Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuwa ce,amma ga shi an sai mata cikin wannan shekarar.ya ce,bari ki ga fa irin gadaje da abokina ya turo min.su ma sai kin zaba. Ta kalle su,ta kalli dad, sun yi yawa.ya ce kar ki damu uwata.zan yi miki duk abin da kike so.zan kashe ko nawa ne gurin auren nan ba tare da jin cewa na yi asara ba.ribar mai daya in aka bani kwangilarsa,zan ribanya dukkan kudin da na kashe. MIMI ta mike.zan sha magani dad,zan kwanta ne. ya ce,to je ki kwanta.ya fada miki za ku fita karfe goma ko?ta ce,eh.ya ce,to sai ku je har da na'ima.ta ce,to.A sama MIMI ke ta nazarin abubuwa.zuciyarta ta fi aminta cewa ta bi umurnin mahaifinta.dubi duk daular da yake shirya mata. gaskiya bai kamata ta bari a ji su ba.ita da mahaifinta.hakuri shi ne kurum mafitarta.za ta huce haushinta a kan abbas ne kurum,wanda ya dage cewa sai ya aure ta. Har ta kwanta da nufin barci,sai agogonta ya buga sha daya.kallon agogon ya zo daidai da ringin din wayarta.khalil ne.gabanta ya fadi.shi da take tunanin shafe babinsa,amma ba ta iya share shi,don haka ta daga.cikin sanyin murya ta ce,dear,ina ka shiga na kasa samun ka a waya?ya ce,na yi kokarin na hakura da ke ne,shi ya sa na kashe wayata,sai na ga ashe ba zan iya ba.zan mutu MIMI.don ALLAH ki fada min yaya za mu yi."
[01/10 9:45 pm] Abdul: ya soma kuka.
itama kukan ta soma yi.
sai kuma ta tuna da batun malam Isma'il. da sauri ta CE, yauwa Khalil zanyi wa malam din nan magana, ko zai bamu magani.
ya ce AI ba irin shine masu yin maga ni ba.
ta ce bari kaji abin da ya CE min...
nan ta fada masa yadda sukayi.
ya CE, OK, ki kirashi yanzu.
sai dai ina so ki Sani ba mu da ishashen lokaci, sabo da kullum kwanakin aurenki kara matsowa yake.
ta CE, to bari in kira shi.
zan fada maka duk yadda m kayi.
ba tare da wani dogon nazari ba, mm ta soma kiran Layin Isma'il.
ya gama shafa'i da wururi kenan, yana kwance kan doguwar dar dumar, duk hankalin shi ya koma katsina, gani yake kamar akwai abin da mahamud yake boye masa.
yana ganin cikin satin nan zai koma gida...karshen wata yayi mashi nisa, duk da saura kwanaki takwas watan ya kare...
Ringing din wayar Sa ne ya katse masa tunani.
cikin sauri ya duba, bai San lambar ba, amma yadda yaga numbobin ya San cewa na musan man ne.
ya daga tare da sallama, yar siririyar murya CE, ta amsa da helo! ya sake yin sallama, ta CE, ni ce mm.
ya CE, baki amsa sallamata ba..."
[01/10 9:45 pm] Abdul: Wanda ya kasance ba ya qmsa sallama wajibi ne a cikin addini.
cikin kosawa ta amsa, sanan Tace, kasan dalilin kiranka..?
ya CE, a a...Tace, ka CE, zaka bani maganin bakin ciki da, yaye damuwa.
sanan kace, zan iya cimma buri na.
Isma'il yayi dan murmushi, amkar yana gaban ta, sanan ya CE, kwarai kuwa...ta CE, to don Allah ka tai maka min ina cikin damuwa, mahaifi nane .yace, dakata!
ba sai naji damuwar ki ba, ko abin da kike ciki ba, sanan zan taimaka maki.
ta ce , nasani malam.
