Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya sa kuka don haushi da takaici.hajiya ta ce,bai gaishe ta din ba.tafi abinka abdulkarim,cikin sauri ya wuce.su hasana ma suka yi dakinsu ita ma hajiya ta juya zuwa dakinta,MIMI ta kalli dad,kawai mu koma kalli fa duk yanda suka watse suka barmu,ya dafa ta karki damu ina zuwa. baki gado hajiya sauda ta zauna ta zabga tagumi,wannan abin ya ci mata rai,a ce mutum kamar alhaji ya dinga irin wannan abu sai ka ce yaro.kirikiri yana gani garkiya sai ya runtse ido saboda son zuciya,bai san cewa haka zai sa kan 'ya'yansa ya rabu ba ne?sallamar shi ce ta katse ta,ta dago ta dube shi,shima ya iso ya zauna bakin gadon.haba hajiya ki sakarwa 'yarki fuska mana?ke ba abin faharin ki bane a ce nafi son 'yarki,duk cikin 'ya'ya na?
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (10) Ya kama hannunta cikin sigar lallashi ya ce,haba sauda kin fa san ina tsananin sonki, sonki ne fa ya shafe ta ko baki lura ba?ta daga ido ta kalle shi,ban musa ba,na san kana so na,amma ni burin na shine ka yi adalci tsakanin yaranka alhaji, ko don gudu rarrabuwar kansu. ya ce,menene na yi mata wanda ban yi masu ba?ta kalli cikin idon shi,ai ba za su kirgu ba,banda nuna tsantsar kulawa a fili, duk cikin yaranka wanene ka kai kasa wajen karatu bayan ita?to indan wannan ne,karatun na su na gida ya fina ta cin kudi sauda. umm, haka dai za ka ce,tunda kana son kare kanka,ya ce, ni dai ina neman alfarma ki sakar mata fuska ki dan ja ta a jikin ki har mu tafi.ta kalle shi,ta rasa me zata ce masa,sai kurum ta ce to. don tana son kawo karshen zancan, ya shafi kumatun ta,na gode,ya matso da bakin shi saitin kunnuwanta,ina son a kyuatata shimfida ta anjima. don na iso da muradin hakan. Ta sake murmushi tare da kallon shi,wai alhaji yaushe zaa girma ne?ta yi tambayar cikin sigar wasa. ya janyo ta jikin shi,wa ya ce miki ana girma da lada? sai dai in mutuwa ce ta dauka.suka sa dariya tare, daidai lokacin aka yi kiran sallar.suka mike, ta ce lokacin sallah yayi bari in fita 'yan mazan nan sai nayi fama sannan su wuce masallaci.tare suka fita ya nufi dakin shi,har lokacin MIMI tana zaune a falo.sai dai lokacin ta koma kan kujerar zaman mutum biyu tana ta chatin. alhaji ya nufe ta yana cewa,mamana kina hutawa ne?ba tare data dago ba,ta ce eh dady.ya ce da kyau.ya wuce dakinsa. hajiya sauda ta dube ta,ki tashi kiyi sallah,ta dago ta kalli hajiyar ta ga fuskarta a daure,ta zabga mata harara na ce,ki tashi ki yi sallah.tsam ta mike ta nufi dakin su usaina inda nan ne take sauka in ta zo,kayan tama cikin suke.sai dai ita bata sm hakan saboda a abuja sasanta dabam, amma a nan hajiya ta hana a yi mata dakinta dabam.ta sami su hasana suna sallah, ta fadi kan gado ta ci gaba da chatin dinta.ga al'ada alhaji in ya fita sallah,
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (11) Yakan kai sha biyu bai shigo gida ba zai yi ta gaisawa da mutane, abokai zuwa 'yanuwa suka ji cewa ya shigo gari.don haka ita ma hajiya bata fito ba sai bayan sallah isha,ta shiga daki alhaji don sake kalailai ce shi,tare da kunna turarukan kamshim daki,ta fitar ma da alhaji kayan barci,ta dama masa fura,ta nufi dakin yaranta don ta tabbatar suna cikin koshin lafiya.daki maza ta fara shiga, umar da aminu suna ta yin home work, abdullahi yana kwance kan gado, sadik yana buga game a tv. ta ce,sarkin game kai ka yi home work dinka? ya ce, eh nayi hajiya ta kalli