Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*ƊAN DABA*💞
```love and romantic story```


` ~``MRS SADAUKI~ ``` 💫

*Dedicated* to My Babbar Yaya Nafissa Laouali Rabo🥰

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀️

____________________
BISMILLAHI RAHAMANI RAHEEM
********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels



Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************

*FREE BOOK NE in kun yi comments shi zai sa na gane kun karɓe shi labarin ya maku kenan,ban buƙatar stickers ko tnx ban son su yadda na ɓata lokaci nayi maku typing ku bada time ɗinku kuma ku yi comments miye duniyar yi min in yi maka ne*🤷🏻‍♀️

Page 1-2


Yaf-yaf-yaf haka ruwan saman ke sauka a hankali yayinda mutane suka fara guduwa,wasu na tsayar da abun hawa wasu kuma na ɗaukar motocin su.
Ganin mutane na watsewa ne ya jawo hankalin Leemat ta waro ido lokacin da idonta yayi tozali da baƙin hadarin da ke wuluniya tare da gangamuwa,da ƙarfi ta furta "hadariii"zumbur Siya ta miƙe tana lalubar ƴar sandarta ta ƙarfe tare da fiddo ido waje cikin muryarta mai kama da ta yara tace "Leemat ki tsayar mana da abun hawa please kafin ruwan ya fara sauka"Leemat wacce ke bakin shagon ta ƙaraso ta kama sandar ƴar uwarta ta tace "ina wani abun hawa a nan tuni ƴan adaidaitu suka tsaya zo mu tafi ko Allah ya datar da mu a hanya"tana faɗin haka ne tare ɗaukar ledar kayan da suka saya.
Leemat na gaba Siya na biye da ita a baya yayinda ƙarfin ruwan ya ke ƙaruwa ahankali,sun yi nisa sosai amman shiru babu abun hawar da ke wucewa kasancewar dare ya tsala sosai ga kuma ga hadari shiyasa mutane suka yi zafin shigewa gida.
Kwalta suke bi suna yin direction ɗin da za ta sada su da gidan su har suka kawo rond-point gouvernorat tsit titin ya ke,kamar waƙiya haka Leemat ta ga giftawar mutum a gaban su cak ta ja ta tsaya har sai da Siya ta kawo mata karo.
"Miye kuma kika tsaya"Siya ta tambaya kafin ta kai ga bata amsa sai jin kukan kare suka "huhuhu🦮"yadda ya ke kukan ya ke tunkaro su shi ya fi komi ɗaga masu hankali,Siya wacce ba gani ta ke ba ta ƙanƙame Leemat tana mai jin wasu hawaye suna shirin zubo mata.Ba ta ida jingina da jikinta ba taji Leemat ta zuba da gudu a waje,ta ɗaga ƙafa da niyyar guduwa ta ji ta kaiwa wani ƙaton mutum karo ko kafin ta kai da tambayar wanene taji ya sungumeta yayinda kukan karen ke take masu baya alamun mai karen ne.
"Wayyo Leemat ki zo ki cece ni zai kashe ni"Siya ta faɗa kanta na ƙasa dan bisa kafaɗar shi ya ɗora ta, Leemat wacce tayi ɗan nisa ta tsinkayo murya Siya abun ka da ƴan uwantaka ta jini sai ta dawo baya tana kiran sunanta "Siya? Siya?Siya?"ko kafin ta ƙaraso ya hahe ƙaton babur ɗin shi routier 🏍️ ya danna mashi huta baƙin karen shi kuma na take mashi baya a guje.
Zaman ƴan bori Leemat tayi tana mai ɗora hannu a kai,daidai nan kuma wata adaidaita sahu ta hasketa shi ya taimake ta ya kaita gida.


Da isar su ya buɗe ƙofar gida ya shiga cikin ɗaki can tsakiyar gado ya cilla Siya,hasken ɗakin ya kunna tare da AC.Zumbur ta miƙe tace "wanene kai?mi nayi maka da za ka raba ni da ƴar uwata?"ko kallonta bai yi ba sai ƙarasawa ma yayi bakin mirror ya fara ɓalle buton ɗin rigar shi wacce ta jiƙe sharkaf da ruwa,faɗaɗen ƙirjin shi wanda ya ke da kwantacen gashi ya shafa kafin ya ɗaga duk hannuwan shi biyu sama hakan ya baiwa murɗaɗin muscules ɗin shi damar ƙara haɓaka.
