Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dakin nan da tagogin
dake dakin yadda babu wanda zai ji abinda za
mu
tattauna. "
Da jin haka sai kalmaru yaje ya rufe kofa da
tagogi cikin sauri ya dawo suka zauna akan
gefen
gado tare da sarki suka fuskanci juna.
Sarki Barham ya numfasa yace, ba zuwa nayi
domin muyi shawara ba, zuwa nayi kawai na
baka
umurni domin tuni na gama yin shawarar Abinda
zamuyi.
A gobe zan aika takarda raddi ta yaki ga sarki
Daryan na birnin musab.
Ina so daga yanzu a cikin wannan dare ka fara
shirye-shiryen yaki kuma duk yadda zakayi ka
tabbatarda cewa ka kammala baiwa dakarunmu
horon yakin da kake so su koya a cikin kwanaki
bakwan nan kafin mu soma wannan yaki.
Na yarda da hikimarka da basirarka kuma na ji a
jikina cewa zaka iya jagorantar wannan yaki
yadda za'a akai ga nasara.
Da wannan furuci nake yi maka sallama sai gobe
da safe zamu hadu a fada.
Koda gama fadin hakan sai sarki Barham ya mike
tsaye da sauri ya fice daga cikin dakin.
Koda ganin haka sai shima kalmaru ya kama shiri
ya sanya kayan yakinsa sannan ya kira daya
daga cikin dakarun dake gadinsa a waje ya bashi
umurnin ya kwashi dakaru talatin su bazama
cikin gari su tattaro sauran dakarun yakin kasar
a hallara gaba daya a cikin gidan sarauta in da
ya basu horon yaki.
Nan da nan kuwa wannan Badakare yaje ya cika
umurni.
Kamar yadda sarki Barham ya tsara haka
al'amura suka kasance, wato kashe gari da safe
sarki Barham yasa aka rubuta wasikar raddi ta
yaki aka tashi manzo ya tafi da ita izuwa kasar
sarki Daryan wato birnin musab.
Al'amarin da yai matukar razana fadawa kenan
kuma yai matukar basu mamaki domin basu taba
tsammanin cewa sarki zai iya yin kundunbala
yace zai tari sarki Daryan bn saumir ba da yaki,
Tunda kura ma tasan gidan mai babbar sanda
kuma ko ba'a gwada ba linzami yafi karfin kaza.
Shi kuwa sarkin yaki kalmaru tun a daren jiya
yaci gaba da baiwa dakarun sababbin horo na
dabarun yaki kamar yadda ya fara.
Bayan sarki Barham ya gama taro da fadawansa
a dakin ganawa
Ya tabbatar musu da cewar yaki zai yi da sarki
Daryan kuma ba gudu ba ja da baya sai gaba
dayansu suka nuna rashin goyan bayansu akan
yakin.
Suka nuna tsananin tsoronsu saboda suna ganin
cewa lallai idan akayi wannan yaki baza a sami
nasara ba.
Al'amarin da yai matukar fusata sarki kenan ya
rufesu da fada kamar zai sa musu duka kuma ya
gaya musu cewa duk wanda yake ganin zai iya
tsayarda wannan yaki sai dai ya zare takobi ya
fara yakin da shi na cikin gida.
Yana gama fadin hakan ya fice daga cikin dakin
ya shiga izuwa cikin gidan sarautarsa.
Sarki Barham na shiga cikin turakarsa ya iske
gimbiya lazima a zaune tana jiransa.
Koda ganinta sai ya cika da tsananin mamaki ya
dubeta yace, yake yata menene ya kawoki cikin
turakata har kika dade haka kina jiran dawowata?
Gimbiya lazima ta mike tseye ta tari sarki
Barham ta kama hannayensa ta rike sannan ta
kaishi izuwa kan wata kujera suka zauna tare
tace,
Ya kai Abbana na sani cewa babu wani gata
wanda baka nuna mini ba a cikin wannan duniya
tun daga ranar da mahaifiyata ta kawoni duniya
kawo izuwa yanzu.
Kuma ka sani cewa baka taba bani wani umurni
ba na ketareshi dai-dai da dakika guda.
A iya zamana da kai ban taba budar baki ba na
nemi wata alfarma koda guda daya ce a wajenka,
Haka ne?" to ka sani cewa a yau gani gareka ina
mai neman wata alfarma guda daya rak a
wajenka wadda nake son ka amince kayi min ita.
