Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

MAZA SUN FADI Part 1

RANA ta take kuma tayi zafi sossai,
Amma hakan bai hana mutane cigaba
da Harakokinsu ba a cikin birnin kowa
ka gani sha’anin gabansa yakeyi, har a
cikin kasuwa kuwa ana ta kai kawo ana saye da
sayarwa.
Kwatam sai aka hango wani matashin saurayi
wanda ba zaifi shekara goma shabiyar ba,
ya ratso kasuwa yana tafe yana layi sakamakon
jini dake zuba a jikinsa har idanunsa suna
lumshewa,
kai da ganinsa kasan cewa yasha fama gudu sai
haki yake,
Rigar jikinsa kuwa ta jike sharkaf da jini, nan take
ya kife kasa da rub da ciki a tsakiyar kasuwar.
Al'amarin da ya matukar razana mutane kenan
domin ba'a san yadda wannan saurayi ya shiga
wannan hali ba.
Nan da nan mutane suka taru suka kewaye
wannan saurayi amma aka rasa wanda zai
taimakeshi,
Sai wani tsoho ne yayi sauri ya tashe shi zaune
ya daura masa ruwa a baki yasha,
Koda tsohon ya dubi fuskar saurayin sai ya
tsorata ainun ya dubeshi cikin dimauta yace ya
kai SHUBAIRU waye yayi maka Wannnan karen
aiki?''
Cikin matukar karfin hali shubairu ya dubi tsohon
ya bude idanunsa da bakinsa da kyar yace,
''kowa yai sauri yayi gudun ransa
domin wadansu yan harine suka biyoni da gudu
da kyar na guje musu na iso nan,
Ina gaya muku cewa suna da tsananin yawan
gaske Idan suka iso cikin garin nan sai sun
kashe kowa kuma su debe mana dukiyoyinmu ''
Koda jin wannan batu sai gaba daya kasuwar ta
yamutse mutane suka fara guje-guje da iface-
iface masu kokarin kwashe hajojinsu nayi,wasu
na bangaje wasu a lokacin gudun, maza da mata
yara da manya, nan da nan labari yakai har cikin
gari.
Shi kuwa wannan tsohon ko juyawa izuwa cikin
rumfarsa baiyi ba,
sai yai sauri ya tashi shubairu tsaye ya kaishi
inda dokinsa yake ya dorashi akai yace,
dashi ''maxa ka ruga izuwa gida ka sanar da dan
uwanka HUZAIRU halin da ake ciki kuma ka gaya
masa ya hanzarta dinke maka raunin dake
bayanka domin sara da akayi maka mai zurfi ne''
Koda jin haka sai hawaye ya zubowa shubairu
yace,
''Yakai Abbana Yaza'ayi na tafi na barka anan
yan sumame su kasheka?''
Tsoho KALMARU ya dubi shubairu a lokacin da
shima kwalla ta cika masa idanu yace, ''idan na
bika muka tafi tare, Biyu babu za'a yi sbd dokin
nawa bashida issashiyar lfy ba xai iya daukarmu
mu biyu ba.
Dolene na tsaya na tari 'yan harin nan nayi iya
kokarina na bata musu lokaci don ka isa Gida da
wuri,
ku sami damar guduwa kai da dan uwanka
huzairu,
Na sani cewa dan uwanka huzairu yanada taurin
zuciya zai iya cewa sai ya dawo nan ya ceceni
to ka gaya masa cewa ko!
idan har ya biyo bayana ya karya alkawarin da ya
daukarwa mahaifiyarku. Na cewa komai rintsi zai
rayu domin ya dauki fansar ranta. ''
Gama fadin hakan keda wuya sai hawaye ya
zubowa tsoho kalmaru ya yiwa shubairu kallon
karshe mai nuna bankwana,
dan ya san cewa baxa su sake saduwa ba.
Nan take kalmaru ya doki bayan dokin da tafin
hannunsa nan take dokin ya zaburi shubairu da
gudu izuwa cikin gari.
