Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yaki da mukayi har da
kake cewa yanzu muka fara yaki dashi alhalin kai
bakaje filin yakin ba?"
Koda jin wannnan tambaya sai sarki Barham yayi
murmushi yace, ai faduwar babbar giwa ba wasa
bace, inda sarki Daryan ya fadi to da ajikinama
sai naji alama,
Baya ga haka bisa binciken da nayi sarki Daryan
ba zai mutu ba a wannnan yaki domin akwai
wadansu abubuwa da aka kaddara masa yinsu
kafin ajalinsa kuma har yanzu bai gabatar dasu
ba,
Koda Kalmaru yaji wannan batu sai jikinsa yayi
sanyi kuma hankalinsa ya tashi ya dubi sarki
Barham cikin alamun damuwa yace, ya
shugabana to ni kuma me kasani akaina bisa
bincikenka?
Sarki Barham yayi murmushi yace Lokacin da ya
dace kasan amsar wannan tambaya taka bai yi ba
saboda haka ka kara sauraro.
Ya kamata ace kun tambayeni ko akwai matsala
anan gida bayan Tafiyarku
Koda jin wannnan batu sai gimbiya lazima ta
matso gaban sarki tace ai tabbas mun san cewa
akwai wani abun da ya faru amma zaifi kyau
yanxu mu karasa gida, inyaso bayan mun huta sai
mu zauna sossai a tattauna,
Da jin haka sai sarki Barham yayi murmushi yace
da kyau 'yata inda kike matukar birgeni kenan
kina da tunanin ya kamata,
Nan sarki ya juya ya kama dokinsa ya hau,shima
Kalmaru sai mayarda takobin daraja cikin rigarsa
ya kama dokinsa ya haye itama lazima ta hau
nata dokin sannnan aka dunguma gaba daya a
juya aka koma cikin birnin zamar.
Ana isa cikin gari sai dakaru da Kalmaru suka
raka sarki har kofar gidan sarauta, sannnan suka
yi masa sallama kowannensu ya nufi gidansu
domin iyalinsa su ganshi,
Da yawa daga cikin iyalan dakarun da suka tafi
wannan yaki sun zo sunyi dafifi a kofar gidan
sarautar tunda labarin yazo cewar gasu nan sun
dawo suna daf da karasowa saboda tsananin
damuwa da kaguwar son tabbatar da sun rayu ko
sun mutu a can filin daga amma da dakarun suka
gama isowa gaba dayansu duk maccen da bata ga
mijinta ba ko 'yan uwan da basu ga dan uwansu
ba sai kaga sun kama kuka,
Komai rashin tausayin mutum idan yaga yadda
wadanan iyalai ke kuka saboda rashin da sukayi
dole ne ya tausaya musu. MAZA SUN FADI!!! LITTAFI NA 4 PART 5

Komai rashin tausayin mutum idan yaga yadda
wadanan iyalai ke kuka saboda rashin da sukayi
dole ne ya tausaya musu.
Shi dai jarumi Kalmaru ana isowa kofar gidan
sarautar bayan an yiwa sarki sallama bai tsaya
duba mahaifinsa Ridwan ba da kuma baiwar
mahaifinsa wacce ya dauketa a matsayin uwa
saboda dama a ranar da sukayi bankwana Ridwan
ya dubeshi yace ya kai dana na yarda da kai dari
bisa dari kuma naji a jikina cewar duk irin
tsananin da xaka fuskanta a wannan yaki sai ka
dawo gida a raye don haka duk ranar da kuka
dawo bazamu fito ba taryar ka ba sai dai mu
jiraka a gida,
A Lokacin da Kalmaru yaji wannan batu daga
bakin mahaifinsa sai yayi murmushi ya
rungumeshi a kirjinsa yace,ya kai abbana nima
nayi maka alkawarin cewar komai rintsi da
tsanani zan dawo gida a raye ko don na cika
maka burinka nason ganin karshen sarki saumir
sai dai idan bai fito wannan yaki ba,
Koda jin haka sai Ridwan ya kamu da tsananin
farin ciki sannnan yasa masa albarka suka yi
bankwana,
Lokacin da jarumi Kalmaru ya baro kofar fada ya
tunkari gida cikin murna da dokin ya isa gidan
domin ya sadu da iyayensa,
Sai kawai yaji tunanin gimbiya lazima ya fado
masa, take ya rinka ganin fuskarta a Lokacin da
take yi masa murmushi sannnan kuma yayi ta
tuno da duk abubuwan da suka faru tsakaninnsu
da ita tun daga ranar da aka tafi wannan yaki
kawo Izuwa dawowarsu kuma yana tuna cewa in
ba don ita da tuni yanzu ya dade da shekawa
barzahu,
Lallai tana binsa bashi a rayuwa, bashin da bai san
da abinda zai biyata shi ba, haka kuma sai ya
tsinci kansa yana mai mamakin irin jarumtakarta
wacce har ta iya cetonsa daga shairin sarki
Daryan
A takaice dai shi yaji ya kamu da tsananin sonta
a cikin zuciyarsa amma sai ya kudiri niya cewa
zai danne soyayyarsa a cikin ransa muddin ba ita
ce ta nuna masa tana sonsa, haka dai Kalmaru
yaci gaba da wannnan zancen zuci har ya iso
gida,
A kofar gidan ya iske mahaifinsa da mahaifiyar
tasa a tsaye sun kura masa idanu sunata
murmushi.