Koda jin wannan batu sai sarki Barham ya sake
kamuwa da tsananin mamaki, ya dubi gimbiya
lazima yace, yake 'yata ke kuwa wacce irin
alfarma ce haka kike son nayi miki?"
Maza ki fadeta in dai ina da ikon yi miki ita sai
nayi, Koda gaba dayan abinda na mallaka zai
kare."
Gimbiya lazima tayi ajiyar numfashi sannan tace,
Ya kai Abbana ba wani abu nake bukata ba face
ka yarje mini a tafi wannan yaki da za'a yi da
birnin musab tare da ni, saboda inason naga irin
jarumtakar sarkin yaki kalmaru a filin daga.ka
sani cewa ban taba halarta yaki ba sai a cikin
littatafan tarihi nake jin yanayin yaki,
Lallai inason naga yadda maza suke faduwa kasa
da idanuna, kuma inason naga yadda kaifi da
tsini ke ratsa jikin bil'adama.
Inason naga yadda jini yake fantsama yana
malala akan doron kasa,
Inason naga mazan kwarai wadanda komai gumu
basu gudu a filin daga. Kuma basa baiwa abokan
gaba baya.
Inason nagani a zahiri abinda na karanta a
littattafai domin na dawo gida na rubutasu da
hannuna a cikin sabon kundin tarihin kasar nan.
Koda gimbiya lazima tazo nan a zancenta sai
hankalin sarki Barham ya dugunzuma ainun ya
dubeta alamun matukar tsoro da damuwa ya ce
Haba yake 'yata hakika inda kinsan menene yaki
da bazaki taba sha'awar ganinsa ba da idanunki
ko fatan faruwarsa.
Yaki bala'i ne wanda an san farkonsa amma ba
asan karshensa ba.
Yaki GUGUWAR ANNOBA ne mai share rayuka da
dukiya.
Yaki masifa ce mai ruda yaro da babba, mace da
namiji , har yasa mutum ya gwammace rayuwar
kabari akan ta doron kasa,
Yaki jaza'i ne mai haddasa talauci, fatara,yunwa
da kirshirwa wacce kesa zubar hawaye ba adadi.
Yake 'yata kiyi sani cewa ni kaina gani nayi bamu
da wata mafita wacce tafi ayi wannan yaki,
Domin idan muka ki yinsa muka cika umurnin
sarki Daryan tamkar mun mika kasar mune da
jama'ar mu a hannun makiyanmu.
Ina mai tabbatar miki da cewa wannan yaki da
zamuje shine yaki mafi hadari da za'a yi a
nahiyar nan wanda za'a yi asarar miliyoyin
rayukan da ba'a taba yiba.
Banida tabbacin zan iya kare kaina yayinda aka
fara wannan yaki bare har na samu tabbacin
kareki.
Ina mai rokonki da ki janye wannan alfarma da
kika nema a wajena.
Da dai kije filin wannan yaki a kashe ki a can
gwara ace an ci ni da yaki an shigo har cikin
birnin nan an kamaki a matsayin baiwa.
Ko ba komai nasan ba za'a kashe ki ba saboda
kyawunki.
Kinga kenan zaki tsira da rayuwarka ya zamana
cewa zuri'ata bata gushe ba a doron kasa, tunda
ke kadai kika rage mini a cikin wannan duniya "
Sa'adda sarki Barham yazo nan a jawabinsa sai
gimbiya lazima ta dubeshi cikin murmushi tace,
Haba ya Abbana ai idan har kayi imani da abinda
masana da matsafa suka fada akan bayyanar
sabon sarkin yakinka ka tabbatarda cewa ba zan
mutu ba a wannan yaki da za'a yi.
Lokacin da gimbiya lazima tazo nan a zancenta
sai jikin sarki Barham yayi sanyi ya sunkui da
kansa kasa yana tunani baice komai ba.
Daga can sai ya dago kai ya dubeta yace,
shikenan na Amince za'a tafi wannan yaki tare
da ke!"
* * * *
Al'amarin waziri kuwa, lokacin da aka watse daga
dakin taron bai zame a ko ina ba sai a kurkuku
wajen Attajiri yunaru.
