Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

muci abinci. Ko kuma ke kici kifinki. Tace kana son jana yawo, ni kuma banason fita. Yace shikenan ba zan matsa miki ba. Tace to bari in shirya muje. Ya ciro wayoyinsa banda wadda ya haska. Kamar ana jira sai ga kira, tamkar kar ya daga, sai kuma ya daga don ya lura da lambar anata kiransa da ita bai ta6a dagawa ba.
7⃣6⃣Kamar yadda ya zata kuwa mace ce, ya amsa suka gaisa. Yanason tuna inda yasan mai muryar.Ta katse masa tunani da cewa, baka ganeni ba ko? Yace cikin qosawa eh. Tace zainabu ce. Sai kuwa Mimi taga ya miqe da sauri tare da fadin zainabu?! Tace eh nice, malam. Zuciyarsa ta shiga bugawa da sauri. Yayi ta maza , yaya gida da mai gida da kuma yara? Tayi 'yar dariya, gida dai lfy mai gida kuwa bama tare. Munfi shekara biyu da rabuwa. Da kuwa qwara daya ne, ya dauki kayansa. Yace, subhanallahi, to Allah yayi miki za6i na alheri. Tace Ameen nagode, na gaisheka. Wannan kuma number ta ce. In ba laifi adan ajeta, don nayi ga kira baka daga ba, qila don bakasan lambar bane. Ban sani ba ko zan kira neman fatawa. Cikin wani shirinka na samu number lokacin daka bada. Yayi 'yar dariya, karki damu zanyi saving dinta, nagode. Kasa kashe wayar yayi, sai itace, ta kashe. Ya zauna bakin gado tare da cewa, auren zainabu ya mutu tun shekara biyu? Kenan ma tun ganin da nayi mata. Yaya tace min tanada aurenta, ashe ba tada shi. Sam ya manta da wata Mimi tana dakin. Ita kam tana zaune hankalinta tashe. Tambayar kanta kawai takeyi wacece kuma Zainabu? Batasan tambayar ta fito fili ba, saida taga ya tsaya cak, daga rawar jikin saving din lambar Zainabu wanda yakeyi. Shi sam ya manta a ina yake ma. Yace, am.. Wata yarinya ce. Ya miqe, ba zaki santa ba. Ya kalleta, ni bari in tafi. Tace zuwa gurin cin abincin fa? Yace mu barshi sai zuwa wani lokaci, zan sha tea in naje gida.
Hankalin Mimi yayi qololuwar tashi, tace, ynxun fa kazo amma har zaka tafi? Yace inada wani uzuri ne, karki damu zan dawo da safe. Bata iya amsa shi ba ya fice. Kai kawo ta dinga yi a dakin. Ta gama yarda cewa tanayi ma ismail wani mugun so, shi yanason wata kenan. Ta fita zuwa dakin yaya Amina ta zauna. Yaya tace yau naga malam ya fita da wuri. Mimi tace, yaya in tambayeki mana? Yaya tace ina jinki. Mimi ta tsura ma yaya ido, wai wacece Zainabu? Yaya tace Zainabu? Kinsan tane? Mimi ta sake tambaya. Tace umm, wata yarinya ce da ismail yayi mata wani mahaukacin So, shine iyayenta suka yaudareshi, suka bada ta ga wani mai kudi. Zufa ta karyo wa Mimi, ta miqe. Yaya tace, yayi miki zancenta ne? Mimi tace kawunsu ummi ne naji suna waya, ta fada masa aurenta ya mutu shine fa ya fita jiki yana 6ari.
