Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya kwarara uban ihu, ai kuwa sai
gaba dayan dakarun nasa ma suka zare nasu
takubban sukayi koyi dashi wato suma suka
kwarara uban ihun.
Nan fa ihun nasu ya cakude da na abokan
gabarsu, suma sai suka zaburi dawakansu suka
rugo izuwa garesu..
Wohoho, tashin hankali ba'a sama rana haka
kuma masifa batada dadi domin wanda bai san
ta ba shi yake fatan ta.
Lokacin da aka ruguntsume da azababben yaki
tsakanin wadannan rundunoni biyu sai ya
zamana cewa an kasa gane abinda ke wakana
domin babu abinda idanu ke gani face shawagin
jini da sassan bil'adama na kowanne bangare a
sararin samaniya yana zubowa kasa tamkar
ruwan sama.
Kunnuwa kuwa bayajin komai sai ihun mazaje da
kururuwarsu a lokacin da jini yaci gaba da
tartsuwa da fallatsi kuma yana kwarara a kan
kasa tamkar teku ta balle.
Kai saboda masifa ta kai masifa babu mai gane
wani in ba don bambancin launin irin kayan yakin
da ya bambanta. MAZA SUN FADI!!! LITTAFI NA 3 PART 3

Lokacin da aka ruguntsume da azababben yaki
tsakanin wadannan rundunoni biyu sai ya zamana
cewa an kasa gane abinda ke wakana domin babu
abinda idanu ke gani face shawagin jini da sassan
jikin bil'adama na kowanne bangare a sararin
samaniya yana zubowa kasa tamkar ruwan sama.
Kunnuwa kuwa basa jin komai sai ihun mazaje da
kururuwarsu a lokacin da jini yaci gaba da
tartsuwa da fallatsi kuma yana kwarara a kan
kasa tamkar teku ta balle.
Kai saboda masifa ta kai masifa babu mai gane
wani in ba don bambancin launin irin kayan yakin
da ya bambanta ba.
Kalmaru da sarki Daryan kuwa duk inda suka
kutsa a cikin abokan gabarsu sai dai kaga maza
na zubewa kasa tamkar ana sassabe a gona
kowannensu jikinsa ya rine da jini, hatta fuskarsu
ma sai ya sa hannu ya share jini sannan yake iya
ganin gabansa.
Kai hatta takubbansu ma sun rine da ruwan jini
kuma dada ragargazar maza suke tamkar ba zasu
taba gajiyawa ba.
Babu abinda zai baiwa mutum mamaki face sai
da aka shafe sama da sa'a ukku ana yin wannan
masifaffan yaki amma ko sau daya kalmaru da
sarki Daryan basu yi gaba da gaba ba,
kowannensu ya bace a cikin yawan dakaru dake
cikin filin yaki da turmutsutsu.
Abu na biyu da zai kara baiwa mutum mamaki
shine yadda dakarun sarki Daryan suka kasa
kararda dakarun kalmaru alhalin sun ninkasu yawa
sau dari, ba komai ne ya janyo hakan ba face
tsananin iya yaki da kuma sababbun dabarun yaki
wadanda kalmaru ya kirkiro kuma ba'a taba ganin
irin su ba.
Wani irin salon yaki suke yaki sai a sami adadinsu
a bayansu a tsaye basa yakin amma da zarar
sunga na gabansu sun fara gajiya sai su karbesu
su shige gaba su kuma su dawo bayansu , kaga
kenan a wannan lokaci su abokan gaba zasu ci
gaba da yaki ne da masu rashin gajiya don haka
cikin kankanin lokaci za'a ga sun rafkesu.
Lokacin da sa'a uku ta cika sarki Daryan ya lura
da yadda duk jikinsa ya rine da jinin abokan
gabarsa kuma yaga cewa bai san iya adadin
rayukan da ya dauka ba na abokan gaba sai ransa
yayi dadi wani irin farinciki ya lullubeshi don haka
sai ya tarwatsa dakarun dake gabansa, ya juyo ya
dubi gabas da yamma, kudu da arewa domin yaga
irin gagarumar nasarar da suka samu a yakin, nan
take hankalinsa ya dugunzuma ainun, wani irin
gagarumin bakin ciki ya mamaye zuciyarsa.