Sai da ya ɗan jinjina su sannan ya riƙe ƙugu ya na kallon kyakkyawar fuskar shi mai ɗauke da saje da manyan ido,sai jajayen laɓan shi masu sheƙi murmurshi ya saki wanda ya baiwa dimple ɗin shi lotsawa.
Sautin murmurshin shi ne ya sa Siya saurin ɗagowa duk da ba ta gani amman taji inda sautin ya fito,tasowa tayi ta nufi gun tare da haɗe hannuwa waje guda alamun roƙo tace "dan Allah kar ka cutar da ni ka taimaka ka mayar da ni Mami na za ta shiga tashin hankali, please ni Makauniya ce fah"juyowa yayi ya na facing ta ya na kallo kyakkyawar Makauniyar fuskarta,jawota ta yi ya na mai furta "shuuut!ba sai kin gaya min ba na fi ki sanin ke ɗin Makauniya ce sannan ke karan kan ki ma dan haka kar ki yi ɓarnar bakin ki na fi ki sanin ke ɗin wacece"murya na ɗan rawa tace "wanene kai?mi nayi maka to da za ka kidnapping ɗina?"murmurshin da ya zame mashi jiki yayi yace "soyayya ce,I love You SIYAAA son ki ya sa haka"fizgewa tayi tace "ƙarya ce mai son ka ba zai taɓa cutar da kai ba"ya fizgota yace "ki rufe min baki in ba so kike na hukunta ki ba,ni age mate ɗin ki ne da za ki ce ina ƙarya"kwaratsin muryar shi ya firgitata ainun hakan yasa ta lafe a ƙirjin shi ta fashe da kuka,bayanta ya shiga bubugawa "yi shiru babyna nima ban so na tsorata ki ba,laifin ki ne ban son raini ko kaɗan"ya faɗi haka ya na mai ɗago fuskarta ya ɗora bakin shi kan tausasan lips ɗin ta.Har ga Allah ba ta son kissing ɗin ta da ya ke amman tsananin tsoron shi ya hanata yi mashi magana,gefen cikinta ya riƙe tayi saurin ja da baya tana mai ɗora hannuwanta akan ƙirjin shi da zumar ƙwace bakinta sai dai bai bata dama ba.
Sai da ya gaji dan kan shi ya ƙyaleta "ki cire kayan jikinki ki saka wasu kar mura ta kama ki"ya faɗa a wahalce,baki na ɗan rawa tace "ban iya ba"hijab ɗin ya kama zai cire mata tayi saurin riƙe shi gam tare da girgiza kai alamar ba ta so "babu abinda zan yi maki Siya juste canza maki kaya zan yi"yadda yayi maganar cikin taushi ya sa ta bar shi ya sauya mata kaya zuwa wata doguwar rigar barci mai nauyi.
Ac ɗakin ya rage lokacin da ya shimfiɗeta a bed, ya shiga ya watsa ruwa sannan ya shirya tsaf cikin kayan barci.Kamar wata matar shi haka ya haye gadon tare da ja masu blanket,wayar shi da ke bisa didilin gado ya ɗauka yayi ƴan danne-danne tare da karawa a kunne.
Jin ta na ta sonné ba'a ɗaga ba yasa shi sanya Hand free "Weeliam xava cmnt vas tu?"murya wata mata ta faɗa cike da fara'a dan ka na jin sautin murmurshin ta, "je vais bien Maman ya kike ina Miki?"ya faɗa ya na juyawa Siya baya.
Tayi dariya tace "ga ta nan kusa da ni tace na faɗa ma ka kawo mata mijinta tayi kewar shi" dariya Weeliam yayi yace "soon za ta ganin shi nima na samo tawa matar"cike da murna Maman tace "congratulations mn bb"yace "Merci à demain muaaah"ya faɗa ya na kashe wayar tare da juyawa ya jawo Siya wacce ke kwance lamo tana sauraren shi tare da juya sunan WEELIAM a ranta.
