Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

uku,yayi magana cikin dakewar murya,waye a nan?ta ce,ni ce.ya ce,ke ce wa?ta ce,na'ima.ya ja dogon tsaki,don allah bar nan gurin.waye ya neme ki da za ki zo ki ta da ni daga barci?ta yi tsuru cikin fargaba.ta ce,yi hakuri,ina jin tsoron dakin ne.ya ce,ina ruwana da tsoronki.da ma abin da kike sone kara taba min kofa.dole ta juya,ta sauka ta koma dakin cikin firgici ta kulle,ta sake kiran wayar momy a kashe.sai ta hakura ta kwanta. Zainabu tana kasa inda kicin dinsu yake, tana ta kici-kicin dora katuwar tukunyar da suke dafa abinci.mudu takwas suke dafawa in shinkafa ce suna yin tazarce ne daga rana har dare.ln tuwo ne,
[7/27, 11:11] A~PROF: (39)Suna tuke mudu hudu ko hudu da rabi.tana hada ice,alhajin ya shigo.sallamar sa kawai ta ji,gabanta ya fadi take ta soma kuka,don ta san abin da ya maido shi gida,ci gaba ta yi da aikint uwargida wadda suke ce mata maman bishira ta ce,zainabu ki je mana ga alhaji can ya dawo.ta kalle ta cikin raunanniyar murya ta ce,wallahi na gaji.lnnar su bishira don allah ki bashi hakuri.ta katse zancen, sakamakon kira da ya kwala mata.ke zainabu,ni saanki ne,kina kallo na shigo kin tsaya?mama bishira ta ce,je ki zan sa miki hannu.laure da ke wanki wadda ita ce ta biyu ta ce,kwadayi mabudin wahala.zainabu ta shiga dakin tana ja baya,tana fadin sannu da zuwa.ya ce,rike sannunki,ba na so.sai da na kira ki,za ki zo?ta ce, ina sanwa ne,da ma zan zo.ya ce,to mu je!ai kin san abin da ya kawo ni ko?ba ta da zabi face mika wuya. shi sam bai san wani wasanni ba.auka wa iyalinsa kurum yake yi.ln ya cimma burinsa sai ya kakkabe jikinsa ya tashi. Rayuwar zainabu a gidan alhaji lawal,abin tausayi ne.ga girka babbar tukunya,abin da bata saba ba,ga fama da wannan miji,uwa uba ga su laure. suke dame ta da nuna kishinsu a kanta.don haka in ba girkinta ba ne, ba ta saukowa,sai in su laure ba sa nan.wani lokacin kuma in yarasu sun shiga dakinta su yi ta wasa ta biye musu. amma duk wanda ya san ta kallo daya zai yi mata ya san cewa ta rame.ta yi baki,kyawunta da cikar budurcin da ta soma,duk komai yayi lakwasa. cikin haka ne wata rana kannanta suka zo.ganin ta suka yi cikin yanayin suka je suka sanar da lnnarsu. washgari sai ga ta salati ta zabga tare da fadin na shiga uku ni.yasu zainabu kin yi ciwo ne?ta ce,aa ta soma kuka,wallahi innarmu na gaji da zaman gidan nan.mutumin nan bashi da imani,don allah ki tafi da ni.kullum sai ya zazzage ni.ga matansa biyu kullum sai su yi ta min habai ci tun ban gane da ni suke yi ba, har na gane.lnna ta ce,duk wadda ta yi miki ki rama ai zamansa suke yi,ke ma haka.to ki fada masa mana. sallamar maman bishira ce,ta katse su.ta shigo suka gaisa
[01/10 10:34 pm] Abdul: (40)Zainabu ta ce,lnna wannan ce uwargidansa,ita dai tana taimaka min sosai. lnna ta ce,na gode baiwar allah,amma su sauran ta ce,suna yi mata habaici.na ce to ba zan lamunci wannan ba.sai in zo in same su har nan don ba ni da hakuri.maman bishira ta ce,ita zainabu yarinta ke damun ta.lnda tana da wayo,za ta ke masa faran-faran,ta daina jin tsoronsa. to da su kansu ba za su soma yi mata haka ba.tsoro za suji kar ta fada masa.kafin wani lokaci za ta dan samu abin da ta samu.amma ita sai raki da tsoro.nan suka yi ta shirya mata yadda wai a ta yi masa.jinsu kawai take yi, ba ta jin za ta iya kallon alhaji da wata kauna ko birgewa.lta