Adaidai wannan lokaci ne ya hango mahaifinsa
sarki saumir a can gefe daya yana ta ragargazar
dakarun su kalmaru, duk inda yasa gabansa maza
ne ke zuba kuma yaki yake cikin wani irin zafin
nama na ban al'ajabi sai ci gaba da yin
mummunar barna yake an rasa wani jarumi da zai
iya tsaida shi domin komai yawan abokan gabar
idan suka yanyameshi suka yi masa rudugudu sai
dai kaga ya tarwatsasu ya rugurguzasu sun zube
kasa filla-filla
Yana cikin yin wannan mummunar barna ne
kalmaru ya ankara dashi kuma ya lura da irin
mummunar barna da yake shi kansa kalmaru sai
da ya razana domin bai taba ganin dattijo mai
tsantsanin jarumtaka ba irin wannan kuma gashi
musaki mai hannu daya,
Koda kalmaru yaga hakan sai ransa ya baci
zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone don
haka sai ya zaburi dokinsa da baya da gudu da
nufin ya kai ya kai inda sarki saumir ketayin
barna,
Ai kuwa sai wani Badakare daga cikin abokan
gaba ya tsire dokin nasa da mashi a wuya, take
dokin kalmaru yayi tutus dashi suka fadi kasa
tare, dokin ya kama shure shuren mutuwa, shi
kuwa kalmaru sai ya mike tsaye zumbur ya daka
tsalle sama ya kama gudu akan kawunan jama'a
ya durfafi inda sarki saumir yake,
Ai kuwa koda dakarun sarki Daryan suka ji
kalmaru yana dira akan kawunansu sai suka rinka
kaiwa kafafunsa sara da takubbansu amma sai ya
rinka gocewa dukkan harin nasu ya zama kamar
tsuntsu mai fukafuki,shi kansa kalmaru sai da yayi
mamakin yadda akayi yayi irin wannan gagarumar
bajinta,domin dama mahaifinsa ne ya
Koya masa irinta amma sai gashi yayi abinda ma
ya wuce wanda aka koya masa din.
A haka yaci gaba da durfafar inda sarki saumir
yake,
yana cikin hakane kuma ya hango sarki Daryan
yaga ashe mummunar barna da yake yiwa
dakarunsa harma tafi wacce sarki saumir keyi
domin a cikin dakiku kadan yake batarda kimanin
dakaru goma.
Nan fa hankalin kalmaru ya rabu gida biyu ya rasa
inda zai fara zuwa,
Shin juyawa zai yi da baya yaje ya tari sarki
Daryan ko kuwa kokari zaiyi yaje ya tari sarki
saumir,
A dai-dai wannan lokaci ne kalmaru yaga wadansu
zakwakuran dakarunsa guda ukku wadanda yake ji
dasu sun afkawa sarki saumir da nufin su hallaka
shi farat daya bisa ganin irin barna da yake yiwa
'yan uwansu, koda suka afka masa da sara da
suka sai yayi wata irin katantanwa a tsakiyarsu
yana mai sunkuyawa kasa ai kuwa sai gashi ya
yanki kowannensu a kirji,
jini yayi tartsuwa daga cikin kirazan nasu sukayi
tsalle da baya suna masu kwala ihu gami da
faduwa kasa,
Koda kalmaru ya hango abinda ya faru ga
wadannan dakarun nasa guda ukku wadanda yake
matukar ji dasu a filin yakin.
Shi azatonsa ma zasu iya jagorantar yakin koda
babu shi,
Shi azatonsa ma zasu iya jagorantar yakin koda
babu shi,
Sai ransa ya baci ya daka wawan tsalle daga inda
yake ya kaiwa sarki saumir wawan sara a wuya
da nupin ya cire masa kai, inba don sarki saumir
yayi wuf ya sunkuya ba da tuni aikin gama ya
gama amma duk da haka sai da karfin takobin
kalmaru ya zabtaro wani sashi na gashin kan sarki
saumir kuma ya sami nasarar dukan kirjinsa da
kafa,
Sarki saumir ya dan ja da baya yayi taga taga
amma sai ya tsaya kyam kamar giwa, Adaidai
wannan lokaci ne kalmaru ya duro kasa bisa
kafafunsa suka kama kallon kallo,
Kada sarki saumir ya kurawa kalmaru idanu
tswaon yan dakiku sai
Ya takarkare ya bushe da dariyar mugunta, a
hakan duk abokin gabar da yazo gaban kalmaru ko
saumir sai kaga sunyi masa kwaf daya ya zube
kasa matacce.
