Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aiyukanki.
Cikin sanyi jiki Zulaima ta juya ta nupi waje,
Koda ta isa bakin kofar fita daga falon sai ta
juyo tayiwa kalmaru wani irin kallo wanda yai
matukar dugunzuma hankalinsa domin kallo ne
mai nuna alamun cewa bazasu sake saduwa ba.
Abinma da ya kara dugunzuma hankalin kalmaru
da sarkin yaki suka hanzarta gama cin abinci
nasu sannan suka fito kofar gida inda suka iske
wani hadimin gidan a tsaye rike da dawakai
kosassu guda biyu.
Nan take sarkin yaki da kalmaru suka kama
dawakan suka hau suka zaburesu da gudu izuwa
gidan sarauta.
Suna cikin tafiya ne kalmaru yaji jiri ya fara
dibarsa kuma yaji wata irin tsananin kasala ta
shigeshi irin wacce yaji tun daren jiya kawai sai
sarkin yaki yaji kalmaru ya fado kasa tim! Daga
kan dokinsa.
Al'amarin da yai matukar dugunzuma hankalin
sarkin yaki kenan yaja linzamin dokinsa yai
turjiya ya sauko da sauri ya kama kalmaru ya
tasheshi tsaye sannan ya dubeshi cikin alamun
tsananin damuwa da fargaba yace,
"ya kai dana mai yai faru gareka haka?"
Yanzu ashe dama bakada lfy amma ka boye mini
baka gaya mini ba? "
Kalmaru ya girgiza kai yace,
"Haba ya Abbana yaya za'ayi nasan banida lfy
amma na boye maka.
Tun a jiya naji sauyin yanayi a jikina bayan naci
abinci nasha ruwan inibi da baiwa Zulaima ta
bani.
Kuma ba wani abu naji ba face tsananin kasala.
A yanzu kuwa Inajin kasalar fiye da wadda naji a
jiya domin ina ganin ma cewa bazan iya sarrafa
takobina ba."
Koda jin wannan batu sai hankalin sarkin yaki ya
dugunzuma ainun fiye da ko yaushe kuma ya
kamu da tsananin bakin ciki ya takarkare ya
kurma uban IHU! Kuma ya fashe da kukan bakin
ciki. MAZA SUN FADI!!! Part 5

A yanzu kuwa Inajin kasalar fiye da wadda naji a
jiya domin ina ganin ma cewa bazan iya sarrafa
takobina ba "
Koda jin wannan batu sai hankalin sarkin yaki ya
dugunzuma ainun fiye da ko yaushe kuma ya
kamu da tsananin bakin ciki ya takarkare ya
kwara uban ihu a lokacin da zuciyarsa ta kama
tafarfasa kamar zata kone,
Kuma hawayen takaici ya zubo masa yace,
"ya kai dana kayi sani cewa tabbas Zulaima taci
amanarmu domin ko shakka babu itace ta zuba
maka sinadarin da yasa maka kasala domin kada
ka lashe wannan gasa da za'ayi.
Duk yadda akayi dan uwana YUNARU ne yasa ta
aikata wannan mummunan aiki sbd kawai
Hamsaru ya sami nasara akanka.
Koda jin wannan batu sai kalmaru ya dubi sarkin
yaki cikin tsananin mamaki yace,
"ya kai Abbana Yaza'ayi Zulaima taci amanarmu
alhalin shekaru tana tare da kai tun kafin a
haifeni kuma ko sau daya bata taba cin
amanarka ba.
Sarkin yaki ya gyada kai yace, "Ai mutum
bashida tabbas ako yaushe yana iya sauya
tunani."
Koma dai menene da Zarar mun koma gida zansa
takobi ta na sare Zulaima karshen zamana da ita
yazo.
Dajin haka sai kalmaru ya fashe da kuka yace,
haba ya Abbana saboda me zaka kashe wadda
take a matsayin mahaifiyata matar da ta dauki
dawainiyata tayi rainona har na girma na zama
mutum? "
Sarkin yaki ya numfasa yace, "bani da wani zabi
wanda yafi na kasheta yanzu domin idan na
barta nan gaba kuma rayukanmu zata nema nida
kai tunda har aka iya hada kai da ita yanzu
domin a cutar dakai a hanaka samun damar
gadon kujerata.
Shin yanzu kana ganin zaka iya tarar Hamsaru a
haka yadda kake jin rashin kwarin jikin naka?"
