Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

ο»ΏπŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦
*MATAR UBA*
πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦
_(A True Life Story_ )
*Short story*
```Story and written by FADEELAH YAKUB (MILHAAT)```
Follow me on Wattpad @milhaat
Join my group on Telegram https://t.me/joinchat/IhnmqM7EjtZ02IV0

🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCATION* πŸ“šπŸ–ŠοΈ
_('Kungiya d'aya tamkar da dubu)_ _____________________________
*MATAR UBA* Labarine Wanda ya faru dagaske banyi shi don cin zarafin kowa ba face don nayi wa Yan Uwa Mata nasiha, idan yazo dai dai to akasi aka samu, Allah ubangiji Ina rokon ka ka bani ikon rubuta abinda zai amfani Yan Uwa musulmai, kamar yanda na Fara lafiya Ina rokon ka kasa na gama lafiya AMEEN.
Dedicated to *MUHAMMAD KARIM MK* much Love.

```CHAPTER 1```
Zaune na gansu a Kan sallaya da alama sun idar da sallah ne. Yara ne Mata Wanda baza su haura shekaru Sha hud'u a duniya ba.

Bangaje kofar tayi ta shigo tana huci Tace "Ke Asiya don ubanki Ni sa'ar kice da d'azu mijina Yana min magana Kika sa Mana Baki?"
Wacce aka Kira da Asiya sai rarraba Ido take ta kasa cewa komai idanun ta sun yi jajir cike da tsoro da fargaban abinda zata Mata,finciko ta tayi tana jaaan kunnen ta Tace "Daga yau idan Ina magana da mijina Wanda ya auro Ni a matsayin matar sa Yana min magana Kika sa min summan Bakin ki" tana maganar tana Jan bakin ta.
"Kar na Kuma ji ko gani kin fad'a Masa cewar bana kyauta ta muku kina jina?" chan Ciki ta amsa da "Eh" maruka masu kyau ta shafa Mata sannan Tace "Kice Ni yar banzar yarinya ce" cikin kuka Tace "Ni Yar banzar yarinya ce" hankad'e ta tayi ta fad'a a kan gado, da sauri ta karaso inda take tana kokarin d'aga ta.
"To Munafuka Meyasa kike rike ta da alama Kema Marin kike bukata,kina hauka ne? Da nice na haifi kamar biri kamar ku da na dad'e da kashe ku" ba b'ata lokaci ita ma ta karb'i nata marukan guda biyu.
"Mahaukatan banza mtwwws" sai tayi ficewar ta.

"Anisah ki daina kuka kinji? Inda sabo ai mun Saba,tashi mu cigaba da addu'ar mu" hannu ta sa ta sharewa kanwar ta hawaye sannan suka koma suka zauna a Akan sallaya, Anisa ce ta d'aga hannu sama Tace "Ya Allah Kaine Allah ka ga abinda matar uban mu take Mana ya Allah ka Kare mu daga sharriin ta" anisah ta amsa da ameen.
Tashi sukayi, sukayi addu'ar bacci sannan suka kwanta.

*WASHE GARI*
Zaune take a parlor tana kallon TV hannun ta rike yake da remote ko me ta tuna sai ji nayi ta kwala Kiran sunan "Anisah!!! Asiyah" shiru ba su amsa ba ta sake Kiran sunan su a Karo na biyu jiki a sanyaye suka fito jikin su a sanye yake da Riga da Wando jeans yayi matukar karb'an su sannan ko Wacce tasa ribbon kalar rigan ta tayi parking gashin ta, sunaa da tsawon gashi, gashi Baki Kirin.


Zuwa sukayi suka tsaya a gefen ta, kallon su ta Shiga yi daga sama har kasa sannan tace "Bakin ku ciwo yake da Kuna ji Ina Kiran Ku baku amsa ba, maza kuyi kneel down Ni sa'ar kuce da za ku Zo ku tsaya min a Kai?" Ba musu sukayi kneel down.

