin Sadeey ce✍️*




*BARKANMU DA SALLAH, FATAN ANYI SALLAH LAFIYA, ALLAH UBANGIJI YA MAIMAITA MANA.*


*Page....35&36*




______A ranar data farka da rana Goggo tace wa baba kaman shatu jego takeyi, don tace taga Nononta suna zuba alamun ta haihu amma ba'a sha su ba,wannan abun ne ya k’arasa Malam Babayo tausayinta.





Gidan Malam Babayo gidan rasuwa ne domin a ranar `Yarsa ta rasuwa ta bar jinjira mace, wacce ke hannun Goggo.




Abunda ya faru a ranar da daddare yayi mugun ba wa Goggo mamaki, da ma tsoro,


Da daddare inna da shatu suna kwance da wannan jinjiran sai ta fara kuka irin wanda jarirai ke yi idan sunji yunwa da dare.




Goggo taji kukan yarinyar tamkar a mafarki daga baya sai taji shuru, jin yarinyar tayi shuru yasata tunani ko bacci ta koma, amma bayan minute sai ta fita waje don zagayawa.




Bayan ta dawo ne kasancewar akwai wuta yasata zuwa wajen makunnan wuta ta kunna, don ganin komai a D'akin.





Abunda idonta ya gane matane yayi mugun bata tsoro, da al'ajabi.



*********
8:30pm su ILHAAM sun gama komai na shiri domin yau ma kaman jiya daga meemy sai ILHAAM, sai dai wannan karon ba IMRAAN ba ne ya Kira Meemy Ahmed ne ya kira Meemy kasan cewar sunyi ya bata number'nshi, don haka yau ma tare suke zaune,





Sai after 9 kafin Ahmad ya kira Meemy cewa suna compound d'insu ya fito, da toh ta amsa.






Zaune yake yau ma a Kujeran baya kaman jiya, sanye yake cikin milk d'in shadda sai maiko yakeyi yana shining, wanda ya samu aiki da brown din zare,kayataccen gashin kansa bak'i sidik ya sanyawa brown d'in hula, haka ma farar kafarsa sanye take da brown din cover shoe kasan cewar sa ma'abocin sa cover shoe ne, haka ma tsintsiyar hannusa sanye take da Agogon fata shima brown colour, sai dai kamilalliyar fuskansa dake hade babu alamun annuri akan fuskar.






tafiya suke cikin takunsu na cikakkun yan mata masu ji da kyau da kuma aji, wad'anda taurarinsu suka fara haskawa,Meemy fuskanta d'auke take da murmushi mai d'aukan hankali,a yayin da fuskan ILHAAM kuma akasin haka ne, domin fuskanta a had'e take tamkar wacce bata tab'a dariya ba.






Tunda ta fito ya zuba mata idanu yana mai ayyana abubuwa da dama a ransa, sanye take cikin gown pink and silver colour mai shegen kyau Takalmanta da Head d'inta sun kasance pink, a yayin da abun wuyanta, Agogon, da Purse d'inta suka kasance silver, ga make-up d'in fuskanta simple mai shegen kyau.





Kauda fuskansa yayi sakamakon turarenta mai sanyi kamshin daya bugi hancinsa saboda bude K'ofar Motar da tayi,





A yau kam Meemy bata je wajen IMRAAN ba kasan cewar Ahmed ya sanar mata.




ILHAAM kuwa abunda yasata yin hanyar motar saboda decon da akayiwa Motar da red an white flowers, wanda ko ba'a fad'a ba tasan Motar amare ne akewa wannan decoration d'in.





A yauma kaman jiya Motar Ahmed ne a gaba sai Motan su IMRAAN wanda yau ba Alee bane ke driving kaman jiya, Sa'id ne daya kasance abokin su shima,







A yauma kaman jiya kawayen a tsakiya suka sakasu inda sukuma suke sanye da maroon gown sai pink head, ba k'aramin kyau sukayi ba, sai dai masha Allah.




An fara gabatar da program cikin ikon Allah da aminci, ba tare da wani cikas ba.




Yau d'inma dai bata changer zani ba, domin rawa kam anyi ba laifi, anci an sha an shashe.




chan na hango *ILHAAM FAN'S GROUP* suma baa barsu a baya ba , don su Aishatu Sa'idu rawa suke tayi ba k'akkautawa.




Sai da aka kusan tashi kafin a raba souveniars wanda aka bawa mata ko wacce paper back mai d'auke da photo amarya da ango, wanda ko ni bansan me aciki ba.




