Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yayyanta kenan.domin kirikiri zata yi laifin da ya kamata a zane ta,amma sai a ce ko kallon banza ba zaayi mata ba.da aka tashi sanya ta a makaranta,sai aka sanya ta a wadda tafi ta kowane yaro tsada a gidan,makarantar da duk wani mai ji da kansa a katsina nan yake kai 'ya'yansa.sai wani babban abin takaici a gurin hajiya sauda yadda kirkir MIMI ta ki lslamiyya. Da ta dage sai an sa MIMI,hakan ya hakura aka sa ta,in ta je bata komai sai kuka da birgima,rannan wani malami ya dan dake ta,saboda ta ki yin shiru kuma ta ki zama ta kage a tsaye,ai ko ya gane kurensa,domin 'yan sanda alhaji bashir ya kirawo wa malamin.lokacin da MIMI ta sanar da shi cewa malaminsu ya duke ta,'yan sanda suka rufe shi,ya ce a rama wa 'yarsa dukan da yayi mata,domin shine mutum na farko daya soma dukn ta.hajiya sauda ta yi bakin ciki matuka,haka nan ita ce taje ta yi belin malamin tare daba shi hakuri.tun daga lokacin ta kawo idanu ta zuba wa mijinta da 'yarsa,ya ce ta daina zuwa lslamiyya,wai sauda ta dinga koya mata a gida,ai ita da ilimi. sauda ta ce,ai ba zai yiwu ba,a ce baza tayi lslamiyya ba,yaushe za ta san kanta bare addinita.sai ya ce,ai ita mace ce,in ta iya na sallah tunda ba waazi za tayi ba,ba limanci zata yi ba ya ishe ta.sauda ta ce,ai kuwa a dai rayu cikin jahilci.
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (50)Tun daga lokacin MIMI bata kara lslamiyya ba, hajiya sauda sai ta dauki matakin tsare ta da bulala tana koya mata,in ta kiya sai ta zane ta.a kan haka suka yi rikici,wai bata son MIMI,shi ko sai ya dauki matakin tafiya da ita duk inda za shi.ta zama tamkar jaka,shi ke kai ta boko ya kuma dauko ta,ko da yana ofishinsa ne,lokacin tashi yayi zai bar komai ya je ya dauko ta.ta na gurinsa,sai zai bar ofis sannan sun koma gida tare.ln ko za shi wata kasa ko wata jihar,to fa zai kashe mata makaranta,tan gefen damansa. hajiya binta tana matukar bakin cikin abinda MIMI ke yi,tamkar ta kashe yarinyar ta ke ji.cikin haka sauda ta haifi 'yan biyu duk mata,hasana da husaina,ta yi murna sosai,tana zaton tunda ga wasu yara mata 'yan biyu ma abin shaawa,to lallai mijin na ta zai rage son MIMI,za su ture mata gwamnati ko ta samu ta yi mata tarbiyyar da ta dace,amma me?sai yana cewa,MIMI fa dabam take,da duk wasu 'ya'ya da ya haifa baya da kuma wanda zai haifa nan gaba. haka hajiya sauda ta kawo ido ta zuba masu, wai sai data kai MIMI ba ta maimaita kayan sawa,sai in ta yi raayi,ci-banza-ci-wofi shine abincinta.amma ba wai abincin kirki ba,wanda aka dafa ba,haka hajiya sauda ta yi ta haihuwarta a kai-a-kai,ta yi abdullahi sai ameen,sannan umar da sadik,a jere ta yi ta haihuwarsu,amma har lokacin MIMI ita ce ta gaba goshi.lokacin da hajiya sauda ta samu cikin husna, lokacin ne ita ma hajiya binta ta samu nata rabon. sauda tayi mata murna sosai ita mata yi farin ciki matuka.kasan cewar wannan ne farko da zata ga kwanta aduniya,lokacin data haihu an samu mace aka sa mata zainab,kishin MIMI yasa suke yawan rigima da mijin,ita wai dole sai yaji da 'yarta kamar yadda ya keji da MIMI. A wannan lokacin ne ya gina wani katafaren gidan gona a malumfashi,kuma ya gina wani gida a cikin garin malumfashi don haka sai sauda ta bashi shawarar ya maida daya daga cikinsu can tsakanin ita da hajiya binta,don ita kan bata son rigima ta gaji da takalarta fada da binta ke yi kan,
