Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dan fari da ido " qalau" ta gyara zama tace ynxun yaya zamuyi, tunda bamuda abinda zamu hura wuta? Yayi murmushi. Fita zanyi in siyo mana abinda zamuci. Tace a'a kawai muje gdn yaya Amina muci. Yace kinsan yau dai ba zasuyi damu ba, amma bana siyo butar dafa ruwan zafi ba? Tace haba? Ni banganta ba. Ta miqe zamu dafa ruwan tea. Yace muje in gani, amma tabbas na siyo Butar ruwan zafi. Sun dafa ruwan zafinsu, suna sha, suna labari kadan-kadan. Daga bisani yayi wanka ya fita.
[27/09 3:47 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa

8⃣6⃣Ranar da suka cika kwana uku, Ismail yaji haqurinsa zai kasa. Don haka yaga babu abinda yafi illa ya ziyarci zainabu. Koda ya shawarci mahmud sai yace masa kar ya soma, ya dai yi qoqari ya sasanta da matarsa. Sam ismail zancen bai shigeshi ba, domin yasan tun filazal ba sonshi da Zainabun sukeyi ba. Don haka ya yanke shawarar kiranta a waya don ya fada mata cewa zai kawo mata ziyara. Misalin qarfe hudu bayan sun fito la'asar ya ciro wayarsa ya soma neman lambar zainabu. Koda yazo kan lambar saida yadan jima yana tunani kafin ya danna kira ya tafi, lokacin zainabu tana kwance a qofar dakin innarta tana buga game din maciji, sai kawai taga kira ya shigo. Ganin sunan dake rawa akan fuskar wayar, saita zaro ido tare da murza idon, sannan ta dauka cikin sauri tare dayin sallama. Sun gaisa sannan yana ganin saqonta na gaisuwar juma'a kuma yana godia, tace ashe kana gani, nayi zaton ma baka gani tunda kuna hulda da jama'a sosai. Yace ina gani, ko zan sameki anjima? Cikin sauri tace, inanan Malam. Yace, qila in shigo anjima. Tace to Malam, Allah ya kawoka. Duk mahmud yana jinshi.Misalin takwas da mintuna mimi tana daki tana danna wayarta, so take ta tsokani ismail tana kiranshi amma yaqi dagawa, sai kawai Mimi taga ya fito cikin shadda wagambari sai maiqo takeyi. Mai kalar blue, haka hularsa. Ta wundo ta hangoshi. Cikin sauri ta 6oye wayar sannan ta fito, ina kuma zakaje da darennan? Yace wata 'yar unguwa zanje bazan jima ba. Tace inzo in raka ka? Ta fadi haka ne don ranta ya raya mata ko gurin wata zashi. Yace a'a ki barshi ba ni kadai bane nida mahmud ne. Tace kasan dai inajin tsoro, don Allah karka zauna. Yace ynxun zan dawo. Tace amma bada mota zakaje ba? Yace da ita zanje mana. Nifa na tuqo motar daga unguwar su mahmud dazu, bare ynxun da babu cunkoso. Ta windon su na sama take leqensa ya fita da motar, sannan ya dawo ya rufe gidan, ta saki labule, ta koma ta zauna tana ta karanta wasiqar jaki. Yana isa gidansu zainabu, ya kira ta cikin waya ya fada mata ya iso. Cikin soron gidansu suka zauna. Sun gaisa sannan ismail yace, gani nazo a karo na biyu, banda zuciya ko? Cikin sauri tace, malam kayi haquri, ko da ba laifina bane. Wlh ina sonka, shine ma dalilin da ban iya zama gidan Alhaji ba. Yayi murmushi, to ina fatan ba zan sake samun matsala ba, don wannan karon banason aja lokaci. Tace ni ko gobe ka turo, don dama zaman jiranka nikeyi. 'yar dariya yayi, sannan yace shikenan ko ban sake zuwa akan lokaci ba zamu dinga waya.