Koda Kalmaru ya hangosu sai ya kasa hakurin ya
karaso akan doki don haka sai ya duro kasa ya
rugo da gudu Izuwa garesu suka rungumeshi duk
su biyun kowannensu na kwalar farin ciki, tsawon
yan dakiku suna kankame da juna sannnan suka
janye yakinsu daga cikin nasa,
Koda ta dubi jikin Kalmaru taga ya cika da tabon
raunuka da dinki sai ta fashe da kuka saboda
tausayinsa da kuma kaunarsa.
Koda ganin haka sai Ridwan yayi murmushi ya
kawar da ita gefe ya dubi Kalmaru yace kada ka
damu da kukanta kasan su mata zuciyarsu tana
da rauni amma ni ko kadan banji tausayinka bisa
wadanan raunikan dake jikinka,
Abinda nake bukata daga gareka kawai shine naji
irin nasarar da ka samo a wannan yaki? "
Koda jin wannnan tambaya sai Kalmaru ya kama
yin murmushi yayi shiru kamar ba shida Abin fada,
hakan ce tasa Ridwan yayi fushi ya daka masa
tsawa yace idan baka da Abin fada ai sai kayi
magana baka tsaya kana yi mini murmushin banza
ba,
Yana gama fadin Hakan sai ya juya ya nufi kofar
gida zai shiga wani irin haske da yaga ya dallare
bangon gidan nasa ne yasa ya juyo da sauri,
Take yayi arba da takobin daraja a hannun
Kalmaru har ya zarato daga cikin kufenta, nan
take idanun Sarkin yaki Ridwan suka zazzaro ya
kamu da tsananin tsoro, mamaki da kuma farin
ciki ya rasa abinda zai yi tsakanin kuka da dariya,
kawai sai ya rugo Izuwa kan Kalmaru ya
rungumeshi yana ta sumbatar goshinsa,
Daga can kuma sai ya janye jikinsa daga cikin
nasa suka fuskanci juna sossai a Lokacin da
hawaye ya zubo masa ya dubi Kalmaru cikin
nutsuwa yace ya kai dana hakika ka sami babbar
nasara wacce ta gagareni tunda har ka iya kashe
babban makiyina sarki saumir
Tsananin farin ciki ne bisa wannan nasara taka ta
haifar da zubar hawayena amma kuma na kamu
da tsananin bakin ciki gamida tsananin tashin
hankali bisa ganin wannan takobi a hannunka,
Akan wane dalili ka dauko wannan takobi? "
Kashe saumir kadai ya isheka abin alfahari ba sai
ka dauko takobinsa ba domin wannan takobi tafi
komai da kowa muhimmanci a wajen sarki Daryan
ina mai tabbatar maka da cewa sarki Daryan zai
ci gaba da farautar rayuwarka da lafiyarka kamar
yadda mai fama da yunwa da kishirwa ke farautar
abinci da ruwa.
