Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai jin murya kawunta ya na cewa "Siya ki na gani na?" "A'a kawu ina dai jin muryar ka"kanta ya shafa yace "isa ok bari yanzu za mu koma gida kin ji ko?"kai ta gyaɗa cikin bagwariyar Hausarta tace "ina Leemat?"yace "ta na gun Mami ɗin ku yanzu za mu wuce jirgi za mu shiga na mayar da ke cin iyayen ki"Siya ba ce komi har suka shiga jirgin ya sauke su a Niger.``` ta na kawowa nan ta buɗe ido cike da furgici ta na kallon tsohon da yasa ta tuna wani ɓangare na labarnta na yarinta, murmushi tsoho yayi yace "ina kambun sarautar ya ke kin tuna?"girgiza kai tayi ta dafe can bayan ƙeya nan ta shiga wani babin tunani.
```Danee bai zarce da su Siya ko ina ba sai gidan da ya saye na Niger ,cikin ƙanƙanin lokaci ya kira yaron shi Darma akan ya na son ya samo mashi matar da za ta aure shi gobe-goben nan ba'a ɗau lokaci ba Darma ya gama shi da Baratu wacce iyayenta suka ce je ki ƙya gani,tamkar wasa yara aka ɗaura auren su da sharaɗin za ta riƙe mashi Yaren shi ta kuwa amince ta riƙe su Siya.Shekarar farko da auren su ta haifi Jasmine,a shekara ta biyu ta haifi Laila nan kuwa ta fara nuna banbanci,inda tun suna yara Leemat ke kula da Siya tun daga wanka wankin kayanta da sauran su.Lokacin da suka fara girma ne Leemat ta ankare da wani abu,shine duk lokacin da Danee ya zo Niger ya na baiwa Siya wani abu ta ci ita kaɗai shiyasa ta fara ƙoƙarin bugun cikin Siya amman ko tayi niyya faɗa mata sai ta kasa.Jasmine da Laila sun kasance ƴan gaban goshin Mami yayinda Leemat da Siya kullum su na ɗaki duk da dai suna nuna soyayyar ƙarya ga Siya kasancewarta makauniya.``` wani liquide ne ya shiga zubowa daga idon Siya ya na ɗiga cikin ragar da tsoho ya ke ciki,da sauri ya tara hannun shi liquide ɗin na zuba a tafin hannun shi sai da hannun ya cika ya shanye daga ƙarshe ya tsaya ruwan na ɗiga a jikin shi,tamkar wanda aka saka cikin injin haka jikin shi ya shiga wawalniya ya na haske yayinda Siya ta koma gefe ta na fidda numfashi,wani irin ƙishi ta ke ji da sauri ta mayar da akwatin ta shiga toilet ta buɗe pampon ta shiga shan ruwa kamar ba gobe.


***

Gonar shi ta gado ya sayar ya haɗawa Laila kayan lefe wanda aka yanke ɗaura masu aure ranar juma'a inda Liman ɗin garin su zai zama waliyinta,Asabe ba ta san wainar da ake toyawa ba ta na gudanar da mulki da isa akan abinda ya ke haƙin shi.Duk in zai kusance ta sai ya bata kuɗi ko ya sawo mata balangu wanda za ta ci ta ƙoshi a hakan kuma wani sa'in ture shi ta ke tun kafin ya gamsu,Muntari bawan Allah haka ya ke bin ta sau da ƙafa dan dai kawai a zauna lafiya.


Laila ce zaune ita ɗaya tayi zugum tana tunanin gida wanda shine karon farko da ta tuna su,ko dan gobe ne za'a ɗaura mata aure?oho kawai dai taji babu daɗi ta so ayi bikinta irin na ƴan ganta sai ya ta iya da ƙaddarar ta?Doli tayi haƙuri.
Wani tsoro ne ya kamata irin wanda kusan duk amarya tayi shi,tunanin yadda first night ɗin su zai kasance kai ta girgiza a zuci tace "kaiii ina ba ma zai kusance ni ba a yadda ni ke ƴar ƙarama ya na babba tausayina zai ji sai na ƙara girma"da wannan tunanin ta yakice fargabai.......