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (51)MIM.ya yarda kuma ya dauki hajiya binta ya maida ta malumfashi, bayan husna,sai cikin hasina shima bata yaye husna bata same shi.wani sabon al'amari,wata jumaa sauda tana daki kwance guraren shadaya na rana,sai jummai mai yi mata aiki ta yi sallama ta ce, hajiya kin yi bakuwa.ta fito taga mace wayayya kuma gogaggiyar 'yar boko,daga ganinta kuma 'yar masu hali ce,ko kuma mijinta mai hali ne.sauda ta ba ta mazauni, ta sa aka kawo masu abin sha.suka gaisa,sauda ta ce, sai dai bangane ki ba fa? bakuwar ta ce,suna na nafisa kuma daga abuja na zo nan,na san cewa ba ki sanni ba.amma ni sai ta dan yi shiru,sauda dai ta ji gabanta yana ta faduwa. cikin zakuwa,ta ce,ina jinki?bakuwar ta ce,za kiyi mamaki idan na ce miki ni matar mijinki ce?gaban sauda ya fadi cikin daga murya ta ce,me ki ka ce? bakuwa ta ce,ni matar alhaji bashir ce maigidan nan.jikin sauda ya soma bari ta ce,karya ki ke yi, mijina ba zai yi aure ba tare dana sani ba wallahi. Nafisa ta daga mata hannu tare da cewa kar ki rantse,domin mun yi aure da shi shekaru bakwai kenan.ta nuna babba daga cikin yaranta ita ce na'ima kuma ita ce 'yarmu ta fari.sai wannan sunan ta suhaila,sai kuma wannan karamin ahmad.na'ima sa'ar abdullahi ce danki,kuma inda MIMI 'yarki tana nan zata shaida miki,domin ita kadai kawai ta sanni,ta san yara na a duk lokacin da alhaji ya je abuja MIMI tana zama a hannu na ne. Na dade ina son ya kawo ni in ganku iyalinshi,ku sanni amma yaki sai ya ce, zai kawo ni,sannan wai baya son ki tada hankalinki, ni kuma naga cewa akwai mutuwa.shi yasa tunda ya sanar dani zai tafi china ni kuma na dauri aniyar zuwa mu gana daku saboda halin rayuwa.hajiya sauda jinta kawai take yi tamkar a cikin mafarki.sai da ta lallashi zuciyarta sannan ta ce,shikenan ba komi.ku jira shi a nan in ya dawo sai ku tafi,nafisa ta ce,ni ma haka ne kudurina,ina son a nuna muga dangi,sauda ta ce, babu damuwa.kwanan su biyu,ALLAH yayi wa mahaifin alhaji bashir rasuwa a masari,
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (54)Kwana su biyu, ALLAH yayi wa mahaifin alhaji bashir rasuwa a masari,da ma bashi da lafiya har misira an fita da shi,amma da yake jikin tsufa sai a hankali.nan suka tattara suka nufi masari, shima dole ya bar komai ya nufo gida,shi da 'yar lelensa MIMI,bayan an natsu hajiya sauda ta gabatar da nafisa ga dangin mijin na su.nan suka yita surutu bai kyauta ba,bai kyauta ba, wasu kuma suce giyar kudi ce.lta kam sauda cewa ta yi,ni haushi na daya,mene ne na kin fada mani,wa zai hana shi aure?kuma da ya ki kawo ta,inda ta ALLAH ta kasance a kanshi ta zo da yara ta ce ita matarsa ce za a yarda cikin sauki? lta kuwa hajiya binta zagewa tayi tana ta tsula rashin mutumci duk da cewa gidan mutuwa ne, karara ta nu na kishinta. Shima duk da yana cikin ciwon mutuwa,ya girgiza da samu nafisa a gidan, sam bai so ba.dole ya