abdullahi,kai fa bawan allah yau da wuri zaka yi barci kenan? ya tashi zaune kaina ke ciwo hajiya shi yasa ki kaji na ce dad ya bari sai gobe mu je super maket din.don ba zan iya kula da su ba. ta ce,ba sai kun yi haka ba,ya ce,kin shiga daki lokacin ta ce,to ka sha magani?ya ce eh!ta ce to allah ya sawwake,ya ce ameen.ta ce,sadik tashi ka kulle muku kofar ku sai da safe,suka ce,to ta ce,kar fa ku manta da yin addua lokacin barci,suka ce to.ta nufi dakin su husna da hasana da kuma zainab yar gidan hajiya binta, wace ta ki komawa wajen uwarta,tun lokacin da alhaji ya saki hajiya binta,ya kwaso yaran ya kawo su nan.hajiya sauda tace sam ba zai yiwu ba,lallai ya mayar da ita,ta rike kayanta. domin ita kanta ba zata sa araba ta da 'ya'yanta ba.shine da ya dawo da ita ya mayar mata da yaran amma ban da zainab,don kuwa ta kekashe ba9a ta bi su ba. lta ta fi son zama a nan, hajiya sauda ta rike ta,ta hada da 'ya'yanta guda goma sha biyu da ta haifa suka zama sha uku.su kam sun fara barci.don haka ta shigo ta yi masu addua tare da kulle masu kofar dakinsu. hasana suna zaune suna kara ma juna haddar alkur'ani mai girma, ita kuwa 'yar gwal,wato MIMI tana kishigide kan gado.tana ta chatin,kai tsaye gurinta hajiya ta nufa ta fisge wayar da sauri MIMI ta dubi wayar cikin bacin rai.tana ganin hajiya sai ta yi kasa da kai kamar munafuka,kin yi sallar ne? cikin tsawa ta ji maganar MIMI,
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (12)MIMI ta yi shiru, ta ce,ba ki ji niba ne?ta girgiza kai tare da fadin banyi ba. hajiya ta rufe ta da fada bangane ba kiyi ba? Anya ma kina yin sallar na kuwa? ta kalli hajiya cikin sauri tare da fadin ina yi mana,hajiya tace,karya ne kalli agogonki karfe nawa ne yanzu?da har zuwa yanzu baki yi ko sallar magariba ba bare lsha.in na lura musulunci ba ya birge ki,lslamiyya kin daina,duk wani abu da lslam yazo da shi,komi na addini kin mayar da shi kauyanci,ke ga 'yar boko ko?MIMI dai bata dago kai ba,hajiya ta ce,na san ko zaa kashe ki yanzu da kyar in zaki iya kawo mini fatiha cikakkiya. kin zauna kina ta danne-dannen waya,in ba ki sani ba ne gara ki sani,kina cutar kanki ne.rayuwar daki ka daukar wa kanki ba mai dorewa ba ce,don haka ba ta dace da ke ba.ki ta shi ki yi sallar yanzun nan, sakarya marar hankali. simi-simi MIMI ta tashi ta nufi bandaki,hajiya ta ce,tunda abin naki ya soma nisa haka,wayewar taki har ta kai ki da gudu salla,to nan gida za ki kare hutunki.ki dau karatu gurin malamin yaran nan,ki koyi salla tun da bani da tabbacin kin na yi.bari baban naku ya shigo,ta juya ta fita da wayar a hannunta.MIMI daga cikin bandaki,kuka wiwi ta dinga yi,ita kam baza ta iya zam har ta gama hutu cikin takurar ba. a silent hajiya ta saka wayar MIMI ta ja durowa ta jefa.MIMI tana kuka ta yi sallar,su hussaina suna kallonta,ta idar ta fada kan gado ta ci gaba da kuka.don ita amshe mata wayar da hajiya ta yi,ya fi bata mata rai fiye da fadan,don jin ta take tamkar an raba ta da ranta, sam bata nisa da wayarta. misalin shabiyu saura alhaji ya shigo,tuntuni yake ta neman layin 'yar lelanshi,amma sai tayi ta ruri har ta yanke ba a daga ba. hajiya ta shiga ta same shi tana cikin shirin barci,ya kalle ta da wayansa a hannu,MIMI fa?ta kalle shi,in kira maka ita ne?ya lura cikin gatse ta yi masa maganar,don haka sai ya ce,aa dama in ji ko ta yi barci ne,saboda ina ta kiran wayarta bata dauka ba.cikin jin haushi hajiya ta ce oho..
