Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

alamu kwabsa min ta ke son yi in taje gun Inna ai shikenan ƙila ma ta riƙe ta".
Wajen Inna ya tafi cike da kunya yace "Inna ya kamata fah kije ki tawo da Asabe "sai da Inna ta dube shi da kyau tace "na ƙi ɗin ai ba ni na aiketa ba, lokacin da tayi yajinta wa ya kaita?yadda ta tafi da kanta haka za ta dawo da ƙafarta dan haka ka sake zance ko ka fita ka ban wuri"Muntari ya sunne ya na jin haushi sam ba haka ya so ba.

Da dare kuwa cikin tsoro Laila ta kwanta can ƙarshen gado ta na jin zuciyar ta na bugawa kamar ko wane dare,ƙuri Muntari yayi mata ya na ankare da ita "tabbas tsorona ta ke shiyasa ma ta kasa barci"ya faɗa a zuci kafin ya fita ya ɗauro alwala.Tafi ya shimfida ya shiga jero nafiloli tare da roƙon Allah ya rage mashi wannan cuta ta sha'awa dan yanzu kuwa ya yarda cewa ta wuce yadda ake so ta zama cuta,bayanta ya kwanta ya na haɗiyar yawu.....



Comment and share Please


Jikar Rabo ce 😎
*ƊAN DABA*
```love
and
romantic story

``` _MRS SADAUKI_ 💫

*Dedicated* to My Babbar Yaya Nafissa Laouali Rabo🥰

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀️

____________________
BISMILLAHI RAHAMANI RAHEEM

*BUY MTN DATA AT AFFORDABLE PRICES*👇🏽

*500MB* 200

*1GB* 300

*2GB* 600

*3GB* 900

*6GB* 1800

(CHECKING BALANCE * 461*4# )

VALIDITY : 1 MONTH

For more enquiry Call or Whatsapp this number: *08066268951*

*PAGE 47-48*


Matsowa yayi kusa da ita ya na shirin kai hannun shi gareta ta miƙe firgigit cike da tsoro ta dire daga gadon,"tashin hankali"cewar Muntari a bayyane ya na mai tashi zaune ya na kallon ta hasken da ya shigo ta window.Sauka yayi daga kan bed ɗin yace "zo ki kwanta ni zan koma falo ma"ya na gama faɗa ya fice,cikin sanyin jiki ta koma ta kwanta har ga Allah barci ne cike da idonta amman tsoro ya hanata rumtsawa.
Muntari kuwa falo ya koma ya samu gefen capet ya kwanta ko matashin kai babu balle shinfiɗa,a haka yayi ta mutsutsu har wahalalen barci ya ɗauke shi Laila ma cikin tsoro tayi barcin cike da mafarkin Muntari.


Washegari ta riga shi tashi ta zo ta buɗe ƙofa dan tuni gari yayi haske,jin an buɗe ƙofa ya farkar da shi yayi addu'a tashi daga barci ya miƙe da sauri ganin sun makkara sallah duk da haka a masallaci yayi sallar shi dan yinta a gida babbar azaba ce.


Laila kuwa ta na gamawa ta share ɗaki ta gyara shi tsaf ta kunna turare sannan ta share tsakar gida shi ma,wuta ta hura ta ɗumama abincin karin kumallo sannan ta je tayi wanka.Muntari bai baro masallaci ba sai da ƙarfe bakwai ta gota,wani sanyi ya ji tun daga bakin ƙofa ƙamshin jikinta da na turaruka ya bugi hancin shi.Bokiti ya ɗauka ya zuba ruwa ya kai banɗaki,jin ƙarar ruwa yasa Laila ɗaukar kwandon sabulu ta aza mashi bisa katanga tare da jallabiyar shi wacce ya ke shiga wanka da ita.


