Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kofa ya nufi masallacin kusa da su. bayan idar da sallar ya dawo ya zauna ya kasafta kudinsa,ya adana sauran ya canza kaya tare da fesa turarurruka masu kamshi.ya yi kyau matuka cikin shadda mai ruwan toka,ya murza hula.ya kosa ya ga zainabu,ga shi tunda ya shigo garin katsina yake ta neman layin mahmud. cikin nishadi yake takawa,duk da lokaci bayan lokaci gabansa yana faduwa.sam ba ya ganin nisan gidan su zainabu daga nasu gidan.a kafarsa ya taka.har ya je kofar gidan,sai kuma ya tuna bai zo mata da tsaraba ba.don haka ya juya,ya tare dan acaba ya hau,sai wani shago ya je inda ya siyo mata waya ta naira dubu biyar.ya sake komawa kofar gidan.kamar an turo shi,sai ga kanin zainabu.kafin lsma'il yayi masa magana har ya juya da gudu ya koma ciki.a ran lsma'il ya ce,
[01/10 9:45 pm] Abdul: (6)Yawwa kira ta,kai ma ka zo ka dan ja wani abu.kwarai idanunsa suka kosa su ga fitowarta.cikin duhun zauren ya ga alamun fitowar mutum.a zatonsa zainabunsa ce,har da gyara tsayuwa. muryar mahaifiyarta ya ji daga sama tana cewa,sannu malam lsma'il da zuwa.cikin faraa ya ce,yawwa lnna. cikin girmamawa ya gai da ta.ta amsa.ta ci gaba da cewa,sai ka samu labarin zainabu ta yi aure ko?ledar wayar da ke hannunsa ta subuce,ta fadi a kasa.cikin in-ina ya ce,mene kika ce lnna?ta ce,zainabu ta yi aure.allah ya sa ba rabonka ba ce.kodayake laifinka ne. tunda baka kawo ko da sallama ba.lsma'il ya ce, inna don allah kar kiyi min haka.da shirina na zo.sai an sa bikinmu zan koma.ta ce assha!ai ka bar shiri tun rani yaro.tana gidan alhaji lawan.ba tare da jiran sake ji daga gare shi ba ta koma ciki. lsma'il ya tsuguna,ya dauki wayarsa jiki babu karfi,zuciyar na tafarfasa,ya nufi gidan yaya amina.da kyar ya kai. sai ganin mutum ta yi babu ko sallama.kan tabarmar da ya gani a shimfide ya zube zaune tare da dora kansa a guiwowinsa.cikin fargaba ta ce,lsma'il lafiya?ta tambaye shi fiye da sau biyar,ya dago kai da kyar ya ce,lafiya lau.ta ce ina fa lafiya,dube ka fa?me ke maka ciwo?ya girgiza kai, babu. ya sake dosa kansa a kan hannuwansa wadanda suke sarkafe a guiwowinsa.ya ce,yaya ashe zainabu ta yi aure?ta ce,au da ma damuwar ke nan?ta sake tausasa murya,ka yi hakuri.allah ya rubuta cewa zainabu ba matarka ba ce.nan ta shaida masa abin da ta ji game da auren. ya ce,mahmud bai kyauta min ba.me zai sa muna waya,amma yaki sanar da ni?ni na san da a ce ina nan ba yadda za a yi a raba ni da ita.sam mahmud bai cika alkawari ba,kuma bai rike min amana ba.yaya amina ta ce kar ka ga laifinsa,domin a boye duk aka yi komai.sai daurin aure aka ji.lsma'il ya sauke ajiyar zuciya,wasu zafafan hawaye suka zubo kan kumatunsa.ta ce,haba don allah lsma'il,sai ka ce ba namiji ba?kamar baka da ilimi.ka fa san komai mukaddari ne.ka yi hakuri,zainabu ba rabonka ba ce.