Babbar matsalar itace bazaka iya mayarda
wannan takobi ba gareshi sai dai shi da kansa ya
karbeta da hannunsa da karfin tsiya, zaman
wannan takobi a hannunka ba karamar masifa ce
ba gamida da babban tashin hankali kuma duk
wanda ma ya rabeka yana cikin bala'i mara
misaltuwa kuma a koyaushe zai iya rasa
rayuwarsa da lafiyarsa.
Koda Sarkin yaki Ridwan yazo nan a zancensa sai
mamaki ya turnuke Kalmaru ya dubi Ridwan cikin
alamun rashin fahimta yace saboda me kace ba
zan iya mayar masa da takobinsa ba? "
Ridwan yace haka sirrin takobin yake kuma duk
iya kokarin da zaka yi wajen mayar da ita ba zaka
iya ba don ko ka kaita can wajensa ba zai iya
riketa ba sai ta dawo da kanta wajenka,
Yanzu dai mu karasa cikin gida domin ka zauna
ka huta kuma kaci abinci, ba tare da gardamar
komai ba kuwa Kalmaru ya bisu Izuwa cikin
gidan.
Bayan Kalmaru ya huta kuma yaci abinci sai
Ridwan ya shigo cikin dakinsa inda ya iskeshi a
kishingide yana kallon rufin dakin alamun tunani,
koda ganin haka sai Ridwan ya zauna a kusa
dashi sannnan ya dafashi, kamar wanda ya farka
daga mafarki haka Kalmaru yayi firgigit ya mike
zaune, Ridwan ya bushe da dariya yace kai dana
hakika nasan cewa ruwa baya tsami banza,
Lallai tunanin da kake yi yanzu na musamman ne,
Ba tunani ne na tashin hankali ba, tunani ne irin
na ma'abota soyayya.
Koda jin wannnan batu sai mamaki ya turnuke
Kalmaru yace ya kai abbana shin kana samun
labarai ne daga wajen aljanu?"
Ridwan ya sake bushe da dariya yace A'a ko
kadan bana samun labarai daga wajen aljanu
tsabar sanin rayuwa ne da kuma lura da irin
yanayin da na ganka a ciki saboda nima na taba
shiga irin yanayin dana ganka yanzu, sa'adda na
kamu dason mahaifiyarka.
Koda yazo nan a zancensa sai nan da nan
idanunsa suka kada suka ciko da kwalla don haka
sai yayi sauri ya kau da kansa ga barin kallon
Kalmaru yace bayan Tafiyarku yaki Izuwa dajin
hajarul maut, waziri da Hamsaru da yunaru sunyi
yunkurin juyin mulki,inba don cewa nayi zargin
hakan zata iya faruwa bana sanar da sarki da tuni
an cimu da yaki acikin gida.
Koda jin wannnan batu sai hankalin Kalmaru ya
dugunzuma ainun ya dubi Ridwan cikin mamaki da
tsoro yace me yasa sarki bai bamu wannan labari
ba dazu sa'adda muka iso?"
Ridwan yayi murmushi yace ai saboda bayason
hankalinku ya tashi ne kuma yasan cewa zaku
sami labari a gari,
Kalmaru yayi dogon ajiye numfashi sannnan yace
ina fatan dai an kashe Hamsaru da waziri? "
Ridwan ya girgiza kai yace ai sun sami nasarar
guduwa,.hakan kuma shine babban tashin
hankalinmu saboda nasan cewa babu inda zasu je
face birnin sarki Daryan domin su sake hada kai
dashi,
Babbar illar itace sun san sirrin birnimu kuma
kusan cewa da dan gari akan ci gari.
Kalmaru ya gyada kai cikin alamun tsananin
takaici sannnan yace haka ne amma babu komai
zamu canja gaba dayan hanyoyin tsaron garin nan
sannnan kuma ina son ka sani cewa dole ne mu
kara matsanancin tsaro a kurkuku saboda a
koyaushe su Hamsaru zasu iya kokarin kawo
harin kubatar da mahaifinsa yunaru saboda shine
kadai garkuwarmu a garesu.
Ridwan yace kwarai kuwa dana hakika kana da
basira sossai da hangen nesa shiyasa nake
alfahari da kai, amma fa inaso ka sani cewa
yanxu fa ba yunaru ne kadai abin farautarsu ba
har da kaima.
