Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nacinsa Daryan kasa
hallakashi.
Ana cikin haka ne Daryan ya sami nasarar buge
takobi guda daga hannun kalmaru ta fadi can gefe
daya.
Kafin kalmaru ya ruga inda takobin tasa take ya
daukota tuni Daryan ya gabza masa wawan dundu
a gadon bayansa, take kalmaru yaji kamar kashin
baya nasa ya karye bai san sa'adda ya kife kasa
ba da rub da ciki yana mai rusa uban ihu, kawai
sai Daryan ya daga takubbansa biyu sama da
nufin ya tsira gadon bayan kalmaru,
A dai-dai wannan lokaci ne gimbiya lazima ta
hango abinda ke shirin faruwa ga kalmaru kawai
sai ta falfalo da azababben gudu daga inda take,
saboda karfin gudun har tashi sama take tana
tsallake mutane amma da zarar kafarta ta taba
kasa sai kaga ta sake yin sama, kafin takubban
sarki Daryan su caki bayan kalmaru tuni gimbiya
lazima ta doki kugun sarki Daryan da kafafunta
biyu ,
Saboda karfin dukan sai da yayi sama fuskarsa ta
gwaru da garkuwar wani Badakare,
Take hakorinsa guda yayi fitar burgu daga cikin
bakinsa ya fado kasa tim kuma magashiyan
amma sai ya yunkura ya mike tsaye ya juyo ya
dubi inda kalmaru ke kwance kawai sai ya hango
gimbiya lazima ta sunkuya ta dauki kalmaru ta
sabashi a gadon bayanta tamkar ta saba silin
kara,
Kawai sai ta juya da baya taci gaba da gudu
kuma kuma tana saran abokan gaba,
A sannan ne filin yakin ya dada kacamewa fiye da
ko yaushe,
Aka ci gaba da asarar dubunnan rayuka ba adadi.
Cikin tsananin fushi sarki sarki Daryan ya kurma
uban ihu yayin da bakinsa ke yoyon jini kuma
kansa ya fara kumbura jini yaci gaba da dibarsa
amma duk da haka sai ya yunkura da nufin ya
ruga ya iske jarumin da ya dauke kalmaru amma
sai dakarunsa suka yi wuf suka rike shi.
Adaidai wannan lokacin ma karfinsa gaba daya ya
kare ya sulale kasa sumamme.
Koda kowanne bangare suka ga shugabansu na
cikin mugun hali sai aka shiga busa kahon
janyewa daga filin yaki,
Nan da nan kowacce runduna taja da baya aka
daina yakin, kowanne bangare suka koma
sansaninsu ya zamana cewa filin yakin ya watse
babu kowa sai gawarwaki dake kwance a kasa
fululu ba adadi sai kuma jini da ya malala yana ta
gudu akan kasa, kai kace idaniyar ruwa ce a dajin
Hajarul maut inda aka fafata kazamin yaki
tsakanin dakarun birnin zamar da dakarun birnin
sarki Daryan,
A can birnin zamar kuwa bayan sarkin yaki
kalmaru ya kwashi dakaru yaki sun fice daga cikin
birnin,
Magariba nayi sa'adda gari yayi duhu sai ga
wadansu dakarun sojojin haya kimanin su dubu
dari sun zo a cikin siffar fatake dauke da hajoji
bisa dawakai, rakumai, da alfadarai,
Ashe a cikin buhunhunan can kasan hajojin akwai
makamansu na yaki a boye,
Kowanne Badakare yayi shiga irinta bafatake,
babu yadda za'a yi a gane cewa shi ba bafatake
ne ba.
Da isowar wadannan fatake sai ga Hamsaru dan
attajiri yunaru yazo daga cikin gari.
Nan take ya gabatar da fataken a wajen masu
gadin kofar yasanar dasu cewa ai bakin
mahaifinsa ne kuma dama an san da zuwansu
Ba tare da anyi musu wani kwakkwaran bincike ba
sai a ka bude musu kofa suka kado ababan
hawansu,
Suka shigo cikin gari, maimakon Hamsaru ya kai
wadannan fataken inda suka saba saukar bakinsu
sai ya hadasu da wani hadimin gidansu suka bi
wata barauniyar hanya suka tafi izuwa wani gida
dake can bayan gari nesa da mutane sossai,
Shi dai wannan gida mallakin wazirin sarki Barham
ne kuma gidan gona ne inda ake kiwon dabobbi
kuma ana ajiye amfanin gona,
Gidan yana da girma sossai don haka zai iya
daukar sama da mutum dubu dari uku ma.