Maimakon kalmaru ya bashi amsa,sai ya ja da
baya kadan yana mai fuskarta sarkin yaki yace,
"jarrabani ka gani ya Abbana,
Ta ko wanne hali bazan yarda Hamsaru ya kai ni
kasa ba"
Kafin kalmaru ya gama rufe bakinsa tuni sarkin
yaki ya zare takobinsa ya afka masa da dukkan
karfinsa yana mai kai masa sara da suka.
Ai kuwa sai kalmaru ya kasa maida martani
yazamana cewa da kyar ma yake kare harin,
Kafin a jima kalmaru ya galabaita ainun kuma
dama gashi ya hadu da tsohon hannu masanin
sirrin yaki kuma gashi sadauki.
Nan take sarkin yaki ya doki kirjin kalmaru da
kafa, ai kuwa sai kalmaru ya zube kasa wanwar
ya yunkura domin ya mike ma ya kasa,
Al'amarin da ya kara dugunzuma sarkin yaki
kenan yaji kamar ya fashe da kuka.
Nan take hawaye ya zubowa kalmaru ya dubi
sarkin yaki cikin takaici da damuwa yace,
"ka gafarceni ya kai Abbana hakika ni kaina
yanzu na gamsu cewar na fadi a wannan gasar,
Sarkin yaki yai shiru kansa a sukuye yana mai
fadawa cikin kogin tunani mai zurfi sannnan ya
dago kai ya dubi kalmaru cikin murmushi yace,
"ya kai dana kayi sani cewa mai rai baya kasa
yin motsi kuma hanyar kashe makahon kare
yawa gareta.
Yanzu wata dabara ta fado min wacce in dai
muka bita lallai zamu sami nasara amma fa dole
ne ka tsuke bakinka ka bar Wannnan al'amarin
Sirri tsakanina da kai har abada domin duk ranar
daka kuskura ka gayawa wani sai ka rasa
wannan kujera kuma dole ne ka bar garin nan
kayi nisa dashi yadda har abada bazaka iya
dawowa ba.
Lokacin da sarkin yaki yazo nan a zancensa sai
kalmaru ya cika da matukar mamaki yace, ya kai
Abbana wannan kuwa wacce irin dabara ce tazo
maka haka?"
Sarkin yaki ya numfasa yace, "Abinda za'a yi
yanzu shine musanya kaya wato ka bani kayan
yaki dake jikinka na sanya,
Kaima ka sanya nawa kuma duk mu rufe
fuskokinmu sannnan mu karasa fada.
Muna zuwa ka wuce kusa da sarki ka zauna akan
kujerar da aka tanadar mini.
Kayi gaisuwa ga sarki amma kada ka kuskura ka
budi baki kayi magana dashi yaji muryaka,
Ni kuma zan shiga tsakiya fili na tari Hamsaru
nayi wannan gasa dashi a madadinka tunda kai
yanzu bakada kuzarin da zaka iya yin wannan
gurmuzu.
Wannnan ce kadai hanyar da zamu iya bi mu
tabbatarda cewa sarauta sarkin yaki bata bar
gidanmu ba kuma wannan ne kadai abinda zan
iya yi maka na karshe a rayuwata domin gyara
rayuwarka ta nan gaba.
Lokacin da sarkin yaki ya zo nan a zancensa sai
hankalin kalmaru ya dugunzuma ainun ya dubeshi
cikin alamun tsananin damuwa yace,
"ya kai Abbana ka tuna fa cewa kai yanzu ka
tsufa,
Hamsaru kuwa saurayi ne mai tashen kurciya da
karfi ta yaya zaka ce ka tunkare shi,ina tsoron
kada ya cutar dakai."
Koda jin haka sai sarkin yaki yayi murmushi yace,
ai faduwar mazan kwarai ba karamin aiki bane.
Ina mai tabbatar maka da cewa har yanzu
jarumtakata tana nan tunda acikin jini take a
nono nasha.
Hakika zan baka mamaki kuma zan nuna maka
cewa kafin MAZA SU FADI sai anyi BAIKIN
ARTABUN da yafi tunanin mai tunani.
Maza ka cire kayanka ka bani kamar yadda na
umurceka,
Kafin ma kalmaru ya fara wani yunkuri tuni
sarkin yaki ya fara cire nasa tufafin.
