Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dz innar su Zainabu. Yau kam
fuska daure ta fita, da nufin bala’i tare da ita. Sai dai
shima tana kallon sa tasan cewa da hakan yazo,
kuma in ba sa’a bama shi ya dama ta ya shanye.
Kafin tayi magana ya riga ta.
Nazo daukar Zainabu ne. Ta lailayo ashar ta maka,
sannan tace, Zainabu ba zata koma ba, sai ya sauke
dubu ashirin da hudu na asibiti. Yace, tunda dai

banyi muku qorafin cikina da kuka zubar ba, to ku
bani matata kawai mu tafi. Inna tace, au tanan ka
biyo? To ai inason ka sani, tuni muka samu labarin
baka son haihuwa, bare kayi wata barazanar banza.
Ba zata koma ko ina ba, sai ka canke kudin mutane.
Yace, haka kk ce? To kuwa ku shirya cin wani bashin
don zaku amsa sammaci, kotu zamu shiga.
Ya ciro wayarsa, iroro dake gefe yace, Alhaji ai sai ka
kira lauyannan naka tukun, domin duk wanda baisan
mutunci ba, gara ayi masa abinda yafi sani. Wato
rashin mutuncin ba. Inna tace, ku kira alqali, ba
lauya ba. Kai kuma dan kanzagi makwadaici kabi a
sannu. Kaje ka nemi sana’a ba maula ba. Iroro yace,
ai indai wannan ne sunanmu daya dake, wato ‘yan
maula. Kwadayinki kuwa ya ninka nawa. Tunda kk
miqa ‘yarki ga wanda bashi ta za6a ba. Alhaji yace, ko
ba haka bama Iroro, ai baka kaita roqo ba, kullum
dan aike yana hanya. Tace, kodai me zaku fada, ku
fada.
Lokacin ne layin ya shiga wanda yake nema. Alhaji
yace, yauwa Barista audu kaji ko? Daga can suka ji
murya tace, eh ina jinka Alhaji lawal. Iroro yace,
Yauwa Alhaji ai gara kasashi a speaker taji. Alhaji
game da zancen da mukayi ne na matata. Ynxun
haka ina gidan uwarta ta hanani matata, don haka
zanzo mu shigar da qara. Daga can sukaji muryar
barista yace, qarar kisan kai zamu shigar, tunda basu
da mutunci. Ina ga ko dan gidan da suka mallaka, sai
sun daida ba tare da kuma sun kare kansu ba. Don
haka kar ka damu. Alhaji yace, shikenan nagode. Ya
kalli inna yayi murmushin mugunta, sai mun hadu a
kotu. Iroro ya sheqe da dariya. Dana sani tanata
bibiyarki. Har sun juya tace, Alhaji ya tsaya. Sannan
ya waiwayo.
Lafiya? Tace, bari in turo ta ku tafi. Kudin mutane
dana aro kuma idan nayi maka Allah ya isa fa? Tare
suka sheqe da dariya, Iroro da Alhaji. Iroro yace,
shegiya wuya! Alhaji yace, inna ai dama Allah
ishasshe ne. Cikin jin haushi, inna tace, ni ba innarka
bace don na tabbata ni kaina ka girmeni. Ta juya
cikin takaici, suna tayi mata dariya. Zainabu tana
kuka, tana komai, ta fito tabi Alhaji, tabar innarta
cikin takaici. Wani qarin abin haushi a lokacin suna
isa gida, saida yayi buqatarsa ya fita, ya barta tana
kuka.
Kishiyoyin suka shigo sunayi mata sannu tare da bata
haqurin rashin zuwansu. Ko kawo mata abinci sunce
Alhaji ne ya hana. Haka Zainabu taci gaba da
Rayuwar gidan Alhaji mai cike da matsi da takura,
gami da wahala, duk ta qara kodewa, ta fige ta lalace.
Kuma ya hana innarta zuwa, kamar yadda itama
yace ta daina zuwa gidansu. Innar Zainabu tasha

