Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba, amma tun ina
yarinya karama nake jin labarin irin jarumtakar da
kayi a daji sa'adda kuka fita farauta kai da
mahaifinka.
Tun a lokacin nake kwadayin na ganka amma
saboda nayi alkawarin sai na girma na zama
cikakiyar budurwa sannnan zan yarda ka ganni
shiyasa ban nemi a kawoka gareni ba.
Lokacin da gimbiya lazima tazo dai-dai nan a
zancensa sai sarkin yaki kalmaru ya kamu da
tsananin farinciki kuma nan take yaji ya kamu da
tsananin son gimbiya lazima.
Abinda ya fara burgeshi game da ita shine, jin
yarda ta dade a cikin jiran ranar da zasu hadu.
Abinda kuma ya bashi mamaki shine yadda ta saki
jiki dashi suke ta hira tamkar dama can dade
tare.
" To wai shin ma menene ya burgeta a game
dashi har ta tsaya take hira dashi haka?"
Nan take zuciyar kalmaru ta kamu da wasi-wasi
yana mai zancen zuci a ransa yana cewa;
Anya kuwa gimbiya zata iya bani wani gurbi
acikin zuciyarta har muyi soyayya? Don ta saki jiki
dani muna hira tana yi mini murmushi bai zama
dole ba ta soni kamar yadda naji inasonta yanzu.
Zaifi kyau na gaggauta cire sonta daga cikin
Zuciyata domin babu yadda za'a ma na aureta a
matsayinta na yar sarki ni kuma sarkin yaki bawan
mahaifinta.
*****
A can gidan attajiri yunaru kuwa, lokacin da suka
koma gida shida dansa Hamsaru,
Sai suka sa aka kawo musu giya tulu guda suka
yita zubawa a kofi suna dirka saboda bakin ciki,
har sai da suka bugu ainun suka kama sumbatu
irin na wadanda suka zautu.
Suna cikin wannan hali ne wani babban hadimin
Hamsaru ya shigo cikin turakar ya risina yana mai
duban Hamsaru yace, ya shugabana yau dai gashi
can gimbiya lazima ta fito filin fada har ta zauna
a kusa da sarkin yaki kalmaru suna ta yin hira.
Koda da jin wannan batu sai Hamsaru ya kurma
uban IHU ya naushi tulun giyar dake gabansa ya
fashe, ruwan giyar ya zube kasa.
Zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone.
Daga can sai ya fashe da kuka ya dubi mahaifinsa
yunaru yace,
Ya kai Abbana yanzu gashi kanaji kana gani na
rasa kujerar sarkin yaki,
Babban burina na farko a duniya.
Shin haka zaka zuba ido kuma na rasa gimbiya
lazima maccen da tun ina yaro karami na kamu
da tsananin sonta.
Koda jin wannan batu sai yunaru ya kama
rarrashinsa yace,
Ka kwantar da hankalinka ya kai dana, kayi sani
cewa indai ina numfashi a doron kasa sai na
karbo maka takobin zinare daga hannun kalmaru,
kuma sai ka auri gimbiya lazima.
Inason ka kwantar da hankalinka ka sani cewa
nan da cika wani lokaci zan shirya tuggun da
kalmaru zai rasa kujerarsa ta sarkin yaki.
Sa'adda yunaru yazo nan a jawabinsa sai hankalin
Hamsaru ya kwanta ya kamu da tsananin farinciki
ya dubeshi yace, ya kai Abbana kayi sani cewa na
yarda da dari bisa dari saboda nasan cewa duk
abinda kasa a gabanka sai kaga bayansa, baka
faduwa
Daga yau zanci gaba da dogoro da kai akan
wadannan burika nawa.
Amma fa ka sani cewa idan na rasa takobin
zinare kuma na rasa gimbiya lazima zan iya rasa
hankalina ko kuma na rasa rayuwata gaba daya.
Attajiri yunaru ya sake kankame Hamsaru a
jikinsa yace, "muddin ina numfashi bazaka taba
rasa wadannan Abubuwa biyu ba. MAZA SUN FADI!!! LITTAFI NA 2 PART 3

Attajiri yunaru ya sake kankame Hamsaru a
jikinsa yace, muddin ina numfashi bazaka taba
rasa wadannan Abubuwa biyu ba.