[01/10 9:45 pm] Abdul: (7)Allah zai baka wadda ta fi ta komai.lsma'il ya ce,shi ke nan yaya na gode.ya ciro dubu uku daga aljihunsa, ga wannan yaya.ta amsa tana fadin, har da kudi haka.ya ce,ba yawa.lna ganin gobe ma zan juya kawai,da ma da kyar alhajin ya bari na taho. ta ce,haba dai ka dan kwana biyu mana?ya ce,aa ba zan iya zama a garin nan ba,ina tuna zainabu.lna bukatar cire ta daga raina. ya mike a kasalance,ya dauki ledar wayarsa ya ce,to ni sai na dawo.ta ce, ba zaka biyo ba gobe ke nan?ya ce sammako zan yi. da kyar ya isa gida.tunda ya bude kofarsa ya fada kan katifa,bayan rufe kofar ya soma kuka.shi kansa bai san yana tsananin son zainabu haka ba sai da ya rasa ta.ya yi kuka sosai,ya dangana,ya fita cikin dare yayi alwala.gurin allah ya yi ta kai kukansa.bukatarsa allah ya cire masa son zainabu,ya ba shi dangana ya sada shi da mafi alheri. daga bisani ya dauki alkurani,yana karantawa. Kafin wani lokaci,salama ta sauka a zuciyarsa.sai da yayi sallar asubahi,ya soma jin barci. yana dawowa daga masallaci ya kwanta.ba shi ya farka ba sai goma saura. shi ma kwankwasa kofarsa aka yi ya farka.ya tashi da kyar ya zare sakatar.mahmud ne,don haka ya dawo ya zauna. mahmud ya shigo,shi ma ya zauna. lsma'il ya ba shi hannu suka gaisa.ya ce,na yi ta kiran wayarka a kashe. mahmud ya gyara zama.ina sane na kashe,domin bana so ka rike ni a ranka.na san dai zuwa yanzu kaji komai.lsma'il ya tsura ma bakin kofa ido,kamar mai kallon wani abu a gurin. mahmud ya ce,ka yi hakuri allah ya kaddara ba matarka ba ce.lsma'il ya ce,duk da haka mahmud,kai ma na ga laifinka.me zai sa ba ka kira ni ka fada min ba?na tabbata zainabu dole aka yi mata,don tana so na.mahmud ya ce,fada maka ba zai kare ka da komai ba.a lokacin da na samu labarin kwana kadan suka rage a daura aure. amma ka yi min afuwa.lsma'il ya ce,ni yanzu zan shirya in koma abuja.malam yana nan kuwa?mahmud ya ce,yana nan.na dai bar shi a gida. haba dai ka ce yau za ka koma?ya ce.tun jiya katsina ta fita daga raina.
[01/10 9:45 pm] Abdul: (8)Mahmud ya ce,allah yasa hakan shine mafi alheri.amma ya kamata ka dan yi kwana biyu.lsma'il ya ce,in na zauna babu abin da zan yi.da a ce na san da wannan matsalar.lallai da ba zan zo ba.mahmud ya ce,shi ke nan allah ya kai ka lafiya.ko wanka lsmail bai yi ba,ya hada nasa-ya-nasa ya shiga cikin gida yin sallama.fatu ta ce, lsma'il sai ka ji batun auren zainabu.bai san lokacin da murmushi ya sauka a fuskarsa ba.ya ce,zainabu ta yi aure.fatana allah ya bata zaman lafiya.fatu ta yi 'yar dariya,ka dangana ke nan?bai tanka ta ba,ya wuce abinsa dakin lnna.ya shiga ya sanar mata cewa zai koma,ya kawo dubu biyu ya bata.ta amsa tana godiya.ta ce ko ka hadu da yan uwanka?ya ce mun gaisa da asuba a masallaci,amma ga wannan ki basu.ya mika mata dubu uku.ta ce,an gode.allah ya saka da alkhairan.sai kuma kaji wannan yarinyar da kake nema ta yi aure ko?ya ce eh na ji lnna.allah bai yi dani ba.ta ce,duk da haka ma sun so yaudararka ne.ka je ka amshi duk abin da ka san cewa naka ne,lna