Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

babu.
Ta na tsaka da gudun ne taji an yi sama da ita ta faɗi can gefe,mai motar ko tsayawa bai yi ba sai mutanen kan titi ne suka taimaka suka sa ta a taxi ya kai ta asibiti.
Siya na farfaɗowa ta gan ta da ƙarin ruwa ga bandeji a ɗayan hannun saboda raunin da ta samu,wata datijuwa ce ta shigo ta dubata tare da tambayar ta jikinta.
Da maganar kurame Siya ta mayar mata duk da dai ba jin English ta ke ba sosai ta fahimta,ashe datijiyuwa ta iya maganar kurame da ta tambayi Siya ina ne gidan su sai ta fashe da kuka tace ba ta sani ba.
Sérum ɗin ta cire mata tare da taimaka mata ta sauka daga gadon,ta na jaye da hannun Siya har ta tsayar da mai taxi ta gaya mashi unguwar da za su.Siya ba ta da wani zaɓi da ya wuce ta bi bayanta kuma sosai zuciyarta ta kwanta da matar shiyasa ba taji wani ɗarrr ba, lokacin da aka kawo su da murmushi ta shigar su cikin gidan wanda ya ke tsit ba kowa sai kukan tsuntsaye da ƙwari.
Tsabar ni'imar gun sai da Siya ta lumshe ido,gidan duk shibke-shibke ne a ciki ga ruwan piscine inda mutum zai yi wanka.Wani tsoho ne ya fito daga ɗakin ya na wangale bakin shi maras haƙora ya na magana da granny ya na kallon Siya,nan ta gaya mashi yadda aka yi ta same ta.
"Papi wacece ni ke gani nan kamar baƙuwa?"muryar wata ƴar budurwa ta faɗa wacce ke can saman bene ta na kallon su,da hannu yayi mata alama ta zo.
Wani irin kallo ta ke bin Siya da shi wanda har sai da tsargu,granny tace "ki tafi da ita ɗakin ki"a nan take tace Siya ba za ta shigar mata ɗaki ba tana gama faɗa ta wuce ɗakinta.
Ƙarƙashin gado ta duƙa ta jawo kwanonta na maita,sosai yawunta suka biya da kurwa Siya tunanin yadda za ta tsotse mata jini ta ke amman ta rasa daga ina za ta fara.
Granny ta koma gun aikinta Papi ya ja hannun Siya zuwa wani ɗaki da ya ke share tsaf sai dai babu komi ciki sai ƙaton akwati irin wanda ake sa kaya,tabarma da matala une place ya shimfiɗa mata.
Cike murna da yaba karamci irin na ƴan gidan Siya ta kwanta ta na jin wani barci na ɗibarta,Papi tsohon maye kuma ɗan iska baki ya ke lasa ya na shafar al'aurar shi ya rasa daga ciki wane zai yi Zina koko canye Kurwa?a haka dai ya fita dan bai son saurin nuna halin shi.



Wani irin tururi ne da masifar zafi ke tsatsafowa ya na fasar simintin ɗakin wanda hakan ya haifar mata da yin zufa sharka duk da AC a ɗakin amman gumin da ke ketowa ya mamaye sanyin.
A wahalce Siya ta farka saboda azabar zafi ji ta ke tamkar an saka ta cikin magasar burodi,gumin goshinta ta goge ta na sauke numfashi kamar wacce tayi tsere.Yadda ya simintin ɗakin ya ke yi mata gizo ya sa ta jin tsoro,tamkar toka haka ta ke ganin shi ga wani hayaƙi da ya ke fitowa,ta na ƙoƙarin tashi sai taji kamar ana magana ta cikin ƙarƙashin ƙasa.
Kunnenta ta kara ai kuwa magana ake sai dai muryoyin ba su fita sosai,cike da mamaki "to ko dai akwai wasu mutanen a cikin gidan bayan uwanda na gani?ƙila akwai wasu tunda ga hirar su nan ina ji"ta faɗa a zuci ta na mai fita waje haka kawai taji ta na son sanin iya adadin mutanen gidan,da ta fito waje ba ta ga wata ƙofa ba da zai nuna akwai wani ɗaki bayan wanda su ke ciki da tunanin abun ta nufi ƙaton piscine ɗin da ta gani tun farkon shigowa.