Har ya gama shiryawa kan Laila a sunne ta kasa ɗagowa har ga Allah ba haka ta tsara rayuwar aurenta ba,a tsarinta komi tare da mijinta za tayi shi wanka,shafa mai da shiyarwa duk sai ta taimaka mashi amman kasancewar Muntari ba yaro ba ne sai ta ke jin nauyin shi.
Kamar ya san abinda ta ke tunani yace "Tom na shirya da kaina sai azo a saka min turare"cike da kunya ta miƙe ta na mai cewa "ina kwana?"ya rungumota cikin muryar Shagwaɓa yace "baby ai kin fi kowa sanin irin kwanan da nayi mai cike da kewa"kai ta ɗan girgiza tace "ai kai ɗin ne babu sassauci ko ɗan ƙetare rana guda ba ka yi min in samu in huta "ya ƙara mannata a ƙirji yace "baby ai sai ki bar ni ko da ɗumin jikin ki naji amman kika mayar da ni falo cikin kujeru"ta furzar da numfashi tare ɗora hannuwanta kan ƙirjin shi saboda yadda ya matseta tace "ai daga jin ɗumin za ka zarcewa ni kuma tsor..."ganin ya ranƙwafo ya matso da fuskar shi kusa da tata yasa ta yin shiru,tayi saurin lumshe ido jin ya lasar lips ɗin ta a hankali ya tura halshen shi cikin bakinta ya na yawo dashi kafin daga bisani ya haɗe bakin nasu ya sumba tare da ɗura mata yawun shi ta na haɗiyewa,sosai suke jin daɗin yanayin a hankali ta ɗan ɗaga idonta ta sauke su bisa fuskar Muntari wanda ya lumshe ido gashin idon shi dogaye sun wani dishidishi tsabar jaraba, dogon hancin shi har baka haka girar shi tamkar wacce ya ke shafawa kwalli tsaf da ita a takaice ta gano mijinta kyakywa ne.

Numfashi ya fuzgar tare da sakinta ta ɗan sheɗa,a buƙace ya ke amman doli ya haƙura ya haɗe maitar shi duk jikin shi ya mutu wata irin kasala ta saukar mashi.
Kan bed ya zube ya kwanta rairan numfashin shi na fita da sauri-sauri,blue wandon na shadda tuni ya ɓace saurin kawar da idonta tayi daga kallon shi ta na ƙoƙarin fita taji murya shi can ƙasan maƙoshi "Lailerrr"wani yam tsikar jikinta tayi a take kuma tsoro ya luluɓeta,cike da shakkar shi ta ɗan matsa tace "na'am"da hannu yayi mata alama da ta zo,ta matsa gaf da gadon ta na kallon fuskar shi wacce ke tsiyayar da hawaye cikin murya buƙatuwa yace "please sau ɗaya tak ki taimaka min kar na mutu Allah ina jin zafi sosai"ambatar mutuwa yasa duk ta ida daburcewa babu yadda ta iya doli ta bashi haƙin shi.

A wahalce dukansu suka yi wani sabon wanka,Laila yau dai ba taji zafi sosai ba dan ya bita a hankali sannan sai da ya daɗe wajen aika ɗan aike ma'ana wasanni😉

Suna gama yin breakfast Muntari ya fice ita kuma ɓingire barci,sai wuraren sha biyun rana ta farka.
Miƙa tayi ta diro daga gado,turus tayi ganin Inna a falo ta na jera abinci cike da kunya ta ƙaraso ta na gaishe da sarakuwarta ta fuska a sake Inna ta amsa.

"Ina yaushe kika zo?"cewar Laila bayan ta fita ta wanke fuskarta da baki,Inna tayi murmushi tace "tun ɗazu mana na zo na tarar ki na barci shine na ɗora maku tuwon shinkafa,ga miyar can bisa wuta"sunne kai Laila tayi ta na wasa da zoben hannunta tace "na gode"abun ma dariya ya baiwa Inna dan ta san kunyarta ne ta ke ji.