nufin wanda ka bata.ka kuma lssafa kudin da ka bata, tallar nan duk a amso su,ya ce,lnna a bar wannan maganar kawai.ban bata don in karba ba.ya mike,ya fito,ta ce,to shi kenan allah ya tsare hanya.nan su ma matan gidan ya basu dubu daya,ya dauki jakarsa. Bayan ya ba mahmud dubu biyu,mahmud ya ce, kudin mene ne?ya ce,kudin albashina mana.dana yi niyyar gabatar da abubuwan aurena har zuwa a sa rana.amma tunda babu zancen,gara in yi alheri in samu lada. mahmud ya ce,na gode sosai.gidan su mahmud suka je,inda ya ba malam dubu uku.ya goya shi a mashin dinsa.har za su wuce tasha,ya ce,kodayake ka kai ni gidan alhaji bishir in gaisa da hajiya sauda.sai da suka je kofar gidan,ya kira layin hajiyar ya ce mata ga shi a waje,ta turo abdullahi suka shiga tare.lsmail bai boye mata komai ba game da MIMI na kin karatu ba.ya sanar da ita halin da yake ciki.ta ce,ba komai kar ya damu da batun MIMI tunda aure za ta yi.yanzu ya koma ya ci gaba da abin da yake yi,a kan zainabu kuma tace kar ya damu,
[01/10 9:45 pm] Abdul: (9)Kila ita din ba alheri ba ce a gare shi.ta ce,in da zai yarda ma da ya koma makaranta don zurfafa iliminsa gaba daya a fannin bokon da kuma lslamiyyar ya ce,shi ma tunaninsa ke nan a yanzu suka yi bankwana,bayan ta ba shi wani turare mai kamshi.ya fito mahmud ya kai shi tasha.bai samu motar abuja kai tsaye ba,don haka sai ya hau ta kaduna. suka miki hanya,zuciyarsa da rauni,bai san lokacin da zai warke ba. hajiyar mardiyya,matar alhaji lsa mani,abokin alhaji bishir ita ce ke kwada sallama a falon hajiya sauda.hasina ce ta fito daga dakinsu ta ce,sannu da zuwa maman su nabila.ta ce,yawwa hasina,hajiya fa?ta ce,bari in duba ta.nan hajiyar mardiyya ta zauna kan kajera.hasina ta fito ta ce, tana wanka ne.hajiya mardiyya ta mike,bari in shiga cikin dakin.kawaye ne sosai,har yanzu ba su yada juna ba,don sun fi mazan nasu zumunci,har da matar alhaji kabiru,hajiya ramatu, abokansa na tun ana talakawa. kan gado ta zauna tana 'yan dube-dube. ke kullum aka zo dakinki kal,sai ka ce amarya.daidai lokacin ta fito tana cewa, me kika ce?hajiya mardiyya ta maimaita.sauda ta yi dariya,to ni ke gyra dakina da kaina.ku ko kun fi son na 'yan aiki.ta ce,to meye aikinsu in ba shara da wanke-wanke ba?sauda ta ce,ku dinga duba masu. kullum ina fada muku,suna yi kuna dubawa,kuma gyara musu. hajiya mardiyya ta ce,ke ni zuwa na yi in ji dalili ko kuma laifin da nai miki baki fada min biki ba,sai dai in ji a gurin alhaji.hajiya sauda ta yi tsaki,kin san allah,ban san komai a kan bikin nan ba.ke in takaice miki,yanzu alhaji fushi yake yi da ni.hajiya mardiyya ta ce,a kan me?ta ce,kin san bata son auren,shi ke so.ya kira ni wai in tursasa mata ta yi abin da yake so.sai na nuna masa cewa ba ruwana, yanzu ne aka san da ni?to ni shawara zan ba ta,tursasawa ba.kar ki dada,kar ki raga.daga wannan shine laifina.wai ni ce ke zuga ta.har yau bai sake ce min kala a kan bikin ba.na'ima take fada wa su hasana ta waya wai nafisa ta je dubai siyan kaya.an kawo lefe,an yi kaza,an yi kaza.
