Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


CANJIN RAYUWA
Halima /k Mashi
Creat:- Shuraih Usman
Littafi na daya 1
Domin dauko wasu hausa ebooks din ko wasu kayatattun littatafan hausa a matsayin hausa ebooks, sai ku ziyarci shafinmu na internet akan wannan Adireshin zaku samu http://shuraih.waphall.com


CANJIN RAYUWA (1)
Hajiya saudat tana zaune kan sallayarta ta idar da sallar azahar tana istigfari, 'yar kimanin shekaru arba'in da bakwai zuwa da takwas,amma ba ta yi kama da shekarunta ba saboda kyan jikinta da kuma hutu.in an ce ka fadi shekarunta za ka iya cewa talatin da doriya,kyakyawa ce mai cikar mutunci. wayarta da ke gefe samfurin nokia tayi ruri, cikin natsuwa ta kai hannu ta dauka tare da kallon fuskar wayar. kamar yadda ta za ta, maigidan ne domin duk yinin yau ba ta samu kiransa ba.sallama ya yi,ta amsa cikin ladabi, sunanta ya kira ya ce,hajiya ki karbi bakuncin mu anjima. cikin taushin murya tace,shine ba ka fada mini ba tun safe? cikin lallashi ya ce,na yi ta neman layin ki bai samu ba, ta ce,da ka nemi ta su usaina,kila network ne domin waya ta kunne ta ke,ya dan murmusa,ba mamaki zan iso da yunwa fa,don haka a tarbe ni,ta yi 'yar dariya,wace irin yunwa?shi ma yayi 'yar dariyarsu ta manya,duk wata yunwa ta,da ita zan zo,ta ce, kar ka damu allah ya kawo ka lafiya,ya ce,amin. ki sa a yi wa uwata farfesun kifi tare za mu zo,take ta hade fuska, tamkar yana kallon ta,ta ce alhaji don allah kar ka zo min da mimi.ya ce,saboda me?ta ce,ka san komai, alhaji MIMI in ta zo gidan ba,ba maaikatan gidan ba.ta sani,na fada mata kar in sake ganinta a gidana matsawar ba ta canza halin ta ba,ba na bukatar ta.yayi shiru domin ranshi ya baci,kusan minti daya duk sun yi shiru. sannan ya ce,sauda, ba zan gaji da fada miki cewa ban jin dadin abinda kike yi wa MIMI ba gaskiya, zai fi kyau ki fito fili ki zage ni sai ya fi min sauki maimakon aibanta MIMI. allah! in ji hajiya saudatu,ta sake tausasa muryarta,ban san lokacin da za ka fahimce ni ba alhaji,amma kayi hakuri.in dai don mu zaka zo,to ka zo kai daya zan fi so haka.cikin dan zafi ya ce,sauda muna hanya kar ki manta da abincin ta na yau da kullum,ki fada ma duk 'yan gidan wanda bai son ganin ta zai iya barin gida har sai ta tafi,
[01/10 12:45 pm] Abdul: STEP (2) sannan ya kashe wayarsa. ta dan ciji lebe tare da lumshe ido cikin takaici,ba ta da zabin da ya wuce yin abinda mijin ta ke so.a fili ta ce ni kan bana son zaman MIMI garin nan,na tsani halin ta,a ce yarinya karama a bar ta tana yin yadda ta ke so.ta mike tana nunke sallaya. Abdulkarim ya yi sallama, ta amsa fuskar ta daure,sannan ta yi tsaki, abdulkarim ya ce,lafiya hajiya?alhaji ne ya kira ni wai suna tafe shi da MIMI. abdulkarim ya ja tsaki,don jin ambaci sunan MIMI, sannan yace,ashe yanzu zan juya a kan sawuna mu gaisa kawai hajiya in sabi jaka ta,ai a wannan sati bani da darasi kamar yau,sai na sake dawo wa. hajiya sauda ta yi yar dariya tare da fadin haba abdul,ka taho tun daga zariya har katsina sannan ka ce mu gaisa kawai ka wuce saboda MIMI?ta ci gaba da fadin ba zai yiwu ba.dauki jakarka kawai ka wuce sashin ku,ka watsa ruwa.barin in sa mutuniyarka tabawa ta kawo maka abinci na san yanzu sun gama na rana.ya ce,ai ni bana son rainin wayonta ne hajiya,a ce yarinya karama kanwar bayanka ta zo tana kawo maka rainin wayo,ba dama ka yi magana.ni kuma kin sanni da zuciya sai in doke