dai kullum zuciyarta tana gurin dan kyakkyawan farin saurayinta lsma'il. Ismail shi da hamisu direba suna jin MIMI duk wayar da take yi,don tana yin maganarta kai tsaye ne,ba tare da wani noke-noke ba.a nata ganin wannan malam lsmail din shi ne wa har da za ta ji shakkar sa.ya san dai ita ba saar aurensa ba ce.ln ma ya ce zai kalle ta a matsayin mata zai bata wa kansa lokaci ne.shi kuwa lokacin fargaba ne ya sake dabaibaye zuciyarsa.tabbas shi rin guduwa take yi,ba ta zo zama ba.tambayar da yake yi wa kansa,yaya ke nan?yaya zai yi,ta nina zai bullo wa lamarin?a filin ya ce,allah da kai na dogara. ya ciro waya ya sake neman mahmud.bayan a dauka ya amsa sallamar, sai ya soma zolayar sa,ango,ango!ya ce don allah ka bar fada min kalmar.da ma zan sanar da kai ne cewa muna hanya. yanzu haka mun kusa kaduna.za dai mu iso dare yayi ne.don allah ina son ka dan tsaya a dakina,mu same ka a nan.ya ce ba damuwa.sai ma in dan share kafin ku iso.cikin zolaya mahmud yayi zancan.tsaki isma'il ya ja,ya canza harshe zuwa larabci, inda yake fada wa mahmud cewa MIMI din nan aka bashi fa tare da sanar da shi halin damuwar da yake ciki da duk yadda abin ya faru a takaice.sai dai bai ja sunan MIMIN ba.ya yi masa misali ne yadda zai gane.bayan sun yi sallama ne hamisu ya ce,ka san allah malam in kana larabanci kyau kake kara yi mi kamar.
[01/10 10:34 pm] Abdul: (41)Balaraben da ma amma ku fulani ne ko?yayi murmushi tare da fadin ta wurin uwa ba.da yake lsama'il saurayi ne kyakkyawa sosai,sak ya debo mahaifiyarsu wadda ta kasance fulanin daura.ga shi da tsafta sosai,ga ilimin addini.na zamanin ma yana kan nema,don duk biyun yake da burin ya hada.yana da tsare gida sosai.amma akwai farin jinin jamaa.duk inda ya shiga mutane suna son sa.kodayake halayyar shi ta janyo don yana da son jamaa da son yi wa jamaa nasiha.ba ya ganin kuskure yayi shiru.ko ina ya shiga da wuya ya bar gurin bai samu wanda ya amshi lambarsa ba ya ce za mu dinga gaisuwa.tare da haka sam ba ya son raini ko cin mutunci ko wulakanci.yam mata da dama suna son sa,musamman dalibai.sai dai ba ya bada fuska, kasancewar ba abin da yake kai shi makaranta ke nan ba.zainabu ya soma so amma ga yadda rayuwa take canzawa,abu ya juye,ya je abuja neman kudin aure,ya dawo da mata.takwas daidai suka shigo kaduna.lsmail ya ce lallai su tsaya su yi salla. hamisu ya rada masa cewa kar mu fita ta gudu. lsmail ya ce,ka rufe motar mana,ka je ka yi.ln ka idar ni ma sai in je in yi.daga nan suka dauki hanyar katsina.jefi-jeri lsmail yana jin MIMI tana tambayar khalil sun kusa kaduna. sha biyu da minti goma suka shiga katsina,lokacin khalil ya kira MIMI wai bai sami motar katsina ba.sai dai ya sauka a kaduna. kuma ya je gida, mahaifinsa ya yi tafiya,don haka kai tsaye ya wuce gurin hajiyarsu don ya san za ta hakura ba,sai ya bata gold dinta.ya ce da safe zai kaita gurin wanda ya saida mawa.da haka ta yi ta yi masa fada da nasiha. ba ta san shi ba abin da ya dawo da shi gida ke nan ba.ya dawo ne don ya dauki mota.ya san ta da barcin safe.don haka sai da ya karya ya fita ya duba lafiyar motar,ya koma dakinta ya ci saar ganin makullin motar tata a kan madubi.ya fita ya dauki motar.maigadi ya ce,ina za ka?ya ce,hajiya ce ta aike ni in sha mata mai.sai bayan ya zo zariya ya tsaya ya sha mai.yayi tambayar ina zai bi in za shi katsina?aka nuna masa wata mota aka ce ya bi ta.
