Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shiga bashi baki sannnan ya dawo
cikin haiyacinsa amma duk da haka sai da ya
yunkura ya mike zaune ya sake yunkurawa zai
mike tsaye yana mai cewa akaishi wajen gawar
mahaifinsa,
A wannan Lokacin kansa a kumbure yake sumtun
kuma gaba dayan jikinsa ya dume da zazzabi,
Kwatsam sai ga likitansa ya shigo da sauri cikin
tantin da zuwansa sai ya dubi sarki Daryan ya
duddubi ko ina a jikinsa cikin alamun tashin
hankali yace ya shugabana jinin jikinka ya zuba da
yawa dole ne ka kwanta muyi maka aiki sossai
mu baka magani kasha, inba haka ba kuwa zaka
iya rasa rayuwarka,
Koda jin wannnan batu sai bakin ciki ya kara
turnuke sarki Daryan a Lokacin da hawaye ya
zubo masa sannnan ya dubi Sarkin yakinsa wanda
ake kira da suna Balwaz yace ayi shirin komawa
gida domin muje mu binne mahaifina bisa al'ada
da addininmu kamar yadda aka saba.
Sarkin yaki Balwaz ya risina yace an gama ya
shugana, nan take Sarkin yaki Balwaz ya juya ya
fice daga cikin tantin shi kuma sarki Daryan sai
ya koma ya kwanta akan shimfidar tasa likitoci
suka kama aikinsu.
Bayan likitan Kalmaru ya gama yi masa aiki an
dinke raunikan dake jikinsa an shafa masa magani
kuma an bashi wadansu magunguna kusan kala
shida yasha sai idanunsa suka fara lumshewa
alamar cewar barci zai yi don haka sai kowa ya
fice daga cikin tantin aka barshi shi kadai domin
ya sami nutsuwa yin barcin sossai.
A can gaban sansanin nasu kuwa gimbiya lazima
ce a tsaye tare da dakaru sun zuba ido Izuwa can
sansanin abokan gaba ko zasu ga an taho kawo
musu sabon hari, tsawon kusan rabin sa'a shiru
basuji motsin kowa ba don haka sai gimbiya
lazima ta tashi dan leken asiri guda daya tace
dashi yaje ya gano musu halin da abokan gaba ke
ciki nan take kuwa wannnan dan leken asiri yayi
wata irin shiga wacce ta saje da kalar kasar dajin
ya ruga Izuwa inda sansanin abokan gabar suke.
Jim kadan sai ga dan leken asirin ya dawo a
nutse cikin kwanciyar hankali, da zuwansa gaban
lazima sai ya risina yace ya shugabata ai tuni
abokan gaba sun hada nasu da nasu sun juya sun
nufi birninsu.
Koda jin haka sai wani babban badakare ya dubi
lazima cikin murna yace ya shugabata ai wannan
wata babbar dama ce muka samu da zamu bisu a
baya mu kai musu harin bazato mu gama dasu
cikin abinda bai wuce sa'a biyu ba,
Koda jin haka sai gimbiya lazima ta dubi
badakaren a fusace tana mai daka masa tsawa
tace tabbas bakada hankali kuma bakada wayo,
Ashe baka san cewa ba a tsokanar mahaukacin
kare ba, shin ka manta ne cewa yanxu sarki
Daryan yana cikin tsananin fushi da bakin ciki
bisa rashin mahaifinsa,
Idan kuma wani tarkon ya shirya mana fa ta
hanyar nuna sun janye yakin? Ni 'yace kuma
nasan irin zafin da zanji idan na rasa mahaifina,
yana da kyau a kyale sarki Daryan yaje gida ya
binne mahaifinsa cikin nutsuwa domin Hakan
zaisa zuciyarsa tayi sanyi,
Idan yana zaton zai iya gamawa da mu farat daya
yanzu ya gane ba haka bane mu ma kuma mun
gane cewa karo dashi ba wasa bane,tunda dai
yanxu mun tabbatar da cewar abokan gabarmu
sun janye daga filin yaki muma sai mu gaggauta
kwashe namu inamu mu juya domin mu koma
kasarmu da wuri muga halin da take ciki.