Nan take sukayi musayar kaya ya zamana cewa
shi sarkin yaki ya sanya kayan yakin kalmaru shi
kuma ya sanya na sarkin yaki kowannensu ya
rufe fuskarsa ya zamana cewa idanunsa kadai
ake gani sannnan suka hau dawakan suka durfafi
fada.
Hakika masu iya magana sunyi gaskiya da suka
ce barewa bata gudu danta yayi rarrafe.
Kalmaru da sarkin yaki suna matukar kama da
juna tamkar an tsaga kara kuma tsawon jikinsu
da kaurinsu duk yazo daya.
Lokacin da sarkin yaki da kalmaru suka iso filin
fada sai suka iske filin ya cika makil da jama'a
babu masakar tsinke kuma kowa ya hallara hatta
jarumi Hamsaru wanda za'ayi gasa dashi yana
tsaye a tsakiyar fili cikin gagarumar shigar yaki
rike da takobi da garkuwa, jama'a suna ta yimasa
jinjina anata shewa.
Makada da maroka kuwa sun bude nasu shafin
kasuwanci,
Sarki ne kawai bai fito ba.
Nan take su kalmaru suka ratso cikin filin fadar
ai kuwa ana hangosu sai dakaru suka bude musu
hanya da karfin tsiya suka wuce izuwa tsakiyar
filin.
Sarkin yaki na isowa inda Hamsaru ke tsaye sai
yaja linzamin dokinsa ya tsaya ya sauka aka
janye dokin nasa daga cikin fili,
Shi kuma kalmaru sai ya wuce kai tsaye izuwa
inda karagar mulki take wacce fadawa suka
kewayeta.
A wannan lokaci YUNARU dan uwan sarkin yaki
Ridwan na zaune acan gefe daya cikin fadawa.
Koda ya hango dan uwansa sarkin yaki ya taho
inda suke zaune fuskarsa rufe sai ya cika da
mamaki domin baiga dalilin da zaisa ya rufe
fuskarsa ba,
Wani abu da ya kara daure masa kai shine a iya
saninsa da sarkin yaki ko yaushe yana tafiya ne
cikin sauri da kuzari kamar zai tashi sama amma
kuma yau gashi yana tafiya a hankali harma yana
dan yin layi kamar wanda ya sha giya ya bugu.
Nan take tunani ya fadowa YUNARU yace, acikin
dukiyarsa anya kuwa sarkin yaki da kalmaru ba
sauyin kaya sukayi ba yadda shi sarkin yakin zai
yi wannan gasa a maimakon kalmaru.
Ina ganin ma cewa saboda haka ne suka rufe
fuskokinsu. MAZA SUN FADI!!! Part 6

"Anya kuwa sarkin yaki da kalmaru ba sauyin kaya
sukayi ba yadda shi sarkin yakin zai yi wannan
gasa a maimakon kalmaru.
Ina ganin ma cewa saboda haka ne suka rufe
fuskokinsu,
Amma idan ma haka ne ai zan gane da Zarar an
fara wannan gasa domin sinadarin da na baiwa
Zulaima ta zubawa kalmaru a cikin ruwan inibin
da yasha dole ne ya kasa yin wannan gurmuzu
tunda ba zai taba samun kuzari da karfi ba a
jikinsa.
Ana fara yin wannan gasa dana Hamsaru zai
kaishi kasa,
To idan har zargina ya zama gaskiya to yaya zan
iya wannan gurmuzu na tona musu asiri alhalin ni
ba kowa bane daga cikin Alkalan gasar kuma in
dai aka fara gasar babu damar a dakatar da ita
har sai an kare"
Koda yunaru yazo nan a tunaninsa sai hankalinsa
ya dugunzuma ainun,
Cikin rudewa ya mike tsaye domin ya karasa inda
manyan fadawan sarki ke zaune gamida alkalan
wannan gasa domin ya sanar dasu abinda yake
zargi amma sai wani Badakare daga cikin
dakarun sake tabbatarda Tsaro a wajen ya daka
masa tsawa ya umurceshi daya koma wajensa ya
zauna.
A dai-dai-dai wannan lokaci ne akaji an fara buga
tambura ana busa algaita alamar cewa ga sarki
nan ya fito.
Nan fa kowa ya mike tsaye har saida sarki ya
shige cikin filin fadar tareda dakarunsa masu
take masu baya ya isa kan karagarsa ta mulki ya
zauna sannan kowa ya zauna.