[01/10 10:34 pm] Abdul: (42)Sha biyu da minti goma suka shiga katsina,lokacin khalil ya kira MIMI wai bai sami motar katsina ba.sai dai ya sauka a kaduna. kuma ya je gida,mahaifinsa yayi tafiya,don haka kai tsaye ya wuce gurin hajiyasu don ya san za ta tausaya masa.ya ba ta hakuri,ta ce baza ta hakura ba.sai ya bata gold dinta.ya ce da safe zai kaita gurin wanda ya saida mawa.da haka ta yi ta yi masa fada da nasiha.ba ta san shi ba abin da ya dawo da shi gida ke nan ba.ya dawo ne don ya dauki mota.ya san ta da barcin safe.don haka sai da ya karya ya fita ya duba lafiyar motar,ya koma dakinta ya ci saa ganin makullin motar tata a kan madubi.ya fita ya dauki motar maigadi ya ce,ina za ka?ya ce,hajiya ce ta aike ni in sha mata mai.sai bayan ya zo zariya ya tsaya ya sha mai yayi tambayar ina zai bi in za shi katsina?aka nuna masa wata mota aka ce yabi ta.lokacin ne kuma ya kira MIMI ya fada mata ya taso daga zariya.su kuwa yadda suka yi jiya,suna isa katsina hamisu ya ce,to yanzu kai ne zaka yi ta mana kwatance har gidanku.haka kuwa aka yi. unguwar shiru.kowa ya rufe gidansa,tunda lokacin sha biyu ta wuce,ga kuma yanayin sanyi.lsmail ne ya fita ya je ya turra kofar gidansu,don ya san bata rufuwa da sakata.mahmud ya bude kofar dakin lsmail ya fito.kana ciki ke nan? mahmud ya mika masa hannu tare da fadin gaskiya kun sha hanya. lsmail ya ce,to bari mu kwaso mata kayanta.suka fito.tare da wayarsa yayi amfani ya haska,ya bude murfin gefen da MIMI take zaune ya ce,ki fito.ba ta yi musu ba.ta sauko.sai dai tana saukowa ta toshe hanci,ya haska mata har ta shiga zuren gidan.ya nuna mata dakin.ki shiga nan.a fili ta ce,tafdi!ta shiga tana kallo ko'ina na dakin ta ce,na yarda dad ba ya kauna ta sam.ko tantabaruna dakinsu yafi wannan.lsmail dai ya juya. jiki a sanyaye ya nufi waje.suka soma shigo da kayanta.can ta rakube da bango a kan katifar,tana sake kallon ko'ina a yatsine, hawaye na ta zuba daga idanunta,tana kara karfafa wa kanta cewa lallai gudu shi ne abin da ya halasta ta yi.