A tare suka sauke numfashi ya jaye pilow ɗin da ta aza kanta ya mata remplacer da hannun shi na dama yayinda ya zagaye na hagun kan ruwan cikinta.




Tas-tas haka Mami ta wanketa da mari tace "shirmen banza kenan da ya ɗauke ta miyasa ba ki bi bayan shi ba?to maza ki fice min daga gida duk gidan ubanda kika kaita sai kin fito da ita kuma ki gaggauta kafin labari ya isarwa ga Abban ku"Leemat ta ɗago da jajayen idonta ta kalli Mami tace "ina zan ganin shi Mami?ta yaya ma da hankalina zan bi bayan *ƊAN DABA* in Fab ya kashe ni"
"Da kashe ki ɗin yayi ai da ya fi sauƙi kan azabar da Abba zai jajaga maki"cewar Laila tana kuka,dariya Jasmine tayi tace "wai kuka ne za ki yi?tab ai ba zan ɓarnar hawayena ba dan kuwa duk wanda ya ji wannan zance ya san shiri ne ba gaskiya ba ne tunda sai da aka hanata fita da Siya amman ta nace kan za ta kula da ita sosai.To yanzu ki faɗa min miye sunan wannan shirin Film ɗin da kika tsara?ohoho wai ma in tambaye ki ya aka yi kika san da *ƊAN DABA* ne hhh yarinya tun wuri ki fito mana da antyn mu kafin mu wallafa maki littafi JIKI MAGAYI"Jasmine ta ƙarashe maganai ta na kimtse fuska da haɗe rai😡 alamar no mutunci.
Mami ta jinjina kai tare da gaskata maganar Jasmine kasancewar ta Barrister ce kuma ta na saurin gane zance....




*To ya a cigaba?*

#COMMENTS
#SHARE

Jikar Rabo ce 😎
*ƊAN DABA*
```love
and
romantic story

``` ~MRS SADAUK~ ```💫


*Dedicated* to My Babbar Yaya Nafissa Laouali Rabo🥰

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀️

____________________
BISMILLAHI RAHAMANI RAHEEM

Page 3-4

Ƙafafun Mami ta dafa tace "ki yarda da ni ba zan taɓa cutar da Siya ba,in da ina da niyyar yin haka da tun tuni nayi ba wai sai yanzu ba"kutufo Mami tayi da ita tare da nunata da yatsa tace "keee!ki shiga taitayin ki,ki tashi ki dawo da ita tun wuri kafin na kira Abban ku na shaida mashi"ta ida maganai ta na mai jan Leemat ƙiiii ta cillata waje ba tare da la'akari da ruwan saman da ake yi ba.
Tsamo-tsamo tayi kamar kazar da aka tsoma ruwan zafi haka Leemat ta miƙe kayanta duk sun jiƙe ta buɗe ƙaton get ɗin gidan.Ba ta san ina ta ke tsoma ƙafarta ba ita dai kawai tafiya ta ke yayinda ruwan sama sai ƙara yawaita suke,kamar daga sama ta fara ganin hasken fitilu na haske ta.
Cike da tsoro ta tsaya cak yayinda ta nemi kukan da ta ke ta rasa, marche arrière ta fara sai dai jin ta kai ma wani abu karo yasa ta fasa ihu tare juyawa suna facing.Wani garjejen ƙato ne baƙi ƙirin da shi fuskar shi sam babu alamun rahama amma duk da haka bai ɓoye ainahin kyawun shi ba,muƙut Leemat ta haɗe wasu yawu da za ta a iya kira na tsoro.Bai ce mata kanzil ba sai nuna mata mota da yayi babu muso ta shiga daidai nan sauran yaran nashi suka ƙaraso,umarni yayi masu da kowa ya zamana cikin shiri ba'a wani ɗauki lokaci ba sai ga wata mota irin uwanda suke ciko dare daga Nigeria.
Tun kafin su ƙaraso aka dalle motar da fitila yayinda wasu suka hahaƙa bindigogi,dolin draver ya tsaya jiki na ɓari duk illahirin mutanen suka fito.
