Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

ANEESA Complete Hausa Novel Document by ANEESA


ANEESA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 103894



ANEESA

Reading Time: 8 Hours

Added On: 10, Aug 2024

Author: Khaleesat Haidar ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 517.98 kb

File Type: txt

Views: 799+

Download: 2062+

Last download: 3 hours ago

Description/Story: ANEESAH 🌹🌹🌹
Na KHALEESAT HAIDAR
👉1
A guje ta fado dakin ta xube kan Amminta
dake linkin kaya tana sakawa cikin jaka,
Ammi ta dago fuskarta a rude tana
tambayarta "lfya? me yafaru?" tana mayar
da numfashi a dan tsorace ta kasa ce ma
Amminta komai, sae da Ammi ta maimaita
mata tambayar a fusace snn ta fashe da
dariya tace "wae Ammi yusuf ne xae dokeni,
don mota ta take masa kwallonsa nayi
dariya," Ammi ta haureta cikin fada ta fara
magana "wae ke yaushe xakiyi hankali ne
Aneesah, ba wanke-wanke na sa ki ba kika
fita waje kina biye ma yusuf, shi yusuf din
kike ma gudu idan ba wauta ba," ganin
yanda Amminta ta fusata yasa ta mike tsaye
da sauri ta marairaice murya tace "kiyi hkuri
Ammi, amma idan na fita wllh dukana xae yi,
kuka fa yake yi," Ammi xata yi magana sae
gashi ya shigo dakin, da gudu tayi bayan
Ammin tana cewa "wayyo ammi kin ganshi
ko," Ammi ta dada mata duka snn tace "kai
yusuf yayar taka xaka duka don ba ka da
kunya," yyi ma Aneesar wani irin kallo yace
"Allah ya taimake ki mutumin ya bani Naira
ashirin na siya wani kwallon," Aneesah ta
dinga dariya tana cewa "Naira ashirin" yace
"eh mana" snn ya fito da sabbin dubu daya
guda biyu, Aneesah ta xaro ido tana
kallonsa, Ammi tace "kai yusuf wa ya baka
wnn kudi hka," yace "mutum da ya fasa min
ball da motarsa yace naje na siya sabo,"
Ammi ta juya tana kallon Aneesah, can tace
"to kawo nn yusuf, anjima da kaina xanje
kasuwa na siyo maka wani, amma kace
masa ka gode ko?" yusuf yace "aa na manta,
snn ya mika mata dubu biyun ya fice ya fice
daga dakin," Ammi tace "oh Allah dae ya
biya wnn mutumin, kmr yasan ynxu tunanin
me xamu ci anjima nake Aneesah," Aneesah
tayi murmushi tace "ki siyo kayan abinci
kawae Ammi," ammi tace "hkn xanyi, bari na
gama hada kayan nn sae na tafi kasuwa,"
Aneesah ta mike jikinta a sanyaye ta fita
daga dakin taje yin wanke wanken dake
tsakar gidan.
.
Aneesah na shirin islamiyya karfe hudu
saura Ammi ta shigo gidan, ta karbi ledojin
dake hannunta da sauri tanai mata sannu
da xuwa ta fito mata da kujera waje snn ta
debo mata ruwa a randa ta kawo mata, ta
xauna gabanta tana tambayarta ya hanya,
Ammi ta ajiye kofin ruwan dake hannunta
bayan ta shanye ruwan tace "maxa ki tashi
ki kama hanyar makaranta lkci na wucewa,
ina yusuf?" tace "nace ya jirani yace shi su
khabir xae bi," ta mike ta dauko goggen
Hijab dinta da Nikaf ta saka snn tace "to
Ammi sae na dawo," Ammi tayi mata Allah
ya kiyaye ta fice daga gidan. Karfe bakwae
saura su ka shigo gidan ita da kaninta,
Ammi na share tsakar gida su ka yi mata
sannu da gida suka shiga daki, tana gama
cire uniform ta fito karbar sharan ammi tace
"su yi sallah, ga abincinsu a kitchen," yusuf
