Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

can duk kin samu amsar tambayoyin ki".
Haka kawai taji ƙyanƙyamin shi dan ita ana ta tunani duk wanda ba Muslim ba to babu amfani alaƙa da shi,ganin za ta ɓata mashi lokaci ya ɗagata cak tare da buɗe ƙofa Mishel ya rugo da gudu ya na zagayen ƙafafun shi tare da yin habshi.
Cikin ƙirjin shi ta ɓoye fuskarta tare da sakalo hannun ta guda bayan wuyan shi ta na sauke numfashin tsoro.
Moton🏍️ shi ya kalla tare da yin wasu formule na tsafi nan moton ya shiga ɓalle kan shi da kan shi ya cure waje guda,sauke Siya yayi ya koma ɗaki ya ɗauko ƙaton kwali ya saka tarkacen moton ciki.Hannunta ya riƙe tare da gyara zaman sac ɗin da ya rataya a hannu, Mishel yayi wata girgiza sai kuwa suka ɓace ɓat😱ba su tsinci kan su ko ina ba sai filin jirgi na Maradi.Ba'a wani ɗau lokaci ba aka fara kira abun mamaki wai har da tiket ɗin Siya da duk wasu shaidu da za su bada damar yin balaguro a jirgi har da hoton carte d'identité ɗin ta, William na gefenta yayinda Mishel ke kwance kusan ƙafafun shi daga ƙasa har jirgin ya ɗaga zuwa Niamey.
Cike da tsoro ta ƙanƙame shi cikin rashin sa'a kuma taji bindin Mishel na motsawa kusan ƙafarta ta buɗe baki za ta ƙurma ihu yayi saurin kai nashi ciki.
Tsit tayi tare da ɗage ƙafafunta sama,shi kuma William da ya ke ba ta ido gare shi ba ya cigaba da kissing nata, mutanen da suka gan shi ba su yi wani mamaki ba dan dama sun san halin turawa ne haka dan kusan ma tabiar su ce yin kiss.
Da suka sauka Niamey wani jirgin suka ƙara shiga suna tsatsayawa har da suka sauka Moumbay,"hu-hu-hu" Mishel ya shiga habshi lokacin da suka fita daga jirgi suka shaƙi iskan garin su.
Taxi suka shiga suka wuce gida,da gudu Mishel ya shiga ya na habshi wuf Mike tayi ta zo tarban shi habshin su ya firgita Siya ta wartse hannunta ta nufi cikin gidan a guje karo ta ci da Maman wacce kuka Mishel ya tabbatar mata da zuwan su.
Rungume Siya tayi tana shafa dogon gashin ta wanda faɗuwar kalabinta ya sa shi fitowa,jinta a jikin mutum yasa ta saurin yin baya tana kiran sunan William.
Dariya yayi mata jin yadda ta ke kiran nashi kamar mai koyon magana,"calme toi bb Maman ce fah"taji muryar shi bayanta.
Haɗa su yayi duka biyun ya rungume sannan ya sake su ya sumbaci Maman a goshi yace "tu ma manqué"tayi murmurshi tace"miss You too,ku shiga"hannun Siya ya kama suka shige.
Babu ko kunya abun ka da turawa bisa cinyar shi ya ɗora Siya ya shiga bata ruwa masu sanyi kafin ya ɗauke ta zuwa can saman étage inda ɗakin shi ya ke.