7⃣7⃣Yaya Amina ta miqe tsaye tabdi! Ai ko duk nacinsa ba zai aureta ba! Shegiya, ko wa ya bata lambarsa? Tuni nasan aurenta ga mutu, amma na share ban fada masa ba. Saboda kar ya koma mata. Mimi cikin fargaba ta miqe tare da fadin saida safe. Yadda yaya taga hankalin Mimi ya tashi ne ya bata mamaki. Har ta miqe da nufin zuwa ta bawa Mimi shawara, sai kuma ta fasa, tace bari in barta ta fara yin shawara da kanta tukunna. Yarinya kinada miji tun tsawon lokaci, amma me kin dage sai an rabu dake. Daga ganin ta kasan kishi ne can qasan ranga. Ta koma ta zauna. Mimi kuwa tana shiga dakinta ana kawo wuta. Sam bata damu da wutarba, duk da cewa fankar data soma kadawa tana kai mata iska. Sitiri kawai takeyi tsakar daki. Ta rasa wane irin tunani zatayi, ta rasa wa zai bata shawara. Ta zauna bakin gado. Na shiga uku na, ni khadija wa zai bani shawara ynxun? Kalaman yaya Amina ke mata yawo cikin kai, "wata yarinya ce da ismail yayi wa mahaukacin so. Ta maimaita sunan wai Zainabu. Ta tuna yadda ya miqe zumbur lokacin da ta ambaci sunanta. Ta tuna yadda ya manta da ita a dakin sbd zainabu. A fili tace, lallai za'ayi tan kuwa. Wani tuquqi ne ke taso mata daga qirji, tace, qila ma suna can tare. Ranar dai su Mimi ba'a runtsa ba, sannan bata qulla ma kanta mafita ba. Barci sama-sama tayi shi har asubahi. Sai da tayi sallah sannan varci ya dauketa.
Ta kai kusan tara na safe sannan ta farka. Ta fito da nufin gaida yaya, sannan tayi wanka, sai kuma taga yayar sanye da hijabi zata fita. Tace ina kuma zakije yaya? Tace nan maqota zan shiga aikin biki, wannan gidan da sukace muje muga lefe. Kinsan yau ne daurin auren. Mimi tace, wai dole ne jn mutum yananan garin sai ya shiga aiki kenan? Ban saba ganin haka ba. Mu in zamuyi biki, ko suna sai akai gurin yin abincj ayi a kawo. Yaya tace, sha'anin masu kudi kenan. Mu nan in baka zuwa, wa zaizo maka? Bakiga sunan Aishatu ba, gidannan cika yayi? Kinsan dai in bana zuwa ba za'a zomin don tsorona ba. Mimi tace, sai kin dawo. Ni dai bana ra'ayin haka. Tayi 'yar dariya. Aishatu tananan tana varci a uwar daki. Mimi tace to. Ta dauki ruwan wankanta wanda ummi ta zuba mata, kamar kullum tunda bata iya jan ruwa.
7⃣8⃣Tana wanka taji shigowar ismail, yana ta sallama ba a amsa. Tana jinshi yana cewa, inma dai yaya Amina batanan, yasan babu inda Mimi zataje, qila tana bandaki. Saida Mimi ta gama ta fito, sannan ta dauki Hijabin Ummi dake kan igiya ta saka. Ta shiga dakin. Yi tayi tamkar bata ganshi ba. Ta wuce, kan madubi ta zauna tana shafa mai. Ta zame hijabin, ya sauka a wuyanta, dogon gashinta ya bayyana. Ta dauki mataji tana tajeshi. Baqi sidik. Ta lakuto manta na gashi tana kallon gashin cikin madubi. A ranta tana cewa, inda nagode ma Allah, duk lalacewar da nayi gashina bai zube ba. Ta kalli fuskarta a madubin, tace wai wane irin kyau mutuminnan yake buqata wanda yafi nawa? Sai dai ko in balarabiya yake son ya aura. A fili tace, zan so ni kuwa inga zainabun nan wace iri ce ita? Kyanta yaya yake? Yace me kk ce? Cikin sauri ta waiwaya, ta dubesbi. Yace yau 'yan miskilancin ne ko? Kin shigo kinyi kamar baki ganni ba. Shiru tayi, sam ta manta yana dakin, tayi zancen zucinta a fili, fatanta Allah yasa baiji taba. Tace kaji abinda nace ne? Yace a'a me kk ce? Ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta maida hankali gurin abinda takeyi. Yace, ki fada min me kk ce mana? Sai naji kamar dai kin ambaci zainabu. Ta danyi dim, sannan tace, wai kai ka damu da wata zainabu, tunda ta kiraka jiya, ka fita hankalinka, harma takai ynxun kunnenka yanayi maka gizo ko? Magana mutane sukayi, sai ka zata sunce zainabu ko? Yace ni bance ba ranki ya dade. Ta zauna tana shafa hoda. Ta gama, taja durowar madubi, ta ciro abin daure gashin ta kamashi a tsakiya. Ta fesa turare sanna ta ciro daguwar rigarta leshi ta saka. Ba tare da ta daura dankwali ba ta nufi kicin. Shi dai yana binta da kallo. Tayi masa kyau a idanunsa. Ta dauko biredinta da ruwan shayi mara madara ta zauna, amma sai damuwa ta hanata cin biredin, sai ruwan shayin take kur6a. Yace nima zansha. Ta miqa masa na hannunta, kar6a. Yace, ki hadamin wani mana. Ta kalleshi, munin nawa har ya kai cikin kofin shayin ne, shiyasa ba zaka iya sha ba? Yace bance ba naga kamar baki qoshi bane, tunda ko biredin bakici ba. Ta daure fuska, nina qoshi. Yace shikenan bani. Ta miqa masa. Kan gado ta koma ta kwanta, fuskarta tana kallon gefe, tana tunanin nafita. Ya kalleta, baisan me take yiwa fushi ba. Sai ya samu kansa da shiga damuwa.
[26/09 9:16 am] Inna👬👫: Canjin rayuwa

7⃣9⃣Yace ki tashi khadija, magana zamuyi, duk da naga yau kina fushi dani.Ta tashi amma taqi kallonsa, kanta yana qasa, tana wasa da yatsun hannunta, fuskarta a daure tam. Yace, to inason zan tare a gidana. Kina ganin ya kamata mu koma tare ne ko kuwa zaki zauna anan? Mimi tayi shiru cikin nazari, sai taga ya kamata ta gwadashi. Tace, kai me ka gani yafi? Ni ko ina daya ne a gurina. Ya dago yana kallonta cikin ido, sannan yace, banason in takura miki ne, kamar yadda nayi fa fada miki a tun baya. Abin da kikeso shi zan miki. Ta tura baki cikin jin haushi tace ni banida za6i. Ranshi ya sosu, cikin fushi ya miqe, shikenan, ni zan tafi. Duk lokacin da kk za6a, saiki fada min. Ni dai zan tare, kuma zanyi aure. Batasan lokacin da ta miqe tsaye a tsakiyar gadonba. Me kk fada? Yace nasan kinji. Tace ka auri dubu, amma kafin nan ka warware nawa auren dake kanka. Yace, nufina kenan don nasan bakida burin daya wuce wannan. Amma sai kina ta shirmenki.
A sanyaye tace, dama kazo ka sakeni ne? Kafin ya amsa, qaramar wayarsa ta soma ruri. Ya daga ya fita a dakin yana amsawa. Mimi ta zauna tasa kanta cikin gwiwarta tana kuka. Batasan dalilin kukan ba bare asalinsa. Wata zuciyar ta ingizo ta tare da rada mata cewa, tayi tafiyarta. Ta sauka ta dauko akwatunanta, ta dauki daya, ta soma kwaso kayanta tana zubawa a ciki. Shikuwa yana gama waya ya dawo, da bango ya jingina yana kallonta. Bai hanata ba kuma bai tambayeta dalili ba, har ta gama ta dauki mayafinta tasa takalmi, sannan taja jakar, dariya ce taso ta su6uce masa, amma sai ya fasa. Ya tare qofar dakin. Tace, ka bani hanya zan wuce! Yace zuwa ina? Tace ina ruwanka dani? In tafi ko ina ma, mun hada zuri'a ne? Kawai ynxun ka bani saki na. Kai ko baka sakeni ba ma tafiya zanyi. Ya girgiza kai, bamu bada zuri'a ba, sai dai bansan gaba ba. Amma ynxun kafin ki tafi tsaya mu gama magana, in yasa sai ki tafi, ba zan hanaki ba. Ya nuna mata bakin gado, ki zauna anan! Fuskarta a daure ta zauna. Shima ya zauna.