Tunda safe aka fara wannan walima ta karshe a
fada sai da rana ta fadi gari ya fara duhu sannan
aka watse.
Tsawon wannan lokaci sarkin yaki kalmaru da
gimbiya lazima suna tare suna ta yin hira basu
rabu ba. Kuma ko kadan basu lura cewar lokaci
yayi nisa haka ba.
Koda suka ga sarki ya sallami jama'a yana
sallama da manyan bakinsa sai hankalinsu ya
dugunzuma ainun domin ko kadan basu son
rabuwa saboda jin dadin hirar da suke yi da kuma
kasancewarsu tare.
Kai inda za'a kyalesu zasu iya kwana a wajen
suna hira.
Nan dai filin fadar ya dade da watsewa ya
zamana cewa babu kowa a wajen daga sarki da
gimbiya lazima sai sarkin yaki kalmaru da dakaru
masu tsaron gidan sarautar.
A sannan ne sarki Barham ya taho gaban kalmaru
sa'adda yake tsaye daf da gimbiya lazima, ya
dubesu cikin murmushi yace,
Ga dukkan alamu matasan nan biyu suna jin dadin
wannan haduwa da sukayi a yau ta bazato."
Koda jin haka sai kunya ta kama lazima da
kalmaru suka sunkuyar da kawunansu kasa.
Sarki Barham ya dafa kafadar kalmaru ya dubeshi
cikin alamun matukar damuwa yace, ya kai
jarumin jarumai kayi sani cewa yanzu ka taka
wani matsayi na musamman a cikin masarautata
don haka dole ne ka sami makiya da yawa.
Daga yau ka zama makusancina kuma abokin
shawarata saboda haka rayuwarka da lafiyarka
suna da matukar muhimmanci a gareni.
Dole ne duk inda kake ya zamana cewa akwai
dakaru masu tsare lafiyarka walau a gida, a hanya
ko a nan fada.
Ka sani cewa yanzu bazaka tafi gida ba sai bayan
munyi taro da dukkan dakarun yakina anan cikin
gidan sarauta bayan munci abinci.
Domin ka gansu gaba daya kuma ka gana dasu ka
raba musu ayyukansu.
Na sani cewar mahaifinka ya baka cikakken horo
akan yadda zaka tafiyarda ayukanka don haka
baza ka fuskanci wata matsala ba.
Koda gama fadin hakan sai sarki Barham ya kira
sarkin gida ya umurceshi da ya kai sarkin yaki
izuwa bangaren da ake saukar manyan baki,
Domin ya huta kafin lokacin cin abinci dare yayi.
Nan take kuwa sarkin gida ya yiwa sarkin yaki
kalmaru jagora izuwa wani bangare dabam a
gidan sarauta.
Sarki Barham da gimbiya lazima kuwa suka nufi
nasu bangaren.
Lokacin da sarki Barham da gimbiya lazima suka
iso wata mararraba inda zasu rabu,shi ya nufi
turakarsa itama ta nufi tata turakar, sai ya dubeta
cikin alamun damuwa yace, akwai bukatar ki
nutsu sossai kuma ki kare kanki domin yanzu ne
zaki shiga wani sabon babi na rayuwa wanda baki
taba tsintar kanki a ciki ba.
Tuni na dade da yanke shawarar bisa cewar ba
zan aurar dake ba face ga gwarzon jarumi wanda
nasan zai iya kula dake ko a bayan raina.
Tabbas na dade da sanin abinda kika gani a cikin
bincikenki na littatafan da kika karanta.
Sama da shekara goma shabiyar baya nasan cewa
kalmaru ne zai zamo sarkin yaki na kuma shine
wanda zaki aura,
Jarumin da zai gawurta a wannan nahiya.
Kuma nan gaba zai haifi dan da zaiyi abin bajintar
da tafi tasa, amma sai nabar wannan al'amari a
cikin Sirri domin saninsa a wajen fadawana ba
karamin hadari bane.
Sannnan kuma akwai wani babban Sirri da baki
ganshi a cikin binciken da kikayi ba wanda shine
Babban abin bakin ciki ga rayuwata wanda zai
ruguje dukkan farin cikina. "
Koda jin wannan batu sai hankalin gimbiya lazima
ya dugunzuma ainun ta dubi sarki cikin alamun
tsananin damuwa tace,
Ya kai Abbana menene Wannan Sirri wanda ni ban
ganshi ba a cikin bincikena? "
Koda jin wannan tambaya sai sarki ya gyada kai
yace, kada ki damu zan sanar dake ko menene
idan lokacin da ya dace ki sani yayi ."