[01/10 10:34 pm] Abdul: (43)A wannan gidan,a wannan dakin za ta yi rayuwar aure?suka gama shigo da tulin jakunkunanta da kayan takalmanta,suka loda su a gefe.lsma'il ya ce. mahmud kuje da hamisu ya kwana gurinka.da safe zai dauki hanya.mahmud ya ce,ba damuwa.mahmud ya kalle ta,to amarya,an iso lafiya?da sauri ta dago idanunta ta balla masa harara,tare da jan dogo tsaki,ta ci gaba da latsa wayarta.haka suka fice.lsmail ya raka su mota, suka shiga suka tafi.shi kuma ya dawo ya dauki buta ya fita waje yayi alwala ya shigo ya ra sakata.duk da yana ta addua,gaban sa bai daina faduwa ba.yayi shafa'i,ya daga tsohuwar akwatinsa ya dauko bargo ya kalle ta,ga abin rufa.ta yi masa hararar sama da kasa,ta ce,tunda dai ka ji ban ce maka komai ba.to ka gode wa allah.amma kar ka sake ka kara yi min magana.ka ga na yi kama da tsumman bargonka ne?lsmail ba ya daukar raini sam don haka ya ce,za ki iya ce masa tsumma,amma naki sabon ina yake?kar ki cuci kanki,ki amsa ki rufa don ana sanyi sosai.ta yi masa wata harara irin ta sama da kasa,ta ce,kar ka zata wai an daura maka aure dani, shi ke yake ba da damar in zama matarka.ya ce,na nawa kuma?sai dai in kar a kara,amma aikin gama ya gama.ta ce,ai ba bisa yardata aka yi ba,don haka babu aure.yayi yar dariya,yadda kika ce ba.amma aure daram, musulunci ya kulla shi.kuma nine kadai zan iya warware shi ta hanyar saki.ta ce,to maza ka warware shi.don ni da gari ya waye zan kama gabana.ya ce,da hakan za ta yiwu tun daga abuja zan yi hakan.sai dai kash na riga da na yiwa mahaifiyarki alkawari.ta daga murya,kai ni yanzu ba ni da wata mahaifiya,ban da iyaye,ban da kowa. mahaifiyar da tana zaune aka gama cin zarafina.ban ji haushinta sosai ba,dama can na san ba wai tana so na bane.don haka zan fi son in tafi inda babu wanda zai ji labarina. ya sake mika mata bargon,ki rufa,sanyi yayi yawa.ta ce,ka bar shi in ya so sanyin ya zama ajalina.lsmail ya ce,ni ma dana huta da tunanin nan.
[01/10 10:35 pm] Abdul: (44)Ta kalle shi sannan ta ja dogon tsaki.tabarma ya shimfida.bata bude sosai ba, don dama gurin da ya rage bai fi gurin salla ba.ya dauko wani zanin gado ya shimfida,ya dauki filo daya ya saka.tunaninsa daya,duk tsananin sanyi,shi ba maabocin yin barci da kaya ba ne,sai dai ya rufa.har ya kamanta haka,dole ya tashi ya cire riga,ya kwanta da dogon wando.lta dai tana inda take rakube,iyaka dai kau da kanta tare da tabe baki.sama-sama yake yin barcin saboda ba ya kwanciyar kasa har ya zuwa lokacin da ya saba tashi don yin nafilfili.ya yi mika,ya saka rigarsa ya waiwaya ya kalle ta,ta takure,kanta yana cinyarta, wayar ta fadi can gefe.da alamu sanyi sosai take ji.ya daga akwatinsa ya ciro malumalun dinsa a goge,tana ta kamshin turaren da yake sawa a kayansa,ya lallaba,ya rufa mata.ya fita don yo alwala. ko da ya dawo ta zame ta kwanta,ta kankame filo,ko fuskar ta ba a gani.yayi sallarsa,ya gabatar da adduoinsa ga mahalicci.abin da yafi alheri kawai yake ta roka tsakanin sa da MIMI.ya sake kwanciya yana fuskantar inda take kwance.bai iya ci gaba da barci ba,sai hasashen me zai faru gobe da jibi?lna zai samu kudin da zai ci da ita irin cimar da take ci?lna zai samu kudin irin tufaein take sawa zuwa kayan shafanta wanda a gabansa ta ce dubu dari albashinsa shine kudin kayan safanta.a haka har asubhi tayi.ya kulle dakin ta baya,ya tafi masallaci.a can suka hadu da yan uwansa,wato yayyinsa maza,suka gaisa. suka yi masa murna mahmud ya zo ya fada musu cewa maigidansa ya ba shi yarinya.ya ce haka ne.babba ya ce.amma ai mu ne ya kamata mu zama wakikanka duk lalacewarmu.lsmail ya gano sun dauki zafi ne,don haka ya fada musu yadda abin ya taso amma duk da haka cewa kurum suka yi,allah yasa alheri ba don sun yarda ba.daga nan gidan yaya amina ya wuce.idar da sallarta ke nan yayi sallama,ta amsa,suka gaisa. cikin murna ta ce,sai ga labari mai dadi.ya ce,uhum yaya ke nan.ta ce,mene ne uhum,kun zo da amaryar ne?ya ce,eh,tana dakina.amma matsalar ba ta so na.