Comment and share Please


Jikar Rabo ce 😎
*ƊAN DABA*
```love
and
romantic story

``` _MRS SADAUKI_ 💫

*Dedicated* to My Babbar Yaya Nafissa Laouali Rabo🥰

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀️

____________________
BISMILLAHI RAHAMANI RAHEEM

*BUY MTN DATA AT AFFORDABLE PRICES*👇🏽

*500MB* 200

*1GB* 300

*2GB* 600

*3GB* 900

*6GB* 1800

(CHECKING BALANCE * 461*4# )

VALIDITY : 1 MONTH

For more enquiry Call or Whatsapp this number: *08066268951*

*PAGE 35-36*


Kafin Asabe ta farga sai jin sanarwa gobe ɗaurin auren Murtala,ɗan ƙaramin hauka ta aza a kan doli sai dai saketa ita ba za ta zauna da kishiya ba.Ko kaɗan Murtala bai saurareta ba balle har ya biye mata,Inna ce ma dai ke dannar ƙirjinta sai dai kamar ma zugata ta ke banda ashar babu abinda ta ke aikawa sai banbami ta ke ta na cewa "dama na san da walakin goro cikin miya tunda na ga ka zo da wannan baƙar ɗiyar na san da akwai abinda ka shirya,kai ni sam ban ma yarda da wannan auren ba munafunta ta kake a waje dan haka akwai lauje cikin naɗi"Inna da ke tarban baƙin da suka zo daga ƙauye ta dubi Asabe tace "kan ki ɗaya kuwa?gare ki farau kishiya da za ki tayarwa mutane da hankali tare da yin sharrin abinda kika san ko da kuɗi Murti ba zai yi shi ba?"cikin kuka Asabe tace "to babu rame mi ya kawo zancen shi?ace ba'a tashi gayamin ba sai yau sai muƙuniya ake da lamarin alhalin Allah ma da kan shi yace a tsananta bincike" "to sai ki bincika"cewar Inna ta na mai shigewa ɗaki inda ake yiwa Laila kitso duk ta na jin abinda suke ita abinda ya bata mamaki duk farin ta amman Asabe ta kirata da baƙa kawai da sharrin kishi.
"In an gama kitson ga ruwan lalle can na tace maki ki yi wanka sannan ki shafe jikin ki da turaren nan kamar kullum na fi son ya kama jikin ki da kyau"da "toh Inna "ta amsa mata.


Cikin ɗaki Asabe ta koma ta zura hijabinta da ɗaukar wasu kayanta ta ƙulle da kallabi ta saɓa su a kai ta fito ko ɗakin ba ta rufe ba ta fice daga gidan mutane sai kallon ta su ke wasu na kiranta ta dawo amman ko waiwaye.
Inna tace "Ku barta ta tafi ba dai yaji ba sai tayi-tayi"kasancewar shi auren gida ne kusan dangin su ne nan suka shiga Allah wadarai da halin Asabe.


Tun daga bakin ƙofa ta tartsa kuka tare da jefar da ƙullin kayanta ta na cewa "na shiga uku na lalace yau ni na ga baƙar rana wai ni Asabe Muntari zai yiwa kishiya "da sauri Ayya( mahaifiyar Asabe )ta fito daga banɗaki ta na cewa "miye?mi naji ki na faɗa koko dai kunnena ne bai jiyo min daidai ba kishiya?"faɗawa tayi jikin Ayya ta na mai ƙara sautin kukanta kamar wata ƙaramar yarinya,tureta Ayya tayi ta dubi ƙullin kayan da ke cikin kallabi tace "kutumar uban can shine kika kwaso jiki kika zo nan da sunan yaji ko mi?"cikin kuka tace "Ayya ba zan iya jurar ganin kayan takaici ba gwara na baro masu gidan dama Inna ba ƙaunata ta ke ba kuma duk munafurcin ta ne ita ta haɗa wannan auren"Ayya tace "baƙar munafuka azzaluma wadda ba ta san darajar zumunci ba har ta ke cin amanar shi,zauna ki huta na sha alwashin wannan auren ba zai je ko ina ba zai ɓare ai kowa ci tuwo da ni miya ce ya sha"cike da jin daɗin matakin da Ayya ta ɗauka Asabe ta wuce ɗaki ta na sharar ƙwalla.