ta. hajiya tace,aa kar ka soma,ka san halin alhaji.ina fatan baka manta da yadda yayanka abbas suka kwashe ba,in ka tuna zungure mata kai kurum yayi,amma ta inda alhaji yake shiga bata nan yake fita ba.tsawon wata shida yaki ams gaisuwar abbas.sai da biki shi sannan alhaji ya sauko,shima sai da abokan abbas suka taro abokan alhajin aka hadu ana taba shi baki, sannan ya hakura da kyar da dokoki a kan 'yarsa. Abdulkarim yayi ajiyar zuciya cikin takaici,sannan ya ce,ban manta ba.hajiya shi yasa nace, zan koma,tace ka hakura da harkanta.yace, gaskiya alhaji ba yayi mana adalci,a ce cikin 'ya'yansa mu ishirin da biyu,amma ya zabi daya rak yace,ita ce star don kawai tana da sunan mahaifiyarsa.allah hajiya abin yana damu na, kanwarmu ce fa,amma ko shawara da ita sai abinda ta ce a family. hajiya sauda ta ce,ku yi ta hakuri,
[01/10 12:45 pm] Abdul: STEP (3) Dadin abin ita dai ta mace ce,duk abinta ai dole ta yi aure ko? abdulkarim ya ce, tabdi, wannan 'yar jin kan?ya zauna a kujera, sannan ya ce,allah ya sa ta saurari wani.hajiya ta ce, ayya abdulkarim dole tayi aure. ba dai mace ba ce?shi kanshi zai so a bar masa ita a gabansa?abdul' ya yi 'yar dariya,sannan yace,kila ya ce mijin ya dinga biyo ta nan gidansa.hajiya ta ce, oho mishi su dai suka sani, suka yi 'yar dariya,ta ce ba su lokaci kawai.ni dai ina ta fada ma allah,ku da ma na haifa ciki daya kuna jin takaici da haushinta,bare wadanda ba ni ce na haife su ba.abdul ya mike tare da saba jakarsa,bari ni kan na isa dakinmu,hajiya ta ce, to ni ma bari in je babban kicin. hajiya sauda ta tafi gefen babban kicin,ka san cewar gidan babban gida ne mai tsari,tun daga waje za ka san cewa mamallakin gidan ya tara abin duniya ba kadan ba.ta isa babban kicin din,mata uku ta samu a ciki suna ta aiki,suka maido da hankalinsu gurinta tare da yin mata sannu da shigowa,ta amsa da sannunku da aiki cikin girmamawa,ta kalli tsohuwar cikinsu ta ce,baba tabawa me aka yi da rana?tsohuwar tace,taliya ce ke kan layi da rana,da dare kuma zamu yi tuwon masara da miyar danye kubewa,ga taliyar nan ma yanzu na sauke. hajiya tace to,a canza na dare a yi mana dan waken gari dawa sannan ayi shi da wuri.baba tabawa tace,maigida yana nan shigowa kenan?hajiya tace eh,suna tafe,suka hada baki guri cewa,allah ya kawo su lafiya.hajiya tace amin.sannan ta kalli jummai muna da kifin ruwa ko?jummai ta ce eh,hajiya ta ce yawwa ki dafa kadan kar ki cika yaji kuma kar ki sa tafannuwa. sannan ki kula kar ya dagargaje na MIMI ne. dukkan su suka hada baki gurin tambayar har da MIMI ne za a zo?jummai ta ce, allah ya fishe ni yin kuskure. hajiya tace kar ki damu, sannan abinda kawai zan fada maku in tazo,ku kawar da kai duk abinda za tayi kun ji ko?cikin karyayyar murya suka ce to shikenan,tabawa ta kalli jummai kar ki sa mata tafannuwa,
[01/10 12:45 pm] Abdul: STEP (4) Wancan zuwan da ta yi maman sani daga sa tafannuwa shikenan ya zama sanadin korarta. jummai tace,zan kula insha allah. hajiya ta kalli ramma tace,da safe me muke da shi?ramma ta ce, shayi ne,hajiya tace,to a canza zuwa kosai da kunun gyada,ta ce to hajiya. tabawa tace akwai kafar safa ko wannan karon ba zaayi ma alhaji ba?hajiya tace,a dora zan dinga zuwa ina dubawa,na zata babu ne,tabawa mutumin ki fa yazo abdul,a kai masa abinci,ina magajiya?tabawa ta ce allah sarki abdul ne yazo zan kai masa ma da kaina maigida sukutum.hajiya ta juya tana