Koda gama fadin hakan sai sarki ya wuce izuwa
cikin turakarsa itama gimbiya lazima sai ta wuce
izuwa cikin tata turakar jikinta a sanyaye,
Kuma hankalinta a dugunzume kamar zata fashe
da kuka.
Lokacin da sarkin gida ya kai sarkin yaki kalmaru
cikin turakar da ake saukar manayan baki yaga
yadda aka kawata dakin da kayan alatu gamida
shimfidu na alfarma, ya kwatantata yadda suke
tafiyar da rayuwarsu shida mahaifinsa sai ya ga
ashe suna cikin talauci ne da kunci na rayuwa.
Tabbas sarakai da attajirai sune suke rayuwa mafi
dadi da kwanciyar hankali a duniya.
Duk da cewar suma ba talakawa bane kuma sun
rabi sarauta.
Kalmaru na cikin wannan tunani ne aka fara
kwankwasa masa kofa.kalmaru ya tambaya yace,
Wanene nan?"
Sarkin gida ne"
Kalmaru yayi masa iznin ya shigo, ya bude kofar
ya shigo ya dubi kalmaru yace, ranka ya dade
sarki da gimbiya suna jiranka a dakin cin abinci.
Da jin haka kalmaru ya mike tsaye yace, "muje ka
kaini garesu"
Nan take sarkin gida ya juya ya fice daga cikin
dakin,
Shi kuma kalmaru ya bishi a baya. Nan fa suka yi
ta kutsawa cikin gidan dakaru suna risinawa suna
gaishe shi.
A sannan ne ya tabbatarda cewa ya zama sarkin
yakin birnin zamar.
Sa'adda suka shiga dakin cin abinci sai kalmaru
ya iske sarki da gimbiya a zaune bisa kujerun
dake karkashin wani katon benci wanda akansa an
dora abinci iri-iri sama da kala dari amma ko fara
cin abincin basu yiba.
Nan take sarkin gida da ya rako kalmaru ya juya
ya fice daga cikin dakin.
Take sarki ya umurci kalmaru da ya zauna suci
abinci tare.
Ba tareda fargaba komai ba kalmaru ya zauna
suka kama cin abincin.
Har suka gama cin abinci babu wanda yace kala,
Amma gimbiya da kalmaru suna ta satar kallon
junansu har suka kasa kawar da kansu.
Sarki yaga halinda suke ciki, kawai sai yayi
murmushi kuma yai shiru baice komai ba.
Bayan sun gama cin abinci sai suka mike suka
fice daga cikin dakin cin abinci suka tunkari wani
katon fili a cikin gidan sarautar.
Suna isa filin suka yi arba da dakarun yaki sama
da mutum miliyan ukku a tsaitsaye cikin shigar
yaki rike da makamai.
Koda dakaru suka ga sarki tare da sabon sarkin
yaki sai gaba dayansu suka risina suka kwashi
gaisuwa.
A sannan ne sarki ya gabatar da kalmaru a garesu
duk da cewa da yawansu sun sanshi tunda sun
halarci taron gasar da akayi a filin fada ya karbi
takobin zinare.
Sarki yaja kunnen dakaru akan lallai su zamo
masu ladabi da biyayya ga wannan sabon
shugaban nasu.
Kuma su bashi dukkan hadin kai domin yaji dadin
gudanar aikinsa lafiya cikin nasara.
Bayan sarki ya gama nasa jawabin sai ya kama
hannun gimbiya lazima ya jata suka koma can
gefe daya suka zubawa kalmaru idanu a lokacin
da ya fara nasa jawabin ga dakaru.
Nan take kalmaru ya fara rabawa dakarun horo na
dabarun yaki kala-kala
Al'amarin da yai matukar daurewa sarki kai kenan
domin ko mahaifin kalmaru Ridwan bai taba zuwa
da sababbun horon yaki ba irin wadannan.
Sai da kalmaru ya shafe sama da sa'a daya da
rabi yana koyawa dakarun sababbin dabarun yaki
na ban al'ajabi
Duk abinda ke faruwa sarki Barham da gimbiya
lazima na kallo suna jin dadi.