Ba tare da gardamar komai ba kuwa dakaru
sukabi umurnin gimbiya lazima aka kwashe komai
daga filin yakin aka kama hanyar zuwa birnin
zamar.
Wannnan karon dai Sarkin yaki Kalmaru akasa a
cikin keken dokin gimbiya lazima kuma itace taci
gaba da jinyarsa ko tari yayi sai ta tambayeshi ko
akwai wani abu yake bukata,
Kai hatta su kansu likitocin basu kaita yi masa
hidima ba,
Kalmaru bai soma jin kwarin jikinsa ba har sai da
kwanaki biyu suka shude,sannnan ne ya fara iya
mikewa tsaye daga kwance amma tafiya ma baya
iya yinta har sai lazima ta taimaka masa ta dora
hannunsa a kafadarta ta talabi kugunsa a haka
take rakashi inda zai je ya kawarda bukata,
Al'amarin da ya daurewa dakuru kai kenan suka
fara zargin anya kuwa babu soyayya tsakanin
Sarkin yaki Kalmaru da gimbiya lazima?
Ba komai ne ya sasu wannan zargi ba face ganin
cewa ita fa gimbiya lazima 'yar sarkinsa ce wadda
babu kamarta a fagen kyau a gaba daya birnin
zamar kuma babu wani da namiji da ya taba
kusantarta haka sai shi Kalmaru barema har
jikinsa ya taba nata amma gashi ita da kanta take
kusantarshi tana hada jikinsa da nata a matsayin
mai jiyarsa bisa rashin Lafiya.
A ranar kwana na uku a yada zango a bakin wata
korama cikin wani daji mai yawan ni'ima sai
Kalmaru ya mike tsaye yana mai dogara wata
santa ya nufi inda karshen karamar take ya baro
inda gimbiya lazima take tare da sauran dakaru, a
wannan Lokaci an baje abinci ana ci amma shi
Kalmaru ko loma daya baiyi ba ya tashi ya bar
abinci.
Al'amarin da ya baiwa kowa mamaki kenan, koda
ganin haka sai gimbiya lazima ma ta mike tsam ta
baro nata abinci a cikin tantinta ta nufi inda
Kalmaru yake inda suka nisanta da sauran dakaru,
Koda Kalmaru yaji motsi a bayansa ya waigo da
sauri don ganin mai zuwa,sa'adda yaga ashe
lazima ce fuskarta cike da annuri da murmushi
mai dimauta da namiji sai yaji zuciyarsa ta
baaQquga da karfi, nan take yaji ya kamu da
tsananin sonta fiye da koyaushe,
Kawai sai ya risina da nufin ya kwashi
gaisuwa,cikin hanzari ta karaso gareshi ta rike
kafadunsa ta tasheshi tsaye tace haba ya kai
dirkar birnina ai yanxu kuma ka wuce matsayin ka
rinka risina mini tunda kai ne na uku a cikin
majalisar birnin zamar tunda daga sarki sai waziri
kuma sai kai.
Koda jin haka sai Kalmaru yayi murmushi yace ai
duk da haka kina gaba dani tunda ke yar sarki ce,
nan gaba zaki iya zama sarauniya ta kuma dole
ne nayi bauta da biyayya a gareki,
Ya shugabata naji dadi da kika zi nan inda zan iya
isar da sakon godiyata a gareki bisa ceton
rayuwata da kikayi daga hannun sarki Daryan,
tabbas kin bani mamaki kuma kin baiwa duk
dakarunmu mamaki domin babu wanda ya taba
zaton cewa kema jarumace haka, Nayi matukar
farin ciki da kika boye kanki ga abokan gabarmu
amma kuma banso jama'armu suka san cewa ke
jaruma ce ba saboda wani abu da zai iya faruwa
nan gaba bayan mun koma gida.
Cikin mamaki lazima ta dubi Kalmaru tace wane
abu ne kuma zai biyo baya saboda sanin
matsayina na iya yaki?"
Kalmaru ya numfasa yace kiyi hakuri ba zan iya
gayamiki amsar wannan tambaya ba taki a yanzu
amma idan kika zuba ido zaki ga amsar da
idanunki, ya shugabata inaso ki sani cewa na yi
matukar bakin ciki mara adadi bisa rashin samun
nasararmu a wannan yaki a matsayina na Sarkin
yaki kuma a matsayin farkon fitowata yaki,
Tabbas kunya da bakin ciki zasu addabi zuciyata
har Izuwa ranar da zan wanke gazawata na ciyo
nasarar wani yakin,
Ko kadan ban taba zaton cewa zan fuskanci
wannan matsala ba.