8⃣7⃣Wasegari ya samu gayyata daga abuja, jami'ar da ya nemi koyarwa. Yaje kuma sun daukeshi, yayi murna sosai. Haka ma dangi sunyi murna, illa mimi kadai da take ganin cewa za suyi nisa da juna. Yayi mata tayin ziuwa abuja tace, ko sha'awar zuwa bataso. Yace, nasan ba zaki iya zama ke daya ba, yaya kk son ayi? Tace zan koma gidan su yaya Amina, in ka dawo sai in dawo. Da kanta tace, ya sakata islamiyya a unguwar su yaya. Sam in kaga Mimi ba zakace ita bace. Sbd dogon hijabi da niqabi. Lecturing daya soma sai ya dauke hankalinsa daga kan batun auren daya so yi cikin gaggawa. Amma dai suna waya da zainabu. Duk sati yake zuwa, wani lokacin sati biyu. Shi mahmud ABU zaria ya samu. Ismai ya kira masu aiki sun duba filin dake gidansa sun tabbatar masa zai iya yin makaranta harda madaidaicin masallaci. Bayan sun bashi tsarin ginin, sai ya soma tunanin yadda zai samu kudin ginin don kudin da aka qiyasta makarantar zataci ba qanana bane. Harkoki sun bude ma ismail, ga alherai da yake ta samu daga jama'a, domin ranar da akayi wata hira dashi a gidan TV na Africa, lokacin gidan TVn yana sabon budewa, har ya sako bayani akan makarantar da yakeson ginawa, ko sati ba'ayi ba, saiga shi mutane sun fara kiransa don son bashi gudunmuwa. Kafin wani lokaci tuni an soma gini. Babban qalubalenshi mata. Ko a makaranta, mata ne keta kawo mashi hari. To don yana malami, shi kam ba waliyyi bane, da yawa ana jarabtar Malamai da son mata da kuma kudi, in bakayi taka tsantsan ba, sai ka fada halaka. Shi yasa ya gama yanke hukunci. Yana samun hutun qarshen zango yazo, to kuwa aure zaiyi, ko ma da wacece. Wata asabar ya dauki takardar da Mimi ta rubuta duk abinda suke buqata, ya shiga kasuwa, sai da yayi rabi, tun daga kan gado zuwa saurensu. Dakin mimi kuwa saida ya tsara mata shi fiye da nasa, sannan yayi mata sayayyar kayan sawa, sannan ga sabuwar waya da kuma layi, tsohon nasa ne ma ya bata. Don har ynxun baisan tanada waya ba.zainabu ma yayi mata 'yar sayayya.
Bayan sunyi hutu, dukda cewa sati biyu ne hutun nasu, amma cikin sati biyun zai yaye ma kansa damuwa. Shiyasa ma washegari da safe yana zaune falon qasa yanashan tea, saida yaga itama tazo ta zauna , sai ya dauki wayarshi yana kiran layin zainabu, da farko hankalinta baya kansa, saida taji yace zainabu, cak ta tsaya ta kada hadiye tea din data kur6a. Yaci gaba ina gari zan shigo anjima yaudai zamu gama magana. Inason kafin hutunnan ya qare zaki zama a gidana. Cikin murna take fadin sai kazo. Yana kashe waya mimi ta maida tea din dake bakinta cikin kofin, sannan cikin wata irin murya tace magana zaku gama? Ya dubeta fuska daure, "khadija aure zanyi" ji tayi tamkar ya soki zuciyarta da qaho. A hankali ta jingina da kujera, sannan ta lumshe ido, ta rasa me ma zatace. Sai kawai ta tashi ta nufi dakinta. Bakin gado ta zauna, rashin wanda zai baka shawara matsalane. Tasan tunda yace mata aure zaiyi, to kuwa yana nufin rabuwarsu tazo kenan. Wata zuciyar tace, lokaci yayi da zaki koma gidan iyayenki. A fili tace, kai da saura. Haka zan koma musu bayan shekara uku, babu wani ci gaba, ba kuma auren da suka daura min, bayan tsohon laifina na baya? Ta girgiza kai, lokaci baiyi ba. Mafita ya kamata in nema. Ya turo qofarta ya shigo. Jikin sif dinta ya jingina. Khadija ban zaci zakiyi fushi ba, Nafi zaton zakiyi murna, don lokaci yayi da zan warware aurenmu.
