Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

*`Yar Amanata*
don nima amanace a wajena.





Kuyi hakuri ku rike juna, karki muzgunawa juna, zaman Aure sai hakuri, shi zaman Aure zaman zomu zauna zomu sab'a, kuyi hakuri dan Allah, kiji tsoron Allah, ku rike junanku, kybk'aunaci juna, kuso junanku.




ILHAAM kam babu magana don kuka take har sai da gaban Hijab d'inta ya jik'e,




Shi kansa IMRAAN jikinsa ba k'aramin sanyi yayi ba, kawai dai saboda yana namiji me.




Daga nan suka wuce palourn Abbah Inda yake zaune da Daddyn Faisal, don musu nasu nasihan,




Daga Abbah har daddy kowa ya musu nashi mai ratsa miki wanda ya karawa ILHAAM imani, a Zuciyar ta, har takejin zata rungumi kaddaranta ta zauna da mijinta,




ILHAAM ce ta Matso gaban Abbah ciki mutuwar jiki irin na mai zazzabi, kana tace



"Abbah bani da bakin da zan maka godiya, amma duk da haka bazan Gaza ba wajen yi maka, Abba Nagode!
Nagode!
Nagode, Allah ya saka ya biyaka da gidan aljanna.




Cikin muryan kuka ta k'ara cewa "Abbah a zamana dakai idan na ta6a maka rai ko wani abu don Allah kayafe min ta k'arasa maganar tana kama kafafunshi,




"Ba abunda kika min Mamana, amma na yafe miki,



"Nima ina neman afuwarki na aura miki wanda baki sonshi baya sonki,





cikin kuka tace "bakamin komai ba ka isa dani ne shiyasa kamin,




kafin Mamy ta d'auke ta don k'arasa wassu abubuwan da basu fad'a ba,


inda IMRAAN ma yazauna don karban nasa lesson d'in.




ILHAAM wacce zuwa Yanzu har idonta ya kumbura abunka da farar mace sai fuskanta tayi jaa zir.



Bayan gama magansu toilet Mamy ta fad'a ta had'a mata ruwan wanka tare da zuba turaruka.




Bayan ta fito ne ta samu Mamy ta ajiye mata zanin julius d'in atamfa mai shegen kyau, d'inki riga da sikat, kana ta mika mata less mai shegen kyau da daukan ido mara nauyi, wanda Mamy ta mata order'nshi wajen Oum Juwairiyya, kalan
milk colour mai ratsin brown, sai Veil brown da takalma flat shoe shima brown, bayan ta gama shirinta sannan *Beauty and beyond* ta ta mata simply make-up , Mamy ta d'auko turare ta fesa mata, tare ta rungumarta sai kuma ta fashe da kuka, itama ILHAAM kukan take tare da cewa

"Mamy ki yafemin a yau ina mai bakin jin bakin cikin rabuwa dake,nasan kinmin komai na rayuwa ke da Abbah bani da bakin gode muku sai da fatan karshe mai kyau, kara rungumeta Mamy tayi tana mai bubbuga bayan ta tare da cewa "na yafe miki duk da ma bakimin komai ba.



Meemy ce ta shigo don neman ILHAAM wacce take kuka tunda ta tabbatar da zata rabu da `Yar uwarta wacce suka tashi tare kaman yan biyu, ganin Mamy rungume da ita ne, yasata itama joining dinsu tare da cigaba da kukanta,


IMRAAN ne wanda suka gama masa nasa ganin dare yayi yasa Abbah ce masa yaje ya d'auko matarsa su tafi dare yayi, domin yace babu rakiya ya dauko matarsa, don haka yayi D'akin sa don yasan anan su Mamy suke amma abunda ya gani ya karya masa zuciya, da sauri yayi kansu tare da shiga group din shima yana jin idanunsa na tsatsatsafo da ruwan hawaye,