INA so be kawai in fada maka, kila zaka tausaya min cikin gaggawa..
ya CE, Allah ne me taimako.
tun da kin zabi ki fada min, INA sauraron ki.." ta CE, dady nane zai yi Mun auren dole...INA kuma da Wanda nake so.
wlh mlm ni dashi Muna cikin wani hali.
shine muke son mafita.
Isma'il yace, mafita dai ita CE komawa ga Allah. Zaki: ya tashi cikin dare..?...ta CE, zan iya ko mai mlm don in cin ma buri na.
ya CE ki tashi karfe ukun dare kiyi alwala, kiyi sallah raka'a biyu ko sama da haka.
[01/10 9:45 pm] Abdul: ki fada wa Allah da muwarki.
in sha Allahu Allah zai yaye maki halin da kike ciki.
sanan ki yawaita zikirin Allah da karatun Alkur'ani mai girma.
ba wai sai can cincikin Alkur'ani ba, ko kanan surorine kiyi ta karanta su, Zaki sami waraka.
Mimi dai shiru, tayi, yana magana ita tana kuwa tana tunanin ta daban...to, shi wanan malamin da yake cewa tayi sallah, baya ganin cewa da ba ta damu da yin sallah ba, yanzu da matsala ya sameta, sai kuma ta wai wayi sallar...?...tam kar ya shiga zuciyar, ta, ya CE, kar ki dubi yawan zunubin ki, matsawar kika t ba, Allah zai yafe maki kurakuran ki sanan, yana da kyau kiyi adu'ar istihara, wato Neman zabin Allah kafin kikyi zabin mahaifin ki.
ta CE, to malam AI ni ban iya ba...duk abin da ka CE min inyi din nan bansan ta inda zan fara ba...
ya CE, in kin amince sai in koya maki yadda zakiyi.
ta CE, to, amma ka bari zan kiraka.
Khalil, ta kira, ta fada masa ko mai.."
[01/10 9:45 pm] Abdul: ki fada wa Allah da muwarki.
in sha Allahu Allah zai yaye maki halin da kike ciki.
sanan ki yawaita zikirin Allah da karatun Alkur'ani mai girma.
ba wai sai can cincikin Alkur'ani ba, ko kanan surorine kiyi ta karanta su, Zaki sami waraka.
Mimi dai shiru, tayi, yana magana ita tana kuwa tana tunanin ta daban...to, shi wanan malamin da yake cewa tayi sallah, baya ganin cewa da ba ta damu da yin sallah ba, yanzu da matsala ya sameta, sai kuma ta wai wayi sallar...?...tam kar ya shiga zuciyar, ta, ya CE, kar ki dubi yawan zunubin ki, matsawar kika t ba, Allah zai yafe maki kurakuran ki sanan, yana da kyau kiyi adu'ar istihara, wato Neman zabin Allah kafin kikyi zabin mahaifin ki.
ta CE, to malam AI ni ban iya ba...duk abin da ka CE min inyi din nan bansan ta inda zan fara ba...
ya CE, in kin amince sai in koya maki yadda zakiyi.
ta CE, to, amma ka bari zan kiraka.
Khalil, ta kira, ta fada masa ko mai.."
