Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ridwan fiye
da dukkanmu?"
Sa'adda mahaifinmu da Ridwan suka ji wannan
tambaya sai hankalinsu ya dugunzuma ainun,
a lokaci guda duk su biyun idanunsu suka ciko da
kwallah har hawaye ya zubo masu.
Mahaifin namu ya dubeni kamar zai fashe da
kuka yace,
Kafin na baku amsar tambayarku nima zanyi
muku wadansu tambayoyi guda ukku rak.
Tambaya ta farko itace,
acikinku nan ku arba'in da biyu waye ya taba
jinyata ta tsawon kwana ukku rak a duk sa'adda
na kwanta rashin lfy ko kuma na sami babban
rauni a daji wajen yin farauta? "
Dajin wannan tambaya sai mu duka muka sunkui
da kawunanmu kasa aka rasa wanda zai ce kala.
Mahaifin namu yace,
ga Ridwan shine kankanin cikinku amma wasu
shekarun baya sa'adda na fafata kazamin yaki da
wani sihirtaccen zaki na sami rauni mai yawa a
jikina sai da ya shekara ukku yana jinyata.
Dare da rana yana tare da ni
Baya gusawa daga kusa dani
Ko tari yaji nayi sai ya tambayeni ko inada
bukatar wani abu
A wannan lokaci sai da raunikan jikina suka
zamo gyambo suka rinka wari
Gaba dayanku
Ku ka daina shigowa turakata don kada wannan
wari da nake yi ya cutar daku,
Shi kuwa ridwan a cikin warin yake kwana da
yini.
Haka zan turashi daji ya tafi neman saiwoyin
bishiyoyin da zai hada mini magunguna.
A tafarkin hakan ne ya rinka shiga garari da
masifu iri-iri amma dai-dai da rana daya bai taba
tsorata ba ko gajiyawa ba
Sai da yaga na sami lfy na warke sumul a cikin
wadannan shekaru ukku.
Tambaya ta biyu a gareku itace,
" Acikinku wanene ya taba sallama rayuwarsa
don ceto tawa?
Duk sa'adda na shiga daji farauta tare daku da
zarar kunga wata muguwar dabba wacce zata iya
hallakani duk sai ku gudu
Ku barni
Shi kuwa Ridwan bai taba guduwa ba
Akwai rana da na fafata da wani katon gwaggon
biri mai tsantsanin karfin tsiya, kuma wanda
sihirin tsafi baya tasiri akansa.
Koda Ridwan yaga birin yayi mini wawan duka na
zube kasa magashiyan kuma birin ya yunkura zai
hallakani
Sai ya kwarara uban IHU ya fito daga inda yake
boye.
Koda birin yayi arba da Ridwan sai ya fasa
hallakani ya nupi inda yake,
A lokacin ne Ridwan ya kalleni yana mai zubda
hawaye
Mai nuna alamar bankwana kuma yayi mini
inkiyar na tashi na gudu domin na tserar da
rayuwata,
Kawai sai gani nayi Ridwan ya durkusa a gaban
wannan birin yana jira kawai ya kashe shi.
Cikin tsananin fusata na mike tsaye zumbur!
Na kwarara uban ihu mai firgita maza
Ai kuwa sai birin ya juyo gareni ya falfalo da
gudu
Nima sai na falfala da gudun tsiya izuwa gareshi
Muna haduwa muka ruguntsume da azababben
yaki na ganan kwatance,
A wannan lokaci yaki nake da dukkan raina da
jikina
Kona mutu
Kona rayu
Bisa mamaki wannan karon sai naga na sami
azababben zafin nama don haka sai na rikirkita
birin
Yazamana cewa baya ma iya kawo mini harin sai
kokarin kare kansa yake kawai
Gashi dai ina saran sassan jikin birin
Amma
Takobin bata yi masa lahanin komai saboda
karfin sihirin dake jikinsa,
A hakan ne kuma birin ya rinka samun damar
kawo mini mugayen
Hare-hare ina kaucewa
Ina cikin wannan gurmuzu ne da birin kawai sai
naga Ridwan ya falfalo da gudun tsiya izuwa kan
birin
Yana zuwa daf dashi sai ya daka tsalle sama ya
sokawa birin wuka a tsakiyar kansa.
Ai kuwa sai wukar ta nutse izuwa cikin kan birin
Jini ya kama tsiri a sama
A dai-dai lokaci Ridwan ya duro kasa bisa
kafafunsa
Nan take birin ya kama ma-ta gungun daga tsaye
yana ruri da kururuwa.