Tsaye tayi bakin ruwan ta na ganin hoton ta a ciki,hannu ta saka da niyyar ɗebowa sai ji tayi an ruƙo hannunta,ta saki ƴar ƙara tare da saurin ciro shi da ƙarfi fatar hannun har tayi kwalkwali cike da tsoro ta miƙe ta na jin zuciyar ta na bugawa.
Wata bishiya ta tsinkaya ta mangwaro sai dai abinda ya bata mamaki sunayen mutane da ta gani a ko wane mangwaro,ta na nan tsaye Papi ya fito ya tsaya daga baya ya na ƙare mata kallo yawun shi na tsinkewa.
Baby ma fitowa tayi cikin wani yare tace "Papi ka taimaka ka bar min ko da ɗan da ke cikin cikinta ne in ya so kai ka ɗauki uwar"Papi ya kalli Baby yace "Ɗan cikin da ko wata ɗaya bai yi ba shine za ki ce na baki dan dai kin cika mayya"ta ɓata fuska tace "haba Papi kai fah ka ce na haƙura na bar ma da yanzu tun tuni har na gama da ita,am yanzu abinda za'a yi bari za mu yi har ta haifo ɗan sai na ɗauka kaji Papi?"kai kawai ya jinjina mata ya fara takawa zuwa gun Siya wacce ke tsaye ta na ta aikin karatu,sunan mutum guda ne ya banbanta da na sauran ta na cikin tunani taji muryar Papi na cewa "mi kike yi yarinya?"juyowa tayi da fara'a ta nuna mashi Mango ɗin alamun ta na so sai dai ƙayar da aka zuzuba gun ya hanata ƙarasawa.


"Wannan ba na sha ba ne tawo ciki sai baby ta kawo maki nunanu masu daɗi da sanyi"ya faɗa ya na mai jawota suka nufi ciki,a falo suka zauna Baby ta kawo mata kayan marmari dayawa cike da murna Siya ke cin kayan ta yayinda Papi da baby suka sakata a gaba suna kallo.





William ne zaune abun duniya sun sha mashi kai , system ɗin shi ya ɗauko tare da buɗe saƙon da Khan ya turo mashi ta email.

```Prety ita ce budurwar Danee ya sun yi soyayya shan minti lokacin suna karatu inda ta samu ciki ta haifi Abbas wanda ya kasance rayuwar Oga Danee duk duniya babu abinda Danee ya fi so kamar Abbas na biyun shi kuma Prety ce wacce tuni tayi aure ya fi goma duk mijin da ta aura Danee sai ya kashe shi inda a ƙarshe ta haƙura ta dawo suna zaman dadiro ita da Danee.Abbas na da mashayar giya tafi goma inda a ko wane gida ya zuba ƴan matan da ya ke hutawa da su,sai dai gidan shi guda ne tal ya na can a unguwar bowa duk jerin gidajen na shi ya fi kowane kyawu da tsaruwa``` wane shine cikakken bayanin da abokin William ya turo mashi tare da hoton shi Abbas ɗin,rufe system ɗin yayi ya shiga toilet ya yo wanka ya shirya ya shirya cikin wata fuskar shi ta sirri.
Mota ya ɗauka bai zarce ko ina ba sai unguwar bowa,da kallo ya ke bin gidajen da kallo har ya samu nasarar ganin wanda zuciyar shi ke raya mashi na Abbas ne.
Horne yayi mai gadi ya buɗe mashi get tare da ƙarewa William kallo ta jikin madubin,ba sai ya tsaya tambayar shi wanene ba shigar shi kawai ta tabbatar da *ƊAN DABA* ne irin yadda ya zuba zabba ga uwar sarƙar wuyan shi kuma rigar jikin shi mai ƙananun hannu ce.