Da isar wadannan dakarun sojojin haya sai suka
iske tuni an shirya musu abincinsu don haka sai
suka yi murna.
Nan take suka zauna suka cika cikinsu sukayi
hani'an kowannensu ya sami wuri ya kwanta yana
huce gajiya.
*** *** ***
Har yanzu akwai sauran rina akaba domin kuwa
akwai sauran asarar rayuka kawai kuyi hakuri ku
biyoni izuwa gobe. MAZA SUN FADI!!!! LITTAFI NA 3 PART 6

Da isar wadannan dakarun sojojin haya sai suka
iske tuni an shirya musu abincinsu don haka sai
suka yi murna.
Nan take suka zauna suka cika cikinsu sukayi
hani'an kowannensu ya sami wuri ya kwanta yana
huce gajiya.
Al'amarin Hamsaru kuwa bai zame ko ina ba sai
gidan waziri inda suka kebe a cikin turakarsa ta
barci,
Bayan sun rufe kofofin dakin da tagoginsa don
kada wani yaji abinda zasu tattauna sai suka
zauna suka fara magana a acikin karamar murya
tamkar masu yin rada,
A sannan ne Hamsaru ya dubi waziri cikin
murmushin farinciki yace ya shugabana na sami
nasarar shigowa da dakarun mu na sojojin haya
ko kyakkyawan bincike ba'a yi ba a kansu.
Koda jin wannan batu sai waziri yai shiru fuskarsa
na nuna alamun damuwa yana tunani,
Hamsaru ya dafashi yace ya shugabana me ya
faru? "
Shin kana ganin cewa asirinmu zai tonu ne?"
Waziri ya kawo gauron numfashi ya ajiye sannan
yace,
Nayi mamakin da kace ba'a yi kyakkyawan bincike
ba akansu alhalin sanan cewa yanzu dole ne sarki
yasa a tsananta tsaro tunda manyan dakarun mu
na yaki wadanda ake takama dasu basu nan sun
fita yaki.
Hamsaru yayi murmushi yace karka ka damu ai
tunda yammacin jiya na siye gaba dayan masu
gadin kofar birnin,
Domin babu wanda ban baiwa albashinsa sau uku
ba,
A yau dinnan kuma na nuna musu ne cewar hajar
da aka kawowa mahaifina riba ce mai, kuma na
kara baiwa kowa albashinsa sau biyu,
Shiyasa suka gamsu suka ki yin kwakwaran
bincike tunda sun san cewa basu taba samun
kudade masu yawan haka ba.
Koda jin wannan batu sai waziri ya bushe da
dariya yace to yanzu naji zance.
Ai inda ba kayi wannan dabara ba da sai nace
sarki Barham tarko ya haka kawai jira yake mu
fada cikinsa ya maida kasa ya rufe,
Yanzu na gamsu cewa mun tsallake matakin farko
a cikin shirinmu, saura mataki na biyu yaya zaka
shirya shi? "
Hamsaru ya numfasa yace,a yanzu haka nasa a
lura da duk motsin sarki a cikin gidan sarautar har
izuwa lokacin da dare zai raba domin musan
acikin dakin da zamu riskeshi muyi masa kisan
farat daya,
Waziri yayi murmushi yace wannan ma yayi dai-
dai,Mataki na uku fa?
Hamsaru ya mike tsaye yayi 'yar tafiya taku uku
sannan ya juyo ya fuskanci waziri yace mataki na
uku yayin da dare ya raba, Zan jagoranci
wadannan dakarun sojojin haya namu na tafi dasu
izuwa can gidan sarauta,
Kasani cewa dama inada mutanena acikin
dakarun dake cikin gidan sarautar don haka da
zarar munje kusa zamu harba kibiyar wuta sama
domin su gane cewa mun iso.
Sune zasu kashe masu gadin kofar gidan sarautar
su bude mana kofar mu fada ciki.