Daga can kuma sai ya sulale kasa matacce.
Lokacin da mahaifin namu yaxo nan a labarinsa
sai gaba dayan mu kunya ta kama mu
Muka sunkui da kawunanmu kasa
Shi kuma Ridwan sai ya kama kuka yana mai
Cewa,
Ya kai Abbana ka daina fadin wadannan
kalamai."

MAZA SUN FADI!!! Part 9

Lokacin da mahaifin namu yaxo nan a labarinsa
sai gaba dayan mu kunya ta kama mu
Muka sunkui da kawunanmu kasa
Shikuma Ridwan sai ya kama kuka yana mai
Cewa,
Yai kai Abbana
Ka daina fadin wadannan kalamai.
Mahaifin namu ya sake
Duban mu duka yace,
"ya kai Ridwan ka kyale ni
na fadi bakin ciki dake Zuciyata
Domin idan ban amayar dashi ba
Zai iya cutar dani
Tambaya ta ukku wadda itace ta karshe A
gareku.
A cikinku ku arba'in da biyun nan waye in
hanashi da barin abu yake bari ko kuma in na
umurceshi da yayi yake yi?"
Mu duka sai muka sake sunkui da kawunanmu
kasa
Aka rasa wanda zai ce kala.
Kawai sai ya kamo Ridwan ya rungumeshi a
kirjinsa a lokacin da hawaye ya zubo masa yace,
"Tunda Ridwan ya taso bai taba ketare umurnina
ba.
Komai tsananin son da yake yiwa abu indai nace
ya barshi, ya bar abin nan
Har abada.
Saboda me zaku ga laifina akan na kaunaci
Ridwan fiye daku na fifitashi? "
Inaso ku sani cewa duk irin kiyayyar da kuke
nunawa Ridwan na santa
Kuma kunsha kokarin hallakashi amma bakwa
samun nasara.
To ku sani cewa daga nan har mutuwarku baza
ku iya cutar da Ridwan ba
Domin na kareshi da dukkan Sirrinkan tsafina.
Daga wannan rana mahaifinmu yaci gaba da
fifita Ridwan akanmu
Mu kuma bamu daina nuna kiyayyarmu a gareshi.
Abinda ya hana sarki ya baiwa mahaifinmu
sarautar sarkin yaki shine,
Sarkin yaki na wannan lokaci dan uwan sarki ne
na jini domin yan maza zur
suke.
Amma duk da haka sai sarki ya yiwa mahaifin
namu alkawarin cewar indai sarkin yaki ya tsufa
ko ya mutu shi zai baiwa sarauta.
Idan kuma baya raye a sannan to zai baiwa
dansa Ridwan.
Lokacin da muka sami labarin wannan alkawari
wanda sarki Yayiwa mahaifinmu sai muka kamu
da tsananin bakin ciki muka sake daura damarar
ganin bayan Ridwan.
Wannan shine Asalin gabarmu da Ridwan,
Kuma gashi har yanzu mun kasa ganin bayansa.
Amma abinda nakeson ka fahimta ya kai dana
shine,
Komai rintsi da tsanani sai na tabbatarda cewa,
Wannan kujera ta sarkin yaki ta dawo hannunmu.
Koda jin wannan batu sai Hamsaru yai ajiyar
zuciya yace,
" ya kai Abbana kayi sani cewa Nayarda da
kwarewarka gamida tuggunka
Amma inaso ka sani cewa,
Muna cikin tsaka mai wuya akan burinmu
Domin idan har boka hizainu yace,
Babu tsafi a cikin nasarar da kalmaru ya samu
Yanzu shikenan fa munyi asara.
Kuma sai ka tafi kurkuku tsawon wata shidda.
Koda jin wannan batu sai yunaru ya bushe da
dariya yace,
Sau nawa zangaya maka cewa,
"kada mage ba yankawa bane?"
Ko ina tsare a kurkuku kuma koda kalmaru ya
hau kan wannan kujera sai nasan hanyar da nabi
na rabashi da kujerar. "
Acan bangaren sarkin yaki Ridwan da dansa
kalmaru kuwa,
Suma sun kebe gefe daya kusa da karagar sarki
sun zauna suna tattaunawa.
Sarkin yaki ya dubi dansa kalmaru a lokacin da
idanunsa suka ciko da kwallah yace,
"ya kai dana yanzu wane mataki ya kamata mu
dauka akan baiwa Zulaima?