Sai 12 kafin kowa ya koma gida cike da gajiya, (fatan Allah ya bada zaman lafiya)



**********
washe gari daya kama Sunday kenan har bakin nesa wassu sun fara tafiya domin a daren za'a kai ILHAAM wacce ko baccin kirki batayi ba domin kuka shine abun ta kwana tanayi washe gari ta tashi da mugun zazzabi wanda ya hanata fita ko nan da chan,
tun Safiyar ranar IMRAAN ko shiga bai yi ba kasan cewar tunda aka fara biki ya kaura daga gidan ya koma wani guest House d'in Abba wanda yake Old gra.




9.PM, na dare zuwa wannan lokacin gidan ya watse sai tsirarun mutane ne kad'ai suka rage.




*****
Mamy ce zaune akan sallaya a D'akin IMRAAN na da, wanda tunda aka fara biki anan take, tunda da ta idar da sallah bata tashi ba, saboda ganawar sirrin da take da ILHAAM wacce ke zaune a gabanta, kus-kus takeyi wanda ko ni Sadeey banji me take cewa ba, nadai ga ILHAAM sai sunne kanta take k'asa alamun maganganun suna bata kunya, domin sun kai morthen 1hour suna magana.




Bayan sun gama ne, ta d'auki wayanta dake gefenta, danne-danne tayi a kai na wassu minute sannan ta kara a kunnenta zuwa wassu seconds naji tace

"kasameni a dakinka,


difff! ta kashe wayan tare da ta kalli ILHAAM wacce tayi kasa da kai sakamakon maganganun Mamy da kuma zazzabin da yake ta nuk'ur-k'ursanta,Wanda taki gayawa kowa,
saboda tsoron magani.




Shigowar IMRAAN ne ya dawo da ita daga dogon tunanin data tafi.




Amsa masa gaisuwar sa tayi tare da nuna masa gabanta Inda ILHAAM ke zaune,



zama yayi daff da ita, don har jikinsu yana goguwa, sannan ya sadda kansa kasa, sai ya kasance suna fuskantar ta.







hannun IMRAAN ta kama ta Dora akan hannunta na dama,asannan ta dauki na ILHAAM ta dora akan na IMRAAN kana ta d'auko daya nata ta Dora akai sai ya zamana hannunta a farko wannan kuma a karshe, shuru tayi sai kuma
Hawaye suka fara silalo mata a kan kunshinta hannu yasa ta fakaici idanunsu ta goge hawayen.




Kana ta kallesu tare yin guntun murmushi kana tace".....✍🏻








*Sadeey ce✍️*

*LAULAM*
( _Kishiyata_)



*Alk'alamin Sadeey ce✍️*




««•––––––––––––––––––•»»
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

•««––––––––––––––––––»»•





*Page 37-38*



_____"Idan nace bana farin ciki a yau to ba gaskiya bane, ina farinciki kaman ko wacce uwa! inajin dajin da ko wacce uwa takeji idan ta aurar da `Ya`yanta.



Sai ga kawaye suna zuba a idanun Mamy at the same time kuma ga murmushi kwance akan fuskarta.




Damke hannayensu tayi sannan ta fara cewa,



"ILHAAM, IMRAN Yayanki ne kuma mijinki, don haka ki basa girmansa a matsayinsa na mijinki sannan ki mutuntashi ki darajashi saboda abunda manzon Allah (S.A.W) yace

*~"da bawa zai iya yiwa wani sujjada bayan Allah, to da nasa mace tayiwa mijinta~*




"Don haka duke abunda yace kiyi kiyi Indai bai sa6a wa Shari'a ba,haka ma idan yace ki bari to ki bari ba tare da jinkirtawa ba,banda raini duke da nasan halinki ILHAAM ke ba mai raina na gaba dake bane,amma dole na tuna miki karki raina mijinki, domin miji ba abun rainawa bane, miji ya wuce gaban wasa,

fatan kinji abunda nace,


"Insha Allah


sannan ta juya ga IMRAAN tace




" IMRAAN!!!


"Na'am

kaji tsoron Allah ka kula da hakkin matar ka dake kanka,IMRAAN kayi koyi koyi da mahaifinka bai taba muzguna min ba,don anyi mana *auren dole* har na haifeka zaman hakuri mukeyi domin banason juna, IMRAAN ILHAAM marainiyace ka kula da maraicinta,karka zalunceta don kaganta mace,wallahi idan ka zalinceka Allah bai zai barka ba, IMRAAN kayi mata adalci IMRAAN karka *HA'INCETA* (my second novel💃💃💃) don kaga tana gida,ka rike ta amana na baka ita ka rikemin amanan `*Yar amanata*
don nima amana ce a wajena.



