Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kenan ta farko in Allah ya so. Rumaisat ko kice ummu suleim, duk sunanta ne. Ba kayi aure ba, amma kana fadin Yarinyar da zaka haifa? To in Maman taqi yarda fa? Maman babyn. Ya rasa dalili, sai yaji gabansa ya fadi, da take Cewa baiyi aure ba. Yace, nasan zata yarda, domin duk matar da zan aura, ba taqi yimin biyayya akan hakaba. Zataso abinda nakeso. Game da batun aure kuwa, zanyi shi da zarar na kammala karatuna. Kafin lokacin na samu mai sona. Mimi ta samu kanta da damuwa, sakamakon amsar daya bata. Tayi shiru. Ya katse ta, bayan ya Kalli agogon hannunsa. Lokaci yana tafiya. Nazo ne muje kiyi ma Rabi'a barka. Karki cemin a'a, duk abinki yaukam sai kinje. Mimi ta 6ata rai. Yace tashi tashi kawai. Ta miqe tana fadin nidai banason fita ne. Yace, kuma saikin fita ba, gashi da nisa kuma a qafa zamuje, dare ne bare kice kar wanda yasanki ya ganki. Tace kai baka gane nufina ba. Ni fa banason inyi hulda da kowa ne, ballantana in saba da kowa. Yaya Amina da kai da yaranta kun isheni. Yace, amma ai kinsan cewa mutum rahama ne ko? Shikenan muje, ba sai kunyi hira ba, bare ku saba. In kinyi mata varka, kiyi shiru.
5⃣5⃣Ta dauki qaramin mayafinta ta yafa. Ya kalleta, kisa hijabi mana khadija. Tace duk fa hijaban da ka kawomin qasa suke ja. Ni ban saba dasu ba, ina yin sallah dasu ne. Yace karki damu kome suke ja, in dai baki sani ba zakiyi sallah da abinki. Bata sake cewa komai ba, ta bude durowar ta ta ciro ta saka, suka leqa tayiwa yaya sai sun dawo, shi kuma tsaya suka gaisa, ya fada mata inda zasu je. A hankali suke tafe iskar damina tana kadasu, zukatansu sun cika da nishadi. Ismail yace, ki tunamin in zamu dawo akwai wani gurin saida kifi, sai mu biya in sai miki. Cikin doki tace, tam, dama nayi kwana biyu banci kifi ba. Nagode. Yayi 'yar dariya, "menene na godiya? Tace, gurinka na koya. Koni ka saima abu in na amsa, sai kace min wai ka gode. Ta dubeshi, kai baka damu da cin kifi ba ko? Yace, aikam bai dameni ba. Amma ynxun na koya a gurinki. Tasa dariya, shikenan mun koya ma juna abu kenan. Yace ai dole kiyi abinda nakeyi. Tace, sbd me? Cikin zolaya yace, kin manta da jinina dake yawo a jikinki, ya gauraye da naki? Tace, daman hakane? To kai ba'a sa maka jinina ba, amma ya ka fara cin kifi? Yayi dariya, sbd ganin yadda ta shiga, ta yarda da abinda ya fada mata. Yace ni ai kara nayi miki. Yadda naga kinata son kifi dinne, shine nima naji ina sonshi. Tayi dariya, "kuna siya a madina ko? Nasan sunada shi, lokacin da mukaje umra da daddy naci sosai, sai dai nasu ba maggi sosai, yace, inaci mana, musamman innaji kewarki, sai in sayi kifi inci. Wani dadi taji a Zuciyarta, Ashe yana tunata. Tace kasan me? Ya dubeta, "a'a. Ban zaci kana tunani ba. Yace, sbd ke ba kya tuna ni, shine kk zaton nima bana tunaki? Ya ce, hakane don yaji ta bakinta. Wa ya fada maka ba na tuna ka? Yace, To in kinyi kewa ta me kkyi? Ta dago ido ta Kalli sararin samaniya babu taurari, sai alamun hadarin dake gudu. Sannan ta dubeshi, "qila zaka manta da wani hankacif daka ta6a bani, in ka tuna, to shine nakan dauko in kalla, wani lokacin ma har in shaqi qamshin turarenka. Dadi yaji matuqa, sannan yace, ashe na kai har haka a gurinki? Kafin tayi magana, yace, gashi har mun iso gidan, sai naga babu nisa ko? Ya fada tare da kallonta. Tace, nima dake fadin nisa, sai naga munyi sauri. Yace, to shiga kimin iso, zan kira angon qarnin ynxun a waya.