hakura ya jure masifar da hajiya binta ta dinga yi masa son ranta,ta fada ma shi maganganu.lta kuma sauda bata ce komai ba,sai rashin yin maganarta yafi daga mashi hankali fiye da masifar da hajiya binta ta keyi.sai da aka yi bakwai sannan kowa ya watse suka koma gidajensu. Daga nan yasa aka maida nafisa abuja,shi ma ya nufi katsina. Har cikin daki ya samu sauda tana shirya yaranta zasu tafi lslamiyya,sai da suka tafi sannan ya zauna kusa da ita ya ce,sauda na san nayi miki laifi,don ALLAH ina son ki yafe min, dama kullum cikin tunanin zuwa wannan ranar nake yi.ta kalle shi laifin me?ya kasa bata amsa,ta tabe baki baka yi min laifin komai ba.ya ce,ai nina san nayi laifi,ki fahimce ni,sam banyi da nufi ba. Tunanin halin da zaki shiga ne ya hana nina fada miki,saboda naga yadda muka yita samun matsala a lokacin auren hajiya binta,ni kuma bana son bacin ranki sam.ta ce,umm!ni yanzu lamuranka babu ruwa na da su,ya ce,don me kika ce haka?ta ce,na zata ni da kai duk daya ne,ko mutuwa zanyi don kishi ai ka fada min in ya so in mutu.kuma bayan kayi ma,ai sai ka fada min.ya ce,to nayi kuskure,
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (55)Ai lokacin auren ne yazo babu shiri don ALLAH bari in fada miki yadda abin ya faru. Lokacin ina son sayan wasu filaye a cikin garin abuja,saboda ina son fara harkan gine-gine ina saidawa,to mahaifinta shine shugaba a maaikatar filaye, da safiyo,ni da lauya na muka je gidansa don ganawa ta musamman kamar yadda ya bukata, shine na ganta,amma har ga ALLAH ba sonta nake yi ba.don in samu saukin wannan harkan shi yasa na nuna ina sonta,kuma alhamdulillahi sai ya bani ita. su alhaji lsa mani ne suka amsar min aurenta, ban zaci zamu dade a cikin auren ba,domin nayi ne na wani lokaci,amma sai mutuncin mahaifinta,da yanda ya sakar min nake samun alherin filaye,shi yasa na hakura.abinda yasa ta kara shiga raina shine yadda take son MIMI sosai har ma wani lokaci ina cewa a ce ita ce mahaifiyar MIMI,domin bata takura mata.hajiya sauda ta ce,wato ita MIMI har da ita a munafunta ta,yayi mata kyau.ya ce,kar ki ga laifin ta,ta ce,kaima ba cewa nayi kayi laifi ba cewa,na yi don me ka boye min?ai aure ba laifi bane,na isa in hana ka yi? ya ce,ba zan kara ba,ta ce, nan gaba in zaka cike ta hudu na roke ka,ka sanar damu.ya ce,ai na gama sauda.ta ce,uhum,haka dai ka ce,ni yanzu na daina yarda da kai.ya shiga lallashinta da fada mata maganganu,tsakanin mata da miji sai ALLAH,nan dai suka sasanta tamkar basu taba samun matsala ba,har ranta tabar abin a kaddara. Tun da ya samu sauda da sauran danginsa suka san da nafisa,sai yaga bashi da matsala,tuni yake son ajiye MIMI a gurin nafisa amma babu hali saboda ina zai ce ya kaita? amma yanzu ga dama ta samu,tuni ya tattara ta ya maida ta,MIMI mata yi murna da hakan,don ta san momy nafisa na sonta. lokacin da za su tafi kalma daya ta fada mishi,alhaji tunda kana ganin zaman MIMI a can yafi guri na,to babu matsala,amma ina son kasan cewa,duk iyayen da basu sa dansu kuka ba, to wata rana sai dan ya sasu kuka ya ce,wannan kuma irin naki tunanin kenan,ni dai zan maida 'yata inda za ta samu 'yanci ta kuma huta.