[26/09 4:09 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa

8⃣0⃣Fadamin mecece damuwarki wadda tasa har zaki tafi ki barmu? Shiru tayi, domin ta rasa me zata ce. In zata fadi gsky, to kishi ne kawai ke cinye ta a zuciya. Amma sai tace, na gaji da kushe ni da kkyi. Duk lokacin da ka tashi, sai kace min mummuna. Sannan kaqi ka cika min alqawari na. Yayi murmushi, ni ban ta6a ce miki mummuna ba. Ta kalleshi, ba girmanka bane yin qarya. Domin kune masu fadin illarta. Jiyan nan kace min ko yaushe ina canzawa. Yace, canzawa nace ko muni nace? Tayi shiru. yace, banda jiya sai kuma yaushe nace miki? Cikin qarfin gwiwa tace, da muke asibiti, lokacin da nace, bana sonka me kacemin? Inka manta in tuna maka. Cewa fa kayi kaima kafison mace mai kyau. Ya sake yin wani murmushin, tabbas nace haka, amma nace bakida kyau? Tace kusan haka ne? Yace ba dai hakan bane tunda kusan ne. To naji wannan sai kuma batun alqawari, duk alqawurran dana daukar miki a gaban Doctor salis wanne ne ban cika ba? Tayi shiru, tabbas yace zai nesanta ta da iyayenta kuma yayi. Yace zai kula da ita daidai qarfinsa, kuma yayi, in zata duba tsawon lokacin da ta dauka tana jinya, sun yi ta dawainiya da ita. Ta dubeshi, sai na rabuwa, shine baka cika ba. Yace banda shi na cika sauran? Ta daga kai, alamun eh. Yace to bari in tuna miki. Kinsan na jima ina yi miki alqawarin cewa zan yi miki fiye da kk taso anayi miki na gata ko? Tayi shiru tana kallonsa. Ya tausasa murya, inason ki jira ni in cika wannan alqawarin, ko zamu rabu, ki bari in gama yi miki gatan dana tsara ma kaina, inji dake wani irin dadin da baki sanshi ba. In yasa nan, sai inyi miki abinda kk so. Tayi wani dan tunani. Sannan tace, zan yarda ne kawai in kaima ka yarda da abinda zan fada ynxun. Yace inajinki. tace zaka daura aure ne lokacin da ka warware nawa auren. Yace ban fahimta ba? Tace, ina nufin ba zaka ki aure ba, sai lokacin daka warware nawa auren. Yayi shiru don shi tun jiya ya gama tsarinsa. Ya tsara zai auri zainabu don ya gaji da zama haka, ita kuma lokacin data gama shirmenta sai su shirya don babu saki acikin zuciyarsa a ynxun. Daga nan sai ya kaita gaban iyayenta ta nemi gafararsu, duk da Hajiya tace zasu nemeshi in lokaci yayi. Amma dubi yadda ita kuma ta 6ullo masa da wata magana.
8⃣1⃣Ta katse masa tunani da cewa, kayi shiru? Yace, kina ganin zamana babu aure ba ragewar mutunci na bane a matsayina na mai fadakarwa? Ta miqe tsaye, tayi dan taku daya zuwa uku, sannan ta kalleshi, ni da kaine kawai muka san cewa ba kada mata, amma Duniya ta jima da sanin cewa kanada aure. Yace naji saidai karki manta ni fa mutum ne, kuma ba yaro ba, wanda yakai. Kinsan dole ina buqatar abokiyar halittata. Kinsan shekaruna nawa ynxun? Tace ban sani ba, qila zaka gota talatin. Yace yauwa, to in na rantse miki ba zanyi kaffara ba, a takure nake, sannan inason yara. Ynzun dubi mahmud, matarsa tanada ciki na biyu. Ya numfasa, khadija saka idonki cikin nawa, ta kalleshi. Yace ina buqatar abokiyar rayuwa. Ta sunkuyar da kai, wannan ai zancenka ne da kuma wadda zaka aura. Kukan Aishatu ta jiyo, ta miqe da sauri, har tana tuntu6e da qafarsa zata fadi. Ya sa hannuwansa ya tare ta. Sai tsintar kanta tayi a jikinsa.Duk zun jisu cikin wani yanayi. Shine yayi ta maza. Yace ina zakije haka? Kike sauri zaki fadi kije ki karye, dama gaki nan kamar 'yar tsinke. Ta tashi da sauri, bakaji kukan Aishatu ba? Da sauri ta nufi gurin Aishatu. Ta shigo riqe da hannunta, sai lallashinta takeyi. "Yarinya tana kuka kin firgice, ranar da kk haifi naki, sai yaya? Ta harareshi cikin wasa, me zai hadani da haihuwa? Yayi qasa da murya, "wai ba kyajin komai game dani? Tace Aishatu dai tana kallonka. Ya miqe, bari dai in gafi tunda kin fasa yajin. In yaya ta dawo ki fada mata cewa nazo, kuma batun tarewa ya kawoni. Ynxu zance in samu mahmud ne muje kasuwa mj sayi abinda ya sauwaqa, mu zuba a gidan, to shikenan.