[22/09 9:54 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa

5⃣6⃣Tana shiga Mahmud din yana fitowa, yace, ga dakinnan, ki shiga. Bari mu shigo, ynxun ya kirani. Ta shiga da sallama dakin mai jego. Tana zama suna shigowa. Suka gaisa, Ismail ya miqa ma mimi yaron, ta amsheshi tare da kallon Ismail, "banfa iya daukar jarirai ba, karka sakemin shi." Hannuwansu suka hadu, dukkansu sun samu kansu cikin wani yanayi sakamakon hakan. Ta kalleshi. "me me ake cewa? Yace, hausawa suna cewa, Allah ya raya ko Allah ya amfanashi da dai sauransu. Ta kalli mai jego, "to Allah ya raya shi, yayi masa albarka. Ta sake kallonshi, haka yayi? Suka sa mata dariya. Mahmud yace, yayi. Nan kuma sai su Ismail suka canza harshe zuwa larabci. Ismail ke tambayar Mahmud "da wa yaron ke kama?" Mahmud yace, da ni mana. Ismail yace, a'a yafi ka kyau. Ismail ya miqa ma Mahmud yaron, tare da qifta masa ido, alamun zai tsokani Mimi, "khadija to in kin haifi naki yaron wa zai daukar miki? Ta harari Ismail, "ni ba zan haifi ko wane yaro ba. Don ko Aishatu ban ta6a daukarta ba saida tayi girma. Rabi'a tace, ba zaki haifi yaro ba. Sai yarinya? Mimi ta zaro ido, ni dai ba ruwana. Suka sa mata dariya sbd yanayin yadda tayi maganar
Ya tsugunna kusa da ita, "yaya kk ga yaron? Cikin harshen turanci tace, yanada kyau sosai. Domingo mimi tafi iya harshen turanci fiye da harshen uwa. Duk lokacin da zatayi magana mai kalma goma, to turanci zai zama guda bakwai. Don haka saddam da Ummi suke qaruwa da ita. Tana taimaka musu da homework. Sun jima a Gidan har goman dare ta gota, sune dai sukeyin Hirarsu, ita dai Mimi jinsu kawai takeyi. Hammar daya lura tanayi ne yasa shi miqewa, "to bari dai mu tafi, yau dai mun hana 'yan barka sakewa. To duk wadda tazo saidai mamansu Rabi'a ta leqo a miqo mata yaron." Mahmud ya miqe shima, "nima wucewa zanyi" sukayi musabaha tare dayin sallama. Mimi ma sukayi sallama da Rabi'a.