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (13)Na zata ita ma nan zamu kwana tare don kar wani abu ya cinye ta. ya mike tare da kama hannunta,sauda kin canza sani na ba haka kike ba.yanzu kin zama mai saurin fushi.ta kalli fuskarsa,kai da 'yarka kuka canza ni.ya ja hannunta,to zo mu zauna in ji mai zan samu.ya basar da wancan zancen.ita ma sai ta biye masa da cewa,duk abinda kake so.ya tallabe fuskarta kin san mene ne sauda?ta girgiza kai kullum na kalli fuskarki.rana mai tarihi a guri na.hajiya sauda ta ce, ikon allah ni kan da a ce kalmar karatu ce,da sai in ce,tuni na haddace ta,tun muna da kananan shekaru. ya yi 'yar dariya ina jin dadin tuna baya,wani lokacin sai in ji tamkar in mai do lokaci.ta lumshe ido, ai alhaji kuruciya cike ta ke da shirme,in ta wuce sai ayi ta kewarta,
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (14)Ni kaina ina son tuna baya,rayuwa tana da sauri,duk da haka in muna tare,sai in rika jin kaina tamkar 'yar kasa da shekara ashirin.yayi dariya,a haka ni ke kallon ki sauda,kullum na kan ce, lokacin na sauri.ta kwantar da kanta a kafadarsa.allah ya kara mana tsaw rai da rayuwa mai amfani.a kunne ya rada mata amin.da ma an ce soyaya bata tsufa, sai dai masoya su tsufa, allah ka yi mana mai kyau. karfe bakwai alhaji bashir yana ta shiri cikin sauri,hajiya tana taimaka masa gurin saka kaya, rokonsa take yi ya dan sa wani abinci a bakinsa,ta ce don kai nasa a yi kunun gyada da kosai,saboda na san kana so.ya kalle ta,ta na saka masa liks a hannun riga ya ce,ki yi hakuri mata ta,ba komai,na yi alkawarin zan gana da wani mutum ne,wanda na fi wata guda ina neman damar ganinsa. ta ce,duk da haka ka karya zai fi.ya ce sai na dawo,domin in na samu damar da nike nema a gare shi,kasuwanci na zai ninka,in ko haka ta samu yaya kika gani?ta ce, umm! kai dai da ma kullum saurin ka bai wuce kasuwanci,a kasuwanci ina ne ba a sanka ba,duk fadin afirka ina ne sunanka bai kai ba! wane irin kudi ne baka mallaka ba kullum cikin samun riba ka ke. ta mika masa hularsa,me ya kamata ka nema kuma alhaji?yanzu baya ga aljanna? murmushi ya yi,ba tare da yaba ta amsar duk tambayoyin da ta jero masa ba.ta ci gaba, ni dai ba zan gaji da baka shawarar cewa,kamata yayi zuwa yanzu kayi murabus ka bar abba da mukhtar su jagoranci kasuwancinka.ya ce,ni kuma fa ta ce,ka zo mu zauna mu huta,mu karasa rayuwarmu,'yan kananan yaranmu su shaku da kai.ya saki dariya tare da cewa,sauda kenan.in ki ka fadi wata magana sai ki tuna mimi tadinmu na farko da ke.ta ce au!kana nufi maganar ma dana fada shirme ce?ya ce,kusan haka,kina cewa in bar ma su abba ragamar kasuwanci,ki na tsammanin za su yi jarumtar kasuwanci kamar ni? bai jira amsa ba,ya ci gaba da cewa,da ma MIMI ce babba,ko da tana mace na san za ta iya.amma su abba shirme kenan,shi yasa kika,
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (15)Ga ko shawara ce na fi son yi da ita koyaushe ta na bani shawara ta musamman yadda ake fadada kasuwanci a duniya ta cikin yanar gizo.su kuwa su abba bakin ku daya.kullum in takaita kasuwanci a iya gida nijeriya,ni kuma na wuce nan tuni. ta ce,ka fahimce ni ba muna cewa kar kayi kasuwanci da waje ba ne aa,ai bunkasar ka ta isa ka yi kasuwanci da waje.harkar shigo da magunguna ne muka ce ka daina,tunda ana yawan zargin kana shigo da haramtattun magunguna da kuma miyagun kwayoyi.ya gyara zaman hularsa,ya sa hannu ya shafi kumatun ta, ki ci gaba da yi min addua sauda,ke ce kurum