Lokacin da gimbiya lazima taji wannan batu sai ta
bushe da dariya, Al'amarin da yayi matukar baiwa
jarumi Kalmaru mamaki kenan yace menene kuma
ya baki dariya? "
Lazima ta dubeshi cikin nutsuwa sannnan tace ai
kai ne kuwa ka sami babbar nasara a wannan yaki
tunda har ka cika babban burin mahaifinka ka
kashe tsohon makiyinsa wato sarki saumir
mahaifin sarki Daryan, bisa wannan daliline ma
nayi maka wani babban tanadi wanda ka manta
dashi kuma wannan tanadi abune mai darajar
gaske domin a duk fadin kasar su sarki Daryan da
fadin mulkinsa babu abinda ya fishi daraja.
Cikin tsananin mamaki ya Kalmaru ya sake duban
lazima yace wane abune kuwa wannan wanda ban
sanshi ba?
Koda jin wannnan tambaya sai lazima ta zaro
wata kyakkyawar takobi daga cikin rigarta, ita dai
wannan takobi kufen ta ma da zallan lu'u lu'u
akayi shi, ita kuma takobin anyita ne da zallar
farin karfen lu'u lu'u. Masana kyalkyali da
makeran duniya sun tabbatar da cewa ba a taba
yin takobi mai kyau, daraja da tsadar wannan
takobi ba,
Bakowane keda mallakin wannan takobi ba face
marigayi sarki saumir.
Kalmaru ya karbi takobin yana mai kura mata
idanu cikin tsananin al'ajabi harma ya zarato daga
cikin kufenta, take haskenta ya dallare masa
idanu kuma ya haskake gaba dayan wajen da
suke tsaye.
Lazima ta dubi Kalmaru tace a cikin bincikena da
karance karancena na samo tarihin wannan takobi
kuma asalinta ta Sarkin farko ce wanda ya fara
mulki a birninsu sarki Daryan, ance babu mai
mallakar wannan takobi face jarumin da zai sami
daukakar da babu kamarta a zamaninsa kuma
dole ne ya kashe mai mallakar takobin Kafin ya
iya amfani da ita,
Ita dai wannan takobi sirrinta shine in dai
mamallakinta yana raye kuma yana tare da ita
koyaushe a jikinsa to har abada baza'a ci birninsa
da yaki ba, kaga kenan yanzu idan sarki Daryan ya
nemi wannan takobi ajikin gawar mahaifinsa ya
rasa hankalinsa zai dugunzuma ainun fiye da
koyaushe ya shiga farautarka dare da rana,
Duk wanda ya mallaki wannan takobi dole ne yayi
nisan kwana a duniya bisa wannan daliline sarki
saumir ya shekara Dari da Ashirin da uku a duniya
sai a wannan yaki ne ka zare masa ruhin
numfashinsa.
** ** ** MAZA SUN FADI!!! LITTAFI NA 4 PArt 3

Duk wanda ya mallaki wannan takobi dole ne yayi
nisan kwana a duniya, bisa wan
nan daliline sarki
saumir ya shekara Dari da Ashirin da uku a duniya
sai a wannan yaki ne ka zare masa ruhin
numfashinsa.
Koda gimbiya lazima tazo nan a zancenta sai
hannun Kalmaru ya kama karkarwa yayi sauri ya
mika mata takobin yace ungo rike ta bazan iya
ajiye taba a wajena,
Cikin mamaki lazima tace saboda me ba zakaka
iya ajiye ta ba a wajenka?"