Duk da ta na makauniya amman ƙamshin ɗakin kawai ya tabbatar mata da haɗaɗe ne, déshabiller su yayi lokacin da suka shiga toilet ya jefa kayan cikin injin wanki kafin ya jawota zuwa cikin ƙaton baignoire wanda aka yi mashi ado da jajayen faranni sai ƙamshi ruwan ke yi.
Gashin kanta ya tuje baya sannan ya fara bin dogon wuyanta da sumba har ya kawo kusan fuskarta ya haɗe bakin su,yadda ya ke kissing ta tamkar wani mafaraucin zaki ashe can wasa ce yayi ba kiss ba sai yanzu ne ta gane banbancin saboda yadda ya ke shan bakinta har wani sauti ya ke fiddawa.
Shan yawu kamar shan alawa haka ya ke mata gefe ɗaya kuma ƴan mitsitsin breast ɗin ta ya ke massaging.
Wannan salon shine ake kira na yarda dan doli dan kuwa Siya ba ta san lokacin da ta ke maida mashi har wani tallabo kan shi ta ke, kasancewar ta Makauniya shi ya hanata ganin halin da William ya ke ciki ita dai taji ya buɗe ƙafafunta tare da shi tsakiyar su,babu zato balle tsammani taji abun da ya gagari tunaninta.
Ihu ta ke son yi sai dai babu damar yi domin bakin shi na cikin nata,kuma can sai ƙoƙarin fasa tantanin budurcinta ya ke.Lokacin da ya samu nasarar shiga ne ta ƙwace bakinta ta ƙwala wani uban ihu tare da damƙe manyan damatsan shi.....



Share Please


Jikar Rabo ce 😎
*ƊAN DABA*
```love
and
romantic story

``` _MRS SADAUKI_ 💫

*Dedicated* to My Babbar Yaya Nafissa Laouali Rabo🥰

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀️

____________________
BISMILLAHI RAHAMANI RAHEEM

*Na gode sosai da comments ɗin ku🥰in kuka dage da yin haka Ni kuma zan cigaba da suburbuɗo maki labari sai dai dan Allah ku aje hankalin ku da kyau ta yadda za ku fahimta*