Kafin muje zan nunawa dakaru namu taswirar
hanyoyin gidan sarautar gaba daya da duk inda
dakaru ke tsaitsaye don haka muna shiga zamu
fara amfani da harba kibiyoyi mu kawar da
dukkanin dakarun dake sama bisa benaye da
wadanda ke kan kwanoni.
Sannu da sannu cikin sauri da daukar numfashi
zamu yi ta yiwa dakarun gidan kissan mummuke,
Kafin su ankara mun kashe kaso biyu cikin ukun
su kaga kenan ko fito na fito mukayi da sauran
dakarun gidan zamu iya gamawa dasu cikin
kankanin lokaci,
Kasan dai babu yadda zaiyi damu tunda sarkin
yawa yafi sarkin karfi barema ko ni Kadai ma ina
ganin zan iya dashi,
Koda jin haka sai waziri yayi caraf yace kada ka
kuskura kace zakayi wannan ganganci,
Duk wannan jarumtakar taka da kake gani ba
komai bace akan ta sarki Barham,
An gayamaka cewa ana zama sarki ne a banza? "
Kada kamanta da alkawarinmu cewar ni da kaina
zan kashe sarki dan haka kada dayanku ya
kuskura ya kasheshi kamar yadda mukayi alkawari
cewa mahaifinka ne zai kashe dan uwansa sarkin
yaki Ridwan da hannunsa lallai nima haka nake so
na kashe dan uwana sarki Barham da hannuna,
Koda jin wannan batu sai Hamsaru ya bushe da
dariyar mugunta yace,kwantarda hankalinka ya
shugabana yadda duk ka tsara haka za'a yi,
Dole ne mu yiwa sarki Barham juyin mulki ko don
na sami damar mallakar gimbiya lazima ta
kowane hali.
Lallai ne a wannan karon maza zasu fadi kasa ina
nufin dole ne sarki Barham ya zama gawa dashi
da babban makiyina kalmaru,
Koda jin wannan batu sai waziri ya bushe da
dariyar mugunta yace ai kama daina batun
kalmaru domin yanzu tuni ya dade da faduwa
kasa,
Tunda na tabbatarda cewar babu yadda za'ayi
yasami nasara yaki akan sarki Daryan don ko ba'a
gwada ba linzami yafi karfin bakin kaza,
Hamsaru ya kyakyale da dariya yace zancenka
dutse ne,
Kamar yadda su waziri suka tsara haka duk
al'amarin ya kasance wato lokacin da dare ya
raba sun sami nasarar shiga har cikin gidan
sarautar kuma sun kashe sama da dakaru dubu
arba'in masu tsaron gidan sarautar, kai sai da
suka sami nasarar shiga har cikin turakar sarki
Barham ta barci.
Nan take suka kewaye gadonsa koda suka yaye
mayafin da yake lullube dashi sai suka ga babu
komai face tulin tsumman kara,
Al'amarin da yayi matukar razana su kenan,
idanunsu suka zazzaro, waziri ya dubi Hamsaru
yace, duk yadda akayi sarki yayi tunanin cewa
zamu shirya mada juyin mulki amma duk yadda
akayi yana nan a boye cikin gidan nan don haka
muyi sauri mu bazama nemansa tun kafin ya
nemo agajin dakaru daga cikin gari, in ba haka ba
kuwa gaba dayan shirinmu zai wargaje.
Gama fadin haka keda wuya sai suka fito gaba
dayansu daga cikin turakar sarki Barham suka
rarrabu suka rinka shiga daki daki sako da logo da
lunguna na gidan sarautar ko ina da ina suna
neman sarki Barham,
Hakika masu iya magana sunyi gaskiya da suka
ce in zaka haka ramin mugunta to ka ginashi dai-
dai da kai,
Abinda su waziri basu sani ba shine tun kafin su
sarkin yaki kalmaru su tafi sai da sarki Barham
yayi tunanin cewa lallai su waziri zasu iya amfani
da wannan dama su yi yunkurin juyin mulki bisa
wannan dalili ne shima yayi nasa shirin a boye ya
tanadi mayakansa sama da dubu dari biyu a
wajen gidan sarautar suka yi kwanto a cikin wani
rusasshen gida wanda yafi shekara dari da
rugujewa kuma ba a shigarsa,
Lokacin da dare ya soma sai sarki Barham yayi
shiga irinta dakarun dake tsaron gidan sarautar ya
sulale daga cikin dakinsa ya fice daga cikin gidan
sarautar yaje ya iske wadancan dakaru nasa dake
cikin rusasshen gidan,
Dama daga cikin rusasshen gidan ana iya hango
duk abinda ke faruwa a kofar gidan sarautar,
Don haka su sarki Barham na nan labe suka
hango an harba kibiyar wuta wato su Hamsaru
sun iso kenan suna yiwa jama'arsu inkiya, har aka
budewa su Hamsaru kofar gidan sarautar suka
shiga su sarki Barham basuyi wani
Yunkuri ba sai da suka bari sun dan jima da shiga
sannan suka fito daga inda suke boye suka nufi
kofar gidan sarautar,
Da zuwa sai suka iske kofar a rufe, kawai sai
sarki Barham ya kwankwasa kofar Badakaren dake
bakin kofar a sannan yana daga cikin irin yaran
waziri don haka sai ya tambaya yace wanene
yake buga mana kofa?"