Washegari ana gama sallar juma'a aka ɗaura auren Muntari Hamza da amarya Laila Dauda,tun da Laila taji ƙarar motoci alamun har sun dawo daga ɗaurin aure ga wata tsohuwa sai rangaɗa buɗa ta ke kawai sai Laila ta fashe da kuka.
Zulfa wacce tayi mata kitso da lalle ta shiga bata haƙuri,dan tuni suka ƙulla ƙawance Inna kuwa da murna ta shigo ta na shaidawa Laila yanzu za'a yi mata wanka fita lalle.
Wata tsohuwa ce ke yi mata wankan yayinda mutane suka kewaye banɗakin suna waƙen amare "iyeee-iyeee lemu-lemu😹lemun Kano lemun Daura😹"ita dai Laila sai sunne kai ta ke ganin tsohuwa sai dirzarta ta ke kamar za ta canza mata fata ga kunya kuma,ana gamawa aka saka mata sabbin kaya tare da luluɓa mata darar amare nan kuwa kuka ya ɓarkewa Laila har da shasheka.


Bayan an kaita ɗakin Inna wasu datijawa maza suka shiga suka yi mata nasiha mai ratsa jiki tare da tsayawa a zuciya,a wannan lokacin Laila neman kukan ma tayi ta rasa sai tunanin shin ina mahaifinta ya ke?miyasa ba tayi haƙuri ta zauna ta jira shi ba sai aurar da ita da kan shi?anya kuwa ta yiwa iyayenta adalci?miye makomar aurenta da mutumen da sati ɗaya ne kawai suka yi a tare ba tayi mashi wani cikakken sani ba?mi za ta faɗawa ƴaƴanta idan suka tambayeta ina dangin su na wajen uwa suke?"wasu zafafan hawaye ne suka shiga zubo mata ta na jin tausayin kanta.


Ango Muntari kuwa ya na can gun mai sayar da magani na islamique Center an haɗo mashi maganin maza (ga masu buƙatar maganin maza na ƙarfi,sha'awa,ko na ƙarin girma duk mu na siyarwa mai su yi min magana🙈😹 har na mata ma akwai amman ƴan Niger kawai).
Cikin leda ya shiga loda mashi su irin su max man,ɗoɗar,zumar maza da na Lipton duk sai da ya kwatanta mashi yadda zai amfani da su tare da bashi shawara kar ya sha tun yanzu ya bari har amarya ta saba.

Cikin mota ya saka ledar maganin sannan ya wuce gida inda abokansa suka haɗa walima,sosai yau Murtala ya ke jin shi cikin wani farin ciki.Abokanai da ƴan uwa kuwa sai gudunmawa suke bayarwa,sosai kuwa ya samu kuɗi fiye da auren shi ma na farko.

Gidan da Murtala ya kama haya bai da wani nisa da gidan su Inna,ɗaki ne ciki da ƙurya wanda ya sha sabon penti.Gado irin na masu ƙaramin ƙarfi ne da drower shi,a falo kuma an shimfida capet sai kujerun roba irin masu bancin nan.Duk da ba'a wani kashe kuɗi sosai ba amman ɗakin ya haɗu bakin gwargwado sai ƙamshin sabon gida ya ke da na penture ɗin meubles.

Bayan an kawo amarya kowa ya watse ango ya shigo ɗakin amarya,a kunyace ya umarce ta taje tayo alwala bayan sun gama sallah suka ci abinda ya shigo da shi bisanin suyi brush.