Sa'adda Kalmaru yaji wannan tambaya sai yayi
ajiyar zuciya sannnan yace ina tsoron kada a
dalilin wannan takobi dake hannuna mutane da
yawa su rasa rayuwarsu,
Na sami labari cewar babu abinda sarki Daryan
bazai iya ba akan bukatarsa,tun muna yara da ya
kullaceni har yanzu wannan gaba mai tsanani
tana nan a ransa kuma koda anyi sulhun yaki
tsakanin kasarmu da tasa, ba zai daina gaba dani
ba face yaga karshen kiyayyar tamu,
Ni bana tsoronsa ko shakkarsa amma ina tsoron
abinda zai sami duk wanda ya rabeni,
Yayin da lazima taji wannan batu sai tayi
murmushi tace ai tunda kasan da hakan dole ne
yanzu ka tsananta tsaro a kanta da duk
makusantanka,
Inaso ka sani cewa babuwanda zai iya ajiye
wannan takobi ta ajiyu face kai domin duk wanda
ya barta a wajensa har tayi sa'a goma sha biyu
takobin ce zata zamo ajalinsa kuma ta bace bat
ta koma hannun mamallakinta in yana raye in
kuma baya raye sai ta koma wajen wanda ya
kasheshi,
Kaga dai kenan baka isa ka guji wannan takobi ba
, ko kana so ko kana ki a duk inda kake sai ta
bika babu mai iya rabaka da ita face sarki Daryan
domin a sirrin da aka yiwa takobin jinin gidansu
ne kadai zasu iya mallakarta su zauna Lafiya,
Abinda yasa na dauko maka wannan takobi daga
jikin gawar sarki saumir shine idan har kajewa
mahaifina da mahaifinka ita sukayi arba da ita
zasu yi farin ciki marar misaltuwa tunda kayi
abinda ya gagaresu tsawon shekara da shekaru
zasu ji tamkar ka ciyo nasarar wannan yaki ne
kuma zasu kara girmamaka su sallamawa
jarumtakarka don ba a taba zaton cewa akwai
jarumin da zai iya kashe sarki saumir ba.
Lokacin da gimbiya lazima tazo nan a jawabinta
sai jikin Kalmaru yayi sanyi sossai ya karbi
wannan takobi daga hannunta saboda yayi imani
da abinda ta gaya masa a kan takobin sannnan ya
boye takobin a cikin rigarsa yayi shiru bai kara
cewa uffan ba.
Nan dai suka baro inda suke tsaye yana dogara
sandar dake hannunsa suna tafiya a hankali har
suka dawo inda suka bar dakaru, kowannensu ya
shige cikin tantinsa.
A can birnin sarki Daryan kuwa Lokacin da ya
dawo gida tare da rundunarsa ta yaki sai mutanen
gari da fadawansa suka taru taru a fada akayi
jugum jugum saboda bisa babban rashin da akayi
wato mutuwar saumir mahaifin sarki Daryan,
Tun kafin rundunar ta iso gari jikin jama'a yayi
sanyi saboda angane cewa lallai ba lafiya ba,
Dalilai kuwa shine duk sa'adda aka dawo daga
yaki tun daga can wajen gari za'a ji ana buga
tambura kuma ana busa algaita alamar cewar an
dawo cikin nasara ko kuma anyi ragas,
Wannan karon kuwa ko da rundunar ta kusanto
gari sai akaji ana buga gangar bakin ciki guda
daya jal.
Duk sa'adda akaji sautin wannan ganga na tashi
to dole ne cikin abu uku daya ya faru,kodai wani
babban mutum ya mutu ko kuma an fadi yaki ko
kuma anyi asarar dukiya mai yawan gaske.
Koda aka budewa rundunar yaki kofar gari suka
shigo babu abinda mutane suka fara yi arba dashi
face gawar sarki saumir,
Ai kuwa nan take garin ya kaure da koke koke,
babu wanda zaka tausayawa a wannan Lokaci
sama da sarki Daryan domin kuka yake yi tayi
kashirban kamar ransa zai fita,
Kai har sai da ma ya rinka shidewa numfashinsa
na sarkewa.
Koda likitansa ya lura da halin da yake ciki sai
yayi sauri ya bashi maganin bacci,
Ko dakika biyar ba'ayi ba barcin ya saceshi, sai
akayi sauri aka saukeshi daga kan dokinsa aka
darashi akan wata karamar karaga aka shige
dashi cikin gidan sarautar,
Sarki Daryan bai farka daga bacci ba sai da ya
kwana ya yini yana bacci, yana farkawa ya tsinci
kansa a gado.
