Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yace "mi kike kallo?"ba ta bashi amsar shi ba sai miƙewa tayi ta zauna kusa da shi tace "yi dariya in gani " "ga taɓaɓe ko?ni mahaukaci sai yin ta dariya ki na kallo"ta marairaice fuska tace "please Dawooddd kawai dimple ɗin ka ni ke son gani"yanayin yadda ta kira sunan sai da ya tsaki zuciyar shi ya riƙo hannun ta yace "wa ya gaya maki sunana?"ƙyafƙyaf da ido ta yi tare da girgiza kai tace "kai ne ko?"yace "a'a ba ni ne ba""to Maye ne ken..."buge mata baki yayi yace "ba na hanaki faɗin sunan shi ba?kin raina ni ko?"yayi maganar ya na tanke fuska ya dawo ainahin *ƊAN DABA* tsoro ne ya kama Leemat jin hatta sautin bugun zuciyar shi ya sauya tsabar ɓacin rai.
Hannunta da ya riƙe ya na wani murzar shi tayi ƙoƙarin janyewa amman ya riƙe shi sosai ya na gana mashi azaba,hawaye na yi mata zuba tace "kayi haƙuri ka sake min hannu zan koma part ɗin mata"saketa yayi ta miƙe tare da ɗaukar hijab ta fita.....


Comment and share Please
********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels



Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************

Jikar Rabo ce 😎
*ƊAN DABA*
```love
and
romantic story

``` _MRS SADAUKI_ 💫

*Dedicated* to My Babbar Yaya Nafissa Laouali Rabo🥰

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀️

____________________
BISMILLAHI RAHAMANI RAHEEM

*QUEEN OF THE MONTH*👸🏻🥳



*BUY MTN DATA AT AFFORDABLE PRICES*👇🏽
*500MB* 200

*1GB* 300

*2GB* 600

*3GB* 900

*6GB* 1800

(CHECKING BALANCE * 461*4# )

VALIDITY : 1 MONTH

For more enquiry Call or Whatsapp this number: *08066268951*

*PAGE 31-32*

Leemat na shiga part ɗin duk kallo ya dawo kanta sai ƙus-ƙus mutane ke yi,gun Ladidi ta nufa wacce ta miƙe ƙafafu saboda yadda cikinta ya tsufa.Gaishe ta tayi tace "wai miye na gani ana ta kallona kamar wacce tayi sata ko mayyta?"cewar Leemat ta na yamutsa fuska,Ladidi tace "Nana ta basu labari wai budurwar Maye ce ke duk yadda Boss ya riƙe ki sai da kika ci amanar shi kika kwanta da abokin shi"ido Leemat ta zaro tare da dafe ƙirji sai kuma tayi gun Nana gadan-gadan ba ta wani ɓata lokaci ba ta rufeta da duka nan kuwa faɗa ya kancame.
Ƴan ɗakin sai ihu suke wanda hakan ya jawo hankalin mazan da ke waje suka shigo raba su,amman abu ya cuttura hakan ya sa ɗaya daga cikin su ya kirawo Arne amman da ya ke Maye ya ji an ce da Nana ne sai ya biyo bayan shi.
Yadda Leemat ta riƙe ta gam ta na bugu kai kace uwarta ce,ganin shilar Boss ce ya sa Arne ja baya ya tsaya tare da daka masu tsawa wai su bari 🙄 Leemat tamkar zugata ne yayi haka ta cigaba da nausar Nana waya Arne ya yiwa Dawood,Maye ganin ana shawowa da Nana ya sa hannu ya fizgo Leemat tare da ɗauke ta da wani mari wanda ya ɗauke jin ta da gani.Ihu tayi tare da yin wani tsalle za ta faɗi Dawood ya tareta ta faɗa jikin shi,ta na shaƙar ƙamshin bodyn shi ta ƙara ƙanƙame shi ta na mai tusa kanta a ƙirjin shi tana jujuya shi tare da cigaba da kuka sai faɗi ta ke "ban gani na makance"ƙara matseta yayi a ƙirjin shi ya na mai ƙanƙance idon shi da suka yi ja lokaci ɗaya.
Sunne kai Maye yayi zuciyar na dukan tamanin tsabar fargaba,duk jama'ar gun watsewa suka yi ya rage su biyar amman sai leƙen su suke dan ganin mi zai faru.
Ɗago kanta tayi tana ƙoƙarin buɗe ido,tsura mata na shi idon yayi tare da ɗan hura mata iska kafin ya kai bakin shi ya na lasar ta saman idonta.Ajiyar zuciya ta sauke ta buɗe idanu idonta ɗaya har yayi ja,saurin mayar da kanta yayi a ƙirjin shi sannan yace "akan wannan abar ce ka daki flower mai tsada?mi tayi maka?minene dalilin marin?ban taɓa kisan kai ba amman yau zan ɗaura ɗamarar fara shi sannan ka sani za ka fuskanci hukunci mai tsanani a guna,Arne samo min reza da bandeji".
Da sauri Maye ya duƙa ya fara bada haƙuri har da kukan shi,dan ya gane kalar muguntar da za'a aiwatar kan shi Dawood zai yanke fatar jikin shi ne kamar yadda ake kalsar rake sannan a naɗe gun da bandeji.
Can ƙasan maƙoshi Leemat ke magana ta yadda Dawood kawai ya ji,wani kallo ya yiwa Nana a nan take ɗan ƙaramin cikinta ya fara zuba.Dawood na shirin magana kiran Oga Darma ya shigo "ka shirya za ka tafi Moumbay gobe saboda an sace ɗan Oga Danee,kai kaɗai ne za ka iya ceto shi a duk yaran mu dan haka sai ka kimtsa"cike da rashin jin daɗin haka Dawood yace "Ok"kafin ya ja hannun Leemat suka nufi part ɗin shi.