Ƙawayen yaran Abbas suka yiwa motar William ganin baƙuwar fuska,cike da gadara ya fito daga mota ya cire baƙin gilashin fuskar shi ya ɗaga gira yace "ya ko za ku dake ni ne?"yadda yayi maganar cikin murya basawa yasa su ja da baya ɗaya daga cikin su yace "Barka da zuwa Oga sai dai kayi haƙuri Boss na cikin fushi wata yarinya ya ƙwamuso bai kai ga shan romo ba ta gudu yanzu haka Boss ya bar gidan ya tafi mashaya bayan yayi mana sanbaɗebaɗ..."bai ida rufe baki ba William yayi mashi wata kumbutsar tsiya a baki a take haƙoran shi rabi suka zube.
Jinin sauran ne ya koma ga akaifa suka bashi haƙuri, "a wace mashayar ya tafi?"wani daga cikin su ya matso yace "Oga mu tafi na kai ka"mota suka shiga ya kai William mashayar da Abbas ya fi so ai kuwa tun daga nesa suka tsinkayo shi zaune a kujera ƴan mata sun zagaye shi ga kwalaban giya a gaban shi.
William na zuwa bai yi wata-wata ba ya kashe Abbas da mari tare da naushi duk wanda ya zo tare mashi haka William ke mazgar shi a ƙarshe ya cakumo wuyan Abbas ya tura shi mota tare da yi mata key......


Comment and share Please🙏🏻

Jikar Rabo ce 😎
*ƊAN DABA*
```love
and
romantic story

``` _MRS SADAUKI_ 💫

*Dedicated* to My Babbar Yaya Nafissa Laouali Rabo🥰

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀️

____________________
BISMILLAHI RAHAMANI RAHEEM

*QUEEN OF THE MONTH*👸🏻🥳

Page 27-28


UDDM babbar University ce ta maradi, students ne birjit kowanensu ya na harakar gaban shi.
Jasmine ce zaune cikin dandazon maza ta baza gashin doki har ya zubo mata har bisa kafaɗu,gefenta Big boy hannun shi kan cinyarta ya riƙe nata sai hira su ke wacce rabinta duk gulma ce da tsiyar gumi duk wanda ya wuce sai sun yi da shi in mace ce su ce ba ta waye ba.
Wani Guy yayi dariya ya kalli Laila da ke tawowa inda su ke zaune yace "wai dan Allah yaushe waccan bagidajiyar ƙanwar ta ki za ta waye ne?dubi fah ƙaton hijab ɗin da ta saka sai kace wacce za ta ja sallah"dukan su ihu suka yi hatta Jasmine sai da tayi dariya ta na nuna Laila wacce tayi turus ta na kallon su.
"Ki tashi mu tafi gida Mami yanzu ta kira ni wai ba ta lafiya"Laila ta faɗa ba tare da ta biye masu ba,kamar ba ta ji ta ba haka ta shiga danna waya kafin ta miƙe tsaye ta na jan hannun Big boy.
Sallama suka yi masu suka wuce inda Big boy ya aje mota,Laila na shirin shiga Leel-H ya ƙaraso ta tamke fuska kamar hadarin bisa tace "dan Allah ni dai nace ka fita harakata in kuma dagaske ka na sona ka turo magabatan ka "ta na gama faɗa ta shige ta bar shi nan tsaye cikin zullimi sam ya kasa gane kan Laila bai san mi ke faruwa ba magana ɗayan biyu yanzu ta ce aure.


Motar na tsayawa Laila ta fita da sauri,a duƙe ta tarar da Mami sai kwarara amai ta ke ba ƙaƙautawa.Sannu ta shiga jera mata kafin ta ɗauko mata mayafinta da takalmi su fita inda Big boy ke jiran su,sai da Laila ta rufe gidan da kwaɗo sannan ta shiga suka wuce asibiti.