A firgice ya mike zaune kawai sai yayi arba da
likitansa zaune a gefen gaddon daf dashi ga
abinci iri iri da ruwan magani,
Abinda ya fara fitowa daga bakin sarki Daryan
shine ina gawar mahaifina? "
Yana gama fadin Hakan sai ya mike zumbur da
nufin ya fice ya tafi wajen gawar a Lokacin da
hawaye ya zubo masa,
Cikin hanzari likitan ya sha gabansa ya dubeshi
yace ya shugabana shin bakason ka dauki fansa
ne akan wanda ya kashe maka mahaifinka, so
kake kaima kabi mahaifin naka?"
Koda jin wannnan tambaya sai jikin sarki Daryan
yayi sanyi ya koma ya zauna a kan gadon yaci
gaba da zubarda hawaye,
A sannnan ne likitan ya tafa hannayensa sai ga
wata amintaciyar kuyanga mai suna Afila ta shigo
cikin turakar, take likitan yayi mata inkiya ta
zauna kusa da sarki Daryan ta shiga bashi abinci
yana ci har sai da taga ya koshi sannnan kuma ta
bashi ruwan wadanan magunguna ya shanyesu
duka faruwar hakan keda wuya sai sarki Daryan
yaji karfin jikinsa ya dawo tamkar bai taba wata
jinya ba,
Nan take ya tura aka kirawo wani babban
hadiminsa ya bashi umurnin yaje yasa a fara
shirye shiryen bikin binne mahaifinsa,
Nan take hadimin ya fice da sauri yaje ya cika
aiki, ai kuwa sai aka fara busa wani irin kaho mai
karar tsiya wanda ba'a busashi face idan sarki ne
ya mutu a garin, kuma nuni ne da cewar za'a fara
bikin binne gawar Sarkin,
Shi kuwa sarki Daryan sai ya shiga kewaye ya
kwanta a cikin bahon wankansa,
Kuyangi suka yi masa wanka sannnan ya fito ya
sanya bakaken tufafi ya nufi wani babban fili dake
tsakiyar gidan sarautar inda kabarurrukan
sarakunan da suka shude suke,
Yana isa wannan wuri ya iske an kawo gawar
sarki saumir a cikin wata akwatin zinare an ajiye
akan wani gini mai tudu, wadansu makadan
gargajiya sun kewaye gawar suna ta kida, a gefe
daya kuma mata da maza da bokayen kasar sun
taru suna ta tika rawa kowannensu na rike da
ganyen wata bishiya a hannu, wasunsu suna tayin
bori, har kumfa na fita daga cikin bakunansu suna
ta suratai na ambaton aljanunsu iri-iri, ta cikin
tsakiyar dandazon wadanan mutane sarki Daryan
ya kutsa ana ta buda masa hanya yana wucewa
har ya isa inda akwatin gawar taken,
Tun daga nesa ya kurawa fuskar gawa idanu ya
fara zubarda hawaye, da ya iso kan gawar sai ya
fada kanta ya rungumeta kuma ya fashe da
matsanancin kuka,
Sai da ya shafe kusan rabin sa'a a cikin wannan
hali sannnan ya tuno da batun takobin daraja,nan
take ya zura hannunsa cikin aljihun gawar ya
kama lalube amma sai yaji shiru, take ya tuno
wani abu da ya faru a filin yakin sa'adda ya
hango gawar mahaifinsa baje a kasa kuma rigarsa
ta Bude babu takobin daraja a cikinta,yana gama
wannan tunani sai ya dago kansa ya juyo da baya
ya dubi jama'ar dake wajen sannnan ya kwarara
uban ihu gamida kiran sunan takobin daraja,
Nan fa kowa ya gane dalilin ihun nasa kuma ba
komai bane face batan takobin daraja,
Cikin tsananin fushi sarki Daryan ya kwalawa
Sarkin yakinsa kira ya rugo Izuwa gabansa ya
zube kasa, sarki Daryan ya dubeshi yace maza
kaje ka zabo manyan dakarun leken asirinmu guda
goma suje su hada kai da wasu dakarun leken
asirin birnin warzas su shiga birnin zamar suyi
bincike su gano wanda ya sacewa ubana
takobinsa ta daraja,
Abu ne mawuyaci idan ma ba Kalmaru bane ya
sace wannnan takobi ba domin shi kadai ne zai
iya ajiyeta har Izuwa wannan Lokaci, inda wani ne
daban da tuni takobin ta hallaka shi ta dawo da
kanta nan.