Kaya ya fara zubawa cikin trolly ta kalle shi tace "ina za ka ?"yace "wai Moumbay kuma ni sam na tsani garin zuciyata ma bugawa ta ke kamar za ta faɗo".
"Ina bin bayan ka"ta faɗa a shagwaɓe yace "no wannan tafiyar fah sai an shiga jirgi ke kuma ba wani paspo gare ki ba kuma ba ma wannan ba aiki ne mai hatsari zan yi sosai"gabanta ne ya faɗi tuna Dawood fah *ƊAN DABA* ne sharrr hawaye suka zubo mata ya rufe trollyn ya zauna tare da ɗaukar ta ya aza a cinyarsa yace "gayamin minene?ki na son zuwa ko?to fine zan sa yadda zan yi amman da haɗari kar a tai siddabarun nawa ya ƙi aiki"ta ɗora hannunta a bayan shi tace "ni ina tsoron kar su kashe ka"yace "su wa fah?"tace "ai na san opération ne aka tura ka,ni dai ban so kar ka tafi"tsura mata ido yayi "ba ki so na mutu ne wly? Miyasa kika damu da ni"gemun shi ta ja tare da yin murmushi tace "kawai dai am babu komi fah"Dawood ya sauke ajiyar zuciya yace "m'aimes tu?"ta tsaya da wasa da gemun shi da ta ke,ya ƙara tambayata"ki na sona?"kokowa ta fara da numfashinta tare da ƙoƙarin tashi ya riƙe ta ya na mai jawo fuskarta ya haɗe da tashi tsinin hacin su waje guda yayinda idon su suka sarƙe cikin na juna,wani shock da wani abu mai kama da zare haka dukkansu suke ji.
Lumshe ido tayi ganin ya fara ɗan karkata kan shi,abinda tayi zaton ne kuwa kissing ɗin ta ya fara na tsawon minti uku sannan ya zare bakin shi.
Lips ɗin ta ya shafa wanda ya jiƙe da yawun shi,ta turo baki shi kuma ya harareta yace "yaushe rabon da ki yi brush ma wai?"wani ƙululun baƙin ciki ne ya kama Leemat wani iskanci bayan ya tsotseta ya ke tambayarta in tayi brush,"tun shekaru biyu da suka wuce"ta faɗa ta na mai tashi ta nufi toilet shi ma tashi yayi ya na dariyarta tace "kar ka biyo ni bar ni nayi wankana cikin nutsuwa"ta faɗi haka ta mai rugawa da sauri ya bi bayan ta.