[01/10 9:45 pm] Abdul: Shi ya sa kike son shi,to ki ba abbas dama ki ga irin tasa.MIMI ta ce,ke yanzu za ki so a raba ki da faisal?ta ce,aa. amma in ta kama zan iya sadaukarwa.ina nufin dad dinki ya cancanci sadaukar da soyayyarki don ki faranta masa rai. MIMI ta ce,na yi yunkurin haka,amma na kasadon haka yanzu mu tsai da shawara ta karshe,ni da khalil.kuma ita ce mafita. mina ta ce,me kuka yanke? MIMI ta ce,kar ki damu,ba sai kin ji ba.suna yin zantukan nan ne a inda suka kebe kansu lokacin da abbas da abokansa suka je gurin manajan hall din da su mina suka ce yayi musu. Duk komai mina da na'ima suka zaba,MIMI ko kallon su ba ta yi.sai kusan daya saura suka nufi gidan da za su zauna.ba su da nisa da gidan iyayen mina. sai murna take yi,wai za ta dinga zuwa a kai,a kai,ga shi gidan ya burge ta.ko MIMI ta yaba gidan a zuciyarta,amma ba ta nuna ba. abbas ya zo kusa da ita,dear ya kika ga gidan naki?saman nan naki ne ke daya,falulluka uku,duk naki ne.da na lura kina son zama a sama,shi ya sa kike abar so kamar tsuntsaye.MIMI ta kau da kai,ina jin yunwa,don haka zan je gida.ya ce,bari mu je gurin cin abinci,mu ci mana. ta ce,aa ba na cin abincin ko'ina,ba komai nake ci ba. ya ce,shi ke nan bari mu fara kai mina ko?ba ta kanka ba ta nufi fita. sun fara sauke mina wadda take ta yaba wa abbas,har MIMI ta soma jin haushinta,ya sauke abokansa gidan cin abinci, ya ce bari ya kai ta gida ya dawo,zai same su a nan.duk zantukan da yake mata tun sad da suka taho ba ta tanka shi ba,har suka zo gidan,yana yi mata magana,ba ta tanka shi ba. ta sauka ta nufi ciki. ko da ya koma,abokansa korafi suka yi masa a kanta.munir ya ce,don tana da kyau sai ta hada da iskanci?don wannan ya wuce jan aji,tana kallon mu sai ka ce ta ga kashi.ya ce,ku yi hakuri abokaina.tana cikin fushi ne,amma lokaci kadan za ku ce tafi kowa kirki a nan gaba.dariya suka yi masa,don sun gane yayi nisa a soyayya.
[01/10 9:45 pm] Abdul: Isma'il yana murna zai soma cusa tauhidi a zuciyar MIMI,ya tanaji abubuwan da zai fada mata don kara cusa mata ALLAH a cikin lamurranta.ya yi ta jiran kiranta,amma shiru.bayan laasar sun fita shi da direban yara,hamisu ke nan, don in an aike shi ko zai kai yara wani gurin,lsma'il kan bi shi don ganin gari.ya kosa su dawo don ya kira ta.haka kuwa aka yi.suna dawowa ya shiga daki,sai da ya zauna tsakiyar katifa ya nemi layinta ya kira.gab da za ta tsinke,ta daga.ya yi sallama.a kagare ta amsa.ya ce,ya ranki ya dade na ji shiru ne?ta ce,malam ka bar shi kawai.mun canza dabara. khalil ya ce naka zai ci lokaci.lsma'il cikin sauri ya ce,amma nawa shi ne mai tabbas,ln kin yi sabanin abin da na fada miki,karshe ki yi nadama.ba lalle ba ne adduarki ta dauki lokaci, domin ALLAH mai jin kan bayinsa ne.ba ki da wata dabara sabanin yi masa biyayya.ta yi jim,ta ce,don ALLAH ka bar shi kawai malam.sai ta yi tsaki.ta kuma kashe wayarta. Ta ko'ina abubuwa sun dauki zafi,domin ko can katsina tuni an daura auren zainab da alhaji lawal.an kuma kai ta gidan.matansa uku ga yara nan kwatsam. gidan bene ne hawa daya. dakinsa ne a saman,sai matarsa ta ukun,sai kuma dakin zainabu.a kasa matansa biyu ne da 'ya'yansu da kuma 'ya'yan wasu matan da suka fita. tunda aka kai zainabu take cikin kuka.bayan kowa ya kama gabansa,ta tashi ta datse dakin alhaji lawal ya taho misalin karfe sha daya da tsarabar kazarsa da abin sha.ya murda kofar amarya,ya ji ta gam.ya yi ta bugawa tamkar zai balla kofar ta ki budewa.ba zainabu ba,ina zaton duk matan gidan suna jin irin zagin da yake surfa wa amaryar tasa.fadi yake,ni zaki kawo wa rainin wayo don ubanki?yar matsiyata, ba za ki bude ba?ln kika bari na balla kofar nan na shigo,sai na karairaya ki,ko in sa a daure iyayenki har sai su biya ni abin da na kashe.lta dai zainabu jikinta sai bari yake yi,tana ta kuka.alhaji cikin takaici ya nufi dakin matarsa ta ukun ya sauke mata wahalar da ya debo ta magungunan da ya dankara.