na ganin shinkafa da miyace ya dinga tsalle
yana murna yau xa su ci shinkafa, Aneesah
ta galla masa harara tace "yau ka saba cin
shinkafa ne? wawa kawae," ya daga hannu
xae kai mata kulli ta goce da sauri tare da
kwala ma Ammi kira ganin wani kullin xae
kai mata, Ammi ta shigo dakin da sauri ta
raba ma kowa nasa tana masu fada snn ta
nemi guri ta xauna tana kallon 'ya yan nata.
Aneesah yarinya ce da bata wuce shekara
17 ba, sun taso cikin wahala da talauci tun
bayan rasuwan mahaifinsu Alhaji Mukhtar,
Alhaji Mukhtar shararren mai kudi ne a
garin Abuja, Allah yyi masa rasuwa shekara
takawas da suka wuce a hatsarin mota da
yyi a hanyar sa ta dawowa Abuja daga kano
bayan ya kai ma 'yan uwa da relatives
ziyarar sallah, tun bayan rasuwarsa suka
fara fuskantar kalubalen rayuwa duk da
dukiyar da ya bari mai dumbin yawa don a
lkcn ma gidajen da ya bari sun kai 6 bayan
motoci da filaye, kiri kiri yayansa Alhaji
shehu ya karbe komai nasa da sunan xae
ajiye har sae yaransa sun mallaki hankalin
kansu, Alhaji Mukhtar shine auta a gun
mahaifinsu malam sule, da mahaifiyarsu
saudat, su uku kadae Allah ya basu duk
maxa, shehu, ibrahim da shi Mukhtar, tun
yana primary Allah yyi ma mahaifiyarsu
rasuwa, yana gab da gama secondary
mahaifinsa ma ya rasu, tun daga lkcin komai
ya tsaya masa don duk yayyinsa sun dauki
karan tsana sun daura masa tun iyayensu
na da rae bare ynxu da suka koma ga Allah,
duk suka juya masa baya ga 'yan uwa ba
xumunci, ya sha wahala sosae a rayuwa
don da kyar da taimakon sana'ar da yake yi
na wankin mota cikin ikon Allah ya kammala
karatunsa ya sami aiki a House of Assembly
Abuja.
.
Yan uwansa na ganin hka suka fara
shisshige masa suna nuna masa so, da yake
shi Allah yyi sa mutum ne mai son xumunci
kuma mara riko, ko kadan bai kullace su kan
abinda suka yi masa ba ya ja su a jiki ya
sama masu aiki don dama duk buga buga
suke, ya kuma taimaka ma yan uwa da
dama tun daga kan relatives har xuwa wa
inda ma bai hada komai dasu ba. Ana hka
suka hadu da Mahaifiyarsu Aneesah Maryam
a bikin wani abokinsa, sunyi soyayyar gskya
wanda ya kaisu ga aure duk da dangin
ubanta basu so hkn ba don auren xumunci
suka yi niyyar mata, amma da yake Allah yyi
shine mijinta a hka su ka yi aurensu wanda
bayan shekra daya Allah ya axurta su da
samun Aneesah, daga ita ko basu sake
haihuwa ba har sae bayan shekara takwas,
don kaninta yusuf na da wata biyu mahaifin
nasu ya rasu, ba karamin girgixa Ammi
mutuwar mijin nata yyi ba, kuma duk da
tsanar da danginsa ke mata don ko kadan
basa sonta a hka ta gwammace ta xauna ta
tarbiyantar da 'ya yanta a gidan ubansu don
iyayenta talakawa ne sosae snn tun tana da
shekara goma mahaifiyarta ta rasu matar
uba ta sa ta gaba, hkn yasa kakarta na
wajen uwarta ta maidota wajenta har Allah
ya hadata da Alhaji Mukhtar suka yi aurensu,
kuma tasan ko ta tunkari gidan mahaifinta
ynxu baxae karbeta ba don duk abinda
matarsa ta gaya masa shi yake bi, kuma
matar bata so ta auri mai kudi ba tunda
yayanta duk ba masu kudi suka aura ba,
to be continued. . .. . . insha Allah
@ #dan_gogori1
Drop ur cmmn
ANEESAH🌹🌹🌹