8⃣2⃣A zaure zuka hadu da yaya. Nan suka gaisa yayi mata bayanin dalilin zuwansa har yadda sukayi da mimi. Dariya yaya tayi, domin ta gama gano mimi tsabar son mijinta takeyi, amma sai bata nuna ma Ismail din ba. Tace khadija kenan 'yar daru, 'yar shagwa6a. Zamuyi magana da ita. Amma ni shawarata karka tsaya bata wani za6in ko nan ko can. Kawai kace mata ku koma, ko don sbd kauda hankalin mazu zaton bakada aure. Yace nima haka nekeso, amma kinsan rigimarta. Gashi zai da'awar in saketa takeyi. Ni kuma gsky sai inga in nayi haka ban kyauta wa mahaifiyarta ba. Yaya tace wannan ma bata taso ba. Kudai koma din, qila ma ku sasanta. Ismail yace, Allah yayi mana jagora. Yaya tace Ameen. Sukayj sallama tayi ciki shi kuma yayi waje. Kafin sati daya, ismail ya sayi abinda ya sauwaqa, sun kai sjn shisshirya. Sannan sun shirya walima, inda su yaya da maqotanta sukayi musu girki, shinkafa ce da waina, sai kaji. Girkin yayi kyau sosai, ga kuma abin sha. Bayan sun tashi daga walimar ne, sannan sukazo suka kwashe kayan sawar mimi, shi da mahmud. Kayan Gado dai tabarma su Ummi. Duk da haka basu koma ba, sbd ismail zasuje kaduna da kuma Abuja, don gabatar da wasu muhadarori, da kuma lakcoci. Haka kuma suna durowa katsina, ya tarar da takardar gayyata daga gwamnatin jihar katsina. A hannun Malam Aminu ya samu saqon. Yace wannan taro ne na manyan malamai, to ni meya kaini gurin? Malam yace daukaka ce daga Allah, ismail. Shawarar da zan baka kayi taka tsan tsan, domin Malamai ma wasu basa tsoron Allab, musamman in sunga Allah ya baka nasibi. Sannan kar kayi sanyi gurin fadar gsky, komai dacinta. Ismail yace shikenan zan kula insha Allah, nagode. Gidasa ya wuce, sai da yayi wanka ya huta, sannan ya fita zuwa gidan yaya Amina. Yayi matuqar qosawa Mimi ta dawo, ko don Abinci. Gashi a gida mai kyau, amma abinci sai ya siya. Can yaci abinci, sannan yace, yaushe zaku raka mimi can gidan? Tace sai jibi.
[26/09 10:32 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa

Washegari ya samu halartar gayyatar da akai masu. Maqasudin zaman dai, sbd tafsir ne na Azumin dake gabatowa. An yi musu jan hankalin hadin kai, su daina zagin juna, da kafirta juna. Sannan kowa yayi wa'azinsa ba tare da izgilanci ba, ko cin mutunci. Ka abinda Allah da manzan sa sukace, a tsage gsky komai dacinta. Malamai sunyi bayani, inda shima ismail yayi nasa bayanin, wanda ya gamsar da dukkan mahalarta taron. Sbd ismail, Allah ya hore masa hikimar iya magana. Shi mutum ne wanda zaiyi wahala yayi maka bayani baka gamsu ba.