[01/10 9:45 pm] Abdul: Zainabu har goman safe ba ta bude kofa ba.sai da ya bar gidan,uwargidan ta zo ta buga,ta ce,bude yarinya ni ce,shi ya fita. matar ta shiga dakin,tana kallon zainabu cikin tausayi,ta ce,ALLAH sarki, ashe yarinya ce karama.ke ko me ya kai ki auren alhaji?cikin kuka,zainabu ta ce dole aka yi min.kudi ya nuna wa iyayenalna da wanda nake so,yake so na.ta ce,amma iyayenki ba su bincika ba ne?ta ce ni fa ban san komai a kan auren nan ba.ta ce,kai iyaye da yawa suna yin kuskure.da zara sun ga kudi,sai su tura 'ya'yayensu kawai,babu bincike. zainabu cikin tsoro, ta ce don allah hajiya me yake yi?ta ce,ba komai,kar ki damu.shawarar da zan ba ki,kar ki sake rufe masa kofa.duk abin da ya ce,ki yi,kar ki ke yi masa gardama hakan zai fi miki alheri,ke da iyayenki.ln kuma kin ki,to zai tozarta ku gaba dayanku. zainabu cikin kuka ta ce,na shiga uku!hajiya to ke 'yar uwarsa ce?aa,ni ce matarsa ta farko.ya aure ni tun bashi da ko kwabo. 'yayana goma da shi. zainab ta zaro ido,dama yaransa goma ya boye min?ta ce,nawa ke nan kadai 'ya'yansa ashirin da biyar,banda masu ciki uku. zainab ta ce ban gane ba. matar alhaji ta ce,matan da ya saka goma cif.ta karshen tana da ciki.sai sauran matansa biyu,duk suna da ciki.zainabu ta sake rushewa da kuka,tare da cewa,ita dai za ta gudu. matar ta ce kar ki fara!zai sa a kama iyayenki,kuma ba zai sake su ba sai ran da ya ji an ce an ganki,kin dawo dakinsa, ta mike, bari in sa a kawo miki abin kari. zainabu ba ta ce aa ba,dm tana jin yunwa,rabonta da abinci tun jiya da safe.koko ne da kosai,duk sun huce,yarinyar da ta kawo za ta kusan saarta.zainabu dai haka ta tuttura. da rana lnna yalwa ta zo, aminiyar lnnarsu ce.zainbu cikin kuka ta fada mata komai.lnna yalwa,ta ce,da allah can, duk karya ta fada miki,kika kama.kishiya ce har za ta ce miki ga laifin miji,ki hau kai?zainabu ta ce,lnna yalwa gaske ne.ga shi nan jiya sai zagi na yake yi dana rufe masa kofar.jiya fa na zo gidan.ln da mutunci bai dace yayi hakan ba.