"Tom ni zan koma gida ki tabbatar dai ki na tsarki da ruwan bagaruwa dan babu wani sirri da ya fi ta karƙo wajen gyara, sannan ki kasance cikin ƙamshi a ko da yaushe ta hakan ne za ki ciri tuta gun miji dan a duk inda ya ke yaji irin turaren sai ya tuna da ke "kai Laila ta jinjina tare da yiwa Inna godiya.
Wanka Laila ta shiga ta na mai ɗaukar ƴar butarta ta ruwan bagaruwa wacce ya ci ace duk macce ta tanade ta domin kula da kanta ba wai shaye-shayen maganin mata ba uwanda a ƙarshe za su kai su baro.
Ta na wanka Muntari ya shigo dan tunda aka yi auren nan ya fidda ranakun da zai rinƙa zuwa kasuwa da wanda zai rinƙa jigila-jigila,ƙamshin miyar da yaji kawai ya tabbatar mashi da Inna ta zo.
A kunyace ta shigo daga ita sai ɗaurin ƙirji sam ba ta tsammaci dawowar shi ba,da sauri ta shige ƙurya ɗaki ganin kallon da ya ke yi mata shi abun ma dariya ya bashi.



A ɓangaren Asabe kuwa ganin aikin boka ya ƙi ci yasa mahaifiyarta ta fara shiryata da haɗaɗun kayan mata na sha da na tsugunnu,wasu ma ba ta san amfanin su kawai dai bata take dan ƴarta tayi zarra yaji ya tsani Laila dan maganin mata ne mai sirki da sihiri.
Asabe ce luluɓe cikin zanen gado ta buɗe ƙafafu da baki yayinda sai ambaton sunan Muntari ta ke,ta na gamawa Ayya ta bata buta mai cike da wasu hakukuwa kafin kuma ta fito ta dama mata wata gumba cike da jin daɗi Asabe ta shanyeta tas.
Bayan sallah la'asar sai ga Muntari ka na ganin shi ka san bai cikin nutsuwa,gaishe da Ayya yayi ta amsa fuska a sake ƙasan zuciya kuwa cewa take "ɗan batta uba ai gashi ka zo ba ka shirya ba". Muntari ya sosa ƙeya yace "Ayya ina ita Asaben?"da murmurshi tace "ta na cikin ɗaki ka wuce mana"cike da kunya ya wuce a kwance ya tarar da ita ta na latsa wayarta sha kiɗinka baƙauye😹.
Sallama yayi mata a karo na biyu ta sheƙe shi, murmurshi yayi a zuci yace "Asabe ba dai jan aji ba nan fannin kawai kika ƙware"mayafinta ya ja ya na leƙen fuskarta ta fizge kayanta tare da hararar shi,bai damu ba sai ma kwantowa da yayi ta na shirin magana ya haɗe bakin su na tsawon second 5 ya zare.
"Bala'i"Asabe ta furta ƙasan ranta saboda jin duk illahirin jikinta ya amsa wanda bai rasa nasaba da kayan matan da Ayya ke ɗura mata.
Cikin fuzgar da numfashi yace "babyta please ki koma ɗakin ki wannan horon ya isa haka duk kin sa na susuce,ungo ta wannan kuɗin cefane ne ki je gida dan Allah"bai jira cewarta ba ya aje kuɗi masu yawa tare da fita ya yiwa Ayya sallama.
Da murmurshi ta ke ƙirga kuɗin Ayya ta shigo ta zauna ta na kallonta,sai da ta gama ƙirgawa Ayya ta amshe kuɗin ta na cewa "yanzu ai sai aje abiya Hajiya Tuwa tunda aiki yayi daga nan sai ta baki wasu kayan uwanda za ki cigaba da amfani da su in kin koma"Asabe ta ɓata rai tace "Ayya kuɗin cefane ne fah" "eh na sani ai yanzu abinda za'a yi ki ɗauki zakara guda cikin keji a yanka sai ki yi maku romo ku ci da burodi ko ya kika gani"fuska Asabe ta ɗan saki tace "to Ayya amman ki ɗan bani wani abu daga ciki"Ayya ta ƙulle kuɗi ga haɓar zane tace "matsalata da ke Asabe son kuɗi ana son yi maki gata amman ba ki gani,doli sai an kashe kuɗi in ana so kuɗi su fito na san tabbas sai ya baki kyauta dan kayan Hajiya Tuwa masu kyau ne"babu yadda Asabe ta iya haka ta miƙe ta nufi kejin kaji ta kamo wani ƙaton zakara tare da baiwa almajirin gidan wani maƙwabcin su ya kai mata shi mafiga aka gyara mata shi cikin ƙanƙanan lokaci.