Tabbas taci amanarmu domin na fahimci cewar
dan uwana YUNARU ne ya hada baki da ita ta
zuba maka sinadarin kashe jiki acikin ruwan
inibin da kasha
Wanda ya cire maka kuzari ya saka maka
tsananin kasala domin Hamsaru ya samu nasara
akan ka.
Ina ganin kawai mu kasheta."
Koda jin haka sai kalmaru ya zazzaro idanu ya
dubi sarkin yaki Ridwan cikin alamun tsananin
tsoro yace,
Haba ya Abbana ka tsaya fa kayi tunani, aduk iya
tsawon shekarun da kayi da Zulaima bata taba
ha'intarka ba ko cin amanarka ba.
Ni kam ina ganin cewa abinda zai sa taci
amanarmu ba karami bane
Abune wanda yafi karfinta
Ni yanzu ma hankalina a tashe yake domin bamu
san a irin halin da take ciki ba.
Don na tabbatarda cewa tana cikin tsananin
damuwa bisa abinda ta akanta. Kayi mini iznin
na koma gida dan na ganota."
Sarkin yaki Ridwan yace,
To idan kuma ka tafi su waziri suka dawo fa
yanzu
Ya zamana cewa gaskiyar mu ta tabbata sarki
zai baka takobin zinare? "
Ai kaga idan baka nan sarki da jama'a baza su ji
dadi ba.
Ni ya kamata na koma gida domin naga halin da
Zulaima ke ciki.
Idan sarki ya nemeni ka gaya masa cewa zan
dawo nan bada jimawa ba."
Koda gama fadin hakan sai sarkin yaki Ridwan
ya mike ya kutsa ta cikn taron jama'a ya fice
daga cikin fadar gaba daya.
SHIN WACE IRIN AMSA BOKA HIZAINU ZAI
BAYAR?"
SHIN TSAKANIN KALMARU DA HAMSARU WAYE
YAKE ZAMA SARKIN YAKI BIRNIN ZAMAR
KUWA? "
Mu hadu a maza sun fadi kashi na biyu don jin
cigaba...
MAZA SUN FADI!!! LITTAFI NA 2 PART 1

Al'amarin su waziri kuwa saida suka shafe Sa'a
guda cur!
Suna tafiya akan dawakai sannan suka iso bayan
gari inda gidan boka hizainu yake.
Da isowarsu kofar gidan sai suka iske wani
hadimin boka hizainu tsaye a kofar gidan wanda
ya kasance gajeren mutum mai dogon gemu
tamkar wada
Amma ba wada bane
Yana da manyan idanu masu dauke da gashin gira
mai kauri.
Ko kadan babu alamar annuri akan fuskar
mutumin.
Ga wadanda suka san tarihin wannan mutum
Ance ba'a taba ganin dariyarsa ba ko
murmushinsa.
Har ma mutane suna yi masa lakabi da wakilin
bakin ciki.
Nan take wakilin boka hizainu ya risina ya gaishe
dasu waziri cikin girmamawa kuma yai musu
barka da zuwa.
Waziri ya dubi hadimin yace,
"ya kai zunnaru maza kaje ka gayawa maigidanka
cewa sarki ya aikiomu bisa wani sako na
musamman wanda yake bukatar amsarsa yanzu-
yanzu"
Koda da jin wannan batu sai zunnaru yace, ya
shugabana ai tuni maigidana yasan da zuwan ku
kuma yasan sakon da kuke dauke dashi har ya
gayamini na shaida muku cewa lallai kalmaru ya
lashe wannan gasa babu sihiri.
Kuma yace a gayawa sarki ya tabbatarda cewa an
baiwa kalmaru takobin zinare
Idan kuwa akayi kuskure aka baiwa waninsa birnin
zamar zai fuskanci annoba da masifu iri-iri.
Koda jin wannan batu sai waziri da sauran
wadannan yan majalisa mutum ukku suka kama
kallon junansu suna muzurai.
Kawai sai waziri ya dubi zunnaru ya daka masa
tsawa yace,
"shin baka ganin cewa wannan aike da sarki yayi
mana sako ne mai muhimmanci wanda ya kamata
ace munji amsarsa daga bakin boka hizainu da
kansa?"
Ta yaya kake tsammani sarki zai yarda da mu
idan muka ce kaine ka sanar damu wannan batu?