A lokacin ne sarki Barham ya dubi gimbiya lazima
yace, hakika koda banyi irin binciken da kika yi ba
a yanzu dana ga irin hikima da basirar kalmaru
dole ne na gamsu cewa shine jarumin da zai yi
gagarumin abin al'ajabin da babu wanda ya taba
yin kamarsa a wannan nahiya tamu."
Bayan sarkin yaki kalmaru ya gama baiwa dakarun
yakin horo sai ya zabi dakaru guda hamsin kacal
wadanda zasu rinka tsaron lafiyarsa a duk inda
yake,
Sannnan yayi wa sauran dakarun sallama akan
gobe zai dawo yaci gaba da basu wadansu
sababbin dabarun yaki. Nan take dakarun suka
cika da tsananin mamaki domin su a tunaninsu
basirar kalmaru ta kare amma kuma sai sukaji
yace gobe ma idan ya dawo wadansu sababbin
dabarun yaki zai basu.
Nan dai kalmaru ya baro wajen dakarun yaje inda
sarki Barham da gimbiya lazima suke.
Wadannan dakarun guda hamsin na take masa
baya.
Kalmaru ya risina ga sarki yayi sallama ya juya
zai tafi ba tare da Yayiwa gimbiya lazima sallama
ba, kawai sai yaji gimbiya ta kirawoshi da ainihin
sunansa.
Cikin mamaki ya juyo ya dubeta a lokacin da sarki
ya tafi ya barsu a wajen
Gimbiya lazima ta dubi kalmaru cikin wani irin
murmushi na musamman tace, laifin me nayi
maka zaka tafi bakayi min sallama ba?
Koda jin haka sai kalmaru yayi murmushi yace, ki
gafarceni ya shugabata, kiyi sani cewa in dai kina
tare da sarki Inajin nauyin na kalleki ma bare na
iya yi miki magana. "
Lazima ta gyada kai tace, na yarda da duk
kalamanka. Ina mai sanar da kai cewa daren yau
shine daren farko a rayuwata da zanyi barci mai
dadi wanda bantaba yin kamarsa ba, ba don
komai ba sai saboda na sami natsuwa da
kwanciyar hankali.
Na tabbatarda cewa wannan birni namu ya sami
jarumi da zai iya kareshi daga dukkan abubuwan
fargabar da nake tunanin zuwansu"
Da jin haka sai kalmaru yayi murmushi yace,
godiya a gareki ya shugabata kuma ina fatan
abinda kike zato a kaina zai tabbata gaskiya.
Lazima tace. Ai abinda ma nake zato ya wuce
hakan, da sannu zan sanar da kai wani abu mai
matukar muhimmanci wanda bazaka taba
mancewa dashi ba Na barka lafiya, sai mun sake
saduwa.
Koda gama fadin hakan sai gimbiya ta juya ta
nupi cikin Gidan sarauta tana waigensa.
Shima sai ya tafi yana waigenta yana mamakin
irin kalaman da gimbiya ta fada masa wadanda
suka jefashi cikin wasi-wasi da rashin fahimta.
* * *
Lokacin da gari ya waye attajiri yunaru na zaune
tare da dansa Hamsaru a turakarsa suna yin
kalacin safe,
Sai ga sarkin yaki kalmaru tare da dakaru sun
shigo har cikin gidan
Kalmaru na rike da wata takarda mai dauke da
hatimin sarki a jiki
Cikin fushi yunaru ya dubi kalmaru ya daka masa
tsawa yace, menene ya kawo ka cikin gidina har
da za ka shigo har cikin turakata tare da dakaru
don muzantawa?"
Kalmaru ya risina cikin alamun girmamawa yace.
Ka gafarceni ya kai kawuna, kayi sani cewa nazo
gidanka ne akan aikina bisa bin umurnin sarkina.
Idan baka manta ba ranar da akayi gasar kujerar
sarkin yaki kunyi alkawari da sarki cewar idan
boka hizainu ya fadi cewar banyi amfani da sihiri
ba bisa nasara dana samu zaka tafi kurkuku na
tsawon wata shidda.?
To yanzu nazo ne na tafi da kai izuwa can
kurkukun bisa umurninsa.
Koda jin wannan batu sai Hamsaru ya mike tsaye
zumbur! Cikin tsananin fushi ya zare takobinsa ya
dubi kalmaru a fusace yace, idan har kaga ka tafi
da mahaifina sai idan ka kasheni.