Page 7-8


Ya cire bakin shi daga nata ya na mai janyo towel ya ɗaura mata,sunne kai tayi sai kuma tayi saurin ɗago shi ganin abinda ya fi ƙarfinta🤭.Towel ɗin iya mazaunanta kawai ya rufe dan bai da wani girma sosai,kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki haka ta fita sukuku.
Yadda jikinta ke juyawa ba ƙaramin ƙara dagula mashi lissafi yayi ba,ya sauke numfashi tare da cire ɗan culotte (gajeren wandon na maza) ɗin jikin.Karon farko da ya taɓa jin wai wata abu sha'awa hakan ya sa shi kan shi bai san yaya ya ke ba a suffar buƙatuwa,lumshe ido yayi ya na perturbé kan shi bai da wani zaɓi banda biyawa kan shi buƙata da hannu dan a rayuwar shi ya tsani zina kuma ba zai fatan ya fara ta ba.Ya ɗauki fiye da minti talatin sannan kawai ya samu kan shi,wankan tsarki yayi tare da alwala ya fito.
Doguwar riga jallabiya ya saka tare da shimfiɗa tapis ya fara jero nafiloli,sai da yayi dogayen addu'o'i sannan ya juyo ya kalli Leemat wacce ta bushe tun tuni tana zaune ta na kallon shi shaye da mamaki ita duk zaton ta ƙaton Arne ne irin gwarawan nan da ba su san Allah ba balle sallah sai ga shi ta ga ya na yin Sallah cikin ilimi da sanin haƙoƙinta ga kuma zazaƙa ƙira'a tamkar Balaraben Sudan.
Gira ya ɗaga mata yace "ya dai?miyasa ba ki shirya ba ko da towel ɗin za ki kwanta?"ba ta san lokacin da ta harare shi ba sai jin tsawar shi tayi "Ni za ki harara?age mate ɗin ki ne ni ?kenan dai ba za ki bar wannan iskancin ba?"Boss ya faɗa ya na mai miƙewa yayo kanta.Zumut ta miƙe ta na rawa jiki kafin ta kai ga cewa yi haƙuri har ya finciko towel ɗin da ta ke faman riƙo,ya ɗaga hannu zai sharara mata ta yi saurin faɗawa jikin shi ta saki kuka.Ya sauke huci ya na jin zuciyar shi na raɗaɗi wanda ya kasa tantance na zafin kukan da ta ke ne koko haushin hararar shi da tayi?
Sosai ya ji babu daɗi kyararta da yayi,bai san ya ake rarrashi ba balle ya rarrasheta kyakkyawan masauki yayi mata a ƙirji ya furta "ya isa haka ni ne ko?"ta gyaɗa kai "to na bari yi shiru mu tai na shirya ki"ya faɗa ya na mai janta zuwa bakin drower, tee-shirt ya saka mata fara ƙal da gajeren wandon iya gwiwa ya kalleta ya ga tayi mashi kyau haka yayi murmurshi yace "gobe zan sa Arne ya sawo maki kayan jiki kiyi tunanin duk abinda kike buƙata kafin gobe"murya na ɗan rawa tace "a nan zan zauna kenan?"yayi dariya irin ta Bassawa yace "au!halan na ɗauko ki ne dan na mayar da ke?"cikin muryar tausayi tace "na aza zuwa gobe za ka mayar da ni gida"yace "toh sauke in dan in maida ki ne miye amfanin ɗauko ki ɗin?"tace "tausayi"yace "ban san shi ba balle har na ji shi,wuce ki kwanta ban son surutu maras amfani"ba ta da wani zaɓi doli ta gusa inda gadon ya ke ta kwanta,shi ma hawa yayi ya na mai rage hasken ɗakin "nace ba miye sunan ki?"ya faɗa ya na mai leƙen fuskarta "Leemat"ta bashi amsa a sanyaye "ok Sa'adiya kenan sunan kakata ne" ya faɗa ya na mai zira hannun shi ta ƙasan tee-shirt ɗin haka kawai ya ji ya na sha'awar damƙe Twins ɗin ta ya kwana da su a hannu.
Ta sauke ajiyar zuciya kasancewar point weak ɗinta da zarar ya taɓa su ji take wani abu na yi mata zirrr,hannunta ta sa da niyar janye na shi sai kawai taji saukar dishashar muryar shi cikin kunnenta "ina son su please kar ki hana ni bar min su kin ji?n..na.nayi massaging ɗin su?"yayi maganar a rarrabe,wani yarrr taji tsikar jikinta na tashi da sauri ta haɗe ƙafafunta tana duƙunƙunewa waje ɗaya wanda yin haka ya baiwa Dawood damar ɗora ƙafar shi ɗaya kan jikinta,zuwa wannan lokacin Leemat ta zama so weak mace ce wadda dama sha'awar ta ke kusa sau tari ta kan yi tunanin yin aure sai dai halin da Siya za ta shiga ne ya ke sa ta ke danne burinta.
"Shikenan zai kashe ni"ta furta ƙasan zuciyarta lokacin da taji bakin shi bisa wuyanta ga kuma nishin da ya ke sauke mata a kunne.
Dawood kuwa ji ya ke kamar an yi mashi gafara tun da ya ke a rayuwar shi bai taɓa yiwa mace kallon sha'awa ba balle har yaji abinda maza kan ji in sun kalli mace, tsakanin shi mace kyara ce da tsangwama shi ma in sun samu masu tsaurin ido a waje kidnapping ɗin.
Karon farko a rayuwar shi ya gano wani sirri na jikin mace wanda shi dai a nashi ganin breast kaɗai sun isa ba sai an ka ga sex ba, nipples ɗin su ya kama ya na ɗan ja wanda hakan ya sa Leemat fashewa da kukan da ba ta san na minene ba.
Ya zare hannun shi ya koma can gefe ya na fitar da numfashi,ba wai dan bai so ba ne ko dan ya gaji ya ƙyaleta a'a kawai kukan nata bai iya supporter.