"
Har zunnaru ya budi baki zaice wani abu sai
kawai suka ga boka hizainu ya bayyana tsulum a
gabansu fuskarsa cike da alamun damuwa.
Kawai sai ya dubi waziri yace,
"Abinda bawanmu zunnaru ya fada muku gaskiya
ne
Lallai ku isar da wannan sakon dana gaya muku
dai-dai idan kuka kuskura kuka fadi wani abu
sabanin nawa zancen
Karshen wannan birnin namu yazo, domin duk
wani babba walau basarake ko attajiri sai ya
mutu "
Boka hizainu na gama fadin hakan sai ya bace
bat daga wajen tamkar bai taba wanzuwa ba a
wajen.
Koda faruwar hakan sai daya daga cikin yan
majalisar yaja waziri gefe daya suka kebe yadda
babu wanda zaiji abinda zasu tattauna.
Dan majalisar mai suna Raziyan ya dubi waziri
yace, ya shugabana yanzu yaya zamuyi kenan "
Kasan yadda muka rabu da attajiri yunaru ya
bamu dukiya mai dimbin yawa domin mu murda
wannan al'amari domin tabbatar da dansa
Hamsaru akan wannan matsayi,
Gashi kuma boka hizainu yace idan ba'a baiwa
kalmaru kujerar sarkin yaki ba manya da yawa
zasu mutu a garin nan.
Shin menene mafita akan wannan al'amari? "
Waziri yai ajiyar zuciya cikin sanyin jiki yace, ai
sawun giwa ya take na rakumi.
Dole ne mu kawar da bukatar attajiri yunaru gefe
daya don ba zamu yarda wake daya ya bata gari
ba"
Koda gama fadin hakan sai waziri ya kada
linzamin dokinsa ya juya da baya.
Cikin hanzari Raziyan da sauran abokan tafiyarsu
suka zaburi dawakansu suka rufa masa baya.
*****
Lokacin da sarkin yaki Ridwan ya sulale ya bar
filin fadar yaje ya hau dokinsa ya zubureshi da
gudu ya nufi gida.
Yana isowa cikin harabar gidan sai hadimin dake
kula da barga dawakai ya rugo da gudu ya rike
masa ya sauka.
Sarkin yaki Ridwan na sauka sai ya dubi hadimin
yace, shin kaga motsin Zulaima kuwa a gidan
nan?"
Hadimin ya risina yace, ya shugabana tunda kuka
fita kaida kalmaru ko motsin Zulaima a yau ban
jiyo ba daga cikin gida kamar yadda ta saba a
kullum. "
Koda jin haka sai hankalin sarkin yaki Ridwan ya
dugunzuma ya ruga da gudu izuwa cikin gidan ya
wuce kai tsaye izuwa turakar Zulaima.
Da zuwa sai ya taba kofar dakin yajita rufe daga
ciki.
A dimauce ya kama kwankwasa kofar yana
kwalawa Zulaima kira, amma sai yaji shiru bata
amsa ba,
kuma bata bude ba.
Sarkin yaki ya zagaya bayan dakin ya leka ta taga
don yaga abinda ke faruwa
Kwatsam! Sai ya hango Zulaima ta daura igiya a
jikin rufin dakin wacce zata rataye kanta tana
kokarin taka wata kujera ta zarga igiyar.
Koda tayi arba da sarkin yaki yana lekenta ta cikin
tagar sai hawaye ya zubo mata tayi masa kallon
karshe.
Sarkin yaki na ganin haka sai ya daka mata tsawa
yace, waye ya baki iznin ki kashe kanki alhalin
kina matsayin baiwata?"
Dajin haka sai hawaye ya sake zubowa Zulaima
tace,
Ka gafarceni ya shugabana ka tuna cewa ka dade
da yantani ni ba baiwarka bace, kawai dai ina
zaune tare da kai ne sbd kauna da shakuwa.
Abinda yasa na yanke hukuncin kashe kaina shine,
banga amfanin rayuwata ba tunda na zama maci
amana na kawo karyewar darajar gidanan kuma
na dakushe ci gaban kalmaru
Ina mai neman gafararka data kalmaru bisa
wannan mummunan aiki dana aikata wanda nayi
shi bisa dole, saboda dan uwanka ne yunaru ya
gayamini cewa idan ban zubawa kalmaru
sinadarin kashe jiki ba a cikin abin shansa zai
kasheka.
Ni kuwa naga da na rasaka
gwara na rasa tawa rayuwar kuma na janyo
rushewar mulkin gidanan.