Kai ina tabbatar maka da cewa ma hankalin sarki
Daryan sai yafi karkata a kanka tunda kana tare
da takobinsa ta daraja sannnan kuma zuciyarsa
tana ruruwa da wutar son daukar fansa a kanka
bisa kashe mahaifinsa da kayi,
Bisa wannan daliline nake son na baka wani
taimako yanzu ina zuwa.
Koda da gama fadin Hakan sai Ridwan ya mike
tsaye ya fice daga cikin dakin ya tafi Izuwa tasa
turakar, jim kadan sai gashi ya dawo dauke da
wata laya wacce akayita da jaf fata, nan take ya
daurawa Kalmaru layar
A wuyansa sannnan ya dubeshi cikin murmushi da
murna yace daga yau komai gumu, duk wuya duk
tsanani kada kayarda wannan laya ta fita daga
wuyanka koda kuwa wanka zakayi har sai a ranar
da ka tabbatar da cewa munga bayan makiyinmu,
Ina mai tabbatar maka da cewa in dai kana tare
da wannnan laya babu wani Aljani da ya isa ya
dosheka da niyar cutar da kai kuma babu wani
sihirin tsafi da zai iya tasiri a kanka.
Koda jin wannnan batu sai Kalmaru ya kama layar
daga jikin wuyansa ya kalleta da kyau kuma ya
sumbaceta sannnan ya yunkura zai cireta daga
wuyan nasa sai Ridwan yayi sauri ya dafe
hannunsa yace saboda me kuma kake yunkurin
cire ta alhalin na gayamaka muhimmancinta? "
Cikin alamun matukar damuwa yace ya kai
abbana nafison kai ka kasance tare da wannnan
laya saboda rayuwarka tafi tawa muhimmanci a
wajena,
Lallai Banason na rasaka kamar yadda na rasa
mahaifiyata ta ainihi.
Koda jin wannnan batu sai Ridwan ya kamu da
tsananin tausayin Kalmaru gamida tsananin
kaunarsa,
Nan take hawaye ya zubo masa sai suka rungume
juna suna kuka har Izuwa tsawon yan dakiku
sannnan Ridwan ya janye jikinsa daga cikin nasa
ya fuskanceshi yace ya kai dana kada ka damu
da rayuwata a kan taka saboda ni yanzu babu
wani buri nawa a duniya wanda bai cika ba tunda
naga girmanka kuma naga Lokacin da ka gajeni
sannnan gashi ka kashe babban makiyina a
duniya, kai kuwa yanzu ne ma ka taka matakin
farko na rayuwarka ka tuna cewa idan fa baka
rayu ba ka sami magaji shi kenan sarautar Sarkin
yaki birnin nan ta bar gidanmu har abada.
Ina mai tabbatar maka da cewa ni zan iya kare
kaina daga dukkan shirin abokan gaba.
Inda kuwa ba zan iya ba da ban kawo yanzu ba
don da tuni sun gama dani,saboda haka sai ka
kwantarda hankalinka, gobe da safe ka shirya mu
tafi Izuwa gidan sarki zamuyi zama na musamman
tare da manyan amintattun 'yan majalisarsa
domin mu tattauna akan matakan da ya kamata
mu dauka don kare birninmu daga shairin abokan
gaba. MAZA SUN FADI!!! LITTAFI NA 4 PART 6

Ina mai tabbatar maka da cewa ni zan iya kare
kaina daga dukkan
shirin abokan gaba.
Inda kuwa ba zan iya ba da ban kawo yanzu ba
don da tuni sun
gama dani,saboda haka sai ka kwantarda
hankalinka, gobe da safe
ka shirya mu tafi Izuwa gidan sarki zamuyi zama
na musamman tare
da manyan amintattun 'yan majalisarsa domin mu
tattauna akan
matakan da ya kamata mu dauka don kare
birninmu daga shairin
abokan gaba.