****Moumbay

Sai dare granny ta dawo,a falo suka zauna suna ta hira ita dai Siya na kallon télé ta na jin lokacin da granny ke faɗa miyasa ya kai Siya ɗakin sirri shi dai bai ce da ita komi ba sai haƙuri da ya bata kafin ya tashi ya faki idon su ya ɗauki kular abinci ya shige ɗakin da aka sauke Siya.
Akwatin ya janye nan wata ƴar ƙofa wacce ta kasance ta raga kamar grillage ta bayyana,wasu ɗalasiman tsafi ya karanta ta buɗe step ɗin da za ta sada ka da ɗakin ya taka ko minti biyu bai yi ba ya fito.


Dare nayi Siya ta shige ɗaki ta kwanta,can tsakar dare taji kamar ana magana da sauri ta tashi zaune.
"Ruwa!ruwa..a bani ruwa"haka ta ke jin muryar na fitowa daga cikin ƙasa,akwatin nan ta janye saboda haƙin da ta gani ta wajen.
Wani tsoho ne ta gani zaune a kan kujera fuskar shi duk ta cika da gashi,ya ɗago kan shi sama ya na ta kiran a bashi ruwa toilet ta shiga ta ciko moɗa ta shiga tsiyaya mashi da sauri ya tara hannu ya na shan ruwan har da suɗe shi tamkar wani abinci.Ganin ruwan kamar ba su ishe shi ba ta ƙara komawa ta ciko ta bashi tayi mayi ya fi sau biyar amman tsohon nan na shanye ruwan kafin daga ƙarshe ta ga ya je ya kwanta.
Mayar da akwatin tayi yadda ya ke sannan ta dawo ta kwanta tunani fal zuciyarta.



A ɓangaren William kuwa tun da ya ɗauko Abbas ya ke gana mashi azaba amman amsa guda ce ya ke bashi shi ma bai san inda Siya ta ke ba,daga ƙarshe William ya fara bugun cikin shi ko ya samu wani sirri dangane da Danee sai dai abinda ya fahimta Abbas bai da labarin miyagun ayyukan da Danee ke yi bayan dabanci.



Dawood na dira garin Moumbay ya mayar da Leemat mutum ba kamar yadda ya shiga da ita a jirgi a matsayin jakar hannu😱,hotel ya kama masu Leemat sai shagwaɓe mashi ta ke.
Suna kwance suna hutawa bayan sun ci abinci wayar Oga Darma ta shigo bayan daga bisani ya bashi wani détail Na gidan da zai fara zuwa.
Washegari gari haka Dawood ya shirya shi da Leemat suka nufi gidan da zai fara yin wani aiki,mai taxi na aje su Dawood ya danna ƙarar rawa Papi ne ya buɗe ya na mai sakar masu murmurshi dan dama ya san da zuwan Dawood ɗin.
Wajen piscine Papi ya fara nufa da su ya na mai cewa "wannan ruwa sun yi shekara da shekaru suna jiran zuwan sai yau Allah yayi nufi"murmushi Dawood yayi yace "haka ne,yanzu ya ne zan yi"Papi yace "shiga kawai za ka yi ka fito kuma ba sai ka cire kaya ba"kai Dawood ya jinjina tare da yin Bismillah ya faɗa kwacal,da sauri Siya wacce ke bayan wasu flower ta leƙo jin ƙarar shigar mutum cikin ruwan da kusan kullum sai Papi yayi mata hani da zuwa kusan su.
Leemat ta ƙurawa ido na wani ɗan lokaci kafin ta maida idonta ta na jiran ganin wanda zai fito,wani abu taji kusan ƙafarta da sauri ta duba sai ta ga wani zare ne duƙawa tayi ta na warware shi ko da ta ida tuni Dawood wanda ya fito daga cikin piscine sun bar gun.....