kuka tare da takaici da kuma da na sanin hada
Zainabu da Alhaji lawal.
Alhaji bashir ya dauki wayarsa ya soma neman layin
Abba. A ringing na biyu Abba ya dauka, ya kara a
kunne yana fadin dad ina kwana? Bayan sun gaisa
Alhajin yace, inason kazo yau ka tafi dani katsina.
Abba yace, amma lfy dai ko dad? Alhaji yace, lfy lau,
inason ganin mahaifiyarku ne, gashi har ynxun bana
jin dadin jikina. Abba yace, shikenan daddy, sai nazo.
Qarfe biyu Abba ya sauka garin Abuja. Tuni daddy ya
turo direba yana jiransa. Suka nufi maitama. Momy
Nafisa batasan da batun ba, saidai taga Abba. Ya
gaisheta tare da tambayar jikin daddyn, tace da
sauqi. Lokacin data shiga don sanarda Alhajin zuwan
Abba, sai yace ta hada masa wasu kayansa na ciki da
kuma wasu takardunsa. Tace, ina zaka Alhaji? Yace
katsina, nine nace wa Abba yazo ya tafi dani. Tace, ba
zaka bari kadan qara samun sauqi ba? Yace, karki
damu, can ma zanci gaba da ganin likita.
Shida daidai suka sauka a filin jirgin sama. Sun samu
direba na jiransu, domin kafin su taso daga Abuja,
Alhaji yasa Abba ya kira direban hajiya sauda,
batasan da zuwan Alhajin ba tana zaune a falo tana
ba Zainab magani, don yau kwananta uku babu lfy,
kullum suna hanyar asibiti. Sai kurum taji Sallamar
su. Bata zaci Alhaji bane, don muryar Abba irin ta
Alhajin ce. Saida taji yaran suna Oyoyo daddy. Da
sauri dago tace, sannu da zuwa Alhaji. Ta miqe cikin
sauri bayan ta kwantar da Zainab, tace, Alhaji baka
sanar dani cewa kana tafe ba. Yace karki damu tu
tunda mun iso lfy. Sun gaisa da Abba sannan ya nufi
gidansa.
Hajiya kuwa ta dauki jakarsa kuma ya bita zuwa daki.
Sannan ta dawo kusa dashi. Ya kamata kayi wanka
ko? Ya kalleta, zan yi wankannan kuwa? Barci nakeji
kuma inajin sanyi, sai inga kamar in nayi wankannan
zazza6i zai iya rufeni. Ta cire masa riga, sai singileti.
Ya kwanta akan gado, ta zauna bakin gadon. Kasha
magungunan ka kuwa? Yace, nasha, sai dai akwai na
ynxun qarfe shida, amma sai zan kwanta sannan zan
sha. Tace, a’a nidai kasha ynxun, yana da kyau kabi
dokar likita.
Ynxun tashi zakayi in taimaka maka kayi wanka,
kasha magani kayi sallah don kaga magriba ta kusa.
Ya tsura mata ido, “sauda nayi miki laifi ko? Ta kama
hannunsa, ni baka min laifi ba, to muje kayi? Yace, to
sauda muje. Kafin yayi sallah har ta shiga kicin da
kanta tayi masa tuwon alkama miyar alayyaho. Yana
zaune kan sallayarsa yana istigfari. Can qasan
zuciyarsa kuwa tunanin mimi takeyi.
Zuwa ynxun ya gama tabbatar ma kansa cewa, son
da yake wa mimi ya zarta tunaninsa, kuma ba zai