Laila da kayanta na atamfa uwanda aka kawota da su ta kwanta,ita duk a takure ta ke duk tsawon rayuwarta ba ta taɓa keɓewa da namiji ba.Muntari wanda ke kwance bayanta tsura mata ido yayi ya na tunanin ta ina zai fara?shi dai ba auren soyayya suka yi ba balle yace yayi mata wasu kalamai hasali ma tun ranar da ta amince da auren shi wata magana mai tsayi ba ta ƙara haɗa su ba.Ajiyar zuciya ya sauke tare ɗan matsowa kusa da ita,kamar munafiki ya kai hannun shi ƙugunta ya na mai ɗan jawota zuwa ƙirjin shi.
Zuciyarta ce ta fara dakan ƴar uku-uku tsabar tsoro,ba ta ida yankewa da lamurran Muntari ba sai da taji ya na yawo da hannun shi a duk sassan jikinta.Lamo tayi ta na karɓar baƙon yanayin ta wani gefen kuma ta na jin tsoro,kuka ta fashe da shi ta na son yin magana sai dai ta kasa kuma ba ta yi ƙoƙarin hana shi ba har sai da taji azabar da tafi ƙarfinta sannan ta fara fizge-fizge da ƙoƙarin ture shi sai dai ko gizau bai ba.
"Allah yi maki albarka ya biya maki dukkanin buƙatun ki na alkhairi,ya kare ki da duk wani ƙunci rayuwa na gode sosai da kyau abu mafi daraja da tsada my Layyyla"cewar Muntari ya na mai ƙara mannata a ƙirji tare da bubuga bayanta alamar rarrashi,sautin kukan ya rage sai shasheka a can ƙasan zuciyata kuwa faɗi ta ke "dama haka ake ji a daren farko?haka maza ke fidda tausayi su akan amarensu?a irin wannan azabar ce har wasu matan ke kai kansu da mazajen da ba na su ba?shin su ma suna jin zafi ne kuwa?"jin yadda Muntari ya kasa rufe baki sai ƙara kwarara mata addu'a ya ke saboda ta bashi tukuicin budurcinta yasa ta lumshe ta na mai jin wani sanyi "alhamdullah Allah na gode maka da ka bani ikon sauke nauyi na kawo budurcina gidan mijina,ina yiwa sauren mata addu'a Allah ya kare su yasa su ma suka na su mutuncin"ƙara tusa kanta tayi cikin ƙirjin shi ta na shaƙar ƙamshin jikin shi, Muntari kuwa sai santi taushi da santsin fatar jikinta ya ke tare sihirtacen ƙamshi da ya ke fitarwa.



***Moumbay


"Kaiii amman Guy ɗin nan fah ya haɗu,ka ga yadda ya aje manyan damatsa har wani murɗiya suka yi daga ganin shi ka ga ƙarfafa mai ji da ƙarfi wai ma dan Allah a ina ka san shi na ga kamar Bature ne?"cewar Leemat wacce ta fito daga wanka ƙugunta ɗaure da towel yayinda ta ke tsane gashinta da ƙarami, system ɗin gaban shi ya ture ya taso tare nufota ya ɗaga gira yace "wai akan wa kike magana?"ba tare da shakka ba tace "wannan ƊAN DABAR mana wanda kuka zo jiya"cikin tsuke fuska yace "to wa ya gaya maki *ƊAN DABA* ne?" "Ai ka na gani ma ba sai an gaya maka ba irin wannan damatsa manya-manya ai sai ku masu gari,wai miye sunan shi gaskiya matar shi na da aiki wai"jin bai ce komi ba ya sa ta aje towel ɗin hannunta ta waigo tace "ya dai?"Dawood ya ɗaure fuska yace "a'a wai da har ki gama yabon kyawun surar shi sai mu cigaba"Leemat ta ce "laaa!ni fah ba yabon shi ni ke ba kawai dai muscules ɗin shine suka burg..."buge mata baki yayi cikin hasala yace "ya isa haka Malama sai kije ki nemo shi tunda son shi kike,daga nan sai ki shiga uku tunda dama kin tausayawa matar shi kin ga shikenan ai"ya na gama faɗa ya shige toilet ya bar Leemat tsaye sororo ta na mamakin to mi tayi kuma?.