Haka suka rungume jinansu suna masu kukan rashin jin dadin rabuwa da junansu,




Abbah ne ganin time yaja kuma baiji alamun tafiyar su IMRAAN ba, ya tashi yayi hanyar cikin gida,


da tamvaya ya samu aka nuna masa inda su Mamy suke,



ganin su a haka ba k'aramin karyar masa zuciya yayi ba,




shima joining yayi sukayi family hug, sai yaga sunyi mai isarsu kafin ya ce




"to ya isa haka,haba Mamyn yara ke da ya kamata ki rarrashesu shine kuke kukan tare? "haba dai,ya k'ara sa maganar yana yana rabasu tare da cewa muje mu rakasu,




Haka suka rakasu har bakin mota,




ILHAAM na ganin za'a tura ta mota sai ta rungume Meemy tare da fashewa da kuka tana cewa



"zanyi kewarki Yar uwata

"Nima haka daga nan suka bude babin kuka cewar Meemy



Abbah ne yayiwa mamy maganan ido,akan taje ta rabasu,


Mamy tayi-tayi amma abun ya faskara,Dom sunki RABUWA, sun manne tamkar dank'o.



IMRAAN ne yaja tsaki ganin dare na k'ara yi,



yasahi zuwa gefen da suke,

hannu yasa ya musu rabiyar karfi, ba tare da yayi magana ba ya tura ILHAAM Mota da hannu ya nunawa Meemy hanya,wacce ba musu tayi cikin gida da gudu tana toshe baki.



Sai dai safe yayi musu tare da shiga mota, a yayin da mai gadi ya bude masa Get yayi waje abunsa, yabar daddy da lallashin mamy wacce hawayenta suka k'i tsayawa,



Acikin motan bakajin karan komai sai na sheshshekar kukan ILHAAM wacce yanzu take kara jin kewan gida, da bakin cikin auren da aka mata, ga zazzabin daya dawo mata saboda har tana ganin duru-duru,


k'iiiiiiiiiiiii da taji ne yasa dagowa ta kalli gaban motan ganin babu komai yasata mai da kallon ta kan IMRAAN,


*LAULAM*
( _Kishiyata_)



*Alk'alamin Sadeey ce✍️*




««•–––––––––––––––––•»»
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

•««–––––––––––––––––»»•



*Page 39&40*


*JOS...*
______Shatu ke shayar da marainiyar jinjirar wacce take ta zuk'an ruwan nono cikin saurin da ke nuna dama a a buk'ace take,




"Innanillahi hande mi woni min Sato, (yau na bonu na ni sato (Amina) mai zan gani haka? Sallamin da ta yi ne ya ya tayar da Malam Babayo da ke bacci a dakinsa, ba shiri ya fito ya na ce wa



"Aminatu lafiya naji kinata sallami acikin silsilin daren nan?



Babu bakin magana, domin kuwa da hannu ta nuna masa gurin da Shatu ke jingine ta na ta bawa baby nono, tana mai k'arasa shiga cikin d'akin, ta yi kansu gadan-gadan don zuwa wajensu Shatu da niyyar ta kar6e babyn.



Gane me take shirin yi ne ya sa Malam Babayo cikin sauri ya ce



"dakata! Aminatu, me kike shirin aikatawa haka?



"K'wace yaron zan yi, ta karasa magana cikin bacin rai,


"Ki barta kawai ta sha ina ga basai kin kwace ba.



"Ya zaka ce na barta, ka na nufin na barta taci gaba da shan nonon mahaukaciya?



danne bacin ran da yaji ta kirata da mahaukaciya ya yi, kana ya ce "eh haka na ce.



Shatu wacce bata san me suke yi ba, domin ita bacci ma ta ke yi, tana mai sauke ajiyan Zuciyan dake nuna tabbas ba k'aramin dad'in ta ke ji ba, da aka sha mata su.




Goggo ganin yarinyar ta k'oshi har ruwan nonon ya fara zuba, alamun Yarinyar ta daina zuk'a, ya sata d'aukan Babyn ta kwantar da ita tare da gyara mata kwanciya, wanda har ta yi bacci abunta.




Tuk daga ranar Shatu ce ta koma shayar da Baby (Hajara) wacce suka mayar mata da sunan mahaifiyarta,




Sai dai tun ranar bata sake d'aukanta da kan taba,


Sai dai idan Yarinyar tayi kukan sai Goggo ta d'ora mata yarinyar tare da ciro nonon daga cikin rigarta,hakama idan ta k'oshi itake cire nonon daga bakin Hajara sannan mayar mata a cikin rigar.