A can birnin sarki Daryan kuwa bayan an gama
bikin binne gawar sarki saumir da kamar bayan
sa'a daya da rabi sai ga su Hamsaru tare da
wazirin sarki Barham sun iso garin, ana ganinsu
aka bude musu kofa suka shige ba tare da anyi
musu wani bincike ba,
Kai tsaye suka wuce har cikin fadar sarki Daryan
anan ne suka tsaya har sai da aka je aka sanar da
sarki isowarsu
Nan da nan kuwa sai ga sarki Daryan ya fito, ko
da yayi arba dasu Hamsaru a tsaye kawunansu a
sunkuye kuma babu wani annuri a kan fuskokinsu
sai jikinsa yayi sanyi kuma hankalinsa ya
dugunzuma domin ya fuskanci cewa lallai basu
sami nasarar yiwa sarki Barham juyin mulki ba,
Sarki Daryan ya dubi waziri da Hamsaru yayi
musu nuni da inda zasu zauna sannnan shima
yaje ya zauna akan karagarsa ta mulki, bayan sun
zauna gaba daya ba tare da ya sake kallon
fuskokinsu ba sai yace, wace irin matsala kuka
fuskanta wacce ta hanaku samun nasara? "
Koda jin wannnan tambaya sai Hamsaru yayi
gyaran murya ya dubi sarki Daryan a cikin
nutsuwa yace ya shugabana babban abinda ya
kawo mana matsala shine sarki Barham yayi
hasashen cewa zamu iya shirya masa wannnan
juyin mulki don haka ashe bai saki jikinsa ba a
wannnan dare dasu Kalmaru suka fito yaki saboda
yasan cewa manyan zakwakuran dakarunsa basa
nan, idan aka kawo masa harin sumame za'a iya
gamawa dashi farat daya, bisa wannan daliline
yayi bad kama a cikin dare ya fice daga cikin
gidan sarautar kuma yaje ya hada runduna ta
mayakannsa a wajen gidan sarautar,
Sai bayan mun sami nasara shiga gidan sarautar
mun kashe gaba dayan dakarun dake tsaron cikin
gidan sannnan shi da rundunar tasa suka shigo
suka ritsami,
Mun fafata kazamin yaki dasu amma cikin
kankanin lokaci suka kashe gaba dayan wadanan
dakaru namu na sojan haya,
Koda muka ga zamu hallaka idan muka ci gaba da
yakin nida waziri sai muka tsalleke katangar gidan
sarautar muka ruga da gudu dama can mun boye
dawakanmu a wani waje,
Muna zuwa wajen muka hau dawakanmu muka
fice daga cikin birnin gaba daya muna masu tsala
gudu amma duk da haka sai da dakaru yan kubau
suka biyo mu suna ta harbo muna kibiyoyi da kyar
da 'yan dabaru muka bace musu muka tsira da
rayuwarmu,
Sa'adda Hamsaru yazo nan a zancensa sai sarki
Daryan yayi ajiyar zuciya sannnan cikin tsananin
takaici sannnan ya dubi waziri da Hamsaru yace
mu ma bamu sami nasara ba a yakin da muka
gwabza dasu Kalmaru kuma a yakin nayi babban
rashi guda biyu,
Koda jin haka sai idanun su waziri suka zazzaro,
zuciyoyinsu suka buga da karfi
Cikin rawar murya waziri ya dubi sarki Daryan
yace ya shugabana wadanne abubuwa kenan ka
rasa?"
Sarki Daryan ya sake yin ajiyar zuciya a karo na
biyu yace na rasa takobin daraja koda jin haka sai
mamaki da tsoro ya kara turnuke waziri da
Hamsaru,
Ba zato ba tsammani sai suka ga sarki Daryan ya
bushe da mahaukaciyar dariya, lokaci guda kuma
sai ya tsuke bakinsa ya turbune fuska yace
hakama mun dauki abokan gabarmu da wasa
shiyasa muka sami wannan matsala duk da cewa
mun yi gagarumin tanadi akansu.
Ko a mafarki ban taba zaton cewa zan kasa
murkushe dakarun birninku ba a cikin kankanin
lokaci, lallai an shammaceni.
Inaso ku sani cewa yanxu ne zamu daura damarar
yin yaki na biyu amma zamu fara ne da yakin
sunkuru.
Abu na farko tuni na tura da kwararrun 'yan leken
asirin kasa domin su gano mini inda Kalmaru yake
a cikin birninku da inda yake ajiye takobina ta
daraja.