[27/09 3:48 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa

8⃣8⃣Ta daga masa hannu. Don Allah ka fita! Inason inyi tunani. Yace inace kin gama tunani daga yau? Ta miqe, ta ra6a ta gefensa ta fita, qasa ta koma ta kwanta kan doguwar kujera. Murmushi yayi, sannan ya shiga dakinsa. Wayarshi ta gani da sauri ta dauka ta shiga kicin. Bata sha wahala gurin ganin sunan zainabu ba. Ta dauki lambarta. Sannan ta dawo da wayr inda ta dauka. Bayan ta shiga dakinta ma harda shiga bandaki. Layin zainabu ta kira, bayan ta daga mimi ta soma magana da kakkausar murya, "kece zainabu?" tace eh nice. Dama na kiraki ne in fada miki cewa ki fita harkar mijina, in har kinason zaman lfy. Zainabu tace wai waye mijin naki? Mimi taja tsaki, "kinsanshi tunda har kina shirin aurensa. Zainabu tace, oh wai kina nufin malam? In shine sai ince kinyi kuskure. Domin aurensa shine abinda nake buri koda zaki zama ajalina. Ki sani kafin ya soki, ni ya soma so. Kuma ina sonshi, aure babu fashi! Mimi tace, mu zuba! Ni dake zanga wanda keda nasara! Ta kashe wayar, sannan ta fito daga ban dakin, ta jefa wayarta akan gado. Ta shiga yin kai kawo a tsakar dakin. A fili take fadin, wai meyasa ni bana burgeshi ne? Dame zainabu ta fini ne? Ta janyo hijabinta da niqabi ta saka, sannan taja durowa ta dauki kudi ta nufi qasa. Bata zaci yana qasan ba. Saida taji yace, ina zaki? Ba tare da ta tsaya ba, tace gidan yana Amina. Ya daga murya. Ba zaki je ba. Ga waiwaya ta dubeshi, fuskarsa murtuk, sama ta koma fuuuu. A zuciyarta da qudirin cewa shima kuwa sai tayi masa abinda ba zai fita anjima ba. Haka suka yini kowanne zuciya babu dadi. Da dare tanata fakonsa , ya shiga dakinsa yana tashi, sai kuwa ta sauka qasa , ta dauke masa makullin mota, ga jefa qasan kujera. Sannan ta kulle qofar falon ta saka makullin cikin rigar mamanta, sannan ta koma dakinta. Tana kwance, rigingine kusan minti shabiyar, sai kurum taji turo qofarsa. Tashin da tayi da sauri shine ya kawo har yaji qaran makullin. Yace bani makullin mota dana qofar fita. Tace ajiya ka bani? Inama zakaje? Ni gsky tsoro nakeji, ba zaka fita ba. Yace, tadi zanje ki bani, karki 6atamin lokaci. Cikin 6acin rai tace, nifa bazan zauna ni daya ba. Yace to kizo muje tare. Da qarfi tace, Allah ya tsare ni.