Tunda har na aikata wannan laifi babu wani
hukunci da zaifi dacewa dani samada mutuwa.
Koda gama fadin hakan sai Zulaima ta yunkura da
sauri ta taka wannan kujera ta mike tseye ta
kamo wannan igiya ta shake wuyanta ta fara
kakarin muruwa.
Cikin tsananin dimauta sarkin yaki ya ja da baya
ya rugo da gudun tsiya yasa kafa ya doki tagar
dakin da dukkan karfinsa da kafarsa.
Take tagar da ginin dakin suka burma ciki.
Sarkin yaki ya fada cikin dakin sannan ya daka
tsalle sama ya sare igiyar data daure wuyan
Zulaima da takobi ta rikito kasa bisa tafin
hannayensa a sume.
A guje sarkin yakin birnin ya fito da Zulaima
rungume a kirjinsa yana ihu yana kuka domin a
zatonsa ma ta mutu.
Yana isowa tsakar gidan sai ya shimfideta a kasa
ya kura mata idanu yana mai zubda hawaye kuma
yana sambatu.
Kwatsam! Ba zato ba tsammani sai yaga Zulaima
ta farfado tana mai yin tari cikin tsananin farinciki
sarkin yaki ya kamo Zulaima ya rungumeta a
kirjinsa ya sake fashe da kukan murna.
Daga can sai janye jikinsa daga cikin na Zulaima
suka fuskanci juna yace,
Yake Zulaima kiyi sani cewa rayuwarki tafi tawa
muhimmanci, tunda ni duk abinda nake nema a
duniya na samu kuma dana kalmaru bashi da wata
uwa a doron kasa wacce ta fiki.
Yaya kalmaru zai kasance idan yazo ya riski
gawarki?"
Kiyi sani cewa da farko nayi matukar bakin ciki
dana gane cewa kin zubawa kalmaru wani abu ya
sha a cikin abin shansa kuma har na yanke miki
hukuncin kisa bisa cin amanarmu, amma kuma sai
kalmaru ya bani shawarar kada na kasheki tunda
baki taba amanata ba a tsawon shekarun da kika
shafe tare dani.
Ki kwantarda hankalinki ki sani cewa burin dan
uwana yunaru ba zai taba cika ba.
Domin bazai iya kashe ni ba kuma ba zai iya hana
kalmaru karba takobin zinare ba.
Ina fatan nima zaki gafarceni bisa zargin dana yi
miki akan wannan laifi wanda bayin kanki bane"
Sarkin yaki Ridwan ya share hawayensa yace, ni
kaina a yau ne na gane cewa irin son da kike yi
mini ya wuce ma irin wanda nake yiwa kaina.
Yanzu ki tashi mu tafi izuwa fada domin ina son ki
gani da idanunki yadda danki kalmaru zai karbi
takobin zinare a hannun sarki.
Koda jin haka sai Zulaima ta mike cikin farin ciki,
ba tare da bata lokaci ba suka fice daga cikin
dakin.
Suna fita sarkin yaki Ridwan ya kira babban
hadimin gidan ya umurceshi da yaje ya kira
magini ya gyara dakin Zulaima.
Bayan nan sai suka je suka hau dawakai biyu
suka garzaya fada.
Acan fada kuwa mutane sun kagu dasu ga
dawowar su waziri domin a kawo karshen wannan
mahawara tsananin jarumi kalmaru da jarumi
Hamsaru a baiwa dayansu takobin zinare.
Shi kansa sarki Barham sai da ya gaji ya kosa da
jira duk da cewar ana debe masa kewa da kade-
kade da raye-raye
Kwatsam! Sai aka hango dawowar su waziri sun
durfafo filin fadar.
Nan take dakaru suka bude hanya mutane suka
dare,
Su waziri suka iso gaban sarki.
Nadeen
Da isowarsu sai suka risina ga sarki gaba dayansu
sannan waziri ya dago kai ya dubi sarki a lokacin
da fadar tayi tsit!
Tamkar babu wani mahaluki mai numfashi
acikinta saboda kowa so yake yaji bayanin da
waziri zai yi.
Attajiri yunaru da dansa Hamsaru kuwa sai suka
kama murmushin murna domin suna ganin cewa
dole ne ma bukatarsu ta biya tunda waziri nasu
ne.
Kuma shine ya jagoranci wannan karbo sako daga
wajen boka hizainu.