Haka RAYUWAR tayi ta tafiya, tunda wannan mahaukaciyar tazo gidan bata taba fita ko nan da kofar gida ba, domin ba'a barinta ta fita.



Haka Hajara tayi ta girma, har ta kai lokacin yaye wanda da taimakon goggo aka yayeta ta hanyar hana bata nonon koda tana kuka,wanda kuma abun mamaki damuwa k'arara take hangowa cikin idanun Shatu, domin har sai da takai ma Hajar ta fara kwana da Malam.


Domin idan dare yayi Hajar ta fara kuka, kafin goggo ta farka a wassu ranakun takan samu Shatu tana neman bawa Hajar nono, wannan dailin yasa Malam cewa Hajar ta dawo da kwana a D'akinsa har sai Shatu ta fara sabawa kafin ta koma.




Domin goggo ta lura cikan nonon ke damunta yasa take neman abunda zai rage mata su.



Cikin ikon Allah har Hajar ta saba, hakama Shatu tunda Mamanta suka daina zuba sai ta daina damuwa.



A dá Goggo najin haushin Shatu idan taga yadda Malam ke kula da ita,amma daga baya data lura tausayine sai ta yasar kawai.




Hajar tana tunda tayi wayo bata da uwar data wuce Shatu.



Mahaifinta shine Wanda ya fara nuba mata Shatu ba mahaifiyarta bane, sai dai ko da ta girma babu abunda ya canja akan lamarin, haka kuma ita ta fara ce mata Ummy.





Wani dare shatu na kwance da Hajar, kasan cewar tunda hajara ta girma basu tab'a raba D'aki ba, don tare suke kwana, don a yanzu takai shekara goma sha takwas.




Hajara bata sani ba, ta tafi da daren ba tare da wani na gidan ya ganta ba, inda Allah ya so bata fita cikin JOS ba, amma tayi nesa dasu a yayin da ta tare cikin wani juji.




Ba k'aramin tashi hankalinsu yayi ba, especially ma Hajar don sai 6atan Ummyn yaso tab'a mata walwalanta.



Wacce sai da ta kwashe kusan wata biyu kafin Baba(Malam Babayo) ya samota a wani anguwan, dalilin zuwan gaida wani abokin kasuwancinshi, da baida lafiya.




Wannan kenan.





*Back to labari*

A 6angaren su IMRAAN kuwa,



"wallahi idan kika kuskura na sake jin kukanki a cikin motannan, sai kin bar min mota, ya k'arasa maganar yana cije lips d'inshi na k'asa.




Shuru tayi tamkar ruwa ya cita, don dama kuka da zazzabin su gama galabaitar da ita, ko bai yi magana ba dama zatayi shuru.




Tada moyar yayi kana suka kama hanyar federal lowcost.



A 6angaren su mamy kuwa,



Gidan ya yazamo musu tamkar rami,don ji suke tamkar mutuwa akayi a gidan,saboda rashin mutum biyu.



Mamy dai Abbah tasa a gaba tana ta hawaye, a yayin da shi kuma yake aikin rarrashinta, duk da shima ba k'aramin dauriya yake ba.





Meemy kuwa tunda IMRAAN ya koreta, ta shiga D'aki take ta kuka, wanda Allah yasa Ahmad ya kira ba'a jimaba yake ta rarrashinta.



★★★★★
Tafiya ba mai tsawo sosai ba sukayi ya kaisu gaban wani flat house
mai shegen kyau, wanda tsaruwarsa kad'ai zai nunawa mai kallo ba k'aramin kud'i aka kashe masa ba.



Tsayuwa yayi a bakin get d'in, kana yayi horn, ba jimawa mai ganin yazo ya wangale musu get.



A filin da aka tanada don ajiye motoci yayi parking gefen wassu manyan motoci guda biyu.




Fitowa yayi tare da amsa gaisuwar da mai gadin yake masa, yayi hanyar wata K'ofa wacce nake tunanin itace zata sadashi da asalin cikin gidan, key ya d'auko a cikin aljihunsa sannan ya b'ude K'ofar, sallahma yayi tare da saka kafar damansa a cikin parlour.