Tsaki tayi Tace "Daga gani cikin ku biyun Nan akwai mayya" tana nuna su da Yar yatsan ta akwai Wacce take kawo Mana matsala a gidan na rashin kud'i gashi Kun sa mun Fara Shiga talauci, ko kud'in da mijina yake kashewa a makarantar ku ma ai asara ce ban ga amfanin ta ba sabida haka na yanke shawara daga yau Kun daina makaranta a gidan Kar ku kuskura naji Kun ambaci sunan makaranta ko da dawasane" ganin tayi shiru suka tashi a tsawace Tace "Don uwar ku wa ya ce ku tashi maza ku koma kneel down, raise up your hands and close your eyes" a tsorace sukayi yanda tace sun dad'e a haka Kan tace "babu abinda kuka iya sai Kama gashi da ribbon zan Baku shawara gara ma kuje ku koyi sana'ar d'inki ko salloon Yan iskan Yara kawaii tashi ku bani guri" cikin sauri suka Mike suka bar gun.

Bayan Mahaifin su ya dawo daga aiki Yana zaune a parlor suka shigo suka tsaya a gaban TV idan ya karkata kansa sai su tare sunyi hakan kusan sau uku sannan yayi Murmushi yace "To naji naji me Daddy yayi wa little angels d'insa Kuma wanna karon?"
Anisah Tace "Daddy Meyasa kace zaka cire mu a makaranta?"
Kallon su yayi d'aya bayan d'aya sannan yace "Na cire ku a makaranta? Me zai Sa na cire ku a makaranta?"
Asiyah Tace "Mummy ce tace Mana za'a cire mu a makaranta"
Cikin rashin fahimta yace "Meyasa?"
Anisah Tace "Cewa tayi babu kud'i Yanzu ana cikin marra"
Murmushin gefen baki yayi yace "Haba duk talauci na bazan ki saku a makaranta ba Kuma Alhamdulillah muna ci muna Sha babu abunda muka rasa, maybe mummyn naku Wasa take muku ko Kuma Bata San me take fad'a ba"

Anisah Tace "Allah yasa dai bata San me take cewa bane" ta Maida kallon ga Asiya Tace "Asiyah Zo mu tafi" d'akin su suka haura suka barshi zaune Baki a bud'e yace "Ikon Allah, wato dai Baraka baza ta canza ba" Kiran Sa akayi a waya Yana wayar ya haura saman su inda ya Samu tana zaune gaban mirror tana taje gashin kanta jikinta Kuma sanye yake da sleeping dress iya gwiwa yellow ne aka Masa flowers da jaan color, sai da ya gama wayar da yake sannan tace "Naji kana maganar tafiya"
Murmushi yayi yace "Eh tafiya xanyi zuwa London next week insha Allah"
"Masha Allah tare zamu tafi ko?"
Yar karamar dariya yayi yace "tafiyar Nan na office ne Kuma sai naje dake? Idan na tafi dake wa zai kula da yaran?"

Tashi tayi a tsawace Tace "Ni fa matar kace ba baiwar su ba, ko Kuma ka auro Ni ne don na Zama baiwar su?"
"Haba Baraka Kar ki manta Kan na auro ki kin San da zaman su Kuma kin tabbatar min da ba matsala Zaki kula dasu Amma Yanzu kiji abinda kike cewa 'ya 'yan ki ne fa?"

A tsawace Tace " 'ya 'yan ka dai zaman ka nakeyi ba nasu ba ka gane ko? Kuma da kake cewa sai da na amince Kan akayi auren do you expect me to refuse your proposal?"
"No no Baraka ba haka nake nufi ba" wayar ta tasa hannun ta d'auka sannan ta nufi hanyar fita Tace "Sai Kuma kayi ai."

"Baraka!! Baraka!!!" Bata tsaya ba bare ta saurare shi.
'''CHAPTER 2'''
πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦
........... Zaune take a Parlor ta d'aura kafa d'aya Kan d'aya tana kallon TV, ji tayi a na kwankwasa kofa tashi tayi ta bud'e ganin mijin taneΒ  yasa tayi Murmushi da saurin ta rungume shi had'e da sumbatar sa a kumatu, ganin mace a bayan sa hannun ta rike take da Ghana most go yasa tayi saurin sake shi Tace "who is she?"
Murmushi yayi yace "Sunan ta maijiddah, na d'auko tane sabida ta Rika Taya ki aiki"

Cike da mamaki take kallon sa Tace "Yar aiki a gidan Nan?"
Ya amsa da "Eh"
Tace "Na d'auka kace baka son yar aiki a gidan ka Kuma ya akayi ka canza shawara?"
"Gani nayi kina wahala sosai da aikace aikacen gidan Nan don gidan babbane Kuma Kinga zata Rika Taya ki kula da yaran Nan"