Kuma zanyi amfani daku wajen cika wannan aiki,
Burina shine nayi kicibis da Kalmaru a Lokacin da
yake tare da takobin tawa na kashe shi na karbi
abata, ku sani cewa muddin wannan takobi bata
dawo hannuna ba banida sauran kwanciyar
hankali kuma ba zamu taba samun nasarar yaki
ba akan sarki Daryan.
Inaso na kashe sarki Barham da tsohon Sarkin
yakinku Ridwan wato mahaifin Kalmaru domin na
dauki fansar ran mahaifina amma na sani cewa
abune mai wuyar gaske yin hakan saboda dole ne
yanzu a tsananta tsaro a birnin naku fiye da
koyaushe amma duk da hakan bayan 'yan leken
asirina sun kawo mini rohoto bisa binciken da na
turasu suyi nima zanyi bad da kama nasan yadda
nayi na shiga birnin don cika burina, masu iya
magana sunce da dan gari akan ci gari.
Don haka ina bukatar na zauna tare daku ku sanar
da ni sirrin duk hanyoyin shiga birninku dana
fitowa da kuma zuwa gidan su Kalmaru.
Bayan duk wadanan abubuwa idan har ban cika
burina akan Sarkinku da Kalmaru to ku sani cewa
kuma baku da sauran amfani a wajena.
Daga yanxu har Izuwa wannan Lokaci zan ci gaba
da baku mafaka ku ci ku sha daga da dadan irin
abinda nake ci kuma ga Kuyangi da barori da zasu
debe muku kewa.
Duk abinda kuke bukata najin dadin duniya ba
zaku rasa ba.
A karshe in dai babu nasara ku hada naku inaku
kubar mini kasata inba haka ba kuwa zaku rasa
rayuwarku domin babu abinda ganinku zai kara
mini face tsananin bakin ciki da tsanarku.
Yanxu babu abinda zamu gabatar har sai na sami
rahoto daga bakin 'yan leken asirina.
Koda gama wannan jawabi sai sarki Daryan ya
mike tsaye ya bar su Hamsaru a tsaye suna masu
binsa da kallo cikin kaduwa da mamaki har ya
fice daga cikin fadar gaba daya.
Nan dai suma suka fice daga cikin fadar suka tafi
Izuwa masaukinsu.
Wannan shine abinda ya faru tsakaninn su waziri
da sarki Daryan bayan sun sami nasarar guduwa
daga birnin zamar a Lokacin da suka yi yunkurin
yin juyin mulki amma basu sami nasara ba.
A can birnin zamar kuwa, Al'amarin da gimbiya
lazima kuwa bayan ta shiga gida ta ci abinci sai
ta shiga turakarta ta kwanta da nufin tayi bacci
domin ta huce gajiyar tafiya da ta yaki amma sai
idanunta suka soye taji ko kadan bata jin barcin.
Al'amarin da yayi matukar bata mamaki kenan
kuma ya bata tsoro saboda bata taba tsintar
kanta ba a cikin irin wannnan hali.
Ashe ba wani abu bane ya hanata yin wannnan
barci ba face tunanin jarumi Kalmaru.
Duk sa'adda ta runtse idanunta sai ta rinka ganin
fuskarsa, kai ko bude idanun nata ma tayi sai ta
rinka ganinnsa yanayi mata gizo a cikin dakin
yana baiyana yana bacewa.
Sai da ta shafe sama da rabin sa'a a cikin
wannan hali, Al'amarin da yasa taji cewar ba zata
iya jure rashin ganinsa ba kenan amma kuma sai
taga cewar ai ba kimarta bace yanzu ta tashi ta
tafi gidansu Kalmaru.
Idan ma taje din me zata ce ya kawota, haka
kuma sai ta tuno da shawarar da sarki Barham ya
bata cewar taja muruncinta da kimarta a wajen
Kalmaru har sai idan ya baiyana mata tasa
soyayyar karara a gareta sannnan itama ta
baiyana mata tasa soyayyar tata.
Koda ta tuno da wannnan batu sai hankalinta ya
kara dugunzuma ainun fiye da koyaushe saboda
ta fuskanci cewar rashin ganin Kalmaru zai iya
haddasa mata wani ciwon.
Da dai lazima ta ga bata da wata mafita a wannan
Lokaci sai ta dauko wani maganin barci mai karfi
wanda likitanta ya bata tasha da yawa fiye da
yadda ma aka ka'idance mata.