Koda jin wannan tambaya sai sarki Barham yayi
irin murya waziri yace nine.
Cikin sauri Badakaren ya bude kofar, koda su sarki
suka shigo yayi arba dasu sai ya firgita ya
yunkura da nufin ya ruga da baya amma sai sarki
Barham ya cakumoshi ya soko masa Wuka a
makoshinsa yai jifa da gawarsa kuma ya tofawa
gawarsa yawu yace wannan shine sakamakon
masu cin amana.
Nan take sarki Barham ya juya ya dubi gaba
dayan dakarun dake bayansa yace to ku shirya
yanzu ne muma zamuyi namu gagarumin yakin
kamar yadda su kalmaru keyin nasu a can dajin
Hajarul maut,
Yana gama fadin haka ya raba dakarun izuwa
kaso hudu,
Kaso daya ya turasu suka tsare gabashin gidan
sannan sauran kason biyun suka tare yamma da
kudu shi kuma sai ya jagoranci kaso na karshe
suka durfafi arewacin gidan sarautar.
Su sarki Barham suka durfafi hanyar da zata kaisu
inda turakarsa take,ai kuwa suna isowa wani
babban fili sai suka yi kacibis dasu Hamsaru nan
fa aka tsaya ankayi cirko-cirko ana kallon kallon,
Hamsaru ya dubi dakarun dake bayansa su dubu
dari yace, maza ku karkasu izuwa kowanne
bangare na gidan domin ansamu a tsakiya,
Kowannenku yayi yaki iya ransa kada ku bari a
kamaku a raye sai dai gawarku,
Nan take dakarun suka rarrabu wadanda suka
rage a bayansa basu fi su dubu ashirin ba,
Koda ganin haka sai sarki Barham ya bushe da
dariya. Lokaci guda kuma ya turbune fuska ya
dubi Hamsaru a fusace yace ya kai Hamsaru dan
yunaru kayi sani cewa ko zaki ya fadi yafi gaban
wargi,
An gayamaka cewa ana zama sarki a banza ne?"
Ai na sani cewa da dadewa mahaifinka
Yanason ya gaji karagata amma bai sami damar
da xaiyi mini juyin mulki sai a yanzu da wannan
yaki ya taso tsakanina da sarki Daryan,
Dama na sani cewa zai iya hada kai da shi don
ganin bayana bisa taimakon mahaifinka wanda
yanzu yana tsare a gidan kurkuku,
To ka sani cewa bana bukatar na kasheku kai da
waziri dan uwana maci amana da kuma
mahaifinka yunaru,
So nake kuje ku taya yunaru zama a kurkuku har
izuwa karshen mulkina bisa wannan babban laifi
da kuka aikata domin ya zamo babban abin bakin
ciki ga rayuwarku,
Koda sarki Barham Yazo nan a zancensa sai
Hamsaru ya bushe da dariya yace kai wannan
sarki kayi sani cewa kada mage ba yanka bane,
ka bar ganin cewa dakarunka sun kewaye mu a
cikin gidan nan, hakan ba zata hana mu cika
burinmu ba akanka,
Idan har kaga a yau dinnan waziri bai hau karagar
Mulkinka ba to bana numfashi a doron kasa kuma
ka sani cewa ko mu bamu sami nasarar kawar da
kai ba da zarar sarki Daryan ya gama dasu
kalmaru acan dajin Hajarul maut babu inda zai
doso sai anan tare da miliyoyin dakarunsa yazo
ya cika da yaki har gida, kuma ya fito da
mahaifina daga kurkuku,
Kafin Hamsaru ya gama rufe bakinsa tuni sarki
Barham ya tari numfashinsa yana mai daka masa
tsawa yace karyaka tasha karya yaro ga maza
nan bisa kanka,
Yana gama fadin haka ya daga takobinsa sama
su Hamsaru sai suka daga nasu takubban aka
rugo izuwa kan juna aka ruguntsume da
masifaffan yaki
Adaidai wannan lokaci ne gaba daya gidan
sarautar ya hargitse da ihun mazaje gamida
karafkiyar karafa, matan da ke cikin gida suna
barci ba shiri suka farka a firgice suka rinka
neman ma maboya,
Da yake sarkin yawa yafi sarkin karfi nan da nan
aka kashe gaba dayan wadannan dakarun sojojin
haya wadanda su Hamsaru suka zo dasu ya
zamana cewa saura mutum biyu kacal ana ta
faman gurmuzu dasu kuma ba wasu bane face
Hamsaru da waziri.