8⃣9⃣Har inda take ya tako, daf da ita ya tsaya, ya sa hannu ya dafa kafadarta, girgiza ta yayi don yaji daga ina yaji qaran makullin. Amma sai baiji qaranba, sbd sun samu mazauni mai kyau a tsakiyar qirjinta, makari guda biyu sun taresu. Sai ya soma yi mata wani irin lalube tun daga qugunta yake shafawa da hannuwa guda biyu gaba da baya. Hakan ya kashe mata jiki, har ya tilasta mata lumshe ido, daga ita harshi. Haka nan yanajin makullin, sai ya zura hannunsa ta saman rigarta don ciro makullin. Ya ciro, amma yanayinsa gaba daya ya raunana, kamar yadda itama ta sukurkuce. Ta bude idanu ta kalleshi, shima fuskarta yake kallo. Cikin ido suka kalli juna, sannan a hankali yace, saina dawo. Ta fahimci muryarsa ta canza. Kan gado ta fada ta soma kuka. Kusan minti biyar ta tashi ta rufe qofarta. Shi kansa baisan meya hanashi yin wani zance mai muhimmanci ba, aun daiyi 'yar hira yace, zai dawo kan batun aurensu, yana sauri ne don matarsa ba tada lfy. Ta so ta fada masa kiran da matar tasa tayi mata, sai kuma ta fasa. Lokacin da ya dawo, ya hau sama, kai tsaye qofar Mimi ya murda, amma sai ya jita gam. Don haka sai ya wuce zuwa nasa dakin, bayan yayi duk abubuwan da yakanyi kafin ya kwanta, sai ya kwanta. Juyi kurum yakeyi tare da tuno yadda ya caje matar tasa. Ya gama yarda itama ko bata sonshi, to kuwa tana buqatarsa, don ya lura da halin data shiga a lokacin. Yanke shawara yayi ya tuntu6eta da batun, amma sai ta huce daga wanna fushin da tayi. Da asubahi, kamar kullum saida ya qwanqwasa mata qofa kafin ya wuce masallaci. Ita kam tuni idanunta biyu, domin dai yau duk satar varci, saida yayi mata haquri. Ta amince, baya sonta tunda har ta zubarda kimarta ta 6oye makulli, amma saida ya dauka kuma ya tafi. Zucigarta dai tanata bata shawara akan ta fito fili ta fada masa abinda ke ranta. Sai dai ita tsoronta kar sai yaji sirrin zuciyarta, sannan yace, ba irinta yakeso ba, kamar yadda yayi ta fadi a baya. Takaici ne ya hanata fitowa daga daki. Koda gari ya waye, shi kuwa shareta yayi, har ya gama komai ya fita, sai dai alamu sun nuna bata bude qofar ba, har ynxun qarfe hudun yamma. Yaje ya daga labulen windonta, tana kwance akan sallaya, da alamu tayi la'asar ne. Yace khadija, ki tashi ki bude qofa mana! Tana jinsa tayi shiru, daman so takeyi ya lallasheta, amma ko zata bude ba ynxu ba. Yace kinci wani abu ne? Bata tanka ba. Ya sauka qasa. Baisan me yarinyarnan keso dashi ba. Yau duk ta hana rayuwarsa sukuni, don koda ya fita, hankalinsa yana gida. Baisan mimi da gske takeyi ba saida yaga anyi sallar isha'i ya dawo bata fito ba. Da ya leqa ya ganta kwance rub da ciki akan gado.
[27/09 9:54 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa

9⃣0⃣Yace kadija ki dubi girman Allah ki bude, muyi magana. Nifa bansan dalilinki ba. Hava khadija ya kk so inyi da rayuwa ta. Ganin bata tanka shi ba, sai ya yanke shawarar kiran mahmud. Kafin isowar mahmud din, ismail yaci gaba da lallashinta, amma ko motsi batayi ba. Bataji takun shigowar mahmud ba, sai dai muryarsa taji yana cewa, don Allah khadija ki bude qofar nan, muyi magana. Don Allah zaki bude ba don ni ba. Kuma ina bayanki akan kowane dalili ne yasa kika rufe qofar. Sunfi minti biyar kafin ta taso ta bude, tana layi. Cikin hanzari ismail ya shiga ya kama hannunta. Dukda qaton hijabin sallar data saka ya hada, ya dauke ta zuwa falon qasa. Yunwa da damuwa sun hadu sun ramar da ita. Ya zaunar da ita akan kujera. Yace haba khadija kowane irin laifi nayi miki, ya dace ki yanke ma kanki irin wannan hukuncin? Cikin raunanniyar murya tace, ku barni don Allah. Mahmud yace, ka kawo mata ruwan zafi, tunda bataci komai ba, hanjinta zai warware. Ya nufi kicin ya hado mata ruwan zafi. Saida yayi ta lallashinta, sannan ta amsa tanasha. Kafin tayi rabin kofi, zufa ta rufe ta. Sannan taji qarfi a jikinta. Ta kama gefen hijabinta tana sharewa. Mahmud ya dubeta khadija bai dace kiyi irin wannan ba. Horon kanki da yunwa, wannan ba dabi'ar musulmi na gari bane. Ismail yace mema akayi mata ne? Taqi bani dama in nuna mata muhimmancinta. Kullum zancenta daya ne in saketa. Nace mata in nayi aure zanyi mata abinda takeso, kuma ynxu na soma neman aure. Sai tazo tanayin irin wannan? Sai kawai sukaji muryarta tace, duk wadda zaka aura, ka aura amma banda zainabu. Cikin sauri ya miqe, sbd me zakice haka? To ai wannan ba huruminki bane. Wadda zan aura sai kin za6a min, sai kace uwata? Ok, na gane nufinki, wato tunda baki sona kar wadda ta soni ko? To na gaji da wannan mulkin naki. Kuka ta soma, tare da fadin dole ka barta, kamar yadda dole tasa na haqura da khalil. Yace in ba haka ba fa? Tace za kayi da ka sani. Mahmud dake kallonsj, bai katsesu ba, sai yayi murmushi. "Da ace zaku fito da abinda ke zukatanku, wlh da kun huta. Sukayi shiru. Yace shikenan zainabu an bar maganarta. Zai canza wata. Haka yayi miki? Tace eh.