Jinin Mami aka ɗiba tare da saka mata ƙarin ruwa en attendant,duk kuɗin da aka buƙata Big boy ya biya.Suna nan zaune cikin room ɗin da aka ba Mami Dr ya shigo daga Big boy sai Jasmine suna ƴan taɓe-taɓen su kasancewar Mami ta samu barci.Result ɗin ya miƙa ya na ce masu "congratulations"duban Big boy Jasmine tayi ta na mai karɓar takardar haɗe da murmushin yaƙe daidai nan Laila ta dawo daga sayen magani.
Jiki a sanyaye Jasmine ta miƙawa Laila takardar "Innalillahi wa'inna iley raji'un cikiii?ciki fah?shikenan Mami kin cuce mu"Laila ta faɗa ta na mai zubewa ƙasa ta na kuka wanda haka ya tayar da Mami ta tsinci muryar Big boy na cewa "to miye dan Mami na da ciki?ba'a haihuwa ke aka haife ki?"ai da sauri Mami ta mayar da ido ta rufe zuciyarta na dukan tara-tara, Jasmine ta ja tsuki tace "shekara Abba wajen biyu kenan rabon shi da ya zo ganin mu to ta ina ta samu cikin?"Big boy ya waro ido yace "duk da haka nan dai soutenir ɗin ta za ku yi ita ƙaddara ai musulmi ta ke ci sai ku yi mata fatan sauka lafiya duk da dai abun ba daɗi"cike da takaici Jasmine ta harare shi tare da ficewa daga ɗakin,bin bayanta yayi ya na faman kiran sunanta.


A kunyace Mami ta buɗe ido ta kalli Laila wacce ke zaune ta na kuka,da jajayen idonta ta kalli mahaifiyarta ta kafin ta sunne kai ta na jin wata irin matsananciyar kunya.
"Laila miye na kuka akan laifin da kika san ba zan aikata ba? wannan gwajin sam ba nawa ba ne sai dai in erreur ce yayi ai kin san dai da hankali na ba zan yi zina ba ko?"cewar Mami ta na marairaice fuska kamar za tayi kuka,Laila ta miƙe tsaye tace "Mami tun da ni ke ban taɓa ganin uwar da ta ke aza ƴaƴanta akan gurɓataciyar hanya ba sai ke,da farko na zata gata ne da wayewa yasa haka sai daga baya na gane hassadar mu kike ba ki ƙaunar mu ne.Maganar kuma ciki ni bai dame ni ba kin fi kowa sanin uban shi dan haka ki gayi maganar ki inda za'a yarda da ita dan ni ganau ce ba jiyau ba sannan abu na ƙarshe da zan faɗa maki daga yau ba ni ba ke tunda na ga alamu so kike mu zama ƴan daba kamar yadda kika mayar da kan ki,zan nisanta da ku naje nayi aure domin gobena"ta na gama faɗa ta fice ta bar Mami shaye da mamakin yadda har ta samu courage ɗin faɗa mata baƙaƙen magana.



Ta na kuka Big boy na bata haƙuri tare da bata giya a maimakon lemu,wani irin luuu ta fara ji yayinda wani duhu ke rufe mata fuska.
Da sauri ya tallabota ta faɗa jikin shi,maɓallan rigarta ya ɓalle tare da cire bra ɗin ta ya fara baiwa Twins ɗin ta wani salo tamkar ita ta haife shi.Cikin maye ta ke mayar mashi da martani,a zazzafe ya raba su da kayan jikin su ba tare da tausayi ko lura da ita ɗin Virgin ce ba ya dadage ya shigeta da ƙarfin tsiya wanda ya maido Jasmine cikin hayyacinta ba tare da ta shirya ba.
Ba ta da wani sauran ƙarfi balle tayi ƙoƙarin hana shi,haka ta na ji ta na gani Big boy ya keta mata haddi babu ji babu gani haka ya ke shigarta.