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (56)Lallai MIMI 'yargatace,domin a dankararren gidan da ya gina a abuja maitama,an tsara gidan sama ne hawa daya,amma saman na MIMI ne kowa yana kasa,dakin baccin ta komai pink don shine kalar data fiso.dayan dakin kayan karatun ta ne a ciki,shi kuma dayan an gyara shi an rufe.lokacin shekaranta goma kacal, momy nafisa tana yin iya yinta don ganin ta danne zuciyarta ta kauda kanta ga abinda alhaji ke yi ma MIMI,ba don komai ba,sai don ta samu shiga da kuma abin duniya da yake sakar mata.amma a badini bata son MIMI,bata kamar tana sonta,kullum burinta yanda zata shiga tsakanin su,don ko makaranta da zai sata wanda 'ya'yan jiga-jiga abuja ke zuwa yasata wata rana za shi katsina shi da MIMI ya ce bari su fara zuwa malumfashi don ya gasu hajiya binta,ya kuma ga gonarsa su wuce, tunda binta ta ganshi da MIMI ta hade rai,lokacin wayoyin hannu basu yi yawa ba,sai ta ga MIMI da dankareriyar waya mafi tsada a wannan lokacin.sai binta ta bata rai ta shiga jero zantuka marasa dadin ji,tana fadin ma alhaji cewa ya cika son kai,ba shi da hakki ya bambanta MIMI da 'ya'yansa nan fa ranshi ya baci an tabo rabin zuciyarsa ya ce,duk abin da zata yi,ta yi mishi don shine ya auro ta,amma ta cire sunan MIMI a bakinta, nan fa suka yi kaca-kaca abin har ya kai su da yi mata saki daya,ya tattara yaranta guda uku suka wuce katsina. Ran sauda ya baci matuka,ta duddungure MIMI a gabansa,ya dai daure fuska amma bai yi magana ba,ta matsa mishi lallai sai ya dawo da hajiya binta,ta ta sashi gaba suka je biko, bayan binta ta dawo ne ta zo kwasar 'ya'yanta amma sai zainab taki binta,saboda suna yin wasa dasu husna,ta yi-ta yi,yarinyar ta ki dole ta hakura ta barta. bayan husna hajiya sauda ta sake haihuwar hasina wadda ta zame mata auta, don ta sha wahala a haihuwar tamkar bazata tashi ba,sai da aka yi maka aiki,alhaji ya firgita sosai don haka ya ce da likita ayi masa taimako a tsaida haihuwar.hajiya binta ta kara biyu najaatu da fadila su biyar kenan.
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (57)Momy nafisa ita ma ta kara biyu mas'ud da aisha.bayan MIMI ta kammala secondary ta ce da alhaji bishir mahaifinta, daddy ni fa nafi son in fita waje america ko england ko spain.ya ce ba matsala ta zabi duk wadda take so, ya sayi hannun jari da sunanta,banda kamfanin da ya bude duk wata ribar tana shiga asusunta,sai da ya gama komai sannan ya samu sauda da batun har yana kara fada mata cewa zata fita karatu waje,hajiya sauda ta ce duk bata yarda ba,sun yi rigima sosai dole ta kyale shi. Shi kuma jin ta kushe kasashen turawa,sai ya ba MIMI shawara ya ce ta tafi dubai,tunda can garin larabawa ne,da kyar MIMI ta yarda ta tafi don yin karatun law,zabin ta shine ta zama lauya,amma in a son mahaifinta ne tayi karatu a kan kasuwanci, don ya dora ta a kan alamuransa.abba ya gama digree dinsa a kan mass com,ya samu aiki a banki,ya na kaduna,kuma ya auri samira wadda suka hadu a a ABU zariya, mahaifinta shine ambasadan najeriya a Egypt.su na da yaro daya, wanda suka sa mishi sunan alhajin suna kiran shi ta karshe,don karatun shi mai tsawo ne,likita ne fannin magunguna.shima abdulkarim shekarar shi ta karshe yake,engineering ya ke karantawa.lta kuma MIMI ta cinye shekarar farko ne ta zo hutu,za ta shiga ta biyu,wannan shine asalin su MIMI. Tunda lsmail ya koma dakinsa yake mamakin MIMI,har me ta dauki kanta da take wani ji da kanta haka?shi kam ba maula yazo ba,don haka baya zaton zai kaskantar da kanshi,ya kira layin mahmud suka gaisa,mahmud yana tsokanarsa,da cewa mutanan abuja garin daula,lsmail ya ce,gaskiya duk da ban fita cikin garin ba a gidan da nike kadai na tabbatar cewa akwai daula.mahmood ya ce,ai mutumin nan ya shahara,to yaya kuka yi da yarinyar nan?lsmail ya ce,kai dai bari,nan ya sanar da shi duk yanda suka yi,mahmud ya ce kar ka ce zaka yi zuciya,ka natsu ka danne zuciyar ka in ta shiryu zaka samu lada.sannan ga mahaifiyar ta, ko don ita ya kamata ka jure.lsmail ya ce shikenan, amma fa sai dai mu zuba.