[01/10 9:45 pm] Abdul: (10)Hajiyar mardiyya ta ce, amma alhaji bai kyauta ba. ko da keke zuga ta.ai kamata yayi ya baki hakkinki na haihuwa.sauda ta ce,ni ma dai shi na gani. don haka nasa musu ido.ya maki zuwa garin nan sam. ko kira waya yayi.sai ya yi ta wani dake-dake yana magana a cije. hajiya mardiyya ta ce, amma da kin yi masa magana da kanki,ki yi masa bayanin nufinki don ki amshi ragamar auren 'yarki. sauda ta ce,kin san allah ba zan kula auren nan ba.kuma ba zan taba yi masa magana a kan wai ya fahimci ban zuga MIMI ba.mu je a na zuga tan.ita ma ba halin kirki gare ta ba.so nake su gane kurensu,dukkansu shi da ita.mardiyya ta ce,shi ke nan,allah ya kai mu.mu dai za muje biki.ln abuja din ne,in nan ne ma dai duk da mu za a yi,allah ya taimaka, in ji hajiya sauda. Ana saura sati daya bikin ne,alhaji bishir ya zo katsina.bai ko sanar da zuwansa ba.barcin rana take yi lokacin da ya iso. yaran suka yi masa sannu da zuwa.kai tsaye ya nufi dakinsa,ya bude ya shiga.ya zuba jakar hannunsa da hularsa zuwa wayarsa a kan kujera. shi kuma ya zauna a bakin gado.hasna ce ta shiga dakin hajiya sauda ta tashe ta,tana sanar mata zuwan dady.ta sha mamaki sosai, domin sai ya sanar kafin ya isa.ta kalli husna,shi ne ya ce ki kira ni?husna ta ce,aa ya shiga dakinsa ne kawai.sauda ta ce,to je ki ina zuwa.har ta mai da kanta ta kwanta,a zuciyarta ta ce tunda da abin da ya zo gidan ke nan ba za ta kula shi ba.amma sai wata zuciyar ta ce, mijinki ne kina kasansa ki je. ta same shi yana cire safar kafarsa.ta yi sallama, ta shiga.daga bakin kofa ta tsaya tana fadin,sannu da zuwa.alhaji a ciki ya amsa da cewa yawwa.ta zauna a hannun kujera,na ji mamaki,ba ka ce min kana zuwa ba,kamar yadda ka saba.ya dago ya dube ta laifi ne?ta lumshe ido,cikin takaici ta ce,aa babu laifi.ta mike tsaye,me kake bukata?ina nufin abin da zaka ci ko sha?ya mike, alhamdulillah ba na bukatar ko daya.ta ce,har wanka?ya dan yi tsaki,kin ga na yi datti ne?ta kautar da kai gefe.
[01/10 10:34 pm] Abdul: (12)Ameen.me kuke bukata a cikin bikin ke da yaranki? ta ce,ba ma bukatar komai bikin da ba a nan za a yi shi ba.mu ma fa yan gayyata ne.ya ce,ba na son kina fadin haka.ba za kuyi ashoben ba?ta ce,aa ba za mu yi ba.ya ce,don me?ta ce,ba za mu samu dinki ba kar ka damu.ya ce,shi ke nan.ya kwana,washegari ya wuce malumfashi.ya koma abuja saura kwana biyar biki.kuma ranar ne aka yi jeren amarya a gidan angonta. lsma'il ya isa abuja yammacin magariba. maigadi da ya soma ganin sa ya sha mamaki.ya ce, malam kai ne ka dawo?ya ce,ni ne daga kiran sallar lsha'i ne,alhaji ya bukaci ganin lsmail a kebe.bayan sun gaisa ne alhaji ke tambayar lsma'il lafiya ya dawo da wuri?lsmil bai boye masa komai ba.ya fada masa abin da aka yi masa,ya ji ya tsanin garin katsina.alhaji ya ce, kar ka damu.allah yasa haka ne mafi alheri a gare ka.lsmail ya ce,amin na gode
[01/10 10:34 pm] Abdul: (11)Ta yi dan huci,ta mike. har ta kai bakin kofa,ta kasa jurewa,ta dawo,alhaji wai laifin me na yi maka da duk ka canza min.ya kalle ta,baki san kin yi laifin ba ko?ta ce,wallahi ban sani ba.ka sanar da ni mana.ba sai in baka hakuri ba.ya ce, ban zaci zan ce ki yi abu ba,amma ki ce min ba za kiyi ba.ni ne na ce kiyi wa MIMI fada kan ta bi zabin da nayi,amma kika ce min ba za kiyi ba,karshe ma sai kika zuga ta ta katse shi,na zuga ta kuma?ln ji ta ne ta ce na zuga ta?shawara na ce zan