Da zuwansa kofar dakin da aka kulle yunaru sai
ya kori masu gadin dake bakin kofa dakin ya dubi
yunaru yace,
"Ai wannan mahaukacin sarkin namu yayi watsi
da gargadin sarki Daryan ya zabi muyi yaki dashi.
Koda jin wannan batu sai yunaru ya bushe da
dariyar farinciki yace, Ai shi kenan lokacin cikar
burin mu yazo.
Hakika yau na gano cewa sarki Barham dakiki ne
mai tosasshiyar kwakwalwa kuma ya cika
mahaukaci.
In banda mahaukaci waye zai yarda yayi yaki da
sarki Daryan, mutumin da yake da mayaka sama
da guda miliyan dari bakwai? "kuma zakwakurai
balle shi kadai ma fasa taro ne.
Ina mai yi maka albishir cewa da zarar sarki
Daryan ya kai sarki Barham kasa kaine sarkin
mu, sai ka baiwa dana takobinsa ta zinare.
Gimbiya lazima kuwa da karfin tsiya zamu aurar
da ita ga Hamsaru.
Inason ka sa a kamo dan uwana Ridwan a
kwantar dashi a kasa a daure da hannuna zanyi
masa yankan rago domin na gusar da kishirwar
kiyayyar dana ke yi masa ta tsawon shekara da
shekaru."
SHIN ATTAJIRI YUNARU DA WAZIRI ZASU SAMI
NASARAR CIKA WADANNAN BURIKA NASU?"
WANE IRIN AZABABBEN YAKI ZA'A YI
TSAKANIN BIRNIN MUSAB NA SARKI DARYAN
DA BIRNIN ZAMAR NA SARKI BARHAM? "
SHIN SOYAYYA ZATA KULLU KUWA TSANANIN
SARKIN YAKI KALMARU DA GIMBIYA LAZIMA? "
YAYA KARSHEN LABARIN 'YA'YAN KALMARU
ZAI KASANCE TUNDA AN FARA WANNAN
LITTAFI NE DA LABARINSU SA'ADDA 'YAN
HARIN SUMAME SUKA KAWO FARMAKI KAUYEN
DA SU KALMARU SUKE?"
SHIN SHUBAIRU ZAI MUTU NE KO KUWA ZAI
ISA GIDA YA RISKI DAN UWANSA HUZAIRU? "
Mu hadu a Littafin MAZA SUN FADI kashi na (3)
don jin cigaban wannan labari.
MAZA SUN FADI!!! LITTAFI NA 3 PART 1

Lokacin da attajiri yunaru yaji wannan batu na
waziri sai ya bushe da dariya yayi ta kyalkyatawa
kamar ba zai daina ba.
Shima waziri yana tayashi da dariyar lokaci guda
kuma sai duk su biyun suka tsuke bakinsu sukayi
shiru suna masu kurawa juna idanu sannan waziri
yace, ai kamar yadda kake da wannan buri Nason
hallaka dan uwanka sarkin yaki kalmaru haka
nima
nake da burin yanka dan uwana sarki Barham
saboda tun muna yara nake kunshe da bakin
cikin
yadda sarauta kasar nan ta kufce daga gidanmu
ta koma gidansu alhalin fiye da shekaru talatin
baya a gidan namu take.
Koda jini wannan batu sai yunaru ya jinjina kai
yace, tabbas nasan kana dauke da wannan
takaici
kuma kakanku ku ne ya janyo muku wannan
babbar hasara a yadda naji tarihin al'amarin.
Ya kamata lallai ka gyara wannan tarihi ka dawo
da bara bana.
Waziri yayi murmushi mugunta yace, ai dama
lokaci kawai nake jira kuma gashi yanzu yazo.
Tabbas bokaye na sun tabbatar mini da cewa a
wannan yaki da za'a yi ne kadai zan sami babbar
damar da zan cika gurina na zama sarkin kasar
nan.
Ya kai wannan attajiri yanzu wace damara ya
kamata mu sake daurawa a cikin wannan
kankanin lokaci domin cika burin mu da kuma
kare duk wata matsala wacce zata iya kawo
mana mishkila.?"
Koda jin wannan tambaya sai attajiri yunaru ya
yafito waziri da hannu yayi masa rada a kunne,
koda waziri yaji abinda yunaru ya rada masa sai
ya takarkare ya bushe da mahaukaciyar dariyar
farinciki saboda ya tabbatarda cewa indai
wannan
tuggu da suka shirya ya tafi dai-dai babu abinda
zai hanasu cika burinsu.