A wannan lokaci ne wazirin sarki ya mike tsaye
ya fuskanci al'umma yace, "yaku jama'ar Birnin
zamar kuyi sani cewa yanzu ne za'a fara wannan
gagarumar gasa don samar da sabon sarkin yakin
mu tunda namu lokacin yin murabus dinsa yayi.
Tabbas wannan gasa da za'a yi yanzu za'ayi ta
ne tsakanin jarumi Hamsaru da jarumi kalmaru
wanda aka tabbatar da cewa a halin yanzu duk
fadin garin nan babu wadansu jarumai wadanda
suka fisu karfin damtse da iya yaki.
Don haka yanzu ba tare da wani bata lokaci ba
za'a fara wannan gasa.
Koda gama fadin hakan sai waziri ya dubi mai
buga tambari, take ya buga wani katon tambari,
wanda ya cika filin fadar gaba daya ta amsa
kuwwa..
Faruwar hakan ke da wuya sai sarkin yaki da
Hamsaru suka gyara tsayuwar su kuma suka fara
kewaya juna, kowannesu na tunanin yadda zai
bullowa dayan.
Kawai sai suka rugo da gudu izuwa kan junansu
suka kacame da azababben yaki ya zamana
cewa suna kaiwa junansu sara da suka cikin
tsananin zafin nama, juriya gamida naci.
Hatta sauran jama'a gari da suke kallon wannan
gurmuzu sai da hankalinsu ya dugunzuma ainun
domin gani suke a koyaushe jaruman biyu zasu
iya hallaka junansu.
Koda aka sami tsawon kamar dakika dari uku da
fara Wannnan artabu sai labari yasha bam-bam
domin nan take sarkin yaki ya fara samun lagon
Hamsaru ya zamana cewa Hamsaru baya iya
maida martani sai kare kai.
Al'amarin da ya matukar bashi mamaki kenan
domin a saninsa duk sa'adda suke yiwa kansu
horon yaki shida kalmaru suna shafe rabin sa'a
ma suna gurmuzu kafin daya daga cikinsu ya
fara samun lagon wani,
Amma gashi yanzu daga fara wannan gurmuzu
har kalmaru ya fara jigatashi.
Su kansu 'yan kallo ma cika sukayi da tsananin
mamaki musamman yunaru wanda hankalinsa ya
dugunzuma ainun fiye da na kowa ya kara
tabbatarda abinda ya ke zargi yaji kamar ya
fashe da kuka saboda bakin ciki.
Babban abinda yafi daurewa mutane kai shine
kowa yasan irin tsananin karfin damtsen
Hamsaru da jarumtakarsa amma yau gashi cikin
kankanin lokaci an nuna masa cewa ruwa ba
sa'an kwando bane.
Haka dai Hamsaru yaci gaba da yin iya kokarinsa
don ganin cewa baije kasa ba amma duk sa'adda
sarkin yaki ya kawo masa sara ya kare sai yaji
kamar katon dutse aka bugo masa har layi yake
kamar zai fadi kasa amma sai ya cije yaki yarda
yaje kasan.
Ana cikin haka ne sarkin yaki ya shammaci
Hamsaru ya gabza masa duka da kafa a kirji,
saboda karfin dukkan sai da Hamsaru yai baya da
gudu tamkar wanda aka janye da majaujawa
sannan yayi wanwar a kasa.
Ai kuwa sai filin fadar ya rude da shewa mutane
suka rinka ihu suna cewa , MAZA SUN FADI "
Saboda tsananin bakin ciki bisa da abinda ya
faru sai yunaru ya kurma uban IHU kuma ya
fashe da kuka sannan ya yunkura ya mike tsaye
ya ruga inda jarumi kalmaru yake ya kwaye
fuskarsa don ya tona masa asiri.
Kwatsam! Sai kawai Aka ga gari yayi dundum! Ko
ina ya disashe da tsananin duhu yadda ko tafin
hannun mutum bazai iya gani ba.
Al'amarin da ya razana mutane kenan aka fara
guje-guje da iface-iface kenan.
Wannan ce damar da kalmaru da sarkin yaki suka
samu suka sauyin kaya a cikin duhun.
Kafin hasken gari ya dawo sarkin yaki ya koma
can kusa da sarki, shi kuma kalmaru ya dawo
tsakiyar filin dagar ya tsaya.