Comment and share Please


Jikar Rabo ce 😎
*ƊAN DABA*
```love
and
romantic story

``` _MRS SADAUKI_ 💫

*Dedicated* to My Babbar Yaya Nafissa Laouali Rabo🥰

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀️

____________________
BISMILLAHI RAHAMANI RAHEEM

*BUY MTN DATA AT AFFORDABLE PRICES*👇🏽

*500MB* 200

*1GB* 300

*2GB* 600

*3GB* 900

*6GB* 1800

(CHECKING BALANCE * 461*4# )

VALIDITY : 1 MONTH

For more enquiry Call or Whatsapp this number: *08066268951*

*PAGE 33-34*

Sai da ya maida Leemat hotel suka ci abinci sannan ya wuce gun Oga Danee wanda ya aiko mota har hôtel aka zo aka ɗauke shi.
Da isar su suka tarar da Oga Danee a farfajiyar gidan zaune kan kujera ta alfarma ƴan mata duk sun zagaye shi,kallo guda za ka yi mashi ka gane uban daba ne.
Murmurshi kan fuskar shi ya ke kallon Dawood ya na mai son karantar zuciyar shi sai ruf ta ke a liƙe bai ganin komi tamkar dai ta William.
Gun zama aka bashi tare da tura mashi hotunan Abbas "aiki biyu za ka yi nemo min Ɗana sai kuma kashe wani gwaggon biri mai taurin kai sai dai kafin nan ina son yayi maka cikaken bayani na inda ya aje *littafin sihirin* da ya wallafa"amsar hoton Abbas ɗin yayi ya duba sai kuma ya saka shi cikin rigar aljihu yace "yaushe aka ɗauke shi ?su waye aboka nan shi?wane wurare ya fiya zuwa?"Oga Danee ya miƙe tsaye yace " aikin banza duk ƙarfin sihirin da ke jikin ka ba zai yi maka aiki ba ne ?ko ba ka yi wanka da ruwan ba ne?"Oga Danee na gama faɗar haka jikin Dawood ya shiga karkarwa jijiyoyin kan shi duk suka fito raɗo-raɗo yayinda idon shi suka fara sauyawa zuwa wasu kala tamkar na zaki.
Cikin muryar basawa Dawood yace "an gama ƴallaɓai am ina son rakiyar wani"murmushi Oga Danee yayi ya ɗaga waya ya kira William cikin ƙanƙanan lokaci ya zo.
Gun da Dawood ke zaune ya sunne kai Oga Danee ya nuna yace "wannan za ka yiwa rakiya daga yau ka zamo abokin shi na aiki na san ba ƙaramin citta abun zai bada ba domin kuwa zuciyoyin ku duk a rufe su ke na san kau wannan karon zan yi nasara hhh".
Tun daga ƙafafun shi wanda suke cikin takalmi har izuwa kan shi da ke sunne William ya ke bin shi da kallo bai san ko miyasa ba ya ke jin faɗuwar gaba.
A ɓangaren Dawood ma haka ta ke,bugun zuciyar shi ne ke ƙaruwa yayinda kwanyar shi ke tariyo mashi wasu abubuwa tun na ƙurciyar shi.
"Dawood ga William babban yarona ne zai yi maka duk abinda kake buƙata,am William wannan shine babban yaron Oga Darma "murmurshin yaƙe William yayi ya na jin zuciyar na ƙara wuntsilawa saboda ambatar sunan Dawood da aka yi,daidaita nutsuwar shi yayi yace "Barka da zuwa garin Moumbay Boss da fatan za ka ji daɗin kasancewa a nan har ka gama aikin da ya kawo ka?"ɗagowa Dawood yayi ya zubawa William ido bai ce komi ba sai tashi da yayi ya mashi nuni da ya biyo bayan shi.
"Bi bayan shi ka gwada mashi gari sannan ka danne zuciyar ka dama Oga Darma yace haka ya ke da shegen jiji da kai da izza sai kace shine *ƊAN DABA* na farko"Oga Danee ya faɗa ya na kallon William da ya bi Dawood da ido,jinjina kai William yayi ya bi bayan shi.
Babur ɗin da William ya zo bisan shi Dawood ya ja ya tsaya ya na mai jin haushin katse mashi tunani da William yayi.
A gaba William ya hau ya na mai tada babur ɗin, Dawood ya hau ya na mai cewa "ina son ka kai ni gidan babban malamin ƴan siddabaru na nan garin"dafa.
Madubin babur ɗin William ya gyara ta yadda zai ganin Dawood da kyau saboda yadda zuciyar shi ke raya mashi wani abu na daban,suna tsaka da tafiya William ya ɗan tsaya yace "gidan malamin siddabaru na nan Moumbay koko na India?"cike da jin haushi Dawood yace "ita Moumbay ɗin cikin wane gari ta ke in ba India ba?kaji wani shashanci"William ya ɗan murmusa yace "ai duk da haka yankin Kulkata shi mutane suka fi kira da India kasancewar nan ɗin Capital ne"banza Dawood yayi da shi tamkar bai ji shi ba.
Ta miror ya ke ƙare mashi kallo kamannin Daddy ne sak suka bayyana a fuskar sabon *ƊAN DABAR* da ya kasance baƙo a gare su,amman inda Dawood ɗin mu ne ta yaya aka yi bai gane ni ba?kuma fah ba lalle ya gane ni ba tunda tun ina ɗan yaro marabin shi da ni,to amman miyasa bai nemi iyayen mu ba?tabbas akwai lauje cikin naɗi doli akwai wani abun na daban ga shi rufafiyar zuciya gare shi balle na gano wani abu"William ke maganar zuci ya na kallon Dawood ta miror wanda shi ma shi ɗin ya ke kallo.