Washegari tun da asubah suka tashi suka yi sallah, Leemat doguwar riga shi ta saka da hijab ɗin ta.Mamakin Dawood sai ƙara yawa ya ke a zuciyata yadda ta ga ya zauna sai karatun Alkur'ani ya ke ba tare da ya koma barcin safe ba,ta na gefe ta na Azkar ɗin safe tare da sauraren shi abun ma ya so ba ta dariya ganin wai har akwai abinda zai sa *ƊAN DABA* kamar Dawood zubda hawaye.
"To in ka na tsoron Allah miyasa kake saɓa mashi tunda ka karanta ka gane?miye na yin kuka dan Ɗan ta'adda ya ji irin azabar da Allah ya yiwa masu laifi?to wai ma wanene wannan bahaggon mutumen?"Leemat ke tambayar kanta a zuci sai dai babu mai bata amsa.
"Ni ba kowa ba ne face bawan Allah yadda ba ki san ko ni wanene ba haka nima ban san waye ni ba"Dawood ke faɗa ya na kallon ƙwayar idon ta kamar yadda ta ke kallon ta shi.Da sauri ta sunne kai zuciyarta dukan uku-uku sosai ta fara tsorata da lamarin shi,ba ta san tafowar shi ba sai da taji ya busa mata iska a goshi ta yi saurin rufe ido ta na jin tsoron shi na fuzgarta.
Knowking aka yi ya matsa tare da fita zuwa can ya dawo a tsaye ya tarar da ita ta na raba ido,leda baƙa ya miƙa mata yace "ki shiga ki yi wanka ki shirya"ya faɗa ya na mai ficewa waje.
Wanka ta faɗa ta tsane jikinta ta shafa mai da turare sannan ta buɗe ledar ta zaɓi doguwar riga guda ta saka,hijab ɗinta ta maida tare da fitowa.

Mata ne da ƴan mata birjit wasu na shara wasu na baiwa flowers ruwa yayinda wasu ke girki,sakin baki Leemat tayi ta na kallon ikon Allah ashe duk inda ta aje Dawood ya wuce nan.
"Boss ya ne ko ita ma shilar ka har da ita za'a rabawa aikin"cewar Arne,juyawa yayi ya na kallonta yadda tayi wani tsaye kamar sakarai ya so ba shi dariya ya san dai bai wuce ta na mamakin yadda ta ga da jama'a gidan ne ta ke.
Bai tankawa Arne ba ya wuce gun ta ya na tafiyar nan ta ƙasaita mai cike da izza,"keee!"ya faɗa can ƙasan maƙoshi a zabure ta juyo ta kalle shi "mi keke kallo a can ɗin?"ya faɗa ya na harɗe hannuwan shi a ƙirji "ba komi "ta ba shi amsa yace "ba komi kuma kike ta kallonta ko ta burge ki ne?"yayi maganar ya na haɗe fuska.Kai ta girgiza tace "tausayi dai ta bani"yace "na mi fah?"tace "tsohon ciki ne da ita kuma an sata yin shara"ya matso daf da ita yace "eh sai aka yi ya?"tace "na gani kamar hakan na bata wahala wajen duƙawa ne"ta faɗa kamar za tayi kuka.
"Mayeee ?" Dawood ya faɗa da ɗan ƙarfi da gudu Maye ya tawo yace "Oga ga ni"ya na mai kallon Leemata,manunin shi ya ɓurma mashi ga ido da sauri Maye ya dafe idon da Dawood ya tsone yace "ayi haƙuri Oga sharrin zuciya ne,am mi zan yi" "ka amshe tsintsiyar hannun wacan guzumar ka baiwa wannan sannan duk wani aiki da za ta yi ka wannan ce za tayi ta na jin tausayinta ne shiyasa ta karɓi duty ɗin"Dawood ya faɗa ya na mai yin gaba ya shige ɗakin shi.
Cike da jin haushi Maye yace "biyo bayana"Leemat ba tace komi ba ta bi bayan shi ya amshe tsintsiyar hannun Ladidi ya baiwa Leemat nan ta fara share gun ta na ja masu Allah ya isa.
Ta na gamawa Maye ya jata zuwa bayan gida inda ake wanki,tulin kayan su ya gwada mata yace ya bata minti talatin ta wanke su.
Leemat na kuka ta na wanki har ta kusa gamawa sai ga wasu ƴan samari uwanda dama a ƙa'ida aikin su ne,bar masu tayi ta ɗarwaye hannunta ta zagaya ta koma can.
"Ke ɗauki tsintsiya ki sake wanke banɗakin can na ga ba su fita ba sosai"Maye ya faɗa cike da mugunta, Leemat na turo baki ta nufi bayin.
Dawood wanda fitowar shi kenan cikin shiga ta alfarma yace "ita kuma wacan ina za ta je"yayi maganar ya na waro ido ganin ta nufi toilet ɗin da ta ke ta kowa da kowa.
Tunanin sunan da da ta gaya mashi jiya yayi sai dai sam ya matan can ya ce "Leemaaaa"cak ta tsaya tare da juyowa duk da ya na daga nesa bai hanata ƙare mashi kallo ba,sanye ya ke cikin riga da wando baƙaƙe ya shace dogon gemun shi tsaf sumar kan shi kuwa sai walwali ta ke.
Da hannu yayi mata alama ta zo,ta yadda tsintsiyar ta tafo tana zuwa gun shi ta fara bubuga ƙafafu ta na shagwaɓa ai kuwa nan kallo ya koma sama wai ɗan cako ya ɗau Giwa.
Yanayin shagwaɓar da yadda ta ke yin magana cikin gunguni ta yadda ba'a ma jin abinda ta ke cewa shi ya shagalartar da shi yayinda mutane suka tsaya suna kallon ikon Allah tare da tausayin irin nau'in azabar da zai sa a gana mata amman abun mamaki sai gani suka yi ya ja hannunta zuwa ɗakin shi.......