[01/10 10:35 pm] Abdul: (45)Ni ma sam bana son ta ko da wasa.nan dai ya fada mata komai.ta ce.to allah dai ya daidaita ku.ka tashi ka je kar ta farka.yanzu to me zaka bata na kari?ya ce,sai dai na je na ji daga bakinta,don ban san da me za ta karya ba.nan suka yi sallama ya nufi gida.kai tsaye cikin gida ya wuce,fatu tana kicin ya ce mata ina kwana?ta dago ta dube shi,aa yan abuja ne?sai muka ji aure.na ce kila dai don mu bamu da zanin zuwa abuja ne.yayi dan murmushi ya wuce.saura suka fito su ma dai ya gaishe su,amma sai sakin magana suke yi.dakin lnna ya shiga tana kwance,ga rushi a gabanta,ya zauna ya gai da ta.ta ce,sai kuma mamuda abokinka ya zo mana da labarin aure.ya ce,eh.abin allah ya kawo shi kafin a yi shiri.ya ce,to allah ya ba da zaman lafiya.mu da har muna cewa kila ka canza dangi ne.ya ce ba haka ba ne.ni ma abin ya zo min ne ba shiri.tana ciki ai tana barci.ta ce,to kuma a nan dakin za ku zauna?ya ce,eh,to sai dai yau zuwa gobe za mu fara neman daki.ya mike,bari in gani ko ta farka. ya sa makulli ya bude dakin.har lokacin bata tashi ba.ya kira mahmud yana tambayar sa ko hamisu ya tashi?ya ce tunda suka yi salla ya koma.ya bar shine ya dan warware gajiya tunda hanya zai kara bi. sai karfe goma da kwata,lokacin tuni lsamail yayi wanka,yayi shirinsa cikin shada mai ruwa siminti.yayi kyau yana ta kamshi.ta farka,mika tayi ta yi tsaki.ya ce,ai kamata yayi ki yi adduar tashi daga barci,ba tsaki ba.yanzu da kin bude ido kin gan ki a kabari fa?ta tashi zaune,da sai na fi murna fiye da in gan ni a dakin nan.da sauri ta shiga neman wayarta.ta dauka ta soma kiran layin khalil,ya katse.ya kira ta, lokacin ne yake fada mata ya taso daga zariya.ta ce, shi ke nan zamu yi ta waya har ka iso.ya ce,shi ke nan,sai na iso din. lsmail ya ce,wai da wa kike ta yin waya ne?ta harare shi,na ce ka daina yin min magana ko?ya ce,to ki tashi ki yi salla.ta harare shi,ta ja tsaki,ba zan yi ba.ya ce kina fashin salla ne?ta mike tsaye cikin mamakin wuce gona da irin.