Waziri yayi gyaran murya sannan yace ya
shugabana mun karbo sakon ka ga boka hizainu
kuma ya gaya mana cewa nasara da kalmaru ya
samu a wannan gasa babu sihiri a cikinta.
Kuma yace Lallai ka damka takobin zinare ga
kalmaru idan kayi sabanin haka kuwa gaba dayan
masu mulkinmu da attajiranmu na kasar nan zasu
zama gawa.
Koda jin wannan batu sai fadar gaba daya ta rude
da shewa aka kama yiwa jarumi kalmaru jinjina.
Attajiri yunaru da dansa Hamsaru kuwa
Sai suka fashe da kukan bakin ciki.
Kawai sai yunaru ya kama hannun Hamsaru ya
janye shi suka fice daga filin fadar gaba daya.
Nan take sarki Barham ya cika da tsananin
farinciki ya mike tsaye aka miko takobin zinare ya
karbata da hannu biyu sannan ya mikawa
kalmaru.
Shima ya karba da hannu biyu.
Ai kuwa sai fadar ta sake rudewa da shewa har
sai da sarki ya daga hannu sannan akayi tsit!
Koda kalmaru ya juyo da baya ya fuskanci jama'a
dake filin fadar sai hango mahaifinsa sarkin yaki
Ridwan tare da Zulaima tsaye acan gefe daya sun
zubo masa idanu suna ta murmushin farinciki bisa
ganin takobin zinare a hannunsa.
Take kalmaru ya sake kamuwa da tsananin
farinciki mara misaltuwa musamman da yaga
Zulaima a raye cikin koshin lfy.
Sarki Barham ya dubi jama'a yace,
Ya ku al'ummata kuyi sani cewa daga yau
kalmaru ya gaji mahaifinsa ya zama sarkin yakin
kasar nan na saba'in da bakwai.
Ina fatan gaba dayan mu zamu bashi goyan baya
da dukkan taimako domin ya sami damar gudanar
da aikinsa kamar yadda ya kamata.
Kuma saboda taya kalmaru murna wannan
matsayi da yasamu zansa a shirya gagarumar
walima anan fadata har tsawon kwana ukku "
Nan take mawaka, makada da maroka suka shigo
cikin fili fadar suka fara baje kolinsu.
Sarakai da attajirai kuwa suka kama likin dinare
da dirhami ana nuna farinciki ana bushasha.
Kamar yadda sarki Barham yayi alkwari haka
al'amarin ua kasance,
Wato sai da aka kwana ukku anyin walima a fada
irin wacce ba a taba yiba a kasar domin sai da
abinci da abinsha suka wadata har ya zama
almubazzaranci.
Sarki Barham yanada wata 'ya budurwa guda
daya mai suna LAZIMA Lazima ta kasance daban
acikin mutane, Domin ra'ayinta da yanayin
rayuwata ya fita dabam da na sauran mutane,
tamkar ma bata kasance bil'adama ba. MAZA SUN FADI!!! LITTAFI NA 2 PART 2

Sarki Barham yanada wata kyakkyawar 'ya
budurwa guda daya mai suna LAZIMA.
Lazima ta kasance daban a cikin mutane, domin
ra'ayinta da yanayin rayuwata ya fita dabam da
na sauran mutane, tamkar ma bata kasance
bil'adama ba.
Dalili kuwa shine, duk irin abinda mutane suka
sabayi, to fa ita sai tayi nata dabam.
Abu na farko, tunda ta taso daga kurciyarta zuwa
girmanta bata taba cin abinci sau uku a rana ba.
Kullum sau daya take cin abinci da hantsi,
Kuma bata cin abinci mai nauyi sossai daga ganye
sai zuma da nono sai kuma naman tsuntsaye,
Bata cin naman rago ko na akuya bare na rakumi
da sauran manyan dabobbi.
Idan taci wannan abinci da hantsi, to fa ba zata
sake cin komai ba har dare sai ruwan shayi kawai
ko ruwan inibi.
Kuma kullum kara lafiya take, jikinta yana yin
kyau tamkar na jaririya.
Abu na biyu shine, kullum bata da aiki sai karanta
littattafai iri-iri na adddinai dana tarihin masarautu
da jaruman duniya.
Sai lazima ta yini tana karatu da nazari, sai idan
ta gaji sannan take dan yawatawa a cikin gidan
sarautar ta mike kafafunta,
Kuma ta shiga cikin lambun sarki ta zauna tana
hutawa, tana kallon furanni da tsuntsaye.