"In ka gama tunanin mu je ka sauke ni hotel tunda na ga alama ba ka san aikin ka ba"cewar Dawood ya na duba agogon hannun shi,cigaba da tuƙin William ya yi ya kai shi gidan mai siddabaru sai dai cikin rashin Sa'a nan aka shaida masu rasuwar shi.


A bisa hanya Dawood ya tambayi William"a ina ne hanyar madafur?"wani uban burki William yayi babu shiri yace "mi za ka yi a can?"Dawood ya tanke fuska yace "a can Abbas ya ke cikin wani gidan gona dan haka kai ni za ka yi ka tawo min da shi"wani irin ƙwarewa William yayi yace "ya aka yi ka sani?"amsa ya bashi da "ƙarfin iko ne da sihiri"ba dan William ya so ba haka ya kai Dawood unguwar ba tare da ya yarda ya kai shi har ƙofar gidan ba.


Makulin gidan ya taɓe tare da shiga cikin gidan ba'a jima ba ya fito da Abbas wanda duk ya galabaita,a tsakiya suka sa shi suka wuce gidan Oga Danee.
Kawo Abbas ba ƙaramin ƙarawa Dawood matsayi ya yi ba a zuciyar Danee,cike da murna ya kira Oga Darma ya shaida mashi aiki yayi kyau da alamu kuma lokacin cin nasara ne yayi, Oga Darma yace "Ni na gaya maka yarona babban *ƊAN DABA* ne kuma mai sa'a yanzu abinda za'a yi nima zan zo Moumbay ɗin ina jiran wani abu ne da ya kammala za ka gan ni "
"To Allah kawo ka lafiya sai dai kar ka manta da ajiyata ya kamata ka ɗaukota saboda bai fi kwana goma ba shekarun BIRTHDAY ɗin za su cika"cewar Oga Danee,cike da dariyar mugunta Oga Darma yace "kar ka damu ka ƙaddara ma yanzu haka ta na garin Moumbay har an kawar da budurci buri ya kusa cika hhh" kasancewar Danee wawa ne sam bai gane komi ba sai sallama da yayi mashi.