bata,kuma na bata. ka tambaye ta wace irin shawara na bata?zan yi mamaki sosai in ka ce ka mance halina.a tunanina mun kai matsayin da zaka san abin da zan iya da kuma wanda ba zan iya ba.don ni yanzun zan iya rubuta kundi a kan halayyarka.haka kuma in an fadi wanda ba za ka iya ba,zan ce sam baza ka iya yin haka ba.kansa yana kasa,yayi shiru,domin ya san cewa gaskiya ta fada.can ya dago kai,me kika ce mata?ta mike ta koma kusa da shi.bayan ta dauki wayarsa ta soma latso lambobin ta kai kan lambar MIMI ta dannan kira,ta latsa handsfree sai da ta soma ringing ta mika masa,ina son ka tambaye ta,mu ji.kafin ya ce,aa,har MIMI ta daga,muryarta ta ratso,inda ta ce,hello dad.ya ce,MIMI,in tambaye ki?ta ce, eh dad.ya ce,me mamarki ta fada miki game da auren abbas?ta ce,wace maman,momy nafisa?ya ce, mahaifiyarki.ta tura baki,dad cewa fa tayi wai in hakura in bi abin da kake so,ko don irin kaunar daka nuna min.wai shawara ta bani.ya ce,shi ke nan. yana kashe wayar sauda ta mike.ya kamo hannunta, kar ki yi fushi matata,ki yi hakuri,na fahimce ki.bai-bai ta dan yi jim,ta ce,shi ke nan ya wuce.ya ce,to zauna muyi maganar auren MIMI.ta ce bani da ta cewa game da auren MIMI,face allah ya bada zaman lafiya. yanzu ka hakura zaka ci abincin?ya girgiza kai,aa sai in kin zauna.ta lumshe ido, ta zauna.ya ce,ni ma na yi miki laifi ban fada miki komai ba.yau saura kwana bakwai.kuma za a yi bikin ne a can abuja.sauda ta ce,babu damuwa. allah ya sa a yi lafiya.ya ce ameen.
[01/10 10:34 pm] Abdul: (13)Washe gari saura kwana hudu biki,amarya ta sha gyara jiki,ita da na'ima.duk abin da aka yi mata,an yi wa na'ima.mai gyara ta musammam momy nafisa ta dauko.an zuba musu zanen lalle har ba za ka iya bambance amarya ba.kawayen MIMI su mina suna ta kai koma don ganin shirye-shiryensu sun kayatar.yammacin laraba za su yi family night. na'ima tayi zaton zuwan 'yan katsina,amma shiru. MIMI bata damu ba,don ta san ita ba zama za tayi ba. rashin zuwansu ma zai fi mata.a ranar alhamis kuwa za su yi 'mothers day, wanda momy nafisa ta shirya.kuma a ranar ne MIMI suka shirya guduwa,ita da khalil dinta.amma momy nafisa a nata tsarin sai daren jumaa,in an dawo daga kumbo,an yi kamu ke nan sai ta sa MIMI ta tubure.daga nan sai ta tura na'ima ta ce wa dad din su ita ta yarda a daura da ita. An yi mothers day lafiya an tashi ana ta daukar hotuna,MIMI ta daga wayarta ta kira khalil ta ce su zo,shi da wani abokinsa kamar za ta yi magana da wani ta fita wajen hall din ta nufe su.da mota suke,don haka ta shige.kai tsaye gidan su MIMI suka koma.babu kowa,duk ana gurin biki,amma dad yana nan.da ta dauko jakarta za ta sauko sai ta ji shi yana waya.tana fitowa ta ji ashe a falonsa yake,amma daf da babban falon nasu. sai ta yi sanda ta fice.da gudu ta ja mota suka tafi. Ta dubi khalil,yanzu ina muka nufa?ya ce,kaduna. don in muka ce za mu kwana a abuja,da safe za a kama mu.haka cikin dare nan suk dauko hanyar kaduna,gudu suke yi sosai. ga shi lokacin sanyi.ga MIMI ba ta son sanyi,kuma kayan jikinta irin na amare ne,ba na dumi ba.ta kudundune duk da cewa khalil ya cire t-shirt din sa ya bata ta dora a kan kayan jikinta.shi kuma ya zauna da singileti.zuciyar MIMI ta kasa natsuwa,wani gefen yana fada mata cewa ba ta kyauta ba,za ta yi nadama,ta kunyata mahaifinta.wata zuciyar kuma tana zuga ta da cewa ke ki tafi kina kan daidai.alamarin dai ga shi nan.