Murmushin gefen baki tayi Tace "Okay idan na fahimce ka karfin d'auko ta da ka yi shine don ta Rika kula da yaran ka ko?"
"Eh Haka ne"
Rai a b'ace tace "To Ni yaushe zaka Fara yin Abu sabida Ni a ko da yaushe maganar 'ya 'yan ka kake, sau nawa nake rokon ka da ka d'auko min Yar aiki Amma kaki? toh ban yarda ba ka maida ta inda ka d'auko ta" tana Kai Nan ta bar gun Yana Kiran ta Amma Bata kulashi ba cikin sauri ya bi bayanta sannan ya dawo yace "Maijiddah ki jira ni anan ko? Ina dawo wa"
Ta amsa da to.

Yana yafiya ta Fara kalle kalle tayi Nan tayi chan har ta hango wani kofa tana Shiga Ashe kofan kitchen ne ga mamakin ta taga Yara biyu suna aiki d'ayar na girki d'ayar kuma na wanke wanke hard'e hannu tayi tana kallon su a zuciyar ta Tace "Ikon Allah kananun yaran Nan da aiki haka har da girki abun tausayi?"

"Haba Baraka meyasa kike min haka ne ya kamata ki fahimce ni ki gane dalili na, Kinga idan Zaki fita yanzu Baki da wata matsala akwai Mai kula da su Kuma Kar ki manta idan na dawo daga London zamu tafi yawon shakawata a Saudi kin ga zai Zo Mana da sauki ko?"

Murmushi tayi Tace "To shikenan she can stay"
Zaro Ido yayi sannan ya durkusa a gaban ta yace "Dan Allah dagaske kin amince?"
Yar karamar dariya tayi Tace "Eh na amince"
"Kaai Mata Mata duk halin ku d'aya"
Dariya kawaii yayi.

Yace "Bari naje na yi magana da ita"
"Ya dai fi Kam Kar na canza shawara"
Tashi yayi yace "Allah ya shirya min ke Baraka" ta amsa da "ameen."
Sai ya fita.

Shigowar sa palon yayi dai dai da fitowar Maijiddah daga kitchen yace "Yauwa Maijidda ta amince Zaki iya Fara aikin ki daga yanzu"
Ta ce "Amma yallab'ai naga akwai wasu Yara su biyu suna aiki Ina ganin kamar ba sai na zauna ba"
Cikin rashin fahimta yace "Yara Kuma masu aiki a gidan Nan? Kaai babu masu aiki ke dai kiyi yanda nace Miki"
Ta amsa da "Toh Yallab'ai"
Yace "Amma kamun Nan Bari na had'a ki da yarana Anisah da Asiyah" ta amsa da "Toh."

"Asiyah!!! Anisah!!"
Shiru yace "Ina yaran Nan sukayi ne? Anisah!!Asiya!!!, bari na duba su a d'akin su yazo zai haura saman su ne yaji motsi kamar da kwai mutum a kitchen dawowa yayi da baya ya tura kofan kitchen d'in "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un me ke faruwa a Nan?"
Kallon sa kawaii sukayi sannan suka cigaba da aikin su.

Rai a b'ace yace "Ku bar wannan shirmen ku biyoni"
Ba musu suka bi bayan sa.
"Baraka!!! Baraka!!!" Rai a b'ace yake Kiran sunan ta.
Cikin sauri ta fito Tace "Lafiya kuwa kake Kiran suna na haka?"
A tsawace yace "Me ke faruwa a gidan Nan wanda ni ban Sani ba?"
"Kamarya ban fahimce ka ba?"

" 'ya 'ya na gani suna wanke wanke da girki yaushe suka Fara hakan?"
Cikin Rawar murya Tace "Haba Taya Za'ayi suyi girki nice fa nake girkin shigowar kane na fita besides ya kamata su koyi aiki bai kamata su tashi da sakalci ba"

"Kar ki Raina min hankali Baraka yaran Nan suna aikin Nan da kwarewa alamu sun nuna sun dad'e suna aikin Nan sun Saba"

"Oh am sorry na manta a makaranta ne aka sa su yin girkin a wannan subject d'in em...emmm home economics ance su koyi girki nutrition, ko ba Haka bane yan mata?" Tana musu wani irin kallo.

Kirkiran Murmushi sukayi sannan sukace "haka Ne Daddy"
Numfashi ya sauke yace "Sai yanzu naji hankali na ya kwanta na d'auka aiki kike sa su yi ai"
"Haba mijina bazan yi hakan ba."

