Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

MIMI ta ce,to ni bana son dad ya ce ban ji maganarsa ba.ta ce,kar ki damu da haka.yanzun nan daga dakinsa nake.ya ce in ya ga kin dage zai hakura. MIMI ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta ce, shi kenan zan tsaya a kan raayina.momy nafisa ta ce,duk runtsi ki ce baki son abbas.MIMI ta ce, "shi kenan." Alhaji kam, hajiya sauda ya kira yana labarta mata komai daya faru,tun daga burinsa har zuwa yanzu.ya ce,ina son ki kira ta ki yi mata fada,ta bar batun wani yaro.......
[01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (4)Ta tsaya ga wanda ni na zaba mata. hajiya sauda ta ce,alhaji ba zan shiga zancenku ba,kai da lelenka.abu daya kawai nake ganin zan iya.shi ne zan kira ta in bata shawara. ya ce ban gane ba zaki shiga zancenmu ba. ta ce alhaji ke nan.yanzu ne da ta kwabe muku ka san da ni?lna uwarta mai son ta wadda aka canza mata da ni,saboda ni ina takura mata ta yi abin da ya kamata?shawara kawai zan ba ta ta yi maka biyayya,amma ba wai in takura mata ba.ldan ta ki yarda,sai ka yi mata abin da take so,kamar yadda ka sabar mata tun tana karama.shiru ya yi,ya kasa magana.sai kuma ya kashe wayar. momy nafisa ta same shi cikin damuwa, yana ta tattauna maganganun hajiya sauda a cikin zuciyarsa.ta zauna kusa da shi.alhaji nayi maga da MIMI.ya kalle ta cikin sauri,ta amince? "MIMI ta ki sam alhaji.kuka take ta yi.da na tsananta mata da lallashi,da nuna mata cewa ta yi maka biyayya, sai ta ce min don na ga bani na haife ta ba.ln dani na haife ta ba zan so a yi mata auren dole ba.ya ce haka ta fada?kenan tana da daurin gindin mahaifiyar tata?domin da na kira ta a kan ta yi mata fada,ce min ta yi ita shawara zata iya ba ta, ba fada ba. Momy nafisa,cikin jin dadi ta ce,amma hajiya sauda ba ta kyauta ma kanta ba.ta yaya za ta hana 'yarka ta yi maka biyayya?"ya ce,shi ne abin mamakin amma zan gwada musu su duka cewa ba su isa ba."ta ce, "abin da ya kamata kenan da ma ku zauna kai da minista ku sa lokacin auren sati uku ko hudu,ku daura kawai,ka wuce gurin kamar yadda na fada maka.ya ce, gobe za mu tattauna da shi.amma MIMI ba ta isa ta ja min asara ba.ta lelo ta koma min kenan. lta kuwa hajiya sauda, wadda ba ta san komai ba, sai da alhaji ya fada mata, amma ita ma yanzun laifin ya shafe ta,ta kira MIMI. can kasa-kasa ta ji muryar MIMI ta amsa sallamar hajiyar.hajiya ta ce"ba ki da lafiya ne?"MIMI ta soma kuka,dad ne wai sai na auri dan minista,kuma ni bana son sa."Hajiya sauda ta ce,ni dai in na isa in fada miki ki ji,to ki bi zancen mahaifinki,
[01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (5)Ki auri wanda yake so.yanzu ke wannan ba abin kunyarki bane,saura 'yan uwanki su ji kina takaddama da ubanku? mutumin da ya nuna miki gata,ya yi miki duk abin da ki ke so,ya nesanta ki da duk wani abu da zai bata miki rai.MIMI na zaci ko wuta babanki ya hura ya ce,ki shiga,za ki shiga ba tare da kin tsaya dogon nazari ba.ashe ba kya yi masa son da yake yi miki. ki yi tunani sosai,kuma ki yi abin da ya dace.shawarata kenan."Ba tare da ta ji uzurin MIMIN ba ta kashe wayar. Alhaji lawal ya kawo sadakin zainabu dubu dari kamar yadda lnnarta ta fada musu.kuma an kawo akwatuna,an kuma sa ranar bikin sati biyu.zainabu na ta kuka kuma har gidan su