Sarki saumir ya nuna kalmaru da dan yatsa yace
kai yaro tsaya iya matsayinka domin kana zartawa
zaka zama tarihi,
Ka sani cewa na gwazba da mahaifinka ma bai ji
da dadi ba,
Tabbas Nayarda cewa kai jarumi ne
Domin tunda aka fara wannan yaki kai ka dai ne
ka sami nasara iya taba jikina kuma ka cire wani
abu daga cikin gashin kaina
Tabbas kana kama da mahaifinka kuma ka gado
shi a jarumtaka amma ka sani cewa yau ka taka
sawun barawo.
Ba kai nakeso na gani ba a gabana, ubanka
nakeso ya tareni domin na dauki fansar abinda
yayi mini amma ni duka hannayen nasa biyu
nakeson na sare maimakon nawa guda daya dana
rasa kuma na kamashi a raye na tsareshi kurkuku
yayi ta kunar bakin ciki har ajalinsa amma tunda
yaji tsoro ya kasa fitowa yakin kuma ya turoka ka
wakilceshi, lallai akanka zan dauki wannan fansa.
Koda sarki saumir yazo nan a jawabinsa sai
kalmaru ya tari numfashinsa yana mai daka masa
tsawa yace kai tsohon azzalumi kayi sani cewa
kunyi sake dan zaki ya girma kuma karen bana
shike maganin zomon bana,
Inaso ka sani cewa mahaifina ba ma tsoraci bane
domin har gobe ruwa na maganin dauda,
Babu yadda baiyi ba akan ya fito wannan yaki
amma sai sarkinmu ya hanashi to ni gashi na fito
amadadinsa kuma
Shima yana da buri ya cika aikinsa ya kaika
lahira, don haka nine zan cika masa wannan aikin,
Koda jin haka sai sarki saumir ya bushe da dariyar
a karo na biyu sannan ya turbune fuska ya dubi
kalmaru yace ai kuwa sai dai mahaifin naka yaga
gawarka ba dai cikar burinsa ba.
Sarki saumir na gama fadin hakan sai ya daka
tsalle sama daga kan dokinsa ya doki kirjin
kalmaru da gwiwar kafarsa ta dama saboda karfin
dukkan sai da kalmaru yayi baya da gudu tamkar
an janyeshi da majaujawa ya fada can jan mayaka
Yana mai yin aman jini amma sai ya mike zumbur
cikin zafin nama da juriya ya daga takobinsa
sama ya riketa da hannu biyu yana mai gyara
tsayuwa.
Koda ganin haka sai sarki saumir yayi masa wani
dan guntun murmushi na mugunta irin wanda
jaruman kwarai sukeyi sannan ya taho gareshi da
sauri yana mai buda hannunsa mai rike da
garkuwa, koda ganin haka sai shima kalmaru ya
rugo izuwa gareshi suna haduwa suka kacame da
azababben yaki, ya zamana cewa suna kaiwa
junansu sara da suka cikin tsananin zafin nama
juriya da bajinta,
Koda aka fara wannan artabu kalmaru yasha
mamaki kuma ya gane cewa tsohon kashi da sabo
ba daya bane
Abinda ya daurewa kalmaru kai shine ta yaya
wannan tsohon mai hannu daya jal yake iya tare
duk hare-harensa kuma yake maida martani,
Harma nashi sara da sukan sunfi nashi zafi, kai
inba don ma kalmaru yanada matukar juriya da
zafin nama ba da tuni sarki saumir ya gama
dashi.
Sai da suka shafe kusan dakika dari uku da
arba'in suna wannan bakin gurmuzu dayansu bai
sami nasarar koda lakutar jikin daya ba,
Al'amarin da ya fusata kowannensu kenan kuma
duk wannan abu da ke faruwa sarki Daryan bai
sani ba
domin yana can yana ta ragargazar dakarun birnin
zamar.
Shi dai kalmaru mamaki ne ma ya ishe shi akan
yadda tsoho mai hannu daya ya zame masa
alakakai.