"Toh shikenan Ni zan koma office, ki nuna Mata d'akin ta sai na dawo"
"A dawo lafiya"
Ya amsa da "ameen"
Ta koma d'aki tayi kwanciyar ta.

Basu d'au lokaci ba suka Saba da Maijiddah sabida Maijidda mutum ne Mai fara'aΒ  da son yara.
Tana Taya su yin assignment sannan Kuma tana Kara musu karatun al'qurani.

Anisah da Maijiddah na gani a Parlor zaune suke da littafai a gaban su da alama assignment suke.

Da sallama ta shigo suka amsa Anisah na ganin ta ta taahi da gudu tana fad'in "Oyoyo oyoyo Aunty Rukayya"

Wacce aka Kira da aunty Rukayya ta amsa da "Oyoyo" hade da rungumar ta.
Tace "ya kike?"
"Lafiya Lau"
"Ina Asiyah take?"
Ta amsa da "Tana d'aki Bari naje na Kira ta" tana Kai nan ta haura sama da gudu.

Maijiddah Tace "Bismillah ki zauna"
Murmushi tayi Tace "Nagode" had'e da Zama.

Tare suka fito da gudu ta rungume ta Tace "Sannu da zuwa Aunty Rukayya"
Shafa kan ta tayi Tace "Yauwa sannu Asiyah ya kikeΒ  ya makaranta?"
"Lafiya kalau"
'Wace ce wannan?"
Tana nuna Maijiddah.
"Sunan ta Aunty jiddah itace Mai kula damu"
"Aunty jiddah wannan itace aunty rukayya kanwar mamar mu Ina nufin mahaifiyarmu Wacce ta haife mu"
"Allah sarki nice to meet you jiddah"
Ta amsa da "Nice to meet you too"
"Zaki ban aron su please zamu fita"
Tace "Toh ba matsala"
"Okay thank you, nazo na cika alkwarin da na d'auka zamu fita outing kuje ku shirya" sai da ta Kare musu kallo Tace "Ko da yake naga a shirye kuke ku sako takalmin ku mu tafi" tsalle sukayi sannan suka haura sama Basu d'au lokaci ba suka fita.

*BAYAN WASU AWANNI*

"Maijiddah Ashe Baki da hankali ban Sani ba Taya zaki Bari a fita da yaran Na ba tare da Sani na ba?"
Kai a kasa tace "Kayi hakuri sir zasu dawo yanzu Kuma Tace min ita kanwar mamar suce"
"Yimin shiru tun d'azu nake Jin magana d'aya jirgin karfe biyar zan bi gashi karfe hud'u yanzu so kuke na tafi ba tare da na ga yarana ba"

Baraka Tace "Ya kamata ka Hana Rukayya zuwa gidan Nan ya za a yi ta Rika yin abinda ta ga dama kawaii don taga bamu gida sai ta d'auke su"

Rufe bakin ta ke da wuya sai suka jiyo sallamar su jiddah Tace "Yauwa gasu Nan ma sun dawo"
Rai a b'ace ya tashi yace "Haba Rukayya ya Zaki min haka? Ya kamata ki daina fita da yaran nanΒ  ba tare da izini na ba"

Kallon sa tayi cike da mamaki Tace "Sadeeq mene don na fita da su akwai wani matsala ne?"
Kan ya amsa Baraka tayi saurin fad'in "Akwai matsala babba ma ki daina zuwa gidana tunda Yar uwarki ta mutu ki rabu da mu Mana ko dai kina Shirin aure min Miji ne?"
Dariya tayi tace "Bani da lokacin ki Baraka"
Shafa kan Asiya da anisah tayi Tace "Zan dawo wani lokacin kunji ku kula da Kan ku" tayi ficewar ta.

A tsawace tace "Jiddah me kike kallo maza ki d'auki akwatin Nan ki fita da shi waje"
Ba musu ta d'auka ta fita dashi riko su yayi Yana Shirin yin magana tayi saurin katse shi ta janye su daga jikin sa sannan ta rungume shi.

Asiyah ta rike hannun Anisah Suka haura sama, sun dad'e a rungume da juna Kan ta sake shi har parking area ta rakashi sai da taga fitar sa sannan ta dawo cikin gidan.