mahmood ta je ta fada masa,ta kuma bukaci ya bata wayar don ALLAH,ta kira lsmail.ya ce mata ai kawai taje tabi maganar iyayenta.lsmail ba abinda zai iya tunda an rigaya an yi mata miji.shi ba ya so ma lsmail din yaji zance ma haka ta tafi ba tare da ta cika burinta ba.lsmail kuma duk kwanakin sai yayi ta fama da muggan mafarkai marasa kai.ln ya kira mahmud,sai ya ce masa kowa lafiya.tun kwanaki da yayi waya da zainabu, mahmud bai sake hada su ba.ln ya ce masa don ALLAH ya je gun ta za su yi waya,sai ya ce masa ba lokaci.daga karshe har ya ji haushi,ya ce,na daina cewa ka kai mata wayarka.da na dawo zan sai mata in huta. mahmud ya ce,ka taimake ni,don ba a son raina nake zuwa ba.lsmail ya kashe wayarsa cikin takaici. kusan kwanaki uku,in lsmail ya shiga gidan don koyar da MIMI,har lokaci ya cika bata fitowa,don haka sai ya kuduri niyyar yau in alhaji ya dawo zai sanar da shi. haka kuwa bayan sun yi sallar isha.sai ya sanar da alhajin.alhaji ya ce zai yi mata magana.ln ma bata fito ba kar ka damu.ka ci gaba da koyar da kannenta. lsmail ya ce shi ke nan.alhaji ya ce in ta fito kuma,to don ALLAH ka dinga yi mata nasiha.ka ji ko?lsmail ya ce,insha ALLAH. momy nafisa ita da naima sun kulle kansu a dakin momy tana sanar da na'imar yaddaa tsarin da ta yi yake tafiya yadda take so.
[01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (6)Ta ce an kusa zuwa gurin kar ki damu. na'ima yanzu fa har hajiya sauda,alhaji haushin ta yake ji.ya zaci ita ce ke zuga MIMI.shekaran jiya MIMIN ke fada min wai hajiyar saudar ta ce lallai ta bi zabin alhaji.na ce mata MIMI kin san dai sai dai mahaifiyarki ta gwada min ta haife ki,amma ba ta kai ni son ki ba ko?MIMI ta ce eh.na ce to ki yi duk abin da na ce,lta kin ga bata yi boko ba,ba lallai ta san 'yancin kanta ba,bare naki. MIMI ta ce haka ne.nan da nan na zuge ta.sai da na goge dan tunanin da ta soma yi na danganar da uwar ta sa ta yi."Na'ima ta ce momy ai na ji dadi.yanzu dad ya fi kula mu a kanta.momi ta ce shegiya ba,ni ma na dan ji tsai,a yi nan dad dina,a yi can dad dina,ta kwaikwayi muryar MIMIN,suka kwashe da dariya.na'ima ta ce,to ba ki ganin dad zai iya daura musu auren,ni kuma fa? tunda kin ce masa kawai su sa rana.momy ta ce,ina so ne a yi mai yiwuwa ne a gama.shi ya sa nake son a sa rana.ke dai duk abin da na ce ki yi,to ki yi kokari ki aikata.na'ima ta ce,"an gama." Alhaji akilu da alhaji bishir suna zaune cikin ofishin alhaji bishir din,su zabi haduwa a nan ne don su tattauna batun auren yaransu.alhaji bishir ya ce,ka san ja'irar yarinyar nan wai ina fada mata sai take neman yi min gardama."haba dai?!"in ji alhaji akilu.alhaji bishir ya ce,"ALLAH kuwa.amma na san duk iyayi ne na yaran nan."alhaji akilu ya ce,ka san mata ba mamaki tana zaton mu ne muka hada su,ba shi ne ya gan ta ya ce yana so ba.ka bar ta kawai.da zaran an yi kiyayyar mace bata dorewa.sai dai in ba ta samu kula ba. Cikin jin dadi,alhaji bishir ya ce na gode daka fahimci hakan.yanzu wane lokaci kake ganin za musa? alhaji akilu ya ce kar mu ja abin;mu yi mu wuce gurin. ni ma haja na gani,in ji alhaji bishir.mafi sauki mu saka sati uku ko hudu.alhaji akilu ya ce,mu bar shi hudun.don naji mata suna cewa za a fita dubai ko chaina hado kayan auren.shi kuma angon ya soma gyaran gidan nan nawa na asokoro.