[01/10 9:45 pm] Abdul: Laifinki ne.yaya zaki rufe masa kofa?lna kika taba jin haka? bayan tafiyar lnna yalwa,ba jimawa yaran gidan suka cika mata daki, wanda gado ne kurum wanda alhaji ya sa mai kyau ne,amma da gani ba sabo ba ne.wadda ya aura nan dakin yake kawo ta.ln za ta tafi kuma ta bar masa gadonsa. ya shigo tana sallar magariba.ya zauna bakin gado,yana ta huci,sai ka ce kumurcin maciji.tsoro da fargaba suka hana ta idar da sallar.sai yi take tana sallamewa.ta sallame ta sake mikewa.ya finciko ta, ni za ki zo mawa da salon salla?magariba dai rakaa uku ce.kuma nafilar da na sani bayan magariba rakaa biyu ce,amma ke da na shigo kike ta zabga salla ko?cikin tsoro da kuka ta ce,aa baba ba haka ba ne. baba?ya tambaye ta,cikin fushi.kuka ta ci gaba da yi. ya kashe ta da mari,nine babanki?to,bari in nuna miki cewa ni mijinki ne,ba ubanki ba! da karfinsa ya yi amfani,ya raba ta da tufafinta,ya jefa ta kan gadon.duk 'yan gida da yara suna jin ihunta.da ma ya yi mata nata shiri na musamman.don kansa ya bar ta,ba don rokon da take masa ba,ko don wahalar da ta sha.ya bar ta yashe ba kulawa bare tausayawa,ya nufi dakinsa. haka ta kwanta babu barci sai kuka take yi.ya fita da wuri,don haka hajiya lndo ce uwargidansa ta zo ta duba ta,ta dafa ruwan zafi ta taimaka mata,ta ba ta abin kari.tsawon sati guda da yayi a dakinta bai raga mata ko sassauta mata ba.haike mata kurum yake yi.don haka ta sha azaba.tsoronsa da tsanarsa sun dasu cikin zuciyarta. khalil ya yi nasarar goge dan imanin MIMI da dan tauhidin da lsma'il ya soma cusa mata.ya zuwa 'yan kwanakin da suka biyo baya,sun yi nisa cikin tsarin yadda za su gudu.ko yanzu da suke yin waya fada mata yake yi,ta nuna cewa ta amince sai daf da auren sai su gudu.suna da bukatar kudi kafin ranar.ya ce,zan dauki sarkar mamana in kai kasuwa in sai da,sbd dad dinmu ba shi da kudi a gida sbd siyasarsa din nan.MIMI ta ce,kai baka da naka kudin ne?ya ce,account dina babu kudi,bai fi dubu ashirin ba.dad baya zuba mana kudi.
[01/10 9:45 pm] Abdul: (2)Dad baya zuba mana kudi sosai yanzu saboda siyasa.ta ce,ka bar shi,ina da kudi a cikin karamin account dina.kamar nawa za mu rike?ya ce,muna bukatar kudi sosai,sbd za mu kama guri mai kyau ne a wani state din wanda ba za su yi tunanin za mu je ba.MIMI ta ce,ok,ka samo,ni ma zan samo,sai mu hada.ya ce,shi ke nan sai mun yi waya. bayan sun yi bankwana ta soma tunanin yadda za ta kwashe duk wani abu nata mai amfani.matsalarta daya.kudinta masu yawa suna cikin babban account dinta.ln kuma ta taba dole ne mahaifinta ya ji alat. Momy nafisa an dawo daga dubai,'yan gidansu abbas sun kawo kayan lefe.ran hajiya sauda ya baci da yadda alhaji ya nuna mata.matsayinta na wadda ta haifi MIMI ya kyautu a bata hakkinta ko da na shawara ne,amma alhai yayi mata dif,tunda ta ce baza ta shiga lamarinsa da MIMI ba,ita 'yar ba da shawara ce.bata fadi hakan da wata manufa ba, sai dai nuna ma alhaji kurensa,amma ya dauka da zafi,don haka ta lashi takobi ita da