ta6a son wani cikin ‘ya’yansa kamarta ba. Amma dole
ya jure sbd ya samu ya ida nufinsa don ta samu
canjin rayuwa. Wasu hawaye suka soma zubo masa.
Sam baiji Sallamar Hajiya sauda ba, har saida ta dafa
shi, sannan ta tsugunna tare da aje abincin dake
hannunta dayan. Duk da saurin da yayi ya share
hawayen sa, saida tace “na shiga ukuna! Alhaji kukan
me kkyi? Cikin sarqaqqiyar murya yace, ba kuka
nake ba. Sauda ta zauna dirshan akan sallayar, cikin
tashin hankali tace, haba Alhaji. Shekarunmu nawa
ban ta6a ganin hawayen ka ba sai yau.
Dole akwai wani babban al’amari. Ta kama
hannunsa. “Na roqeka karka 6oyemin komai.
Idanunta suka cika da hawaye yadan matsa
hannunta, “sauda karki tada hankalinki ba wani abu
bane. Sannan inason don Allah ki yafe min nasan
cewa, na sa6a miki da yawa. “qara firgita tayi, gani
takeyi tamkar Alhajin mutuwa zaiyi ya barta. Sai ta
soma kuka. Jikinsa ya janyo ta.
Haba sauda, mene ne na kuka kuma? Tace Alhaji don
Allah karka tafi ka barni. In kuma wata matsala ce
tasa zubar hawayen, don Allah ka fadamin. Yace,
sauda bazan 6oye miki ba, ina kuka ne sbd mimi.
Saida na rabu da mimi nasan cewa, inayi mata
mugun son da bansan adadinsa ba. Tunanin ta ne ya
hana sugar na sauka, na sani. Ya dago fuskarta mai
dauke da mamaki. Ta kalleshi cikin ido, “sbd mimi kk
cikin wannan tashin hankali? Yace, eh sauda. Tace to
me zai hana ka tashi muje gurinta ynxun a asibiti?
Yace, lokaci baiyi ba.
Sauda ynxun zan sanar dake dalilina na aura wa
mimi talaka. In kince ban kyauta ba, to zanje gurinta
ynxun, in kuma raba auren ta, sannan in fita da ita
wajen qasarnan don nema mata lfy. Hajiya sauda
tace, kafin nan bari in baka abinci da kuma magani.
Tunda munyi sallar isha’i, sai inje in sallami yara na
inzo in saurareka har zuwa asubahi. Yayi guntun
murmushi. Ta janyo tiren, ta zuba tuwon a cikin
plate, tasa a gabansa. “in baka a baki?” yadan
karkatar da kai, “bana tuna shekaru na matsawar ina
gabanki. Ki bani zanci da hannayenki masu albarka.
Ta soma bashi tuwon, bayan yayi bissimillah. Bai iya
tuna lokacin da yaci abinci kamar na yau ba sam.
Tana bashi tana masa hira har yayi qat. Ta bashi
magani, sannan ta jashi da wata hirar, tunda ta gano
maganar Mimi ce damuwarsa.
Batun ‘yan uwanta ta dauko masa na auren ‘ya’yan
sa’ade ‘yar uwarta, da irin gudummuwar da ta basu.
Yace, nima zan bada tawa. Kullum inason in nazo
inje in gaida ya Dikko sai abubuwa susha min kai.
“sauda tace, har na gaji dayi mata qaryar cewa, kana
gaida ta. Kwanaki tazo tayi sati hudu. Har yaya jabiru