Ya aje waya yace "William kai Boss masaukin shi sannan ka dawo akwai plan ɗin da za mu shirya kafin zuwan Darma am Dawood ka tabbatar da ka bincike shi da kyau"kai Dawood ya jinjina.
Har cikin farfajiyar hotel ɗin William ya shiga da shi,haka kawai Dawood ya ji ya na son ƙulla alaƙa da William har ya juya babur yace "am ka shigo daga ciki ka ga inda na sauka"cike da murna ya bi bayan shi knowking yayi Leemat ta buɗe ɗakin ta waro ido ganin baƙuwar fuska,gaban William ya bada dam a zuci yace "mi ya kawo leemat nan kuma?miye alaƙarta da shi?".
"Ka ga inda na sauka nan al gobe ka zo tun da wuri sai mu wuce tare"kai kawai William ya jinjina yayi saurin fitowa.


Ko da ya shigo gida bai tsaya komi ba ya wuce cikin ɗakin shi,book ɗin sirrin shi ya ɗauko ya shiga bincike har ya kawo wata page inda aka rubuta *ƘADDARA ZUKATA BIYU* (My next book in shaa Allah).

```Yadda ƙaddarar ka da Siya ke manne da juna haka ma ta ɗan uwanka Dawood za ta kasance da ta ƴar uwar Siya, wannan ƙaddarorin sune nasarar mu da farko haɗuwar kowanen ku da ɗan uwan shi,na biyu ku ɗin garkuwar juna ne,na uku ta hanyar Dawood farin cikin ka zai dawo``` tsayawa yayi ya shiga nanata "farin cikina zai dawo,farin cikina zai dawo to kamar yaya fah ban gane ba?"da yaji kan shi ya ɗau zafi kawai ya shige toilet ya sakarwa kan shi shower.

Da ya fito daga wanka falo ya wuce inda Maman ke zaune ta na cin abinci, kissing yayi mata a goshi ya saka hannun shi suna ci tare.
Kallon Miki yayi wacce ta kasa zaune sai zirganiya ta ke,tashi yayi yace "Maman ina gani fah kamar naƙuda ta ke"Maman ma ta fidda hannunta ta ƙarasa gun Miki wacce ta fara kuka zuwa wannan lokacin kuma alamun haihuwa sun bayyana,ba tare da sun kimtsa ba kan baby ya fara fitowa Maman da yau ne karonta na farko ta fara karɓar haihuwa kusan rikicewa tayi.
Kafin wani lokaci yaro ya faɗo tare da cibiya,komi na shi sak irin na mutane suna tsaka da gyara shi Miki ta fara wata birgima a sannu surarta ta fara sauyawa zuwa ta mutum har ta dawo farar mace bafultana, atishawa ta shiga yi ta na mai duban su Maman da su ma ita su ke kallo .
"sannu Madam"cewar William ya na mai sakar mata murmurshi,sharrr hawaye ke zuba kan fuskarta ta na mai kallon Michel da ke habshi.
Gefen da ta ke kallo William ya duba ya na mai cewa "Michel !"matsowa yayi ya na mai zagayen William,murya na ɗan rawa tace "shi ɗin mijina,a da mun kasance cikin farin ciki da rayuwa mai daɗi sai dai shigowar Dauda(Danee)ya rusa shi"zama William ya gyara yace "ta yaya kenan?ko zan iya sanin dangantakar ku da Danee?"
```Dauda da Auwal ƙane da magaji ne sun taso cikin maraici sai dai dukiyar da iyayensu suka bar masu ya sa ba su wani sha wahala ba, dukkanin su sun kasance masu son kuɗin tsiya babu ma kamar Dauda domin shi ya na karatu ne ya na gamawa da kasuwanci.Ban san abinda ya gama su da Auwal ba kawai dai na ga ya na fushi da yayan nashi kasancewar lokacin da ya koma India da zama ya kan zo mana musamman lokacin da na haifi Siya wacce ya ke so sosai dan har India ya taɓa zuwa da ita tayi wasu shekaru a can,da farko nayi tunanin larurar da ta samu Siya ce ta makanta a dalilin Dauda yasa suka samun saɓanin sai daga baya ne na gane akwai wani ɓoyayyen sirri da bai son in sani.
Sosai na sa mashi ido a nan na gano wani abu ta hanyar fifita Siya da ya ke a kan ƴar uwarta Leemat,ya kan yi abubuwa dan ganin farin cikin Siya inda kusan kullum ya kan ce "gwara kiji daɗin ki tun yanzu kafin lokaci yayi"a ƙarshe kuma ya zubar da hawaye.Ranar wata Laraba da ba zan taɓa mantawa ba Dauda ya ziyarce mu a ɗakin baƙi suka keɓe ni ban san abinda suka tattauna ba kawai dai na ga ya fito ya na murmurshi sai kuma ya ɗauki su Leemat wai za su je shopping,fitar su ke da wuya na ji ihun Auwal da gudu na nufi ciki sai dai mi?birkiɗa na tarar ya na yi yayinda bidin kare ya bayyana ta bayan shi.Cikin soyayya irin ta mata da miji na nufe shi na rungume duk da tsayar da ni da ya ke kar in ƙaraso amman ina tuni na jawo mijina wanda taɓa shi ke da wuya naji wani ƙaiƙayi duk jikina,gefe na koma ina susar jiki a gaban idona Auwal ya rikiɗe ya koma kare kafin nima na halittata ta fara sauyawa zuwa wannan lokacin Dauda ya dawo gefe ya koma ya na ƙyarƙyatar dariya ya na cewa "da kyau!da kyau ke uwar karanbani kika taɓa shi ke mai miji"daga nan na ida zama karya``` ta na kawowa daidai nan ta fashe da kuka.
William ya fassarawa Maman duk abinda ta ce tunda ita ba Hausa ta ke ji ba,ita ma kuka tayi tare da duban William tace "ya kamata kai ka ƙarasa ba mu labarin"William ya girgiza kai yace "Oga Darma ne zai ƙarasa domin shi ya san komi tun daga A har Z gobe ya ke shigowa yace min akwai wani Gift da zai bamu ni da ke sai tun kafin ya bani tuni na gano miye"ya ida maganar ya na murmushi.