Gidan Inna ta wuce ko sallama babu ta shige ɗakinta,murhu da itace ta fiddo ta ɗora girkinta.
Jin motsi ne yasa Inna fitowa da ta na cewa "ikon Allah wa ke yi min daka cikin gid..."turus tayi ganin Asabe na dadaka atarugu da tafarnuwa.
Babu kunya Asabe tace "ina wuni Inna?"cikin sakin fuska Innar ta amsa ta na mai komawa ɗakinta.
Da sallama Ayya ta shigo gidan Inna ta amsa nan suka shiga gaisawa kafin daga bisani ta ɗora da cewa "to ga dai Asabe nan ta dawo ɗakinta ɗazu ni ke yi masu faɗa ita da Muntarin,zaman aure ai sai haƙuri" "uhumm"kawai Inna ta ce kafin Ayya ta miƙe ta wuce ɗakin Asabe wacce ta fito daga wanka ta na shafa mai,da fara'a ta tarbi mahaifiyarta ta.
Ayya ta kwanto wani garin magani cikin ƙasa da murya tace "wannan cikin abinci za ki saka mashi ki tabbatar ya ci,wannan kuma da zuma za ki kwaɓa shi ki matsa in zaki kwantawa sai kuma ki mitsitsike shi cikin tafin hannu kice na lashe Muntari😹"karɓa Asabe tayi ta na godiya.



Bayan sallah isha'i Muntari ya shigo ɗauke da kwanon abinci wanda duk dare Laila ke fiddawa Inna,bayan ya aje ne babu kunya ya yi mata sallama ya wuce ɗakin Asabe ba tare da ya yiwa Inna maganar dawowarta ba.
Ƙamshin turaren huta ke ta tashi da murmurshi kamar gonar auduga ya shiga ɗakin,sai da Asabe ta ja aji sannan ta amsa sallamar.
Ruwa masu sanyi ta bashi tare da yi mashi sannu da zuwa ya amsa ya na murmurshi,abinci ta gabatar mashi wanda ya sha maganin da Ayya ta kawo mata cike da zaƙuwa ya fara cin naman kajin ya na gamawa da burodi har ya ƙoshi.
Ruwan wanka ta kai mashi yayi,ko ya shigo da mamaki ya ke kallon Asabe wacce ta shirya tsaf cikin kayan barci wanda tunda suka yi aure bai taɓa ganin haka ba.
Da ɗan saurin shi ya zo zai rungumeta ta ja da baya tace "Muntari miye haka ai ka jira har ƙafa ta tsana na san halin ka kai ba kada sirki"kafin yace wani abu yaji maganar Inna a bakin ƙofa "Zo ka rufe gida ni zan tafi gun waccan baiwar Allah na tayata kwana"da "to" ya amsa Inna na jin haka ta fice ta nufi gidan Laila.
A zaune ta tarar da ita ta saka abinci a gaba ta kasa ci,jin sallamar Inna ne yasa tayi saurin goge hawayen da suka zubo mata.Murmushi ta ƙirƙiro tace "Inna ce ina wuni?""lafiya lau Lailatu ya gida " "alhamdullah"ta amsa a takaice kafin ta tsiyayawa Inna ruwan sanyi nan suka fara taɓa hira wacce rabinta duk nasiha ce Inna ke yi mata.


Tamkar Muntari ya taka rawa dan murna jin Inna ta bar gidan za ta kwana gun Laila,da sauri ya rufo gida ya dawo.
Wata wawura ya yiwa Asabe ya na sauke numfashi kafin ya ɗauke ta ya dire a kan gadonta da ya sha sabuwa drap,ƙamshin da jikin Asabe ke yi shi ya ƙara dagula mashi lissafi ya fara romance ɗin ta Asabe yau duniya ta dawo mata sabuwa jinta ta ke tamkar wata amarya a zuci ta ke cewa "dama haka ake ji in an sha maganin mata,hum ashe na cuci kaina da ban farga ba ni ke zamanni na hakanan"soyayya lubayya yau kam Muntari ya gamsu iya gamsu kyaututtukan da ya yiwa Asabe ba su lisafuwa ciki kuwa har da gidan da suke ciki😹.
Gefe ya koma ya na mayar da numfashi tare da ƙura mata ido sai ya ga tamkar an sauya mashi Asaben shi,yadda ya jita da ni'ima kamar lokacin da ta na amarya ga wani sihirtacen ƙamshi da ta ke fitarwa,ta na ƙoƙarin tashi ya ruƙo hannunta tare da mayar da ita yayi mata rumfa( Ni kuma nace bari nayi gaba tunda na ga alamu abun ba mai ƙarewa ba ne su Muntari an samu yadda ake so😹Ni India zan koma)