[01/10 10:34 pm] Abdul: (15)Amma da yaje daki na musamman suka kama,sam ba ya fitowa ko kofar daki.duk abin da suke so sadau ke zuwa ya sai musu.su kuwa su momy nafisa ba su ankare ba,suna can suna ta hidimar ganin kowa ya samu abinci. a zatonsu tana can suna hotuna da kawayensu sai lokacin da na'ima ta zo tana cewa momy ina sis MIMI?ga abbas sun zo da abokansa.nan fa aka shiga neman amarya,ba ta babu dalilinta.hankula suka tashi. nan dai biki ya kare.momy nafisa kuka wi-wi.nan ta kira alhaji bishir tana fada masa cewa MIMI ta zo gida?ya ce babu wanda ya zo gidan nan.shi ma zuwansa ke nan.daidai lokacin da suke yin wayar da a ce ya waiwayo da zai ga MIMI,tunda gilashi ne ya raba falonsu da nasa. Ta ce masa,to MIMI dai an neme ta an rasa ta,ko kasa ko sama.har zuwa sha biyun dare ana ci gaba da neman ta lungu da sako, banda wayoyi da ake ta yi don ji gurin abokanen arziki. matuka hankalin alhaji ya tashi sosai.alhaji akilu ya kira shi yana jajanta masa. ya ce,amma alhaji bishir da ma yarinyar nan ba ta hakura ba?alhaji bishir ya ce,ta hakura mana.ga shi ana ta biki.sai yau a ce ta gudu?alhaji akilu ya ce,baka ganin ko yaron da suke yin soyayyar ne ya zo ya sace ta?alhaji bishir ya ce, komai zai iya faruwa.amma bari mu gani zuwa da safe.alhaji akilu ya ce,in ko ya tabbata yaron nan sace ta yayi,lallai babu abin da zai hana shi zaman gidan yari.ka ga halin da abbas yake ciki kuwa?ya ce,ko ni ma ba zan kyale iyayansa ba bare shi,tunda daga gani ba da yardarta ya sace ta ba, domin bata bar wani sako ba,ba ta dauki komai na sawarta ba.alhaji akilu ya ce,kun kira lambarta?ya ce tana ta ringing ba ta daga ba.kusan karfe dayan dare alhaji bishir ya kira hajiya sauda tana barci,ta dauka, tana fadin,alhaji lafiya?ya ce ina fa lafiya,an sace MIMI.ta diro daga kan gado.an sace MIMI kuma?ya bata labarin komai hajiya sauda ta ce,ko dai guduwa suka yi tare da saurayin nata?ya ce, bana tunanin haka,ta nuna min ta hakura.kuma sun shirya komai da mijinta, har kudi ta cire a account din ta don gyaran jiki.