Ai kuwa tana gama shanye maganin ta baje akan
gado sai barci ya saceta. MAZA SUN FADI!!! LITTAFI NA 4 PART 7

Kuma na karshe

Da dai lazima ta ga bata da wata mafita a
wannan Lokaci sai ta dauko wani maganin barci
mai karfi wanda likitanta ya bata tasha da yawa
fiye da yadda ma aka ka'idance mata,
Ai kuwa tana gama shanye maganin ta baje akan
gado sai barci ya saceta,
Al'amarin 'yan leken asirin da sarki Daryan ya
aika Izuwa birnin warzas domin su hada kai da
dakarunsu na can wato yan uwansu yan leken
asiri sai da magarib ta kawo kai sannnan suka
iso birnin na warzas.
Birnin warzas ya kasance wata 'yar karamar kasa
wacce gaba dayan jama'ar dake cikinsa ma basu
wuce adadin miliyan daya da rabi ba.
Sarkinsu kuwa wani mashahurin dan caca ne
wanda babu abinda yakeso a rayuwarsa sama da
kudi, indai zai samu kudi to fa babu abinda ba
zai iya ba.
Ya kware a kasuwanci, kai yana da yara ma
wadanda suka kasance mashahuran barayi.
Bisa wannan daliline yake da kwararrun dakarun
'yan leken asiri a birninsa wadanda suke gano
masa inda za'a sami dukiya mai yawa.
Shi dai wannan sarki na birnin warzas ana
kiransa da suna murzalu.
Duk irin tsananin son kudin sarki murzalu bai taba
tunanin kai wargi ba a kasar zamar da birnin
sarki Daryan ba don komai ba sai don kura ma ta
san gidan mai babbar sanda.
Shugaban dakarun leken asirin da aka tura birnin
warzas sunansa zilla kuma ya kasance sadaukin
gaske wanda bai san tsoro ba.
Lokacin da sadauki zilla tare da yaransa mutum
tara suka iso birnin warzas sai suka wuce kai
tsaye Izuwa gidan sarki murzalu.
Cikin tsananin farin ciki da mamaki sarki murzalu
yayi musu tarba ta karamci yasa aka kawo musu
abinci da abin sha na alfarma suka kimtsa.
Bayan nan ne ya dubesu yace ya ku wadanan
baki masu daraja wane sako kuka kawo mini
daga wajen Sarkinku? "
Koda jin wannnan tambaya sai zilla yayi gyaran
murya sannnan ya janyo wata katuwar jaka da
suka zo da ita ya budeta sai ga dinare acikinta
mai yawan gaske.
Koda ganin wadanan kudade sai sarki murzalu ya
dimauce, idanunsa suka zazzaro, bai san sa'adda
yawu ya dalalo daga bakinsa ba yace, wannan
dukiyar fa ta mecece?"
Ko da jin wannnan tambaya sai sadauki zilla yayi
murmushi yace, wannan dukiya sarkina ne yace a
kawo maka bisa wani gagarumin aiki da yake son
ka aiwatar masa.
Yayin da sarki murzalu yaji wannan batu sai
jikinsa yayi sanyi ya dubi zilla cikin alamun
tsananin damuwa yace ina fatan dai Sarkinka
baso yake na baku gudunmuwar dakarun yaki ba
a kan yakin da kukeyi da sarki Barham?
Koda jin wannnan tambaya sai zilla yayi
murmushi yace, Ya shugabana ba haka bane,
amma dai bukatar taso tayi kama da hakan.
Abinda yake da bukata kawai shine ka zabo
kwararrun 'yan leken asirinka ka hadasu damu
domin mu shiga cikin birnin zamar saboda mu
gano sirrin hanyoyin shiga birnin dana fita da
kuma hanyoyin shiga gidan sarautar su da gidan
tsohon Sarkin yakinsu domin a zuba ido a kan
jarumi Kalmaru asan inda ya ajiye takobin daraja
ta sarki Daryan.
Koda sadauki zilla yazo nan a jawabinsa sai
hankalin sarki murzalu ya dugunzuma ainun
domin ga bikin zuwa ne amma babu zanin
daurawa.