Tunda aka haifi lazima bata taba fita ba daga
cikin harabar gidan sarautar, bisa wannan dalili ne
mutane da yawa a kasar basu santa ba sai
labarinta kawai suke ji.
Idan har mutum bai zamo babba ba cikin masu
sarautar birnin ba, to bai isa yaje inda ma zai ga
gimbiya lazima ba.
A ranar da za'a ayi walima karshe ta bikin
sarautar kalmaru ta sarkin yaki gimbiya lazima na
zaune a cikin turakarta tana nazarin wani littafi na
tarihi sai taga kuyanginta gaba daya sun ci ado
sunzo gabanta sun durkasa.
Kawai sai shugabarsu ta dubi gimbiya lazima tace,
Ya shugabata muna neman izini a wajenki ki
amince mana muje mu halarci walimar karshe da
za'a yi yau ta murna bikin nadin sarautar sarkin
yaki. "
Koda jin wannan batu sai idanun Gimbiya lazima
suka zazzaro ta dubesu tace,
Yanzu ashe har an nada sabon sarkin yaki a garin
nan amma baku bani labari ba?"
Shugabar kuyangin ta sukui da kanta kasa tace,
"ya shugabana ai kinsan cewa kin hanemu gaba
daya da gaya miki abinda ya shafi harkokin
sarauta shiyasa bamu sanar dake ba.
Lazima ta gyada kai tace,
Acikin jerin sarakan yaki na kasar nan wannan
shine na nawa?"
Shugabar kunyangin tace, naji sarki yana cewa
kalmaru shine na saba'in da bakwai. "
Koda jin haka sai gimbiya lazima ta mike tseye
zumbur! Cikin tsananin farinciki tace,
Ku shirya mini fita izuwa fada. Lallai inason na
gana da wannan sabon sarkin yaki.
Koda jin wannan batu sai gaba daya kuyangin
suka tsaya suna noke-noke
Cikin fushi gimbiya lazima ta daka musu tsawa
tace,wai shin ba kwa ji nane, maza ku tashi kuje
ku shirya mini fita zuwa fada.
Cikin hanzari kuyangin suka mike tsaye suka je
suka fara shirye-shiryen tafiya.
Ita kuwa gimbiya lazima sai ta shiga cikin
turakarta ta cabo ado na kure adaka.
A can filin fadar kuwa, a yau mutane sunfi cika
fiye da kullum saboda yau ne rana ta karshe a
bikin sarautar, don haka duk inda mutum ya duba
sai dai yaga mutane fulufulu babu masakar tsinke.
Sarki Barham tare da yan majalisarsa na zaune
acan sama bisa wani gini mai tudu.
A hannun daman sarkin yaki kalmaru ne, a hannun
hagunsa kuwa sarkin yaki ne na da, wato Ridwan
mahaifin kalmaru.
Waziri da mukarrabansa na gefe daya suna
surutunsu na gulma.
A wannan lokaci ana ta raye-raye da kade-kade a
tsakiyar fadar don debewa mutane kewa, manyan
baki suna ta shaye-shayensu suna kyalkyala
dariya.
A kusa da sarkin yaki kalmaru baiwa Zulaima ce
itama ta caba ado saboda farinciki har idanunta
na cika da kwalla saboda murna.
Kwatsam! Sai akaji an buga tambari alamar cewa
wani babban mutum zai fito daga cikin gidan
sarautar.
Al'amarin da yai matukar baiwa kowa mamaki
kenan sbd an san cewa in banda sarki babu
wanda ake bugawa wannan tambari, tunda shi
kadai ne yake fitowa daga gidan sarautar.
Shi kansa sarki Barham sai ya bude idanu yana
kallon kofar gidan sarautar domin yaga wanda zai
fito.
Ba zato ba tsammani sai sarki yaga ashe gimbiya
lazima ce ta fito, kuyangi da dakaru na take mata
baya, ta caba ado na gaban kwatance, tana taku
dai-dai tamkar toron dawisu.
Wohoho! Nan fa gaba dayan jama'ar dake filin
fadar suka kura mata idanu akayi tsit! Tamkar
mutuwa ta kawo ziyara.
In banda sautin sawun gimbiya da na masu take
mata baya babu abinda kunne keji,
Saboda ganin tsananin kyawun gimbiya lazima,
Mutane da yawa basu san sa'adda suka wangame
baki ba suna dalalar da yawu tamkar
mayunwaciyar kura ta ga nama.