Bisa dole duk su biyun suka dan ja da baya kadan
suka yi cirko cirko suna haki da kallon juna kamar
zakaru.
Kowannensu acikin zuciyarsa yana tunani da
nazari hanyar da zai bi ne ya sami nasara
gamawa da dayan,
Kowannensu acikin zuciyarsa yana tunani da
nazari hanyar da zai bi ne ya sami nasara
gamawa da dayan,
Kamar hadin baki sai suka rugo izuwa kan juna a
lokaci guda kowannensu yana ihu da karaji, suna
haduwa suka sake kacamewa da azababben yaki
amma wannan karon sai sarki saumir ya sauya
salon yaki ya hada da naushi da bugu da hannu
da kafa,
Da yake yafi kalmaru zafin nama sai ya
shammace shi ya doki kashin gwiwar kafarsa ta
hagu take kashin ya goce daga jikin dan uwansa,
kalmaru ya kurma uban ihu sakamakon tsananin
zafi da zojin da yaji,
Kafin yayi wani yunkuri saumir ya sake kawo
masa wawan sara a ciki da nufin ya farkeshi,
cikin zafin nama ya da baya amma duk da haka
sai da ya kawo masa suka da tsinin takobi a
gefen kirjinsa na hagu,take takobin ta lube acikin
kirjin, kalmaru ya sake kurma uban ihu kuma yayi
sauri ya rike takobin da hannunsa guda a lokacin
da saumir ke kokarin danna takobin domin ta
lume gaba daya ta faso gadon bayansa,
Kalmaru ya dage iya karfinsa ya hana sarki
saumir ida nufinsa kuma gashi jini na kwararowa
daga cikin kirjin nasa, gashi a durkushe ya kasa
mikewa sakamakon gocewar kashin gwiwar tasa,
Hakika duk wanda yaga halin da kalmaru ke ciki
a wannan lokaci dole ne ya tausaya masa yasan
cewa ya cika zarto kuma jarumin kwarai,
Adaidai wannan lokacin ne sarki saumir ya fara
kyalkyalar dariyar mugunta sannan ya dubi
kalmaru yana mai ci gaba da kokarin danna
takobin a cikin kirjinsa yace ai na gayamaka
cewa sai dai mahaifinka yaga gawarka ba dai ya
cika burinsa ba,
Kwatsam ba zato ba tsammani kafin saumir
yagama rufe bakinsa sai yaga kalmaru ya zare
takobin da karfin tsiya daga cikin kirjinsa, jini yayi
wata irin tartsuwa yayi 'yar dungure a kasa
gaban saumir
kafin saumir ya leka kasan nasa takobin kalmaru
ta soke masa tasa takobin a makoshi take
takobin kalmaru ta nutse a cikin wuyan saumir ta
bullo ta keyarsa nan fa ya kama mata gungun a
tsaye yana mai kwalawa dansa kira cikin ihu
wato yana mai kiran sunan sarki Daryan
Sarki Daryan na cikin ragargazar dakarun birnin
zamar sai ya jiyo sautin murya mahaifinsa acan
bayansa,
A dimauce ya juyo da dokinsa baya ya tarwatsa
abokan gaba kuma ya kutsa ta cikinsu da karfin
tsiya yana kai sara da suka ta damansa da
hagunsa ya samarwa kansa hanya ya durfafi inda
ya juyo sautin murya mahaifin nasa a lokacin da
zuciyarsa ke daka bisa zargin cewa lallai ba
lafiya ba,
Ai kuwa tunda daga nesa kadan ya fara hango
kalmaru tsugune a kasa ya kasa mikewa,amma
ya zubo masa idanu fuskarsa na ya tsine,
Koda ya dubi gefen kalmaru yaga gawar
mahaifinsa kwance a kasa sai ya takarkare ya
kwarara uban ihu wanda ya razana gaba dayan
mayakan dake filin dagar aka jujjuya da baya aka
daina yakin aka zuba masa idanu a lokacin da ya
karawa dokinsa kaimi ya sukwanoshi da gudun
tsiya izuwa kan kalmaru yana mai sakin linzamin
dokinsa da sake zaro wata takobin a gadon
bayansa wato ya hada takubba biyu a hannunsa,
A wannan lokaci komai yawan dandazon mayaka
idan suka hango sarki Daryan sai sun firgita sun
watsar da makamansu sun arce saboda tsananin
kwarjininsa da kuma muguwar fusatar da yayi,
Idanunsa sun kada sunyi jajur tamkar garwashin
wuta da ya ruru ainun,
Kuma gashi dama duk jikinsa da takobinsa guda
sun rine da jini
Kuma gashi dama duk jikinsa da takobinsa guda
sun rine da jini
Koda kalmaru yaga yadda sarki Daryan ya
durfafoshi cikin tsananin fishi da mugun nupi sai
ya tabbatarda cewa lallai idan ya riske shi haka
yadda yake a tsugune kuma a galabaice tamkar
gurgu, farat daya zai yi masa kissan gilla cikin
tsananin juriya irin ta manyan mazaje kalmaru
kalmaru ya kama kashin gwiwar kafar tasa ya
durguzashi wato ya maidashi dai-dai yadda yake
da saboda tsananin zafin da ya ji bai san sa'adda
ya kurma uban ihu ba,
Ya fadi kasa, sa'adda kwallah wuya ta cika masa
idanu, yaji kamar sare kafar tasa akayi.