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (58)Tunda lsmail ya koma dakinsa yake mamakin MIMI,har me ta dauki kanta da take wani ji da kanta haka?shi kam ba maula ya zo ba,don haka ba ya zaton zai kaskantar da kanshi,ya kira layin mahmud suka gaisa, mahmud yana tsokanarsa, da cewa mutanan abuja garin daula,lsmail ya ce, gaskiya duk da ban fita cikin garin ba a gidan da nike kadai na tabbatar cewa akwai daula. mahmood ya ce,ai mutumin nan ya shahara to ya ya kuka yi da yarinyar nan? lsmail ya ce,kai dai bari,nan ya sanar da shi duk yanda suka yi,mahmud ya ce kar ka ce zaka yi zuciya,ka natsu ka danne zuciyar ka in ta shiryu zaka samu lada sannan ga mahaifiyar ta,ko don ita ya kamata ka jure. lsmail ya ce shikenan,amma fa sai dai mu zuba. lta kuwa gimbiyar,wato MIMI,sintiri ta dinga yi a falon tana nazarin wannan mutumin wane irin hukuncin ya kamata ta yanke masa?wata zuciyar ta ce, don kin kore shi,ai ba ki rama ba,kin shirya me zaki ce ma hajiya?kar ki manta dai data gargade ki sosai sannan aka turo min ki shi.a fili ta ce,to me zan mi shi in huce?ta kalli wayarta, yawwa bari in kira mina dakingari. Bakin gadonta ta shiga, bedroom ta zauna,mina ta daga tare da fadin khadija masari ya?MIMI ta ce,lafiya dakingari,kin san mene ne? (ta ci gaba)mom di ta ce in fada miki ta dage sai wani malami ya koya min karatun islamiyya.mina ta ce,mene ne laifi?MIMI ta ce, dan rainin wayo ne,kinga yanda yake son nuna min iyaka ta?nan ta kwashe komai ta fada mata,mina ta ce,kin san me zaki yi masa? MIMI ta ce,aa,mina ta ce,in dad din ki ya dawo ki sa a kira shi,sai ki ce kina son a ware lokacin karatun ku minti talatin ko awa daya,yanda dai kika zaba, kinga ba zai taba tashi daga gurin karatun ba sai lokaci ya cika,MIMI ta ce, yawwa kin kawo shawara, kin ga sai in yi masa duk cin mutumcin da naso na tsawon lokacin,kuma dolen shi ya tsaya ya saurare ni, mina ta ce,in kin ga zai wuce gona da iri,ki mari fuskarsa,suka sa dariya ta ce,kin san ba na son taba jikin talakawa,
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (59)Amma zan tsirta mishi yawu,mina ta ce,haka yayi. yaya khalil dinki? oshshh!kin tabo rabin rayuwata,yana lafiya,ya ya faisal dinki?mina ta ce,sun gama hutunsu ya koma jiya, ta ci gaba da cewa,ina mamakin irin son da kike yi wa khalil dinki,kamar ba ki tsane shi ba,MIMI ta ce,kin san me mina?can dama ina son khalil tun lokacin da na soma ganin shi,na ja aji na ne kawai.mina ta ce,don ALLAH da gaske?MIMI ta ce,ALLAH kuwa,mina ta ce,kin iya jan aji kuwa to, shikenan in kunyi waya ki ce,ina gaida shi,MIMI ta ce, zai ji.bayan sun yi sallam ta shiga nazarin mau'du'in wulakancin da ya kamata ta dinga yiwa malami. Tara daidai lokacin cin abincin su na dare kenan,ta sauko da 'yar jar doguwar rigarta da kadan ta wuce gwiwarta,kamar kullum ta yi ado da gashin kanta,kowa ya hau kan teburin,tuni yara sun soma ci ma,sai da ta isa kusa da mahaifinta ta gaida shi, sannan ta dawo gurin zamanta ta kalli momi nafisa,mommy kin dawo?ta ce,ai ban dade ba MIMI,alhajin ya ce,ina kika je?ta ce,gidan hajiya adama na je,in duba masu takalma,ta dawo daga lngila.MIMI ta ce,kin samo mana?ta ce,duk kina da shigen su,ke kuma na san baki son duk wani abin ki ya zama gama gari.amma ta ce,wasu kayan na zuwa. MIMI ta ce,mommy ki bar shi ma kawai.takalma sun min yawa,akwai wadanda har yau ban sa su ba.na'ima ta ce,sis ina wadanda ki ka ce za ki ba ni?MIMI ta ce,ki tuna min da safe,ALLAH ya sa suyi miki,ke da katon kafar nan na ki,duka suka sa dariya. Alhaji ya ce,MIMI ke komai na ki daidai aka yi maki,kuma mai kyau,kalmar ta soki zuciyar momy nafisa ta ce,duk dai dan adam tara yake bai cika goma ba,ya ce,me ki ke nufi?ta maida abin wasa. ahaji na gani ne koyaushe sai ka wasa mamarka cikin dariya tayi maganar,shima cikin dariya ya ce,kin ga laifina kenan. Ya kalli MIMI,uwata ci abinci mana,ta zuba farfesun kaza ta soma ci tana yi,tana chating,bayan sun gama ne,alhajin ke ce ma MIMI zai yi bako ranar lahadi,ina so ayi masa tarba ta musamman,