Nan fa waziri ya rungume attajiri yunaru yana ta
sunbatarsa saboda farinciki.
Kashe gari da sassafe dakaru suka taru a kofar
fada a cikin shigar kayan yaki
Wasu akan dawakai dauke da guzurinsu
Wasu kuma a kasa sunyi sahu sahu layi-layi
amma gaba dayansu adadinsu bai wuce miliyan
ukku ba da dubu dari biyu da Arba'in.
Bayan wadannan dakaru sun shafe kusan dakika
dari da ashirin tsaitsaye suna jira sannan aka
busa algaita kuma aka buga tambari sai ga sarki
Barham ya fito daga cikin gidan sarauta, sarkin
yaki kalmaru na take masa baya, koda suka iso
gaban wannan runduna sai suka tsaya cak suka
fuskancesu.
Ai kuwa sai gaba dayan dakarun suka risina suka
kwashi gaisuwa ga sarki Barham.
A sannan ne kalmaru ya dubi dakarun a cikin
nutsuwa yace ya ku dirkokin.wannan birni namu
mai albarka inaso ku sani cewa wannan yaki da
zamu fita yanzu yaki ne na rai ko mutuwa.
Yaki ne na kwatar 'yanci da kare lafiyarmu,
iyalanmu, dukiyarmu da rayukanmu. Ku sani
cewa idan bamu yi nasara ba a wannan yaki
matayenmu, 'ya 'yenmu da jikokinmu zasu zamo
bayin mutane birnin zamar kuma dukiyoyinmu
zasu zamo ganimar, don haka ya zama wajibi a
garemu mu kawar da makiyanmu ta kowane hali
idan munason mu kare martaba mu.
Da dai mu dawo gida babu nasara gwara gaba
dayanmu mu zamo gawarwaki a cikin filin yaki.
Inason mu jajirce kuma mu zage damtse iya
karfinmu da iyawarmu don tabbatarda
nasararmu.
Kamar yadda na gayamaku da farko cewar kada
yawan abokan gaba ya razana ku ko firgitaku
domin zuciyar da ta kekashe ga barin tsoron
mutuwa bata faduwa.
Indai muka rike wannan a cikin zukatanmu kuma
kukayi duk abinda na umurceku dayi sai mun
sami nasara a wannan yaki.
Koda gama fadin hakan sai kalmaru ya daga
hannunsa sama kuma ya wangame bakinsa ya
kurma uban IHU irin wanda dakaru keyi ai kuwa
sai gaba dayan dakarun suka kwarara uban ihu
cikin hada baki.
Sautin ihun nasu ya cika birnin gaba daya da
amsa kuwwa yadda ko mutum a cikin rijiya yake
sai ya jiyo.
Nan da nan aka fara shirin tafiya yaki ana loda
guzuri da makamai a kan dawakai,rakuma da
alfadarai.
Adaidai wannan lokaci ne aka ga gimbiya lazima
ta fito daga cikin gidan sarautar a cikin
kasaitacen ado mai tsantsanin kyau, nan fa gaba
dayan mutanen dake wajen suka rude suka
dimauce kai kace lu'u lu'u ne guda daya jal aka
jefa a cikin bakin ruwan tabo saboda irin haske
da kyalkyalin da gimbiya lazima take.
Shi kansa sarki Barham bai san sa'adda
murmushin farinciki ya subuce masa ba.
Saboda yasan cewa Allah ya bashi kyakkyawar
'ya ta gaban kwatance kuma abar misali.
A cikin keken doki lazima ta fito kuyanginta guda
bakwai na biye da ita bisa ingarmun fararen
dawakai kuma duk fararen tufafi suka
sanya.kuma ita kuwa gimbiya lazima koren tufafi
ta sanya masu duwatsun lu'u lu'u hatta takalmin
dake kafarta kore ne hakama mayafin da ta
lulluba a kanta.
Kai duk da namijin da yayi arba da gimbiya
lazima a wannan lokaci sai yaji kamar ya saceta
ya gudu da ita koda kuwa samun damar kallonta
kadai zai samu na dakika ashirin bare ya yi dace
ace zai kalleta ne a lokacin da take yi masa
murmushi, murmushin da ka iya wanke bakin ciki
shekara dubu kuma ya kawar da damuwar da ta
hana rai sukuni. abinda ya daurewa mutane kai
shine ganin yadda gimbiya lazima ta fito a cikin
shirin tafiya wannan yaki mai mugun hadari haka.