Jin kaman bata biyoshi bane yashi juyawa,ganinta zaune a cikin mota ya kara hatsalashi,



Cikin daga murya kadan yace



"Wallahi karki bari nazo na sameki a wajennan don na lahira sai ya fiki jin dadi, da kika zauna zamanme kikeyi a gurin? Ya k'arasa maganar yana k'arasa shiga cikin parlour tamkar bashi yayi maganan ba.




ILHAAM wacce zazzabi ya shiga jikinta sosai ga kuma sanyin da takeji yana shiga cikin nama da kasussuwan jikinta, ba shiri ta fido da kafafuna wad'anda sukasha jan lalle sukayi kyau waje, tare da fitowa gaba daya, hanyar da taga ya bi ne yasa bin ganyar itama,




Hannunta ta na dama ta daura akan Handle d'in K'ofar tare da yin bismillah,sannan tasa K'afan dama tare da yin sallahma, kaman yadd Mamy tace tayi.





Sanyin Ac may had'e da khamshin turaren wuta,dana Room freeshner, tare da khamishin sabon wuri,suka had'u wuri suka bada wani kamshi na musamman, su ne suka hancinta a lokacin data sa kanta a cikin palourn.




"Masha Allah shine abunda nace, ganin tsaruwa da kyawun da palourn yayi,
Kujeru ne Royal masu kyawun gaske ash colour, labulaye, karfet suma ash, sannan K'aton telebijin dake facing d'in K'ofa.



Palourn bashi da wani shirgi, sai dai ba k'aramin haduwa yayi ba.





ILHAAM kam zama tayi a akan d'aya daga cikin kujerun dake cikin palourn.



Kallon agogo ash colour dake manne a bango ta saman TV, tayi ganin sha biyu 12 ta gota yasata sauke numfashi tare da kallon dayan gefen da aka ajiye wassu frames guda uku, daya ita da IMRAAN a ranar juma'a kafin su tafi reception, a dayan ma itada shi amma na ranar dinner, sai dayan kuma daya kasance family picture ne domin taga Abbah, Mamy, IMRAAN, Meemy, ita,wanda suka dauke shi ranar juma'a duk hotunan ba k'aramin kyau sukayiba.



K'aran mord'a Handle d'in d'ayan K'ofar da ta taji ne yasata kallon wajen,


IMRAAN ta gani sanye cikin mayan bacci alamun yayi wanka.



"Ke! ya fad'a da d'an karfi, don wallahi ya manta da wata halitta ya shigo gidan,yanzu ma ruwa ya fito d'auka da ya kwanta.




"Meya zaunar dake nan? ya k'ara jefo mata tambaya,



" jimin tambayar rainin wayo a wajen mutumin nan, ILHAAM ta raya a ranta,




ganin bata amsa bane yasa ya ta6e baki tare da fara haura dan steps din a akayi don is a Dining Room, sai da ya d'auko bottle na ruwa kafin yace mata "biyoni.



Tashi tayi tare da bin bayansa, kaman jela.



Bayan sun shiga ta k'are wa wajen kallo ganin nan d'inma parlour ne, wanda bai kai wancan girma da tsaruwa ba, da hannu ya sake nuna mata wata kofa a yayin da shi kuma ya bud'e wata kofa ya shiga.




Inda ya nuna mata ta yi tare da murd'a Handle d'in ganin wani corridor ne, sai wassu kofofi da suke opposite din juna,




Da na hagun fara, ganin dakine da toile mai shegen kyau babu wani tarkace a dakin daga furniture's d'in shi kenan, babu wani abu,
Fitowa tayi, kana tayi dayan kofar dake kallon wanda ta bud'e.



Shiga tayi shima, sai dai wannan ta gane shine dakinta,saboda taga favourite colour dinta, watoh light brown and milk, kana ga Boxes d'inta a jire a gefen gado.



k'arasa shiga tayi kana ta zauna abakin gado tana sauk'e numfashi.



Yana shiga dakin sa daya gaji da had'uwa shima ba jimawa ya kwanta kasan cewar bacci yakeji, amma sai dai ina ido yace baisan da zancen ba, tunani yake a ransa, yabi abunda zuciyar sa take gaya masa, ko kuwa? bayason raini ya shiga tsakaninshi da yafinyar nan kwata-kwata,



Amma koma mene ya san dole wata rana za'a zo wajen, da wannan tunanin ya juya baya.