*** *** ***
Karshen dadi karewa!!!
~~~~~~~~~~~~~~~
Shin wanene zai samu nasara a cikin wannan yaki
da akeyi a gidan sarauta tsakanin sarki Barham
dasu Hamsaru da waziri? "
Mu hadu a Littafi na hudu don jin cigaban wannan
labari.
Daga mai debe muku kewa a kullum da ko
yaushe.
MAZA SUN FADI!!! LITTAFI NA 4 PART 1

Shi dai waziri ya rufe jikinsa da fuskarsa gaba
daya, idanunsa ne kadai a waje kuma yana da
bakaken tufafi yana ta ragargazar dakarun sarki
ya zame musu alakakai an rasa yadda za'a yi
dashi acan wani bangaren daban na gidan
sarautar,
Shi kuwa Hamsaru an rasa wanda zai kusanceshi
sai sarki kuma sai da suka shafe sama da sa'a
guda suna gurmuzu amma dayansu ya kasa
samun cutar da dayan,
Al'amarin da yayi matukar baiwa Hamsaru
mamaki kenan domin shi a zatonsa zai iya
gamawa da sarki farat daya, nan fa hankalinsa ya
dugunzuma ainun domin ya fahimci cewar lallai
dukkan shirinsu ya lalace kuma idan ya tsaya yaci
gaba da wannnan yaki da sarki komai zai iya
faruwa, ko dai karfinsa ya kare, sarki ya sami
logonsa ko kuma ya rasa rayuwarsa gaba daya
Abu daya ne ya dan kara masa kwarin gwiwa
kuma ba komai bane face jiyo karafkiyar karafa a
can wani bangaren daban na gidan sarautar,
Hakan ne ya tabbatar masa da cewa waziri na
raye kuma da shine ake ta yin wannnan
karafkiyar, tunda shima ya kasance tsohon
gwarzon jarumi mai dakawa maza gumba a
hannu.
Koda aiyana Hakan sai Hamsaru ya shammaci
sarki da dukkan dakarunsa ya daka tsalle sama ya
dira akan rufin dakunan gidan sarautar ya kama
gudu a kansu ya nufi can inda yake jiyo sautin
karafkiyar karafa,
Ai kuwa shima sarki Barham sai ya daka tsallen
sama ya dira a kan rufin dakunan suka kasa
tsere.
Lokacin da ya iso inda ake fafatawa da waziri
yaga yadda dubunnan dakaru sukayi masa
rubdugu sai hankalinsa ya kara dugunzuma
saboda ya tabbatar da cewa shuma nan da dan
wani lokaci karfinsa zai kare a cimmasa,
Hamsaru ya waiga bayansa yaga sauran kiris
sarki Barham ya cimmasa kawai sai ya yunkura
kamar zai daka tsalle ya dira a inda ake gurmuzu
da waziri amma kuma sai ya juyo cikin zafin
nama da shammace ya doki kirjin sarki Barham
saboda karfin dukan sai da sarki yayi baya a sama
tamkar an jamyeshi da majajjawa ya fada kan
rufin wani dakin, hannunsa na hagu ya bugu har
kashinsa ya tsage ya fado kasa a matukar
galabaice.