ILHAAM kam babu magana don kuka take har sai da Gavan hijab dinta UA jike,


shi kansa IMRAAN jikinsa ba karamin sanyi yayi ba,don da badon ya daureba ba shima sai dai aka yana hawayen,


daga nan suka wuce pallon Abbah Inda yake zaune da daddyn Faisal, don musu nasu nasihan,




Daga Abbah har daddy kowa ya musu nashi mai ratsa miki Wanda ya karawa ILHAAM imani,a zuciyar ta,har takejin zata rungumi kaddaranta,

daga nan aka rufe taro da Addu'a.


ILHAAM ce ta Matso gaban Abbah ciki mutuwar jiki irinna mai zazzabi,


ta fara magana cikin kuka Wanda tayishi har ta gode,don har tana cid'ewa,

tace"Abbah bani da bakin gode maka domin ka gama min komai na RAYUWA kayi min Abu da mahaifina bai min ba, babu abunda zan iya ce maka sai dai Addu'a Mara yankewa,


dan Allah a zamana da mai idan na bata maka rai kayi hakuri ka yafemin,ta karasa maganar tana kama kafafusa tare da gashewa da kukan daya kara karya zuciyar Abbah,




"a zama na dake babu abu da kika taba min domin ke yace ta gari wacce ko wani abu zayyi alfahari d ita,
hatsalima nina miki laifi ta hanyar aura miki Wanda bakyaso bakisan shiba, don haka na yafee miki Allah ya baku zaman lafiya da zuriya dayyiba ya karasa maganar hawaye na silalowa,


daga nan ILHAAM gaban daddy taje shima ta nemi yafirsa kuma ya yafe mata,


mamy ce ta dauketa don karasa gaya mata wassu abubuwan,


ILHAAM inaso na tunatar dake cewa *Zaman aure* sai da *Hakuri*
idan bakiyi hakuri ba wallahi bazaki mori komai ba zaman duniya, domin dole wassu abubuwan kiji kik'i ji, gani kik'i gani,idan kuma bakiyi *Hakurin* ba bazaki iya kyalewa,ni kaina da like ganin da bandon HAkiri ba da van kao wannan matakin ba,


ILHAAM ina mai horanki daki kasance mai tsafta a ko wani hali kike kada ko bari wani ya ganki da wani aibu na kazamta,nasan kinada tsapta Amma ki Kara domin zaman aura sai da tsafta.















Idan nace bana farinci a yau to ba gaskiya bane, ina farinciki kama wacce uwa! inajin dajin da ko wacce uwa takeji idan ta aurar da 'ya'yanta,sai ga kawaye suna zuba a idanun mamy at the same time kuma ga murmushi kwance akan kamilan fuskanta, damke hannauesu tayi sannan ta fara cewa,


ILHAAM, IMRAN *yayankine kuma mijinki* don haka ki basa girmanasa a matsayinsa na yayanki sannan ki mutumtashi ki darajashi saboda abunda manzon Allah (S.A.W) yace

*da bawa zai iya yiwa wani sujjada bayan Allah to da yasa mace tayiwa mijinta* don haka Duke abunda yace kiyi kiyi India bai saba Shari'a ba,haka ma idan yace ki bari to ki bari ba tare da jinkintawa ba,banda raini duk da nasan ke ba mai raina na gaba dake bane, amma dole na tuna miki karki raina mijinki, domin miji ba abun rainawa bane, miji ya wuce gaban wasa, juyawa tayi kan IMRAAN sannan tace




" IMRAAN!!!
ba tare da tajira ya amsa ba taci gaba da cewa




"kaji tsoron Allah ka kula da hakkin matar ka dake kanka, kayi koyi halayen da mahaifinka bai taba muzguna min ba, don anyi mana *Auren dole* har na haifeka zaman hakuri mukeyi domin bamason juna, ILHAAM marainiyace ka kula da maraicinta, karka zalunceta don kaganta mace, wallahi idan ka zalinceka Allah ba zai barka ba, kayi mata adalci, ka rike ta amana na baka ita ka rik'emin amanan

Please Login or Register in order to submit comment