Sa'adda Sarkin yaki yaji wannan batu sai ya mike
tsaye da sauri yace an gama ya shugabana
sannnan ya bar filin bikin binne gawar gaba daya,
Nan dai aka ci gaba da bikin binne gawar amma
sai da dare ya raba sannnan aka binne gawar
sannnan kowa ya kama gabansa aka watse.
Al'amarin birnin zamar kuwa sarki Barham na
zaune a fada kan karagarsa ta mulki sai ya mike
tsaye ya kama kai kawo cikin alamun tsananin
damuwa da kaguwa,
Ba komai ne ya jefashi cikin wannan hali ba face
rashin dawowar dakaru masu kibiya wadanda aka
tura su kashe sadauki Hamsaru da waziri.
Suma fadawan na sarki Barham hankalinsu a
tashe yake kuma basu da burin da yafu suji ance
ankawo su waziri ko kuma an kashe su,saboda
cin amanar kasa da suka yi da kuma janyo
sanadin asarar dubunnan rayuka.
Ana ckin wannan hali ne aka ga wadanan dakaru
'yan kubau sun dawo sun shiga cikin fadar da
sauri,da isowarsu sai shugabansu ya zube kasa
gaban sarki Barham ya risina cikin biyayya yace,
Ya shugabana kayi sani cewa munyi iya
kokarinmu wajen ganin mun riski su waziri amma
mun kasa duk da cewa muna ta harba musu
ruwan kibiyoyi saboda sun bamu tazara mai yawa
da kyar ma muke iya hango kurarsu, sannu a
hankali kuma sai muka fara amfani da sawayen
dawakansu, sa'adda muka iso dajin Sahara sai
sawajen dawakan nasu ya bace bat muna muka
nemishi muka rasa, duk da haka bamu daina
nemansu ba har sai da.......
Kafin ya gama fadin abinda ke bakinsa sai sarki
Barham ya tari numfashinsa yana mai daga masa
hannu yace ya isa ba sai ka karasa bayaninka ba
domun na fahimci cewar waziri da Hamsaru sun
yaudareku sun buya a cikin daji kuma sun boye
dawakansu ta hanyar amfani da tsofaffun dabarun
yaki.
koda gama fadin Hakan sai sarki Barham yasa
aka shirya masa doki ya hau, tsirarun dakaru suka
yi masa rakiya basu zame ko inaba sai kurkuku.
*** ****
Mu hadu anjima da dare don jin cigaban wannan
kasaitacen labari na maza sun fadi kashi na hudu MAZA SUN FADI!!! LITTAFI NA 4 PART 4

Koda gama fadin Hakan sai sarki Barham yasa
aka shirya masa doki ya hau, tsirarun dakaru suka
yi masa rakiya basu zame ko ina ba sai kurkuku.
Attajiri yunaru na zaune a cikin dakin da aka
kulleshi cikin tsananin farin ciki da murna domin
zatonsa saura 'yan dakiku kadan ya fice daga
cikin wannan kurkuku,
Kwatsam ba zato ba tsammani sai yaga sarki
Barham ya durfafoshi tare da tsirarun dakaru suna
take masa baya kuma fuskarsa cike da murmushi,
Nan take zuciyar yunaru ta buga da karfin gaske
ya tabbatar da cewar hakansu bai cimma ruwa
ba,
Sarki Barham ya iso daf da kofar tagar dakin da
yunaru ke ciki suka yi kallon kallo na taawon yan
dakiku sannnan sarki Barham ya sake yin
murmushi a gareshi a karo na biyu sannnan yace
ya kai yunaru babban Attajiri kayi sani cewa
ramin da kuka haka kai da danka da kuma dan
uwana waziri yayi zurfi da yawa don haka ba zaku
iya fitowa ba daga cikinsa kaga kenan ci gaban da
kuka samu iri daya ne dana mai hakan rijiya.