A Wannnan lokaci tuni kasuwar ta dade da
watsewa,
babu mutum koda guda daya jal a cikinta face
tsoho kalmaru.
Kawai sai kalmaru ya ruga izuwa cikin rumfarsa
ya dauko takobi da garkuwa sannan ya fito ya
hau kan wani dogon mumbari dake tsakiyar
kasuwar ya tsaya cak!'' yana kallon hanyar da
yan harin zasu shigo.
Kallo daya mutum zai yiwa tsoho kalmaru ya
tabbatarda cewa ya kasance tsohon Sadaukin
Jarumi,
domin da gani babu tambaya sbd ya kasance
dogo mai murdadden jiki, duk da kasancewar
shekarunsa a yanzu sun haura saba'in (70)
kasancewar akwai sauran kuzari a tare dashi,
kuma komai takamar Jarumi zai yi shakka yayi
masa shiga farat daya, saboda kwarjininsa.
Bayan tsayuwar tsohon kalmaru da kamar tsawon
dakika dari da ashirin sai ya jiyo sukuwar
dawakai babu adadi sun durfafo kasuwar.
Duk da cewa kalmaru yanada dakakkiyar zuciya
irinta manyan maxaje sai da tsoro ya darsu
acikin zuciyarsa,
Ba wai tsoro bane na mutuwa ko irin fafatawar
da xaiyi ba,
tsoro ne na takaicin irin barna da wadannan
dakarun sumame zasu yi idan suka shigo wannan
karamin kauye nasu.
Shi dai wannan kauyen nasu tsoho kalmaru ana
kiransa da suna HIDAIMAT mutanen kauyen gaba
dayansu masu sana'ar kera jirgin ruwa ne,
kasancewar kauyen yana bakin teku
Asalin kauyen tsoho kalmaru ne ya kirkireshe
domin shine ya fara zama a bakin tekun, tun
kafin matarsa ta haife masa ya'yansa guda biyu,
SHUBAIRU DA HUZAIRU
Kafin tsoho kalmaru yayi aure ya kasance
mataimakin sarkin yakin birnin zamar kuma sai
da ya shekara ashirin da biyu yana yiwa sarki
Barham bauta.
Duk sa'adda kalmaru Ya jagoranci yaki sai an
sami nasara ba'a taba samun akasi ba,
Al'amarin da ya janyo kishi kenan tsakaninsa da
sarkin yaki HAMSARU sbd shi kuma duk sa'adda
ya jagoranci yaki anfi yin RAGAS ba'a cika
samun nasara ba,
Wani babban abun takaici shine sarkin yaki
Hamsaru da kalmaru sun kasance 'yan uwan na
jini domin dan wa da dan kane suke,
Mahaifin Hamsaru ne yayan mahaifin kalmaru,
Tun sa'adda kalmaru da Hamsaru suka taso da
kurciya ya xamana Cewa ana basu horon yaki a
gidan sarautar zamar, kasancewar a wannan
lokaci mahaifin kalmaru ne sarkin yaki,
Burin mahaifin kalmaru shine dansa ya gajeshi
amma sai ya zamana cewa Hamsaru yafi
kalmaru tsagwaron karfin damtse da iya yaki,
Shi kuma kalmaru sai yazamana cewa yafi
Hamsaru sa'a gamida taurin zuciya.
Komai hadarin yaki da yawan abokan gaba
kalmaru baya ja da baya.
Lokacin da tsufa ya riski mahaifin kalmaru sossai
har ya zamana cewa baya iya zuwa fada bare
yaje yaki sai kalmaru da Hamsaru ne suke
walkitarsa sai sarki Barham yasa aka kirawoshi
suka kebe inda ya dubeshi yace ,
''ya kai dirkar birnin zamar kasani cewa kai yanzu
tsufa ya riskeka har ta kai cewa ka kasa ruke
mukaminka, sai ya'ya'nka ne suke kula dashi, sbd
haka inason a cikin ya'yan nan naka ka zabi daya
daga cikinsu wanda kake ganin cewa shine mafi
cancanta daya gajeka,
Lokacinda sarkin yaki yaji wannan batu na sarki
Barham, sai hankalinsa ya dugunzuma ainun sbd
shi baxai iya zabar daya daga cikinsu kalmaru
ba.