Kai tsaye lazima ta karasa wajen sarki Barham
suka rungume juna sannan ya janye jikinsa daga
cikin nata ya sumbaci goshinta ya dubeta a cikin
wani irin yanayi mai nuna tsantsar damuwa a
lokacin da idanunsa suka ciko da kwallah kamar
zai fashe da kuka yace, yake yata kin sani cewa
bamu taba rabuwa ba sai yau.
Naso ace nima zanje wannan yaki domin ya
kasance bamu nisanta da juna ba kuma ya
kasance zan taimaka wajen baki kariya duk da
cewar kina daga bayan filin yaki kuma nasan
cewa sarkin yaki zai iya baki duk irin kariyar da
zan iya baki.
Na sani cewa Kinada son kallo don haka ki tsaya
a baya baya kada ki kuskura ki bari dakarun
birnin musab suyi tozali dake.
Koda jin wannan batu sai gimbiya lazima tayi
murmushi tace ka kwantar da hankalinka ya kai
Abbana lallai na tabbatarda cewar babu abin da
zai sameni a wannan yaki zan dawo gida lafiya.
Sarki Barham yayi murmushi yace nasan da
hakan amma dai duk hakan zan mikaki amana a
hannun sarkin yaki kalmaru inaso ki sani cewa
tsakanin ke da sarkin yaki tamkar bawa ne da
mai gidansa.lallai ki ja mutuncinki da darajarki
kada ki kuskura ki fara nuna soyayyarki a gareshi
kuma kada ya nuna miki tasan kema kija ajinki
kuma kijashi a kasa kafin ki karbi soyayyar tasa.
Wannan wani karatu ne da ya faru a baya akan
mahaifiyata nake biya miki shi domin ki kare
martaba ki da darajarki.
Sa'adda gimbiya lazima ta ji wannan batu sai
murmushi ya subuce mata tace, lallai kuwa zan
kiyaye bisa duk wadannan Abubuwa daka zaiyana
mimi. Koda jin haka sai farinciki ya lullube sarki
Barham ya kama hannun lazima ya jata izuwa
wajen kalmaru suka tsaya daf dashi yadda babu
wanda zai ji abinda zasu tattauna.
Sarki ya fuskanci kalmaru yace, ga 'yata nan na
baka amanarta.
Ka lura da lafiyarta, mutuncinta da rayuwarta
kamar yadda mahaifinka ya kasance mai biyayya
da rike amana a garemu.
Koda jin wannan batu sai sarkin yaki kalmaru ya
tsuguna kasa bisa guiwoyinsa gaban sarki
Barham kansa na sunkuye yace na rantse da
darajar gemun ubana zan kula da lafiyar 'yarka,
mutuncinta da rayuwarta kamar yadda zan kula
da nawa.
Koda jin wannan batu sai farinciki ya lullube sarki
Barham ya kama kafadun kalmaru ya tasheshi
tsaye suka rungume juna sannan yayi masa rada
a kunne yace,
Ba a zama sarki a banza sai ka saka wadansu
matakai guda ukku,
wannan yaki da zaka jagoranta shine mataki na
farko kuma samun nasararka a yakin shine
hayewarka matakin.
Sauran matakan guda biyu kuwa kai da kanka
zaka gansu da idanunka ayayin da kake ganin
cigaba a kan matattakalar benen rayuwarka. MAZA SUN FADI!!! LITTAFI NA 3 PART 2

Ba'a zama sarki a banza sai ka saka wadansu
matakai guda ukku, wannan yaki da zaka
jagoranta shine mataki na farko kuma samun
nasararka a yakin shine hayewarka matakin
Sauran matakan guda biyu kuwa kai da kanka
zaka gansu da idanunka ayayin da kake ganin
cigaba a kan matattakalar benen rayuwarka.
Lokacin da sarki Barham yazo nan a zancensa sai
mamaki ya turnuke kalmaru kuma kansa ya daure
saboda ya kasa fahimtar abinda sarki ya gaya
masa.