Faruwar hakan ke da wuya sai wannan duhu na
ba zato ya yaye, gari ya sake yin haske fayau!
Tamkar wani abu bai taba faruwa ba.
Ashe duk wannan abu da ya faru sarki da
fadawansa basu motsa daga inda suke zaune ba
, haka ma dakaru masu tsaro, mutanen gari ne
kawai suka firgice.
Koda jama'a suka ga gari ya dawo yadda yake
sai kuma aka rinka dawowa fada a guje anaci
gaba da yin shewa da jinjina ga kalmaru bisa ga
wannan nasara da yasamu ta lashe gasar sarkin
yaki.
Makida da mawaka kuwa suka kama aikinsu,
shikuma Hamsaru sai ya kasa tashi tsaye tun
sa'adda yaje kasa yaci gaba da zama dirshan
yana zubar da hawayen takaici.
A dai-dai wannan lokaci ne mahaifin Hamsaru
wato YUNARU ya taso daga inda yake zaune ya
taho wajen Hamsaru ya tasheshi tsaye ya
dubeshi yace,
Daina kuka ya kai dana Kayi sani cewa yanzu
take zansa a rushe wannan gasa domin kuwa
anyi algus acikin gasar."
Gama fadin hakan keda wuya sai yunaru yaja
Hamsaru suka isa har gaban sarki suka risina
suka kwashi gaisuwa, a sannan fadar tayi tsit!
Kowa ya zuba musu idanu yana sauraro don aji
abinda zasu fadi.
Sarki ya dubi yunaru yace. " ya kai abdul
Hamsaru fadi abinda ke bakinka muji"
Yunaru yayi gyaran murya yace, " ya shugabana
inada korafi akan wannan gasa har guda biyu
wanda na tabbatarda cewa an shirya algus da
manakisa kafin a sami nasarar kai dana kasa."
Koda jin wannan batu sai mamaki yakama gaba
daya jama'a dake fadar.
Shi kuma kalmaru sai hankalinsa ya dugunzuma
ainun ya rasa abinda ke masa dadi.
Da ganin haka sai sarkin yaki ya dafa kafadar
kalmaru yace, ka kwantar da hankalinka babu
abinda zai taba wannan nasara da ka samu
domin naga akamar cewar ubangijinmu ma yana
goyan bayanmu akan wannan gasa. "
Sarki Barham ya dubi yunaru cikin mamaki yace,
muna sauraronka ya abdul Hamsaru fadi
korafinka muji. "
Nan take fadar ta sake yin tsit! A karo na biyu
tamkar mutuwa ta gifta.
Yunaru ya dago kai ya dubi sarki cikin natsuwa
yace , ya shugabana wannan gurmuzu da akayi
bada kalmaru akayi ba da mahaifinsa akayi kaga
kenan an zalunci dana yayi fada da wanda dama
yafi shi jarumtaka "
Koda jin wannan batu sai kowa ya cika da
tsananin mamaki, filin fadar ya rude da hayaniya
kowa yana fadin albarkacin bakinsa har sai da
sarki ya daga hannu sannan akayi shiru.
Sarki Barham ya dubi yunaru yace, ya kai abu
abdul munji korafinka amma sai kazo muna da
cikakiyar sheda wadda zata tabbatar Muna da
zarginka.
Yunaru yace, kwarai kuwa inada cikakiyar hujja.
Idan har kalmaru ne yasami nasarar kai dana
kasa dole ne ya zamana cewa har a yanzu
yanada karfi da kuzari a jikinsa.
Na yarda ni na tareshi a yanzu mu fafata
Idan ya Kai ni kasa ya tabbata cewa shine ya kai
dana kasa tunda dai kowa a garin nan yasan
cewa ni ban kasance jarumi ba, asalima ban taba
fita yaki ba.
Koda jin wannan batu sai hankalin sarkin yaki ya
dugunzuma saboda yasan cewa ko kadan babu
kuzari a jikin kalmaru, koda karamin yaro suka
fafata ba zai iya kaishi kasa ba. MAZA SUN FADI part 7

Koda jin wannan batu sai hankalin sarkin yaki ya
dugunzuma saboda yasan cewa ko kadan babu
kuzari a jikin kalmaru, koda karamin yaro zasu
fafata ba zai iya kaishi kasa ba,
Shikuma kalmaru sai ya dubi sarkin yaki yayi
masa murmushi yana mai yi masa inkiya da kada
ya damu zai iya.