5⃣7⃣Suna fitowa shagwa6a66iya Mimi tace, Ni kam na gaji kawun su Ummi, bazan iya tafiya da qafa ba. Yace, ba don kince min kawun su Ummi ba, da na goya ki hai gida. Cikin hamma hade da shagwa6a, ta ce, don Allah kawun su Ummi, ka mu hau abi hawa. Kaga inajin varci kaji? Yace kin cika langa6ewa khadija. Tace ni ba kaga qoqarina ba, don Allah ban ta6a yin tafiya kamar ta yau ba fa. Nayi qoqari mana. Yace, ba zamu samu mota ynxun ba, kuma ko da mun hau mota, inda za'a sauke mu da nisa, tafiya sosai kafin aje gidanku, sai dai in aca6a. Tace eh naji mu hau aca6a din. Yace, ni banason mata suna hawa aca6a. To ka siya mana mota mana. Yace lokaci ne, insha Allah. Mahmud ya fito, "har ynxun baku tafi ba? Ismail yace, tana nan tana shagwa6ar ta, ba za ta iya zuwa gida a qafa ba. Mahmud ya miqo ma Ismael makullin mashin dinsa, tare da cewa, kuyi amfani da mashin dina tunda ban kaiku nisa ba. Kuma ga hadari yana haduwa. Ismail yace, to kar ruwa ya sameka fa. Mahmud yace, ko ya sameni kaga ni daya ne. Ismail ya amsa, tare da fadin shikenan muje ko? Tace, yaya zan hau? Ka san fa sau daya na ta6a hawa mashin, lokacin zanje in samu khalil a gareji. Saboda sauri ban san ta yaya na hau aca6ar ba, na dai ganni akai. Ina tsoron mashin da yawa. Yace ki dafa ni ki hau. Ta dafa shi ta hau suka soma tafiya. Don ya tsorata ta, sai ya taka birki, a tsorace ta qanqame Ismail, tana salati. Ya sa dariya. "Ya kamata ki rage tsoro. Ita kam batasan ma yana yi ba. Illa hannuwanta da tasa ta zagaye cikinsa ta riqe gam. Sannan ta kwantar da kanta a Gadon bayansa. Wani irin nishadi Ismail ya tsinci kansa aciki mara misaltuwa. Don haka maimakon ya nufi Gida kai tsaye, sai ya dinga shawagi ta layuka, sannan ya sassauta gudu, iga iskar hadarin tana ta kadawa, sai Ismail ke ganin kamar su kadai ne a garin katsina da kewayenta. Ita kuwa Mimi wani daddadan varci ne taji yana fizgarta, iskar tana ratsa ta ko ta ina. Ga kuma qamshin turaren Ismail dake saka Zuciyarta shiga cikin wani yanayi mai wuyar fassara.
[23/09 5:32 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa

5⃣8⃣Can yace, zamuje siyen kifin ne, ko muje gida? Ji tayi tamkar suyi ta yawon su a haka har abada. Don batason abinda zai tashe ta daga yadda suke. Amma kifi fa? Sai tace zanci kifi mana. Ya karkata kan mashin zuwa Gidan suya. Gurin ya burge Mimi musamman tunda taji qamshi yana dukan hancinta. Ya kalleta, zamu ci anan ne? Tace, amma zamu yi ma su yaya Amina tsaraba in munci bamu ko? Yace, yadda kika so, tace, in ba mutane muci, sai mu sai musu nasu. Babba daya ya sai musu, sai tataccen 'ya'yan itace mai sanyi, wanda za'a taceshi a juye maka cikin kofi a gabanka. Sunaci, Ismail yana kallon Mimi, wadda ke ta yin hannu baka, hannu qwarya. Yayi murmushi, "ci sannu Dija! In bai usheki ba zan qara miki." Ya shiga salo mata tsokar kifin sala-sala, yana ajiye mata a gabanta. Ta lumshe ido, "kar kaga laifina, inason abin nan. Ta salo tsokar ita ma ta aje a gabansa, "In baka ci, nima sai ya ginsheni. Ya dauka ya saka a bakinsa. Haka sukayi ta salo ma juna tsokar kifin, suna turawa a gaban juna, har suka cinye. Suka sha abin shansu. Yace, zaki qara? Ta girgiza kai, "cikin yayi dam. Dama banci abincin dare na ba." Yace, kunyi tuwo kenan? Tayi 'yar dariya, "shine kam. Na kasa sabawa da tuwo. Shi kadai ne har ynxun bai min ba, duk a abincin mu na Hausawa. Yace yaya ta fadamin, kin kasa sabo da tuwo. Amma kikanci kadan. Kafin tayi magana, sai sukaji iska mai qarfi alamun tasowar hadarin. A tare suka miqe, da sauri, ya biya sannan suka dauki nasu yaya Amina suka dane mashin. Fatansa tayi irin zaman dazun wanda itama hakane muradinta. Tana lafe a bayansa suna keta gudu, sai ko ga ruwa mai qarfi ya sauka. Sake qanqameshi tayi. Yayin da shi kuma ya rage gudun sbd ya Kalli gaban shi da kyau. Sha biyu da wasu abubuwa suka tsaya a qofar Gidan su yaya, sun jiqe sharkaf. Ya sauka ya buga gidan sosai, kafin suka ji takun Abban su saddam. Sai da ya tambaya wanene? Ismail yace, mune. Sannan ya bude. Mimi ta kalleshi, "kazo ciki mana ruwa yayi sauqi! Yace karki damu, gara in tafi sbd dare zai qara yi. Abban saddam yace, to ka kwana mana anan? Yace, a'a duk na jiqe kayana suna gidanmu. Saida safenku. Ta daga masa hannu tare da fadin bye! Sai da yaga abban saddam ya rufo qofa, sannan ya wuce. Ita kuma tana shiga taba abban saddam ledar tsarabarsu. Yace, bari in taso miki Ummi, don irinki ce, sarkin tsoro taqi varci a dakinku, wai ita kadai.