yazo suka tafi baka zo ba. Yace, wannan karan zan
huta a gurinki sauda, zanje in ganta jabiru dai ya
hanamu ita, da ynxun tana nan. Sauda tace, ai bazai
yarda ba shiyasa na haqura.
Ya qura mata ido na ‘yan kakwanni. Ta shafi
kumatunsa, “wai wannan kallon fa? Yace, karki
tsorata sauda. Nasan tsoranki, kar in mutu in barki
ko? Ta matsa hannunsa dake cikin nata. “wlh tsoron
kenan Alhaji. Ko tuna hakan nayi ina zubar da
Hawaye bare ace ta kasance. Ya sauke ajiyar zuciya.
“sauda ni kaina banason in mutu ba tare da na cika
burina ba.
Burina in saku cikin farin ciki bayan mutuwa. Tace,
wace irin mutuwa zakayi inyi farin ciki in ba ni na
riga ka ba? Burina in rigaka. Yace, a’a sauda, ni ya
dace in tafi in barki, domin ‘ya’yanki su samu
tarbiyyar ki. Ko mimi inayi mata takaicin rashin
samun tarbiyyarki. Ma’anar in na mutu kuyi farin ciki
shine, in daidaita tsakani na da Allah da kuma tsakani
na da iyalina da sauran mutane.
Hajiya kuwa ta dauki jakarsa kuma ya bita zuwa daki.
Sannan ta dawo kusa dashi. Ya kamata kayi wanka
ko? Ya kalleta, zan yi wankannan kuwa? Barci nakeji
kuma inajin sanyi, sai inga kamar in nayi wankannan
zazza6i zai iya rufeni. Ta cire masa riga, sai singileti.
Ya kwanta akan gado, ta zauna bakin gadon. Kasha
magungunan ka kuwa? Yace, nasha, sai dai akwai na
ynxun qarfe shida, amma sai zan kwanta sannan zan
sha.
Tace, a’a nidai kasha ynxun, yana da kyau kabi dokar
likita. Ynxun tashi zakayi in taimaka maka kayi
wanka, kasha magani kayi sallah don kaga magriba ta
kusa. Ya tsura mata ido, “sauda nayi miki laifi ko? Ta
kama hannunsa, ni baka min laifi ba, to muje kayi?
Yace, to sauda muje. Kafin yayi sallah har ta shiga
kicin da kanta tayi masa tuwon alkama miyar
alayyaho. Yana zaune kan sallayarsa yana istigfari.
Can qasan zuciyarsa kuwa tunanin mimi takeyi.
Zuwa ynxun ya gama tabbatar ma kansa cewa, son
da yake wa mimi ya zarta tunaninsa, kuma ba zai
ta6a son wani cikin ‘ya’yansa kamarta ba. Amma dole
ya jure sbd ya samu ya ida nufinsa don ta samu
canjin rayuwa. Wasu hawaye suka soma zubo masa.
Sam baiji Sallamar Hajiya sauda ba, har saida ta dafa
shi, sannan ta tsugunna tare da aje abincin dake
hannunta dayan. Duk da saurin da yayi ya share
hawayen sa, saida tace “na shiga ukuna! Alhaji kukan
me kkyi? Cikin sarqaqqiyar murya yace, ba kuka
nake ba.
Sauda ta zauna dirshan akan sallayar, cikin tashin
hankali tace, haba Alhaji. Shekarunmu nawa ban
ta6a ganin hawayen ka ba sai yau. Dole akwai wani

babban al’amari.
Ta kama hannunsa. “Na roqeka karka 6oyemin
komai. Idanunta suka cika da hawaye yadan matsa
hannunta, “sauda karki tada hankalinki ba wani abu
bane. Sannan inason don Allah ki yafe min nasan
cewa, na sa6a miki da yawa. “qara firgita tayi, gani
takeyi tamkar Alhajin mutuwa zaiyi ya barta. Sai ta
soma kuka. Jikinsa ya janyo ta. Haba sauda, mene ne
na kuka kuma? Tace Alhaji don Allah karka tafi ka
barni. In kuma wata matsala ce tasa zubar hawayen,
don Allah ka fadamin. Yace, sauda bazan 6oye miki
ba, ina kuka ne sbd mimi. Saida na rabu da mimi
nasan cewa, inayi mata mugun son da bansan
adadinsa ba. Tunanin ta ne ya hana sugar na sauka,
na sani.
Ya dago fuskarta mai dauke da mamaki. Ta kalleshi
cikin ido, “sbd mimi kk cikin wannan tashin hankali?
Yace, eh sauda. Tace to me zai hana ka tashi muje
gurinta ynxun a asibiti? Yace, lokaci baiyi ba. Sauda
ynxun zan sanar dake dalilina na aura wa mimi
talaka. In kince ban kyauta ba, to zanje gurinta
ynxun, in kuma raba auren ta, sannan in fita da ita
wajen qasarnan don nema mata lfy. Hajiya sauda
tace, kafin nan bari in baka abinci da kuma magani.
Tunda munyi sallar isha’i, sai inje in sallami yara na
inzo in saurareka har zuwa asubahi. Yayi guntun
murmushi. Ta janyo tiren, ta zuba tuwon a cikin
plate, tasa a gabansa. “in baka a baki?” yadan
karkatar da kai, “bana tuna shekaru na matsawar ina
gabanki. Ki bani zanci da hannayenki masu albarka.
Ta soma bashi tuwon, bayan yayi bissimillah. Bai iya
tuna lokacin da yaci abinci kamar na yau ba sam.
Tana bashi tana masa hira har yayi qat. Ta bashi
magani, sannan ta jashi da wata hirar, tunda ta gano
maganar Mimi ce damuwarsa.
Batun ‘yan uwanta ta dauko masa na auren ‘ya’yan
sa’ade ‘yar uwarta, da irin gudummuwar da ta basu.
Yace, nima zan bada tawa. Kullum inason in nazo
inje in gaida ya Dikko sai abubuwa susha min kai.
“sauda tace, har na gaji dayi mata qaryar cewa, kana
gaida ta. Kwanaki tazo tayi sati hudu. Har yaya jabiru
yazo suka tafi baka zo ba. Yace, wannan karan zan
huta a gurinki sauda, zanje in ganta jabiru dai ya
hanamu ita, da ynxun tana nan. Sauda tace, ai bazai
yarda ba shiyasa na haqura.
Ya qura mata ido na ‘yan kakwanni. Ta shafi
kumatunsa, “wai wannan kallon fa? Yace, karki
tsorata sauda. Nasan tsoranki, kar in mutu in barki
ko? Ta matsa hannunsa dake cikin nata. “wlh tsoron
kenan Alhaji. Ko tuna hakan nayi ina zubar da
Hawaye bare ace ta kasance. Ya sauke ajiyar zuciya.
“sauda ni kaina banason in mutu ba tare da na cika