Sai after 2 kafin ILHAAM ta gama komai cikin shirinta na kayan bacci riga da wando,fari mai ratsin pink, don Yanzu da tayi wanka da ruwa mai zafin gaske taji zazzabin yadan sauk'a mata, wayanta ta d'auka ta fara dann-danne, domin idonta ya bushe batajin bacci, sai after 3 ganin har yanzu batajin alamun bacci yasa kawai shiga Toilet ta d'auro alwala ta Fara nafilfili, wanda bata tashi akan sallayanba sai bayan asuba,komawar kwanciyarta ba'a jimaba IMRAAN ya shigo da niyyar tada ita,


Kallo ya kare mata kasan cewar bata rufuba, kafin ya fara tada ita ta hanyar d'aka mata suka wanda ya tada ILHAAM ba shiri,



Ganin ta bude ido ne yasa shi tamke fuska cikin tsaren gida yace

"tashi ki yi sallah
ya fad'a cikin yanayin dake nuna kaman an masa dole.



Shuru ta yi tak'i magana don bakarami shak'a ta yi ba, da irin salon tayar da itan da ya yi ba.


Wai "ba ki ji abunda na ce ba ne? cewar Imraan ILHAAM ta ce "To ban yi ba ne? Imraan ne ya ce "yaushe kenan?"


"Tunkafin kayi tun kafin ta yi, cewar ILHAAM,



Acikin ransa yake raya lallai Yarinyar nan, kin raini amma ba komai, zanyi maganinki.


Daga haka ya fita ba tare da ya sake magana ba.


11 ta na bacci taji an fad'o kanta, ihu tayi ta mike ba shiri,ganin Meemy ce yasata jan tsaki tare da ce wa



"Amma wallahi kin cuceni, mutum bacci ma ba za ki samu ya maida ba, bayan jiya ban yi na dare ba,



Cikin dariya Meemy ta ce


"Ai na san ba ki yi bacci ba, ba sai kin fad'a min ba Hajiya,



Jin abunda ta ce ne ya k'ara hatsala ILHAAM ta ce


"Dallah sarkin changer magana ni kam ba abunda kike tunanin ba ne,



Dariya Meemy ta yi sannan ta ce "to abar kaza cikin gashinta,


"A figeta ma inji ILHAAM



ganin rana ta yi ne yasa ILHAAM tashi don yin wanka,



Wayan Meemy ne ya yi k'ara ganin wanda yake kira ne yasata picking tare da sallahma,


Daga cikin wayan taji ya ce


"Ta kawo min breakfast d'ina d'aki daga haka ya kashe abunsa,



Murmushi ta yi tare da ce wa "su Yaya IMRAAN manya,


"Ki kai masa breakfast dinshi dakin,



shuru ta yi batare da ta tashi ba,

Ganin ba ta tashi ba ne ya sa Meemy ce wa "ba za ki ne ba? "eh ba zan je ba" cewar ILHAAM



"zan gayawa Mamy baki dauki nasihu da fad'an da ta yi miki ba,


Sanin zata aikata ne ya sa ILHAAM mikewa tare da d'aukan katon Hijab dake nad'e akan sallaya wanda tayi sallah dashi da asuba, da niyyar zata saka.



Ai ba shiri Meemy ya diro daga kan gado tare da wabce Hijaab d'in ta ce "wallahi ba za ki je da wannan Hijab din ba,


Ganin yadda ta sha mur yasa ILHAAM tsumewa ita ma tare yin hanyar waje.




Hongo basket a kan dining ya sata yin hanyar, abinci ta had'a masa da komai akan babban try wanda ta dauko a kitchen sannan ta nufi karamin pallow, kofar dataga ya yi jiya ita ma ta yi.



Bud'ewa ta yi tare da sallama jin an amsa ya sata kutsa kai cikin d'akin IMRAAN ne ta gani zaune akan sofan dakin yana waya.


******
*JOS*

murmushin ne kwance akan fuskar Shatu, tamkar ba'a cikin yanayin hauka take ba.