Duk da cewa a zuciyarsa yafi son dan cikinsa
kalmaru ya gajeshi sbd bayason wani abu da xai
kawo sabani tsakaninsa da dan uwansa wato
mahaifin Hamsaru. Sarkin yaki yai shiru yana
tunani har izuwa tsawon wani dan lokaci
sannnan ya dago kai ya dubi sarki Barham yace,
''ya shugabana kai da kanka ka sani cewa
Hamsaru yafi kalmaru tsagwaron karfin damtse
da iya yaki,
Amma kuma kalmaru yafi Hamsaru sa'a da taurin
zuciya da naci.
Ni ina ganin cewa bani ne ya kamata na zabi
wanda zai gajeni ba daga cikinsu ba. MAZA SUN FADI!!! Part 2

Ni ina ganin cewa bani ne ya kamata na zabi
wanda zai gajeni ba daga cikinsu.
Kamata yayi kai da sauran yan majalisa ku zauna
kuyi tunani kuyi zabin da kanku bisa wanda kuke
ganin yafi cancanta,
Kasani cewa idan na zabi dana kalmaru zan sami
matsala da dan uwana mahaifin Hamsaru wato
YUNARU,har zumuncin mu ya raunana ''
Sa'adda sarkin yaki yazo nan a zancensa sai sarki
Barham yai shiru yana nazarin al'amarin.
Daga can sai ya dago kai ya dubeshi yace,
''ya kai dirkar birnin zamar hakika na karbi
uzurinka,
Amma baza mu zabi magajinka ba Nida yan
majalisata kadai ba,
Abinda zamuyi kawai shine, zamu shirya gasa ta
jarumtaka tsakanin kalmaru da Hamsaru, su yaki
juna a tsakiyar fada agaban alkalan gasa, 'yan
majalisa da mutanen gari.
Wanda da duk yasami nasara kai wani kasa daga
cikinsu shine zai gajeka,
Koda jin haka sai mamaki da tsoro ya kama
sarkin yaki ya dubi sarki Barham cikin tsananin
damuwa yace,
'' haba ya shugabana ai bai kamata ayi hakan ba
tunda kowa ya san cewa Hamsaru yafi kalmaru
karfin damtse da iya yaki.
Sarki Barham yai ajiyar zuciya yace,
''ya kai abokina kasani cewa kai aminina ne
kuma tun muna yara muka taso tare,
Bamu taba rabuwa ba,
Ko ayanzu daka tsufa har takai cewa baka iya
zuwa fada, bana shafe kwana 2 bankai maka
ziyara ba har gidanka,
Wannan tsufa naka da rashin kuzari a jikinka
yanada nasaba da asirin da dan uwanka yayi
maka yasa maka rashin lfy sbd bakin cikin
kasami sarautar sarkin yaki shi bai samuba,
Ka sani cewa duk fadin kasar nan ni Kadai ne na
san wannan Sirri kuma bantaba gayawa wani ba.
Ta yaya kake tsammani cewa zanso dansa ya
zama sarkin yakina? ''
A koda yaushe ciwon dake jikinka xai iya zama
ajalinka,
Idan har ka tafi ka barni zanso ace na rinka
ganin danka akusa dani tunda kammaninku iri
daya ne sak tamkar an tsaga kara, tunda idan ina
ganinsa zan samu saukin kewarka.
Lallai zanso ace kalmaru ya gajeka,
Zan iya amfani da karfin kujerata na tabbatarda
cewa kalmaru ya gajeka,
To amma idan nayi hakan jama'a zasu ce nayi
son zuciya sbd ansan kusancina dakai.