Koda gama fadin hakan sai yunaru yai sauri ya
sha gaban Hamsaru yace, kada ka damu ya dana,
Ai wata shidda kamar yanzu ne amma nayi maka
alkawari sai kalmaru ya mika maka takobin zinare
da hannunsa.
Kada ka zargeshi da laifin komai akan aikinsa
yake umurni yake bi kawai. "
Gama fadin hakan keda wuya sai yunaru ya juyo
ya dubi kalmaru yace, muje ka cika aikinka. " MAZA SUN FADI!!! LITTAFI NA 2 PART 4

Gama fadin hakan keda wuya sai yunaru ya juyo
ya dubi kalmaru
yace, muje ka cika aikinka. "
Nan take kalmaru yasa dakarunsa suka sawa
yunaru sarka aka tusa keyarsa gaba aka fice
daga
cikin gidansa.
Hamsaru yaga an tafi da mahaifinsa a gaban
idanunsa yana ji yana gani, kuma babu abinda zai
iya yi
Sai ya kamu da tsananin bakin ciki, ya kwarara
uban IHU ya kama saran komai dake falon har
sai
da ya tarwatsa komai sannan ya zauna a kasa ya
fashe da kuka.
Kwana biyu da kai attajiri yunaru kurkuku wasika
tazo daga wata kasa da ake kira MUSAB.
Birni musab na karkashin mulkin wani
gawurtaccen jarumin sarki wanda ake kira
SADAUKI DARYAN
Sarki Daryan ya tara manyan zakwakuran
mayakan da babu kamarsu a nahiyar gaba daya a
yawa da iya yaki.
Bisa wannan dalili ne gaba dayan sarakunan
dake
nahiyar suke matukar tsoronsa.
Sarki Daryan ya kasance azzalumin sarki mara
imani da tausayi ko kadan,
Kuma a rayuwarsa babu abinda yake so sama da
kudi da son tara dukiya.
Gashi kuma birninsa cibiya ce babba ta
kasuwanci a nahiyar gaba daya, amma sai ya
sanya haraji mai tsantsanin yawa ga yan kasuwa
yadda duk irin ribar dazasu samu sai sun biya
harajin da ya fita yawa.
Attajiri yunaru aminin sarki Daryan ne,saboda
shine bafatake da yafi kowa biyansa haraji mafi
tsoka idan yazo yin fatauci birninsa.
Ban da ma haraji da yake biya.
Yakan debo wadansu kudaden masu dumbin
yawa ya baiwa sarki Daryan.
Lokacin da aka kawo wasikar sarki Daryan cikin
fadar sarki Barham gaba daya yan majalisarsa na
nan,
Shima sarkin yaki kalmaru yana zaune a gefe
daya.
Koda aka ji cewar wasikar ce daga sarki Daryan
sai hankalin kowa ya dugunzuma domin an san
cewa ba wasika bace ta alheri.
Nan dai sarki Barham ya umurci maga-takarda da
ya karanta wasikar a fili kowa yaji abinda ta
kunsa.
Nan take maga-takarda ya bude wasikar ya fara
karantawa kamar haka...
" wasika daga hannun sarkin sarakuna,
Daryan ibini saumir mai mulkin kasar musab,
Zuwa ga sarki Barham na birnin zamar
"Ya kai wannan sarki kayi sani cewa labari yazo
mana bisa irin rashin adalcin da kayi a
masarautarka na bayarda sarautar sarkin yaki ga
mutumin da bai dace ba,
Wanda yai amfani da karfin sihiri wajen lashe
gasar da akayi ya sami nasara.
Sannan kuma kasa aka daure mahaifin wanda ya
lashe gasar bisa gaskiya
Ina mai gargadinka da ka hanzarta karbe takobin
zinare daga hannun kalmaru ka mika ta ga
Hamsaru dan yunaru kuma ka gaggauta fito da
attajiri yunaru daga kurkuku ka bashi matsayi
babba a fadarka daga nan zuwa cikar kwana
bakwai.
Idan har ka saba wannan ka'ida zamu yake ka
domin mu tabbatarda adalci acikin kasarka"
Lokacin da maga-takarda yazo nan a karatun
wasikarsa tuni jikin sarki Barham ya kama
karkarwa saboda tsananin fishi da takaici.