Nan take sarki Barham ya dubi kalmaru wanda ke
tsaye a tsakiyar fili yace,
"ya kai magajin sarkin yaki kaji korafin da wannan
dan uwan mahaifinka yazo dashi, shin zaka iya
kare kanka? "
Kalmaru ya gyada kai yace, zan iya ya
shugabana. "
Koda jin haka sai yunaru ya karbi takobi a wajen
wani Badakare ya dagata sama ya ruga da gudu
izuwa kan kalmaru cikin mugun nupi,
kai da gani kasan cewa so yake kawai ya kashe
shi.
Kalmaru ya tsaya cak! A inda yake ko motsi baiyi
ba, kuma baiyi wani yunkuri ba na nupin kare
kansa ba ko kai hari.
Da isowar yunaru daf da kalmaru sai ya kawo
masa mugun sara a wuya da nupin ya cire masa
kai,
cikin zafin nama kalmaru ya sunkuya takobin ta
sari iska kafin yunaru ya juyo ya kawo masa
wani harin sai kalmaru yasa hannunsa ya doki
bayansa,
Nan take yunaru ya kife kasa da rub da ciki har
bakinsa ya fashe yana zubar jini.
Ai kuwa sai fadar ta sake rudewa da shewa.
Hamsaru da mahaifinsa yunaru kuwa sai suka
kara kamuwa da tsananin bakin ciki.
Nan take sarki ya kirawo kalmaru yaje daf dashi
ya tsaya, sarki ya mike tsaye ya karbi wata
takobi ta zinare daga hannun wazirinsa wacce
duk wanda aka baiwa ita ya zama sarkin yakin
kasar.
Dama takobin a hannun sarkin yaki take amma
tun a jiya sarki ya tura a karbota.
Koda sarki ya karbi takobin ya juya zai mikawa
kalmaru sai kawai akaji yunaru yace, "A dakata"
Cikin mamaki kowa ya zuba masa idanu, yunaru
ya mike tsaye yana mai goge jinin bakinsa,
sannan ya tako ya taho wajen sarki ya sake
risinawa a karo na biyu yace, " ya shugabana
inada korafi na karshe. "
Sarki ya gyada kai cikin alamun damuwa yace,
zan baka dama ka bayyana korafinka, amma idan
ya zamana cewa baka da cikakiyar hujja kawai
hassada ce tasa ka fadeshi zansa a tsareka a
kurkuku tswaon wata ukku. "
Yunaru ya gyada kai yace "na yarda "
Sarki yace fadi korafinka muna sauraro"
Yunaru yai gyaran murya sannan yace, ya
shugabana a dazu sa'adda kalmaru Ya sami
nasarar kai dana kasa , nan take gari ya disashe
da tsananin duhu ta yadda mutum ko tafin
hannunsa baya gani.
Ina mai tabbatar maka da cewa ba kusafin rana
bane, tsafi ne sarki yaki yayi domin kawai su
sauya tufafi shi da dansa yadda mutane baza su
gani ba.
Amma tabbas bada kalmaru akayi wannan gasa
ba da sarkin yaki akayi ta"
Koda jin wannan batu sai jikin kowa yai sanyi a
filin fadar.
Sarkin yaki da kalmaru kuwa sai hankalinsu ya
dugunzuma ainun domin sun tabbatarda cewa
asirin su ya tonu.
Sarki yai shiru yana tunani da nazari har tsawon
'yan dakiku sannan ya dago kai ya dubi yunaru
yace, hakika wannan korafi naka abin dubawa ne
kuma ta hanya daya kadai zamu iya tabbatarda
gaskiya "
Nan take sarki yace, " ina BOKA HIZAINU YAKE?"
Waziri yace, " ranka ya dade ai boka hizainu bai
zoba,
dama ya aiko an gaya mini cewa ba zai sami
damar halarta wannan taro ba saboda ya shiga
halwar wani aiki mai muhimmanci. "
Koda jin haka sai hankalin sarki Barham ya tashi
ya sake yin shiru yana tunani a karo na biyu.
Daga can sai ya dubi waziri yace, "Ba zamu tashi
daga nan ba har sai mun tabbatarda gaskiyar
abinda muke zargi.
Ya kai waziri na umurceka da ka tafi izuwa gidan
boka hizainu yanzu ka sameshi,
kace dashi nace ya duba mana yanzu ya gano
mana gaskiya al'amarin.