burina ba. Burina in saku cikin farin ciki bayan
mutuwa. Tace, wace irin mutuwa zakayi inyi farin
ciki in ba ni na riga ka ba? Burina in rigaka. Yace, a’a
sauda, ni ya dace in tafi in barki, domin ‘ya’yanki su
samu tarbiyyar ki. Ko mimi inayi mata takaicin
rashin samun tarbiyyarki. Ma’anar in na mutu kuyi
farin ciki shine, in daidaita tsakani na da Allah da
kuma tsakani na da iyalina da sauran mutane.
Hajiya sauda, cikin mamaki tace, kana da wani hali
ne na daban? Domin in da za’a tambayeni halinka,
zan bada shedar cewa, kai mutum ne na gari. Yace,
“sauda kowane dan Adam ajizi ne, in dai ba
ma’asumi bane. Harkoki na sunsa bana samun yin
sallah akan lokacin ta. Harkokina sunsa ‘ya’ya na basu
samu soyayyata ba. Harkokina sunsa ‘yan uwa
maqota ban basu nasu haqqinba.
Shawararki da nayi ta guje mawa ynxun na gano
itace mafita. Zan aje tunani na na kullum, wato
maida Naira ta zama Dala, ko ko taro ya zama sisi. Ta
kamashi, tashi ka koma kan gado, bari in kwashe
kwanukannan, in kuma tabbatar da yarana suna
cikin makwancinsu. Ya miqe tare da komawa kan
gadon. To karki jima maman yara. “Bayan fitowar ta
ne ta tsaya bakin qofar, sannan ta daga hannunta
sama, “Alhmdlh, ya Allah ka qara sa mijina akan
hanya madaidaiciya.
Kamar kullum daga dakin su Abdullahi ta soma har
zuwa dakin su Zainab dasu Hasina. Nan ta dan 6ata
lokaci don sai da taba Zainabu magani sannan ta fito.
Zata shiga dakin su usaina saiga su sun fito. Tace, ina
zakuje? Suka ce munason mu sake yiwa daddy sannu
da zuwa, sannan muga jikinsa ne. Tace, to kuje yana
ciki, ina zuwa nima. Dakinta ta shige don ta dan sake
kintsawa cikin kayan varci. Su Hasana suka shiga
dakin daddyn su bayan sunyi sallama, ya kuma basu
izini.
A hannun kujera suka zauna suka gaida gaida shi tare
da sake tambayar jikin sa. Ya tashi zaune daga
kishingidar da yayi. “kuzo nan yarana! Suka kalli juna
cikin mamaki, sannan suka nufeshi. Ya ce, ku zauna
bakin gado kyawawan ‘yan biyu na. Suka zauna. Ya
dora hannunsa akan kafadar ko waccensu. ‘Yan biyu
kuma fa kun girma, masha Allahu. Hajiyarku tace
min zakuyi jamb da Waec ko? Suka sake kallon juna,
sannan sukace “eh daddy mun kusa mu fara. Yace, to
Allah ya baku sa’a. Suka ce Ameen.
Ya sake cewa, me kuke karantawa ne? Ina nufin Art
ko science? Usaina ta kalleshi “‘Hassana ce take
science class, ni Art nike. Yace, Hassana zamu doctor
kenan? Ta kalleshi cikin Jindadi tace, eh daddy inason
in zama medical doctor. Yace, Usaina fa? Tace, daddy
nikam ‘yar jarida nakeso in zama, ina sha’awar haka,