[01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (7)Alhaji bishir ya ce, ka fasa sai da shi ke nan? ya ce,ba dole in fasa ba, tunda abbas ya dage gidan yake so?gidan yayi masa girma,amma shi wai tsarin gidan yayi masa.alhaji bishir ya ce,to a bar masa. ALLAH ya sa hakan ya fi alheri.alhaji akilu ya ce. amina.zan turo waliyyan nasa,kanina da alhaji sa'idu abokina za su zo.alhaji bishir ya ce,babu matsala. ni ma zan yi wa nawa kanin da kuma alhaji kabiru magana.yaushe ne za su zo?alhaji akilu ya ce cikin satin nan.za dai muyi waya. bayan sun gama tsarinsu ne suka koma batun kasuwancinsu. Abu kamar wasa,zance ya soma nuna,don an kawo sadaki.kuma momy nafisa da wata kawarta sun shaki kudi gurin alhaji sun nufi dubai siyayyar kayan kicin, ta zage kuma tana ta zabar masu kyau da tsada,domin tana fatan su rikide su zama na na'ima. Tafiyarsu da kwana biyu,sai ga khalil da mahaifiyarsa har gidan su MIMI.yadda abin ya faru kuwa,hajiya amina ta ga danta ya shiga damuwa da tashin hankali ta rasa gane kansa,sai ta tsare shi a daki don ya fada mata damuwarsa.ta yi ta lallashin sa da nuna masa cewa,ita ce ta fi dacewa da ta san matsalasa,kuma ta magance masa,in har za ta iya.jin haka ya sa shi koro mata komai.ba ta yi kasa a guiwa ba ta sanar da mahaifansa wanda hankalinsa yake kan siyasa. nunawa yayi wannan ba damuwarsa ba ce damuwarsa kawai khalil ya yi karatu ba tare da zabin da ya wuce bai wa dan nata hakuri,gami da shawarar tsayawa kan karatunsa.amma cikin kwanakin sai ga yaro kwance warwas,ba ci ba sha,duk ya fita hayyacinsa. ba arziki ta taso shi zuwa abujan don rokon a bar masoyan su ci gaba da soyayyarsu har zuwa lokacin da za su hattama karatunsu,sai a daura musu aure. na'ima da ke falo ita ce ta amshi bakuncin nasu. suka gaisa.ta ce,kun zo gurin momy ce?ga shi ba ta nan.hajiya amina ta ce, mahaifinku fa?na'ima ta ce, yanzun nan ya fita.khalil ya ce MIMI fa?na'ima ta ce tana samanta;in kira ta ne? hajiya amina ta ce,eh.kudundune take cikin bargo.yau tun safe zazzabi ke jikinta.
[01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (8)Na'ima ta yi sallama,ta shiga ta sami MIMI.baki aka yi.sun ce in kira ki.ta ce daga ina?ki ce su hawo,ba zan iya sauka ba.na'ima ta raka su har falon MIMI,ta ce,sis ga su nan.MIMI ta yunkura za ta tashi,ta kasa.ta ce,tambaye su na'ima,daga ina?ba zan iya tashi ba.na'ima ta tambaye su.sai ko hajiya amina ta mike mu je kawai,in yi mata bayani. Ta zauna bakin gado,ta kamo hannun MIMI,yata ni ce mahaifiyar khalil.da sauri, MIMI ta tashi zaune.sannu da zuwa momy.wa ya nuna miki gidan nan?ta ce, ga shi nan a falo,tare muke. da sauri MIMI ta sauko daga gadon don tabbatar wa idanunta khalil dinta ne kuwa?sabbin hawaye suka soma zubo mata.ta je ta zauna a kujerar da ke kusa da shi.cikin damuwa ya ce, dubi yadda kika rame,don ALLAH MIMI ki yi hakuri.ga momy na nan na kawo ta za ta yi magana da momy dinku ko dad. MIMI cikin kuka ta ce,ba zai saurare ku ba.don sun yi nisa da shirin aura min abbas.hajiya amina ta dafa bayan MIMI.bayan ta zauna a hannun kujerar da take,sai ta ce,kar ki damu 'yata.yaya za a yi in gan shi?MIMI ta ce bari in gwada kiran sa ko zai daga,don yanzu bai damu da daga kirana ba, Sai a kira na biyu,sannan ya daga me ya faru MIMI? abin da ya soma tambayar ta ke nan,bayan ya daga wayar.ta soma kame-kame am,am da ma wannan ne, baki ne suke son ganin ka. Hajiya amina ta amshi wayar,sannu da kokari alhaji.ya ce,yawwa,wace ce?ta ce,sunana hajiya amina daga kaduna.kuma ni ce mahaifiyar khalil saurayi MIMI,wanda take so. Haushi ya kama alhaji bishir,amma sai ya danne, ya ce,to lafiya?ta ce,na zo ne ina son ganin ka don mu yi magana a kan yaran nan. ya ce,babu bukatar wata magana domin na riga na ba da ta.yanzun haka nan da sati uku ne bikin.don ALLAH ki bawa dan naki hakuri.ta ce,amma alhaji kana sane cewa ba ta so ko?ya ce,ba damuwata ba ne,kuma ke ma ba damuwarki ba ce.ln kin zo nemawa danki aure ne, tuni ya kamata ki yi haka ba yanzu ba.yanzu kam kun makara.na gode.sai an jima.ya kashe wayar.