Nayarda da sa'ar danka kalmaru gamida da
nacinsa don haka nayi imani cewar zai iya lashe
wannan gasa''
Lokacin da sarki Barham yazo nan a zancensa
sai idanun sarkin yaki suka ciko da kwallah har
hawaye ya zubo masa yace,, ''yakai abokina
nasani cewa kana son ka kasance dani da
zuri'arka har karshen rayuwaka to amma dole mu
rungumi kaddara domin hakan baxai taba yi yuwa
ba.
Na yarda batun wannan gasa da kashirya kuma
ina yiwa mai sa'a fatar samun nasara ''
Koda gama fadin hakan sai sarkin yaki Yayiwa
sarki Barham sallama ya mike tsaye da kyar! Sbd
laulayin rashin lfy da tsufa ya fice daga cikin
dakin dasu ka gana.
Tafiyar sarkin yaki ke da wuya sai sarki Barham
ya kira wani babban hadiminsa wanda ake kira
zilla ya umurceshi da yaje yasa ayi shelar
wannan gasa da za'a yi a fada a gobe kuma ana
gayyatar kowa da kowa birni da kauye.
Nan take kuwa zilla yaje ya cika umurni,
Lokacin da mutanen gari suka ji wannan shela
sai aka cika da tsananin mamaki domin a tarihin
masarautar ba'a taba shirya gasa ba akan zaben
sarkin yaki.
Kawai sarki ne yake duba cancanta ya zabarwa
kansa sarkin yaki,
Lokacinda kalmaru yaji ansa gasa tsakaninsa da
dan uwansa Hamsaru akan takarar kujerar sarkin
yaki sai hankalinsa ya dugunzuma ainun don
haka sai ya shiga cikin turakar sarkin yaki ya
sameshi kuwa a zaune yayi tagumi yana tunani.
Kalmaru ya xauna daf da sarkin yaki ya dubeshi
cikin alamun tsananin damuwa yace,,
''ya kai Abbana saboda me kana raye da lafiyarka
kuma kanaji kana gani zaka bari a aiwatar da
abinda zai haddasa gaba tsakanina da dan
uwana Hamsaru kuma ya lalata zumuncin dake
tsakanika da dan uwanka?''
Ina mai rokonka daka hanzarta komawa yau
wajen sarki ka nemi alfarma a janye wannan
gasa,
Ni kam na hakura na baiwa dan uwana Hamsaru
wannan kujera.
Shin ka manta ne da halin mahaifin Hamsaru? ''
Akan Hamsaru ya mallaki wannan matsayi babu
abinda baxai iya ba koda kuwa sai ta kai cewa
an hallakani ko kai an hallaka ka''
Koda jin wannan batu sai hawaye ya zubowa
sarkin yaki, ya dubi kalmaru yace,,
''ya kai dana kayi sani cewa bakin alkalami ya
bushe.
Domin babu abinda zanyi wanda zai sa sarki ya
janye batun wannan gasa,
Hakika so sone amma son kai yana gaba da
komai ,
Babu yadda za'ayi naso wani ya gajeni face kai,
Kawai kaje ka fara shirye-shiryen wannan gasa
da za'a yi gobe,
Wanda keda rabo a cikin ku shine zai gajeni,,
Daga yanzu zuwa gobe ka tsare kanka domin
za'a iya yunkurin cutar dakai ko kuma a
hallakaka.
Na sallameka kuma banason naji wani korafi
daga bakinka,
Cikin alamun tsananin damuwa kalmaru ya juya
ya fice daga cikin turakar sarkin yaki.
******
AL'AMARIN Hamsaru kuwa lokacin da yaji cewar
sarki ya shirya gasa tsakaninsa da dan uwansa
kalmaru akan zaben sarkin yaki bisa cewar duk
wanda ya kai wani kasa shine zai sami mukami
sai ya kamu da tsananin farinciki sbd yana ganin
cewa tunda yafi kalmaru karfi da iya yaki dole ne
ya sami nasara lashe gasar sarkin yaki.