5⃣9⃣Bayan ta kunna tocila, sannan ta rufe qifar, ta cire kayanta ta maida na varci. Tayi lamo akan Gado, sam varcin yaqi zuwa mara. Sai tuno yadda suka kasance da Malam takeyi. Bata ta6a jin a kafatanin rayuwarta irin na yau ba, domin batasan ya zata fasalta yadda taji ba har a fahimce ta. Saidai a can qasan Zuciyarta tana tambayar kanta shin yadda ta ta6a jikin Malam ya dace, su da zasu rabu? Ta sake yin juyi akan gadon tare da maqale filo, sbd sanyin da taji yana ratsata. A fili tace, kai gsky bayansa yafi katifar nan dadin varci. Wata zuciyar tace, ba wani laifi domin har ynxun mijinki ne, tunda baku rabu ba ai. Haka tayi ta tunani tare da surutai barkatai har varci gwanin iya sata yayi gaba da ita. Washegari yaya tayi ta ma Mimi tsiya, tana cewa, mun zaci ko kun kama daki ne, mu biyo ku da kayanku? Mimi tace, munje siyan kifi ne ruwa ya tare mu. Tace, muma munci kifi, gsky sun iya gashi. Dariya kurum Mimi tayi.
Tun kwanakin baya Mimi tana yawan tuno mahaifanta, haka kuma har abada ba zata manta da gatan da dadynta yayi mata ba. Kewar ganinsu takeyi. Sau da dama takan zauna daki taci kukanta ma'ishi, ta share hawaye, saidai tanajin kunyar tunkarar mahaifinta sbd ta kasa yi masa abinda ya dace, a lokacin daya dace. Duk da cewa ya nuna wa momy Nafisa cewa zai haqura in taqi yarda kamar yadda Momyn tace mata. Amma ita ta yarda cewa tafi kowa laifi don me yasa ba tabi abinda yace ba tun farko? Don haka ta tattara duk wasu laifuka ta dora a kanta. Sannan zata jira lokacin da Allah zai sake hadasu don ta roqesu gafara. Kwanaki biyu da fara azumi, Mimi tana zaune a saman gadonta tana karatun littafin tahzib mai fassara da hausa, duk lokacin da take karanta littafin dashi da Al'adab, sai ta dinga tunanin cewa gsky rayuwar da tayi ada, rayuwa ce irin ta dabbobi, tunda batasan komai game da addininta ba. Abinda ya kamata ace ta sani tun tana ajin rauda shine take karantawa ynxun. Bokon da dauka a matsayin wayewa, ashe qauyanci ce ga wanda baida ilimin addini. Duk ilimin Bokon da take taqama dashi, wani lokacin Ummi ke cinta gyara a fannin addini. Kai ta fahimci ko maganar fatar baki ta mai ilimin addini ta bambanta da ta mai taqama da boko.