ki ke fada min son ranki in ji ban ji haushi ba.ya cire takalminsa tana fesa masa turare ya ce,ban sani ba ko zamu gama tattaunawa da wuri ko ba zamu gama ba, amma ko yaya ne dai daga can zan wuce malumfashi. in duba su binta da yara sannan in kewayo gona ta, na jima ban leka ta ba.inda lokaci zan shiga masari can ma na jima ban je ba.kin ga sai na kwana kenan,gobe zan dawo in dauki uwata mu koma inda muka fi wayo.ta ce,allah ya tsare sai ka dawo din amma batun tafiya da MIMI ne nake tunani a kai.ya kalle ta, kamar yaya?ta ce,sai ka dawo dai allah ya tsare,ya dan tabe baki amin.suna fitowa falo yara suka nufo suna yi masu sannu da fitowa tare da gaishe shi,ya amsa da daidai,ya kalli usaina,MIMI fa?ta ce tana kwance dady,ya ce,shikenan zamu yi waya.hajiya ta raka shi har mota,ba sabon abu bane,haka ta saba tun suna da kuruciya.falo ya kacame,yaran suna ta karin kumallo,sai hayaniyarsu da karar kofuna.MIMI ta fito sanye ciki riga da wando masu dan kauri na barci. sauri ta ke yi,tare da fatan allah ya sa dad dinta bai fita ba,don ba za ta taba bari ya fita ya bar ta ba.ta iso gurin hajiya,fuskar ta babu annuri ta ce,ina kwana hajiya?ba tare da ta dube ta bata ce,lafiya lau.MIMI tayi tsaye shiru,tana son yin magana amma tana tsoro.hajiya ta dago ta dube ta,ga kayan shayi can a kan dining,na san ba kya shan kunu,ta ce tam!ehemm!da ma zan gaida dady ne,yana ciki ne? hajiya ta ce a'a.
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (16)Ya tafi malumfashi sai gobe zai dawo.MIMI ta zaro idanu yaya dady zai min haka ya tafi ya bar ni,ta kalli hajiya wanda ta soma watsa mata harara ta ce,hajiya don allah ina waya ta?hajiya ta ce,sai za ku tafi zan baki,don ni ba za kiyi mani chatin din naki ba a nan,ki karya ki je ki yi wanka,in malamin su hussai ya zo zaki bisu,ki je daukar karatu a gurinsa.ina sa ran ma alhaji ba zai tafi da ke ba,nan zai bar ki sai kin san addininki za ki tafi,ko da zaki cinye hutun ki a nan. cikin sauri MIMI ta koma daki cikin kuka sai da tayi me isarta ta shiga wanka,a fili kuwa fili kuwa fadi ta ke, allah ba zan zauna ba, shi ya sa na tsani zuwa katsinan nan.dolenta ta saka atamfa riga da siket,a cikin durowarta ta ciro don tana da kaya a nan gida, duk lokacin da aka yi wasu usaina sai an yi mata.ta shirya tsaf ta koma kan gado ta kwanta tana tunanin yadda za ta yi.amma ko ta halin kaka baza ta zauna cikin irin takurar ba.can ta hango wayar hasana kan durowar ta.cikin sauri ta tashi ta dauko,layin dad ta kira wanda ta san in ta kira zai dauka da sauri,cikin kuka ta soma magana,bayan ya daga dad kaga hajiya ta dauke min waya ta,kuma wai ba zan tafi ba,ni dai dad wallahi bazan zauna ba.ya ce,ya shiru uwata kar ki damu ba zan barki ba ni ma,yanzu me kike so?ta ce,phone di na,ya ce,shikenan zan ce ta ba ki,kin ci abinci?ta ce,aa ya ce,to kije ki ci zan sata baki wayarki kin ji? ta na zaune a kan dining ta hada shayi tana sha da cokali cikin hankali don ita sam bata da hanzari,tana kallo lokacin da hussaina ta kawo ma hajiya waya ta ce,dady ya kira,ta daga.ta na jin lokacin da hajiyar take cewa,tsaya kaji alhaji, sai kuma tayi shiru,da alama ya katse ta ne,ya hana ta magana,don taga hajiya tayi shiru,amma ranta a bace yake.sai kuma tace to alhaji naji zan bata, amma bana son chatin din nan data keyi.MIMI ta yi murna,a ranta tace dady na kenan,ta nufi daki da murna,alhaji ya ce,kar ki damu sauda,'yarki mai kamu kai ce.ita da kowa ya shaida ko saurayi ba.