Shower ya sakarwa kan shi ya na jin wata irin ƙuna har ƙasan ran shi,tabbas Dawood ya san shi ma cikakken namiji ne mai ƙwanji sai dai William ya fi shi manyan damatsa su ma bai wuce dan shi William ma'abocin ɗaukar ƙarfe ne.
Pampon ya kashe saboda yadda ya ke jin zafin ruwan suna ƙara mashi raɗaɗi,da ya fito ko inda ta ke bai kalla ba ya buɗe frigo ya ɗauko gorar ruwa masu sanyi sosai ya kafa a baki sai da ya shanye sannan ya fara shiyawa a gaggauce.
Shareta ɗin da yayi sai yaji duk babu daɗi,ta miƙe tsaye doguwar rigar da ta saka ta fara jan ƙasa,murya a raunane tace "David..."sai kuma ta ƙyale,wani irin sarawa kan Dawood yayi ya riƙe shi ya na son tuna wanda ke kiran shi da irin wannan sunan amman sam ya kasa.
Huging ɗin shi tayi ta baya,cikin zafin rai ya ɓanɓare hannuwayenta da ta zagaye cikin shi da su tare da tunkuɗeta ta tafi tangal-tangal za ta daki miror yayi saurin tarota da hannun shi😂.
Kanta ƙasa yayinda ta ɗan rankaya baya shi kuma ya duƙo saboda tareta da ya yi,ƙuri suka yi ma junansu suna kamar masu son tantance wani abu,turo baki tayi tace "Ni ka bar kallona ka wani kafe ni kamar mayy..."ba ta ida maganar ba ya saketa ta faɗi ji kake gum ta buge kai da katako,harara ya watsa mata ya na jin wani irin haushinta wanda bai san dalili ba.
Agogon shi ya zura ya kama hanyar fita "tsaya min"Leemat ta faɗa tana ƙoƙarin tashi yayinda hannunta ke dafe da kai.
"Non tu restes ici"ya faɗa ya na mai ficewa tare da rufe mata ƙofa,wani uban kuka ne ya zowa Leemat ta shiga yi gashin kanta da ta gyara duk ta hargitse shi.


Inda William ya ke jingine gaban mota ya nufa,gaisawa suka yi suna masu sakarwa junan su murmurshi.
William na tuƙi Dawood n gefen shi ya na tunanin Leemat a yadda ya tsara a tare za su tafi shiyasa ma yace William ya zo da mota amman yanayin ƙwalliyar turawan da tayi ba ƙaramin kyau tayi ba haka kawai yaji bai son ta fito,tausayinta ne kwance cikin zuciyar dan har alƙawari yayi mata za su zaga gari da ita.
Wata sanyayar ajiyar zuciya ya sauke, William ya ɗan waigo ya kalle shi sai ya ga idon shi a lumshe.
Jin sun tsaya yasa Dawood buɗe ido sai dai da mamakin shi cikin filin jirgin sama ne suka zo,kafin ya kai ga tambayar William sai ganin Oga Darma yayi ya na tunkaro su.....