Wasu mutane kuwa sai suka dimauce suka kama
sumbatu.
Shi kuwa sarki Barham bai sa'adda ya mike tsaye
ba daga kan karagarsa yaje ya tari gimbiya a
lokacin da itada kalmaru suka kurawa juna idanu
ko kiftawa basa yi duk da cewa basu san juna ba.
Bata san cewa shine sarkin yaki ba, sai bisa ganin
takobin zinare a hannunsa.
Shima kuma labarinta kawai yake ji a gari, amma
bai taba ganinta ba.
Koda sarki ya tari gimbiya lazima sai ya dubeta
cikin matukar mamaki yace,
Yake 'yata menene ya fito dake wajen gidan
sarauta, alhalin baki taba fitowa ba?"
Hakika kin rugaza mini shirina domin banso
jama'a suka ganki ba a yanzu,
So nayi sai a ranar da zan gabatar da gasar
neman aurenki sannan zan bayyanaki kowa yaga
wannan tsananin kyawun naki.
Koda jin wannan batu sai gimbiya lazima tayi
murmushi tace , "ya kai Abbana kayi sani cewa a
cikin Karance-karance na da kuma bincikena a
littattafai na tarihi wadanda masana da matsafa
suka yi hasashe naga cewar wannan nahiya za'a
sami wani sarkin yaki wanda zaiyi gagarumar
jarumtakar da ba'a taba yin kamarta ba,
Kuma zai auri yar sarkinsa.
Bincikena ya nuna cewa wannan sarkin yaki shine
na saba'in da bakwai a cikin jerin sarakan yakin
kasarsa, kuma zai fito ne daga birnin da babu
kamarsa a girman kasa da karfin arziki.
Ya Abbana wannan sarkin yaki da ka nada tabbas
ance shine na saba'in da bakwai, sannan kuma ka
sani cewa a gaba daya nahiyar nan babu wata
kasa mai girman tamu da karfin arzikinmu.
Idan har hakane kuwa ashe wannan sarkin yaki
daka nada shine zai zamo mijina.
Kaga ashe banyi laifi ba don na fito domin naga
mijin da zan aura."
Lokacin da gimbiya lazima tazo nan a jawabinta
sai sarki Barham ya cika da tsananin mamaki
kuma hankalinsa ya dugunzuma ainun ya dubi
gaba daya kuyangin dake bayan gimbiya lazima
wadanda sunji duk abinda ta fadi yace,
Duk wanda ya furta wannan zance ga wani daga
cikinku a bakin ransa! "
Koda gama fadin hakan sai sarki ya dubi gimbiya
lazima yace,
Yake 'yata daga yau ki guntse bakinki domin idan
kika furta wannan zance 'yan majalisata suka ji
zai iya haifar da tashin hankali da fitina wacce
ba'a san karshenta ba.
Gama fadin hakan keda wuya sai sarki ya kama
hannun gimbiya lazima yajata izuwa inda
karagarsa take.
Har jarumi kalmaru ya mike tsaye zai baiwa
gimbiya lazima kujerarsa ta zauna sai ta dubeshi
cikin murmushi mai taushi tace,
"Yi zamanka ya kai mai kai maza kasa, dirkar
birnina.
Kawai sai gimbiya ta zauna a kujerar dake kusa
data kalmaru suka kama hira
Ta fara da yimasa barka da samun nasarar gasar
da akayi tsakaninsa da dan uwansa Hamsaru.
Koda jin haka sai kalmaru ya dubeta cikin mamaki
yace, dama kin san dan uwana Hamsaru? "
Lazima tayi murmushi sannan tace, dan uwanka
Hamsaru shine sarauyi na farko wanda ya tareni
gaba da gaba ya bayyana mini sirrin zuciyarsa
bisa yadda ta kamu da tsananin kaunata. Amma
kuma ni dai-dai da dakika daya ban taba jin
inasonsa ba.
Na sani cewa duk garin nan babu wani attajiri mai
yawan dukiyar mahaifinsa,
Hatta mahaifina kuwa sarki.
Gaba dayan sarakai da manyan kasar nan suna
shakkar attajiri yunaru kuma suna girmamashi,
sarki ne kawai baya shakkarsa amma yana
shakkar tuggunsa.
Kai kuwa ban taba ganinka

1 Comments On MAZA SUN FADI 1 to 4
avatar
abubakar-abdullahi-6

10 months ago

Reply

yes

Please Login or Register in order to submit comment