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (60)Nan zamu yi diner da shi,inda zai zo da iyalansa,sai na fi yin murna. mommy nafisa ta ce wane ne?ya ce alhaji akilu bala, ministan man fetur,MIMI ta kalli mahaifinta,dad,ka samu ganawa da shi kenan,ya ce,uwata ai yanzu mun zama abokai tamkar tare muka taso.shi yasa na gayyace shi don ya ga iyalaina,MIMI ta ce dad insha ALLAH za mu tarbe su.kiran hajiya sauda ya katse shi,ya daga bayan sun gaisa ta ce,ya binciki MIMI ko ta yi karatun,ya ce,ki daina damun kanki sauda,za ta yi,suka ci gaba da maganarsu,jin haka ne bayan ya gama wayar ya mike daga kujerar ya nufi dakin shi,MIMI ta ce.amma dad dama ina so muyi magana a kan malamin nan.lna son a tsaida lokacin da zan dauka,don koya min karatu,ya ce kamar ya ya?ta ce,dad yau karatun minti hudu ya yi min,ya ce, ok na gane,da safe zan neme shi mu yi magana.ta ce,ok dad ni ma zan fito da wuri don a yi komai a gaba na ya ce,to bari in shiga ciki,ta ce tam,dad ni ma zan koma sama ne sai da safe ya ce,ALLAH ya kaimu. lsmail yana tsaye bakin kofar falon,tunda ya danna baa bude ba,kusan minti biyu,ya sake dannawa sai lokacin aka bude,daga ganinta 'yar aiki ce,kuma ba musulma ba ce,ta ce kaine malam?ya ce eh,ni ne,ta ce, ka shigo,a nan cikin falo ya same su dukkan su,ya kalli alhaji cikin girmamawa ya gaida shi,sannan ya gaida mommy nafisa,ya ce gani alhaji,malam hamisu ya ce,kana nema na. Alhaji ya nuna masa kujera zaka iya zama a kan kujera,MIMI ta kalle shi da gefen ido,aa dad kar ka bashi damar zama a kan kujera,ya kalle ta,saboda me?ta ce,dad bai kai matsayin ba,shi mabukaci ne a gurin mu,ta kalle shi, zauna a kan kafet,ya danne zuciyarsa,babu damuwa in maganar ba mai tsawo ba ce zan iya tsayawa alhaji,alhajin ya ce,kar ka damu zauna a kan kafet din abin ya bawa lsmail mamaki,amma sai ya zauna saboda alhajin ne ya bukaci hakan.ransa ya ce, lallai dama an ce karshen zamani baiwa zata haifi uwar gijiyarta.
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (61)Muryar alhajin ta katse shi,malam wanene ma sunanka?ya ce lsmail, alhaji ya amshe da cewa, yawwa lsmail,MIMI ce ta bukaci ka sa lokacin da za ku dinga yin karatu,da kuma tsawo lokacin da za ka dauka gurin yin karatun. lsmail ya ce hakan yana da kyau,wane lokaci ne ta tsaida?alhajin ya kalle ta, uwata wane lokacin ki kafi so ya koyar da ke?ta dan yatsina baki sannan ta kalli damfareren agogonsu a jikin bango kirar dubai,ta ce, kamar sha daya sai ya dinga zuwa don kada ya ce sai an aika a kira shi,ni bana son jira,nafi son a jira ni.lsmail ya yi dan murmushi a ransa ya ce,son kai, amma a fili sai ya ce,to mu tashi nawa?ta kalle shi sama da kasa.tsawon awa daya za mu yi gurin karatun.lsmail ya kalli alhaji, ba damuwa kullum zan zauna karfe shadaya mu tashi sha biyu kenan.ba lallai hakan ba ta katse shi. zaka iya zuwa misalin sha daya ya zama ban sauko ba,kai dai in ka zo shadaya daga lokacin dana sauko, daga saman na zo gurin karatu shine zaa dauki

1 Comments On CANJIN RAYUWA
avatar
mariya-6-8

11 months ago

Reply

In HAUSA language

Please Login or Register in order to submit comment