Koda jin wannnan batu sai fuskar attaji yunaru ta
juye Izuwa tsananin damuwa amma sai ya dubi
sarki Barham cikin nutsuwa yace, wace irin
nasara dakarunku suka samu a filin yaki?
Sarki Barham yace ai kamata yayi ka fara
tambayata irin nasarar da kuka samu a nan birnin
a kokarin yi mini juyin mulki kafin kaji wacce
muka samu a filin yaki.
Attajiri yunaru yayi dan guntun murmushi mai
nuna alamun rashin karayar zuciya yace ai na
sani cewa shirinmu na juyin mulki ya tarwatse
saboda inda bai tarwatse ba da yanzu ba zan
ganka ba a raye amma kuma na tabbatar da cewa
Baka dana da waziri ba kuma baka kamasu ba
domin ina da yakinin cewa baza ka taba samun
nasarar hakan ba a kansu, ko kasheni kasa akayi
yanzu banida sauran nadama muddin baku ne
kuka yi nasara ba a filin yaki domin na tabbatar
da cewar sai sarki Daryan ya shigo har cikin
garinan ya kasheka ya baiwa waziri karagarka ,a
sannnan ne nima zan kamo dan uwana tsohon
Sarkin yakinka na danneshi na yanka don na
kawar da tshohon bakin cikin daya dasa mini a
zuciyata,
Lokacin da yunaru yazo nan a zancensa sai sarki
Barham ya bushe da dariya yayi ta kyakyatawa
kamar ba zai daina ba, daga can kuma sai ya
tsuke bakinsa ga barin yin dariya sannnan ya dubi
cikin tsananin fushi yace, ya kai tsohon abokin
gaba kuma maci amanar kasa kayi sani cewa
bambanci dake tsakanin haske da duhu a baiyane
yake don haka har abada adali yana kan azzalumi,
Na yarda da Sarkin yaki Kalmaru dari bisa dari
don haka na tabbatar da cewa ba zai taba bani
kunya ba a wannnan yaki don haka ka saurari
dawowar su zakaji bakin labari mai daci wanda
zai kona zuciyarka da ranka gaba daya har sai
kaji kamar gwara mutuwarka da rayuwarka,
Danka Hamsaru da waziri sun sami nasarar
guduwa amma ka sani cewa zanci gaba da
farautarsu dare da rana bazan gaji ba har sai na
cafkesu kuma kaima bazan yanke maka hukuncin
komai ba har sai ka gama wa'adin kwanakin da
aka diba maka a cikin kurkukun bisa alkawarin
dana dauka a gaban jama'a.
Koda gama fadin Hakan sai sarki Barham ya juya
ya fice daga cikin kurkukun gaba daya yana mai
kyalkyala dariyar farin ciki har yana gwara kansa
akan sandunan karfen dake jikin tagar dakin kuma
yana kwarara uban ihu kai kace wata azaba akeyi
masa mai radadin gaske.
Da yammaci sakaliya rundunar yaki ta dawo birnin
zamar,
Tun kafin rundunar ta iso labari dawowarsu ya
riski sarki Barham don haka sai mike da sauri yayi
shiri tare da manyan fadawansa domin taryar su
Kalmaru,
Nan da nan su sarki Barham suka yi hawa suka
fice daga cikin birnin zamar. Tafiyar da sukayi
bata kai ta rabin sa'a ba suka hango rundunarsu
Kalmaru, nan take farin ciki ya kama sarki ya
bayar da umurnin a tsaya a jirasu Kalmaru su
karaso,
Take kowa yaja linzamin dokinsa aka yi cirko
cirko kuma aka zuba idanu akan hanya ana jiran
karasowarsu Kalmaru,
Lokacin da rundunarsu Kalmaru ta kusanto sai
fuskar sarki Barham ta sauya yanayi daga
walwala Izuwa damuwa,
Ba komai ne ya haddasa hakan ba face hango
'yarsa gimbiya lazima a cikin shigar yaki bisa doki
ta jero da Kalmaru sannnan kuma ya lura da cewa
akwai dinkin raunika da yawa a jikin Kalmaru
Al'amarin da yasa ya gane cewa lallai ba karamar
wahala Kalmaru yasha ba a wannnan yaki kuma
lallai akwai alamun nasara amma Abin tambaya
shi ne akan wane dalili lazima ta sanya kayan
yaki alhalin taje yakin ne da niyar kawai ta rubuta
duk abinda tagani, haka dai zuciyar sarki Barham
taci gaba da wasuwasi gamida zargin abubuwa da
yawa har su Kalmaru suka iso,
Nan take Sarki Barham ya sauko daga kan
dokinsa itama lazima sai ta sauko daga kan nata
dokin ta ruga Izuwa gareshi suka rungume juna
bisa farin ciki saduwa a Lokacin ne shima
Kalmaru ya sauko daga kan nasa dokin ya tsaya
yana kallonsu cikin murmushi,
Nan fa shima yaji yana sha'awar ace yayi aure
kuma ya sami 'ya ko da wanda zai kaunaceshi
kamar yadda sarki Barham da gimbiya lazima ke
tsananin kaunar juna.