Kawai sai ya mike tsaye zumbur! Ya kwace
wasikar daga hannun maga-takarda ya yayyagata
ya kama huci yana muzurai.
A dai-dai wannan lokaci ne waziri da sauran
fadawa suka zube kasa gaban sarki suna cewa,
"zuciyarka tayi sanyi ya mai birnin zamar " sai da
suka fadi hakan har sau uku sannan waziri ya
mike tsaye ya fuskanci sarki yace,
"ya shugabana inason ka bi al'amarin nan a
hankali domin idan muka ce mu ketare umurnin
sarki Daryan babu abinda zai haifar mana face
mugun yaki wanda zai janyo asarar dumbin
rayuka da dukiya.
Kasani cewa sarki Daryan ya fimu yawan dakaru
da karfin mayaka ba zamu taba samun nasara ba
akansa kuma idan ya cimu da yaki kaima bazaka
tsira da rayuwarka ba"
Koda gama fadin hakan sai gaba dayan ragowar
fadawan suka sake hada baki sukace,
Abinda waziri ya fada gaskiya ne a tsaya ayi
nazari da tunani kan haka.
Koda jin hakan sai sarki Barham yai ajiyar zuciya
cikin tsananin takaici sannan yace,
Baza muyi gaggawa yanke hukunci ba bisa
wannan al'amari don haka a bani zuwa gobe nayi
tunani tukunna.
Na sallami kowa ina bukatar na kadaita.
Gama fadin hakan keda wuya sai fada ta watse
kowa ya kama gabansa.
A wannan lokaci sarkin yaki kalmaru yaso ace
sarki ya kirashi sun kadaita domin suyi shawara
amma daya ga sarki baice masa uffan ba sai ya
tafi gida cikin damuwa.
Kalmaru yana isa gida ya iske mahaifinsa Ridwan
wato sarkin yaki na zaune a turakarsa tare da
Zulaima suna hira cikin nishadi suna ta dariya.
Koda suka ga kalmaru ya shigo jikinsa a sanyaye
kuma fuskarsa cike da alamun matukar damuwa
sai suma hankalinsu ya dugunzuma.
Ridwan ya mike da sauri ya kama hannayen
kalmaru ya zaunar dashi suka fuskanci juna yace,
"Bani labari ya kai dana, menene ya faru a yau a
fada ka dawo gida fuskarka na cike da alamar
damuwa?"
Koda jin wannan tambaya sai jarumi kalmaru yaja
dogon numfashi sannan ya kwashe labarin duk
abinda ya faru a fada ya zaiyane masu dangane
da abinda wasikar sarki Daryan ta kunsa da
kuma irin shawarar da fadawansa su ka bayar.
Koda jin wannan batu sai Ridwan ya kyakyale da
dariya, al'amarin da yai matukar ba wa Zulaima
da kalmaru mamaki kenan.
Daga can sarkin yaki Ridwan ya hade fuskarsa
ya dubi kalmaru yace, ya kai dana idan ba ka
mance ba a shekarar da nayi yaki na karshe
Na umurceku ku ya'yana ku duka ku bini izuwa
yakin.
Gaba daya yan uwanka mutuwa sukayi a wannan
yaki, kai ka dai ne ka dawo gida a raye saboda
tsananin juriyarka, Nacinka da karfin damtsenka.
A tarihin kasar nan ba'a taba yin matsainacin
yaki ba irin wannan kuma yakin ya faru ne
tsakanin kasar nan tamu da kasar musab,
Kuma a wannan lokaci mahaifin sarki Daryan ne
akan karagar Mulki.
Hakika munyi bakin gurmuzu a wannan yaki kuma
mun sha tsananin wuya mu da dakarun kasar nan
ban taba tsammanin zamu sami nasara ba.
Da kyar da sidin goshi na kai sarki saumir kasa
na sare masa hannunsa na dama.
Ina shirin zan kashe shi ne dansa Daryan yai
wuf! Ya sureshi daga gabana ya dorashi akan
doki suka janye yakin.
Koda Ridwan yazo nan a zancensa sai nan take
tunanin abinda ya faru a lokacin ya fadowa
kalmaru.
Duk da cewa a zamanin da akayi yakin kalmaru
baifi shekara goma sha bakwai ba sai gashi yana
tunowa da al'amarin tamkar a sannan abin ke
faruwa.