Murmushin da suka gani ya saka sauran yan gidan ma farinciki, musamman Hajar da ta ke jinta a cikin tsananin farinciki.



Domin ji suke tamkar warakarta ne ya zo, gani suke kaman ta kusan jin sauki.



Da badon rashin magana da suka ka har yanzu ba ta yi ba, da wallahi babu abunda zai hanasu cewa ta warke ba.



Hakan yasa Malam Babayo siyo musu kasassun kaji da daddare suka zauna sukaci su ka yi hanik'an, kana suka bishi da madara mai sanyin gaske.



Malam Babayo duk da yana mamakin meya sanyata murmushi, ita da tunda suke da ita in banda hawaye babu abundan takeyi.



Don haka ya yanke dole zai fara nema mata magani, duk ya na ji a jikinsa tamkar sauk'inta ne ya zo.



Ba zai yi k'asa a gwuiwa ba, wajen nema mata magani, duk da kuwa jinkirin a ya yi akan hakan....✍🏻




*Sadeey ce**LAULAM*
( _Kishiyata_)



*Alk'alamin Sadeey ce✍️*




««•–––––––––––––––––•»»
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

•««–––––––––––––––––»»•





*Page 41&42*



______Isa tayi gaban sa ta ajiye Trey d'in cikin sanyin murya tace "Ina kwana, "Lafiya kawai yace ba tare da ya kalli inda take ba.





Baki ta ta6e, ba tare da ce komai ba ta juya da niyyar tafiya.




Cikin kamewa ta tsinkayi muryan ya ce
"Zonan"




Juyowa tayi tare dawowa gabansa kana tace
"gani"


"da kika kawo abinci ina ruwan tea?


Ko haka zanci abincin?



Ba tare da tace ko uffan ba babjuya ta nufi kofa.





Kai ya kad'a yana mai jinjina miskilancinta,



Da isarta kitchen ɗin ta ƙarewa kallon ganin had’uwar da yayi.



Ganin tsayuwar bazata fishshe taba yasata bud’e drower tukunya kama ta d'auki tukunya guda daya, medium size.



Gass ta kunna kasan cewar an had’ashi, d'auraye Tukunyar tayi tare da saka ruwa kana ɗaura,


Bai ɗau lokacin ta tafasa saukewa tayi tare da juyeshi a flaks, sannan ta sake had'a wani tray mai dauke da ,cups Teaspoons, Sugar&Honey,sannan ta d’ora d’an madaidancin Flaks d'in akai ta fita,



Sallahma tayi tare da shiga,ganin yana zaune kaman yadda ta barshi yasata taɓe baki,


Haɗa masa tea din tayi tare tashi da niyyar sake tafiya, don wallahi ba ƙaramin haushi takeji ba,


Tsayar da ita yayi ta hanyar kada mata yatsu,



Zama ta ƙarayi tare da sauke numfashin ka isheni,




Plate d'in data rufe akan na abinci ya buɗe tare da tura mata gabanta,


Tea ɗin ya had'a sai daya cika cup ɗin ya k'ara tura matashi gabanta, tare da matsawa suka saka plate din a tsakiya, (ni Sadeey Inaganin ikon Allah)




Batace komai ba d'auki spoon d'in ta fara ci,
Abinci suke ci bakajn ƙarar komai sai na, fork da plate, duk da kuwa da spoon d'aya suke anfani, haka ma tea d'in.



Sai dai har suka gama, cin abincin sannan ta tattara tafitar dasu kitchen batare da magana na fatar baki ya haɗasu ba.




Bayan ta kaisu kitchen wankesu tayi tare da dan gyare kitchen d'in zuwa parlour, sannan ta koma
daki don yin wanka.


Zuwa wannan lokacin ma azahar ta kawo kai,



Duk tsiyar da Meemy ke mata na zaman da tayi bata kulata ba, karshe ma Toilet ta fad'a don wanka.