Kuɗaɗe da abubuwan da suka sawo duk aka ƙwace sannan aka suka kwanta har sai da ƴan daban suka tsere sannan suka mimiƙe suna jera Allah ya isa.


Duk duhun motar bai hana ta ji a jikinta ana kallonta ba,face da shi ta waigo sai ta ga idon shi na kanta,tayi saurin yin ƙasa da kanta ta na share hawaye.
Wanda ke tuƙa motar ogan ne yace "ke Malama kar na sake jin kukan ki ko ba ki san da Boss mai kaca kike zaune a wuri ɗaya ba?zan ɓalla..."Boss ya katse shi da "Arneee!"ba Leemat da ke baƙuwar jin muryar shi ba hatta Arne da ke ɗan gaban goshin shi sai da ya firgita da tsawar da Ogan nashi ya daka mashi.
"Tuba ni ke Oga"cewar Arne ya na mai cigaba da sharara gudun shi,rakuɓewa Leemat ta ƙara yi sai dai abun mamaki sai ji tayi Boss ya ɗauke ta kwancakwakwam ya ɗora akan ciyoyin shi.
Hannun shi ya saka a hijab ɗin ta ya fara shafar sassan jikinta ya na sauke numfashi,jikin Leemat ne ya ɗau rawa jin ya na wasa da ƴan biyunta sai damƙar su ya ke kamar ya samu maƙiyan shi.Wani kukan baƙin ciki ne ya kubce mata ganin abun na shi sai ƙara yawa ya ke,dariya ƙeta Arne yayi a zuci yace "dama ai da ka ga kare na sunsunar takalme to ɗauka zai yi,yau karon farko Oga ya faɗa tarkon mace ke kam kin shiga uku na san da sauran ƙura a gaba sai ma mun isa masauki Oga ya juye tazurancin shi kan ki dama abun ka da ba'a taɓa yi ba ƙila ma ki tashi daga aiki hhh"bai san dariyar ta shi ta fito fili ba sai da yaji ƙafar Boss ta bugi kujerar da ya ke zaune.
A kasalance ya sake ta tayi saurin sauka daga kan cinyar shi tana ja mashi Allah ya isa a ƙasan zuciyar ta,"uban mi kake wa dariya?"Boss ya faɗa a dake Arne da ke danna horne mai gadi ya buɗe mashi get yace "a'a fah Boss ba da kai ni ke ba"shiru Boss yayi ya na jin haushin kwabsawar da yayi gaban yaron shi dan a kullum har faɗa ya ke masu mi suke ji da mace ne da har suke son kasancewa da mata?tare da yi masu tunƙawo shi bai ga macen da za ta jan ra'ayin shi ba balle har ya kai da jin sha'awar ta sai dai abun mamaki tunda ya ɗora idon shi kan Leemat ya fara jin ashe shi ma namiji ne.


Tamkar safiya haka gidan ya ke tsabar fitilun da aka saka a ko ina,gidan ya na da girma sosai tare da ɓangarori dayawa.Ko da suka yi parking kowa ficewa yayi yayinda wani matashin saurayi ya nufo ƙofar Boss buɗewa yayi ya na cewa "Barka da zuwa Boss har kun dawo?"gyaran murya kawai yayi,Maye ya kalli Leemat wacce ta fito ta tsaya "Oga wannan furen fah?"kallon shi Boss yayi ya ga yadda Maye ke haɗiyar yawu sai kace kare ya ga nama.
"Ta Boss ce wannan ka kawar da idon ka in ba marmarin makanta kake ba"cewar Arne da ya fito daga mota, murmurshin gefen baki Boss yayi har ƙasan ran shi ya ji daɗin yadda Arne ɗin ya tari numfashin Maye.
Tafiyar ƙasaita irin ta jaruman Mazan nan masu Izza Boss ya fara ya na dosar wani ɓangare mafi kyawu daga cikin duk ɓangarorin,Arne yayiwa Leemat alama da ta biyo shi tabi bayan shi yayinda suka bar maye da haɗiyar yawu😂.