Adaidai wannan lokaci ne sarki Daryan ya iso daf
dashi ya kawo masa wawan sara da takubbansa
biyu cikin nufin guntule masa kai,
Cikin bakin zafin nama kalmaru ya sunkuya
takubban suka sari iska suka hadu da junansu
wani irin tartsatsin wuta ya tashi kalmaru ya
wurgina sau uku a kasa can gefe daya,
Kawai sai gani akayi ya mike tsaye zumbur yana
layi sakamakon jini dake zubawa daga cikin
kirjinsa, cikin kuzari kalmaru yasa hannunsa guda
ya yage rigar jikinsa ya toshe ramin raunin nasa
kuma ya daure raunin tamau da ragowar
tsumman rigar tasa don kada cikon ya cire jini
yaci gaba da zuba. MAZA SUN FADI!!! LITTAFI NA 3 PART 4

Kawai sai gani akayi ya mike tsaye zumbur yana
layi sakamakon jini dake bulowa daga cikin
kirjinsa,
Cikin kuzari kalmaru yasa hannunsa guda ya yage
rigar jikinsa ya toshe ramin raunin nasa kuma ya
daure raunin tamau da ragowar tsumman rigar
tasa don kada cikon ya cire jini yaci gaba da
zuba.
Koda ganin wannan jarumtaka da kalmaru yayi sai
sarki Daryan ya duro kasa daga kan dokinsa ya
tsaya cak
Sa'adda tazarar dake tsakaninsa da kalmaru bata
wuce taku biyar ba,
Koda ya sake duban gawar mahaifinsa a karo na
biyu sai hawaye ya subuto masa kuma zuciyarsa
ta kama tafarfasa kamar zata kone saboda bakin
ciki,
Bai san sa'adda ya kwarara uban ihu ba sannan
ya dubi kalmaru fuskarsa nayin gantsin wutar
tsana da gaba na ruruwa a cikin idanunsa,
Yace, na rantse da kaunar da nake yiwa Mahaifina
ko ni ko kai a filin yakin nan,
Bazamu daina yaki ba har sai dayanmu ya kashe
daya,
Yana gama fadin haka ya zaburo da gudu izuwa
kan kalmaru, shima kalmaru sai ya zaburo izuwa
kansa,
Suna haduwa suka ruguntsume da azababben yaki
kamar zasu cinye junansu danyu,
Ai kuwa sai sauran dakarun ma suka dada
kacamewa....
Yaki ya dawo sabo kuma danye tamkar ma a
sannan aka farashi
yazamana cewa ihun mazaje da karafkiyar karafa
ta cika dajin gaba daya ta razana duk wani abu
mai rai dake bisa doron kasa da karkashinta.
Sai da sarki Daryan da sarkin yaki kalmaru suka
shafe Sa'a daya da rabi cif suna kaiwa junansu
sara da suka amma ko sau daya babu wanda ya
sami nasarar yiwa dan uwansa rauni koda bille
kuwa,
Al'amarin da ya fusatasu kenan duk su biyun, don
haka babu shiri suka yi ja da baya suka tsaya
suna haki da hararar juna kamar yadda akayi dazu
tsakanin kalmaru da sarki saumir,
Ko hutun dakika ashirin basu yi ba, suka sake
kacamewa da sabon azababben yakin gaba,
kamar zasu ci naman junansu danye,
Wannna karon
Sai labari yasha bam-bam domin sun sauya salon
fada domin sun hada da tsalle-tsalle da kwance-
kwance a kasa gamida kai naushi da bugu.