"Haba baby miye na kuka? Big boy ɗin ki ne fah in ba mu mori ƙurciyar mu ba yanzu sai yaushe za mu ci kenan?"Big boy ke faɗa ya na mai yiwa Jasmine wanka cikin ƙaton bawo,kai ta girgiza cikin kuka tace "ka cuce ni ban shirya kyauta da budurcina ba,tanadi na yiwa miji ne to yanzu mi kake son na ce mashi a daren farkon mu?"ya shafi kanta yace "to waye mijin bayan ni ?ke da har ki na tunanin auren wani wanda ba ni ba?to sha kurumin ki mu na gama karatu za mu yi aure mun kin ji babyna?"yayi maganar ya na sakar mata murmurshi wanda ya sanyaya zuciyar Jasmine.


A ɓangaren Mami kuwa sérum na idawa ta fita bakin titi ta samu abun hawa ya kaita gida,tun a bakin ƙofa ta ci karo da kayan da Laila duk ta zubda alamun ta yi mata bincike.
Cike da fargaba ta duba drower nan ta ga babu gwala-gwalai ɗin da ta ke saya masu in sun tashi aure sai kuɗi kuma an taɓa su.Waya Mami ta ɗauka ta kira Nas babu jimawa ya zo,cikin kuka Mami tayi mashi bayanin cikin da Dr yace ta na da sai dai mi?ƙarara Nas ya nuna murna tare da rungume Mami yace "shikenan zan samu Ɗa daga sanyin idaniyata,ki bar min bbyna ina son shiii"ya ida maganar ya na mai fara sumbatar ta.
Kasancewar Mami ba ta san ciwon kan ta ba haka ta biyewa Nas suka aikata masha'ar su kamar ba gobe,turus Jasmine tayi jin sauti na fitowa ɗakin Mami ta budar da ke jikin ƙofa ta leƙa nan idonta suka yi mata baƙin gani.
Wani yammm Jasmine ta ji tsikar jikinta duk da yau ne ta rasa budurcinta amman ganin halittar Nas ya sa ta son kasancewa da shi.


Da sauri ta shige ɗakin su zuciyarta na buguwa da sauri,laɓewa tayi zuwa can taji ƙarar saukar ruwa sai ta fita waje can ƙofar gida ta na jiran fitowar shi.
Ya na ɓalla batoran rigar shi ya fito daga gidan,Jasmine ya kalla wacce ke latsa waya ta na dariya kamar dagaske wani abun ta ke.
"Hy !"Nas ya furta dan tun ranar nan ya ga fuskarta,ɗagowa Jasmine tayi tare da sakar mashi murmurshi "ko zan samu lamba?"Nas ya faɗa kai tsaye dan dama tuni ya na da labarin ta na zuwa Club,babu wani jan aji ta bashi yayi godiya ya wuce bakin titi ya samu abun hawa.
Cikin daidaita tafiyarta ta shigo ɗakin, Mami na zaune ta na kallon tv da sauri ta miƙe ta na tambayar Jasmine yaushe ta dawo.
"Yanzu na dawo Mami ya jikin naki?" "Da sauƙi ba ki ga kowa ba a hanya?"Jasmine tayi dariya tace "Mami kin taɓa ganin titi ya tsaya babu mutane?"murmurshi kawai Mami tayi ta na mai jin daɗin Jasmine ba ta gamu da Nas ba.


Comment and share Please

Jikar Rabo ce 😎
*ƊAN DABA*
```love
and
romantic story

``` _MRS SADAUKI_ 💫

*Dedicated* to My Babbar Yaya Nafissa Laouali Rabo🥰

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀️

____________________
BISMILLAHI RAHAMANI RAHEEM

*QUEEN OF THE MONTH*👸🏻🥳

Page 29-30


Shiga motar tayi wacce ita kanta ba ta san inda za'a kaita ba,mota na cika suka ɓaga zuwa Dakoro ana kawowa kowa ya fita banda Laila wacce ke rabar ido.