shiyasa mass com zan karanta. Cikin farin ciki yace,
nagode ma Allah. Allah ya cika muku burinku yara
na. Daidai lokacin Hajiya sauda ta turo ta shigo da
sallama. Ta kallesu da fara’a ” ‘yan biyu azo aje ayi
varci ko? Suka miqe, sannan suka sake cewa, daddy
Allah ya baka lfy. Yace, Ameen nagode. Suka ce,
Hajiya saida safe.
Tace, mu kwana lfy karku manta da Addu’a. Suka ce,
to. Ta zauna tana kallon fuskarsa, “sun dameka da
surutunsu ko? Yace, inason su saki jikinsu dani.
Tace, ya kamata kam. Yace, “ynxun wace shawara
zaki bani? Ta kalleshi “tame? Maganar da nayi miki
dazun, ta damqa harkoki na ahannun yara, kamar
yadda kike ta bani shawara tuntuni. Tace, ynxun
kwanta kasha magani fa, in ka samu varci, gobe idan
Allah ya kaimu, sai muyi maganar ko? Ya kwanta tare
da cewa, Allah ya kaimu. Itama ta kwanto masa, tare
da kashe fitilar dakin.
Alhaji Bashir ya jima bai samu varci kamar na yau
ba. Yaji dadin jikinsa daya farka, har masallaci yaje.
Sannan da gari ya dan yi haske, sai yace, ki fitomin
da kayan motsa jikina, zan dan fita. Likita yace, in
dinga motsa jiki sosai, zufar da zan fitar tana fita da
cutar.
Hajiya sauda tace, tunda yarannan suna hutu, to ka
fita dasu Abdullahi mana da Sadiq da Ameen da
Umar. Take ya yarda sbd ynxun kam burinsa bai
dara kusantar duk ‘ya’yan nasa ba. Suka fito cikin
kayan motsa jiki. Yaran sun sa gajeran wando da riga
mai gajeran hannu, yayin da uban yasa mai dogon
hannu da kuma dogon wando. Yaran cikin murna,
domin suna son fita motsa jiki sosai, Hajiya ce take
hanasu, wai tace, batasan da wadanne irin abokai
zasu hadu ba in sun tafi can gurin motsa jikin. Alhaji
ya dube ta, “sai mun dawo.” Cikin salon tsokana tace,
“to Alhajina. “Ta kalli Abdullahi, “Yarana masu
albarka, ku lura min da mijina. Gaba daya suka sa
dariya. Tace, da gske nakeyi Abdullahi, kar yayi gudu,
tafiya kawai zakuyi. Suka ce “To” suka jera suka fita,
biyu nan, biyu nan, suka sa mahaifinsu a tsakiya.
Kafin ya dawo tuni ta dama masa kunun alkama da
qosai.
Qarfe takwas suka dawo, duk yayi zufa, yaran suka
nufi dakinsu don yin wanka. Shi ko Alhaji har
taimaka don yin wanka. Shi ko Alhaji har taimaka
masa tayi tayi, yayi wanka don nuna kulawa. Bayan
yaci abinci, yasha magani, sai yace, ki shirya zamu
fita. Tsaf tayi kwalliya cikin koriyar super da hijabinta
wanda kyansa ya nuna tsadarsa. Qamshi take yi, ta
bar sallahun komai gurin masu aiki tare da sauran
yaran, sannan suka fita. Direban shi ya taso, Alhaji
yace, je ka huta. Nine zanja motar. Saida ta zauna a