Kai tsaye Hamsaru ya wuce izuwa cikin gidansu
fuskarsa cike da walwala da annuri,
Yana isa turakar mahaifinsa sai ya iske
mahaifinsa da mahaifiyarsa a zaune sunyi jugum-
jugum kamar anyi mutuwa.
Al'amarin da yai matukar baiwa Hamsaru
mamaki kenan ya dubesu cikin damuwa yace,,
''yaku iyayena menene kuma ya faru haka na
ganku acikin yanayin damuwa?
Dajin wannan tambaya sai mahaifiyarsa ta dago
kai tace,, ''ya kai Hamsaru sbd me ba zamu
kasance a cikin tsananin damuwa ba alhalin mun
kwallafa burin mu gaba daya akan gasar da za
kayi gobe kuma gashi bamuda tabbacin cewa
zaka lashe gasar,
Koda jin haka sai mamaki ya sake turnike
Hamsaru yace,
Me kike nupi da cewar burinku yana kan wannan
gasa da zanyi kuma sbd Me kuke shakkar
nasarata alhalin kunsan cewa nafi kalmaru karfi
da iya yaki,
Dajin haka sai YUNARU mahaifin Hamsaru ya
numfasa ya dubeshi yace,
Kai yanzu kana ganin cewa zaka iya kai kalmaru
kasa ne da karfin damtsenka da iya yakin ka?"
To ka sauya tunani tunda wuri domin kuwa idan
bamuyi amfani da yaudara ko ha'inci babu yadda
za'ayi ka sami nasara akan kalmaru sbd ya fika
naci da juriya,
Ina mai tabbatar maka da cewa zai iya jure duk
irin wani sara da sukan da zaka rinka kai masa
gami da naushi da bugun hannu da kafa har
izuwa lokaci mai dan tsawo sa'adda zaka gaji ya
sami nasara akan ka. MAZA SUN FADI!!! Part 3

Na fuskanci cewar har yanzu kana shakkar abinda
nake fada maka,
Shin kun taba yin gurmuzun da ya kai na rabin
sa'a kai dashi a yayin da kuke baiwa juna horo? "
Koda jin wannan tambaya sai jikin Hamsaru yayi
sanyi yace,
Ai bamu taba yin gurmuzun da yakai na tsawon
dakika dari biyu ba ni dashi,
YUNARU yayi dan guntun murmushi yace,
Shiyasa ba zaka taba fahimtar bam-bamcinka
dashi ba, ai kallon kitse kake yiwa rogo.
Na rantse da darajar iyayena bazaka iya kai
kalmaru kasa ba domin ya gado kakanmu a
tsananin juriya da naci,
Hatta yanayin jikinsa da sifofin jikinsu duk iri
daya ne,
Har kakanmu ya bar duniya ba'a taba samun
jarumin da ya kai shi kasa ba kuma komai yawan
dakaru shi kadai yana iya tarwatsa su,
Hakika MAZA SUN FADI!!!
Inda ace kakanmu har yanzu yana raye a doron
kasa a wannan zamani kuma yana cikin koshin
lfy da rashin cutar tsufa irin wacce ta kama dan
uwana sarkin yaki a yanzu da zai iya mulkar
duniya Gaba daya,
abu daya nake tsoro.
Wani boka ya tabbar mini da cewa idan har
kalmaru ya yi aure to zai iya haihuwa dan da zai
sami gagarumin karfi irin na kakanmu kuma xai
iya mulkar duniya Gaba daya.
''Ya kai dana kayi sani cewa dole sai idan ka
lashe wannan gasa akan kalmaru sannan zamu
iya hanashi yin aure bare har ya haifi dan da zai
mulki duniya."
Sa'adda YUNARU yazo nan a zancensa sai kan
Hamsaru ya sake daurewa yace,, Ta yaya zaka
iya hana kalmaru yin aure ta hanyar amfani da
karfin kujerata ta sarkin yaki? "
YUNARU ya sake yin murmushi a karo na biyu
yace,, "kada ka damu zaka sani nan gaba idan ka
hau kan kujerarka.