Comment and share Please


Jikar Rabo ce 😎
*ƊAN DABA*
```love
and
romantic story

``` _MRS SADAUKI_ 💫

*Dedicated* to My Babbar Yaya Nafissa Laouali Rabo🥰

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀️

____________________
BISMILLAHI RAHAMANI RAHEEM

*BUY MTN DATA AT AFFORDABLE PRICES*👇🏽

*500MB* 200

*1GB* 300

*2GB* 600

*3GB* 900

*6GB* 1800

(CHECKING BALANCE * 461*4# )

VALIDITY : 1 MONTH

For more enquiry Call or Whatsapp this number: *08066268951*

*PAGE 37-38*


Cike da mamaki Dawood yace "Oga dama yau ne za ka zo?na zata sai nan gaba dan naji kace kamar ka na wani abu mai muhimmanci ne"murmurshi Oga Darma yayi wanda Dawood zai iya cewa "yau ne karon farko da ya gan a kan fuskar uban gidan nashi,bai bashi amsar tambayar tashi ba sai cewa "ina ita Leemat ɗin?"ya na maganar tare da shiga gidan yayinda William ya zauna seat ɗin draber, Dawood shanye da mamaki ya shiga baya ya na mai tambayar shi ko dai kunnuwan shi ba su jiyo mashi daidai ba?amman kuma kamar ya ji ya ambaci sunan Leemat?to ta yaya ya san a tare suka zo yaushe ma ya santa? Dawood bai yanke da lamarin ba sai da ya ga sun nufi hotel suna tsayawa Oga Darma yace "yi sauri kaje ku tawo tare sauri mu ke"babu muso Dawood ya fita,zuciyar shi na das..das.das haka ya nufi ɗakin.A kwance ya tarar da ita tsakiyar gado daga ita sai towel da alamun wani wankan ta sake bayan fitar shi,surar jikinta ya fara ƙarewa kallo Leemat kuwa jin ƙara buɗe ɗaki da shigowa kuma taji shiru shiyasa tayi shiru hakan ya sa ta juyo,ɗan turo baki ta na mai tashi ya taɓe baki ya nufi wadrob ya ɗauko mata wata rigar shi ya saka mata da kan shi sannan ya shafa mata mai da turare.
Mayafi ɗan ƙarami na riga ya yana mata a kai ai kuwa Leemat tace ba ta san wannan ba ita ba za ta fita a haka ba,gira ƙasa da ta sama ya game ya na shirin yi mata magana ya ƙara jin wani kiran ya shigo da sauri ya ja hannunta dan kar ta ɓata mashi lokaci.

Oga Darma da Dawood tuni sun fito daga motar suna shirin shiga ciki dan kuwa Oga Darma ya fi kowa sanin wanene Dawood ya ga damar yayi siddabarun da za su ɓace,cak Leemat ta tsaya ta na kallonsu su ɗin ma ita su ke kallo da sauri ta koma bayan Dawood ta laɓe jiki na karkarwa hannunta ɗaya kan kafaɗar shi ɗaya kuma ga ciki.
Cikin murya mai cike da furgici tace "Alhajin Abba ?wlh *ƊAN DABA* ne kar ka matsa kusa da shi shan jini ya ke kum kuma munafuki ne"Leemat ke faɗa ta na kuka, murmurshi Oga Darma yayi dan dama ya san za'a rina.
Cikin mota ya koma ya na kallon yadda Dawood ke tambayarta tare rarrashinta dakyal ta bi bayan shi suka shiga mota William yayi mata key ba su zarce ko ina ba sai gidan su.

Ta ƙanƙame Dawood ta na mai fashewa da kuka,"yi shiru mana kin san dai in ina nan ga guri ba zan bari ya cutar da ke ba ko?"kai ta gyaɗa tare da tashi daga kan ƙirjin shi suka fito inda su William ke tsaye suna jiran su suka taka.


A falo suka tarar da Maman gefenta Momy ce ta na shayar da bbynta,duk waje suka samu suka zauna bayan sun gaisa ne Oga Darma ya gyara zama.