#COMMENTS
#SHARE Dan Allah


Jikar Rabo ce 😎
*ƊAN DABA*
```love
and
romantic story

``` _MRS SADAUKI_ 💫

*Dedicated* to My Babbar Yaya Nafissa Laouali Rabo🥰

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀️

____________________
BISMILLAHI RAHAMANI RAHEEM

*Na dai gaya maku in babu comment no posting*🤷🏻‍♀️

Page 9-10


A hankali ta ke buɗe idonta da ta ke jin sun yi mata wani sanyi kamar an watsa mata ƙanƙara,tas ta buɗe su suka sauka kan kyakkyawar fuskar Weeliam wanda sam bai cikin nutsuwar shi ƙoƙarin gamsuwa kawai ya ke ya na shiga da fita cikin jikinta.Azabar da ta ke ji tamkar ya na yi mata jajagen atarugu ne a ƙasanta amman babu bakin yin ihun,ƙuri tayi mashi tana kallo har lokacin da ya zare jikin shi.Ruwan da su ke ciki duk sun ɓace da jini,buton ya danna ruwan suka tsiyaye ya tara wasu kuma masu ɗan ɗumi ya na mai jawota jikin shi.Ƙuri suka yi ma juna can ƙasan maƙoshi yace "yanzu ki na gani na?"kai ta jinjina mashi kawai sai ya haɗe bakin su waje ɗaya,ture shi tayi ta mashi alama da hunnu"wanene kai?"da sauri Weeliam ya tashi daga kishingiɗen da ya ke "wata sabuwa in ji ƴan caca,miye kike maganar kurame ba ki iya magana ne ?"kai ta ɗaga mashi alamar eh.
Fita yayi daga ruwan ya ɗaura towel ya fice daga toilet ɗin,wani book ya fiddo daga ƙasan drawer ya buɗe shafi na uku ya fara karantawa ```Ranar da idonta ya buɗe to a ranar bakinta zai rufe saboda ƙarfin sihirin da ke cikin jikinta ba zai bari tayi magana in kuwa tayi magana tamkar mahauciya za'a ɗauke ta dan kuwa abinda za ta faɗa hankali ba zai ɗaukar shi.Weeliam kar ka yi ƙasa da gwiwa kayi ƙoƙarin hana faruwar kafuwar wannan ƙungiya ta tantirai,sannan ka sani kai ne garkuwa Shamsiya duk ranar da ta bar hannun su za su nemeta ne ruwa a jallo kar ka buɗe masu wata ƙofar```har buɗe page ta gaba ya ga can ƙasa an rubuta NB: *Sai wata buƙatar ta taso sannan ka tafi a page ta gaba*
Ajiyar zuciya William ya sauke ya na mai jinjina wannan cakwakiya,Siya ta fito ɗaure da towel ta na gwale ƙafa harara ta banka mashi kafin ta wuce ta zauna bakin bed.
Tausayi ta bashi ga shi dai idonta sun buɗe ta na gani kamar kowa sai dai kuma wata masifar ta sake samunta ta liƙewar baki,ƙarasawa yayi kusa da ita yace "ya jikin ki?"ta ɗago ta dube shi ta mayar da kai ƙasa ta na mai cigaba da tunanin cakwakiyar da ta ke fuskanta.Ta yaya hakan ta faru?miyasa idonta ya buɗe alhalin ita Makauniya ce?wanene William?mi ya sani game da ni da har ya san idona sun buɗe alhalin ban faɗa mashi ba?"wannan sune tambayoyin da Siya ke yiwa kanta.
Kaya ya ɗauko tare da miƙa mata ya fice daga ɗakin,ba ta da wani zaɓi doli ta shirya ta shafa mai tare da kwantawa saboda tsabar gajiyar da ke tattare da ita.
William ko da ya dawo ya tarar tayi barci shi kaɗai ya ci abinci kafin ya shirya cikin wasu riga da wando baƙaƙe sannan ya ɗauko wata fuska ya shiga sawa kan tashi ɗaram ta zauna ya dawo wani kumurcin namiji in ka gan shi ka zata dama tun farko haka fuskar ta shi ta ke.
Bindiga da alburushi ya ɗauka ya na mai lanƙama wani abu a kunne sannan ya fice,Mishel na ganin fitowar shi ya rugo ya na habshi tare da zagayen shi.Shafar shi yayi yace "t'inquiète ba jimawa zan yi ba"sai da Mishel ya lashi hannun shi sannan ya wuce,mota ya shiga ya fara gudu ya na nufar hanyar fita gari sai da yayi nisa sosai sannan ya rutsi daji.
Wani tangamemen gate na ƙarfe mai gadi ya buɗe mashi ya shiga,ya na gama parking ya wuce ciki inda tuni aka fara gudanar da taron.