***India

A gaggauce ya ke shiryawa yayinda da Daddy, Oga Darma da William ke gefen shi ko wane da abinda ya ke gaya mashi.
William yace "please ka bari na raka ka kaji?"Dawood ya kalle shi yace "no kayi zaman ka dama ba wata isassar lafiya ne da kai ba in uwannan Mayun suka gan ka ka da fitowa da ranka ai sai ta"murmushi William yayi yace "to ai kafi ni kyawu kuma fah naji sauƙi ban jin komi yanzu kawai raɗaɗi ne marar cutarwa"dariya duk suka yi mashi Daddy yace "William ina ka taɓa ganin an ce raɗaɗi kuma ace bai cutarwa?kawai kayi haƙuri ya tafi shi ɗaya in sha Allah zai dawo cikin ƙoshin lafiya kuma da nasara" Oga Darma ya karɓe zancen da cewa "tabbas domin kuwa Dawood ɗina jarumi ne"murmushi kawai Dawood yayi yace "ok zan tafi sai na dawo" "fatan nasara"suka faɗa a tare Oga Darma na seta allon sihirin shi izuwa Masarautar Mayu.

A hankali ya ke taka step ɗin yayinda ya ke gyara zaman agogon hannun shi,ƙafar fita ya nufa yayi tamkar bai ganta ba.Da gudu taje ta rungume shi tare da fashewa da kuka,lumshe ido ya na jin zuciyar shi na dokawa a fili ya furta "ya Allah"domin tun tuni ya yarda Leemat ce raunin shi tun lokacin da ta harare shi haɗe da yi mashi gwalo ya fita harakarta ya na shareta cikin ƙarfin hali.
Hannuwanta ya riƙe uwanda ta zagaye cikin ya da su kafin ya juyo ta izuwa gaban shi,ido ya tsura mata yadda ta ke zubar da hawaye kamar wata ƙaramar yarinya.
Rasa abinda zai yi ya yi kawai sai ya kai bakin shi kan nata ya na mai tura tongue ɗin shi caraf ta riƙe ta shiga tsutsa,wani irin azababen sonta ne ke fuzgar shi mai haɗe da feeling ba dan ya so ba ya cire bakin shi ya maida duban shi gareta sai ajiyar zuciya ta ke saukewa.Ba tare da yace mata komi ba ya raɓa ta gefenta ya wuce,babur ya hau tare da saka hular kwano ya bashi huta.Wawuyar ajiyar zuciya ta sauke ta na juyowa suka haɗa ido da Maman da Momy uwanda suke tsaye suna kallon ikon Allah😂,sunne kai Leemat tayi ta na wasa da yatsunta "ki je ki ɗauki David kar yayi kuka mu za mu shiga kitchen"cewar Mama ta na murmurshi.
Sumi-sumi ta wuce ɗaki ta tsaya kallon little Dawood wanda ake kira da David,har ƙasan ranta ta ke jin son yaron ko dan ya na da sunan masoyinta ne oho.