Muntari na dawowa daga sayen abinci ya yiwa motar shi key ya nufi gida ba tare da yayi la'akari da Laila da ke can ƙarshen mota,"tsaya min"ya ji muryarta lokacin da ya ya kashe mota ya na ƙoƙarin sauka.Ya waro ido cike da mamaki sai da ta fita sannan yace "wacece ke?miyasa ba ki sauka tun atasha ba?"hawaye sharrr suka zubowa Laila tace "ni marainiya ce ban san kowa ba gidan da ni ke aiki kuma suka koro ni dan Allah ka taimaka na zauna gidan ka"tunda ta fara magana Muntari ya ke kallonta har ta kai Aya,ajiyar zuciya ya sauke ya na mai nunata mata cikin gidan shi wanda ya ke na laka an yi mashi yaɓe.Ta shiga sallama ɗauke da bakinta Inna kawai ta amsa yayinda Asabe ke binta da wani kallo,gaishe su tayi Inna ta amsa cikin fara'ar ta wa ta ke nema?bayanta ta waiga sai ga Muntari ya shigo yace "Inna tare mu ke da ita ai"cikin sakin fuska Inna ta nuna mata gefen tabarma tace "zauna yarinya ya gajiya?"Laila ta zauna tace "alhamdullah Inna"ta na mai aje ƴar ƙaramar trollynta.
Aje wankin da ta ke tayi ta bi bayan Muntari da ya shiga ɗaki "ban gane tare kuke ba?wacece ita?"Asabe ke faɗa cikin ɗaga murya har su Laila da ke waje suna ji,cikin tausasa murya yace "haba Asabe yanzu ko sannu da zuwa ba ki yi min sai masifa?to ban sani ba ki zura ido ki kalle ta tunda ba bisa kan ki ta ke ba"ya ida maganar a hasale saboda sam a rayuwa Asabe ba ta da wani uzuri ga ɗan karan nace ga shi ba ta ganin girman shi.
Fita yayi waje sai ya tarar tuni Inna ta zuba mashi ruwan waka ta kai mashi bakin banɗaki,ya shiga ya yo wanka sannan ya samu kujera ya zauna.
Ludayi Inna ta miƙa mashi sai ya saka shi cikin furar da Laila ke sha,duk da kasancewar ta ƴar birni sai da taji kunya saboda duk talaucin Muntari bai ɓoye ƙwar jinin shi duk da dai bai da wasu shekaru dayawa dan ba zai wuce 43years ba.Haka suka dinga shan furar har Laila ta aje ludayin ta ya kalleta yace "har ta ishe ki haka?"ta ɗaga kai tace "ai na sha sosai"Inna tayi murmushi tace "to tashi ki ɗauko alala cikin ɗaki sai ku ci duk da ba wani yawa gare ta ba yau kam na samu ciniki"babu muso taje ta ɗauko ta wanke hannunta suka faraci daman ta na son alala,suna ci hannun su na haɗu ita Laila sam ba ta damu da hakan ba Muntari dai ne ya ke jin wani iri ganin ta na son alala ne ya fidda nashi ba dan ta ishe shi ba.
Alwala yayi domin tafiya sallah asar haka ma Inna da Laila suka yi, Asabe kuwa ta na can ɗaki baƙin halinta ya hanata fitowa.


Ƙarfe biyar nayi Inna ta ɗora tukunyar tuwo Laila na daga gefenta ta na ɓanɓarar tafarnuwa dan kuwa tace ita za ta yi miya,tamkar sun saba haka su ke ta firar su ita da Inna wacce ke tankaɗe gari.
Wani murhun Laila ta sawa itace ta ɗora miya,a haka har suka gama komi kafin magrib nan Laila ta shiga wanka ta canza kaya.
Har ɗaki Inna ta kaiwa Asabe tuwonta sannan ta zuba miya ita da Laila suka ci suka yi nar, Muntari da ya shigo ɗakin matar shi ya wuce ya ci nashi.