*WASHE GARI*
Ta dawo daga yawon gantalin ta tarar dasu su jiddah na musu assignment a tsawace Tace "Me ke faruwa anan?"
Jiddah Tace "Assignment nake musu?"
"Assignment?Karki manta ke Yar aiki ce a gidan na"
"Aunty na sani Amma ai nayi makaranta kawaii dai Allah baiyi zanyi gaba bane "

"Ina magana kina magana? Ke tashi ki haura sama ki tattaro tsumma karanki ki ki bar min gida tunda Wanda ya kawo ki baya Nan"
Jiddah Tace "Amma..." Kan ta Karasa taji saukan Mari a fuskar ta "ki fita nace"
Ta watsar da littafaan tace "Uban me kuke kallon ku tashi ku bar Nan" a tsorace suka bar gun.

Asiyah da Anisah na kuka jiddah na rarrashin su, zata tafi ba don ta so ba.

*NEXT DAY*
Yau ya kasance Monday sun shirya cikin shigar su ta uniform Riga da skirt ne skirt d'in green ne sannan rigar yellow sunyi kyau sosai bayan su kuma sun rataya jaka.

Har kasa suka durkusa Asiya Tace "Mummy mun shirya zamu tafi makaranta"
A tsawace Tace "Don uwarki sau nawa nace muku Ku daina kirana da Mummy Ni ba uwar ku bace ban haifi biri ba, sannan nace muku Kun daina makaranta yanzu ki ajiye Jakar Nan, Ke Asiyah ki d'auke roban Nan da nasaΒ  lemo a Ciki ke Kuma Anisah ki d'auki ledan pure water Nan kuje ku sayar min"

Sai da suka Karewa lemo da pure water kallo Kan suka kalli juna sannan suka Maida kallon su gare ta.

CHAPTER 3
πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦
............ "Maza ku daina kallo na ku wuce ku cire uniform d'in Nan kusa wani Kaya, kun tsaya Kuna kallo na da ido kamar na mayu."

Ba musu suka haura sama Tace "Minti biyu na Baku ku kifo Kar ku wuce Nan, Wai mummy zamuje makaranta da wani kud'i za a biya muku? Mtssws" bayan sun fito ne ta d'aura musu talla.

Sun dad'e a yawon tallaan sai wajen karfe uku suka dawo gida.

Karb'an kud'in tayi Tace "Masha Allah Ashe Kuna da amfani" Nan ta Shiga irga kud'in sai taga naira hamsin da bakin sa ya d'an gutsire ta kalli kud'in dakyau Tace "Toh wannan Kuma waya cinye?"
Basu ce mata komai ba sai kallon junan su kawaii suke.

Tace "banda rashin hankali ma Kuna ganin kud'i ba kyau ku karb'a, ku Shiga Ciki Ku huta,idan Allah ya kaimu gobe tunda Kun sayar da wannan duka zamu sayo wasu"
Kallon Juna suka yi cikin Rawar murya Asiyah Tace "Mummy yunwa muke ji"
"Yunwa kuke ji?"
A tare suka amsa da "Eh yunwa muke ji"
Gyara Zama tayi Tace "Kuna nufin yunwa yunwa na cin abinci?"
Suka amsa da Eh.
Langwabe Kai tayi Tace "Allah sarki kun ga abin da nake fad'a muku Kenan Nima tun jiya banci komai ba"

Anisah Tace "mummy na kasa fahimtar abinda ke faruwa mun talauce ne ko me?"
Yar karamar dariya tayi Tace "Eh mun talauce Amma Alhamdulillah tunda muna raye, to yanzu ya zamuyi Kenan tunda Kuna Jin yunwa?"

Kallon ta kawaii suke suna rarraba idanu, Murmushi tayi ta sa hannu ta d'auko naira hamsin d'in Nan da ya yage tace "me wannan zai saya Mana muci tunda Allah ya had'a Ni da monkeys?"

Anisah Tace "Mummy Dan Allah ki Kira Daddy muyi magana dashi"
Tashi tayi Tace "Kina nufin na Kira mijina? Baku girma bane ta yanda zaku Rika fita Kuna neman kud'in da zakuci abinci? Wato na Kira shi?" tana maganar tana nuna kanta.
"Eh please call our Daddy he promise us that we will never lack anything"

A tsawace Tace "would you shut up your dirty mouth,I should call him kuce Masa me? Idan Kika kuskura Kika sake fad'a min magana makamanciyar wannan Anisah sai na karya ki"

Anisah Tace "But mummy..."
Katse ta tayi a tsawace tace "Get out from here useless children" tana maganar had'e da ture robobin da suka dawo dashi.