Bayan an fito ne, ismail ya miqa hanya da nufin neman dan aca6an da zai kaishi gida, sa6anin sauran malaman da suka zo da motocinsu. Wannan dalilin shine ya kawo inda aka bincika cikin malaman da suka halarci taro, aka fidda guda hudu wadanda basuda abin hawa. Washegari saiga mota sabuwa dal, babu ko lamba an kawowa ismail. Lokacin da Malam Aminu ya kirashi yazo, shiru yayi ya kasa magana, lokacin daya gabatar masa da motar. Bai san da wace kalma zai fara magana ba, duk wani alheri da zaizo masa ta gurin Malam Aminu yake tahowa. Yace Malam, Allah ya saka maka da aljanna. Sunyi ta murna. Ya kira mahmud. Dama mahmud ya iya mota. Nan suka shiga suka zagaya gari, tare da zuwa gurin abokan arziki. Sunje gidansu, inda 'yan gidan suka fito suka ga mota sunata murna. Ta fito wanka , tana shafa, ummi ta shigo da gudu. "Aunty zo kiga motar kawunmu, sabuwa dal, baqa kuma qatuwa. Mimi tayi dariya sbd yadda Ummi ta jero maganar, tare da cewa, Allah yasa alheri. Sai gashi da kansa, khadija kizo ki gani mana, munyi mota. Mimi ta miqe taje taga mota, kuma tayi murna. Yace ki shiga mana ko kin manta da yadda akeyin tuqi? Murmushi tayi, sannan ta amshi makulli, su Ummi suka shiga, ta tashi motar ta tuqa zuwa cikin layi, suka dawo. Ummi sai mamaki takeyi, tana cewa, anty yaushe kk koyi tuqa mota? Ismail ma cewa yayi ashe baki manta tuqin ba. Tace in manta tuqi? Ashe zan manta da yadda zanyi tafiya da qafata. Suka sa dariya.
8⃣3⃣Washegari Ismail da mahmud suka soma fita don koyo ma ismail tuqi. A yammacin ranar ismail, ya kira yaya Amina yace, su shirya zasuyi tasu walimar a gidansa. Bayan la'asar suka zo kwashi su yaya Amina, suka biya suka dauko Rabi'a da innarsu mahmud. Bayan sun kaisu ne, sai suka koma suka dauko su inna, dasu fatu. Dukda ba wani alatu. Ismail ya zuba a gidanba, gidan yayi kyau sosai. Katifu ne a dakunan da sabbin zannuwan gado da fuloli, sai labulaye masu tsada. Sai falon ne ma ya gyarashi sosai, don tsadaddun kujeru ya zuba da kafet din tsakiyar, shi ma mai tsada ne, TV da sauran kayan kallon zamani. Sai dai falon saman bai saka komai ba. Yace sai ahankali zai saka komai. Mimi taga qorarinsa sosai, tunda tasan shi talaka ne. Sun je sun kawo musu abin sha na gora. Daf da magriba suka koma kai su innarsa, sannan su yaya Amina. Mimi harda kuka wai abar mata Ummi. Yaya tace a'a za dai tazo miki hutu, kuma kinsan zata tayani aiki, ga makaranta. Mimi tace yaya baga saddam ba. Kuma indai makaranta ce ai zan kaita tunda ga mota a hannun kawunsu. Tace kiyi haquri har suyi hutu. Ismail dake kallonta burgeshi takeyi, don yanason shagwa6arnan tata. Shiyasa ma yaqi sa musu baki, don yanason kallonta a haka. Ita kuwa yaya Amina, taqi barin Ummi ne don zamansu, su biyun wata hikima ce, tana sa ran su shirya kansu. Sun barta da Rabi'a in sun dawo kaisu yaya, sai mahmud ya tafi da matarsa. Bayan tafiyar su ne, sai kuma suka shiga kicin don ganinsa. Freezer ce, sai tukwane da kuloli, plates da cokula, amma babu risho ko wani gas. Rabi'a tayi dariya, tace to da me zakuyi girki? Mimi tace oho masa. Suka koma sama sukayi sallah, sannan suka dawo qasa suna 'yar hira.