Kamar kullum yau ma Siya sai da ta baiwa wannan tsohon ruwa ya sha,sai dai abun mamaki sunanta da taji ya ambata daga can ƙasan maƙoshi.Baki na rawa tace "na'am"sai kuma tayi mamakin buɗewar bakinta hakan yasa tace "tsoho ka na ji na?"kai ya ɗaga mata yace "ina jin ki Siya,gaya min ina ne aka aje kambun sarautar matsafan👑 duniya?"da sauri Siya ta rufe idonta tare da dafe kanta da ya fara sara mata.

```wata yarinya ce ƴar ƙarama wacce ba za ta wuce shekara biyar ba,zaune ta ke cikin wata roba wacce ta ke maƙil da jini wanda ya rufe dukan jikinta kanta kawai ake gani.Wani baƙin aljani ne mai dogon gashi ya ke zagayarta ɗan ƙaramin kaskon huta na hannun shi ya na zuba wani garin magani,yayi hakan kusan minti talatin sannan ya tsamota daga cikin jinin ya zuba wani gari cikin huta ya tsugunar da ita hayaƙin na shigarta.Ya na nasata cikin wasu ruwa farare ƙal duk ta kakafe waje guda,cirota yayi ya kaita gaban wani madubi wani haske ne ke fitowa ya na shiga idonta kusan awa guda kenan sannan ya janye ta daga nan kuma ganinta ya ɗauke ba ta ƙara sanin komi ba

Please Login or Register in order to submit comment