Kafin ya mike tsaye tuni Hamsaru ya juya ya daka
tsalle ya dira a tsakiyar dakarun da suka lullube
waziri ya tarwatsasu da sara da suka,
Damar da yasamu kenan ta tsayawa daf da waziri
yace, dashi shirinmu fa ya watse dole ne mugudu
inba haka ba sarki da jama'arsa zasu sami nasara
a kanmu kuma na fuskanci cewar sarki so yake a
kamamu a raye yadda zai iya cin mutuncinmu.
Kafin Hamsaru ya gama rufe bakinsa sai suka
juyo takun sawayen sarki Barham a kan rufin
dakuna ya durfafo inda suke ba shiri suka sake
tarwatsa dakarun dake zagaye dasu suka kutsa ta
cikinsu da karfin tsiya suna masu falfalawa da
fudun tsiya,
Kawai sai suka sake daka tsalle sama a tare suka
dira akan rufin dakunan suka ci gaba da gudu a
kasa suka nufi inda katangar gidan sarautar take.
Koda sarki ya hangosu sai ya bisu suka kasa
tsere a sama kuma a Lokacin ne dakarun masu
kibiya suka fara harbawa su Hamsaru kibiyoyi
amma cikin sa'a ko kibiya daya ba ta samesu ba.
A haka dai da kyar da sidin goshi suka isa inda
katangar take suka sake daka tsalle a tare suka
haye katangar suka dira kasa,
Ashe dama tuni sun tanadi dawakansu a wani
sako dake bayan gidan sarautar Don gudun
faruwar bacin rana, don haka suna dira a kasan
suka sake rugawa da azababben gudu Izuwa
wannan soko suka kwance dawakansu suka
hayesu gamida da zaburarsu da gudu,
A dai-dai Lokacin ne sarki Barham ya duro kasa
gaban katangar gidan sarautar ya hango su
Hamsaru bisa dawakai sun tada kura, cikin
tsananin fushi sarki Barham ya kurma uban ihu
har sai da kwallar bakin ciki ta zubo masa, domin
a sannnan ne ya tuna cewa yayi babban kuakure
da bai yi tunanin toshe duk wata hanya ba dasu
Hamsaru zasu iya guduwa,
Nan take sarki Barham ya kwallawa dakaru masu
kibau kira ya umurcesu dasu hau dawakai su bi
bayan su Hamsaru suyita harbinsu har sai sun
hallakasu sannnan suzo masa da gawarsu.
Nan take kuwa dakarun sama dasu dubu talatin
suka hau dawakai suka zaburesu da gudu suna
masu bin sawun dawakansu Hamsaru,
A dai-dai wannnan lokaci ne sarki yaji hannunsa
yayi masa nauyi da yawa. Koda ya dubi hannun
sai yaga ya kumbura suntum sakamakon tsagewar
da kashin ya samu, nan take ya kwalawa likitansa
kira, nan da nan dakaru suka rugo da gudu dauke
da karaga aka dora sarki a kai aka shiga dashi
cikin gidan sarautar, likitansa na biye dashi,
Wannan shine abinda ya faru a birnin zamar yayin
dasu waziri suka yiwa sarki Barham yunkurin juyin
mulki amma basu sami nasara ba.
Al'amarin su gimbiya lazima kuwa Lokacin da ta
saba Kalmaru a bayanta ta falfala da gudu dashi
bata tsaya a ko ina ba sai a can inda suka kafa
sansaninsu ta shige dashi cikin tantinta, ashe tun
sa'adda sarki Daryan yayi masa wannnan wawan
dundu a gadon baya ya suma kuma har Iyanzu bai
farfado ba.
Koda gimbiya lazima ta shimfida Kalmaru akan
shimfida taga babu alamun numfashi a tare dashi
sai ta rude kuma kuma ta dimauce, a dai-dai
wannnan lokaci ne taji dakaru sun fado cikin
tantin sun ritsata da makamai saboda ba'asan ko
wacece ita ba, dalili kuwa shine a can cikin keken
dokinta an iske huzen a kwance sanye da
tufafinta
Koda lazima taga dakaru sun kewayeta rike da
makamai kuma ga Kalmaru kwance a kasa cikin
mugun yanayi sai tayi sauri ta cire hular karfen
dake kanta
Kyakkyawan dogon gashin kanta ne ya fara
zubowa kasa. Koda dakaru sukayi arba da
kyakkyawar fuskarta sukaga itace sai dukkaninsu
suka zubarda makamansu suka zube kasa cikin
biyayya da tsananin mamaki.