Abinda ya fara Tambayar kansa shine ya za'a yi
ya zama sarki alhalin bai gaji sarauta ba? "
Nan dai sarki Barham da gimbiya lazima da sarkin
yaki kalmaru suka yi bankwana kowa yaje ya hau
dokinsa kalmaru ya jagoranci mayaka mutum
dubu dari takwas da sittin kadai suka fice daga
cikin birnin gaba daya suka nausa daji suka yita
tafiya ba sassauci.
Tunda aka fara wannan tafiya kalmaru bai yarda
ya gusa daga kusa da keken dokin gimbiya lazima
ba kuma a duk inda aka yada zango gimbiya ko
kewaye zata yi don kawar da bukatarta shi yake
rakata kuma sai ya caje ko ina a duk inda zata
shiga ya tabbatarda cewa babu wani mugun abu a
wajen sannan baya yarda a sami tazarar da tafi
kamu goma a tsakaninsa da ita a duk inda take
sai dai kawai ya juya mata baya tayi abin da
zatayi sannan ta fito su koma cikin sansaninsu.
A cikin wannan tafiya kalmaru yayi wadansu
dabaru wadanda suka baiwa kowa mamaki domin
tabbatar da tsaro.
Duk sa'adda akayi 'yar doguwar tafiya ta Kimanin
sa'a daya sai a tsaya cak a tura dakarun leken
asiri suje su gano lafiyar hanya kuma su binciki
karkashin kasa da saman bishiyoyi ko abokan
gaba sun binne tarkuna ko kuma sun buya don
shirya mugun hari.
Ai kuwa a hakan sai da aka gano mugayen
tarkuna kimanin guda arba'in na irin dakarun birnin
musab kuma sai da aka kashe dakarun birnin
musab kimanin mutum dubu uku wadanda suka
bubbuya a cikin duhuwar bishiyoyi.
Haka dai aka ci gaba da wannan tafiya har tsawon
kwana ashirin ana tsallake mugayen hare-haren
abokan gaba cikin nasara ba tare da an rasa ko
da Badakare daya ba na birnin zamar har aka iso
bakin wani daji wanda aka yiwa lakabi da Hajarul
maut.
Shi dai wannan daji na Hajarul maut an mai dashi
tamkar filin yaki na nahiyar gaba daya.
Duk kasashen da zasu yi yaki to Hajarul maut ne
mahadarsu don haka ko yaushe ba'a rasa kwaran
gwalolon bil adama a cikinsa kuma baya rabo da
ungulaye da aljanu masu shan jini.
Lokacin da rundunar yaki ta birnin zamar ta iso
bakin dajin Hajarul maut sai sarkin yaki kalmaru
ya daga hannu yana mai bayar da inkiyar a tsaya
Nan take kuwa kowa yaja linzamin dokinsa aka
tsaitsaya cak.
A wannan lokaci keken dokin gimbiya lazima yana
can tsakiyar rundunar kuma kalmaru yasa
wadansu zakwakuran mayaka guda dubu biyu sun
yi masa kawanya ta kowanen bangaren dan bata
kariya.
A cikinsu har da masu manyan garkuwowi, kwari
da baka, masu da takubba amma in mutum ba'a
cikinsu yake ba babu yadda za'a yi ya gane cewa
suna aikin tsaron lafiyar gimbiya.
Bayan rundunar ta tsaya cak sai aka yi tsit,
in banda sautin numfashin dakaru dana dawakai
babu abinda kunne keji.
Sai da kalmaru ya zuba ido a bangaren da makiya
zasu bullo kuma ya kasa kunne har tsawon dakika
dari uku da sittin ko da yaji shiru sai hankalinsa
ya dan tashi domin ya fuskanci cewar abinda
yake gudun faruwa shine zai faru duk da cewa
kuwa yayi tanadi akan hakan amma yasan cewa
ba a bari a kwashe dai-dai.
Kawai sai aka ji sarkin yaki kalmaru ya bayarda
umurnin cewa kowa ya tsuguna kasa ya rufe
jikinsa da garkuwarsa, nan da nan kuwa kowa yabi
umurnin, hatta keken dokin gimbiya lazima sai da
aka lullubeshi da wadansu irin manyan hijabai na
karfe.