[01/10 10:35 pm] Abdul: (46)Na mutum,ta ce,cikin daga murya,zo ka matse ni ka duba ka ji ko?ta zare idanu a karshen maganarta. ya mike,mai da wukar.me za ki ci?ta sake hararar sa,kai har ka mallaki abin da za ka iya ciyar da ni?ta sauka daga kan katifar ta nufi jakarta wadda ta sa jakarta mai kudi a ciki.ta ciro ta zo zata zauna,sai ta ga malum-malum dinsa,ta sa kafa ta ture.ya ce,oho dai ta yi miki amfani. ba ta kula shi ba ta kwance kudin sadakin da aka bata a gefen gyalenta,ta zuba a cikin jakar,ta dauko karamin akwaiti cikin jerin akwatunanta,ta bude akwatunan tana zabar kayan da za ta sa.yawanci kananan kaya ta diba.ta bude wata jakar ta dauki kayan ciki da na shafa,sai takalmi daya ta saka jakarta mai kudi,ta rufe.ta sauka daga kan katifar.ya ce,wai ke ko fitsari ba ki ji ne,duk sanyin nan da ake yi?ta ja tsaki,ban ga gurin da zan iya tsugunawa ba.ya ce,mu shiga cikin gidan.daga nan sai ki gai da lnnata.tunda ya ambaci fitsari,sai ta ji ya matse ta har kamar zai zuba.shiru ta yi,sai ya dauko buta,mu je in raka ki.ta dauki mayafinta ta dan yafa.suka fito zaure a share fes.don tun kafin ya shiga wanka ya share.suna shiga tsakar gida,matan gidan suna ta aikace-aikacensu.ta sa gefen mayafinta ta rufe hancinta.ya ce,ki gai da su mana.ta zabga masa harara,ta ce,nuna min toilet ni kam.ya nuna mata,ta shiga da kyar ta yi yin fitsari saboda zarni da kuma rashi inda zata tsugunna.ba ta taba ganin irin wannan ban dakin ba,don ko na kauyen su dad da ta tsani shiga yafi wannan kyau.ta fito duk ta bata kafafunta.sai da ta fito ne take ta wanke kafarta,tana zubar da miyau.cikin sauri ta bar tsakar gidan.sai da ta je soro ta sauke numfashi ta soma kuka.matan gida suka yi ta kallon kallo.fatu ta ce,salo da yayi,wai kaza ta ji shikar dare.lsmail ya ce,ku yi hakuri ba laifinta ba ne,ba ta saba da ganin haka ba.suka sa dariya,gami da shewa,to a kai ta inda ta saba,ln ji fatu. shi dai fita yayi ya bar su suna ta habaici da kananan zagi.
[01/10 10:35 pm] Abdul: (47)Ta shiga cikindakin ta dauki wayarta ta soma kiran khalil.ya ce,mun kusa ki ba ni minti talatin.gudu nake yi sosai,kin ji dear ta ce,to inda nake ne ko dakin karen gidanmu ya fi shi.ran lsmail a bace,ya ce karya kike yi.lna sake fada miki karya kike yi.ta ce,dakin karenmu akwai tayils,na fa? ya ce,dakina akwai alkurani da littattafan addini.ke nan dakina yafi naki ma,duk kyawunsa.ta sake bin dakin da kallo,tana tabe baki.ta ce,tsayawa yin musu da kai bata lokaci ne. ta sake mikewa ta zage wani zif din akwati ta ciro muhimman takardunuta,ta zage jakar da za ta tafi da ita ta zuba.ta zauna ta yi tagumi,jifa-jifa tana duba agogo,shi kuma ya kasa ya tsare ya ga inda za ta. Na'ima amarya kuwa an yi barci sama-sama a gidan abbas sai takwas ta farka ta zauna zugum a bakin gado.ta dauki wayarta ta soma kiran layin momy.momy tana dagawa ta ce,na'ima an tashi lafiya?bata jira amsa ba,ta ci gaba da cewa,da dinku jikinsa fa ya tashi kamar yadda na ce miki jiya.yanzun haka mun koma asibiti.ki fada wa maigidanki.na'ima ta ce to kawai don ta san babu damar ta yi korafi a cikin wannan halin.wanka ta shiga,ta yo alwala.ta dan fi MIMI tunda ita takan yi sallah ko da dai ba kullum ba.ta zo ta yi kwallaiya,ta bude wardrobe dinta ta ciro sabuwar jallabiya mai shegen kyau ta saka,ta yafa mayafinta irin yadda MIMI ke yi,ta fesa turarruka,ta saka lallausan silifas na zaman gida,ta nufi sama abbas.ta jima a tsaye bakin kafar tana tunanin bugawa.can dai ta daure ta murda kofar,sai ta ji ta a kulle.daga ciki ta ji an ce waye?ta dan yi shiru tare da zaro ido.a sanyaye ta ce,ni ce.a lokacin ya riga ya zo zai bude kofar ya ga ko wane ne.duk da haka bai fasa ba,sai ya bude.ganin ta sai ya bar kofar a bude.ta shiga da alama wanka ya fito don ga rigar wankan a jikinsa. a hannunsa akwai karamin tawul,yana goge kansa.ta tsuguna har kasa,ina kwana?ya bata rai ya kau da kai lafiya.ta ce,da ma momu ce ta yi min waya wai dad dina ba shi da lafiya.an mai da shi asibiti.