********
*MARU*


Hajiya Inna RAYUWA ta mata dadi, fiye da daa domin Yanzu ko izinin kiwo idan bata bashi ba bazai jeba, ga kuma abunda ta tsira na saida shanu ba gaira ba dalili,




Bappah ya rame yayi baki, domin sai da shanun nan shi yafi komai damunshi don yasan shanun ba nashi bane, amma bazai iya mata magana ba hasalima, shi bai san shanun waye bane, sai dai bazai iya tuna na waye bane,




Sai dai mafarkin da yake har yanzu bai daina ba, amma ya canja masa salo.




Haka kuma zuwa yanzu hankalinsa ya fara dawowa jikinsa, domin a yanzu ba kasafai yakejin tsoron ta ba.






Inna hankalinta a tashe, domin a yanzu boka kullum cikin sanar mata da asirinta na dab da tonuwa.



Sai dai tashin hankalin baya tasiri idan taga yadda ya ke mata komai cikin rawan jiki.
(Abunda bata sani ba, kuwa yanzu bayajin tsoron ta kaman da, )




*After one week*
A kwana a tashi asaran mai rai,har Aurensu IMRAAN ya cika sati ɗaya, kuma tunda akayi auren Mamy ce ke aiko musu da abinci, so yau 1 week daga yau zata fara girki,kuma ta gama komai na abincin dare,kasan cewar yanzu 2pm.





A yayin da oga IMRAAN kuma tunda yasa kai ya fita da safe bata sake ganin keyarsa ba, duk da tanason tayi masa maganan school, amma tana jin irin wani kasan cewar har yanzu zaman nasu sai a hankali, sai dai tasan duk inda yayi zai dawo kodon ruwan dake shirin saukowa.



2:40pm ya shigo gidan, bayan yayi sallan la’asar, leda ne a hannunshi mai d'auke da tambarin *BANDIRAWO SUYA*




Hanyar dakinsa ya nufa ya don yanason watsa ruwa,




A yayin da ILHAAM kuma take D'aki don bata jima da fitowa daga wanka ba.





Bayan wasu minutes ya fito cikin jallabiya fari kall sai ƙamshi yake zubawa kamar wanda yayi wanka da turare,




Dining ya nufa ganin Kuloli akan Dining d'in, buɗe su yayi duka,yanaso yaci amma kuma yana tunanin tayi ƙarama ta girka Abinci mai ma'ana, bayason cin abunda zaizo ya b'ata masa baki, amma bashi da wani option.




Shahada yayi kana ya ja kujera ya zauna tare ɗaukan d'aya daga cikin plates din d'aya gani a wajen.





Fried rice d'in ya ɗiba a gefe sai coslow sannan ya ɗebi pieces din kazan, kana ya matsar da bottle ɗin kunnun aya, yayi bismillah, ya fara hambud'a.





Hmm abun daya bawa IMRAAN mamaki sai da ya cinye wanda ya dibo tare da shanye Bootle na kunun aya, Alhamdulillah yace "tare da mik'ewa yana mamakin yaya akayi wannan Yarinyar ta iya girki haka, koma dai yaya ne chan mata.




3:40pm
direct d’akin ILHAAM ya nufa bayan yaje d’akin shi yayi alwala tare da sake brush, samunta yayi a kwance akan gado tana danna waya kasan cewar taci nata tun kafin ya dawo,




Ciki tsare gida yace "Tashi kije kiyi alwala,


Ganin yanayin fuskansa yasata cewa "toh",bayan ta fito ne.




Sallaya ya shunfud’a tare da nuna mata bayan sa. A bayan sa ta tsaya bayan ta sanya Hijaab,





Sallahn la’asar ya jasu kana d'ora raka'a biyu tare da dafa goshinta yamata Addu'a, tare da tambayoyi akan addininta, bayyi mamakin jin ta amsa masa komai ba,kasan cewar yasan ita d'in rainon Mamyc
Mamy ne.




Ledan daya shigo dashi ya bud'e tare mata bismillah


"nakoshi ta fad'a cikin sanyin murya, don ba k'aramin tsorata tayi da lamarinsa ba,




" Zokici shine abunda yace,



Don dole yasata cin Naman da bata san hanyar da yake bi ba.


Suna gama ci bayan sunyi brush,
ya sauke labulaye sannan ya kashe wutan dakin nan take duhu ya gauraye D'akin, tare

Please Login or Register in order to submit comment