Faruwar hakan ke da wuya sai ga ruwan kibiyoyin
wuta a sama daga can bangaren da abokan gaba
suka fito, saboda yawan kibiyoyin a sararin
samaniya sai mutum yayi zaton cewa tsuntsayen
duniya ne kaf! Suka taru suke shagalin biki
Kaico, masifa bata da dadi, nan fa kibiyoyin wutar
suka rinka zubowa akan garkuwoyin dakarun
birnin zamar amma saboda yawansu sai da
wadansu kibiyoyin suka rinka sukan dakarun a
kafafunsu, kai wasu ma garkuwoyin karfen suka
rinka hudawa suna soke dakaru suna mutuwa
gashi babu damar a mike a mai da martani.
Kafin a ankara abokan gaba sun kashe sama da
dakaru dubu biyu nasu kalmaru,
Al'amarin da yayi matukar fusata kalmaru kenan
ya kwarara uban IHU yana mai yin inkiya ga
dakarun nasa na musamman masu bakaken kaya.
Nan take kuwa kasa ta tsage sai dakarun suka
shige cikinta kimanin su dubu uku suka bace bat
a cikin karkashin kasa basu baiyana a ko ina ba
sai a can gaba kimanin nisan tafiyar sa'a guda
inda rundunar su sarki Daryan take kawai sai gani
akayi sun taso sama daga cikin karkashin tsakiyar
abokan gaba sunyi sama tamkar daga cikin baka
aka harbosu sun luluka kafin su dawo kasa sai
suma suka rinka jeho mugayen wukake da kibiyoyi
suna kashe dakarun da suke harba wadannan
kibiyoyin wuta ga rundunar su kalmaru. Nan fa
abin al'ajabi ya faru domin kuwa cikin kankanin
lokaci suka kashe kaso biyu cikin kaso uku na
dakarun masu kibiya.
Koda ganin abinda ya faru sai sarki Daryan ya
fusata ainun shima ya kwalawa nasa dakarun
masu bakaken tufafi kira, ai kuwa sai gasu suma
sun ratso kasa sun taso sama sun afkawa nasu
kalmaru suka ruguntsume da azababben yaki a
sararin sama tamkar tsuntsaye.
Da yake sarkin yawa yafi sarkin karfi sai aka fara
karkashe dakarun su kalmaru. Koda shugaban su
ya ga ana yi musu barna sai ya busa wani kaho,
take shida yaranasa suka yo kasa suka nutse a
cikin kasa.
Har dakarun sarki Daryan masu bakaken tufafi sun
yunkura zasu bisu izuwa cikin karkashin kasar sai
sarki Daryan ya hanasu yana mai daka musu
tsawa sannan kuma ya kece da dariyar mugunta
yace, ai fada da gudu tsoro ne,
Na tabbatarda cewa kibiyoyin wutar da muka
harba musu dole ne muyi musu mummunar barna,
ko ba komai mun karya lagonsu don sai sun firgita
damu bare kuma yanzu mu karasa garesu suga
wannan tsananin yawa namu tunda mun ninkasu
sau dari.
Yanxu zamu karasa bakin dajin Hajarul maut inda
za'a yita ta kare.
Koda sarki Daryan yazo nan a zancensa sai
mahaifinsa sarki saumir ya kyakyale da dariya
yace, da kyau dana nima na sani cewa wannan
shiri da mukayi bana wasa bane,
Kasani cewa a wannan yaki ne zan cika burina
na daukar fansa a kan tsohon sarkin yakinsu
Ridwan.
Koda jin wannan batu sai sarki Daryan ya dubi
saumir yace, ya kai Abbana kayi sani cewa babu
yadda zakayi ka dauki fansa a kan sarkin yaki
Ridwan face idan mun shiga har cikin birnin
zamar saboda Ridwan bai fito wannan yaki ba
bisa rahoton da 'yan leken asirinmu suka kawo
mini, shima sarki Barham bai fito ba.
Wanda yake jagorantar mayakan birnin zamar ba
wani bane face tsohon abokin fadana kalmaru
saboda sarkin yakinsu wanda suka yi gasar
matsayinsa da Hamsaru dan attajiri yunaru.
Koda jin wannan batu sai mamaki da takaici ya
kama sarki saumir yaji kamar ya fashe da kuka
saboda ya dade yana shiri akan yadda zai rama
abinda sarkin yaki Ridwan yayi masa wato shima
ya sare masa hannu, ashirin sama duka
hannayen biyu yake so ya sare masa kuma
bayason ya mutu, so yake ya kamashi a hakan
ya tsareshi a kurkuku har izuwa karshen
rayuwarsa yana kunsar bakin ciki da takaici iri-iri
Cikin tsananin fishi sarki saumir mai murabus ya
dubi sarki Daryan yace haba ya kai dana me
yasa tuntuni baka gaya min wannan al'amari ba
sai yanzu?"