Ai kuwa nan take labarin yasha bam-bam domin
sun fara yiwa junansu rauni duk da cewa kusan
karfinnsu yazo daya sarki Daryan ne ya fara
samun nasarar yankan kalmaru a kafadarsa ta
dama.
Kafin ya kara kai masa wani harin tuni shima ya
samu nasarar yankarsa a kafadar hagu,
Haka dai suka cigaba da samun nasarar yiwa
junansu rauni har sai da kowannensu ya sami
rauni bakwai a jikinsa ya zamana cewa jini na
zuba a jikinsu amma saboda naci gamida tsananin
juriya basu fasa cigaba da yaki ba,
Kamar ma a sannan suka fara yakin.
Al'amarin gimbiya lazima kuwa wacce ke zaune a
cikin keken doki a tsakiyar dakarun birnin zamar
sa'adda aka fara wannan bakin masifaffen yaki an
barsu ne a can baya bisa tsaron dakaru dubu
arba'in,
Batada ikon barin wajen sai dai ta hau saman
keken dokin ta hango abinda ke faruwa acan filin
yakin sannan ta rubuta acikin wani littafi wanda
tazo dashi.
Tsakanin inda take da sansanin yakin akwai
tazara ta kimanin taku dari hudu da saba'in da
shidda
don haka tana hango mutane da ke can sansanin
yakin ne y'an mini mini saboda nisa.
Bisa wannan dalili ne hankalinta ya dugunzuma
ainun kuma ranta ya baci saboda batada halin
ganin ainihin abinda ke faruwa a filin yakin sai dai
in angama yakin wadanda suka tsira da rayuwarsa
su bata labari.
Nan fa gimbiya lazima ta koma cikin keken doki
nata tayi zamanta ta shiga tunani hanyar da zata
bi ta sulale taje cikin sansanin yakin ba tare da an
ganeta ba.
Tana cikin wannan tunani ne wata dabara ta fado
mata kawai sai tayi kiran sunan daya daga cikin
dakarun dake tsaronta.
Huzen ya yaye labulan keken dokin ya leko da
kansa yana mai risinawa cikin biyayya yace,ya
shugabata meye bukatar ki?
Lazima tayi murmushi mai taushi ga Huzen tace,
ina son ka shigo cikin keken dokin nan ka zauna
tare da ni domin ka debe mini kewa da tsoron da
nake fama dashi bisa jiyo ihun mazaje da nake ji
daga can sansanin yaki.
Koda jin wannan batu sai mamaki da tsoro suka
kama sadauki Huzen ya dubeta cikin alamun
matukar damuwa yace , ya shugabata kina so
sarki yasa a tsirani ne idan ya sami labarin cewa
na kadaita dake a cikin keken dokinki.
Lallai wannan laifi ne mai girma a wajen sarki,
Kiyi hakuri bazan iya ba.
Koda jin haka sai fuskar gimbiya lazima ta juye
izuwa tsananin fushi tayi wuf ta zare wata wuka
mai tsananin kaifi da tsini daga kugunta ta dorata
akan makoshin Huzen har wukar ta dan tsireshi
jini ya fito sannnan tace ko kayi abinda na
umurceka ko kuma na kasheka sannan na kashe
kaina in yaso raina ya rataya a wuyanka
Mahaifina ya kama iyalinka da daginka gaba daya
ya kashe su.
Duk wannan zance dake wakana tsakanin gimbiya
lazima da sadauki Huzen babu mai jinsu domin
cikin karamar murya suke maganganinsu.
Cikin tsananin tsoro jikinsa na karkarwa ya kunna
kai ya shige cikin keken dokin
A wannan lokaci sauran dakarun basu lura da
shigarsa ba don sai da ya faki numfashinsu a
matsayinsa na shugabansu wanda basa sa masa
ido.