```Shekarun baya da suka wuce mu uku mun kasance manya abokaina,tun a makaranta Danee ya kasance mai son fifiko da nuna mana izza ba mu ɗauki komi ba mu ka rinƙa bin shi sau da ƙafa.Mu ukun nan mun kasance kowanenmu na da buri,Ni siyasa ni ke so na zama shugaba,Danee kuma mai son faɗa a aji a rinƙa tsoron shi duk duniya ta san shi yayinda Daddyn ku (cewa da su William)ke son zama shugaban ƴan dramer da siddabaru.Da mu ka zauna mu ka yi lissafi kuwa sai mu ka gane doli ko wane buri sai da kuɗi zai cika duk da dai mu na da kuɗi bakin gwagwardo,ba'a wani ɗau lokaci ba Danee ya kawo mana wata proposition mu shiga wata ƙungiya ba tare da binciken mi ƙungiyar ta ƙumsa ba mu ka amince nan ya kai mu gun Ogan su.Abu kamar wasa haka kowanenmu cikar burin shi ta fara tafiya kamar yadda ya kamata muna ta jin daɗi ba tare da mun san akwai tashin hankali gaba ba,abinda ƙungiya tace kowa ya bada jinin mutum ɗaya daga cikin ahalin shi to a nan ne fah Daddyn ku ya farga da ƙungiyar asiri ce kasancewar shi musulmi yace Indai sai ya bada jinin wani to daga yau ya fita,hankalin Oga ya tashi saboda ya na matuƙar ji da Ahmad saboda ko wata opération za'a je da salon siddabarun shi ya ke ɓatar da idon jama'a akan mutanen mu wannan ne ya sa ƙungiya tace banda shi tunda dama dai ba kuɗi ake bashi ba kawai ƙarfin iko ne.Ni kuwa Kakata wacce ta riƙe ni na bada, ɓangaren Danee kuwa Ɗa ɗaya tal gare shi sannan Abbas kuma bai ji zai iya bada ɗan uwan shi Auwal ba shine ya bayar da ƴar sa,maƙasudin mayar da ita makauniya daga zuwa Vacance ya sa Auwal bin didigi a ƙarshe ya tonowa kan shi abinda ya fi ƙarfin shi to nan ne fah Danee yayi mashi barazanar mutuwa shi da duk ahalin shi in yace zai tona asiri,bayan wasu ƴan watanni ne ƙungiya ta gano tabbas Auwal in ya na raye komi zai iya faruwa Danee yayi tsalle bisa yace ba za'a kashe mashi ɗan uwa ba nan ne kuwa aka bada shawar mayar da ƙwaƙwalwar shi irin ta kare da farko ɗabi'un shine suka fara sauyawa daga na mutane zuwa dabbobi a ƙarshe kuma Danee ya je har gida ya baɗe shi da wani magani har ya zama kare.Danee na shaida min abinda ya faru naje na ɗauke Michel da Miki na aje su guna ba tare da ya sani ba,matsayin Oga Danee ya ƙaru haka ma ƙarfin tsafin shi to a nan fah alƙalamin tsafin shi ya gano yaron Ahmad ne zai zama sanadin rushewar duk wani mulki na shi,kasancewata na hannun damar shi ya aike ni dan kashe shi a lokacin ya na makarantar India ta koyon tsafi,ban wani sha wuya ba wajen tawo da David saboda malamin ya san ni abokin Ahmad ne tun daga wannan lokacin kuma nayi amfani da tsafina na mantar da Dawood duk wani abu da ya shafi rayuwar shi sannan na sanya mashi a kai ƴan fashi sun tare su kuma ni na cece shi daga nan kuma na cigaba da rainon shi sannan na saka shi makaranta addini gefe guda kuma ana bashi training.Saboda gudun matsala mu ka gama ƙarfi da Danee wajen ɗauke Ahmad mu ka ɓoye shi dan kar ya san an kashe Dawood, dukkanin mu ba mu san ya na da wani ɗa ba sai daga baya ne gane na nemo William inda mu ka fara shirin yaƙar Danee sai na kai mashi William a matsayin ƙwararen *ƊAN DABA* duk da lokacin nan bai daɗe da zama soja ba amman sai yaje da wata fuskar wacce ba tashi ba,cikin ikon Allah Danee ya aminta da shi har ya ke gaya mashi wasu sirrika to a nan ne William ya fara samun labarin Siya ni kuma na bashi labarin komi to fah tun daga nan ne ya kamu da tausayin iyayenta soyayyar ta kuma ta shiga zuciyar shi ba tare da ya sani ba.Michel da Miki suka dawo hannun shi ya cigaba da kula su,a waje guda nayi wasa da hankali William shine aje wani book a matsayin na Daddyn su ne ya aje mashi shi.Ni na tura William gidan Danee na Niger a matsayin almajiri a lokacin kuma tuni an ɗaura igiyar auren su, yayi aikin shi ya samu nasara,daga nan kuma sai na kira Dawood

Please Login or Register in order to submit comment