Tun kafin Dawood ya ƙaraso jama'ar Masarauta suka tsaya cirko-cirko kamar wasu zakaru suna kallon shi,kashe babur ɗin yayi ya na kallonsu.Maza da mata ne yara da kuma ƙanƙana nasaru,baƙar fata da kuma larabawa kowane ya na haɗiyar yawu wanda kallo guda za ka yi masu ka gane sun amsa sunan MAYU.
Ba tare da ɗar ko shakka ba Dawood ya cire hular kwanon ya nufi hanyar da ya ke tunanin ita ce za ta sadaka da cikin Palais ɗin.
Wasu dakaru majiya ƙarfi ne suka zaburo tare da tare Dawood, murmurshi yayi ya rikiɗe ya koma kalar su ya fara yi masu magana ta ido kamar yadda Mayu kan yi dan ba kowane lokaci suke magana da baki ba.
Da sauri suka bashi hanya suna wasa baki ɗaya daga cikin su yace "ashe duk mu ne bari nayi maka iso gun shugaba"murmurshi Dawood yayi ya na mai take mashi baya har suka isa cikin wani ɗaki inda anan ne faɗar SARKI DANEE SHUGABAN MAYU ta ke.
Ido cikin ido suke kallon juna kafin Oga Danee ya saki murmurshi ya yiwa Dawood alama da hannu ƙaraso mana,ƙarasawa yayi ya zo daf da shi miƙewa DANEE yayi yace "maraba da shigowa Masarautar Mayu,masarautar da in aka shigo ba'a fita hahaha"ya ƙarashe maganar ya na kecewa da wata irin dariya, Dawood ya tai yayi magana sai ganin wata sarƙa yayi ta dabaibaye shi ta na mai yin sama da shi.....



*Kuyi haƙuri a gaskiya ban samu damar yi maku Posting sau biyu a rana saboda yanayin ciwona da ya tashi,banda lafiya ina fama da Jinnu ina barar addu'ar ku Allah ya bani ikon yaƙarsu su ida ficewa daga jikina*🙏🏻


Comment and share Please

Jikar Rabo ce 😎
*ƊAN DABA*
```love
and
romantic story

``` _MRS SADAUKI_ 💫

*Dedicated* to My Babbar Yaya Nafissa Laouali Rabo🥰

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀️

____________________
BISMILLAHI RAHAMANI RAHEEM

*BUY MTN DATA AT AFFORDABLE PRICES*👇🏽

*500MB* 200

*1GB* 300

*2GB* 600

*3GB* 900

*6GB* 1800

(CHECKING BALANCE * 461*4# )

VALIDITY : 1 MONTH

For more enquiry Call or Whatsapp this number: *08066268951*

*PAGE 49-50*


Ƙoƙarin fita ya ke daga ragar amman ya cuttura ya na shirin fara karanta formules ɗin tsafi wasu manyan ƙatti suka zo suka ja shi,babu yadda Dawood ya iya doli ya bi su izuwa wani ɗaki mai shegen duhu.A ciki suka jefa shi suka rufe ƙofar da wani narkeken kwaɗo,tsafi da siddabarun duniya Dawood yayi amman ya ƙi yi abinda kuma bai sani ba Palais ɗin Oga Danee arnan aljannu ne cikinta uwanda suka sha sihiri shekaru dubanai da suka wuce da zarar mutum ya taka ƙafar shi ciki to fah shikenan asirin jikin shi zai fita ne ya koma ga uwannan aljannu.
Su Oga Darma da ke can suna kallon allon sihiri a gaban idon su wani abu kamar ruwa ya shiga fita daga jikin Dawood ya na shigewa cikin ƙarƙashin ƙasa, wannan ya dugunzuma hankalin su ashe duk yadda suka yi tunanin Oga Danee ya wuce nan.
Miƙewa William yayi yace "Ni zan je na tawo da shi ba zan bi ta ƙofa ba"Oga Darma ya girgiza kai yace "zuwan ka ba shine solution ba domin kuwa in ka shiga ba ta ƙofa ba doli a ta ƙofa za ka biyo domin an shinfiɗawa Palais ɗin matakan tsaro ta yadda ba'a abu biyu duk waje ɗaya"William yace "kar ku damu in dai na samu na fito da shi fitowar bai wuya"Daddy ya ɗaga masu hannu alamun su dakata ya yi tunani.
Allon sihirin ya duba can ya ɗago kai ya kalle su yace "da buƙatar mu canza salon farauta, William ka bi ta ɓarauniyar hanya ka kuɓutar da Dawood mu kuma za mu je mu tsaya tsakiyar farfajiyar Masarautar mu janyo hankalin Danee ta yadda zai fito ya na fitowa kawai sai Michel yayi cikin shi ya cije shi ta yadda jini zai fito ka ga jinin na taɓa bakin Michel zai dawo a mutum sauran sihirin da ke jikin shi kuwa sai ya wuce Palais dan ya fita daga gare shi ya koma gun aljannun"ko da Daddy ya faɗi haka habshi Michel yayi wanda ke gefen su zaune alamun jinjinawa basira irin ta Daddy,ba su wani ɓata lokaci ba kuwa duk suka fita Michel na gefen su cikin mota.
Ana zuwa bakin Masarauta William ya ɓace ɓat bai dira ko ina ba sai ɗakin da aka rufe Dawood,ɗakin ne ya ɗauki haske kamar an sa ampoule nan kuwa duk cikin shirin William ne.Da murmurshi ya rungume ɗan uwan shi tare da tambayar shi ya aka yi ya shigo,nan William ya shaida mashi plan ɗin su ba'a kau ɗau lokaci ba suka jiyo muryar Oga Darma ya na ƙwalawa Danee kira.