Ridwan yace, yadda nasan irin burin da kaci a
wannan yaki idan na sanar da kai ba karamin
bakin ciki zaka yi ba amma tunda yanzu ka sani
ina rokonka da ka hakura ka koma gida saboda
ina mai tabbatar maka da cewa wannan yaki da
za muyi yanzu ban taba yin mai hadarinsa ba da
muninsa a wannan nahiya.
Abba banason na rasaka don haka zai fi kyau ka
koma gida.
Ina mai tabbatar maka da cewa mune zamu sami
nasara a wannan yaki saboda zamu sami hadin
kan wasu daga cikin birnin zamar kasan kuwa
ance da dan gari akanci gari, ka sani cewa muna
da goyan bayan wazirin sarki Barham da attajiri
yunaru.
Akwai wani makirci da suka shirya mana wanda
shine gudunmuwarsu kuma sai bayan su sarkin
yaki kalmaru sun iso nan dajin Hajarul maut
sannan za'a kulla makircin a can cikin birnin
zamar,
Ina nufin su kalmaru suna nan suna yaki za'a
yiwa sarki Barham juyin mulki, tuni an gama duk
wannan shiri harma an shigar da dakarun sojojin
haya wadanda zasu taimakawa waziri ayi
wannan yaki kuma suna yin nasara za'a fito da
attajiri yunaru daga kurkuku.
Koda sarki Daryan yazo nan a zancensa sai
farinciki ya lullube saumir yace, ya kai dana
hakika kwakwalwarka tana ja sossai kuma yanzu
na gamsu cewar lallai mune zamu sami nasara a
wannan yaki koda kuwa anci galabarmu a nan
filin yaki.
Kayi hakuri ya kai dana bazan iya komawa gida
ba tunda har nayi damara na fito wannan yaki
har sai takibina tasha jinin abokan gaba mai
yawa.
Koda jin haka sai idanun sarki Daryan suka ciko
da kwallah saboda yasan halin mahaifinsa indai
yayi magana baya sauyawa.
Ba komai ne yasa idanunsa suka ciko da kwallah
ba face bokayensa sun gaya masa cewa lallai a
wannan yaki zai rasa wani babban masoyinsa.
Da farko yayi tunanin cewar a cikin manya
abokansa ne zai rasa daya wadanda suna daga
cikin manyan dakarun yakin kasar wadanda ake
takama dasu amma da yaga mahaifinsa ma ya
fito wannan yaki sai zuciyarsa ta kama wasi-wasi
yana mai zargin cewa anya kuwa ba mahaifinsa
zai rasa a wannan yaki ba?"
Amsar da ya kasa baiwa kansa kenan,
Kawai sai ya zare takobinsa ya kwarara uban
IHU, suma sauran miliyoyin dakarun nasa sai
suka zare takubbansu suka kwarara uban ihun
nasu ya cika dajin gaba daya da amsa kuwwa ya
firgita komai da kowa domin har sai da kasa ma
tayi girgiza tamkar duk abinda ke kanta zai rufta
cikinta.
Hatta su kalmaru dake can bakin dajin Hajarul
maut sai da suka jiyo wannan ihu kuma suka
firgita ainun amma saboda suna da tsananin
Kishin kasarsu
Gamida da kekashasshiyar zuciya sai suka dake
suka tsaya cak a inda suke ko motsi basuyi ba
har sai da aka hango abokan gaba sun taho a
cikin azababben gudu sun ta da kura suna
wannan ihu da kiraji har dudufniyarsu ta haddasa
karamar girgizar kasa saboda yawansu.
Duk wannan kwarjini nasu baisa dakarun su
kalmaru sun razana ba.
Sai da ya rage tazarar kimanin zira'i arba'in a
tsakanin rundunonin biyu sannan kalmaru ya zare
takobinsa shima

1 Comments On MAZA SUN FADI 1 to 4
avatar
abubakar-abdullahi-6

1 year ago

Reply

yes

Please Login or Register in order to submit comment