"Ku d'auki robobin Nan ku fice min daga gani"
A tsorace suka bar pallon.

A garden na gidan suka zauna Asiyah Tace "Anisah Dan Allah na roke ki wata alfarma?Β  ya kamata ki daina tan kamata idan tana magana"
"Meyasa kikace haka?"
"Sabida zata kashe mu wataran idan Kika cigaba da Mata Haka"

Murmushi tayi Tace "To Asiyah me banbanci mu da matattu, ba abinci, ba zuwa makaranta muke ba, ba kayan sawa kin San duk ta Kona Mana su,ba Uwa ba uba, har yaran da suke gidan marayu sun fimu da komai, to me Kuma ya rage? A raye muke dai Amma ta kashe mu"

"Na San da hakan Anisah Amma ya kamata ki d'auki magana ta Kinga nice gaba dake ko?"
"To shikenan zanyi yanda kikace"

Asiyah tashi tayi tace "Yauwa ko kefa Tashi muje muyi sallah muyi Shirin zuwa islamiyya"
"Gaskiya ni bazanje ba jiri ma nake ji Ina sallah zanyi bacci"
"To shikenan Nima baccin zanyi kawai."

Ganin ta nayi ta fito daga kitchen hannun ta rike yake da plate, fried rice ne aciki da cinyoyin kaji manya manya, d'ayan hannun Kuma kwalin Hollandia ne, Kai tsaye dinning table ta nufa tana ajiye plate d'in wayan ta ya Fara ringing tana picking ta amsa da "Hello qawata"

Bayan sun gaisa Tace "Ke dai Bari kawai qawata nayi duk yanda zanyi Amma shiru kike ji na rasa meyasa ban haihu ba sai faman bauta nake wa yan iskan yaran Nan."

Tana d'an yi shiru da alama tana Mata magana Wanda Ni na kasa ji sai ji nayi Tace "Ai wallahi Ina haihuwa Zan Kori monkeys d'in Nan a gida na, Kema kin sanni ai wallahi ba ruwana da inda zasu je suma mutu Mana"

"Okay to shikenan ki gaida min 'yarki" kashe wayar tayi ta cigaba da cin abincin ta, suna shigowa suka tarar da ita ta na yagar nama ganin suna kallon ta banka musu wata muguwar harara had'e da fad'in "baza ku bar Nan ba?"
Da saurin gaske suka bar gun, a Haka suka kwana da yunwa sai Ruwan da sukayi ta Sha.

Yau ma tun safe suka fita don sayar da lemo da pure wata.
Wata bakar motar na gani kirar Benz tazo ta gifta su.

Cikin motar wata yarinya sa'ar su Asiyah tana kallon su Asiyah cike da mamakiΒ  Tace "Mom ya akayi na ga su Asiyah suna tallah?"
Murmushi tayi ta Maida hankalin ta sosai Kan tukin da take, sai Tace "Toh mene ne aciki don sunyi tallah akan su aka Fara ne?"

"Toh Amma Meyasa Ni bana yi"
A tsawace Tace "yimin Shiru Allah ya raba ki da tallah, Suma d'in kaddara ce kuma Kar naji kin sake fad'in Haka, kuma kar ki fad'awa kowa kina jina ko?"
"Toh bazan fad'a ba"
Shafa kanta tayi Tace "Yauwa YesmiinΒ  'yar Albarka,Bari nayi sauri nayi dropping d'inki a makaranta Kar ki makara ko?"
Tace "To mommy"

Sai yamma liss suka gama sayar da komai da komai babu abinda ya rage, a galabaice suke tafiya Asiyah Tace "Anisah har yanzu zazzab'in Bai sake ki ba?"
Cikin kasala Tace "Eh jiri nake ji, ji nake kamar zan fad'i"
"Sannu bari na rike ki, mun ma kusa Isa gidan" rike ta tayi suna tafiya Kan ta Ankara Anisah ta zube a kasa, ihu Asiyah ta Fara yi tana kuka tana neman taimako dake a GRA suke unguwan Shiru ba kowa ta dad'e a Haka Kan ta hango wasu Samari su biyu da gudu suka nufota, d'aya daga cikin su yace "Me ya same ta Haka?" Cikin kuka tace "Suma tayi"Β  chaak ya d'aga ta

Please Login or Register in order to submit comment