Abinda nake da kai shine , ka kwantar da
hankalinka tuni na gama tunani akan yadda zaka
sami nasara akan kalmaru ka kaishi kasa kuwa a
daren yau zangama shirina,
Kaje kayi kwanciyarka kasha barcinka,
Kada ka wahalarda kanka wajen kokarin baiwa
kanka horon yaki a yau sbd gasar ta gobe,
Dajin haka sai Hamsaru ya mike tsaye ya fice
daga cikin fallon ya tafi izuwa dakinsa yana mai
mamaki zullumi gamida tunanin irin abin da
mahaifin nasa xai shirya don tabbatarda samun
nasararsa a Wannnan gasa,
Har izuwa wannan lokaci Hamsaru bayajin
shakkar komai a cikin zuciyarsa bisa fuskantar
kalmaru,
Abin da Hamsaru baisaniba shine,
Kalmaru baya sakin jikinsa da karfinsa gaba daya
a duk sa'adda zasuyi gurmuzun sbd yana
girmamashi Amatsayinsa na yayansa wanda ya
girmeshi a shekara
*****
LOKACIN da kalmaru ya isa turakarsa sai ya iske
mai kula da abincinsa wata baiwa mai suna
ZULAIMA ta shirya masa abincinsa akan tebur ta
kawo ruwan inibi acikin tulu ta ajiye,
Zulaima tsohuwa ce wadda shekarunta sun haura
saba'in,
Tun kalmaru baifi shekara shidda ba a duniya
Zulaima take rainonsa sakamakon mutuwar
mahaifiyarsa har kalmaru ya girma bai san
uwarsa ba sai Zulaima domin itace take masa
komai kamar yadda kowace uwa keyiwa danta,
Kalmaru da Zulaima sun shaku ainun kuma sun
yarda da juna ainun,
Shi kansa sarkin yaki ya yarda da Zulaima dari
bisa dari domin tun tana budurwa ya siyeta a
matsayin baiwa har yazo ya 'yantata amma wani
abu bai taba shiga tsakaninsu ba domin ya
dauketa tamkar 'yar cikinsa,
Duk da cewa ya yantata sai ta kasa tafiya ta
barshi, tayi alkawarin zata zauna tare dashi har
izuwa karshen rayuwata tana yi masa bauta gami
da kula da dansa guda daya jal! Wato kalmaru,
Lokacin da sarkin yaki yaji wannan batu na
Zulaima sai ya cika tsananin mamaki yace, yake
Zulaima kiyi sani cewa ni tunda nake ban taba
ganin bawan da aka yanta shiba amma ya ki
karba 'yancinsa ba sai ke.
Sbd me kika zabi ki karar da rayuwarki a cikin
bauta? "
Koda jin wannan tambaya sai hawaye ya zubowa
Zulaima tace,,
''ya shugabana kayi sani cewa tun inada shekara
tara a duniya 'yan hari suka shigo birninmu suka
kashe iyayena da dukkan mutanen garinmu,
A sannan ne aka kamani a matsayin baiwa aka
tafi dani aka siyar dani a can wata Nahiyar
daban,
Haka akayi ta yawo dani kasa-kasa har aka
kawoni nan birninku na ZAMAR ka siyeni,
Bani da kowa a yanzu kuma bani da komai sai
kai.
Na daukeka tamkar mahaifina domin kaine ka
debe mini kewar iyayena, haka kuma gashi na
shaku da danka kalmaru ina kallonsa tamkar dan
cikina duk da cewa ni ban taba yin aure ba bare
ma na haihu,
Idan na tafi na barku da wa zan ci gaba da
rayuwa wanda xai aminta dani kamar yadda kuka
aminta dani?"
Koda Zulaima tazo nan a zancenta sai tausayinta
ya turnuke sarkin yaki har kwallah ta cika masa
idanunsa ya rungume Zulaima yana mai Cewa ni
kaina idan kika tafi kika barni zan zamo acikin
tsananin takaici bakin ciki da tunani domin kin
zama tamkar jinina"
Daga wannan rana Zulaima taci gaba da zama a
gidan sarkin yaki cikin kwanciyar hankali da
nutsuwa.