9⃣1⃣Ismail zaiyi wata magana mahmud ya daga masa hannu, tare da fadin an wuce wannan. Ka samu Malam, akwai wani sanata faruk da ya samu malam da maganar 'yarsa. Banji dai kan zancen ba, amma tabbas naji malam yace mutumin ya baka 'yarsa. Ismail yace, Hanan umar faruk kenan. Nasan yarinyar daliba ta ce a Abuja. Tanan kuma ta biyo? Mahmud yace bakamin zancenta ba. ismail yace banida ra'ayin auren yaran masu kudinnan, amma tana da hankali. To in anyi haka ya zanyi da zainabu? Banyi mata adalci ba. Duk zantukan da zukeyi, mimi mutuwar zaune tayi. Sai alokacin ta gane ba wai zainabu kawai take kishi ba. Duk matan duniya takeyin kishi dasu akan mijinta. Saidai ba tada ikon cewa komai akan wannan. Sun juya harshensu zuwa larabci, inda ismail ke qorafin ba'ayi ma zainabu adalci ba. Mahmud yace kafin kayi masu, sune suka fara yi maka. Sannan yarinyarnan tana matuqar sonka. Ina mamaki da kullum kuna tare, amma ni na gane hakan, kai ka kasa. Ismail yace nima inaso in fahimci hakan, sai tayi ta maganar saki, saki. Shiyasa naga kawai in haqura. Yace to ka gwada mana, zaka iya ganewa ta hanyar ta6a jikinta. Mahmud kaqi yarda cewa kana sonta. Alhalin shine dalilin daya hana ka daketa. In kaqi yarda dani ynxun, zaka yarda dani a gaba.
Mahmud ya miqe, tare da cewa, bari inje gida nima, kar Rabi'a ta kullemin qofa. Ismail ya kalli mimi, ya tausasa murya, ina makullin motar in saukeshi a gida? Ta kalli kujerar da suke kai, tana qasan nan. Suka ciro suna dariya. Ismail yace babu irin leqen qasan kujerar nan da banyi ba, ashe yana ciki. Sai daya miqe mahmud yace, dama saboda ta nuna makullin nayi shiru, amma da mashin nazo.