Na KHALEESAT HAIDAR.
~2~
Sallamar wata makwabciyarsu ne ya sanya
Aneesah ta dago tana goge fuskarta, ta
karaso cikin gidan Aneesah ta gaida ta ta
amsa tana tambayrta ya karatu, ta shiga
dakin ta gaida Ammi snn ta ajiye kwano
tace "gashi a ba yusuf ya kara Ammi, bbu
yawa," Ammi tayi mata godiya tana
tambayrta danta umar, tace "yana can waje
suna wasa" snn ta fice. Ammi ta jawo
kwanon ta bude taga dumamen tuwo ne,
tasan kila yusuf yace mata yana jin yunwa
ne shine ta kawo abincin don matar tana da
kirki sosae duk da su ma manage suke don
sae mijinta ya fita yyi shoe maker snn suke
samun abinda xasu ci suma , ta kira
Aneesan su xo su ci, bakin ciki da takaici
yasa taji ta daina jin yunwan ma kwata
kwata tace bata ci, da kyar Ammi ta lallabata
ta ci dn tasan halinta. Karfe sha biyu saura
Ammi ta fito da dinkekken atamfarta da
kakarta ta aiko mata da wani sllh, Aneesah
ta tambayeta inda xata da shi ganin tayi
shirin fita ne, Ammi tace "xan je kasuwa ne
na sayar Aneesah kafin su Hajiya salamatu
su dawo," Aneesah tace "haba Ammi ke knn
kullum sayar da xani don Allah don annabi,"
Ammi tace "to meye amfaninsu Aneesah," ki
kula da yusuf kafin na dawo don daga can
xan siyo abinda ya sauwaka na abinci," bata
jira cewar Aneesahn ba ta fita daga gidan.
Tana tsaye bakin kofar dakinsu bayan ta
gama shirin boko, yusuf yace "Anty mu
wuce kar su Jamila da khabir su ruga mu
yau ma," Aneesah ta jawo sa tace "kasan me
yusuf, maxa ka bisu ni ina nn xuwa kaji,"
bae yi mata musu ba ya fice daga gidan,
Ammi tace "to ke me kike jira Aneesah,"
Aneesah ta shigo cikin dakin ta xauna tana
kallon Amminta tace "kudin waec nd Neco
Ammi, kuma ance kar mu xo yau idan har
mun san xa muyi kuma bamu kawo kudi
ba," Ammi ta tsura mata ido tana kallonta
tace "to yaushe ma ya bada kudin
makarantar da har xa'a tunkaresa da wani
kudin waec, amma dae ki shirya kije ki
samesa ki gaya masa ynxu kila Allah ya
daura ki a kansa Aneesah" Aneesah ta hade
rai, can ta tabe baki tace "bbu inda xanje
Ammi, gwara kar na sake xuwa makarantar
ma kwata kwata," Ammi ta galla mata
harara tace "to ki xauna," Aneesahn tace "to
wnn mutum ne Ammi, ko fa naje ba bani
xae yi ba sae dae ya walakanta ni ma, ba
gwara kawae kar naje ba," Ammi tace "ko
ma de mae xaki ce, yayan babanki ne,
baffanki ne dn hka ki iya bakin ki, kuma ki
tashi ki shirya ki tafi kafin ya fita," ta mike
jikinta a mace ta tube uniform dinta, ta
dauki wani material dinta ashe da maroon
ta saka, duk da talaucinsu in ta fita baka
taba cewa tana cikin wahala don kullum fes
xaka ganta. Ammi ta bata kudin motar tace
ta barshi kawae xata taka, dole ta tilasta ta
ta amshi kudin dn can cikin gari xata da
nisa sosai. Aneesah na isa gidan baffan nata
ta danna kararrawa daga waje mai gadi ya
leko ta gaishe shi ya bude mata gate din ta
shigo, ta tambayesa ko kawunta na ciki yace
eh, da kyar
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download ANEESA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album