Kamar yadda Zulaima ta saba a koda yaushe
lokacin da taga kalmaru ya shigo cikin turakar sai
tayi masa barka da zuwa kuma ta janyo masa
kujera daga karkashin tebur domin ya zauna yaci
abinci,
Cikin sanyi jiki kalmaru ya zauna a kujerar,
Koda ya dago kai ya hada ido da Zulaima sai
yaga idanunta sun kada sunyi jawur kuma sun
ciko da kwallah,
Al'amarin da yai matukar bashi mamaki kenan
kuma ya dugunzuma hankalinsa ya dubeta yace,,
'' yake Zulaima menene ya faru da a gareki har
naga kwallah a idanunki?"
Kamata yayi yau ace kina cikin tsantar farin ciki
bisa abinda xai sameni gobe idan na lashe gasar
da za'a yi tsakanina da dan uwana Hamsaru."
Koda jin wannan tambaya sai jikin Zulaima yyi
sanyi ta zauna akan kujerar dake fuskarta
kalmaru tace, ya shugabana kayi sani cewa tun
kafin mahaifiyarka ta rasu ta damka amanarka a
hannuna,
Amma yanzu gashi inaji ina gani bazan iya kare
rayuwarka ba tunda gobe zakayi wannan gasa
mai mugun hadari wacce zaka iya rasa
rayuwaka."
Koda jin haka kalmaru yayi dariya yace, haba
Zulaima ai indai dan Wannnan dalilin ne kika
tashi hankalinki to ki cire dukkan damuwa,
Ina mai tabbatar miki cewa babu abinda zai
sameni koda kuwa Hamsaru yakaini kasa,
Sa'adda kalmaru yaxo nan a jawabinsa sai
Zulaima ta fashe da matsainacin kuka ta mike
tseye zumbur ta ruga da gudu izuwa cikin
dakinta ta turo kofa ta rufe,
Cikin tsananin tashin hankali kalmaru ya mike
tsaye ya ruga izuwa kofar dakin na Zulaima ya
rinka kwankwasa kofar yana kiran sunanta kuma
yana rokonta akan ta bude kofar amma sai taki
bude kofar kawai taci gaba da rusa kuka.
Al'amarin da yai matukar baiwa kalmaru mamaki
kenan kuma ya jefashi a cikin zullumi,
''To wai shin anya kuwa babu wani boyayyen
al'amari dake shirin faruwa wanda Zulaima ta
boye masa?" MAZA SUN FADI!!! Part 4

" To wai shin anya kuwa babu wani boyayyen
al'amari dake shirin faruwa wanda Zulaima ta
boye mini? "
Amsar da kalmaru ya kasa baiwa kansa kenan,
Ya Juya ya koma izuwa kan tebur ya zauna ya
cigaba da cin abincisa har sai da yaji koshi
sannnan ya zuba wannan ruwan inibin a cikin kofi
har ya kai bakinsa xai kurba sai ya fasa
sakamakon ganin sauyin yanayi acikin ruwan
inibin,
Wannnan karon launin ruwan inibi ya dan sauya,
Kalmaru yai shiru yana tunani yace a ransa,
" yau kuma me Zulaima ta kara acikin ruwan
inibin nan?"
To menene ma zan damu tunda na tabbatarda
cewa babu yadda za'ayi Zulaima ta cutar dani ko
kuma a hada baki da ita a cutar dani.
Yana gama fadin hakan sai yasa kofin a bakinsa
ya kama sha.
Nan da nan ya shanye kofin guda ya sake
karawa har sai da ya shanye kofi shidda sannan
mike tsaye ya shige cikin dakinsa ya baje akan
gado ya kama barci.
Kashe gari da sassafe sarkin yaki ya tashi ya
kimtsa domin yanason ya raka kalmaru izuwa
fada domin ayi wannan gasa agaban idanunsa,
Yana shiga cikin dakin kalmaru sai ya cika da
mamaki domin ganinsa yayi a kwance yana ta
faman sharar barci.