[27/09 9:55 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa

9⃣2⃣Bayan ya rakashi ya tafi, shi kuma ya kulle gida, ya kulle qofa. Har lokacin mimi tana zaune anan, amma ta zurfafa a tunani. Wacece Hanan? Ya zauna kusa da ita, "khadija hakan yayi miki ko? Ta kalleshi firgigit, batasan ma yazo kusa da ita ba, ta sauke ajiyar zuciya, "wai itama Hanan din kana sonta? Yace ban sani ba, sai naje na ganta sosai. Ya kalli cikin idanunta data tsareshi dasu. Kishi ya gani qarara a ciki. Tace, itafa tana sknka? Yace gsky tana sona, domin ta nuna min alamu. Tace, dama kana iya gane alamun mace, tana sonka? Yace, sosai kuwa. A ranta tace, to baka qware a wannan fannin ba, tunda ka kasa gane irin wanda nakeyi maka. A fili sai tace, tanada irin kyawun da kake so kenan? Yace banyi mata kallon qurilla ba. Ya rufe wannan da cewa, yau kin tsorata ni. Don Allah karki sake yi min haka kinji? Kallonsa kawai Mimi keyi, amma ita tamaicinta yafi tunaninsa. Ta miqe, bari inje in kwanta. Yace duk yinin da kikayi a gado a kwance baki gaji ba? Tace, karka damu bana gajiya da varci kai ka sani. Ya bita da kallo, damuwarta tana matuqar damunsa. Ya miqe shima yabi bayanta. Tana fitowa ban daki ta ganshi zaune a bakin gadonta. "Lafiya?" ta jefo masa tambaya. Yace, babu inda yake miki ciwo? Ta girgiza kai, a'a yace naga kina cikin damuwa ne har ynxun. In dai maganar zainabu ne ki dauka ya zama tarihi. Tace kaje ka kwanta kawai, ya wuce nima. Ya miqe ya nufi fita, sai kuma idanunsa suka hango wayarta dake kan madubi. Yace waccan wayarfa? Tare suka isa gurin, ya rigata dauka. Cikin sa'a ta amshe, tare da cewa, wayata ce bani. Yace shine baki ta6a kirana ba? Tace, ni bana kira da ita, sai dai inajin rediyo. Yace shikena saida safe.
9⃣3⃣Ya jima yana kai-kawo a dakinsa, zai tattara alamomin so da mimi take nuna masa, to me zai hana ta fada masa? Kuma meya kawo ta dinga batun saki? Wata zuciyar tace kaima ya kamata ka tantance kanka, shin kana sonta ne? Ko tausayinta kk ji? Ko ko sbaquwa ce? Can qasan zjciyarsa sai yaji an amsa da cewa duka ka hada. A fili yace, khadija! Babu batun saki. Ko da baki sona, balle zan gwada ki in gani. Washegari da safe, tana kicin tana hada masu abin karyawa, ya shigo cikin rashin walwala, ta kalleshi, "barka da safiya? Yace barkanmu. Ya kusanto ta, "bar ynxun baki huce ba Dija? Ko itama Hanan din baki sonta ne? Ta kalleshi, sannan ta ta6a baki. "in kai kana sonta, me ya shafi khadija? Yace Allah in bata miki ba, sai in fasa. Ta zaro ido, ni asuwa dan wake a hotel? Yace da gske nakeyi, amma in zaki yarda da wani sharadi guda daya. Tayi 'yar dariya, "inji sharadin. Yace zan turo miki a message. Sai ki bani amsa. Tace, sbikenan ina jira. Ta dauki tiren da abicin karin su, muje mu karya. Ya lura da yadda ta saki ranta daga yin wannan 'yar maganar. Suna karyawa, kowa da tunaninsa. Bayan sun gama ya miqe bari in fita. Tace Allah ya tsare. In ka shigo anjima zanje na wanke gashi na. Yace ki bari na kaiki da dare. Da mimi taji alamun shigar saqo a wayarta, sai ta duba, sai taga MTN ne. Kusan biyar na yamma ya dawo. Tayi kwalliya cikin riga da siket na atamfa. Ta yi masa sannu da zuwa. Ledojin daya shigo dasu ta amsa ta nufi kicin. Ya biyo ta a baya, kin jini shiru ban dawo ba? Tace nasanka da uzuri ai. Daidai lokacin ta bude ledar, kaji ne guda hudu, sai dayar kuma danyen kifi. Ta soma zubawa a freezer, tana cewa farfesun kifi zamu sha anjima kenan? Yace naje sai miki kifin, sai ga wani bawan Allah. Sai kawai ya biya, Kuma yasa asa min kaji. Shiyasa kk ga bana son yin siyayya a unguwar da aka sanni. Sai kawai wani yace zai biya. Tace, arziki ne hakan ma.