gidan gaba, sannan ta kalleshi da murmushi. “kai da
baka da lfy?
Yace, sauda kowane lokaci in muna tare bana son
mu samu na uku. Sai inga tamkar mu kadai ne a
duniyarmu. “Tasa dariya, daidai lokacin daya tada
motar. Tace, to kaba ni in tuqa mu. Kaifa jiya kazo.
Yace, baki lura ina ganinki na samu sauqi ba. Ynxun
ma kinsan ina zamuje? Tace, a’a. Sai da ya hau titi
sosai, sannan yace, gidan saukar baqina. Inason
muyi hirar da muka dade bamu yi irin ta ba. Sannan
mu tattauna muhimman zantuka. Murmushi tayi
batace qala ba.
Kwance suke a tsakiyar gadon na dakin baqin, suna
fuskantar juna, yace sauda na buqaci muzo nan ne
musamman don in baki haquri, sannan in fada miki
dalilaina. Sauda nasan cewa, na sa6a miki lokacin
dana rabaki da ‘yarki na kaita ga wata, wanda harga
Allah lokacin soyayyar Mimi ta rufemin ido har na
aikata haka. Amma kika yi haquri. Sannan na biyu
kece kadai zanyi wa ‘yarki abinda nayi mata, wato
aurar da ita ga talaka ba tare da kin dagamin hankali
ba.
Da wata ce, cikin sauran matan, na tabbata da ranar
aurenmu da ita zai mutu. Sai na qarshe kece kadai
‘yarki zata samu hadari, in hanata zuwa, kuma ta
hanu. Sauda duk inda ake neman mace ta gari, kin
kai. Ina roqon Allah yasa ki zama shugabar matana a
gidan Aljannah. Cikin murmushin jin dadi tace,
Ameen Alhaji. Ya tashi zaune. “sauda dalilina na aurar
da Mimi ga malam Ismail, tare kuma da yanke duk
wata alaqa da ita tare da cire ta cikin ahalina shi ne.
Kashhh! Mu hadu cikin littafi na hudu, kuma na
qarshe. K. Mashinku ce, sai na jiku a 08081165107