Adaidai wannnan lokaci ne likitocin dakarun yaki
suka shigo cikin tantin suka shiga duba Kalmaru
suna kokarin ceto rayuwarsa,
Koda gimbiya lazima taga likitocin sun shafe yan
dakiku masu yawa a kan Kalmaru amma ko motsi
baiyi ba sai sai hankalinta ya dugunzuma ainun,
nan take idanunta suka ciko da kwalla har
hawaye ya subuto mata bata sani ba,
Cikin sauri ta juyawa jama,a dake cikin tantin
baya don kar suga zubar hawayen nata,
Kwatsam sai aka ji Kalmaru ya farfado yana mai
dogon numfashi gamida furzar da wani irin gudan
jini daga bakinsa, Kalmaru ya yunkura zai mike
zaune amma sai likitoci suka mayar dashi kwance
babban likitan ya dubeshi yace, ya kai dirkar
birnin zamar kayi sani cewa kashin bayanka ya
bugu sossai kuma ba karamar sa'a kayi ba da bai
karye ba sannnan kuma inba don gimbiya lazima
ta ceci rayuwarka ba da tuni sarki Daryan ya
hallaka.
Koda da jin wannnan batu sai Kalmaru ya fara
kallon mutanen dake cikin tantin a sannnan ne ya
hango lazima tsaye can gefe daya ta juya baya.
Cikin tsananin mamaki Kalmaru ya dubi shugaban
likitocin yace,ban gane abinda kake fada ba, ta
yaya gimbiya lazima ta ceci rayuwata alhalin tana
can bayan sansanin yaki a cikin keken dokinta,
Kai huzen meye ka juya mini baya ko ka sabawa
umurnina ne shiyasa baka son mu hada ido?"
Koda jin wannnan tambaya sai lazima ta juyo
sukayi arba ita da Kalmaru, cikin tsananin mamaki
Kalmaru ya kurawa gimbiya lazima idanu ya kasa
cewa komai,
Koda ganin haka sai gimbiya ta dubi likitocin da
sauran dakarun dake cikin tantin tace ku fita ku
bamu wuri.
Nan take kuwa dakarun da likitocin suka fice gaba
dayansu.
A sannnan ne gimbiya lazima tazo ta zauna a
gefen shimfidar da Kalmaru ke kwance ta dubeshi
cikin murmushi mai taushi tace, tabbas nice na
ceci rayuwarka daga shairin sarki Daryan a
Lokacin ya kaika kasa yana shirin soke gadon
bayanka da takubbansa, ni kuwa sai na dako tsalle
daga inda nake na doki kugunsa, naga Lokacin da
yayi sama kansa ya bugu a kan garkuwar wani
badakarensa har hakorinsa guda ya fita daga cikin
bakinsa, ina mai zaton dai shima ya suma kamar
yadda ka suma, ya kai dirkarbirnin zamar nasan
cewa.
Kayi matukar mamaki bisa jin wannnan labari
daga bakina to ka daina mamaki domin tun ina
yarinya karama mahaifina yake koya mini yaki a
boye har Izuwa girmana ba tare da kowa ya sani
ba
Ba don komai ya koya mini yaki ba sai saboda irin
wannnan rana,
Lokacin da aka fara wannan yaki ina can bayan
sansani a cikin keken doki sai na fito na hau
saman keken domin na hango abinda ke faruwa a
filin yakin na rubuta a cikin littafina kamar yadda
burina ya kasance amma sai naga bana iya hango
abinda ke faruwa, Al'amarin da ya dugunzuma
hankalina kenan na fara tunanin hanyar da zan bi
naje daf da filin yakin yadda zan iya ganin duk
abinda ke faruwa,
Tunda dakaru da yawa sun tsareni kuma ka basu
umurnin kada subar wani abu yazo kusa dani
kuma kada a barni naje ko ina,
Nan take dabara ta fado mini na ribaci huzen na
sumar dashi a cikin keken dokin nayi musayar
kaya dashi na fito daga cikin keken dokin ba tare
da dakaru sun shaudani ba,
Lokacin da na iso sansanin yakin da nufin na kalli
abinda ke faruwa na rubata sai na hango kana
kwance kasa sarki Daryan na shirin hallakaka
shine na falfala da gudun tsiya na ceci rayuwarka
wannnan shine iyakar abinda ya faru, koda
gimbiya lazima tazo nan a zancenta sai hankalin
Kalmaru ya dugunzuma ainun ya dubeta cikin
alamun tsananin damuwa yace kinyi babban
kuskure da baki hallaka sarki Daryan ba a
wannnan lokaci tunda kin samu dama.