Koda gama fadi hakan sai sarki ya dubi mutum
ukku daga cikin fadawansa wadanda ya Aminta
dasu ya tabbatarda cewa sun kasance masu
gaskiya yace dasu, ku kuma kubi waziri a yi
komai a gabanku domin ku zamo shaida.
Sannnan inason dakaru dari suyi muku rakiya
izuwa gidan boka hizainu domin tsaron lafiyarku
saboda wannan sarauta ta sarkin yaki sarauta ce
mai muhimmancin gaske a cikin mulkin kasar
nan,
Idan har aka bayar da ita ga inda bai dace ba
za'a sami babbar matsalar da zata iya janyo
rushewar mulkina."
Nan take waziri da fadawa ukku suka mike tsaye
aka kawo musu dawakai ukku suka hau sannan
dakaru dari suka yi musu rakiya.
Tafiyarsu ke da wuya sai wadansu kyawawan
'yan mata su goma sha daya cikin kyakkyawar
shiga iri daya suka shigo cikin tsakiyar filin tare
da wadansu Makada,
Take makadan suka fara aikinsu na doka manya
ganguna suna fitar da sauti mai dadi da sanyaya
rai.
Su kuma yan matan suka fara tikar rawa iri daya
a tare mai kayatarwa domin debewa sarki da
jama'a dake wajen kewa kafin su waziri su dawo
daga gidan boka hizainu.
A sannan ne kuma kuyangi suka rinka kawowa
sarki da yan majalisarsa kayan shaye-shaye da
ya'yan ita tuwa suna ci dasha.
Ana cikin wannan hali ne Hamsaru da mahaifinsa
suka kebe gefe daya suka zauna.
Hamsaru ya dubi yunaru yace, ya kai Abbana jiya
ka gaya mini cewa na kwantar da hankalina lallai
ka aiwatar da abinda kake ganin cewa sai na
sami nasara a wannan gasa ta ko wanne hali,
Yanzu gashi kalmaru ya kaini kasa a gaban
kowa.
Tabbas idansu waziri suka dawo daga gidan boka
hizainu da amsar cewa ba tsafi su kalmaru sukayi
ba, shikenan fa damarmu ta kare kuma burin da
yake gabanmu na hana kalmaru samun damar
haihuwa ya rushe. "
Sa'adda Hamsaru yazo nan a zancensa sai
yunaru ya kyakyale da dariyar mugunta.
Al'amarin da yai matukar baiwa Hamsaru
mamaki kenan, yai shiru kawai yana kura masa
idanu kawai........
Daga can sai yunaru ya hade fuska yai shiru ga
barin dariyar sannan yace, " ya kai dana inaso ka
sani cewa, kada mage ba yankawa bane.
Koda ban sami nasarar doraka akan karagar
sarkin yaki ba yanzu, nan gaba sai na sami
nasara, kuma koda ina tsare a cikin kurkukun.
Kada ka manta cewa a gaba daya kasar nan
babu wani attajiri mai yawan dukiyata.
Inaso ka sani cewa babu abinda kudi ba zai iya
siya ba, ka sani cewa rabin yan majalisar sarki
yarana ne, ko cewa nayi su jefa kansu a cikin
wuta sai sun jefa.
Shi kansa waziri na hannun damana ne, a cikin
fadawa ukkun ma da aka turasu gidan boka
hizainu yanzu akwai mutum daya nawa,
Ina tabbatar maka da cewa koda boka hizainu
yace ba tsafi akayi ba zasu iya sauya maganar
su ce yace tsafi ne, "
Koda jin wannan batu sai Hamsaru yai ajiyar
zuciya cikin alamun damuwa yace, abu daya
nake tsoro.
Idan har boka hizainu ya taso da kansa yazo ya
bayarda shaida da bakinsa anan fada agaban
kowa shirin nan duk da akayi ya watse.
Ni kuma babban bakin cikina a yanzu shine naga
sarki ya mikawa kalmaru wannan takobi ta zinare
ya zamana cewa bani ya mikawa ba.
Koda jin haka sai yunaru ya gyada kai yace,
Tabbas abinda ka fada yanzu zai iya faruwa,
amma duk da haka kada ka damu ka kwantar
hankalinka.