8⃣4⃣Ranar Mimi harta dan saki jiki da Rabi'a, don ta lura Rabi'ar ta san me takeyi. Rabi'a tace, niko da ace zaki yarda da na baki shawara. Mimi tace, me zai hana? Rabi'a tace kar kibar wata mace ta shigo gidannan a matsayin matar malam ismail. Mimi ta tattaro hankalinta gurin Rabi'a. Ta yaya zanyi hakan? Nasan dai kinsan komai dake tsakaninmu da malam din, tunda Aminin mijinki ne. Bafa son juna mukeyi ba. Rabi'a tace ni kuwa sai ina kallon so acan cikin qwayar idanunku. Na farko da baya sonki, da tuni ya sakeki. Rashin sakin jikinki shine ya hanashi nuna miki. Mimi tayi murmushi, ya fada miki ne? Rabi'a tace a'a nice nayi hasashen hakan. Mimi tace bana zaton zai soni, sbd na samu labarin yadda yakeson wata Zainabu. Rabi'a tace, tabbas yanason zainabu, amma da kinso, da tuni kin mantar dashi ita. Kiyi tunani. Mimi ta sauke ajiyar zuciya, ni damuwa ta ma ko auren namu yananan daram ko ya lalace? Oho. Kafin Rabi'a tayi magana, sai gasu sunyi sallama. Don haka, sai suka rufe bakin hirar. Tare suka tafi dukkansu, aka kulle gidan. Mahmud ne ya jasu zuwa gidansu. Sun danyi hira, sannan Mimi ta jawosu zuwa gida. Ismail yaji dadin yadda Mimi ta saki jiki da Rabi'a. Bayan tayi wanka tayi isha'i, ta saka kayan varci, ya buga qofarta, taja hijabi ta saka, sannan tace, shigo mana. Bakin katifa ya zauna, sannan yace kinga dan kayan dake kicin din ko? Sai a hankali zamu qara abinda bamuda shi. Tace maimakon kabar wani abin ka siyo gas ko risho, to dame zamuyi girkin? Ya zaro idanu, alamun sam ya manta da Risho. Sannan yayi dariya, lallai yau akeyinta. Sam na manta fa. Kinsan abubuwan da yawa, gashi ba wai inada kudin bane. Amma karki damu zuwa gobe ko risho dinne, sai in samo. Gas daga baya zamu samu. Ina son ma ki zauna ki rubuta abinda muka fi buqata, sai muyi ta siya a hankali. Ki fara da wanda muka fi buqata. Tace mu bari saida safe. Yace rubuta dai ynxun. Ta dauko takarda da biro, shi kenan dame zamu fara? Yace kayan gado, sai falon sama, abubuwan cikin ban daki, sai me? Tayi dariya sannan ta soma tuno wasu tana fada, suna rubutawa. Sun kai kusan sha daya, kafin yace mata bari ya tafi saida safe.
[27/09 7:59 am] Inna👬👫: Canjin rayuwa

8⃣5⃣Ya jima kafin yayi varci, sbd gsky haqurinsa zai gaza. Ko da bayason Mimi, to yasan yana muradinta a gefensa. Ballantana yana da tabbacin cewa wani sashe na zuciyarsa yanason Mimi. Duk lokacinda yazo da niyyar sanar da ita hakan, sauta 6ullo masa da zancen saki, sai dai wasu abubuwan da takeyi, sai yana zargin cewa tana sonshi. Washegari da safe, yana zaune a falon qasa, yana duba wani littafi, ta sauko tayi wanka tasa daguwar riga ruwan qasa, mara nauyi, bata daura dankwali ba, ta kama gashin kanta a gefe. Tunda ta nufo shi ya kasa daina kallonta har tazo ta zauna akan kafet kusa dashi. Tace ina kwana? Yayi murmushi, "lafiya lau" kefa kina lfy? Tayi

1 Comments On CANJIN RAYUWA
avatar
mariya-6-8

11 months ago

Reply

In HAUSA language

Please Login or Register in order to submit comment