MAZA SUN FADI!!! LITTAFI NA 4 PART 2

Koda gimbiya lazima tazo nan
a zancenta sai hankalin Kalmaru ya dugunzuma
ainun ya dubeta
cikin alamun tsananin damuwa yace kinyi babban
kuskure da baki
hallaka sarki Daryan ba a wannnan lokaci tunda
kin samu dama.
Lazima tace ai inda kuma na tsaya kokarin hallaka
sarki Daryan kai kuma zaka iya rasa rayuwarka
gaba daya
Kalmaru yace ai in dai sarki Daryan zai rasa tasa,
rayuwar tawa ba a bakin komai take ba,
Ki sani cewa hankalina a tashe yake sossai
saboda ina tunanin cewa zamuyi biyu babu,
Abinda nake nufi shine yanxu gashi a nan munyi
ragas dasu sarki Daryan tunda babu bangaren da
suka sami nasara a wannan yaki kuma inaji a
jikina cewar wani mugun abu na faruwa acan
birnin zamar. Shin bakiyi tunanin cewa Hamsaru
da waziri zasu iya shiryawa sarki wani mugun
tuggu ba tunda ni da dukkan manyan mayakan
kasar bama nan mun fito yaki?"
Koda Kalmaru yazo nan a zancensa sai hankalin
gimbiya lazima ya dugunzuma ainun bata san
sa,adda ta dafa kafadar Kalmaru ba tace ya kai
jarumi Kalmaru yanxu menene matakin da ya
kamata mu dauka? "
Sa'adda Kalmaru yaji wannan tambaya sai yayi
ajiyar zuciya sannnan yace,bai kamata muyi
gaggawar dauka wani mataki ba tunda bamu san
abinda abokan gaba ke shirin yi ba,
bamu sani ba ko zasu ci gaba da wannnan yaki
ba ko baza su ci gaba ba tunda mu dasu kowa na
sansaninsa.
Yana gama fadin Hakan sai ya kwallawa
shugaban likitocin kira, likitan ya shigo cikin tantin
da sauri ya zube kasa gaban Kalmaru,
Kalmaru ya dubeshi cikin nutsuwa yace tsawon
wane lokaci zan iya mikewa na ci gaba da yaki?
Likita yayi ajiyar numfashi cikin alamun karayar
zuciya yace ya shugana a kalla kwana biyu,koda
jin haka sai hankalin Kalmaru ya dugunzuma ainun
fiye da koyaushe, kawai sai ya tura aka kirawo
manyan dakarun yakinsa, da zuwansu sai ya
dubesu yace daga yanxu gimbiya lazima ce
shugaba a wannan yaki itace zata baku umurni
kubi, idan kuma abokan gaba sun janye sun bar
sansaninsu mu ma sai mu janye amma yanxu
inason a tashi manzo ya tafi Izuwa can birninmu
domin yaje ya gano halin da garin ke ciki domin
ina zargin cewa akwai abinda ke faruwa. Nan take
dakaru suka durkusa a gaban lazima suna masu
yin mubaya'a a gareta sannnan kuma aka tashi
manzo da sauri ya tafi Izuwa birnin zamar,
Acan sansaninsu sarki Daryan kuwa Lokacin da
aka shigar da sarki Daryan cikin tantinsa aka
shimfideshi bisa shimfida a matukar galabaice sai
ya fashe da matsanancin kukan bakin ciki ya
kama ihu da shure shure har saida dakaru suka
danneshi aka

1 Comments On MAZA SUN FADI 1 to 4
avatar
abubakar-abdullahi-6

10 months ago

Reply

yes

Please Login or Register in order to submit comment