A harzuƙe Danee ya fito dan ko a mafarki yaji murya Darma zai gane ta,fitowar shi a hasale niyyar shi ya lashe kurwar shi kawai sai jin yayi an yi tsaraf da ƙafar shi tare da gantsara mashi cizo har sai da ta fasa kafin mutanen gun su farga tuni Michel ya zama mutum tare da rugawa da gudu ya shige Palais 😂nan kuwa ya ɗau wani irin caji sihiri ya fara fita jikin shi har ya dawo daidai ya shiga malaya amai baƙi ƙirin.


Danee na ganin Auwal ya rugo da gudu da niyyar rungumar shi sam ya manta da ciwon ƙafar shi, kallon-kallon suka tsaya yi Danee ya fashe da kuka yace"Auwal kai ni ke gani ko kuwa idona suke min gizau?"kafin yace wani abu sai tsinkayo muryar Dawood suka yi ya na karanta Ayatul Ƙursiyu wani irin ihu Danee da duk wani maye na ɗakin suka shiga yi saboda maitar su ta aljannu ce mai sirki da sihiri,jin ihun ne yasa su Darma saurin ƙarasawa cikin Palais tuni suma sihirin jikin su ya tsiyaye ganin haka ne suma suka shiga karanta Ayar Allah da ƙarfi William dai ɗan kallo ne dan bai san komi ba dangane da addinin Musulunci.
Ƴan jarida tuni sun kawo ayari suna ɗaukar rahota kan kace wani abu tuni duniya ta ɗauƙa "Ɗan majalisa Darma ya tunkari Masarautar Mayu wacce ta hana jama'a gari shaƙat yau dai jarumin ɗan majalisar mai kishin ƙasa yayi gaba da gaba da su dan kawo ƙarshen su tuni kuma ya fara cin galaba ga yadda Mayu sai ihun ceton rai suke yayinda a wani sashe na masarauta ta fara ci da wuta".
Ganin haka ne su Dawood suka fice daga Masarauta suka tsaya baiwa ƴan jaridu amsoshin tambayar su, Dawood ya fara yin magana "eh mun tunkare su ne da jagoranci Darma saboda yace ba zai karɓi shugabanci ba alhalin mutanen shi na kuka da irin mace-macen da ake yi a gari ba kuma duk a dalilin masarautar nan ce wadda *ƊAN DABA* Danee ya kafa"nan dai aka cigaba da yi masu tambayoyi suna amsawa.

Cikin awani huɗu Masarautar Mayu ta zama labari tamkar ba'a yi ta ba,wasu sun yi rai tare da rauni wasun su kuma sun mutu Oga Danee an samu an fita sai abun mamaki ƙafar shi ɗaya ta koma ta kare wacce Michel ya ciza.
A tsanake cike da murna suka koma gida,Momy wacce gabanta ke faɗuwa tun ɗazu suka yi ido huɗu da Auwal mijinta cike da murna ta je ta rungume mijinta alamun sun nuna ba ta ma san tayi hakan ba dan daga baya kuma sai taji kunya dariya duk suka yi mata.

Washegari tun da safe Dawood ya fita bai dawo ba sai wuraren sha biyun rana,a zaune ya tarar da familyn su na hira Leemat sai zuba ta ke

Please Login or Register in order to submit comment