Abinda ya fara fadowa kalmaru a rai shine,
Yadda filin yakin ya hargitse aka bude kasuwar
dauka rayuka.
Mazaje suka rinka faduwa kasa sa'adda sara da
suka ya yawaita, ihun mazaje ya cika dodon
Kunne,
Sannan jini ya rinka fallatsi yana fantsama.
Komai kallon kurillar mutum a wannan lokaci bai
isa ya iya tantace bangaren da ke samun nasara
ba a yakin domin kare jini biri jini akeyi.
Duk da cewa kalmaru yaro ne sai gashi yana ta
kutsawa ta cikin abokan gaba yana ta sara da
suka,
Duk inda yasa gabansa sai dai kaga maza na
zubewa kasa.
Yana cikin yin wannan mummunar barna ne
tsulum! Yaga wani matashin saurayi sa'ansa
daga cikin abokan gaba yasha gabansa, nan fa
suka fara sabon azababben yaki shi da wannan
sarauyi amma sai ya zamana cewa karfinnsu
yazo daya,
Domin sai da suka shafe kusan rabin sa'a suna
kaiwa junansu sara da suka amma dayansu bai
sami nasarar koda lakutar jikin daya ba har ya
zamana cewa takubbansu sun dakushe.
Ba shiri suka yadda takubbansu suka kaure da
fadan hannu suna masu naushi da bugun juna.
Nan da nan kuwa suka hadawa kansu jini da
majina tun suna da kuzarinsu har sai da ta kai
cewa sun galabaita ainun suna maye a tsaye
kamar sun sha giya sun bugu.
Amma saboda naci da taurin zuciya basu fasa
bugun juna ba.
Suna cikin wannan hali ne sukaji an busa kahon
janye yakin daga bangaren kasar musab.
Bisa dole suka ja da baya cikin tsananin takaici
suna huci da haki da hararar juna
A sannan ne wancan jarumin saurayi ya bushe da
dariyar mugunta yace,
"Sunana yarima Daryan "da" ga sarki saumir mai
birnin musab. Nine DODON MAZA kuma mai kai
maza kasa.
Yaro kayi arziki da aka tsaida wannan yaki.amma
da sai na kaika barzahu."
Koda jin wannan batu sai shima kalmaru ya
bushe da dariya yace, "kai.yaro ai jiki magayi ne,
ina mai tabbatar maka da cewa nine jarumi
kalmaru" da" ga sarkin yaki Ridwan na birnin
zamar.
In ba don an busa kahon tsayarda wannan yaki
ba da tuni MAZA SUN FADI amma nayi maka
alkawari komai daren dadewa nan da shekaru
dari idan muka sake haduwa a filin yaki sai na
kaika kasa kuma na kashe ka.
Da jin haka sai Daryan yayi kaki ya tofar da jini
sannan ya dubi kalmaru yace, shikenan mu zuba
mugani ai lokaci shine maganin gardama,
Ni da kai zanga wanda zai cika Alkawarinsa,
lokacin da yazo dai-dai a tunaninsa ne yaji
mahaifinsa Ridwan ya dafa kafadarsa.
Nan take yayi firgigit! Kamar wanda ya farka
daga barci.
Ridwan ya dubeshi yace, ya kai dana lokaci yayi
da duniya zata sanka, ina mai tabbatar maka da
cewa dole ne muyi yaki da birnin musab a karo
na biyu.
Kuma kaine zaka jagoranci wannan yaki
Babban takaicina shine, ni yanzu na tsufa bazan
iya fita yaki ba. Ga kuma lalurar dake damuna
mai alaka da sihiri, amma da sai na fita yakin nan
na karasa aikin dana fara."
Koda jin wannan batu sai kalmaru ya dubi
Ridwan cikin mamaki yace, "ya kai Abbana me
kake nupi da ka karasa aikin da ka fara?
Ridwan yayi murmushi sannan yace "A wancan
yakin danayi na karshe na sarewa sarkinsu hannu
daya.
Zanso ace yanzu zamu sake haduwa mu fafata
na kaishi kasa gaba daya, ina nufin na kashe shi
domin na huce takaicin da ya cusa mini acikin
Zuciyata.