dariya tare da fadin kowa ya duba abinda babu sai yazo ya fada min. Da kanta ta nufi wajen me wankinsu yana ta gugar kayan yara,ta ce masa ka je ka fadawa mai gadi da mai kula da fulawa cewa MIMI za tazo anjima,sannan yau direba ya same ni a falo.ta sake cewa,danladi na fada maku ne don ku kiyaye bana son ana korar min ku,danladi yace,zan fada masu.ya nufi gurin mai gadi,ya turo mata direba ya sanar da su zuwan MIMI nan suka dinga tattauna rashin mutuncin MIMI,ya same ta tana duba nono a cikin firiji.domin tasan aladan shi ta sha furan dare. Direba yayi sallama cikin girmamawa,hajiya ta amsa,ya gaida ta sannan yace,ga ni tace,malam yau da ma ina son sanar da kai ne,yau MIMI zata zo na san ba ka santa ba.amma ka samu labarinta?cikin in'ina yace eh naji gurin su danladi.tace to ka tafi filin jirgi tun misalin hudu da rabi,gara ka jira su,domin da jiran da suka yine wancan direban namu shine sanadiyyar korar shi da MIMI ta sa alhaji yayi.ya ce zan kiyaye insha allah. Tun hudu yau ya nufi filin jirgin,jiran zai fi masa sauki da haduwa da fushin MIMI. biyar da minti talatin suka iso,Alhaji bashir aliyu masari ya fito daga cikin jirgi,MIMI tana biye da shi, sanye cikin riga da wando masu kalar pink sun dame ta tsam.sai after diress baka mai sheki,sannan ta gaba an ratsa pink hakanan rigar ba ta kai kasa ba.don haka ana ganin wandonta, dan siririn mayafinta ba shi da girma,
[01/10 12:45 pm] Abdul: STEP (5) Shima pink bai rufe dogon gashinta ba. Kafarta sanye cikin takalmi shima pink dinne,da ratsin baki marar tudu mai igiyoyi,purse din hannunta da wayoyin ta kirar nakia duk kalar pink ne.can sama goshinta zaka iya kallon wani katon gilashi irin wanda wayayyun 'yan mata masu jin kansu suke sakawa.da gudu yau ya nufe su domin duk da bai san MIMI ba ya san maigida na su.cikin ladabi ya yi masu sannu da zuwa,ya amshi jakar hannun alhaji, alhaji ne kawai ya amsa, MIMI kan ko kallon shi ba ta yi ba. ya bude kofofin motar sannan ya sa jakar alhaji a kujerar gaba,bayan sun fito daga filin yana hawa titi zai raraka da gudu,alhaji ya ce tafi a natsuwa MIMI bata son gudu,yau yace,to ranka ya dade. shi kanshi mai gadi a waje ya tsaya yana jiran zuwan su,yana hangosu da gudu ya nufi ciki ya wangale get din,kamar yanda MIMI ke so,don bata son jira.ko da direba ya tsaya ya bude masu sannan ya cire jakar ya bi bayan su MIMI ta kalli gidan sannan tace,Dad gidan nan yana son fenti yayi datti,ya yi 'yan kalle-kalle,yace,na lura da haka za a sabun ta shi da fenti.direban ya ajiye jakar a kujera sannan ya kalli alhaji Alhaji, na barku lafiya ya fita.Alhaji yaso ma kiran hajiyata-hajiyata,ta fito,dankwali a hannun ta,domin lokacin ta gama saka kayan,ta yi adonta cikin super kalar blue da ratsin yellow sai kamshin turare take yi. Ta kalli mijinta, sannu da zuwa alhaji,ya ce,yawwa sauda ta dubi MIMI wadda tunda suka shigo falo ta natsu saboda duk iya-shegenta tana tsoron uwarta,ta san hajiya sam bata daukar reni.ta dago ido cikin fargaba ta kalli mahaifiyarta sauda tace, sannu hajiya,ta amsa yawwa,ya mominku nafisa da kuma sauran kannenku?ta ce kowa lafiya,hajiya ta ce,masha allah,ta dauki hular alhaji da jakarsa da kuma malun-malun dinsa ta nufi dakinsa tana fadin za a hada ruwan wanka ko? aa rabona da abinci tun safe shima ba wani abinci na ci mai nauyi ba coffee ne,ta karasa dakin ta aje kayan hannunta ta fito tana fadin mu je Dining.