[23/09 5:37 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa

6⃣0⃣Ummi ta katse mata tunani da cewa, kunna TV dinki kiga kawunmu yana yin tafsir. Sai tsalle Ummi keyi. Ita kanta Mimi batasan meyasa ta sauri ba don ganin ta kunna TV. Dirshan ta zauna a gaban TV din tana kallon Ismail cikin qaton masallaci, mai cike da jama'a sunyi tsit suna sauraron daddadar muryarsa. Ta qaro sautin TV din ta koma saman gado tana kallonsa. Tsawon awa daya daya dauka yana yin wa'azin, haqiqa ya ratsata. Bata ta6a zama ta saurari wa'azi ba kamar yau tunda take. Yaya ta shigo tana cewa, kinfa kawunsu Ummi ko? Mimi tace, gsky yanada basira sosai, ya iya tafsir. Yaya tayi dariya, ji tayi tana alfahari dashi. Mimi kuwa, qosawa ma tayi ta ganshi. Inda ya sake burgeta, yadda ya yita amsa tambayoyin mutane da sukayi ta rubutowa bayan an gama wa'azin. Haka ya yita basu amsa cikin ilimi da hikima tare da kawo hujjoji cikin Qur'ani da Hadisai, ko kuma ittifaqin malamai. Mimi dai Ismail ya burgeta har qarshe. Don haka yau da sukayi qosai da kunun gyada, da kanta ta debi nasa ta shirya masa, ta shinfida darduma tana jiran zuwansa. Amma har kusan tara baizo ba. Bata ta6a damuwa don Ismail baizo ba irin yau. Jiya ma da yazo Ummi ce ta kawo masa abin buda baki, amma yau wata kimarsa ce ta qaru a idon Mimi. Tayi ta kai kawo a cikin daki, ta qosa sosai ta ganshi. Agogon dakin ya buga qarfe tara da kwata, ta miqe da nufin ta tambayi yaya, wai yau Kawunsu Ummi ba zaizo ba? Sai kawai taji muryarsa yayi sallama ya shigo gidan. Ta koma baya ta zauna a bakin Gado. Qosawa tayi su gama gaisawa da yaya Amina ko ya shigo, amma ya jima can kafin ya shigo. Da farko ta tsara zata tareshi cikin murna, amma yana shigowa sai taji wani jinkai ya taso mata, ta kishingida tare da fadin sannu da zuwa. Ya zauna bakin gado, sannunki da hutawa. Tace, kaine da sannu. Yau kam bakazo shan ruwa ba? Yace, eh wani bawan Allah ne ya gayyace mu shan ruwa. Can mukaje. Tace ok.
6⃣1⃣Sun danyi shiru na wasu 'yan daqiqoqi, kafin Mimi ta kori Shirun da cewa, mun kalli tafsir dinka, yau kayi qoqari. Yace, to nagode. Wayarsa ta soma ringing. Ya dauka tare da sallama. Ta amsa, macece. Yana qoqarin tambayar wacece, sai ta katseshi da cewa Malam mun yini lfy? Yace lfy Qlw. Tace dama Malam ba kira ne in gaisheka. Wani haushi ne ya tirniqe shi a zuciya. "Amma don Allah kaiki sake kirana." ya kashe ba tare da ya jira jin amsarta ba. Mimi ta kalleshi, "wacece?" shima ya dubeta, "Nima bansan ko wacece ba. Tace, ina ta samu number dinka? Yace ina zan sani? Kinsan Allah, khadija abinnan yana bani haushi da Mamaki. Wai mata masu daraja da aka sansu da kima shine suke tallar kansu ga mazaje. Kafin tace wani abu, sai daya wayar ta soma ruri. Tamkar kada ya dauka, amma saibya daga, kamar yadda yayi zato itama macece. Kamar ya kashe, saidai ya fasa, ya amsa gaisuwar da takeyi masa a qagare. Tace, din Allah Malam zanyi talbaya ne akan bashin azumi da nasha, gashi har wani azumin yazo. Jin cewa ita neman fatawa takeyi, sai ya saurareta, yayi mata kuma cikakken bayani yadda zata gamsu. Mimi dai tana kallon Ismail cike da birgewa. Duk abinda yayi sai taga yayi masa kyau. Ya kalleta. Bari inzo in tafi. Tace da wuri haka? Yace dama nazo ne in duba ku. Akwai wasu litattafai da zanyi nazari, sannan zan qara karatu a gurin Malam, duk a daren nan. Tace ok. Yace, babu wani abu ko? Ta girgiza kai, tare da fadin babu jolai. Yace shikenan in tafi sai gobe kenan? Ta daga kai.