"Sake ni Muntari,ka sake ni kar na tara maka mutane"Asabe ta faɗa ta na fizge zanen ta da ke hannun shi,cikin rarrashi yace "ki yi haƙuri ki bar ni in yi dan Allah,Asabe haƙina ne fah kar Mala'ikun Allah su la'ance ki"ya na maganar ne ya na ƙoƙarin jan ɗan tohinta (sket ɗin nan wanda ake sakawa daga ciki) "su yi ta tsine min ɗin amman wlh yau ba za ka ko gan shi balle ka..."saurin janyota yayi zuwa jikin shi ai ko ta fasa ƙara da sauri ya saketa tare da sauka kan gadon ƙarfen ya na jin wata masifafar sha'awa na taso mashi amman babu halin kawar da ita,zagayen ɗakin ya fara kamar mai zikiri ya rasa ya zai yi da ran shi bai san miyasa a ko da yaushe in sun samu matsala da Asabe ta ke mashi hukuncin hana mashi kanta.Duk abinda ya ke ta na kallon shi ƙasan ranta kuwa fal farin ciki ko ba komi ta gulala mashi sannan za ta huta tayi kwana ba tare da ciwon jiki ba.

Washegari Muntari ya tashi da wani ciwon mara idon shi sun jawur kamar wanda aka sawa barkono,a haka ya daure ya zo ya gaishe da Inna wacce ta ke yi mashi kallon tsaf dan jiya ƙarar da Asabe tayi sun ji ita da Laila dan dare suka raba suna hira.
Cike da tausayawa ta kalli Murtala tace "ba tun yau na ce ka sake yin aure ba amman ka ƙi,saboda Allah rayuwa tayi haka?yanzu shekara ku biyar da aure amman har yanzu babu canji dangane da lafiyar ka tsabar baƙin ciki kuma ta sha maganin hana haihuwa dan kar ta haihu da kai amman kai uban naci ka liƙe mata"sunne kai Murtala yayi cike da kunya,dan shi har ga Allah kunya ya ke ji tun ranar da aka gano ƙarfin sha'awar shi ne ya ke yawan sa shi ciwon mara dan har sai da aka yi mashi opération to nan ne fah aka haɗa su auren gida da Asabe dama shi tun farko ya na sonta ita ce dai ba ta son shi dan ita burinta auren mai kuɗi ne gaban ta.

"Inna ba auren ba ina zan saka matar ?sannan kuma ni banda budurwa"Inna ta gyara zama ta na murmurshi jin ya dai yarda zai ƙara auren tace "ba ga Laila nan ba"yace "wace kuma haka?"Inna tace "wacce ka zo da ita jiya"Muntari yace "haba Inna ni da ban santa ba kawai daga ganin ta jiya sai aure?".
"To minene?jiya sai da ta bani labarin ta kaf babu wanda ta rage min a ƙarshe tace in dai kuma mu ka ce sai mun maidata kashe kanta za tayi dan haka kawai ka aureta"nan Inna ta bashi labarin Laila a taƙaice kamar yadda ta gaya mata.
Murtala yace "to ki na ganin za ta iya aure na?"Inna tace "mi zai hana kuwa tunda ita dai mijin aure ta ke nema ta samarwa rayuwarta inganci"Murtala na shirin magana Laila ta shigo da sallama "ina kwana Yaya?"sai da ya ɗan ƙare mata kallo ya amsa,a shagwaɓe ta zauna kusa da Inna tace "layi na iske sosai kingin kaɗan nayi zuciya na dawo"dariya duk suka yi mata ta juye wainar cikin kwano.



***

Dariya yayi yace "wai wannan zumɓurar bakin duk na miye?"ta sake turo baki tace "ya lalace ne shiyasa nike yi mashi haka ko ya sha iska ya dawo daidai"ya harareta yace "kuma shine kike magana raɗau haka?"ta miƙe tace "tunda kuwa Allah ya tsaga shi"ƙafa ya sa ya taɗeta ta faɗi ƙasa, dariya ƙeta ya shiga yi har da riƙe ciki ya na nunata ita kuwa shagala tayi da kallon shi a zuci ta ke tambaya "dama ya na dariya har haka?"ya ɗaga gira

Please Login or Register in order to submit comment