[01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (9)Ta yi shiru,ta rasa me zata ce wa yaran,ga shi sun tsare ta da idanu.ta ce,ku hakura kawai.tashi khalil mu tafi.MIMI ki bi zabin iyayenki.sai kawai ta ga sun soma kuka su duka biyu.MIMI ta riko hannunta, don ALLAH momy ku gudu da ni.ba zan iya rayuwa babu khalil ba.zan mutu,don ALLAH.momy ta ce,ba zai yiwu ba 'yar nan rufa min asiri. shi ma ya ce,momy don ALLAH mu tafi da ita. uwar ta kalle shi,lallai ba ka da hankali.ta dafa kafadar MIMI,ki yi hakuri 'yata.mu yi addua ALLAH yayi mana zabi na gari.har kasa MIMI ta biyo su da kuka,har gurin motarsu.maaikatan gidan wadanda ba su san me yake faruwa ba,sai kallon MIMI suke yi.sun fi zaton mutuwa ce aka yi gagaruma.fatansu allah ya sa ba maigidan ba ne domin gudun tarwatsewar aikinsu. Na'ima ce ta kama ta suka nufi cikin falon kasa.ta zauna ta ci gaba da kuka, na'ima tana bata hakuri. daidai lokacin lsmail ya shigo falon,don lokacin karatun sa ne da yara.ganin MIMI cikin halin da take ciki, har zai koma sai ya tambayi na'ima,lafiya dai ko?banza ta yi da shi cikin salon wulakanci.ya dan yi jim,can ya ce,baiwar ALLAH kuka bai taba zama mafita ga bawan da musiba ta auka masa ba. ldan kina da bukata zan ba ki maganin damuwa da yaye bakin ciki.kila ma ki cimma burinki.duk ba su tanka shi ba har ya fice. MIMI ta fi saa guda tana kuka har kanta ya soma ciwo.na'ima ta yi lallashi ta gaji,don haka ta kira momy nafisa ta fada mata abin da yake faruwa.momy ta yi ta kiran MIMI bata dauka ba,da yake tana kasa, wayar kuma na sama.sai da ta soma jin jiri.ta mike ta nufi saman.ta jima a kwance kafin ta ji rurinta. cikin sauri ta dauka. tunaninta khalil ne,ashe momy ce.ta dauka, muryarta can kasa,ta ce, momy'momy ta ce,na'ima ta fada min komai.lna so ki kwantar da hankalinki.na fada miki baza ki auri abbas ba.ta soma kuka,kin yi min alkawari momy?ta ce,ko rantsuwa nayi miki,ba zan yi kaffara ba.don haka nayi miki alkawari.lna dai sake fada miki,ki tsaya a kan raayinki.ta ce,shi ke nan momy.