Har cikin babban falon Arne yayi mata iso kafin ya fito,kalle-kalle ta fara ta na kallon yadda falon ya haɗu iya haɗuwa babu abinda babu har tv da ƴar ƙaramar frigo.
Gabanta ne ya ishi-ishi ya faɗi sakamakon ganin sangamemen ƙaton nan daga shi sai ɗan kanfe irin na maza gemun shi na ɗigar da ruwa alamun wanka yayi,dafe kai yayi yace "wai nan ya kawo ba ɓangaren mata ba?"da sauri ta sake ɗago kai ta kalle shi tace "wane ɓangaren mata kuma?"sai kuma tace "yi haƙuri"da alamu ba ta san tayi maganar ba.
Jin muryar ta yayi mugun tafiya da Boss har bai san lokacin da ya ƙaraso gun ta ba,ta ja da baya yayi murmurshi mai sauti yace "ki matso ki dawo inda kike tun farko ko na shayar da ke mamaki"yi tayi kamar ba taji abinda yace ba ai kuwa ya sungumeta ya nufi bedroom da ita,bai tsaya ko ina ba sai cikin toilet.
Tun daga sama har ƙasa ya yarɓe doguwar rigar atamfar jikinta,ta rumtse ido hawaye na shatata lokacin da ya mayar da ita zir haihuwar uwata.
Cikin cool voice yace "kar ki ji komi ƴan mata ki buɗe ido ki kalle ni domin kunyar maras kunya asara ce Boss da kunya tamkar hannun riga ne kin gane?am happy nima yau nayi gamo da abokiyar tarayyata"ya faɗa ya na mai jawota jikin shi tare da sakar masu shower ruwa na zuba a jikin su, numfashin ta har fizgewa ya ke tsabar yadda ruwan ke dukanta hakan yasa ta ɓoye fuskarta a ƙirjin shi.


Wata irin duniya ce Boss ya shiga sakamakon sabuwar rayuwar da ya tsinci kan shi a ciki ba tare da ya taɓa tunani ko tsammanin zuwanta ba.Ƙarfin ruwan ya rage ya maida su can ƙasa,ya ɗago haɓar ta ya na kallonta cikin ido ita ma shi ɗin ta ke kallo a tare zuciyoyinsu ke bugawa kowanensu kuma na saƙa abubuwa iri-iri a rai.
"Miyasa ya zaɓi yin ta'addanci kan wata sana'a?a yadda ya ke kyakkyawan nan sam yin fashi bai dace da rayuwar shi ba" Leɓenta na ƙasa ya sumbata ya saki har sai da ya ɗan bada sauti yace "ban yin kaina ba ne nima doli ta sani yin haka"tayi saurin sunne kai tare da jin tsoro ashe a fili tayi maganar ta zata a zuci ne.
Ɗagota yayi yace "please ina son sumba sosai ki bar ni nayi ta sumbatar ki dan hakan na burge ni,in yi?"sororo Leemat tayi tana kallon shi a zuciya kuwa cewa ta ke "ka ji ɗiyan iskanci yanzu da ka tuɓe ni tambayata kayi?"Boss yace "a'a ban tambaye ki ba amman wannan ina son ki bani izinin yi"tsabar tsoro yasa Leemat yin tari,ya tara hannun shi ruwa na zuba nan ya shiga bata har sai da tarin ya lafa yace "please in yi?"kai ta ɗaga mashi da sauri ya cabki leɓenta tare da tura halshen shi cikin bakinta.
Riƙe shi tayi jin ta fara jin daɗin abun hakan da tayi ya ƙara baiwa Boss dama juyata ya taɓa ta da bango ta jingina ya cigaba da kissing ɗin ta.......