Inaso ka sani cewa mahaifin Daryan wato sarki
saumir ya dasa mini bakin ciki da har abada ba
zai kankare ba daga cikin Zuciyata face naga na
kashe shi da hannuna domin a wancan yakin ne
na rasa dukkan ragowar ya'yana yan uwanka su
biyu wadanda suka kasance yayyenka.
Koda Ridwan yazo nan a zancensa sai ya fashe
da kuka a lokacin da itama Zulaima ta fashe da
kukan.
Al'amarin da ya jefa tsananin tausayinsu kenan a
cikin zuciyar kalmaru shima ya kama kukan.
Daga can sai Ridwan ya dago kai ya dubi
kalmaru yana mai share hawayen idanunsa yace,
ya kai dana abinda nake so da kai shine, idan har
sarki ya kiraka ya nemi shawararka bisa wasikar
da sarki Daryan ya aiko,
Ka gaya masa cewar kawai a aika masa da
amsar wasikar raddi ta yakin.
Ina mai tabbatar maka da cewa wannan yaki da
za'a yi shine yakin farko da sunnanka zai shahara
ko ina a wannan nahiya. Kuma shine yakin da
zaka kawo babban ci gaba a kasar nan.
Kuma ina san ran cewa zaka karasa abinda na
kasa karasawa.
Ka cire tsoro da fargaba komai daga cikin
zuciyarka kamar yadda na sanka da dakakkiyar
zuciya irin ta manyan mazaje tun kana yaro
karami.
Koda jin wannan batu sai kalmaru ya mike tsaye
zumbur! A lokacin da jikinsa ya kama tsuma ya
dubi Ridwan yace,
Ya kai Abbana nayi maka alkawari komai rintsi
da tsanani sai na cika wannan aiki naka kuma
sai na ga bayan dukkan makiyan sarki da
makiyan wannan kasa tamu mai albarka.
Koda jin haka sai farinciki ya lullube Ridwan
shima ya mike tsaye ya rungume kalmaru yana
mai yi masa jinjina da godiya.
Nima a lokacin na mike tsaye na rufe littafi na
wuce izuwa masallaci. MAZA SUN FADI!!! LITTAFI NA 2 PART 5

Sarki Barham bai nemi sarkin yaki kalmaru ba har
sai da dare ya raba sannan ya taso da kansa a
sirrance ba tare da kowa ya sani ba yazo gidan
sarkin yaki Ridwan.
Koda masu gadin gidan suka ga sarki Barham
yazo da kansa sai suka zube kasa suka kwashi
gaisuwa sannan suka yi masa iso har izuwa cikin
dakin kalmaru.
A wannan lokaci Ridwan da baiwa Zulaima tuni
sun dade da yin barci basu san abinda ke faruwa
ba.
Kalmaru na tsaye a cikin dakinsa yana kai kawo
yana tunani da zullumi bisa wannan al'amari da
ya
taso sai kawai yaji an turo kofar dakin an shigo.
Cikin zafin nama ya zare takobinsa domin a
zatonsa makiya ne suka kawo harin shammace.
Kwatsam! Sai ya ga ashe sarki ne da kansa yazo,
cikin tsananin mamaki ya risina ya kwashi
gaisuwa sannan ya mayar da takobinsa cikin
kufe
ya dubi sarki yace,
Ya shugabana menene ya kawoka gidan mu a
cikin wannan tsohon dare?"
Ai kamata yayi ka aiko nazo, bai kamata kazo da
kanka ba, ana cikin irin wannan hali domin
rayuwarka ma abar farauta ce a wajen makiya.
Koda jin wannan batu sai sarki Barham yayi
murmushi yace, ai shi makiyi kullum a cikin kawo
harin shammace yake don haka dole ne kaima ka
rinka shammatarsa, idan kanason ka tsira daga
sharrinsa.
Babu wanda zai taba tunanin cewa zan fito daga
cikin gidan sarauta ni ka dai a cikin wannan dare,
shi yasa ma kaga banzo ba tare da dakaru.
Kasani cewa makiyanmu suna jikinmu don haka
dole ne muyi taka tsan-tsan a cikin duk abinda
za
mu kulla ya zamana cewa muna da cikakken
Sirri.
Yanzu inason ka rufe kofar

1 Comments On MAZA SUN FADI 1 to 4
avatar
abubakar-abdullahi-6

10 months ago

Reply

yes

Please Login or Register in order to submit comment