[01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (10)MIMI tana tsaye a windonta na falo,wanda yake kallon boys quaters da kuma lambun gidan. fararen tantabarunta take kallo masu yawa,wadanda dad ya sai mata tun shekaru da dama da ta ce tana so.hamsin ya sai mata, amma yanzu sun fi guda dubu,duk da cin su da suke yi.ta tuna ta yi kwanki rabonta da zuba musu abincinsu.sai masu aiki ke ba su.duk da kayan barci ke jikin ta,haka ta sauka. na'ima tana cewa ina zaki? ta ce,zan duba tantabaruna ne.tunda aka soma matsalolin nan ban je gurin su ba.ta kicin ta bi zuwa barandar baya,inda nan abincinsu yake.ta diba ta watsa musu.duk da ba safiya bace,yanzun lokacin da ta saba watsa musu,sai ta ga suna nan da yawa. har ta yi mamakin hakan, domin da rana suna fita. Kamar an ce waiga,sai ta hango malam lsmail yana shanya a gefensu.da alama ya wanke kananan kayansa na ciki ne.take zantukansa suka fado mata. in kina bukata zan baki maganin yaye damuwa da bakin ciki.kila ma har ki cimma burinki.lna ya san tana da wani buri? kodayake shi malami ne, kuma ta ji ana fadin malamai suna yin magani.ta tuna mina kawarta ta taba ba ta labarin cewa kishiyar mamansu ta yi wa babansu magani,sai abin da ta ce.a fili ta ce,zan nemi taimakon malamin nan, amma ta yaya zan yi masa magana? Da wannan tunanin ta hau samanta.ta jima kafin ta yanke shawarar kiran na'ima.bayan ta daga ne,ta ce,ina son ki je ki amso min lambar malam din nan mai koya mana karatu.na'ima ta dan yatsina,ba ki san ba na son zuwa boys quaters ba sam.bari in tura polina.MIMI ta ce,aa ki sa malam hamisu kawai ya amso miki ki kawo min.ta ce,ok. Na'ima ta amshi wayar MIMI da ke hannunta ta saka mata lambar lsmail,ta yi mata saving da malam.ta mika mata.MIMI ta ce,aje kawai.har na'ima za ta fita, sai kuma ta dawo.sis wai me zaki yi da lambarsa? MIMI ta kalle ta,ki je kawai. kar ki damu sai kin san dalili.tun fitar na'ima,MIMI take tufka da warwara a kan kiran malam lsmail.ln ta kira shi me zata ce masa?kuma yaya ma zai dauki zancen nata.
[01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (11)Kuma yaya ma zai dauki zancen nata? wanan tunanin shi ne ya dauke ta har zuwa karfe takwas din dare,wanda har lokacin ba ta tsai da matsaya ba. Sallamar mahaifinta ne ya zaburar da ita cewa an bude kofar.ta waiwayo,ta dube shi.kwanaki kusan hudu ba ta sa shi a ido ba, domin yana fushi da ita. cikin in-ina ta amsa sallamar, ta dinga kallon sa cike da kewa.ya zauna kusa da ita.cikin sigar lallashi ya ce,uwata ta kaina.ta dube shi,dad na yi kewarka.don ALLAH ka yi hakuri a kan abin da na yi. ya ce,kar ki damu.kina ji na MIMI,ki tashi ki je ga abbas can ya zo don ku tsara irin shagalin bikin da kuke so lokacin bikinku,ku zabi kasashen da za ku tafi shakatawa. MIMI ta yi shiru tana tunani,kamar ta amince,sai kuma ta tuno zance momy nafisa da ta ce duk runtsi ta tsaya a kan raayinta.don haka sai ta ce,dad don ALLAH ka taimake ni. wallahi dad ba na son shi. ya ce,"what?! lna cewa mun gama wannan maganar.ya rike kansa yana tunanin yadda zai bullo mata.can ya saki ya dube ta cikin lalama.MIMI ki yi nazari da kyau.tunda kika fito cikin mahaifiyarki nake dawainiya da ke.na fifita ki cikin 'ya'yana.na yi miki dukkan gata.MIMI zan tambaye ki,na taba neman wani abu gurinki? ta ce,dad,ni ba ni da komai da za ka nema.ni ma da kai nake takama. ya ce,to yau ina neman alfarmarki,ki taimake ni ki min biyayya,ki auri abbas.ta ga kamar zai sauko ya runsuna mata.sai ta yi sauri ta ce,na amince dad.ta soma kuka wi-wi.ya rungume ta.na gode 'yata. ni da ma na san irin son da kike mini ba za ki ba ni kunya ba.daina kuka.ki share hawayenki.ki je ku yi magana.ln kun gama,ni ma ina son mu yi magana da ke.za mu je store din wani abokina ki zabi kalolin gadon da kike so.gidanki dakunan barci shida ne; gaba dayansu zan zuba miki gadaje na alfarma 'yan dubai da chaina da lndiya. zan nuna miki wata mota da na yiwo miki oda.ba ta karaso ba.amma hotonta yana cikin laptop dina don ki yi yawon amarci in kun dawo....