Ƙarasawa yayi ya zauna ya na kallon farin allon da Oga Danee ke expliquer yadda attaque ɗin zai kasance,shiru William ya yi ya na kallon komi can ya miƙe ya nufi gun Oga Danee yace "bai kamata mutanen mu su tsaya a nan ba dan akwai tsaro sosai da zarar an yi digil za'a iya kama su, rond-point na biyu ya kamata su tsaya dan bai fiya mutane sosai ba,sannan za mu rufe hanyar global ta yadda motar kuɗin za ta sake hanya suna zowa daidai rond-point sai a halbi tayar motar amman a sa bindigar silence ta yadda ƙararta ba zai fito ba,ka ga doli drever ya tsaya duba ko lafiya daga nan sai Rohan ya kashe shi tun da ya fi kowa iya saiti."ganin Oga Danee na kallon shi yace "No Oga shawara ce in hakan bai yi ba ana iya canzawa tsari"ya faɗa ya na mai komawa mazaunin shi.
Oga Danee ya ɓata rai yace "yadda na faɗa maku haka za ku yi kun ji ko?"mutanen gun suka amsa a tare "Yes Oga"su na masu sanya masque baƙa wacce daga baki,ido da hanci kawai ke waje.Bindigogin su suka yi chargé tare da ficewa har William zai bi bayan su Oga Danee ya tsayar da shi,"yau ba da kai za'a fita ba"da sauri Weeliam ya waigo yace "saboda mi Oga ?"ƙara tamke fuska Danee yayi yace "ina ka tafi tsawon sati guda ba tare da neman izini ba?" amsa ya bashi "ban jin daɗin jikina ne kuma ai na gaya maka duk bayan wata uku ina zuwa ganin likita"Danee yace "amman ai ba kai wata uku kayi waccan tafiyar ba" "eh ai nace ma jikin ne naji ya na son motsa min shiyasa nayi riga kafi"kallon cikin ido Oga Danee ke yiwa William amman sam ya kasa ganin abinda ke cikin zuciyar shi saɓanin sauran mutane.
"Ina so ka rakani"Oga Danee ya faɗa ya na mai juya baya, William yace "ba damuwa ina za mu je?yaushe ne kuma tafiyar?"murmurshin gefen baki Danee yayi yace "yanzu za mu tafi mana sanin kuma ina za mu in ka shirya kawai ka matso"ba tare da tsoro ko fargaba ba William ya matsa.
Hannun shi Oga Danee ya matse tare da karanto wasu ɗalasimai na tsafi,kamar walƙiya haka suka ɓace suka aniya gudu cikin iska tamkar guguwa sai da aka ɗauki tsawon sakonni sannan suka bayyana gaban wani gabjejejen Kogi.
Waro William yayi kamar mai jin tsoro da fargaba yace "ina ne nan?ya aka yi na gan mu ba..ban gane ba"shiru Oga Danee yayi bai tanka shi ba sai ma wasu suratai da ya fara karantowa ido rufe ya miƙe dukan hannuwan shi ya na mai fuskantar kogin da ya fara rikiɗewa ya koma wuta🔥har wani ɓulɓulowa ta ke.
"Hahhh,uwayyyyy uwayyy"haka wani sauti marar daɗin ji ya fara fitowa daga kogin yayinda wani haƙi dogo ke ta wuwulniya ya na ƙara tsayi da kauri har sai da ya kai iyakar da ido bai iya gani sannan kogin yayi girgiza sai ga wani tsoho ya bayyana jikin shi fari fuskar shi baƙa yayinda gashin kan shi ya ke a murɗe ya zubo har ga kafaɗa.
Buɗe ido Oga Danee yayi lokacin da ya ji aljani Gamsak na magana cikin murya shi mai kama da ɓarɓarkiya "wannan zinaren da ni ke faɗa ma tun tuni shine cikar burin ka hhh ya daɗe tare da kai amman sai yau kawai ka gano shi dama na faɗa maka in ka aje hankalin ka za gane shi,yanzu abinda za'a yi ka riƙe shi matsayin makamin ka domin wannan ya na wata baiwa wacce shi kan shi bai san da ita ba"murmurshi ɗauke a kan fuskar Danee ya ke kallon aljani Gamsak cikin jin daɗi yace "ina maka fatan nasara kai ma na zama shugaban aljannu na duniya"aljanin Gamsak bai ce komi ba sai wani abu fari ƙal da miƙawa Danee a hannu ya ce ya sawa William shi a haure,bai wani ɓata lokaci ya buɗe bakin William ya laƙa mai shi daram ya zauna tamkar hauran Makka.
Wani irin haske jikin William ya ɗauka tamkar an saka shi cikin ƙwan fitila,hannun shi Danee ya kama ɓat suka koma ɓacewa.