In dai ina raye a doron kasa koda kalmaru ya
zama sarkin yakin birnin nan sai na shirya tuggun
da sarki zai saukeshi daga kan matsayin ya maye
gurbinsa da kai.
Sai na jefa rayuwarsa da ta mahaifinsa cikin
mugun tsananin da kunci yadda zasu gwammace
mutuwa akan rayuwa.
Lokacin da yunaru yazo nan a zancensa sai
Hamsaru ya dubeshi cikin mamaki yace,
Ya kai Abbana ni kuwa na dade inason nayi maka
wata tambaya tun-tuni,amma ban samu dama
ba.
Wai shin menene dalilin da yasa ka tsananta
gaba tsakaninka da sarkin yaki da dansa kalmaru
alhalin kuma sarkin yaki ya kasance dan uwanka
na jini tunda mahaifinku daya? "
Yayin da yunaru yaji wannan tambaya daga bakin
dansa Hamsaru sai yai ajiyar zuciya cikin alamun
tsananin takaici yace,
Gabata da dan uwana sarkin yaki ta samo asali
ne tun muna yara kanana sbd mahaifinmu ya
kaunaceshi fiye da kowa a cikin ya'yansa duk da
kasancewar mun kai mu arba'in da uku.
Ba wani abu bane yasa mahaifinmu yake son
sarkin yaki ba fiye da kowa a cikin mu sai
saboda irin jarumtakar da yake da ita da kuma
tausayi.
Shi dai mahaifinmu ma farauci ne wanda ya
shahara a fagen farauta, domin Shi kadai yana
iya shiga daji ya kamo katon zaki ko giwa yazo
dasu cikin gari a raye.
Bisa wannan dalili ne ya sami dukiya mai yawan
gaske a wajen sarkin dake mulki a wannan
zamani wanda shine mahaifin sarki Barham na
yanzu,
Tun a wannan lokaci sarkin yaso ya baiwa
mahaifinmu sarautar sarkin yakinsa sbd ya
jarraba jarumtakarsa yaga cewa babu wani ma
yaki kamarsa a gaba daya nahiyar wanda idan
dakaru sama da dubu suka lullubeshi da sara da
suka sai ya kaisu kasa.
Acikinmu gaba daya babu wanda ya gado
jarumtakar mahaifinmu face sarkin yaki Ridwan.
Bisa wannan dalili ne yake fifitashi akanmu,
kuma ko gidan sarki baya zuwa tare dayanmu sai
da Ridwan kadai.
Wannan dalili yasa mu duka muka tsani Ridwan
muka fara tunanin hanyar da zamu bi mu rabashi
da duniyar gaba daya.

MAZA SUN FADI !!! Part 8

Wannan dalili yasa mu duka muka tsani Ridwan
muka fara tunanin hanyar da zamu bi mu rabashi
da duniyar gaba daya. Amma sai muka kasa
saboda shi mahaifin namu ya kareshi da sihirin
tsafinsa.
Kai hatta Sirrinkansa na daji da sirrin farauta a
dajin mahaifinmu ya baiwa Ridwan duka.
Mukuma sauran yayansa babu wanda ya samu
guda daya.
Lokacin da muka ga munyi iya kokarinmu akan mu
hallaka Ridwan mun kasa,
sai muka taru gaba dayanmu
muka je gaban mahaifin namu inda muka iske shi
a cikin turakarsa tare da Ridwan a zaune suna cin
abinci tare.
Koda mahaifin namu ya ganmu mu duka mun
shigo cikin turakarsa mun zauna sai jikinsa yai
sanyi
ya tsame hannunsa daga cikin akushin da suke
cin abinci,
Ya dubemu cikin alamun mamaki da damuwa
yace,
ya ku ya'yana yau kuma menene ya faru kuka
taro kanku gaba daya kukazo wajena?"
Koda jin wannan tambaya sai na nayi ajiyar
numfashi nace,
"ya kai Abbanmu zanyi magana da yawun sauran
yan uwana a matsayina na babbansu,
muna da bukatar ka bamu amsar wata tambaya
guda daya wacce ta jefamu cikin wasi-wasi
gamida da tsananin damuwa da tashin hankali a
tsawon shekaru.
Wannan tambaya kuwa itace,
"menene dalilin da yasa ka fi kaunar

1 Comments On MAZA SUN FADI 1 to 4
avatar
abubakar-abdullahi-6

10 months ago

Reply

yes

Please Login or Register in order to submit comment