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (17)Shi yasa nike dubawa don in samo mata miji wanda zai kimanta min ita,ya bata kulawa fiye da wanda take samu a guri na.
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (18)Hajiya ta ce umm!allah ya taimaka,ai ni dana zaci ma baza ka iya auradda ita ba(cikin gatse tayi maganar)ya ce,kash kin ji ki da wata magana kuma sauda,in ban aurar da ita ba ai kuma na cuce ta.ina maki kaga an taba haka?ke dai kiyi mana addua,ta ce,allah ya taimaka,kun gama ganawar ne?ya ce,eh,yanzu haka muna hanyar malumfashi sai na dawo ta ce,allah ya tsare,ka dawo lafiya,ya ce, amin,ga dai uwata nan amana naba ki,katse wayar yayi ba tare da ya jira jin amsa daga bakinta ba.ga zaton MIMI tana aje wayar alhaji zata zo taba ta tata,amma sai taji shiru. ta sake fitowa falo nufin ta kila hajiya ta ganta ta tuna,idan ta manta ne, amma sai taga hajiya ta ci gaba da lamuranta.yaran duk suka yi wanka suka fito,husna da hasina suka shiga falo da gudu suna cewa,ga malam nan yazo.ga mamakin MIMI sai ta ga duk yara sun rude, wasu sun dauko alkur'anin su suna karantawa da sauran littafai da yake masu.a ranta ta ce ni ko bari in ga wanene malamin ,kai har naji na tsane shi tun kafin in ganshi.a zaton ta nan zai shigo sai ta ga abdullahi da umar da aminu da sadik sun soma fitowa bayan dawowansu sai zainab da hasana da hussaina suka fita. hasina da husna kuma sun dukufa suna ta karbarma juna hadda,kafin a zo kansu.MIMI ta tabe baki tare da cewa,wahalar da kai,basu dade ba suka dawo.su hasana sun mike kenan hajiya ta fito daga daki ta ce,ke ma tashi kije, ta nuna MIMI ta hada rai,sai dai bata da damar yin musu,don babu alhajin da zai tare mata.hasana ta ce. yaya MIMI sai kin sako hijabi fa,ta banka harara,ban dauko ba,ina wasa da ke ne?in ki ka kara yi min magana sai na mare ki. suka yi shiru suka wuce,ta warware dan kwalin kayanta ta yafa,tana biye da su har falo baki,kafin su shiga sai da suka kara gyara hijabansu suka yi sallama suka shiga,ta tsaya tana mamaki wai malami ne suke yi ma bare-baren, malamin ma wai na lslamiyya,ita malami ko na boko bata dauke shi wani abu ba,face bawan ta mai ci a karkashin su.bare da ba zata iya,
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (20)Saboda ba son karatun ta ke yi ba.ka soma mata daga fatiha don ba na zaton ta iya,don allah malam lsmail kar kayi mata da sauki.lsmail ya ce, ba komai hajiya.amma ta saka hijabi ta ce,to ba komai bari in sasu hasana su kawo mata,in ta ki yi ka dake ta ko ka kira ni. hajiya ta fita shi kuma ya kai duban shi gare ta, MIMI ta cika tayi tam.ya na zama hasana tana shigowa da sallama,shine ya amsa,ta ce,yaya ga shi, harara ta watso mata,ta ki amsa,hasana ta aje a hannun kujeraq da take zaune ta fita. ya kalle ta,malama ki saka hijabinki mana,cikin sauri ta dago kai ta dube shi duban tsana mai tsanani,domin ba a taba ci mata mutunci kamar yau ba a gaban kaskantacce irin wannan.ba a taba rena mata wayo ba kamar yadda shi din ya yi mata,ya ganta sarai,amma ya ce,bai ganta ba.abin yayi mata ciwo fiye da abinda hajiya tayi mata.ta harare shi sama da kasa sannan taja tsaki, malam baya daukar reni,sabi da haka sai ya hada rai tare da rufe alkuranin shi. ta ce kai waye suna da ake kiranka? ina son ka sani na wuce ka rena min wayo kuma kai baka