Sai da sarki da lazima suka shafe yan dakiku
masu yawa a kankame da juna sannnan ya janye
jikinsa daga cikin nata ya dubeta yace hakika gani
ya kori ji domin tunda na ganki sanye da kayan
yaki nasan cewa ba karamar masifa akayi ba a
filin daga,
Tabbas yanzu kinga amfanin koya mike yakin
danayi tun kina yarinya karama
Banason naji labarin komai daga bakinki sai daga
bakin Sarkin yakina.
Koda gama fadin Hakan sai ya juya ya fuskanci
Kalmaru,
Kalmaru ya taho ga sarki da sauri ya zube kasa
bisa guiwarsa guda ya kwashi gaisuwa, sarki
Barham ya sunkuya ya kama kafadun Kalmaru ya
tashe shi tsaye suka fuskanci juna sossai yana
mai murmushi a gareshi sannnan yace ya kai
dirkar birnina ina matukar alfahari da kai saboda
nasan cewa ba zaka taba bani kunya ba yanzu
wane albishir kazo mini dashi bisa wannan yaki da
kikayi? "
Sa'adda Kalmaru yaji wannan tambaya sai ya
sunkui da kansa kasa yai shiru cikin alamun
karayar zuciya sannnan yace ya zura hannunsa
cikin rigarsa ya fiddo takobin daraja ya mikawa
sarki Barham da hannayensa biyu kansa na
sunkuye sai da sarki Barham ya dan ja da baya
cikin alamun razana da tsananin mamaki sannnan
kuma fuskarsa ta kama murmushi.
Sarki Barham ya matso daf da Kalmaru ya dafa
kafadarsa cikin matukar murna yace ya kai
jarumin jarumai tabbas yau ka sharewa
mahaifinka hawayensa kuma kayi abinda babu
wani mahaluki daya taba yinsa a wannan nahiya
tunda gashi ka kashe sarki saumir har ka dauko
takobinsa,
Ka sani cewa banida ikon karbar wannan takobi
daga hannunka saboda kai kadai ne zaka iya
riketa ka zauna Lafiya to amma fa ka sani cewa
ka tsokano tsuliyar dodon da zai tada hankalin
duniya domin kuwa zaman wannan takobi a
hannunka dai-dai yake da tsokano yakin duniya
gaba daya.
Ina mai tabbatar maka da cewa a halin yanzu ka
dauko gunguma gunguman itatuwa ka zuba a cikin
wutar gabarka da sarki Daryan tunda ka kashe
masa mahaifi kuma ka rabasu da takobin daraja,
Takobin da a halin yanxu duk duniya babu wata
takobi wacce ta fita daraja
Ya zama dole musa ido a birnin nan namu kuma
mu tsananta tsaro fiye da koyaushe domin sarki
Daryan sai yabi kowace irin hanya don ganin ya
mallaki wannan takobi ta koma hannunsa kuma
yaki tsakaninmu dashi yanzu aka fara
Yakin da kuka je tamkar sharar fage ne.
Sa'adda sarki Barham yazo nan a jawabinsa sai
Kalmaru ya dubeshi cikin mamaki yace, ya
shugabana yaya akayi kasan cewa sarki Daryan
bai mutu ba a wannnan

1 Comments On MAZA SUN FADI 1 to 4
avatar
abubakar-abdullahi-6

10 months ago

Reply

yes

Please Login or Register in order to submit comment