[01/10 12:45 pm] Abdul: STEP (6) Hajiya ce ta janyo masa kujera ya zauna,ya kalli MIMI zauna mana uwata.ya mayar da kallon shi ga hajiya sauda, an yi mata farfesun kifin? hajiya ta kalli MIMI cikin daurewan fuska,sannan ta ce,an yi,MIMI ta turo baki tare da hada rai. hajiya tana zuba masu dan waken cikin plate tare da colslow,ta janyo wani plate din tana zuba masa farfesun kafar sa,ta tura gabansa tana fadin alhaji ba ka tambayi yaran gidan ba?ya kalle ta cikin 'yar zolaya yace,duk ganin ki ne ya mantar dani.ko da dai na san zuwa yanzu suna lslamiyya ko?ta ce eh,yau kam ma da murna suka fita,don na gaya masu cewa kana tafe,ya ce ga shi ban riko masu tsaraba ba.amma bari in sa direba ya sayo masu,ta ce aa zai fi kyau ka fita dasu don yaran nan basa samun kulawarka,kamar fa sam basu shaku da kai ba. Ya kalli MIMI wacce ta jibga tagumi,ya ce zan gani ko da lokacin,kin san fako a can ba samu zama nake yi ba.shiru tayi don ta san kome za tace ba fahimtar ta zai yi ba,ta jima tana yi mishi nacin cewa,ya dinga baiwa yaran ko da awa daya ne a cikin lokacinsa, amma sam ya ki.ko su da suke matansa basa ganin shi a kan lokaci,sai yayi wata ko sati uku in kuma yazo kwana biyu yake yi, nan guri ta ya kwana daya ya je malumfashi wajen hajiya binta ya kwana daya tunaninta ya katse lokacin da ta ji yana tambayar MIMI menene uwata?na ga duk kin bata ranki?ki ci kifinki mamana. ya kalli hajiya sauda ina kifinta?hajiya ta nuna kular da cokali,ga kular kifin nan gabanta?ta dauka mana ko a baki zan bata?MIMI ta sake tura baki tare da kallon mahaifiyarta,ni na koshi,hajiya sauda ta ce, karyarki dubu wallahi kin yi kadan ki ce a dafa miki abin, yanzu ki ce baza ki ci ba,saboda bakin raini ai na lura da ke tunda ku ka shigo gidan nan na san baki so zuwa ba, ko katsinar ce baki so zuwa ba oho miki, amma bakin ranki ya kare miki can. Sauda!alhaji ya katse ta tare da daga hannu, gaskiya ni bana son abinda ki keyi,a ce ke da 'yarki ta cikinki amma ba ki kaunarta?....
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (7) Hajiya tace, ba kaunarta bane bana yi, halinta ne bana so.kuma in har ta ga mun zauna inuwa daya da ita to ta tabbatar ta canza halinta,in ko ba ta canza ba to sai dai ta nemi wata uwar ko da yake tana da ita ma. ya tausasa murya ai ba maganar fada bane, amma gaskiya ba zan iya kallo kina mata irin kalaman ba, kullum tana yi mini korafin ba ki sonta,ita in fada mata gaskiya ko dai bake ce ki ka haife ta ba?ya aje cokalin hannunshi,na rasa me take miki,ita dai ba ma a kasan nan take karatun ta ba.sai ta zo hutu irin haka,amma sam ba kya ko yin kewar ta. hajiya ta tsiyaya masa lemun abarba,wanda ta hada masa,a cikin kofi sannan ta tabe baki ta ce,halin ta kawai zata canza,in dai tana son soyayyata.yanzu baka kalli shigar da tayi ba? tun daga abuja ka sako ta gaba har katsina, kana mahaifinta ga shi kanta a waje,kayar jikinta duk sun dame ta,wai ita dole ta waye. ya kalli MIMI sannan ya kalli sauda, da dan murmushi,ina laifin kwalliyarta,ni ban ga aibun ta ba,haka 'yan mata matasa irin ta ke yi.ya kalli MIMI,ci kifin ki uwata kar ki damu kin ji?tsaki hajiya ta yi ta nufi dakinta.sai lokacin MIMI ta samu damar yin mita,kaga ko dad,sai da nace ka barni can in gama hutu na,ka ce aa sai na zo, ni daman na san hajiya ba za ta taba so na ba. Ta mike tsaye tare da kallon jikinta,shiga tafa, mene ne aibunta?ya kalle ta cikin sigar lallashi yace, ban ga laifi ba.ita hajiya wai sai tace,sai na saka hijabi da atamfa,ni kuma ba zan iya sa iri wannan kayan zafin ba.na yi karatu na waye ni ba irin su usaina ba ce kauyawa.yayi murmushi,shgwabarta tana burge shi.kallon ta ya ke yi tamkar 'yar shekara biyu. ya mike ya zagayo wajen ta ya dafa kafadarta,kar ki damu uwata.mamanki tana sonki,na san ta ga nafi damuwa da kene cikin 'ya'ya na,kin san don ita ce ta haife ki,shi ya sa fa.in da a ce kamar hajiya binta ce ko nafisa da tuni na sallame su,kin manta na taba kora hajiya binta saboda ke?ta ce na tuna Dad,