Oga Danee ya gyara zama ya na kallon William da ke yi mashi kallon tuhuma,"William na zaɓe ka ne ka zamo makamina saboda cikar wani ɓoyayyen burina da na daɗe ina son gani, tabbas ba'a ɓoyewa abokin cin mushe wuƙa dan haka zan gaya maka kaɗan daga cikin labarin da fatan za ka riƙe min sirrina?"yayi maganar ya na mai zaunawa a kujerar da ke facing da wadda William ke zaune,"ina sauraren ka Oga Danee kar ka damu ni ɗin mai bin umarnin ka a ko da yaushe"cikin jin daɗin amsar shi Danee yace "wannan mutumen da ka gani ba ɗan Adam ba ne aljani ne"waro ido William yayi da sauri yace "aljani?ta yaya ka san haka?to ina ma ka ga mu da shi"yayi maganar a ruɗe.
Oga Danee yace "calm down kar ka wani ji tsoro ba zai cutar da kai ba,shi ɗin ya kasance aljanin da ni ke bautama ya na taimako na a duk lamurrana ya bani abubuwa masu tasirin gaske wanda kallo idon mutum kawai zan yi na gane abinda ke ran shi,to aljanin Gamsak ya faɗan burina ba zai taɓa cika ba sai na samu wanda ya fi ni ƙarfin iko wanda sam ba zan iya ganin abinda ke zuciyar shi.Na daɗe ina nema har ƙasashe da dama na

Please Login or Register in order to submit comment