Chanjin rayuwa book 4
1⃣Saboda ta samu canjin rayuwa, daga jahilci zuwa ilimi, daga rashin tarbiyya zuwa tarbiyya, daga mara mutunci zuwa mai mutunci. Sauda, da farko nayi wa Mimi wannan auren ne don in quntata mata, in qona mata rai, kamar yadda ta qona min. Amma daga baya tunani ya shige ni, nayi nazarin dalilin wannan auren zata iya samun canjin rayuwa. Ismail zai iya bata ilimi na addini wanda ta rasa daga gareni. Sannan, ilimi zaisa ta zama mai tarbiyya ko dan yaya, tunda anbar shiri tun rani. Dalilin da yasa nace kar kuje gurinta, nima nace kar su sake nemana, sbd idn bata tare damu, zata fi samun tarbiyya. Shi ba zaiji shakkar mu ba, ko tsoron mu in tayi abin hukunci. Kuma yanda na lura dashi, bashi da shakka, kinga kenan ba zaiji tsoron duk wata barazanar ta ba. Haka kuma ba zamu taimaka musu da kudi ba, sbd shi kansa banason mu kashe masa zuciya, ya kasa neman na kansa, ko yaushe yana jiranmu. Haka kuma ita kanta rashin taimaka musun zaisa ta saba da Rayuwar babu, wadda bata sani ba ada. Yanke alaqa dasu shine zaisa ita da shi suyi abinda ya kamata.
Hajiya sauda ta sauke ajiyar zuciya, "Na fahimceka sosai Alhaji, saidai nayi wani kuskure daya. "ya kalleta, na tura musu dubu dari. "karki damu, saidai karki sake tura musu kudi. Da zaki iya ma ko wayarsu karki sake kira. Ta danyi shiru tana nazari. Ya katseta, kar kisa ma kanki damuwa, nayi miki alqawarin bibiyar miki labarin duk halin da suke ciki. Ta tsura masa ido, a cikin qwayar idanunsa ta tabbatar da abin da yake fada. Tace, shikenan Alhaji. Allah yasa mu dace. Yace, "Ameen matar qwarai". Ya kama hannunta, "nasan ranki ya nutsu da yaron, kuma nima na fahimci cewa, yaron mai hankali ne. "Sukayi dariya. Yace, kinsan menene sauda? Tace a'a. yace, "Ni kaina ina cikin matsanancin kewar Mimi. Na sani sarai tunaninta ne ya hana ciwwonnan sauka. Tace, nasan za'ayi haka, amma tunda kanada wannan qudurin, wajibinka ne ka daure, ka jure, ka kuma kauda kai, sannan mu hada da Addu'a, Allah ya taya mu. Yace, Ameen ya rabbi. Ynxun kuma na samu natsuwa tunda Allah yasa kin fahimceni. Ranar nan suka yini suna qoqarin kyautata ma juna.
2⃣Haka itama Mimi tayi ta jinya, yaya Amina da Ismail suna matuqar kula da ita. 'yan uwan mamansu na Daura sunzo, sun duna jikin Mimi, sannan sun kawo musu kudin gonarsu da aka saida. Don haka shirye-shiryen tafiyar Ismail ya kankama. Haka nan 6angaren Mimi, zuwa ynxun Ismail yayi nasarar saka Mimi ta fara sallah dole, ba don ta so ba. Yawan nasiha da nacinsa ya sata sauraronsa. Ya nuna mata yadda zatayi sallah, kuma ya dauki nauyin yi mata akwalla. Ranar daya fara tsananta mata tayi sallah da kuka tayi sallar. Da farko ma bata yi ba, sai da yace shikam ba za yayi jinyarta ba, matsawar ba zata yi sallah ba. Ya nuna mata shifa tafiyarsa zaiyi. Yaya Amina ita ma cikin son ta tsorata ta tace, in ko ka tafi, nima zaman me zanyi? Kinga kenan saiki zauna babu mai jinya, ba mai kula dake. Tana kukan nata tace, yayi mata alwalla. Tun daga ranar, duk lokacin sallah in yayi, sai ta yita. Wani abin da yaba Mimi al'ajabi shine tunda ta soma sallah, sai ta samu kanta cikin wata natsuwa, ta kuma qara imanin cewa sallah tana kusanta bawa ga ubangijinsa. Haka kuma lokacin da yace zai dinga koya mata gajerun surori, bata qi ba sbd sallah.
Kwanci tashi har taci wata daya da sati daya a asibiti. Lokacin ne kuma da Doctor din dabyayi mata dori ya dibar mata zaizo ya duba in dori yayi kyau, sai ya kwance. Ranar litinin da misalin qarfe goma na safe, likitan suka shigo shida doctor salis. Kallon qafafun nata kawai yayi, yace inasa ran cewa dorin yayi kyau. Zan kwance shi ynxun sai ku kaita ayi mata hoto, sai ku kawo mu gani. Ismail cikin murna yace, Alhamdulillahi, dama na gaji da zaman asisibitin nan, har ita ma khadijan ta gaji ko?. Ya fada tare da kallonta. Mimi ta kalli likitan, kenan in hoton ya nuna cewa, dorin yayi za'a sallameni ne? Likita yace, eh, to ku daiyi hoton mu gani. Bayan an kwance tana ta shagwa6a, ta qanqame yaya Amina. Likitan yace, a kaita hoto ynxu. Ismail ke tura ta a kujerar tura marasa lfy suka nufi gefen hoto. Yaya tana jere da shi suna magana. Yace, "Yaya Allah yasa hoton babu tsada sbd Kinsan fa babu sauran kudi, gashi kudin dakinmu dana sake biya ya qare. "Wai saura nawa ne ma kudinnan da aka ajiye sbd tafiya? Yace "ta6" ai baifi saura dubu goma ba acikin dubu hamsin din dana ba Mahmud don kar in kashe, amma duk sun qare. Tace, ai dama zara bata barin dami.
Barkanmu da sallah sis 🙌
[17/09 1:18 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa

5⃣A qofar gidansu yakeyin wankin, amma yanajin

1 Comments On CANJIN RAYUWA
avatar
mariya-6-8

11 months ago

Reply

In HAUSA language

Please Login or Register in order to submit comment