*To yaya kun fara fahimta?labarin ɓangare biyu ne in kun yi comment yadda ya kamata sai mu ɗora*


Jikar Rabo ce 😎
*ƊAN DABA*
```love
and
romantic story

``` ~MRS SADAUK~ ```💫


*Dedicated* to My Babbar Yaya Nafissa Laouali Rabo🥰

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀️

____________________
BISMILLAHI RAHAMANI RAHEEM


*Har yanzu comments ɗin ku bai ƙayatar da ni ba,dan rabin mutane ko taɓo zancen abinda ke cikin book ɗin ba su yi*🤷🏻‍♀️

Cette page est dédiée à toi grande sœur de valeur *Halimatou* depuis Diffa son so
Page 5-6

Janye hannun shi tayi ya sake maidawa ya na mai lanƙwaso shi can ta ƙasan cikinta,cikin Hausar shi da za ka gane ta koyo ce ba iyata yayi ba ko yaren shi yace "ki nutsu ki kwanta gobe za mu wuce"Siya tace "ina za mu wuce kuma?"a take ya bata amsa da "Moumbay"cikin tsoro tace "wajen mi?ni ban san kowa ba can please ka maida ni gidan mu wajen ƴar uwata"juyota yayi suna facing juna yace "calme toi baby can ma gidan ku ne har ya fi gidan ku haɗuwa kuma a can za ki fi samun kulawa ok?"fararen idonta masu boule baƙi ta juya kamar ta na ganin shi tace "wanene kai please kamar na taɓa jin irin wannan muryai?am dan Allah ka bar ni ƙasar mu ban son zuwa garin ƴan iska kuma ka ga..."bai bata damar ida maganar ba ya cabke lips ɗinta,hannu ta sa ta tsamike cikin shi wai dan ya sake ta amman ina William rumfa yayi mata ya na mai cigaba da embrassé ta.Shiru tayi tana jin abun da ya zamana sabo a rayuwarta,can ya cire bakin shi ya furzar da numfashi cikin halshen French yace "ki bar tambayata akan abinda ke ce za ki ga amsar su soon" "mi zan gani?"ta tambaya cikin muryata irin ta yara muaaah ya sumbaceta yace "bn8 kwanta kar ki sa mu makkara"ta faɗa ya na mai ɗora rabin jikinta bisa fafaɗen ƙirjin shi yayinda ya mata matangali da ƙaton damtsen shi.
Shiru tayi tana sauraron yadda zuciyar shi ke bugawa duk cikin daƙiƙa ɗaya,tunanin halin da Leemat ta ke ciki ya tsaya mata a rai ko yaya ta isa gida lafiya?da wannan tunanin barci ɓarawo ya ɗauketa.
Jin saukar numfashinta ya sa William ya lumshe idon shi ko zai samu barci amman tsabar farin ciki ya hana shi rumtsawa.

Tun da safe Mishel ya zo bakin ƙofa ya na habshi wanda hakan ya tada William daga barcin da ya ɗan samu, pilow ya jawo ya maida mata kanta bisa firgigit ta farka tare da karanto addu'ar tashi daga barci.
Hannunta ya ja zuwa toilet bai wani tsaya tambayar ra'ayinta ba ya cika baignoire da ruwa ya tuɓeta ya sakata ciki.
Duk da ta saba ayi a gida Leemat ke yi mata wanka amman wannan karo sai taji abun banbarakwai tare da kunya,shi kuwa William ko a jikin shi sai da ya wanketa tas sannan ya fiddata tare da ɗaura mata towel ya kaita kusan ɗan ƙaramin pampon yace "kiyi alwala"ba ta ce komi ba ta fara shi kuma ya na kallonta har ta gama sannan ya ja hannunta zuwa falo.Hijab ɗin ta ya saka mata wanda ya ke dogo sannan ya shimfiɗa mata wata rigar shi,sai da ta fara sallah sannan ya koma toilet yayi wanka.
A zaune ya tarar da ita ta na zikiri,mai ya shafa tare da turare ya shiyar cikin riga da wando farare sannan ita ma ya shiryata cikin wata abaya baƙa ɗan kwalinta ya yafa mata a kai sai ta fito tamkar wata Balaraba.
"Mu tafi"William ya faɗa ya na mai kamo hannunta "amman ai ba ka yi sallah ba" Siya ta faɗa tana kallon shi "je suis pas un musulman"ya bata amsa "ba musulmi ba ne kai?to wane addini kake?"
"Stop Siya ce n'est pas le moment ki bari in mun isa

Please Login or Register in order to submit comment