yaranta babu inda za su je,domin auren abba a nan katsina aka yi shi,na MIMI in baza a kawo nan ba,to su je can su yi kayansu. biki saura kwana goma MIMI ta yi wanka,ciki sauri ta zura doguwar rigarta atamfa,sai dan bakin karamin mayafi. takalmi mara tudu ta saka,ta kwashi katinta na ATM daga jakarta da take zuwa banki,ta zuba su cikin jakarta da takan je saloom,ta ra aya takar.ta kwashi wayoyinta.tana sauka kasa,momy zata hawo saman ta ce,aa sai ina haka MIMI? ta ce,za ta je saloon.na'ima ta ce yayi wuri sis.saura kwana goma biki fa?MIMI ta tabe baki,ke kika san da wani biki,ni kam ban san da shi ba. momy nafisa ta ce,ki zo ga tela,zai gan ki sbd dinkunan kayan biki,kin ki zuwa ki ga kayan ki.MIMI ta ce.momy har da ke a wannan maganar bayan kin san komai?ni fa ba son shi nake yi ba.momy ta sassauta murya,yanzun dai ki bi ni kawai.ln lokacin da za ki ce wa alhaji baki son abbas yayi,zan sanar da ke ki tubure kawai.a ran MIMI ta ce,ke ma baki san namu shirin ba.a fili ta ce,
[01/10 9:45 pm] Abdul: (3)A fili ta ce,shi ke nan momy.tela ya gwada MIMI sosai.kafin ta fice,makullin motar momy ta dauka ta fita.lta ta ja motar zuwa bankinta na karamin asusunta,inda ta kwashe kudinta kaf.ta nufi babban asusun da ke wani bankin daban,ta dibi dubu dari biyu.za ta kara sai kiran dad ya shigo.ta daga ya ce,MIMI kina ina ne?ta ce, ina banki ne.dad ya ce,yaya kika taba wannan account din MIMI?ta ce,dad ba ni da kudi ne,kuma zan yi gyaran jikina ne.ya kalli alhaji akilu,ya ce,shi ke nan ya isa,ki bari zan ba ki kudi. kar ki kuma cira daga wannan account din,ina son yi miki wani tsari ne da kudin.za ki yi kasuwanci kina daga gida,kuma na manyan kudi kin gane?MIMI ta ce,eh dad ba zan kara cirewa ba.ya ce,shi ke nan. alhaji bishir cikin dariya ya ce,ka ji 'yar kwal uba? wai tana fadin bata so,amma ta zo tana dibar kudi wai za ta yi gyaran jiki.suka sa dariya.alhaji akilu ya ce,me na fada maka?kiyayyar mata ba ta zuwa ko'ina.amma shi ma abbas din ai shi ya dace ya ba ta kudin gyaran jikin. alhaji bishir ya ce,ai ita da shi duk daya ne.ka rabu da shi,zan ba ta.alhaji akilu ya kira layin abbas.bayan ya dauka,ya ce abbas ya baka bai wa amaryarka kudin gyaran jiki ba?abbas ya ce,dad ta ki ba ni damar in san abin da take bukata ne.amma zan ba ta anjima. ya ce,shi ke nan ka je ka ba ta.ka lallabe ta,ka san yarinya ce.abbas ya ce, insha allah dad. MIMI gida ta wuce ta adana kudinta da duk abin da ya kamata ta tafi da su,amma banda kaya. lsma'il ya dangana har zuwa ranar ashirin da tara da alhaji bishir ya yi musu albashi.duk da kin karatun da MIMI ta yi,bai sa alhaji canzawa daga dubu darin da ya alkawarta zai ba shi ba.lsma'il yayi ta juya kudin a cikin dakinsa,yana farin ciki.sam bai taba rika su ba a hannunsa ko na wani ma bare nasa.lalle goben nan sai katsina,ya je ya biya kudin gaisuwa,ya hada kayan sa rana,ya sai ma zainabu waya,yayi alheri,yayi sabbin dinkuna,yana ta baje burinsa.nan ya kira mahmud ya sanar da shi cewa gobe yana tafe.