[01/10 10:35 pm] Abdul: (48)Ya waiwayo ya kalle ta,irin kallon kashi din nan,to me zan yi masa?ln za ki je.ga ki ga hanya,amma ni bani da lokaci.kin gane?ta mike a sanyaye.har ta kai bakin kofa sai kuma ta waiwayowa,am na ce me zan dafa?ya sake waiwayowa,bana bukata. ranta ya dan sosu.ta mike ta nufi dakinta tana kuka. Bakin gado ta zauna, lallai za ta shiga matsala babba.da ma abbas bai amshe ta ba?shi ne ya amince ya aure ta don kawai yayi mata wulakanci?haka ta yi ta kuka.ko kayarwa bata yi ba har kusan karfe biyu,sai ga kannen momy,su anty rukayya.suka ce lafiya ke kuma kike kuka?anty jamila ta ce,wawiya mana,yanzu an daina wannan abin dan.kin yi daren farko a gidan miji,kiyi ta wani kuka.ta ce,ba haka bane.ta fada musu komai ta ce,ya san bai yarda ba tun farko ba sai ya ce,aa ba.sai yanzu ne zai fara yi min wulakanci?anty rukayya ta ce,ke dai sakarya ce.don wannan za ki yi kuka.ki saurare mu kiji.tunda daga ke sai shi a gidan,abu ne mai sauki ki ja raayinsa.anty jamila ta ce,ina kananan kayan nan da momy dinku ta siyo miki daga dubai?ta ce,suna cikin akwatunan da kuka zo da su.ta nuno shi,ga su can. suka je suka bude.suka ce yawwa ki gwada mu gani.ta yi ta gwadawa suna tafa mata,tare da koya mata kalolin sanya su yadda za ta ja raayinsa.ba su bar gidan ba sai da suka tabbatar da haddace duk abin da suka koya mata.ba su jima da fita ba,sai ga dangin abbas da masu aiki an kawo mata.da dattijiya da mana yarinyar dai yarinyar gwari ce,sannan ta kuko namiji.karfe tara na dare na'ima ta yi wanka sosai,ta yi gayu kamar yadda suka ce maties din ta suka ce.ta saka rigar da suka zuba mata wadda ita ce ta dace da ita a wannan dace.hannu din rigar gare ta.shi ma kulle shi aka yi kirjinta a waje.tsawo rigar bai kai guiwa ba.ta kama gashinta a tsakiyar kanta,ta yi wanka da turarurruka masu daukar hankali.ta soma rihasal din yadda za ta shiga dakin da yadda za ta tunkare shi da duk abin da suka ce ta yi.sai da ta tabbatar zata iya ta nufi saman abbas, duk da tana fargabar kar ya gwasale ta.
[01/10 10:35 pm] Abdul: (49)Ita kuwa MIMI kamar karfe shabiyu sai ga kiran khalil.ta daga ya ce,kina ji na?ta ce eh.ya ce,na iso.ta mike ta bude jaka lsmail suna tsane da mahmud a kofar gida suna tattaunawa a kan inda zai nemi dakin yanzun nan hamisu direba ya wuce bayan ya kawo mahmud sun yi sallama ya lsmail ya ce masa godiya,mahmud yana cewa,mu je mu samu malam.mahaifina kayi mai bayani,lna zaton akwai daki a gidansa na kofar guga amma can bayan gari ne,ba mutane sosai a gurin.gidan dai mutane biyu ne,amma daki uku ne ciki da falo.lsmail ya ce,to da ma ina da kudin nan.mahmud ya ce,ka san ma ba zai amshi kudinka ba.

1 Comments On CANJIN RAYUWA
avatar
mariya-6-8

11 months ago

Reply

In HAUSA language

Please Login or Register in order to submit comment