Ismail ya soma karatun nan da qafar dama inji hausawa. Domin kafin azumi ya raba, saida labarin basirarsa da hikimar wa'azinsa ya watsu cikin birni da qauyukan katsina. Faya-fayan karatunsa da kasina naji dana gani, sun fantsama a kasuwa. Su kuwa wasu shaidanun matan, labarin kyawunsa sukeyi, da yadda yake shigarsa ta manyan kaya da kuma jallabiyu 'yan gske. Wasu kuma yadda yake fitar da larabci da turanci tamkar yarensa shi ke burgesu. Kai ko hausa Ismail keyi zakaji hausarsa mai burgewa. Wasu kuma suce, iyayi da salo.
[25/09 9:26 am] Inna👬👫: Canjin rayuwa

6⃣2⃣Masallacinsu kam yana cika tantsam har ta harabar makarantar. Ganin haka sai Ismail ya kawo ma manyan malamai dasu Malam Aminu shawarar cewa, me zai hana su kafa asusun marayu don taimakon marayun dake unguwarsu da maqotan Unguwar. Suka amince. Shida Mahmud suka soma bada tasu gudunmuwar har yace ga ta yayarsa da kuma matarsa. Shi kuwa Mahmud harda ta dansa mus'ab ya saka. Daganan sai Ismail yace yanason kowa ya saka tashi sadakar a ranar na duk abinda Allah ya hore masa. Ranar dai yayi wa'azi ne akan falalar dake cikin taimakon marayu da tsabar ladar da hakan ke dashi. Kafin wani lokaci mutane sukayi ta zuba kudi, wadanda kuwa basuda shi sukayi alwashin kawowa gobe. Kafin sati daya saida takaisu ga bude asusu a Banki. Sbd, wadanda suke kallon wa'azin a TV kuma suna son su bada tasu sadakar. Wannan al'amari ya haskaka Ismail, amma dukda haka bai kasance daga cikin malaman da in daukaka tazo musu, zakaga sunayin girman kai ba. Yana bin duk malamin daya san zai samu qaruwa dashi, ko da kuwa ya girmi malamin. Hakanan ko qaramin yaro ya nuna masa kurensa a harkar karatu yana kar6a. Sannan ko yau yayi tafsir, bayan ya tashi wani yace masa, jiya fa kaza ba daidai bane, in ya dawo gobe zaiyi bayani cewa jiya nace kaza, ba daidai bane, wani dan uwa yayi min gyara. Haka nan shi yayi imani cewa, daukaka ta Allah ce, ba wai iliminsa ne ya kaishi ba. Daukaka daban, ilimi da hikimar wa'azi daban. Ismail ya zama cikin uzurin da sai yayi kwanaki baije gidansu Mimi ba. Ita kuwa Mimi sai take zargin ko don yaga ya soma zama wani abu shine zaija baya dasu. Yau kwana uku tanason ganinsa don taji wacece matarsa din daya bada sadaka harda ita. Amma baizo ba, saidai su ganshi a TV in yana tafsir ko lacca, wadda aketa faman gayyatarsa. Yana yiwa maza ko mata, wata lacca da aka nuna yayi wa mata mai taken Ramadan lacca. Tasha mamakin yadda yake fadawa mata su riqe mazajensu, da hanyoyin kula da miji. Ya kuma kwadaita musu irin romon ladan da zasu samu a gurin mahaliccinsu. Sai taga duk ta zama wata sokuwa, domin ita kanta da take macen bata san abubuwan dashi ya sani ba, na game da yadda ita kanta mace zata kula da kanta. Ta jima tana Mamaki, kuma ta sake yarda Ismail ya dara kallon da takeyi masa.6⃣3⃣Shikam Ismail yakan kira yaya Amina su gaisa, yaji lafiyar Mimi a gurinta, kuma tana sanar da Mimin, domin bashida lokacin kansa. Ba su suka ga Ismail ba, sai azumi yana ashirin, misalin qarfe uku, lokacin Ummi tana daga citta zata kai niqan geron kunun tsamiya, ta gai dashi. Ya amsa tare da cewa, ina mamanki? Mimi qin dago kai tayi. Ummi