isa ka koya min karatu ba.ya daga hannu tare da katse ta da cewa ke.ba ki da ladabi ne? gaskiya ba tarbiyyar nan gidan ba ce,domin yaran gidan nan mazansu da matansu nayi shedar su guri ladabi game da sanin darajar mutane,ke ma ina yi maki nasiha ki canza.kuma ina son ki sani karatun nan in kin yi kin ma kanki ne bani ba,don haka ka da allah yasa ki yi,ya mike ya fita abinsa. yana jiyo tsakinta gami da cewa, talakan banza kana ci a karkashin mahaifi na ka nuna ni da yatsa,to bari ka gani lokacin barin ka aiki yayi.har ya tafi ya dawo ke ma dukiyar daki ke takama ba taki ba ce,ta mahaifin ki ce,ina son ki sani ba keki ka dauke ni aiki ba bare ki sallame ni.ba kuma maula nake zuwa yi a gidanku ba,ina son ki san wannan.kafin ta sake yin wata magana ya wuce ya barta cikin takaici,lallai sai nayi maganin sa,shine mutum na farko a tun tasowar ta da ya taba fada mata abinda ya ke so,
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (19)Face bawan ta mai ci a karkashin su.bare da baza ta iya bambamce shi da maigadi ko mai sharan gidansu,kosawa ma ta yi ta shiga ta gani wane gaja ne? ta jingina da kofar,sannan ta kai kallonta gurin shi,yana zaune kan kujeran zaman mutum daya sanye yake da jallabiya mai ruwan madara mai dogon hannu da maballi a hannu,tare da kwala a wuyarta.ga wani dan ado da zare mai ruwan kasa da aka yi a wuyar da hannun rigar,bata kai can kasa ba,irin dai shiga ta sunna,hular kanshi baka ce irin wanda ake kira minista. ya na rike da alkurani yana bude inda suke.su kuma su hussaina suna zaune a kasa kan kafet a gabanshi duk suna rike da alkuraninsu,MIMI ta tabe baki tare da harde hannuwanta a kirjinta,tana kare masu kallo.a ranta ta ce,tabdi,ai ba a yi mutumin da zai zo gidan ubanta ta zauna a kasa yana kan kujera ba.malam lsmail ya dago ya kalli bakin kofa da kyawawan idanunsa,duhun mutum ya gani,ya sa shi kallon gurin ya kalli MIMI da ke tsaye ta watso masa wani kallo da ba zai iya fassarashi ba.ya mayar da kanshi ga abinda yake yi.su hussaina suka ci gaba da kawo masa hadda yana yi masu 'yan gyare-gyare, suka kamalla,sannan suka soma sauran littafai. ta shiga ta zauna tare da daukan rimote ta kunna tv, ya dago ya dube ta, tamkar zai yi magana,amma sai ya fasa. ya san da gadara tazo, bayan su hussaina sun kamalla,sai hussaina tace, yaya kizo mun gama,ta kalle su cikin harara,ku fita mana, suka fita suka je suka sanar da hajiya ko mai.ita kam suna fita ta mike tana tafiyar nan tata, ta isa kan kujerar gefen shi ta zauna. ya dago ya dube ta,ya mike tare da tattara littafansa,ya nufi fita,a bakin kofa suka ci karo da hajiya zata shigo,ya dakata ta kara so suka gaisa,ta ce, har ka mata karatun?ya ce, wace kenan?ta ce, MIMI, bangan ta ba ai,hajiya ta ce aa ta shigo ciki falon, ta ce gata nan fa,ya dawo cikin falo,ok!wannan ce? na ganta amma ban zaci karatu za ayi mata ba.ita kuma bata fada min ba. hajiya ta ce,ai ba zata fada maka,
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (21)Kuma tana son ya zama na karshe, takaicinta ma talaka ne shi, ba wani isashshe ba. daf da zai fita daga cikin gidan,abdulkarim ya yi masa sallama,ya tsaya suka gaisa ta hanyar yin musabaha.ya

1 Comments On CANJIN RAYUWA
avatar
mariya-6-8

11 months ago

Reply

In HAUSA language

Please Login or Register in order to submit comment