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (8)Ya ce to kar ki damu ina son mahaifiyarki ko da bata haifamin ke ba, bare ta haife ki. kina son a ce mahaifanki biyu ba su tare?ta ce ba zan so ba dad.amma ka yi mata magana ta daina matsa min,ya ce zan yi mata, amma ke ma ina son cikin kwana biyun nan ki canza kaya sawarki,ki rinka saka irin wadanda take so.ta ce zanyi in dai za ta bar ni in yi abinda na ke so,ya ce za ta barki mana kin ji,ki dai na kuka.ya yi ta lallashinta har ta daina kuka. suna cikin cin abinci hajiya ta sake fitowa daidai lokacin yara suka dawo daga lslamiyya da sallama suka shigo, ita ce ta amsa sallamar,husna da hasina ne a gaba,suka ce sannu da gida hajiya ta ce yawwa sannunku da dawowa yara na.ina sauran? kafin suba ta amsa sai ga su suna ta yin sallama,da hannu ta nuna masu gurin dining,ga dadin ku,suka nufi gurin suna gaida shi da daidaya.ya dafa kan husna da hasina, su ne kanana a gidan, yana ta amsa masu.MIMI ta hada rai ita ba ta son hayaniya. dady ya ce,ba ku gaida sista MIMI ba.suka kalle ta don suna tsoron ta,sannu yaya MIMI,cikin daure fuska ta ce,yawwa,na amsa duka ne ba sai kowanne ya gaishe ni daya bayan daya ba.hasana da usaina sune 'yan matan da suke bi MIMI a haihuwa.dad ya kale su ku shirya da kannen ku, yau yazo ya kai ku super market ku sayo tsarabarku, don ban riko komai ba, kowa ya je ya zabo abinda ranshi ke so. Yara suka shiga murna hasana da hussaina suka ce dad,mu kam ba zamu je ba.ya ce,saboda me?suka ce,muna da karatun hadda gobe,malamin mu zai zo, bin abdulrahaman.hajiya ta ce,tabbas ba ku da halin fita, in ba haka ba zaku sha dukan tsiya gurin shi.duka kuma?in ji dad dinsu,hajiya tace sun wuce duka kenan?karatu sai da zare ido.abdulkarim ya yi sallam, ya shigo falo suka amsa,ya iso gurin dadin shima ya gaida alhajin.MIMI tana ta chatin dinta ba ta dago kai ba,shima bai ko kalle ta ba. ya dubi su hasana ya ce, kun dawo?suka ce eh! yaya sannu da zuwa, dazun hajiya ta fada mana zuwan ka. mun je dakin ku kana wanka,
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (9) Kuma lokacin lslamiyya ya yi dole muka tafi.ya ce,na ji shigowar ai, ya ya zauna,usaina na fadin,lslamiyya lafiya,munyi murajaa ne yanzun. ya ce, kun kusa fara jarabawa kenan suka ce eh! hasana ta ce,yawwa yaya don allah ka amsar mana hadda in anjima mun yi magariba, gobe da safe muna da malamin gida bin abdulrahaman.abdulkarim cikin sigar tsokana ya ce, bani da lokaci,ku ce gobe zanyi kallon duka. usaina ta ce agaji yaya abdul, bulalarshi akwai zafi,suka sa dariya tare.ya ce,bari mu yi sallah sai in karbar maku,suka ce,yawwa yayanmu mun gode. MIMI daga wurin da take zaune tana jin su tana kuma kallon su,sai ta soma mita,ni na san duk 'yan gidan nan ba sa so na,dole kawai suke gani na,kalli yaya abdul,ko kallo na bai yi ba.alhaji yace,kai! abdulkrim,ya ce naam,ya zo ga ni dad.ya ce baka ga MIMI ba ne?ran abdulkarim ya baci,nan a take fuskarsa ta nuna,cikin wata murya marar dadi ya ce,na ganta mana dadi.shine ba za ka yi mata magana ba? Kafin ya yi magana hajiya ta amsa da cewa, in duniya da gaskiya ita da shi wanene gaba?shine ya kamata ya gaida ta,ko ita ce ya da ce ta gaishe shi?. alhaji ya ce,amma ita bakuwa ce.bayan haka kuma yaushe rabonsa da ganinta?a kalla ya nu na kewarsa gare ta ko?kan abdul yana kasa tamkar
DOWNLOAD
DOWNLOAD

1 Comments On CANJIN RAYUWA
avatar
mariya-6-8

2 months ago

Reply

In HAUSA language

Please Login or Register in order to submit comment