[01/10 9:45 pm] Abdul: (4)Tun dare yake ta shirin sa,washegari ya kira hajiya sauda ya fada mata cewa yau yana son zuwa gida ya ga 'yan uwa.ta ce ba laifi,sai ka iso.ln ka zo kuma don allah ina neman ka.ya ce babu matsala.sai dai ina son don allah ki sanar da alhaji sbd ban san lokacin da zai fito ba.ta ce,ya ba ka albashi dai ko?ya ce, wallahi ya ba ni.ki yi min godiya.ta ce,to zan sanar da shi yanzun nan. ba a yi minti talatin ba, sai ga hamisu direba ya ce lsma'il ya je in ji alhaji.a falo ya same shi.ya zauna,ya gai da alhajin cikin girmamawa.alhaji ya ce, sauda ta kira ni,ta sanar da ni cewa zaka je gida yau. haka ne?ya ce,eh alhaji.lna son in je in ga 'yan uwa ne. alhaji ya ce,da fatan ba mu takura maka ba ko?ina nufin ka ji dadin zama da mu?lsma'il ya ce,na ji dadi sosai.alhaji ya ce,to ina fatan za ka dawo.lsma'il ya ce,eh to,na ji ana cewa za a yi wa wadda na zo in koyar da ita aure,shi ne ban sani ba ko hakan yana nufin ni ma na gama aikina ke nan?alhaji yayi murmushi,ai in na lura ita din bata yin karatun,amma kannenta suna yin karatun. kana yi mana salla.ga yaran nan suna yin karatu sosai,suna yin salla a kan lokaci.wannan ya fi min komai.yanzun ma da ka ce zaka je gida din,na kira ka ne in ji ko kwana nawa za ka yi?lsma'il ya ce,to ina ganin dai zan yi kamar sati daya.alhaji ya ce,har sati daya?na zaci baza ka wuce kwana uku ko biyu ba.har me zaka yi haka?lsma'il ya ce,eh to ina so dai za a sa ranar aurena ne tukuna.alhaji yayi 'yar dariya,oho haka ne?to ba damuwa.allah yasa alheri.ya laluba aljihunsa,dubu biyar ya kara masa.ga wannan kayi kudin mota.ka amshi lambata gurin sauda.ln ya so in ka tashi kira na.sai ka kira ni kai tsaye,ba sai ka bita gurin hajiya sauda ba.lsma'il ya ce,to na gode sosai. bayanan fitarsa ne momy nafisa ta ce,na lura yaron nan yayi maka ko?alhaji ya ce yana da hankali sosai.lna son mutum haka.har gareji, hamisu direba ya kai lsma'il,bayan yayi sallama da dukkan maaikata gidan.
[01/10 9:45 pm] Abdul: (5)Kowa yayi kewarsa, damuwarsu kar ya dade ko ya ma ki dawowa. shida na yamma daidai ya isa gida.matasan da suke zama a gindin bishiyar da ke kofar gidansu suna nan zaune kamar yadda suka saba.hirar ta kwallo ce sai ta siyasa.dukkansu sun juyo suna yi wa lsma'il sannu da isowa,bayan dayansu ya sanar da su cewa ga lsma'il nan ya dawo.ya isa gurinsu ya babba su hannu suka gaisa.suna ta yi masa murna da samu aiki a abuja. wasunsu har suna cewa.ustaz ka ga yadda ka yi kyau kuwa?gaskiya abuja ta amshe ka! shi dai godiya yayi musu,ya shige gida.kai tsaye cikin gidan ya shige.matan gidan suna ta haramar sauke girki, sallamarsa suka ji.fatu ce ta soma ganin sa.cikin irin faraar da bata taba yi masa ba ta ce,ga yan abuja,ga yan abuja!nan dai aka yi ta masa sannu da zuwa.ya amsa cikin jin dadi da mamakin fatu.a wata zuciyar ya ce,kila don dai ta daina ganin sa ne. dakin lnna ya shiga ya gaishe ta,sanan ya mika mata tsarabarsu.ya tashi ya koma dakinsa ya bude,yayi kakkabe-kakkabe a gurguje,sbd lokacin salla ya kusa.ya shimfida katifarsa,ya dauki bokitin ruwa wankansa ya kulle kofar da makulli,ya nufi cikin don yin wanka.da ya dawo,yayi alwala ya zura jallabiyarsa ya sake kulle

1 Comments On CANJIN RAYUWA
avatar
mariya-6-8

11 months ago

Reply

In HAUSA language

Please Login or Register in order to submit comment