tace, tana ciki. Yaya ce ta fito tana fadin dan gyangyadi ne ya soma dauka ta, sai kuma naji muryarka sama-sama. Yace, nine kun ganni sai yau. Ya saci kallon Mimi, cikin zolaya yace, 'yar amanata ma na lura fushi takeyi dani. Ko kallo ban isheta ba. Mimi ta dago ta dubeshi, ya dan rame, hakan sai ya qara masa kyau. Shaddar jikinsa mai tsada ce sosai, mai ruwan siminti, hular kansa ta dace sosai. Ta maida kanta taci gaba da firar dankalin da dama shi takeyi tun kafin ya shigo. Ta kammala ta kwashe 6awon sannan ta kai kicin ta wanke hannunta, duk yana kallonta, suna 'yar hira da yaya. Ta zo ta shige dakinta. Ya bita tare da cema yaya, bari inyi lallashi. Can saman Gadonta ta harde qafafun ta. Ya shigo da sallama,a ciki ta amsa. Ya tsaya a gaban gadon, "yau fushi kkyi dani? To, kiyi haquri. Ya ranqwafo tare da sa hannuwansa duka biyu ya dafa gadon. Kinji. Sam ta kasa fada masa cewa, rashin ganinsa ne ya bata haushi. Sai ta kauda kai. Yace, kullum ina fada ma yaya ta gaisheki, sannan ina fada mata uzururruka na, ko bata fada miki? Ta turo baki, ni fa rashin zuwanka bai dameni ba. Cewa din dakai ni matarka ce. Ya zauna, na fada a ina? Cikin salon shagwa6arta ta nuna TV, "anan mana, daka bada sadaka, harma kace, da na yaya. Yayi murmushi, yana son salon shagwa6arta. Yace amma nace matata khadija? Ni fa nufina wadda zan aura. Ta ware idanunta ta kalleshi, zakayi aure ne? Yace eh mana insha Allah. Ta ta6a baki tare da cewa, Hu'um! Zuciyarta fal da takaici. Ta dubeshi, "to ni yaushe zamu rabu? Tayi tambayar cikin daurewar fuska yace, kinsan dai ko ba lokacin azumi ba, laifi ne mace ta nemi a sake ta, babban laifi ne ko!? Ta sake turo baki, ai shi ma alqawari cikashi abu ne mai kyau ko? Yayi murmushi, "haka ne, amma banda haramtaccen alqawari. Ina nufin kayi alqawarin laifi. Misali mutum ne yayi alqawarin aikata wani laifi da Allah baya so, to ba'ason ya cika. Tace, jiya fa naji kana cewa saki halasne, a cikin tafsirinka. Yace, sai kuma nace me? Allah baya sonshi, dukda halas ne. Na lura in kinyi ilimi nan gaba za'ayi fama dake kema.6⃣4⃣Yasa hannu cikin aljihu ya ciro kudi 'yan dari biyar-biyar. Yace zan sallameku sbd batun sallah dake gabatowa. Tace, ai yaya zaka bawa kudi. Ni ina zuwa kasuwa? Yace, nima bance kije kasuwa ba ai. Tace, to naga zaka bani kudi ne. Yace na fasa baki ki shirya gobe muje tare. Tace, kana son sole sai wanda ya sanni ya ganni kai kam. To shikenan, ki rubuta min abinda kk so. Ya miqe ya shiga dakin yaya ya qirga dubu goma ya bata, yace ta saima yara kayan sallah. Tayi godiya tare da cewa, kaima da kk fama da kanka. Kaima fa dalibi ne har ynxu. Yace wani bawan Allah ne ya sameni nayi masa bayanin yadda zai fidda zakkarsa, shine da ya cire ya bani. Yaya tace, Allah ya taimaka. Ai ranar da kayi wa'azin zakkarnan, dole zukatan mutane su raunana, indai da sauran imani, su fito da zakkar su ba da. Yace kinsan kudi shiga zuci ne dasu. Sai su dinga ganin kamar in sun bada zakka kudin zai qare. Ba su san in sun cire

1 Comments On CANJIN RAYUWA
avatar
mariya-6-8

11 months ago

Reply

In HAUSA language

Please Login or Register in order to submit comment