Cikin fushi sarkin yaki ya daka masa tsawa da
karfi,
Afirgice kalmaru ya farka firgigit! Ya mike zaune
yana mai bude idanunsa da kyar!
Yana mika.
Kawai sai yaji wani irin rashin kuzari a jikinsa
wanda bai taba jin irinsa ba,
Sarkin yaki yace,
" Baka da hankali ne da zaka kwanta kayita
sharar bacci gashi har rana ta fito Alhalin kasan
cewa yau ne zakayi gasar neman kujerata? "
Cikin alamun damuwa kalmaru ya dubi sarkin
yaki yace,
" ka gafarceni ya kai Abbana ni kaina nayi
mamakin ganin yadda akayi na makara kuma
yanzu ma dana tashi sai naji Inajin muguwar
kasala."
Koda jin haka sarkin yaki ya dubi kalmaru cikin
firgici da tsananin damuwa yace,
"shin kafin ka shigo gida wani ya baka wani abu
ne kaci?
Kalmaru yace " ai ban yarda naci komai ba sai da
nazo nan gida sbd na kiyaye gargadin da kayi
mini."
Sarkin yaki ya gyada kai yace, shi kenan maza
kaje ka kimtsa zan jiraka a falo kazo muyi kalaci
tare sannan mu tafi fada.
Na tabbatarda cewa yanzu haka fada ta cika
makil,
Banason muje a makare bayan sarki ya fito
domin laifi ne babba."
Dajin haka sai kalmaru ya sauko daga kan
gadonsa da sauri ya shiga kewaye yayi wanka.
Har kalmaru ya gama wankan ya sanya kayan
yaki ya dauki takobinsa da kufe bai daina jin
wannan rashin kuzari ba a jikinsa,
Sai ya dangana al'amarin da yunwa tunda jiya da
daddare ma bai tsaya yaci wani abinci ba mai
yawa ba,
da wannan ruwan inibin ya cika cikinsa,
Yana zuwa ya iske sarkin yaki a zaune ga abincin
kalaci bisa tebur a gabansa,
Kalmaru yaje ya zauna akan kujerar dake
fuskarta ta mahaifin tasa suka bude kwanukan
abinci suka fara ci.
A daidai Wannnan lokaci ne Zulaima ta kawo
musu shayi a cikin buta bisa kan faranti dauke da
kofuna biyu,
Zulaima ta a ajiye farantin shayin a tsakiyarsu
sannnan ta juya zata koma cikin dakinta,
Sai sarkin yaki ya kira sunanta ta waigo, ya
dubeta yace,
"yake Zulaima wai shin menene yake damunki ne
jiya cikin dare na jiyo shesshekar kukanki daga
cikin dakina.
Yanzu ma da kika zo gabana naga alamun kinsha
kuka da safen nan domin ga idanunki nan sunyi
jawur.
Yanzu ashe har akwai wani abu da zai dameki ki
kasa sanar dani?"
Sarkin yaki ya dubi kalmaru yace, ko kai ta
gayamaka abinda ke damunta?"
Kalmaru ya gyada kai yace , bata gaya mini
komai ba. "
Koda jin haka sai Zulaima ta sunkai da kanta
kasa tace,
Tun jiya da naji za'ayi wannan gasa ne hankalina
ya tashi na rasa sukuni harma jiya cikin barcina
sai da nayi mafarki mai ban tsoro.
Dajin haka sai sarkin yaki yai murmushi yace, "in
dai don wannan ne ki kwantarda hankalinki babu
wani abin damuwa,
Ina mai tabbatar miki da cewa kalmaru zaije yayi
wannan gasa lfy kuma zai dawo gida lafiya cikin
nasara.
Maza kije kici gaba da yan
DOWNLOAD
DOWNLOAD

1 Comments On MAZA SUN FADI 1 to 4
avatar
abubakar-abdullahi-6

3 months ago

Reply

yes

Please Login or Register in order to submit comment