Huzen na shiga cikin keken dokin sai gimbiya
lazima ta shammace shi ta gabza masa wawan
naushi a kuibin kasan kunnensa na hagu, nan take
numfashinsa ya dauke yayi suman tsugune, zai
fadi kasa kenan sai tayi sauri ta tallafoshi ta ajiye
shi kasa a hankali,
Cikin sauri ta tube kayan jikinta tayi musanya
dana Huzen sannan ta kishingidar dashi tamkar
barci yake yi.
Hatta hular karfen dake kansa sai da ta cire tasa
akanta,
Shima sai ta rufe fuskarsa da irin kyallen da ta
rufe fuskarta
Lazima ta fito daga cikin keken dokin a hankali
yadda ko motsinta ba'a ji ba
Kawai sai ta dubi mataimakin huzen tayi masa
inkiya da zataje can sansanin yakin ta gano halin
da ake ciki.
Ba tare da ta jira taji abinda zai ce ba sai kawai
ta falfala da gudu ta nufi inda sansanin yakin
yake.
Cikin alamun tsananin damuwa mataimakin huzen
ya dubi daya daga cikin dakarun yace,amma fa
Huzen yayi babban ganganci domin bisa dokar
sarkin yaki ba zai taba gusawa daga nan inda aka
umurcemu da tsayawa ba face ya tabbatarda
cewa muke samun nasara a wannan yaki kuma
gashi babu wanda yasan halin da ake ciki.
Koda jin haka sai Badakaren yayi ajiyar numfashi
yace, kwarai kuwa abinda ka fadi gaskiya ne
To amma inbanda abinka ta yaya zai iya gane
hakan idan baije kusa da sansanin yakin ba.
Badakare ya gyada kai yace hakane to amma dai
ai sarkin yaki yace komi ake ciki zai aiko mana da
umurni bisa abinda ya kamata muyi,
Mataimakin huzen yace to idan kuma yakin ya
rincabe fiye da yadda ake zato ya zamana cewa
shi sarkin yaki ya rude ya manta damu da gimbiya
gaba daya fa?"
Ai wani lokacin sai anyi kundunbala sannan ake
samun abinda zaifi, ina ganin fa ya kamata ka
leka cikin keken dokin nan domin mu san halin da
gimbiya lazima ke ciki don tun dazu da ta leko
waje a karo na uku bata sake lekowa ba.
Mataimakin huzen yace maganarka gaskiya ce,
nan take ya yaye labulen keken dokin ya leka,
Ai kuwa sai yaga gimbiya a kishingide alamar tana
barci.
Cikin tsananin mamaki ya juyo da baya da kansa
da sauri ya dubi Badakaren yace ai barci take yi.
Koda jin haka sai gaba dayan dakarun dake gadin
keken dokin suka zazzaro idanu,
Badakaren ya dubi mataimakin huzen yace, ta
yaya gimbiya zata iya yin barci alhalin muna cikin
wannan mugun tashin hankali na yaki,
Daga nan ma tana jiyo ihun mazaje da karar
haduwar makamai? " MAZA SUN FADI!!! LITTAFI NA 3 PART 5

Koda jin haka sai gaba dayan dakarun dake gadin
keken dokin suka zazzaro idanu,
Badakaren ya dubi mataimakin huzen yace, ta
yaya gimbiya zata iya yin barci alhalin muna cikin
wannan mugun tashin hankali na yaki,
Daga nan ma tana jiyo ihun mazaje da karar
haduwar makamai? "
Sa'adda mataimakin huzen yaji wannan tambaya
sai ya gyada kai yace ai kasan wani lokacin
tashin hankali yakansa mutum yasha maganin da
barci zai daukeshi don kada razana tasa ya fada
cikin wani mugun hali
Koda jin wannan batu sai hankalin kowa ya
kwanta
Akayi tsit babu wanda ya kara yin magana ko
cewa wani abu.
Al'amarin gimbiya lazima kuwa lokacin da ta
durfafi cikin sansanin yaki a cikin shigar sadauki
Huzen sai ta zare takobinta taci gaba da falfala
gudu har ta iso inda ake yakin.