[28/09 3:34 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa

9⃣4⃣Yace bari inje inyi wanka, zamu fita da ismail. Gabanta ya fadi. Ina kuma zaku je malam? Ya dubeta, gidansu Hanan. Ta rufe freezer, sannan ta biyoshi, to ba ka fadi sharadinka ba. Ko dama kana yi min wasa ne? Yace oh na manta. Ina zuwa. Ya shiga dakinsa, bakin gado ya zauna. Ya rubuta cewa, "in kin yarda in sumbaci bakinki sau daya kullum, to zan haqura da Hanan. Idanu ta zaro, tana qara maimaita abin da ta karanta. Sai taji tanajin kunyar bashi amsa, amma tunda ya ta6a bata amsa da cewa shiru alamu ne, to tayi shiru. Baiga amsa ba. Don haka yayi shirinsa na fita. Ba wani gidansu Hanan zasu ba, don dai ya gwada tane. Rashin ganin amsarta, sai ya zata ko batayi na'am ba, don haka, sai ya shareta. Ita kuwa tanajin fitarsa, amma kunya ta hanata fitowa. Har washegari ba suyi batun ba, duk da sunci abincin dare tare, daren ranar qananan kaya yasa, abinda bata ta6a ganinsa da su ba. Ta kasa daina kallonsa don burgeta da yayi. Sam baiyi niyyar fita ba, kuma dama ya siyo qananan kaya ne don ya burgeta. Amma sai yayi nufin gwada ta. Ya dauki makullin mota zai fita, da sauri tace, ina zaka? Yace, khadija ya kamata ki daina tambayata in zan fita kamar wannan lokacin tunda kinsan komai. Ya kusa kai bakin qofa ta rasa me zatayi, sai kawai ta riqe ciki, "wash Allah na cikin! Ya waiwayo da sauri, yasan cewa qarya tayi, amma sai ya biye mata. Ya riqeta, ya kwantar da ita a cinyarsa, yaja rigarta sama kadan, ya soma yi mata addu'a yana shafa mata a cikin. Lamo tayi cike da burin dama su kwana a haka. Can yace, kinji sauqi? Tace eh, amma kar ka fita. Yace shikenan na bari sai gobe. Tuni Hajiya taba Alhaji shawara akan su miqa ma minista jikansa, sbd dalilinta data fada masa cewa, mutuncinka zai zube a idon jama'a, in kayi la'akari da cewa Abbas shine ubansa. Gashi 'yan jarida sunata bin shari'ar, ana ta yada ku a media. Yace shikenan. Da kansa yaje Abuja, ya kira Abbas yace ya zo ya dauki dansa. Sai dai sati biyu da daukar yaron ya farka da ciwan kunne. Sun kaishi Asibiti sun dubashi, sun basu gado. Kafin yamma ashe ciwon ajali ne, sai kuwa yace ga garinku nan. Hankalin ko wane 6angare ya tasbi. Na'ima kuwa kamar zatayi hauka. Amma dole suka dangana. Allah ya raba musu gardama. Abbas ya tura ma Na'ima saqon sakinta. Bayan watanni kuma sai ta nemi jami'a anan Abuja ta samu ta shiga, amma duk ta rame. Yanxun burinta taga mimi ta nemi gafara. Momy Nafisa kuwa tafi Na'ima da na sani. Hasana da Husaina sun sama mazaje, suna shekararsu ta biyu a jami'ar 'yar adua. Usaina, Abokin yaya mukhtar, kaduna yake. Ita kuma Hasana, Lecturer ne na makarantarsu, amma dan Gusau ne. An basu, amma sai sun qare karatu sannan za'ayi bikin. Shi yasa suka matsawa Hajiya sauda kan don Allah suna son abarsu suje gurin Sis mimi tunda an fada musu unguwar da take. Sun san Gidan ma. Hajiya sauda tace, susa ransu a inuwa daddyn sh ma yace, in ya dawo daga ganin likita a England zamuje gidan gaba dayanmu. Suka dauki murna.

1 Comments On CANJIN RAYUWA
avatar
mariya-6-8

11 months ago

Reply

In HAUSA language

Please Login or Register in order to submit comment