Sarki murzalu ya dubi zilla kamar zaiyi kuka yace,
ya kai wannan manzo kayi sani cewa wannan
aiki da Sarkinku yake so nayi masa yanada
matukar sauki a wajena tamkar cire sillin gashi
daga cikin tandun mai amma kuma hadarinsa dai-
dai yake da mutum ya tafi farautar ajalinsa.
Abinda yasa na fadi haka kuwa shine idan har
sarki Barham ya gano cewa akwai sa hannuna a
cikin wannan aiki da za'a yi zaizo birnina ne a
dare daya ya murkushemu.
Koda zilla yaji wannan batu sai ya bushe dariya
sannnan yace ai tuni sarkina yayi tunani akan
hakan kuma ya samar da dabarar da zata kawar
da faruwar hakan.
Dabarar kuwa itace daga cikin zakwakuran
mayakanka masu tsananin juriya da naci, kuma
dole ne su shiga a cikin shiga da siffar da baza a
taba gane cewa daga birninka suka fito ba.
Mataki na karshe kuma shine dole ne. su tafi da
shirin cewar da zarar sunga asirin su zai tonu a
kamasu dole ne su kashe kansu kafin suje hannu
bisa wannan daliline ma ya aiko maka da
miliyoyin wannan dinare domin ka baiwa dakarun
da zasu yi wannan aiki dukiya mai yawan gaske
wacce zasu iya siyar da ransu akanta kuma duk
da haka kaima sai ka sami rarar kudin masu
yawan gaske.
Sa'adda zilla yazo nan a zancensa sai sarki
murzalu ya bushe da dariyar farin ciki ba don
komai ba sai saboda yasan cewa tabbas ya sami
mafita.
Nan take ba tare da bata wani lokaci ba sarki
murzalu ya tura aka kirawo masa wadansu
zakwakuran dakarunsa mutum goma.
Shida daga cikinsu wadansu kyawawan 'yan mata
ne na gaban kwatance kuma sun kasance
sadaukai, gwanayen iya yaki, juriyar wahala
gamida nacin tsiya.
Babbar cikinsu ana kiranta da suna Rizaila.
Sauran mutum biyar din kuwa wadansu matasan
samari ne majiya karfi masu takama da karfin
damtse gamida jin samartaka.
Lokacinda wadanan jarumai guda goma suka
gabata gaban sarki murzalu sai suka zube kasa
suka kwashi gaisuwa sannnan suka mike tsaye
suka koma gefe daya suka jeru a layi.
Zilla ya karewa dakarun kallo cikin alamun raini
sannnan ya dubi sarki murzalu yace haba ranka
ya dade yanzu har da mata zaka hadamu a cikin
wannan aiki, lallai kuwa ashe ba zamu taba
samun nasara ba.
Koda jin wannnan batu sai sarki murzalu yayi
murmushi sannnan ya dubi Rizaila yace yake
Rizaila fito tsakiyar fada
Nan ki tsaya,take Rizaila tabi umurni ta taho
tsakiyar fadar ta tsaya tana mai gyaran tsayuwa.
Sannnan ta zare takobinta sarki murzalu ya sake
yin murmushi ya dubi zilla yace na yarda ka
umurci gaba dayan yaranka su yaketa, idan suka
sami nasara a kanta ka dauke jakar kudI nka ku
tafi ka gayawa Sarkinka cewa na kasa.
Koda jin wannnan batu sai sadauki zilla ya dubi
sauran yaransa su duka suka bushe da dariya
kuma yayi musu inkiya, take dakarun nasu su
tara suka zare takubbansu suka ruga da gudu
Izuwa kan Rizaila aka kacame da azababben
yaki, nan fa gaba dayan jama'ar dake cikin fadar
suka fara ganin al'ajabi dakarun guda tara suka
yiwa Rizaila zobe suna kai mata sara da suka ta
sama da kasa amma sai ta rinka kare duk hare
haren nasu kuma tana maida martani.
Ai kuwa sai gashi tana tarwatsasu da karfin tsiya
da kuma tsagwaron iya yakinta, sai da aka shafe
dakiku masu yawa a haka amma an rasa mutum
daya

1 Comments On MAZA SUN FADI 1 to 4
avatar
abubakar-abdullahi-6

10 months ago

Reply

yes

Please Login or Register in order to submit comment