Koda ta iso da nufin ta tsaya a gefe daya tayi
kallo kuma ta rubutasu abinda take gani sai ta
kasa domin hankalinta ne ya dugunzuma ainun
bisa ganin yadda ake ta ragargazar dakarun
sarkinta duk da cewa kuwa suma suna kashe
abokan gabar ta hanyar amfani da sababbin
dabarun yaki da kalmaru ya koya musu,
Babu abinda ya firgita gimbiya lazima face ganin
tsananin yawan abokan gabar tasu akan nasu
dakarun.
Gashi dai kashesu akeyi amma kamar matattun
nasu ne suke kara tasowa,
Koda ganin wannan al'amari sai zuciyar gimbiya
lazima ta kama tafarfasa,
Take taji dukkan tsoro ya kau daga cikin
Zuciyarta,
Ta tuna cewa itama fa tun tana yarinya karama
mahaifinta sarki Barham
Ya koya mata yaki a sirrance ba tareda kowa ya
sani ba har izuwa girmanta amma dai bata taba
jarraba hazakarta da kokarinta kuma bata taba
halarta yaki ba sai wannan karon.
Nan take taji kishin al'ummata ya kamata kawai
sai ta kutsa da karfin tsiya izuwa cikin
turmutsutsun yakin ta hau dakaru da sara da
suka.
Nan da nan ta rinka dauka rai kai kace dama can
tsohuwar jaruma ce wadda ta saba gurmuzu a filin
fama,
Ita kanta sai mamaki ya turnuke ta bisa ganin irin
tsananin zafin namanta da jarumtakarta saboda
ganin yadda take tarwatsa abokan gabar da karfin
damtsenta tana gididdibasu da ratsawa ta
tsakiyarsu tamkar tana sassabe a gona,
Koda dakaru suka ga Huzen ya shigo cikin filin
daga anci gaba da yaki da shi sai suka cika da
tsananin tsoro gamida mamaki saboda zaton ko
an kaiwa gimbiya lazima hari ne a can inda take
amma kuma da suka ga jarumtakar huzen ta wuce
yadda suka santa sai kansu ya kulle don haka sai
ya zamo tamkar ya kara musu kwarin gwiwa ne,
Suma sai suka kara zage damtse,
Haka dai gimbiya lazima taci gaba da kutsawa
cikin sansanin yakin har ta iso tsakiyar yazamana
cewa itama gaba daya cikinta ya rine da jini, su
kansu abokan gabar da suka ga sabon mayaki
daga cikin dakarun birnin zamar ya shigo cikin
wannan sansanin yana ta ragargazar jama'arsu
sai suka firgita suka rinka yi masa rubdugu amma
duk a banza domin bankesu yake yi yana ci gaba
da ragargazarsu, kai kace wutace ta kama
karmami,
Kai da yawa daga cikin dakarun ma cewa sukayi
wannan ba mutum bane, aljani ne kawai yayi
basaja
A can bangaren sarki Daryan da sarkin yaki
kalmaru kuwa al'amarin ya sake muni domin sun
sake yiwa junansu rauni guda bakwai bakwai, jini
dake zuba a jikinsu yafi na da har takai cewa jiri
na dibansu amma saboda bakin nacinsu sun ki
faduwa kasa babu abinda zai baiwa mutum
mamaki face yadda karfin damtsensu da iya
yakinsu yazo kunnen doki kai kace 'yan biyu ne su
a komai.
Shi dai sarki Daryan yana yin wannan yaki ne da
dukkan karfinsa da zuciyarsa don ganin ya dauki
fansar ran mahaifinsa saumir don haka yana
kaiwa kalmaru hari yana ihu da kururuwa bai fasa
ba,
Shi kuma kalmaru yana kare kansa gamida maida
martani,
Saboda tsananin bakin ciki dake ran sarki Daryan
sai ya zamana cewa taurin ransa yafi na kalmaru
don haka sai yaci gaba da Kaiwa kalmaru
mahaukacin hare-hare ba sassauci
Kafin kalmaru ya kai masa hari daya shi ya kai
masa uku.
Nan da nan ya kuntata kalmaru har ta kai cewa
da kyar kalmaru ke iya tare hare-haren nasa kai
har ta ma kai cewa karfin saran Daryan da
Nauyinsa suna sawa kalmaru na durkushewa kasa
amma saboda juriyarsa da

1 Comments On MAZA SUN FADI 1 to 4
avatar
abubakar-abdullahi-6

10 months ago

Reply

yes

Please Login or Register in order to submit comment