[01/10 10:34 pm] Abdul: (14)Dayan dare suka shigo garin kaduna.sadau abokinsa shi ne ya kawo shawarar su shiga cikin wata unguwa su nemi otal,kar su kama na bakin hanya.ta titin kagoro suka shiga,inda suka sami wani otal suka kama.MIMI ta ce su kama mata dakinta daban khalil ya ce,dear za ki iya kwana ke kadai?ta ce,eh mana kar ka damu.ta yae,shi ke nan. daki biyu suka kama a sama.khalil ya kalli sadau bayan sun kwanta,abokina ina kake ganin ya dace mu je?sadau ya ce,gobe ku shiga motar sakkwato ko zamfara.ba za a yi tunanin za ku je can ba.khalil ya ce,ni da lagos na so mu tafi,mu boye kamar na sati daya.sadau ya ce,kai banza ne.wane sati daya.ai in ni kai sai na dinke yarinyar za mu fito. yadda dole za a aura min ita.khalil ya tashi zaune,ban gane ba.sadau ya ce,ina nufin,yayi kwatance da hannunsa da cikinsa.khalil ya ce allah ya sawwake.ba ni da niyyar in cutar da MIMI zan barin mu yi halastaccen aure da ita. sadau ya ce,ka ji matsalarka.a shawarwarin da na baka,wacce ce aka samu matsala?na ce ka sai da gwal din mom dinka,mun sai da na ce ka dauke ta ku gudu.ba ga shi ka yi nasara ba?khalil ya ce,ban dauke ta da niyyar aikata wani abu ba,sai don in fid da ta daga auren wani na.kai dai naka da safe ka kai mu garejin mota mu tafi.kai kuma koma gidanku mun gode. MIMI kuwa ta kasa barci, sai juyi take yi.wayarta tana,silent,amma tana kallon kira.da wani ya yanke,wani zai shigo da farko ta ki dubawa,amma daga baya sai ta duba.kiran dad dinta ne da momy nafisa har da su na'ima. kuka take ta tayi tare da tausayin mahaifinta.ji take kamar ta daga ta ce su zo su dauke ta,kuma ta amince za ta auri wanda suke so.amma sai shaidaniyar zuciyarta ta kangare,ta kuma hana ta aiwatar da hakan.da zazzabi ta farka tare da ciwon kai mai tsanani,don haka sai batun tafiya ya fasu.sun fita suka sayo mata doguwar riga da hijabi ta saka,suka dauke ta zuwa asibitin biba.gado likita ya bata,don tana cikin damuwa.hankalin khalil ya kara tashi, tsoron sa kar wanda ya san shi ya gan shi burinsa su bar kaduna,
[01/10 10:34 pm] Abdul: (16)Ba ta dauki komai ba. hajiya sauda ta ce,allah ya kyauta.amma a zuciyarta tafi yarda cewa MIMI kudi ta diba suka gudu.ta ce to yanzu wane mataki ka dauka?ya ce,mun sanar da yan sanda,gobe za mu je kaduna gidan iyayensa. hajiya sauda ta ce,to ku kuwa hada da addua. bayan sun yi sallama da kansa ya taka gefen masu masu aiki ya kwankwasa kofar dakin lsma'il ya yi sallama ya amsa,don lokacin yana ta juyi cikin damuwar rashin masoyiyarsa zainabu.jin muryar alhaji ya bude kofar cikin fargaba.ya ce.alhaji lafiya?ya ce baka ji abin da yake faruwa bane?lsma'il ya ce,ban ji ba alhaji.a zatosa ma barayi ne suka shigo gidan.alhaji ya ce mu shiga daga ciki.a tsakiyar dakin suka yi cirko-cirko. alhaji ya ce,malam lsmail a gurin shagalin biki aka sace MIMI.aka sace MIMI?lsma'il ya maimaita.alhaji abbas ya ce,na zo gurin ka ne ina son a taya mu da addua kafin gobe in samu malamina saboda ya duba min inda suka boye ta.lsmail ya ce,allah ya kyauta,ya kuma bayyana ta sai dai alhaji baka tunanin ko sun gudu ne? alhji ya ce,bana tsammani, tunda bata bar wata alama da za ta nuna hakan ba.ba ta dauki kaya ba.lsmail ya ce haka ne.shi ke nan insha allah zan taya da addua. ikon allah a gabana suka hau mota alhaji da zasu tafi. to ni dama muna yin isha'i,na yi shafa'i nake shiga in kwanta da wuri saboda ina tashi cikin dare. alhaji ya ce,to bari mu je mu yi sauraro.lsma'il ya ce allah ya jishe mu alheri. bayan fitar alhaji,lsmail yayi ta mamakin MIMI.tabbas sun gudu ne,tunda ta fada masa cewa sun samu mafita,ya kira

1 Comments On CANJIN RAYUWA
avatar
mariya-6-8

11 months ago

Reply

In HAUSA language

Please Login or Register in order to submit comment