[01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (12)Shakatawa tashi maza ki je kin ji MIMI. MIMI ta mike cikin kasala ta nufi dakinta.mayafi kawai ta dauko,suka jera da mahaifinta har kofar falon baki ya raka ta.sai da ta shiga sannan ya dawo. Ta zauna kujeri biyu tsakaninta da abbas.ya mike ya dawo wadda suke daf da juna ya zauna. sabon kuka ta soma.abbas ya ce,haba MIMI,wai ta ina ALLAH ya rage ni ne da kike ta ki na har haka?ta dago ta dube shi,"Ya rage ka ta soyayyata.abbas don ALLAH ka taimaka min ka rabu da ni.khalil kadai nake so.ya tausasa murya,MIMI ki ba ni dama ni ma in nuna miki kalar tawa soyayyar. na yi miki alkawarin zan koya miki sona har sai kin manta cewa an taba halittar wani da namiji a doran duniya in ba ni ba. Ta ci gaba da kukanta.ya ci gaba da fadin,gobe karfe goma zan zo mu fita.ki fada ma kawarki amina, zan zo da abokaina don mu duba guraren da za mu yi shagalinmu.me da me kike son mu yi?ni dai ina son dinner. Ta ja tsaki,don ALLAH ka bar ni,ka shiga tsakani na da mahaifina.ya ce,kin kasa yi masa biyayya ne MIMI?me zai sa ba zaki yi wa mahaifinki sakayyar son da yayi miki ba?ta mike,zan je in kwanta,kaina ciwo yake.ya ce,ba ki ba ni amsa ba.MIMI ta ce,ba ni da amsar da zan ba ka.amma ka sani in ka matsa cewa sai ka aure ni,nadama da dana sani sune karshen lamarin. shi ma ya mike, ban damu da su ba MIMI, saboda ban taba sanin su ba.kada ki manta gobe karfe goma za mu zo. fatana za mu same ki da kawarki.suka fito a jere.ta ce,ban taba ganin mutum mai son kai irin ka ba.ya ce, ban taba ganin mara tausayi irin ki ba.ko barci fa bana yi.amma ban damu sosai ba,da kin zama a gefena,zan rama duk barcin da na ci bashi.tsaki ta ja,har yanzu ban taba hasashen hakan ba.ko cikin mafarki aurenmu ba zai kasance ba,na yi ma kaina alkawari.daidai lokacin suka iso babba falon,ya runsuna ya yi wa dad bankwana tare da sanar da shi cewa gobe za su fita don duba guraren da ya dace su yi bikinsu.dad ya ce ba damuwa,sai ka zo.ya kalli MIMI wadda ke shirin...
[01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (13)Ya kalli MIMI wadda ke shirin yin samanta ya ce,ki taka masa mana zuwa gurin mota.ba ta yi gardama ba, suka fita. Ya dube ta, nawa kika sa in auren ya kasance?ta ce,in har auren nan ya kasance,na yi maka alkawarin halaka kaina.ya waigo ya dube ta,ni kuma nayi miki alkawarin hana hakan faruwa.sannan zan yi kokarin ganin mun samu 'yan biyu a haihuwarmu ta farko.rasa me za ta ce ta yi,sai ta ja tsaki,ta koma ciki tana jin shi yana cewa,mu kwana lafiya. Dad ya ce,zo uwata zo ki ji.ya bude laptop dinsa ya dinga nuna mata kalolin kayan kicin din da momy nafisa ta siya ta turo masa ya gani.ya ce,suna da kyau, sun yi miki?cikin kosawa ta ce,eh.ya nuna mata motarta.motar ta ja hankalinta don ta shekara mai

1 Comments On CANJIN RAYUWA
avatar
mariya-6-8

11 months ago

Reply

In HAUSA language

Please Login or Register in order to submit comment